Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ita kuwa Mazalish sai da ta ci kukanta ta ƙoshi, sannan ta ci gaba da tafiya a sararin samaniya, tana đauke da su Jafar a gadon bayanta.
Ba ta gushe tana tafiya ba, sai bayan sun shuɗe sa'a bakwai, sannan ta sauko ƙasa suka a tsakiyar wani irin jeji mai ababan al'ajabi kala-kala.
Bayan su Jafar sun sauka daga kanta, sai ta girgiza ta dawo cikakkiyar siffa irin ta mutane sosai. Mazalish ta dubi su Jafar har yanzu hawaye na zuba a idanunta tace, "Yanzu na dawo cikin ainihin halitta ta siffar da kuka ganni da ita ɗazu ba komai ba ce face sirrin tsafi."
Yayin da Mazalish ta zo nan a zancenta, sai Jafar ya dubeta yace, "Yake 'yar uwa ya akai kika zama mutum kamar mu alhalin kin kasance jinsin mayu?"
Nan Mazalish ta basu labarin yadda aka yi mahaifinta ya cire mata maita da kuma yadda ya bata rabin ƙarfin damtsensa da rabin tasirin tsafinsa.
Jafar ya sake duban ta ya ce, "To mene ne dalilin da yasa kika ceci rayuwarmu kuma har kika harbi mahaifinki da hannunki?"
Koda jin wannan tambaya sai Mazalish tayi ajiyar zuciya sannan tace, ''Ba wani abu ba ne ya sa na ceci rayuwarku face hujjoji guda biyu. Huja ta farko itace mahaifina ya bayar da ni ga wani bafadensa wanda na tsana fiye da komai a rayuwata.
Kuma na san cewa idan na aure shi har na sami ciki dole ne maita ta dawo jikina,ni kuwa da na zama maiya irin mahaifina da mutanensa gwara na rasa rayuwata. Hujja ta biyu ita ce kimanin shekaru biyar baya na taba ziyartar wani boka a wata babbar ƙasa na sanar da shi cewa ni kam na gama kewaye wannan duniya tamu amma ban ga wani namiji dana ji ina ƙaunarsa a zuciyata ba, har na iya aurensa, shin ina ne zan ga wanda zai iya aurensa? Lokacin da bokan ya ji wannan tambaya tawa sai ya ƙyalƙyale da dariya,sannan ya yi nuni da hannunsa izuwa ga wani ƙaton madubi sai ga hoton wani kyakkyawan saurayı yana gagarumin yaƙi tare da wani hamshaƙin barde kuma matsafi, a cikin wata duniya dabam ba irin wannan da muke ciki ba. Ina ganin wannan saurayı na ji ina mutuwar sonsa.
Boka Arjiwala ya dube ni yace, "Ya kika ga wannan saurayi kina sonsa?" Cikin tsananin murna nace ai tunda nake ban taba jin SO ya shiga zuciyata ba sai akan wannan saurayi, ya kai wannan boka maza ka sadani da duniyar wannan saurayi ni kuwa na saka maka da duk abin da kake buƙata iya tsawon rayuwarka. Boka Arjiwala ya sake bushewa da dariya yace, "yake wannan 'yar sarki ki yi sani cewa ba ni da ikon kai ki duniyar da wannan saurayi yake amma idan kika yi haƙuri nan da shekara biyar masu zuwa waɗansu mutane za su zo daga can kuma sanadiyar sune za'a yi gagarumin yaƙi tsakanin mutanen ƙasar sarki Azbir da mutanen ƙasarki,zaki rabu da mahaifinki da ƙasarki da kuma wannan duniya amma idan kina son ki je ki ga wannan saurayi wanda zuciyarki ta kamu da son sa sai kin ceci rayuwar waɗannan baƙin mutane, ki sani cewa hanyar da suka bi suka zo hanya ce mai matuƙar wahala, domin ta cikin wani sihirtaccen littafi ne da ake kira KUNDIN TSATSUBA ba kuma za su fita daga cikin sa ba,su koma duniyar su sai bayan shekara ashirin daidai. Za su yi ta ziyarar duniyoyi iri-iri ne suna shiga masifu kala-kala."
Lokacin da boka Arjiwala ya zo nan a zancensa sai na dube shi cikin matuƙar damuwa nace, "Ya kai wannan boka ka yi sani cewa koda zan tsufa tukuf a yawan neman wannan masoyi nawa ba zan kasa ba. Zan jira waɗannan mutane nan da shekara biyar har su zo kuma zan jure kowacce irin masifa da zamu tunkara a cikin littafin KUNDIN TSATSUBA. Abin da nake so da kai shi ne kawai ka sanar da ni sunan wanann saurayi. Boka Arjiwala yayi murmushi yace, "sunansa Hubalru, kuma ya kasance ma'abocin wani addini da ake kira Musulunci. A yanzu haka yana tsakiyar soyayya da wata kyakkyawar mace wai ita gimbiya Sima." Koda jin wannan batu sai kishi ya turnuƙeni nace, "wacece kuma gimbiya Sima? Shin ta fini kyaune ko kowa mahaifinta yafi nawa ƙarfin mulki?"
Arjiwala ya ce ba ta fiki komai ba, amma za ku iya yin kunnen doki a fagen kyau. Babu ruwana da ita abin da na șani kawai koda zan zama baiwa mafi ƙasƙanci sai na auri Hubairu. Nan take na kawo alheri mai yawa na baiwa boka Arjiwala sannan nayi masa bankwana na tafi. Daga wannan rana na cigaba da jira har izuwa yau ranar da na sadu da ku."
Yayin da Mazalish ta zo nan a zancenta sai Jafar ya dubeta cikin mamaki yana mai tunani.
Mazalish ta dube shi tace, "Tunanin me kake yi?"
Jafar yace, "Ai sunan da kika faɗi na saurayin da kike so nake tuno mai shi. Tabbas mun san waye Hubairu kuma mun yi hulɗa da shi."
Koda jin haka sai murna ta kama Mazalish tace, "Ba ni labarinsa na ji."
Jafar yace, "Haƙiƙa ya cika kyakkyawa kuma cikakken jarumi ne, domin shi ne ya taimake mu ya kashe sarki Lu'umanu har muka samu damar sato wani aljani wai shi Markahul sabus wanda ya đauko mana kubar MIFTAHUL ZARBIL wacce da ita ne muka buđe littafin KUNDIN TSATSUBA. Littafin daya zame mana alaƙaƙai kuma shine sanadin zuwan mu wannan duniya taku."
Koda jin haka sai Mazalish ta dubi Jafar cikin rashin fahimta ta ce, "Ban gane wannan jawabi na ka ba?"
Jafar ya nuna Mashrila ya ce, "Kin ga wannan a cikin KUNDIN TSATSUBA muka haɗu da ita,kamar yadda muka haɗu da ke."
Nan take Jafar ya kwashe labarinsu kaf tun daga farko, har ƙarshe ya sanar da Mazalish. Bayan ya gama ne ta cika da tsananin mamaki, kuma ta ɗauki alƙawarin tafiya tare da su har a gama karanta shafukan KUNDIN TSATSUBA, don ta haɗu da masoyınta jarumi Hubairu bin Mas'ud wanda ba ta taɓa ganinsa ba sai a madubin tsafi kusan shekaru biyar baya.
Bayan Jafar ya gama baiwa Mazalish labarinsu, sai suka miƙe gaba ɗaya suka nausa cikin wannan jeji suka yi ta tafiya ba tare da sanin inda suka dosa ba. Kwatsam sai suka ga wata rijiya,dama ƙishirwa ta addabe su.
Ita dai wannan rijiya tsohuwa ce ainun kuma an rufe ta da ƙaton murfin ƙarfe. A bakinta an yi rubutu da ruwan zinare kamar haka.
"BABU MAI BUƊE WANNAN RIJIYA YA SHA RUWAN CIKINTA SAI BAƘIN DA SUKA ZO DAGA WATA DUNIYAR."

Topah,ko mai faru???
Anan zamu dakata,sai wani karon idan Allah ya kaimu,fatan alheri.
Ina muku fatan alheri da nasara.Matsatsubi 1
Typing:-Ahmad Munir Muhammad
Posting:-Ahmad Munir Muhammad
Part G

A baya mun tsaya ne a inda:-
Kwatsam sai suka ga wata rijiya,dama ƙishirwa ta addabe su.
Ita dai wannan rijiya tsohuwa ce ainun kuma an rufe ta da ƙaton murfin ƙarfe. A bakinta an yi rubutu da ruwan zinare kamar haka.
"BABU MAI BUƊE WANNAN RIJIYA YA SHA RUWAN CIKINTA SAI BAƘIN DA SUKA ZO DAGA WATA DUNIYAR."

######
Koda gama karanta wannan jawabi sai Jafar ya dubi Yelisa da Gulzum yayi murmushi ya ce, "Ai domin mu aka yi rijiyar nan. Yakai Gulzum maza ka buɗe mana mu sha ruwa ko ma huta da ƙishirwa."
Cikin fushi Gulzum ya ce, "Waye bawanka har da za ka bani umarni na bi?"
Koda jin haka sai Yelisa ta dakawa Gulzum tsawa, ta ce, "Daga yau umarnin Jafar umarnina ne,maza ka yi abin da yace."
Cikin hanzari da biyayya Gulzum yasa hannu ɗaya ya ɓanɓare murfin rijiyar da ƙarfin tsiya. Yana yaye shi wata irin iska mai tsananin ƙarfi tayi fitar burgu daga cikin rijiyar ta zuƙe Jafar,Yelisa, Gulzum, Mashrila da Mazalish, ta bar sarki Azbir shi kaɗai, su ka zama 'yan ƙanana suka shige cikinta, sannan murfin rijiyar ya koma ya rufe kansa. Azbir ya fashe da kuka.
Su Jafar dai ba su tsinci kansu a ko'ina ba sai a cikin ainihin tasu duniyar gaban KUNDIN TSATSUBA.
Har yanzu shafi na goma sha biyu ne a buɗe. Koda Mazalish ta miƙe ta ganta a cikin wata sabuwar duniya sai ta kama kalle-kalle kamar ɗan ƙauyen da bai taɓa shigowa birni ba.
Wannan shi ne abin da ya faru ga su Jafar bayan sun shiga shafi na goma sha biyu a cikin KUNDIN TSATSUBA.

*****************************************

Al'amarin su Jarumi Hubairu kuwa lokacin da sarki Hudais ya haɗa shi da manyan dakarun Musuluncin nan don zuwa gidan bokanya Samaratu ɗauko gimbiya Sima wacce har yanzu tana nan a kwance tana barcin tsafi, saura 'yan sa'o'i kaɗan ta rasu in dai ba a tashe taba daga barcin. Sai suka ƙara himma wajen gudu da sauri a cikin samaniya.
Ba su isa gidan Samaratu ba sai da ya rage saura sa'a đaya da rabi gimbiya Sima ta rasa rayuwarta. Da zuwa suka iske hadiman Samaratu a shirye suna tsaron gidan. Da yake an fi ƙarfinsu. Nan da nan aka kashe su a cikin abin da bai wuce daƙiƙa ɗari da ashirin ba.
Daga nan su Hubairu suka shiga neman inda gimbiya Sima take. Ɗaki-ɗaki, lungu-lungu, sako-sako,nan ma sai da suka shafe sa'a guda da kusan rabin rabi na sa'a sannan suka risketa a cikin ɗakin tsafin Samaratu kwance bisa wani gadon ƙarfe wanda wata irin tsafaffiyar wuta ta kewayeshi sama da ƙasa. Hubairu ya ruga da gudu don isa gareta,koda yaje daf da gadon sai ja da baya da sauri saboda tsananin zafin wannan tsafaffiyar wuta domin ji yayi kamar naman jikinsa zai narke, koda ganin haka sai wani dakare waishi labahan yace, "ya kai Hubairu shin kamanta cewa mun shigo gidan ma'abota tsafine,lallai bazaka iya dosar wánnan gado ba face da neman tsari daga Ubangiji." Sa'adda Hubairu ya ji wannan batu sai kawai ya fara karanta addu'o'i,kai tsaye ya nufi wannan gado. Yayin da ya tunkare shi sai yaji zafin wutar na raguwa ya yin da yake kusantarsa, a hankali sai wutar ta rinƙa zuƙewa da kanta tana ƙanƙancewa,koda ya je daf da gadon kuwa sai wutar ta ɓace gaba đaya. Ba tare da ɓata lokaci ba Hubairu ya soma karanta addu'ar nan wacce sarki Hudes ya bashi yana tofawa a jikin gimbiya Sima.
Yana gama tofawa kuwa sai hannayenta da ƙafafunta suka fara motsi, daga can kuma sai idanunta suka buɗe a hankali. Cikin firgici ta miƙe zaune zumbur tana mai kalle-kalle, koda taga jarumi Hubairu a gabanta sai tayi hamdala ta rungumeshi cikin farin ciki sannan tace "ya kai masoyina ina wazirina Kuddaru,ina su Jafar, wai shin nan ma a ina muke, su waye waɗannan a tare da kai?" Ya yin da jarumi Hubairu ya ji wannan tambaya, sai ya janye jikinsa daga nata suka fuskanci juna sannan yace, "yake abar ƙaunata kiyi sani cewa yau kwananki casa'in da huɗu kina barci sai yau Allah ya nufa kika tashi, su kuwa su Jafar da wazirinki Kuddaru bansan a inda su ke ba,nima ina da sauran shan ruwa a duniya shi yasa muka sake saduwa." Cikin tsananin mamaki gimbiya Sima ta tattaro nutsuwarta ta ƙurawa Hubairu idanu ta ce, "Ban gane wannan batu na kaba.
Ya akayi nayi barci har na tsawon kwana casa'in da huɗu aini tsammani na duk bai wuce suman 'yan daƙiƙu bane." Hubairu ya yi murmushi sannan ya kwashe labarin duk abin ya faru garesu shi da waziri Kuddaru lokacin da sarki Lu'umanu yasa aka đauresu don ya hallakasu har mahaifinsa Mas'ud da aljani Abtarul Hudes suka kawo muşu ɗauki ya kawo izuwa lakacin da suka yi gumurzun faɗa shi da sarki Lu'umanu har a karo na biyu da yadda ya koyi yaƙi a wajen sarki Hudes har ya sami labarin inda take yazo yanzu don ceton rayuwarta. Koda Hubairu yazo ƙarshen labarinsa sai farin ciki ya lulluɓe gimbiva Sima ta fashe da kuka ta sake rungumeshi tana mai cewa, "da yardar Allah wannan karon babu mai rabamu har sai mun zama miji da mata." Sima ta ƙara da cewa, "kai amma fa lamarin sarki Lu'umanu akwai al'ajabi. Yanzu ashe bai mutu ba yana nan a raye. Ni fa a gaban idanuna ka karya masa wuya. Tabbas wannan mutum ya cika shaiɗani kuma hatsabibn matsafi."
Hubairu yace, "ƙwarai kuwa ai abin da na fahimta shine duk wannan artabun da nayi dashi ba dashi bane da wani aljanin dabam nayi. Gangar jikin tasa ce kawai amma ba ruhin saba ne. Yake masoyiyata ki sani cewa yanzu bamu da wani lokaci na doguwar hira zaifi kyau mu hanzarta tafiya."
Kafin gimbiya Sima ta buɗe baki kawai sai suka gaba đayan ginin ɗakin da suke ciki an daukeshi can ƙas an barsu a tsakiyar fili tamkar a ɗauke murfin tukunya a ajiye a gefe guda.
Kawai sai ganin waɗansu jibga-jigan aljanu kimanin su miliyan ɗaya sun yi musu ƙawanya kowannensu riƙe da mugun makami.
Ba zato ba tsammani kuma sai ga sarki
lu'umanu bisa dardumar tsafi ta sauke shi daf da jarumi hubairu suka fuskanci juna sai ya murtuke fuska yace, "ya kai babban maƙiyina kayi sani cewa babu inda zaka shiga a cikin duniya nan ka ɓace mini,ka tuna cewa munyi gagarumin faɗa ni da kai har sau biyu ko kuma nace sau uku munyi kare jini biri jini, ina tabbatar maka da cewa wannan karan na zo da cikakken shirin irin wanda ban taɓa yi ba don haka dole ne naga bayanka.
Tabbas yau sai nayi gunduwa-gunduwa da sassan jikinka.
Ita kuwa masoyiyar taka dole na mallaketa ko tana so ko bata so."
Jarumi hubairu ya dakawa lu'umanu tsawa yace, "kai tsohon maƙiyin ALLAH babban mushiriki ma'abocin fasiƙanci domin ina tare da ubangijin musulunci addinin da ya zamo shugaban addinai kuma tafarkin gaskiya.
Duk wanda ya riƙe shi yafi ƙarfin masu yin waninsa da izinin Allah zan samu rinjaye akanka kuma da sannu zamu ƙarar da ire-irenku a doran ƙasa mu kawar da kafirci mu shimfiɗa musulunci ya baibaye duniya gaba ɗaya."
Koda jin wannan batu sai sarki lu'umanu ya sake tuntsirewa da dariya sannan ya dubi waɗannan dakarun aljanu guda miliyan ɗaya waɗanda Shamharu ya tsafance su tsahon shekaru dubu kuma ya tsuma makamansu a tsumin dafi tsawon shekaru dubu yace dasu, "me kuke jira ne da abokan gabarmu maza ku ragargaza su ku ratattakasu banda gimbiya Sima kaɗai har sai sun zama ruɓurɓushi.
Nan take wuri ya yamutse aka fara ɗauki ba daɗi.
Jarumi Hubairu da sarki Lu'umanu kuwa suka ware gefe ɗaya suna zagaya juna da kallon kallo kowennan su na tunanin irin harin da zai kai. Ita kuwa gimbiya Sima an barta ita kaɗai a tsaye a waje guda jikinta na karkarwa don tsananin razana domin tunda take bata taɓa ganin gwarazan aljanu ba irin waɗannan. Su kansu dakarun Musuluncin sun isa abin tsoro ballantana kuma kafiran aljanun guda miliyan đaya waɗanda sun ninka musulman sau arba'in. Nan fa aka shiga bugegeniya da sokaiya, ƙarajin aljanu dana makaman su ya cika dodon kunne. Jini ya rinƙa fantsama tamkar ana ruwan samansa. Haƙiƙa gumurzu ya kasance kare-jini-biri-jini domin kowane ɓangare suna wahala da asara, kuma kowane ɓangare na aiki da abin dogaransu. Su kafiran aljanun nan na tsafi suke tayi da amfani da ƙarfin damtse,su kuwa musulman aljanun suna kiran sunan Allah ne tare da nuna tsantsar jarumtaka.
Duk sa'adda suka ambaci sunan Allah saidai kafiran na ɓace ɓat, sai dai kawai a sake ganinsu tsulum sun baiyana ta hanyan shammace. Idan kuwa suka yi
nasu tsafin sai ƙarfin addu'a ya hanashi tasiri, saboda haka babu abin da yake tasiri a filin dagar sama da ƙarfin damtse da iya yaƙi.
Sarki Lu'umanu da jarumi Hubairu suka ja da baya taku bakwai-bakwai sannan kowannansu ya rugo da gudu don a haɗu a tsakiya riƙe da makami a sama,shi dai Lu'umanu ihu yake yi da kururuwa mai firgita gungun mayaƙa shi kuwa Hubairu babu abin dake fita daga bakinsa face kabbara.
Yayin da suka haɗu a tsakiya takubbansu suka gwaru sai tartsatsin wuta ya tashi ƙasa tayi girgiza gaba ɗaya wajen ya hau tambal-tambal kai kace naɗe ƙasar wajen za'ayi. Tabbas kasancewa manyan baradene suka yi karo, nanfa sukaci gaba da kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama,juriya da bajinta tamkar jikkunansu bana jini da tsoka bane, na karfene. Sai da suka shafe sa'a shida cur suna wannan mugun gumurzu amma ɗayansu bai samu koda karcewa ba a jikinsa ba. Da kansu suka rabu kowa ya ja da baya yana haki da tunanin dabarar da zata fishsheshi. Tabbas ƙarfi yazo daya,mamaki ya kama sarki Lu'umanu ya ce a zuciyarsa yanzu duk irin shirin nan da mai girma Shamharu yayi mana ni da waɗannan dakarun nasa ya tashi a banza kenan,kai lallai waɗannan mutane sun cika hatsabibai kamar yadda sarki Lu'umanu ke wannan tunanı haka shima jarumni Hubairu ya kasance domin ya tsinci zuciyarsa na mai cewa dashi kai waishin su Lu'umanun nan waɗanne irin hatsabibai ne.
Haƙiƙa Allah ya ara musu lokaci amma in ba don haka ba ya za ai ace mun kasa samun nasara a kansu har yanzu duk da cewa kuwa muna addu'o'i da kiran sunan Allah akansu. Bayan kamar daƙiƙa ɗari da tamanin Lu'umanu da Hubairu na kallon juna sai kawai Lu'umanu ya sake yin kukan kura ya tasammasa suka sake garƙamewa da azababben yaki. A wannan lokaci yaƙi ya ƙara tsamari tsakanin kafiran aljanun da kuma musulman masu taimakawa Hubairu domin kusan kowane ɓangaren sun rasa rabin adadinsu, har yanzu gimbiya Sima na nan a gefe guda tana ganin abin dake wakana, tun tana tsaye har sai da ta faɗi ƙasa kuma tun tana iya yin addu'a har sai da ta kasa da saboda ƙura da hayaƙin yaƙi wanda ya turnuƙe wajen gaba ɗaya domin bisa đole ta toshe kunnuwanta saboda ƙarar makamai da ihun mazaje.
Ana cikin hakane Lu'umanu ya faɗo inda Sima ke kwance,sa'adda jarumi Hubairu yayi masa wani wawan duka da ƙafa a ƙirji koda Lu'umanu ya ganta daf dashi sai ya kamobta yasa takobinsa akan wuyanta ya dubi Jarumi Habairu yace in ka ƙara kusantata zan yanke mata maƙogaro. Bisa dole Hubairu yaja da baya kaɗan. Nan take yaƙi ya tsaya cak tamkar babu mayaƙan a wajen,baka jin komai sai nishin naƙasassu waɗanda suka rasa sassan jikin su.
Gawarwaki kuwa gasu nan birjik babu adadi,jini kuwa sai malala yake yana gudu kamar idaniyar ruwa.
Nan take sarki Lu'umanu ya dubi daddumarsa ta tsafi wacce ke tsaye a cikin iska take daddumar tazo gaban sa ta shimfiɗa kanta,kawai sai ya hau kanta tare da gimbiya Sima har yanzu bai cire kaifin takobinsa daga wuyan ta ba kuma ya ƙurawa jarumi Hubairu idanu don tsoron kada yayi wani yunƙuri.
Daddumar tsafin ta bar doron ƙasa ta dira akan ɗaya daga cikin baraden aljanun nasa kawai sai Lu'umanu yayi wani tsafi gaba ɗaya wajen ya gauraye da tsananin duhu cikin abinda bai wuce daƙiƙa ba,kafin su jarumi hubairu suyi wani yunƙuri tuni su sarki lu'umanu sun ɓace kuma sun ɓace ne tare da gimbiya sima.
Cikin hanzari jarumi hubairu ya karanta
wata addu'a sai wannan duhu ya yaye
haske ya baibaye tamkar ba'a taɓa yin
duhu ba.
Koda hubairu yaga babu su lu'umanu kuma babu gimbiya Sima sai hankalinsa ya tashi cikin sauri ya bada
umarni abi sawun su.
Ai kamar an harba kibiyoyi dakarun
musuluncin suka harba jikkunansu suka luluƙa cikin gajimare suna masu
tsananin gudu cikin sahu sahu abin
gwanin ban sha'awa kaikace tsuntsaye ne ke bikin gasar gwada tsere.
Wannan shine abina ya faru tsakanin
su jarumi hubairu da su sarki lu'umanu yayin da aka fafata baƙin gumurzu a gidan bokanya samaratu don ɗaukar gimbiya sima.

*****************************************

Anan zamu dakata, sai wani karon idan Allah ya kaimu.
Fatan alheriMatsatsubi 1
Typing:-Ahmad Munir Muhammad
Posting:-Ahmad Munir Muhammad
Part H

A jiya mun tsaya ne:-
Wannan shine abina ya faru tsakanin
su jarumi hubairu da su sarki lu'umanu yayin da aka fafata baƙin gumurzu a gidan bokanya samaratu don ɗaukar gimbiya sima.

*****************************************

Tun sa'adda aljani durfus ya tafi ya barsu a cikin kejin tsafi bisa sharadin cewa idan sun amince ya zama shugabansu zai dawo ya kuɓutar dasu.
Sai suka kasance cikin halin damuwa
da shawarwari. Markahus sabus ya dubi ummansa bokanya samaratu yace, "yake ummina tun ɗazu boka Jinshan da boka sulbaini sunata faɗin albarkacin bakinsu bisa shawarar da
ya kamata mu yanke akan sharaɗin da aljani durfus ya gindaya mana.
Amma ke kinyi shiru ba kice komai ba
ko kina da dalili?"
Samaratu tayi murmushi tace, "yakai
ɗana kayi sani cewa shifa aljani Durfus bawa ne ga boka sulbaini don haka ya fi saninsa shi ya kamata ya bamu shawarar abin da ya dace muyi."
Koda jin haka sai sulbaini yayi farat yace, "haba Samaratu ai in ki ka faɗi
haka baki yi mini adalci ba. Ki tuna fa
cewa wannan durfus din na yanzu ba shine na da ba wanda na sani ma'ana
ina nufin cewa a halin yanzu aljani Durfus ya taka matsayin da ban sani
ba. Ni ina ganin kawai mu amince da
zama bayinsa in yaso bayan ya kuɓutar damu sai muyi masa tawaye ta hanyar yaudararsa har mu kai ga samun nasara akan SHAMHARU."
Yayin da sulbaini yazo nan a zancen sa sai boka Jinshan ya tuntsire da dariya yace, "wai shin kai ina ka kai tunaninka ne ka ajiye shi har ka manta dashi.
Tsaya na gaya muku gaskiya na gaba
yayi gaba na baya sai labari.
Ai dama ance wanda duk ya rigaka barci dole ya rigaka tashi idan har muna so mu sami nasara akan shamharu dole ne muma mubi irin hanyar da yabi ta neman zama MATSATSUBI."
"Ta yaya zamu zama MATSATSUBAI kaima ka zo da zancen banza abinda ba zai yiwu ba." Markahus sabus ne yayi wannan furuci.
Jinshan yace, "to shi shamharu ya aka yi ya shahara har ma yake bin hanyar zama MATSATSUBIN? Duk abin da yayi ya shahara muma shi zamu yi domin ance sannu ba ta hana zuwa sai dai a dade ba'a jeba."
Koda jin haka sai Samaratu ta sake
tuntsirewa da dariya a karo na biyu tace, "haƙiƙa na fuskanci kuna neman zautuwa shin kun manta ne cewa shi SHAMHARU aljanine ba mutum kamar
ku ba. Ku tuna fa sai da shafe ɗaruruwan shekaru yana tara ilmin tsafi sannan ya shahara.
A cikinku nan waye zai iya daɗewa a duniya kamar yadda ya daɗe?
Waye zai iya zuwa wuraren da ya je? waye zai iya jure irin wahalar da ya sha? Tabbas ni kaɗai ce a cikinku nake da damar zama MATSATSUBIYA sai kuma ɗana gashi tunda mun kasance aljanu kamar boka Shamharu."
Ko da jin wannan batu sai jikinsu boka Jinshan ya yi sanyi suka yi shiru ba su ƙara cewa uffan ba. Markahul Sabus ya yi ajiyar zuciya cikin alamun matuƙar damuwa ya dubi mahaifiyarsa Samaratu yace "ya ke Ummina ki yi sani cewa ni yanzu babu abinda ya dame ni face batun masoyiyata gimbiya Sima. Tabbas idan ban mallaketa ba zan iya haɗiyar zuciya na mutu. Yanzu gashi yau kwananmu biyu a cikin kejin nan aljani Durfus ya zo ya ce damu zai dawo don ya ji ta bakinmu har yanzu shiru ba mu ƙara ganin sa ba,anya kuwa lafiya? Ni kam na fara tunanin ko shima ya faɗa hannun aljani Rafkanagu."
Samaratu tace "Komai zai iya faruwa amma abin da nake so da kai ɗana shi ne ka sa a ranka cewa in dai ina numfashi a doron ƙasa sai na mallaka maka Gimbiya Sima ko ta halin ƙaƙa. In.kuwa kaga baka mallaketa ba, ba na raye a duniya."
Lokacin da Markahul Sabus ya ji wannan batu na mahaifiyarsa bokanya Samaratu sai farin ciki ya baibayeshi ya rungumeta yana mai fatan su samu damar kuɓuta daga cikin wannan tsafaffen keji.
Suna cikin wannan hali ne suka ga aljani Durfus ya bayyana gabansu jina-jina, duk jikinsa raunuka ne, sai numfarfashi yake kamar ba zai rayu
ba. Cikin ƙarfin hali ya dubesu yace, "Ku yi sani cewa yau kwana biyu kenan ina tafka yaƙi da wasu dakarun boka SHAMHARU waɗanda ya turosu su hallaka ni. Da ƙyar da siɗin goshi na samu na karkashesu, ko ɗayansu ban bari ya tsira ba. Nayi bincike na gano cewa rayuwata da taku na cikin mugun haɗari don haka dole ne mu haɗa kai idan har muna son mu ga bayan wannan babban maƙiyi namu wato SHAMHARU SHAHARARRE." Yayin da Durfus yazo nan a zancensa sai Markahul Sabus ya dubeshi yace,
"To yanzu yaya batun sharaɗin daka
gindiya mana?"
Darfus ya yi murmushin ƙarfin hali yace,
"Ka bar wannan magana yanzu. Abin da nake so da ku shine ku saki jiki dani zan tafi da ku izuwa fadar tsafin a can ne zan iya fito daku daga cikin wannan keji sannan sai mu tattauna akan hanyar da zamu ɓullowa al'amarin."
Ko da jin haka sai murna ta kama su boka Sulbaini. Gaba

2 Comments On MATSATSUBI Book 1
avatar
armiyau

11 months ago

Reply

For fun

avatar
muhammad-musa-2

10 months ago

Reply

Akwai matstsubi

Please Login or Register in order to submit comment