Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mijinki. Kuma banda katuwar loma a gaban miji. Murmushi tayi hade da kuka ta sake fadawa jikinsa. Baba wa zaku rinka gani a gidan nan idan na tafi? Umma ce ta bata amsa bayan ta fyace hanci cikin yaran Yaya Shafiu matarsa tace na dauki duk wadda nake so. Baba ya dauko wata leda ya damka mata. Ga wannan dubu hamsin ne. Cikin kudin da na samu ne. Zan ajiye miki sauran. Ki rinka amfani dashi. Allah Yayi miki albarka. Basu fito ba sai da Malam babansu Hajara yazo ya buga kofar. Haka suka tafi tana ta rusa kuka ita da Hajara. Anti Faiza tace gulmammu duk wadda bata son auren sai mu koma da ita. [9/25, 3:48 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 29

Batul Mamman(Mrs)





Idan kaga dakin Zuhra baka ce na yar Mal Bashir kafinta bane. Tabbas duk dakunan gidan sunfi nata kaya masu kyau da tsada. To amma itama nata iyayen sunyi kokari sosai. Gida ya cika da yan kawo amarya. Izzatu ita kadai ce a daki dama ita ba mai rakice rakicen kawaye bace. Daga ita sai 'ya'yanta. Duk da tasawa ranta bazata kula Zuhra ko tayi kishinta ba sai da tayi kuka da aka shigo ana guda. Adabiyya da Hamida sunfi kowa rawar kafa Yaya yayi amarya. Hakuri da nasiha aka sake yi mata sannan suka tafi. Hajara da wasu yan uwanta ne karshen tafiya bayan sun sake gyara mata daki. Tashi tayi ta cire mayafin jikinta saboda su hudu ne kawai a dakin. Hajara tayi saurin mayar mata.
"Abinda ake son amarya da jan aji. Kin wani cire mayafi, idan wasu suka sake shigowa fa."

Sake cire mayafin tayi "ke kyaleni nasha iska. Da zafin gari zanji ko na rabuwa dasu Umma." Tana magana idanunta suka cika da hawaye.

Hajara ta ja hannunta suka koma kan gadon. Sake gyara mata dauri tayi aka fesa turare."to mu zamu tafi amarya. Kada ki tashi nasan ango na hanya. Kuma ki dena kukan su Umma haka. Irin haka sai yaga kamar auren dole aka yi muku.

A zuciyarta Zuhra tace meye maraba. A zahiri kuwa godiya tayi musu suka tafi. Sai da taji dakin tsit ta tashi tana leka ko ina. Wurin yayi kyau sosai ga kamshin turaren wutar da kanwar Umma ta hada mata. A hankali ta bude kofar toilet ta shiga. Wani murmushu tayi. Irin wannan bandaki kamar a gidan shugaban kasa. Ta mika hannu sink taga ruwa ya fito tun kafin ta kunna famfon. Zabura tayi da gudu zata fita don a zatonta famfon ya lalace ne , kada ace ita ta lalata. Ko da ta juyo sai taga ruwan ya dauke. Gabanta na dukan uku uku ta sake komawa tana mika hannu saman zata kunna sai taga bai sake fitowa ba. Har tayi ajiyar zuciya ta sake saka hannu a wurin fitar ruwa sai gashi ya sake fitowa. Fita kawai tayi ta rufe toilet din. Allah Yasa tayi sallar Isha. Dama nafila take son yi, sai ta hakura.

Tun tana jira ko angon nata zai shigo har ta fitar da rai. Dama bata sa a ka ba. Wuri ta samu a tsakiyar gadon tayi kwanciyarta ko kaya bata chanja ba. Bata dade ba bacci mai nauyi yayi gaba da ita.

Hamza bai shigo gidan ba sai shadaya da rabi na dare. Tun kayan jikinsa na daurin aure bai dawo gida ba. Babbar rigarsa da hula duk a hannu ya shigo dasu ya hadu da Tala tana ta gyara gidan. Ita kam dole a yaba mata wurin tsafta. A gajiye yake sosai, tayi masa sannu da zuwa ya amsa ya haye sama.

Sai da yaji ba dadi da ya kalli kofar dake hagun dakinsa. Wai matarsa ce a ciki. Ko alamar zuwa baiyi ba. Kofar dakin Izzatu ya taba yaji bata rufe ba. Muryarta a shake alamar taci kuka yaji tace
"Waye?"
Shiga yayi ta taso da sauri ta rungume shi tana kuka. Bai hanata ba sai da tayi shiru don kanta.
"Ina su Nana?" Ya tambaya lokacin da yake cire takalmansa.

"Suna sabon dakinsu. Tala zata rinka duba min su." Yadda take maganar kasan har yanzu tana bakin cikin canza musu daki da aka yi.

Kiss Hamza yayi mata a kumatu." Goodnight Izzy. Kije ki kwanta" Ya juya zai fita. Kansa ke ciwo kamar ya tsage. Yau baici wani abin kirki ba tun safe. Yana son tambayar Izzatu amma yasan idan bata da nutsuwa girki ma baya gabanta.

Saurin biyoshi tayi. Ta rike masa hannu" Don't tell me wurin Zuhra zaka kwana".

Hannun nata ya saki." No, dakina zani. Na gaji kema ki kwanta haka"

Kallon tuhuma take masa." Are you sure?". Kai ya gyada mata. Baya son magana saboda yadda kansa ke sarawa "Ko nazo mu kwana? Ina fargabar ranar da zaka kwana dakin yarinyar nan. Zan iya mutuwa saboda kishi." Ganin baya son magana yasa ta kyale shi. Tasan bazai fadi magana ba yaki cikawa.

Bayan ya tafi itama sake gyara jikinta tayi tabi bayansa. Da ya tambayeta abinci tace babu amma bari tayi sauri ta dafa masa wani abin. Jallop din taliya tayi masa. Kafin ta gama yayi wanka. Abinci yaci ya dan zauna ya fada masa. Suka kwanta shi da Izzatunsa. Ba wata hira tsakaninsu domin kuwa akwai abinda ke damunsa.
[9/25, 3:49 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 30

Batul Mamman(Mrs)




Zuhra anji dadin bacci saboda gajiyar da ta tara ta biki. Ba ita ta farka ba sai bayan tara. A firgice ta tashi ganin hasken rana a dakinta. Ko sallar asuba batayi ba. Sai da ta shiga bandakin ta tuna da matsalarsa ta jiya. Gashi ta makara sallah. Banda bahon wanka daga gefe wata yar matakala ce mai karamin bene da yayi kasa akwai shower a wurin. Kunnawa tayi ruwa ya watso mata saboda yayi karfi. Da kyar ta iya rage karfin ruwan. Cire kayanta tayi ta koma tayi wanka tare da alwala.

Tun kafin ta gama shiryawa cikinta ya soma kukan yunwa. Nan fa ake yinta. Zuhra bata jurar yunwa gashi tunda aka kawota ko motsi bataji a kofar dakin ba. Haka ta gama duk abinda zata yi ta sami wuri ta zauna. Tunanin iyayenta ne ya zo mata ta soma kuka.

Izzatu da Tala sun gama hada komai na breakfast suka jera akan dinning table. Sama ta hau ta kira Hamza. Sanye yake da jallabiya light brown sai kamshi yake. Yayi kyau sosai sai dai fuskarsa da ta zama maabociyar damuwa yan watannin nan. Yaransa duk suka yi masa kiss a goshi kamar yadda suma iyayen suka saba yi musu. Sannan suka zauna Izzatu tayi serving dinsu. Lomar farko da zai kai bakinsa ta tuna masa da Zuhra da ke daki tun jiya ko lekata baiyi ba. Tsaki tayi ya tura kujerarsa ya tashi.

"Baby what is wrong?" Izzatu ta tambaye shi itama tana mikewa tsaye.

Sama ya kalla ya sake yin tsaki "zan kira yarinyar nan tazo taci abinci ne."

A take Izzatu ta hade rai. "Ka bari Tala ta mika mata mana. Ai ba sai kaje dakinta ba."

"Hakkinta ne na ciyar da ita" yana fadin haka ya hau saman.

Ya kusa minti biyu kafin ya murda kofar ya shiga. Akwai kamshi dai saboda dakin amarya ne sai dai zafi sosai duk da tagar a bude take. Ko meyasa bata kunna AC ba oho.

A tsaye take tana jera kayanta a wardrobe har ta kusa gamawa taji an taba kofar. Cikinta sai da ya bada sauti saboda tsoro. Ko da ya shigo duk rashin kunyar da taso yi masa sai ta fasa saboda yadda ya cika mata ido. Bata taba kare masa kallo ba sai yau. Da ace zaman lafiya suke yi da ta fada masa yadda yayi kyau. Shima ita yake kallo. Riga da skirt tasa na atampa fuskar nan tasha farar hoda. Kana ganinta ita daban fuskar ma daban. Ga hannun breziya ya fito ta kowane gefen hannun rigarta. Ya dan tabe baki....kai kuma irin taka jarabawar kenan Hamza.

"Ke baki iya gaisuwa bane?"

Saurin durkusawa tayi tare da jin kunya.
"Ina kwana, an tashi lafiya"?

Bai amsa ba ya juya"ki sauko muyi breakfast".

Kafin ya kai kofa ta biyo bayan shi. Yunwa take ji sosai. Ace yau har shadaya saura bata ci abinci ba. Ita kanta tasan tayi abinda zaa jinjina mata.

A baya ta rinka binsa har suka sauko. Izzatu ta kai karshe wurin bacin rai, sai kawai ta danne. Kujera ta samu kusa da yaran ta zauna tare da yin sallama. Khalifa ne kawai ya amsa. Ya kalli Mamansa.
"Mummy wannan ma mai aiki ce?"

Hamza ya ce masa yayi shiru kawai yaci abinci. Zuhra tana sane bata ji ya gyara masa yace ita ba mai aiki bace ko da bai kirata matarsa ba.

Izzatu ko daga kai batayi ba bare ta bashi amsa. Itama Zuhra taki kallonta. Yadda take jin haushin Izzatu ko kallo bata isheta ba. A dalilinta tazo gidan nan da bata da wata kima a idon mazauna cikinsa. Muryar Hamza ce ta katse mata tunani.
"Wai ba kya gaishe da mutane ne?"

Ta dago fuska suka hada ido. "Na gaisheka a daki"

Da kansa yayi mata alamar bata gaishe da Izzatu ba. Amma lallai ya rainata da yawa. Su basu ce 'ya'yansu su gaisheta ba sai ita zata gaishe da matarsa. Kamar bazata yi ba sai kuma tace "ina kwana"

Maimakon ta amsa sai kawai ta tashi ta koma dakinta. Hamza ya bi bayanta. Yaran ma suka gama suka tashi. Suna tafiya Zuhra ta janyo flask ta bubbude sannan ta debi abinda zata ci ta hada tea. Sai da taci ta koshi sannan ta tashi daga dinning area din ta koma wurin yaran inda suke zaune suna kallo. Tambayarsu sunayensu tayi suka bata amsa. Junior yace "ke kuma ya sunanki?".

Murmushi tayi "sunana Zuhra". Khalifa yace "nice name, will you be my friend?"

Ido ta dan zaro "tohhh kun iya turanci tun yanzu..." da haka suka rinka hira da ita tana jansu da wasa. Hatta Nana mai kyuya ta yarda da Zuhra.

Hamza ya dauko laptop zai fara aiki sai kuma ya rufe. "Izzy kirawo yarinyar nan, I need to talk to both of you"

Wani irin kallo tayi masa. " sweety nice zani dakin Zuhra? Allah Ya kiyaye. Kuma ai bai kamata ta shigo mana bedroom ba. As far as am concerned ni ban dauketa matarka ba."

"Gashi kuma na biya sadaki" yadda yayi maganar tasan har yanzu yana ganin laifinta a matsayin wadda ta jawo masa auren.

Tana fitowa ta jiyo muryar Junior yana cewa Zuhra ta yi masa tatsuniya. Daga saman ta leka ta kirawo Khalifa. Shi ta fadawa ya rako Zuhra dakin daddysu yana jiranta.

Rike da hannun Khalifa suka shiga dakin. Wata irin niima taji. Ita nata dakin sai zafi. Falo ne a farko sannan kofar dakin daga ciki. Wurin ya tsaru sosai ta tsaya tana kallo. Izzatu tace da Khalifa yaje wurinsu Junior.

Babu wadda ta kula yar uwarta har Hamza ya fito. Kusa da Izzatu ya zauna. Ita Zuhra kasa ta zauna kan kafet saboda gudun kada ace tayi laifi. Gyara zamansa yayi fuskarsa ta nuna alamun ba wasa. Sannan ya soma magana

"Kamar yadda kuka sani dukkaninku matana ne duk da cewa circumstances behind auren kowacce is different......

Zuhra anzo wurin...gabadaya jumlar karshe bata fahimta ba.

.....bana son tashin hankali a gidan nan. Izzy kece babba ina so kija girmanki. Ke kuma ya juya ga Zuhra ki bata girmanta. Tun farko na gargadeki akan auren nan kika ki ji. So duk abinda kika gani sai kiyi hakuri. Sannan a yanzu baki da kitchen don sai an gyara miki daki a kasa. For now idan Izzy tayi girki zata baki. Saboda haka babu zancen rabon kwana sai an gama kitchen din." Ya kallesu duk su biyu. "Ko akwai mai magana?"

Izzatu tana ta kumbure kumbure tace " ka fada mata ta fita harkar yarana".

Bai ce mata komai ba yace da Zuhra tana iya tafiya. Tunda ya soma magana bata daga kai ba. Yayi tsammanin zata nuna bacin rai amma sai yaga tayi shiru. Kanta a kasa ta fita daga dakin ta koma nata. Tana rufe kofar ta suma kuka duk yadda taso daurewa ta kasa....ba son Hamza take ba amma babu macen da zata so a nuna mata ita ba komai bace a gaban kishiya.
[9/25, 3:50 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 31

Batul Mamman(Mrs)





Sai karfe uku da rabi Tala ta kwankwasa mata kofa. Ko da ta bude abinci ne a plate an rufe da wani sai ruwa roba daya mai sanyi da cup. Godiya tayi mata ta karba. Gara a rinka kawo mata don ita bata jin zata iya jurar zama tare da mutanen da basa kaunarta su ci abinci.

Dama tuni ta soma jin yunwa. Tana budewa taliya ce da miya sai coleslaw a gefe. Kare masa kallo tayi tana mamaki. Abin kuma harda rowar abinci? Abincin dan kukut a plate kamar zaa bawa Khalifa. Tas ta cinye ta sha ruwa rabin robar. In ba haka tayi ba tasan bazata koshi ba.

Hamza tun bayan azahar suka fita da wani abokinsa. Gidansu Zuhra suka je yi musu ban gajiya. Su Umma sunji dadi sosai. Har ta cire kunyarta ta tambayeshi ya Zuhra ta kwana. Murmushi yayi sannan yace mata lafiya kalau. Tana gaishe su. Da zasu tafi Baba ya bawa Hamza wayar Zuhra. A jakar Hajara ta manta ta daren jiya. Juya wayar ya rinka yi, banda tsufa ta dade da fita yayi.

Da daddare ma har daki aka biyota da abincin. Macaroni ce da vegetable soup. Sai dai Zuhra ta tsani macaroni. Duk yunwar da take ji dole ta hakura. Gudun kada aga kwadayinta ma ko naman dake cikin miyar bata ci ba ta dauki tray din ta sauka kasa dashi. Tana tafiya Hamza da Izzatu dake zaune a dinning table na binta da ido. Bata ko tanka musu ba ta wuce ta ajiye abincin a kitchen. Ta fito kenan Tala ta biyota da sauri.
"Naga baki ci abincin ba"

Dan murmushi tayi "na koshi ne".

Tana wucewa idonta ya kai kan nasu abincin. Shinkafa suke ci, wato ita suka hada da macaroni. Hamza na lura da irin kallon da take musu har ta wuce.

Wurin karfe goma da rabi Zuhra tana zaune tunani duk ya isheta gashi ta manta wayarta a gida. Ga uwa uba yunwa. Turo kofar taji anyi tayi saurin tashi zaune ta saka hijab. Daga ita sai daurin kirji saboda zafi ya dameta.

Kafin ta rufe jikinta ya kula da daurin kirjin. Ba karamin tsanar sa yayi ba. Bai tsaya jan zance da ita ba yace..
" kina jindadin cin abincin ke kadai ko zaki rinka ci tare damu?"

Tasan har ransa ba so yake taci dasu din ba." Zanci ni kadai"

"Fine, sai ki rinka fada da wuri idan bazaki ci ba saboda a dena wasting. An kawo miki kin mayar batare da kin taba ba".

Idan kika yi shiru zaki kwari kanki shine abinda zuciyarta ke raya mata. Ta dan rage murya "bana cin macaroni ne"

"Macaroni kuma? Mtsw ke bana son karya."

Turo baki tayi "ni ba karya nake ba. Abinda aka kawo min kenan."

Dafa kansa yayi yadda yake idan yana cikin damuwa." Me yasa bakiyi magana ba. Anyway nasan shinkafar bata kare ba idan kina so kije ki ci."

Tana kallo ya karaso cikin dakin ya kunna wani abu. Da yake tana setin AC din tuni ta fara jin iska. Yana gani tayi murmushi. Sannan tace.
"Don Allah ina ka kunna? Jiya zafi ya isheni na zata da sankarau zan tashi da safe"

Ta kusa sashi dariya sai ya gimtse. Idan ya sakar mata fuska zata yi tunanin ta sami karbuwa ne. Remote din AC din ya nuna mata sannan ya miko mata wayarta da chaja a cikin leda. Murna tayi sosai tayi masa godiya.

Sai da ya kama hannun kofar ta sake magana tana sosa keya.
"uhmmm"

Ya tsaya yana kallonta
"yes" ganin taki magana.

"Dama, dama famfon bandakin ne naga kamar sun lalace."

"Kin lalata su dai" ya fada yana shiga ciki. Ya duba duka komai lafiya kalau. Ya fito "wai ni abokin wasanki ne? Babu famfon da ya lalace"

Bata ce komai ba tayi saurin shiga. Hannu ta tara a famfon sink da baho duk ruwa ya fito da kansa. Sai da ya tsorata ta duk da ta gani jiya. " ka gani ko, yau tun sallar asuba da shaya nake yin alwala."

Wannan karon murmushi yayi. Sannan yayi mata bayanin yadda kan famfon yake. Tun kafin ya fita ta rinka bi tana tara hannu ruwa na zuba. Dariya take yi don abin ya burgeta. Yace to kada ki karar mana da ruwan gidan. Kunya taji tayi saurin cire hannunta ta fito. Shi kuwa tuni ya fice ya tafi nasa dakin.
[9/25, 3:51 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 32

Batul Mamman(Mrs)




Haka rayuwa ta kasancewa Zuhra a gidan Hamza. Kullum safe, rana da dare duk zaa kawo mata abincin marowata kamar yadda take kiransa. A kullum zata yi waya da iyayenta. Idan bata kira ba zasu kira ta. Idan aka tambayeta Hamza tace yana nan kalau. Bata taba tunanin fadin komai ba domin Anti Faiza tace zaman gidan miji yana bukatar sirri. Ko Hajara ta hanata ta sanarwa komai na dangane da gidan aurenta. Hamza dai yasan ana bata abinci saboda haka bai taba damuwa da sanin yawansa ba. Idan ta fito sauka da kwanunkan abinci suka hadu da Izzatu zata gaisheta a ciki ciki. Itama da kyar take amsawa. Don Hamza yayi mata fadan baya son gaba ne da ko kallon Zuhra bazata yi ba. Shi kuwa matsalar kamfaninsa tasa shi a gaba, bashi da lokacin gidansa sosai.

Ranar alhamis da safe Tala ta kawo mata abinci kamar kullum. Tea ne a dan karamin cup irin mai saucer dinnan wanda kurba biyar zuwa shida zai kare. A plate din kuma sliced bread ne guda uku. Wani irin kallo Zuhra ta yiwa abincin. Ta dauki bread daya taji shi a bushe da tauri. Murmushin yake tayi... Tala yau kuma bushasshen brodi kike kawo min. Tala ta dawo ta dan durkusa gabanta amarya ai wannan tos ne. Tala zata yi sa'ar Izzatu ko ta girmeta da kadan. To...to me? Zuhra ta fada tana yamutsa fuska. Tala tace tos. A tosta ake sakawa sai kiga ya fito ta sama kamar an jeho shi. Har dan bota na shafa miki don kiji dadinsa. Zuhra ta gyada kai, naga alama. To nagode.

Bayan fitar Tala tayi ta juya bread din a hannunta. Tunda tazo gidan breakfast dinta na farko ne kawai ta taba koshi. Kullum sai dai rage hanya, gashi bata taba ganin alamar za'a fara aikin nata kitchen din ba. Ba yadda ta iya a dole ta fara cin bread din. Kana ganin fuskarta kamar mai shan madaci. Ko rabi bata ci ba ta shanye tea din. Ta sake kai bread din bakinta Hamza yayi sallama ya shigo batare da ya jira ta amsa ba. Zaune take da tray a gabanta kanta babu dankwali. Doguwar riga ce a jikinta ta wani material. Dinkin dai yayi kyau sai dai wadda tasa kayan ce sai a hankali. Sunkuyar da kanta tayi kasa tace ina kwana?
Bai amsa ba yana daura agogo a hanunsa ya dubi plate din gabanta. Ashe ma zaki iya ci. Dama naga toasted bread aka yi nayi tunanin baki saba ci ba a baki wani abincin. Zuhra tayi sauri ta tofar da na bakinta akan tray din. Wallahi bana iya ci, hakan ma dauriya ce kawai.

Hamza ji yayi kamar ya amayar da abinda yaci. Wannan wace irin kazanta ce ta gama jika bread a bakinta ta dawo dashi. Fuskarsa na kallon gefe yace naga saura biyu da rabi ki cinye. Tashi tsaye tayi tana karkade hannuwanta...wallahi dama uku ne. Dan murmushi yayi...haka Izzatu take bata son ayi abinci da yawa, a cewarta zasu yi kiba suyi loosing shape. Farkon aurensu har rama ya rinka yi. Daga baya sai yake siyan biskit da cake a ajiye a office. Kyalesu zaiyi, kila idan Zuhra ta dan horo zata nemi komawa gidan iyayenta. Sai ya saketa cikin sauki. Ba tare da ya kalleta ba yace zansa a kawo miki wani abincin. Da ya juya zai tafi yaji tace adawo lafiya, Allah Ya kiyaye, Ya bada sa'a, Ya tsare kuma Ya kare dukkan sharri. Adduar tayi masa dadi yace Amin a hankali. Wannan adduar kullum Umma sai tayiwa Baba idan zai fita wurin sana'arsa.

Tunda ya fita bata ga alamun abinci ba sai uku saura aka kawo na rana. Cikin kankanin lokaci ta tayar da abincin. Ta fito daga toilet kenan Tala ta shigo tace amarya kinyi baki. Shikenan anzo wurin.....kullum addua take yi kada tayi baki saboda bata san me zata basu ba, yau gashi wasu sun zo. Tunani ta soma yi lokaci guda idea ta zo mata. Kanta ta rike da hannu biyu ta rufe ido. Tala kaina ciwo yake min sosai kamar zai tsage. Tala tayi saurin karasawa ta riketa har bakin gadonta. Sannu amarya ko na karbo miki magani wurin Anti Izzatu? A'a Zuhra tayi saurin dakatar da ita. Nima ina da shi. Kice su hawo nan bazan iya saukowa ba. Tala duk tausayin Zuhra ya kamata tace ba komai amarya. Kafin ta fita Zuhra tace ki dan taimaka musu da ruwan sha don Allah.

Tana fita Zuhra ta gyara kwanciya. Bata san ko su waye ba amma dai tasan gidan amare ana son a bawa baki dan abin kusa da baka. Ita kuma bata da komai, idan za'a bata ma karba zata yi.

Ba jimawa yan uwansu na Ajingi suka shigo. Kirikiri Zuhra taki tashi tana ta langabewa ita mara lafiya. Da muguwar rawa gwamma kin tashi. Anti Faiza ce ta rako su. Suna ta mata tsiya ko har an fara laulayi ne na kwana biyar. Ita dai sai murmushi take yi a dole taji kunya. Tala ta kawo musu ruwa harda lemo a jug da kofona. Basu dade ba suka ce gobe zasu koma Ajingi. Tayi musu godiya ta rakasu har kofar daki. Sai da suka sauka kasa Anti Faiza ta dawo da sauri take tambayarta yaya zaman nata. Kuka Zuhra tasa mata ta sanar da ita ko abincin kirki ba'a bata. Anti Faiza tace kiyi hakuri gobe za'a kawo gararki. Akwai kudi ne a wurinki? Zuhra ta share hawayenta tace eh Baba ya bani. Duka ta debo ta bata Anti Faiza ta dauki dubu goma a ciki ta bata sauran. Zanje kasuwa gobe kafin azo kawo garar zan zo in sha Allah. Ta dafa kafadarta...ki kara hakuri kuma kada ki bari Izzatu ta san ba kya jindadin zaman. Daga ita har mijin nata so suke kiyi abinda zai sakeki. Kuma In sha Allah kinzo kenan, yadda iyayensa suka yi miki kokari kema ki dage nemawar kanki wurin zama a zuciyarsa. Zuhra ta tura baki ni me zanyi dashi Anti? Ai kawai idan ya gaji ya sakeni. Anti Faiza toshe mata baki tayi. To banza na sake jin zancen saki sai na fasa miki baki. Biskit ta dauko guda biyu a jakarta ta bawa Zuhra sannan ta sauka kasa suka tafi.

Fitarsu ke da wuya Izzatu ta shigo tare da Tala. Zuhra tana kwance akan kujera ta gansu. Tashi tayi zaune tace lafiya cike da tsiwa. Fuskar Izzatu a daure tace ke kika ce Tala ta bawa bakinki ruwa da juice a jug dina? Zuhra ta kalli Tala tayi tsuru tsuru. Kiyi hakuri na zata mijinmu ne ya saya shiyasa nace ta taimaka ta kawo. Izzatu ta soma fada rai a bace...mijinmu fa kika ce? Yanzu Zuhra don baki da kunya sai ki hada baki da inlaws dina ki auri mijina kawai don kinga ina sakar miki fuska. To Tala mai aikina ce ni kadai kuma kada ki sake taba min kaya. Ignorant fool yadda kika zo haka zaki fita ki bar min gida. Zuhra tayi yar dariya ko na kwana daya ne Izzatu kin taba zama da kishiya a tarihin rayuwarki. Izzatu ta tsaya tana kallon Zuhra..dama bata da kunya? Kwafa tayi sannan ta fita tare da buga kofar da karfi. Tala ta dauki tray din Zuhra na bata hakuri tace babu komai. Ita sai mamakin wannan aure na ubangidanta take da yadda suke wulakanta amaryar. Zuhra tayi murmushi ko ba komai yau ta dan gasawa Izzatu magana taji dadi.

Daren ranar ba'ayi girki ba ana jiran Hamza ya kawo abinci daga tantalizers. Da yake bai fito office da wuri ba abincinsu ya kare sai snacks ya siyo. Yana

Please Login or Register in order to submit comment