Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gama karanta wannan jawabí a fili sai iskar KUNDIN TSATSUBA tayi fitar burgu ta zuƙe su gaba đaya su biyar ɗin suka zama 'yan ƙanana mini-mini suka faɗa ciki.
Kawai sai gani suka yi sun faɗo cikin wani jeji mai girman gaske,babu komaí a cikinsa face wani katafaren dutse mai ƙaton kogo. Ko'ina ka duba a jejin iyakar ganinka wannan dutse ne ba'a íya ganin ƙarshen sa. Lokaci guda su Jafar suka mimmiƙe tsaye suka yi nazarin dutsen sannan suka dubi junansu. Yelisa tace, "Yanzu mene ne abin yi?"
"Abin yi kawai mu shiga cikin kogon nan tunda babu wata hanyar da zamu iya samu a jejin nan ko ina dutse ne." Mashrila ce ta ba da wannan amsa.
Gulzum,Jafar Mazalish suka amince da wannan shawara ta Mashrila. Ba tare da ɓata wani lokaci ba,suka kunna kai cikin kogon. Wani abin mamaki shi ne koda shigar su cikin kogon sai duhu ya yaye haske ya baibaye cikinsa ya zamana suna ganin komai.
Babu komai a cikin kogon face tsiraron duwatsu,ƙananan bishiyoyi, da kuma gurɓatattun damomi. Haka dai su Jafar suka yi tafiya a cikin kogon be tare da sun ga komai ba,kuma ba su ji motsin komai ba har tsawon sa'a hudu. A wannan lokaci duk sun gaji ainun Gulzum ne kaɗai bai gaji ba.
Jafar da Yelisa kam har haɗa ƙafa suke suna rangaji a hanya tamkar waɗanda suka bugu da giya.
Kwatsam sai suka yi kiciɓis da wata ƙatuwar rijiya wadda aka rufe ta da murfin ƙaton mummulallen ƙarfe mai nauyin tsiya. Dukkaninsu sai suka yi turus a gaban rijiyar. Jafar yace, "Me ya kamata mu yi da rijiyar nan?"
Mazalish ta ce, "Kawai mu buɗe ta ai dama duk muna jin ƙishirwa sai kowa ya jiƙa maƙogwaronsa."
"Kai anya kuwa za'a iya samun ruwa a cikin rijiyar nan ku duba fa ku gani bakinta a bushe yake ƙyamas babu alamar ana ɗiban ruwa a cikinta.'' Yelisa ce tayi wannan jawabi. Ita kuwa Mashrila sai ta daka mata harara tace, "Ke dai kin cika tsoro,to ki sani har abada matsoraci baya zama gwanı."
Cikin fushi Yelisa tace, "To na ji ni matsoraciya ce, tun da ke jaruma ce ai sai ki buɗe mana rijiyar ko."
"Wannan kuma aikin sarkin ƙarfi ne Gulzum." In ji Jafar.
Gulzum ya murtuke fuska duk da cewar an yabeshi. Nan take Gulzum ya sa hannu ɗaya da nufin ɗauke murfin rijiyar amma sai ya kasa.
Mamaki ya kama shi ya saka hannayensa biyu ya taƙarƙare iya ƙarfinsa ya ɗago murfin,amma sai ya
kasa đaga shi gaba ɗaya. Nan fa su Jafar suka cika da mamaki, domin ba su taɓa ganin aikin ƙarfin da ya gagari Gulzum ba sai yau,tun sa'adda suka shigo cikin KUNDIN TSATSUBA.
Koda ganin abin da ya faru sai Mazalish tace, "Gulzum gafara nan ka bani wuri tunda ka kasa buɗewa."
Gulzum yace, "To 'yar sarkin mayu ai sai ki jarraba ƙarfin maitarki anan mu gani."
Mazalish ta daka masa tsawa,tace "Kar ka sake kirana maiya tunda dai ni ba maiya ba ce, kuma na baro maita a can mahallinta."
Kawai sai Mazalish ta nuna murfin rijiyar nan da ɗanyatsanta guda. Take wata siririyar iska ta fito daga cikin ɗanyatsan ta ɗaga murfin rijiyar nan sama ta ajiye shi a gefe guda. Mazalish ta dube su gaba ɗaya tace, "Ni kaɗai ce zan iya yin tsafi ya yi aiki a cikinku saboda na sami tsafina ne a cikin duniyar KUNDIN TSATSUBA,ku kuwa kun samo naku tsafin daga wata duniyar dabam."
Mazalish na gama rufe bakinta kenan sai wasu irin halittu suka yo fitar burgu daga cikin rijiyar nan suna yin wata irin ƙara mara daɗin ji wacce ka iya kashe dodon kunne.
Su dai waɗannan halittun 'yan ƙanana ne mini-mini,domin girmansu ba zai wuce na fara ba,amma kuma surar aljanu gare su. Gaba đaya jikinsu,hannaye ne masu zaƙwa-zaƙwan farata. Adadin su ya kai dubu,kuma gaba ɗayansu suka fito waje daga cikin rijiyar nan. Ai kuwa nan take suka hau yakusar jikin su Jafar. Cikin ƙanƙanin lokaci suka yi musu fata-fata,kowa ka duba jini ke zuba a jikinsa,kuma jiri na ɗibarsu suna faɗuwa da miƙewa da ƙyar.
Koda Mazalish taga zasu hallaka gaba ɗaya sai tayi tsafi suka zama hayaƙi. Hayaƙin ya shige cikin rijiyar nan,sannan murfin ijiyar ya taso daga
inda yake ya rufe rijiyar ya zamana halittun ba su sami damar binsu cikin rijiyar ba. Sai duk suka yanyame kan rijiyar suna ta yin wannan ƙarar ta su mara daɗin ji. Yayin da hayaƙi ya faɗa cikin rijiyar sai ya rikiɗe ya zama Mazalish,Yelisa,Jafar,Gulzum da Mashrila. Cikin fushi Jafar ya dubi Mazalish yace, "Don me za ki shigo da mu cikin rijiyar nan bakya tunanin za mu iya riskar abin da yafi waɗancan halittun haɗari?"
Mazalish tayi ƙwafa tace, "Kash! Dana san zaka faɗi haka da na barka a can kai kaɗai. Shin baka taɓa jin an ce abin da ya koro ɓera ya shiga wuta,yafi cutar zafi ba? Ai da masifar da ka sani gwara wadda baka sani ba."
A daidai wannan lokaci ne kuma hankalin su gaba ɗaya ya koma kan inda suka tsinci kan su sai suka ga ashe a tsakiyar wani ƙaton gari ne. A cikinsa ga gidaje nan da kayayyaki irin na rayuwar mutane sosai,amma kuma ba su ga koda mutum guda ɗaya ba a garin. Garin ya yi tsit,ko kukan gyare babu.
Al'amarin da ya yi matuƙar jefa su cikin mamaki kenan. Kawai sai suka cigaba da tafiya su shiga nan su fita can,har tsawon sa'a uku sannan suka iso ƙarshen garin inda yayi iyaka da gaɓar wata teku.
Kwance a bakin gaɓar tekun wasu gumaka ne bila adadin masu surar ifiritan aljanu. Anan su Jafar suka tsaya suna kallon waɗannan gumaka cikin al'ajabi.
Jafar yace, "Kai amma fa abin al'ajabi baya ƙarewa,wai shin to ina mutanen wannan birnin,kuma me suke yi da waɗannan gumakan?"
"To wa kake tambaya ka san dai a cikin mu nan kaf babu mai iya baka amsa." Gulzum ne ya faɗi haka cikin ɗacin rai. Jafar ya fusata yace, "Wai kai me na tare maka ne a rayuwarka kake tsangwamata ko kuwa mun haɗa neman aure ne?"(🤣🤣🤣🤣 Tambaye sa dai Jafarun mu🤣)
Koda jin wannan tambaya sai kowa ya bushe da darıya har shi kansa Gulzum ɗin. Yelisa tace, "haba Jafar yanzu in banda daraja ta ina kai ina yin hamaiya da Gulzum ai yafi ƙarfin ka ta ko'ina."
Mazalish ta ce, "Kun ga ba hira zamu tsaya yi ba gwara mu yi abin da zai fishshe mu."
Kawai sai ta nufi inda gumakan nan suke. Da zuwa sai ta hau duba su tana tattaɓasu,ko zata ga wani abun da yake akwai raunika a jikinta kuma har yanzu jini bai daina zuba ba sai jinin jikin nata ya ɗiga akan ɗaya daga cikin gumakan. Faruwar hakan ke da wuya sai ruhi ya shiga jikinsa nan take,ya miƙe tsaye ya yi kururuwa yana mai zazzago harshen bakinsa wanda girmansa ya kai na ƙatuwar bishiya.
Cikin firgici su Jafar suka juya da baya suka runtuma da gudu suka bar Mazalish nan tsaye gaban ifiritin ta kasa gudu don tsananin razana,sai ihu take faman yi kawai. Ifiritin nan ya sake taƙarƙarewa ya wangame ƙaton bakinsa yana mai ruri ya rinƙa aman mutane daga cikin bakinsa. Sai da ya amayar da kusan mutum dubu. Sannan hankalinsa ya dawo kan Mazalish wacce har yanzu tana nan tsaye a gabansa tana ihu. Cikin zafin nama ya kawo mata wafta don ya ɗauke ta,ita kuwa ta goce cikin zafin nama sannan ta ruga da gudu ta nufi inda suka Jafar suka yi.
Ifiritin nan kuwa ya bita a guje suka kasa tsere. ldan tayi gudu,tayi gudu,sai ta ga ifiritin nan daf da ita yana jeho harshensa waje don ya lasota, kawai sai ta ƙwala ihu ta ƙara ƙaimin gudu. Haka dai ya cigaba da binta har suka riski su Jafar. Koda su Jafar suka waigo suka ƙaton ifiritin ya kusan cimma Mazalish sai suka ƙara ƙaimin gudunsu. Kawai sai wasu fukafukai guda biyu suka fitar da kansu daga jikin ifiritin nan ya tashi sama ya riski Mazalish ya lasota da harshensa sannan ya haɗiyeta. Daga nan ya bi su Jafar ɗaya bayan ɗaya duk ya haɗiye su.
A gaban KUNDIN TSATSUBA su Jafar suka tsinci kansu,har yanzu jini na zuba a jikinsu sakamakon raunukan nan da 'yan mini-mini aljanu sukai musu.
Kuma shafi na goma sha huɗu ne a buɗe jikin tafin KUNDIN TSATSUBA. Nan take su Jafar suka yanke jiki suka faɗi ƙasa kamar sumammu. Sai bayan sa'a guda sannan kowannansu ya dawo cikin haiyacinsa. Yelisa ce ta fara miƙewa zaune ta dubi kowa tace, "Tabɗijam amma fa wannan karon mun sha baƙar wuya."
Mashrila tayi tsaki tace, "Ai in dama
wahalar ce zallah babu tashin hankali ai da sauƙi."
Shi kuwa Jafar sai ya dubi Mazalish yace, "Wai ke ina ƙarfin tsafin naki ya tafi,me ya sa baki cece mu daga sharrin wannan ifiritin ba?"
Mazalish tayí murmushi,sannan tace, "Lallai yanzu na tabbatar da cewa kai yaro ne. Ai idan ka ji ana cewa ga ƙi gudu to sa gudu ne bai zo ba."
Jafar yace, "Wai ina ruwan filfilwa ai ban san cewa Gulzum na da gudu ba, sai sa'adda ifiritin nan ya biyo mu,kafin na waiga bayana tuni Gulzum ya wuce mu gaba ɗaya,duk girman nan na sa da nauyin jikinsa bai hanashi gudu ba, don sai ya zamo kamar soso akan ruwa."
Gaba ɗaya aka tuntsire da dariya,shi kuwa Gulzum sai ya turɓune fuska yace a ransa, 'Ina fatan naga ranar da zamu gama karanta KUNDIN TSATSUBA sai na nunawa yaron nan cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne. Tabbas rainin da ke tsakaninmu yayi yawa."
Kafin wani daga cikin su ya ƙara cewa wani abu KUNDIN TSATSUBA ya buɗe kansa izuwa shafi na goma sha biyar. Nan take suka yi arba da hoton wata alƙarya.
A ƙasanta an yi rubutu kamar haka....
".....WANNAN ALƘARYA,ALƘARYA CE TA BALA'I, AN SAMAR DA ITA KIMANIN SHEKARU DUBU HUƊU. MAI KARATU SHIGO CIKINTA KA SHA KALLO..."

Topah,me zai faru gasu Jafar a wannan alƙarya?
Mu haɗu a babi na gaba idan Allah ya kaimu.
Fatan alheri.
Contact:- 08167757245
Matsatsubi 1
Typing:-Ahmad Munir Muhammad
Posting:-Ahmad Munir Muhammad
Part P
Takun ƙarshe

A baya mun tsaya a inda:-
A ƙasanta an yi rubutu kamar haka....
".....WANNAN ALƘARYA,ALƘARYA CE TA BALA'I, AN SAMAR DA ITA KIMANIN SHEKARU DUBU HUƊU. MAI KARATU SHIGO CIKINTA KA SHA KALLO..."

######
Siririyar muryar nan ce ta karanta wannan jawabi. Muryar na ɗaukewa iskar cikin KUNDIN TSATSUBA ta sake zuƙe su Jafar gaba ɗayansu. Kawai sai tsintar kansu suka yi a tsakiyar wani babban birni mai yawan cikowar mutane,maza da mata,yara da manya,duk inda suka duba sai su ga kowa na ƙera kwale-kwale ɗan ƙarami daidai shigar mutum ɗaya.
Duk inda suka wuce sai dai su ga ana kallansu kawai,amma babu wanda ya kula su.
Al'amarin da ya jefa su cikin mamaki kenan. Haka dai suka yi ta yawo a cikin garin har suka gaji,sannan suka sami wuri suka zauna, don su huta.
Jafar yace, "Kai ku tsaya fa an ce ruwa baya tsami banza. Ina ganin zai fi kyau mu ma kowannan mu ya ƙera nasa kwale-kwalen domin an ce idan ka je gari kaga kowa ya ɗaura jela a bayansa kaima ka ɗaura."
"Ƙwarai kuwa ka zo da shawara mai kyau domin babu mamaki akwai masifar da zata zo kuma in mutum ba shi da kwale-kwalen hallaka zai yi."
Ba tare da wani da gardama ba suka miƙe tsaye gaba ɗaya don tafiya neman kayan aikin ƙera kwale-kwale. Kawai sai suka ga wani babban mutum ya tunkaro su yana sanye da hular saurata akansa,mutane na biye da shi. Koda zuwansa gare su sai yace, "Yaku waɗannan baƙi ku yi sani cewa kun kawo kanku mahallaka,domin akwai masifar da zata zo mana nan da kwana biyu,damu daku babu wanda zai tsira
da rayuwarsa, sai mai nisan kwana."
Cikin mamaki Jafar ya dubi mutunin yace, "Wace irin masifa ce wannan take zuwa muku?"
Mutumin ya yi gyaran murya yace, "Ni sunana sarki Makanul Habasi,gaba ɗaya mutanen garin nan a ƙarƙashin mulkina suke,muna da wata matsala guda ɗaya. Kimanin shekaru dubu huɗu baya wani taƙadarin maridi ya taɓa zuwa mana, koda zuwansa sai ya kama gaba ɗayan mazajen garin nan ya ɗaure su tamau da sarƙoƙi. Su kuwa matayen mu ya bisu ɗaya bayan ɗaya yayi lalata da kowacce. Da ya gama wannan ɓarna sai ya ɓace aka neme shi sama da ƙasa aka rasa.
Bayan tafiyarsa ne matayenmu suka yi ta kuka da baƙin ciki,da ƙyar suka samu suka kwankwance mu daga ɗaurin sarƙar da muka sha.
Haka dai muka rungumi ƙaddara muka ci gaba da rayuwa har tsawon wata tara bamu ƙara ganin wannan maridiba. Koda wata taran nan ya cika sai gaba ɗayan matayenmu suka kama zubar da jini tamkar annobar amai da gudawa. Wannan jini ya rinƙa yawo a cikin gari ya malale ko'ina kai ka ce teku ce ta ɓalle. Ba zato ba tsammani kuma sai jinin ya rinƙa rikiɗa yana zama tsutsutsi masu girman gaske, waɗanda ka iya haɗiye mutum. Nan fa tsutsotsin nan suka hau yagar naman jikin mutane,aka yi ta guje-guje da iface-iface. A wannan rana babu waɗanda suka tsira face waɗanda suka faɗa cikin teku. A cikin tekun ma wasu da yawa sun mutu saboda haɗuwa da muggan halittun cikin ruwa.
Waɗannan tsutsotsi ba su iya shiga cikin teku. Daga sannan wannan masifa ta ci gaba da wakana bayan kowanne kwana arba'in. Wannan shine dalilin da ya sa kuka ga muna ta ƙera kwale-kwaleka ba don komai ba ne sai don mu shiga cikin teku akansa don neman tsira da rayuwarmu. Yaku waɗannan baƙi gashi yanzu kun zo a rashin sa'a domin yau saura kwana biyu rak wannan masifa tu zo."
Yayin da sarki Makanul Habasi yazo nan a zancensa sai hankalin su Jafar ya dugunzuma suka rasa abin dake musu da daɗi,Yelisa tace, "Yakai wannan sarki yanzu wane irin taimako zaka yi mana?"
Makanul Habasi yace, "Babu abin da zan iya yi muku face na baiwa kowannen ku kyautar kwale-kwale da zarar kun ga wannan masifa tazo sai ku ruga izuwa cikin teku,idan kuna da nisan kwana sai ku rayu. Idan kuwa ba ku da shi a cikin tekun zaku hallaka.
Yana gama faɗin hakan ne ya sa aka kai su Jafar masauki aka ba su abinci da abin sha,kuma aka sa musu magani a jikin raunikan da ke jikinsu.
Kwana biyu na cika wannan annoba ta wakana wato matayen garin suka kama zubar da jini,jinin ya rinƙa malala yana yawo a cikin garin ya game ko'ina sai dai ka ga mutane na ta guje-guje akan jinin kowa na ƙoƙarin zuwa bakin teku. A wannan ranar har dasu Jafar ake wannan gudun ceton rai,sai da ya rage saura ƙiris gaba ɗayan mutanen su riski bakin teku sannan tsutsotsin suka rinƙa ƙurewa mutane gudu suna kama su,suna yagar naman jikinsu suna ci,kai kace karnuka ne ke walima da naman ɓeraye.
Lokacin đa su Jafar suke ƙoƙarin isa bakin teku wata tsutsa guda ɗaya ta tuso su a gaba tana neman ƙure musu gudu. Gulzum ne a gaban kowa,sai Jafar ne ya zamo na ƙarshe, sai da ya zamana tsakanin Jafar da wannan tsutsa bai wuce tazarar taku biyu ba. Duk inda ya đauke ƙafarsa sai ka ga ƙafarta ta dira a wajen ta caki ƙasa. Take wurin zaiyi rami zururu kamar an haƙa rijíya. Sa'adda Jafar yaga tsutsar ta kusan cimmasa sai ya rinƙa ihu yana kiran sunan Gulzum,yana roƙonsa daya kawo masa đauki. Duk da cewar Gulzum na cikin tashin hankali saida dariyar mugunta ta ƙwace masa yace,
"Shegen yaro sai yau ka san ina da amfani to ai ni ba wawa bane bare na koma da baya a ƙoƙarin cetonka ayi biyu babu."
Da yake Yelisa na kan kafaɗar Gulzum ne sai taji abin da ya faɗa. Nan take ta dakawa Gulzum tsawa tace, "Maza ka juya da baya ka ceto rayuwar masoyina Jafar in kuwa ka ƙi na rantse da darajar mahaifina duk sa'adda muka koma duniyar mu sai nayi maka hukunci mai zafi."
Koda jin wannan batu sai Gulzum ya fashe da kuka don tsananin takaici,domin babu abin da ya tsana a rayuwarsa sama da Jafar. Gashi kuma yanzu an tilasta shi akan ya juya ya ceto rayuwarsa. Wanda yin hakan na iya jefa tasa rayuwar cikin ƙila-wa-ƙala.
Bisa dole Gulzumn ya juya da baya cikin tsananin gudu har ya riski Jafar ya sure shi ya aza bisa kafaɗarsa kusa da Yelisa,sannan ya juya cikin zafin nama don ya cigaba da gudu. Kafin ya juya tuni tsutsar nan ta kawo sara kawai sai ta zabtare wani ƙaton nama a duga-dugin Gulzum.
Gulzum ya ƙwalla ihu,cikin tsananin juriya da jarumta ya daɗa mannewa da gudu jinı na zuba sharaf daga dugadugin nasa,amma bai fasa gudun ba,har suka isa bakin teku kowa ya shiga kwale-kwalensa suka miƙa cikin ruwa.
Shigarsu cikin tekun ke da wuya wata irin ƙatuwar macijiya mai tsananin tsawo,kuma mai kawuna bakwai ta taso sama daga cikin ruwan ta rinƙa bugun mutane tana farfasa kwale-kwalensu. Kafin wani lokaci ta zama sanadiyari gawarwaki akan ruwan. Lokaci guda ta wangame bakinta ta haɗiye su Jafar su duka biyar ɗin hár ma da kwale-kwalensu gaba ɗaya. Su Jafar dai sai gani suka yi an jefo su cikin ta su duniyar tare dá kwale-kwalensu sun faɗo gaban KUNDIN TSATSUBA.
A dugadugin Gulzum akwai wannan ƙaton rauni,kuma jini bai dai na zuba ba. Köda raɗaɗi da zogi ya ishi Gulzum sai ransa ya ɓaci yace, 'Ai kuwa tunda na shiga wannan hali a dalilin ceto rayuwar wannan yaron banga amfanin hưtún mu ba,gwarama mu ci gaba da shan wahala kówa jikinsa ya gaya masa."
Kafin wani yace wani abu tuni aljani Gulzum ya daka tsalle ya buɗe shafin KUNDIN TSATSUBA na goma sha shida. Take suka yi arba da hoton wata guguwa. A samanta an yi rubutu kamar haka........
"WANNAN GUGUWA,GUGUWA CE TA MASIFA DA BALA'I. ẢN HALICCE TA KIMANIN SHEKARU DUBU SHIDA BAYA,MAI KARATU SHIGO CIKI KA SHA KALLO........."
Gulzum na gama karanta wannan jawabi a fili sai iskar cikin KUNDIN TSATSUBA tayi fitar burgu ta zuƙe su gaba ɗaya suka zama 'yan mini-mini suka faɗa cikin KUNDIN TSATSUBA.

YAYA ƘARSHEN HIKAYAR JARUMI NAZMIR DA GIMBIYA LUZAIYA ZATA KASANCE??
SHIN JARUMI HUBAIRU ZAI IYA SAKE ƘWATO GIMBIYA SIMA DAGA HANNUN SARKI LU'UMANU??
INA LABARIN BOKA SHAMHARU WANDA HAR YANZU BAI FITO BA DAGA HALWAR TSAFIN SA TA ZAMA
MATSATSUBI??
SHIN YAUSHE NE ZA'A GAMA AIKIN RUBUTUN SABON KUNDIN TSATSUBA??
SHIN SU BOKANYA SAMARATU ZASU SAMI NASARAR SAMO ABUBUWAN DA SUKE NEMA DON YIN GALABA AKAN SHAMHARU??
WACE IRIN MASIFA SU JAFAR ZASU GANI A CIKIN WANNAN GUGUWA??

Mu haɗu a cikin MATSATSUBI littafi na biyu don jin cigaban wannan labari.
DAGA MAI ƊEBE MUKU KEWA
ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI
Masha'Allah,anan muka kawo ƙarshen littafin Matsatsubi na ɗaya, Allah ya bamu ikon kawo muku littafi na biyu.
Zaku iya yin sharhi.
Fatan alheri.
Contact:- 08167757245

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


2 Comments On MATSATSUBI Book 1
avatar
armiyau

11 months ago

Reply

For fun

avatar
muhammad-musa-2

10 months ago

Reply

Akwai matstsubi

Please Login or Register in order to submit comment