Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gida. Tashi yayi ya bita dakinta sai dai a rufe yaji dole ya koma ya kwanta. Da kyar ya iya bacci saboda yunwa.

Washegari saboda tana fushi bai sami breakfast ba. Da yayi magana tace ta dena girki sai ya janye maganar party. Shi kuma yace ta bashi atm card dinsa na wurinta maganar soke party babu fashi. Baram baram suka rabu. Har mamanta ta kira a waya ta fadawa tace kada ta damu idan bata da kudi ne zata turo kaninta ya kawo mata.

Hamza gani yayi an cigaba da shirye shirye. An siyo katons din lemo da ruwa. Ga gifts duk an gama hadawa a wata jaka mai hoton Nana duk an ajiye a store. Ya sake wa Izzatu magana tace ai ba kudinsa bane. Maganar Mama ya sake bi ya kwashe yaran ya kaisu gidansu.

Su Hajiya sunyi mamaki da farinciki ganin Hamza yaji maganarsu. Aka sa Ibrahim dasu Mariya suka kawo nasu yaran. Tuni su Khalifa suka saki jiki cikin yan uwansu. Idan suna Hausa sai ka rantse daga turai suka dawo. Kwatakwata basu iya sosai ba ,sai turanci. Nana kuwa dama bata iya magana sosai ba. Tunda suka zo ta likewa Adabiyya take kiranta Anti Adab.

Izzatu tayi mamaki da ta dawo daga supermarket ta tarar yaran basa nan. Tala ce ta sanar da ita sun fita da daddynsu. Sai dai tasha takaici da ya dawo shi kadai yace a can zasu kwana. Tasan saboda maganar party ne. Tayi ta rokonsa da koke koke duk a banza. Har zaunar da ita yayi yana mata nasiha amma ta kafe. Shi kuwa yace indai zata iya zuwa gidansu ta dauko yaran shikenan. Bata san gatse ba ta tafi ana sauran kwana biyu sai dai ta tarar duk sun tafi Kumo. Babu kowa a gidan sai maigadi. Kuka kam ranar ba'a magana. Izzatu tayi fushi sosai da Hamza tare da alkawarin sai ta rama duk ranar da dama ta samu.
[9/25, 3:31 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿13

Batul Mamman(Mrs)💖




Fada sosai Hamza da Izzatu suka yi sai da kyar ya samu ya rarrasheta suka daidaita. Amma kudirin ramuwa yana nan a ranta, dama kawai take jira.

Kusan wata biyu suna zamansu lafiya. Architect Hamza na kokari wurin cigaba da kulawa da iyalinsa. Su Hajiya ma yana wadata su da abubuwan bukata. Hatta kawunsa da aka kora aiki sai da ya aika masa da dubu dari. Hajiya taji dadi sosai har waya tayi masa abinda bata yi sai da dalili saboda dan fari ne tayi masa godiya. Wannan wayar tasa shi jindadi mara misaltuwa. Shiyasa ya cigaba da yin abinda zai kyautatawa iyayensa. Itama Mama taji dadi ya dauki shawararta don Izzatu bata nuna musu bacin ranta game da tafiyarsu Kumo da 'ya'yanta ba.

Zuhra an gama koyon saka Baba ya kukuta ya siyo mata injin saka tsoho ne ma amma bai lalace ba. Tayi murna sosai shiyasa sakarta ta farko shi da ummanta ta fara sakawa rigunan sanyi masu kyau da kauri har uku uku. Duk da suna tsokanarta taki karatu amma sakar tayi kyau sosai. Umma ta bata shawarar duk lokacin da aka bata kudi ta sayi kulu tayi sakar ta ajiye kafin lokacin sanyi tunda ya kusa sai tq sayar.

Wata rana Hamza ya fita zuwa gidansa da suke shirin komawa tun safe saboda aikin yazo karshe. Gida ne da ya tsara komai na ginin da kansa sannan kamfaninsa ke ginin. Izzatu tana kitchen yayarta dake aure a Alaska ta kirata a waya. Suna hira ne Izzatu ke tambayarta ina yaranta. Zeenatu tace sun fita da babansu siyan kayan da zasuyi amfani dasu na HALLOWEEN. Izzatu tace kai sis har kin tuna min lokacin da muke siyan namu da Daddy. Gaskiya ba karamin missing America nake yi ba. Zeenatu tace ba kinga dan fillo duk kin rude ba. To amma meyasa bakiyi a nan? Hmmm kinsan yan Nigeria da kauyanci kada ma yan kauye suji labari. Gidadancinsu yayi yawa...ko kin manta yadda muka yi da inlaws dina game da birthday din Nana? Zeenatu tayi dariya haba Juliet din Romeo duk soyayyar taku har zakiyi korafi. Ba haka bane sis, abin ya bani haushi sosai. Amma gaskiya zamuyi halloween this year. Ba don yana wani aiki ba ai da dole mu taho sai muyi celebrating tare. Zeenatu tace muma zamu taho nan da December a gida zamuyi new year.

Bayan kwana biyu da wayarsu zancen halloween ya tsayawa Izzatu a rai. Lokacin da suna Canada da iyayenta suna celebrating tare sa sauran turawa. Nan da nan ta fara shirye shiryen yadda zasuyi nasu a gida. Hamza ta tambaya kudi don ya dena bata atm card dinsa. Tunda tace kaya zata siya bai hanata ba saboda rigimarsu ta party ta wuce. Washegari ta debi yara suka je manyan shopping malls din Kano da kyar ta sami abinda take so ta dawo rai a bace. Me zaayi da Nigeria abinda bai taka kara ya karya ba sai ka nema ka rasa. Washegari Khalifa ya tashi da zazzabi dama mura yake suka fita wannan siyayyar. Abu kamar wasa sai da suka kaishi asibiti da daddare, sai da safe aka sallamesu bayan an gama kara masa ruwa. Da suka dawo ne wurin karfe takwas ya kira Mama ya sanar da ita.

Ranar ta dace da talatin da daya ga watan october wadda a irin wannan ranar ne turawa suke yin halloween. Izzatu bata fadawa Hamza ba domin bata dauki abin a cikin irin wadanda ya hana ba tunda ba gayyato mutane zata yi ba. Ita da 'ya'yanta zasuyi abinsu a gida. Bayan Hamza ya fita tasa Tala tayi musu wanka ta koma kitchen. Ita kuma ta dauko musu kayansu da ta siyo ta saka musu. Harda Khalifa mara lafiya. A ka'idar wannan rana ta halloween wadda take da sunaye da yawa harda Day of the Dead ana yin abubuwa masu yawa. Nasara mabiya addinin kirista suna celebrating wannan rana ne domin tunawa da matattunsu. Kamar waliyai, manyan masu bauta da shahidansu. Ana saka kaya na ban tsoro a ranar kamar riga mai alamun jini, fuskar shaidanu, yin shigar da baza'a gane mutum ba, tsorata mutane a gidajensu ko waje, zuwa wuraren ban tsoro kamar makabarta, tsohon kango ko gidan da babu mutane. Kai hatta horror films(fim na ban tsoro) ana gani a wannan ranar ko ka ziyarci malamin duba da sauran abubuwan firgici dai. Haka halloween yake ko kadan bashi da alaka da musulunci. Amma wani lokacin musulmai yan uwammu idan suka sami kansu cikin yahudu da nasara sai kawai su dauki al'adunsu suna ado dasu ba tare da sunsan ainihin dalilinsu na girmama ranar ba. Zama a kasar waje ba shine dalilin da zaisa mu dauki dabiar nasara wadanda suka bata da yahudu wadanda Allah ke fushi dasu ba. Allah Ya tsare mana imanimmu. Amin

Izzatu ta sakawa Khalifa da Junior kayansu. Rigace mai dogon hannu da dogon wando duk sun dame musu jiki ga kuma fuska wadda aka fitarwa hudar idanu da wurin numfashi. Kayan bakake ne. Idan daga nesa ka hangosu zaka rantse kwarangwal ne saboda zanen kayan da yanayinsu. Bayan ta shiryasu ta daukesu hoto ta turawa Hamza a waya. Daga nan taje ta dauko na Nana. Su kuma jajaye ne harda safar hannu mai alamar farata zako zako. Fuskar(mask) kuwa kamar ta aljanu harda kaho biyu a sama. Nana tana ta dariya Izzatu ta gama shiryata ta daukota zasu fito falo sai Nana tace Mummy poo. Izzatu ta san halin Nana bata kashi a pampers duk yadda za'ayi da ita. Dole ta cire mata ta zame mata wandon ta dorata a po ta tafi kitchen duba girki don shabiyun rana ta wuce. Junior da Khalifa suna falonsu suna kallon cartoon.

Tana kitchen taji sallamar su Mama. Da sauri ta fito tana musu sannu da zuwa. Duk su biyun rungume su tayi yadda ta saba. Hajiya sai dan yake take don wannan halin na Izzatu na bata kunya. Bayan sun zauna ta gaishesu Mama tace ina Khalifan? Ashe baiji dadi ba. Izzatu tace eh amma yau da sauki sosai. Zazzabi ne da mura. Hajiya tace to Allah Ya bashi lafiya. Mama tace kirawo shi mu ganshi. Dazu babansa yayi min waya da safe shine muka zo duba shi. Izzatu tace Tala ta dauko musu ruwa da lemo.

Tala na tashi Nana ta fara ihun Mummy na gama da dan gwarancinta. Izzatu tace jeki kiyi mata tsarki bari na kawo musu. Tashi tayi tana kiran su Junior su zo ga su Hajita ta shige kitchen.

Ba'a fi rabin minti da shigar Tala ciki ba ta fito falo tana ihu. Gabadaya jikinta rawa yake sosai tana kuka. Hajiya da Mama suka tashi a firgice suna tambayarta abinda ya faru. Cikin kuka tace mutanen boye sun bayyana. Mama tace su wa? Tala tace aljanun. Yau na gansu da idona ra'ayil aini har su biyu. Wallahi sai ga yarsu zaune akan po din Nana dayan kuma yana mata wasa. Na higa uku na lalace kwarankwatsa ko a kauyenmu ban taba gamo ba he yau. Izzatu ce ta fito da sauri daga kitchen tace ke Tala bana son rashin hankalin nan naki.
[9/25, 3:33 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿14

Batul Mamman(Mrs)💖




Tala ta zazzaro idanu tana kallon Izzatu. Na rantse ba karya nake ba. Hajiya da Mama sai kallonsu suke yi. Tala na maida zance suka ji kukan Nana tana kiran Izzatu. Tare duk suka yi hanyar inda suka ga Tala ta fito. Hajiya ce a gaba. Sai da cikinta yayi mugun kadawa saboda abinda ta gani zaune akan po yana miko hannu alamar ta dauke shi. Na kusa dashi kuma mai siffar kwarangwal ya rugo da gudu zai rungumeta. Da kyar ta iya cewa Hasbunallahu wa ni'imal wakil sannan tayi baya kamar zata fadi. Mama tayi saurin tareta itama a tsorace har ta fara tunanin kada aljanun su rufe kofar gidan su hanasu fita. Tala tace kun gani ko Hajiya ai na fada muku. Nana dai tasowa tayi ta nufo su shima Junior haka. Khalifa da yake kwance a daki shima ya fito saboda hayaniyar da yaji. Mama ta karewa aljanun uku kallo tace Hajiya gidan Yaya ba lafiya. Izzatu ce karshen shigowa tana ganin abinda ya kidima surukanta ta kyalkyale da dariya harda hawaye, karshe sai da ta kai kasa. Hajiya da Mama sai kallon kallo a zatonsu ma ko aljanun sun taba ta. Sai da tayi mai isarta suna kallonta sannan tace Hajiya su Nana ne fa. Kaya ne na saka musu yau halloween. A gabansu ta cire musu fuskar kayan tana mai cigaba da dariya.

Ransu Hajiya yayi matukar baci. Tala kuwa karasawa tayi gaban yaran tace Khalifa kaine tana tattaba musu jiki. Ta dago kai tace Hajiya ai kuwa su din ne. Mama ta dubi Izzatu, hallo...me kika ce? Izzatu tace halloween. 31st October ake yi. Lokacin da muna Canada muna yinsa sosai. Tsabar bacin rai Hajiya ta kasa magana ma. Karshen wulakanci da cin mutumci Izzatu tayi musu.

Mama tace Hajiya ai sai mu tafi ko, don banga dalilin zamanmu ba. Su Junior suna ta binsu suna cewa zasu bi su. Cikinsu babu wadda ta iya kula yaran saboda yadda zukatansu ke kuna. Izzatu tace muje falo ku sha ruwa don ita bata dauki shirunsu a matsayin bacin rai ba. Sun kai bakin kofa zasu fita idon Mama ya kai kan wani mutum mutumi mai siffar mutum kafarsa ta akuya ga kaho har a saman hanci. Shima duk cikin kayan kwalliyar gidan ne na halloween. Cikin Mama har murdawa yayi, gabanta ya fadi don abin ya bata tsoro har kafarta ta goce ta fadi kasa. Hajiya tayi saurin durkusawa ta taimaka mata ta tashi. Junior da Khalifa ma suna ta cewa sannu Grams. Ita kuwa Izzatu wata dariyar ce ta subuce mata. A ranta tace ko ba komai ta rama abinda suka yi mata na sa Hamza ya hana su party.

A fusace Hajiya ya dago kanta cikin zafin rai zata yiwa Izzatu magana Hamza yayi sallama. Ganin Mama na kokarin mikewa yayi saurin karasawa gabanta yana tambayar abinda ya faru. Dama zuciyar Hajiya a kusa take maimakon ta bashi amsa ta kwashe shi da mari. Falon a take yayi tsit Tala tayi saurin komawa dakin su Khalifa ta ga an mari ubangidanta. Falon yayi tsit Izzatu ta hadiye sauran dariyarta. Shi kuwa hannuwansa biyu yasa ya dafe kumatunsa ya dubi mahaifiyarsa a razane. Mama tace haba Hajiya ya zaki dauki hukunci kan wanda baiji ba bai gani ba. Murmushin takaici Hajiyan tayi tace tunda nake ban taba ganin wulakancin da yayi min ciwo irin wannan ba. HAMZA ka guji ranar da zanyi maka baki.....idanunsa sunyi jawur yana mamakin sunansa da ta fada da kuma dalilin bacin ranta. Yace da Izzatu me ya faru? Ta dan tabe baki babu komai. Don basu dade da zama ba suka tashi. Hajiya da Mama suka yi hanyar kofa yana ta basu hakuri da son jin abinda ya faru sunki sauraronsa. Har bakin mota ya biyo su. Sai da dreban ya tada motar sannan Hajiya tace wallahi in dai da raina da lafiyata Hamza bazan kara taka kafata nazo gidanka ba. Mama da yake tunanin zata bata hakuri ko kallon inda yake bata yi ba. Sai ma kwalla da yaga tayi saurin sharewa kafin motar ta fita daga harabar gidan.

Da sauri ya shiga gidan yana kwalawa Izzatu kira. Ta fito hankali kwance tace sweetheart abinci zaka fara ci ko wanka. Izzy kina da hankali kuwa? Ya dubi su Junior kai ku koma dakinku. Sai da yaran suka tafi yace idan naki iyayen ne suka fita haka zaki musu? Ki fada min gaskiya me akayiwa su Hajiya. Izzatu tace ni ban sani ba. Suna ganin su Khalifa suka kama hanyar fita. A daidai can ne mama ta dan fadi. Hamza yace ta fadi? Ya karasa yaga gunki a wurin ya dago shi..meye wannan kuma? Izzatu tayi yar dariya na halloween ne. Ka tuna sanda akeyi a Canada? Akwai da yawa naso gama jerasu kafin ka dawo. Ya ce wane irin hoto kika turo min dazu? Ni abinda ya dawo dani kenan. Izzatu ta riko hannunsa zo mu zauna babyna. Ta kira yaran sai a lokacin ya kula da kayan jikinsu. Na nana yafi tada hankali ya mike a fusace izzy dont tell me haka su Mama suka ga yaran nan. Tace haka suka gansu mana. So what? Dafe kansa kawai yayi yana karanta Innalillahi a zuci. A hankali yace Izzy don Allah ki ajiye al'adun wasu a gefe mu zauna lafiya. Yadda Hajiya ta rantse ta bar zuwa gidana na miki rantsuwa da Allah idan kika sake dauko min wani abu da bai dace da dabiar musulmi ba sai na bata miki rai. Bacin rai wanda sai kinyi nadamar aurena. Iya nasihar da zanyi miki nayi nima na gane rashin kyautuwar abinda muka yi a baya. Kina zaune lafiya da iyayenki baki isa ki rabani da nawa ba. This....ya nuna ta da dan yatsa is my last warning.
[9/25, 3:33 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿15

Batul Mamman(Mrs)💖




Yana gama magana ya tashi yana kwalawa Tala kira. Da yake tana labe a bayan kofa da gudu ta fito jiki na rawa yace jeki ki cire musu kayan nan ki kawo min mota ina jiranki. To kawai tace ta kwasa da gudu tayi ciki. Izzatu ta kalleshi itama rai a bace kudi fa nasa na sayi kayan nan. Me zakayi dasu?. Ya dan daga gira daya Allah ko? Tunda kudin nawa ne babu ruwanki da abinda zanyi. A iya zamansu basu taba samun sabani kamar yadda suke yi yan watannin nan ba. Kirikiri iyayensa ke nuna mata kiyayya amma zata yi maganin abin. Ta yanke shawarar bazata taba bari maganganunsu suyi tasiri a ranta ba har ta dena rayuwarta yadda ta saba. Ita tasan iyayenta sun bata tarbiyya irin wadda ta dace kuma ga yayarta da mijinta suna zamansu lafiya sai ita kadai ce zasu takurawa.

Horn Hamza ya rinka dannawa da karfi sai ga Tala kamar an jeho ta. Ta mika masa kayan. Har ya dan ja motar sai ya dawo ya sake kiranta. Ke fada min gaskiya me ya faru da su Hajiya suka zo dazu? Ai kamar jira take ta soma bayani dalla dalla. Dama banda tsoron da taji ba karamin mamakin Izzatu tayi ba da tayiwa surukanta dariya. Fuskar nan ta Hamza kamar bai taba dariya ba ya ja mota ya nufi gidan iyayensa.

Hankalinsa a tashe ya gyara parking din motarsa saboda yaga alamun Alhaji na gida. Yana shiga falo Adabiyya da Hamida ya gani suna kuka. Gabansa ya fadi yace ku meye haka? Adabiyya ta taso ta rungumeshi tana cigaba da kukan. Dama duk ta fisu raguwar zuciya. Hamida tace Mama akeyiwa gyaran kafa. Me kika ce??? A razane yake maganar tace gocewar kashi ta samu. Matsar da Adabiyya yayi daga jikinsa ya shiga falon Alhaji. Mama ya gani zaune a kasa tayi gumi sosai Hajiya na rike da hannunta. Kafarta ta hagu daure da wani farin yadi. Gefe kuma mai dori ne durkushe gaban Alhaji zai karbi kudinsa. Mai dorin yace in Allah Ya yarda gobe da safe zan dawo na duba. Allah Ya kiyaye gaba.

Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki haka Hamza ya karaso cikin falon. Mama ce kawai ke kallonsa, ita Hajiya kawar da kai tayi gefe. Alhaji Nasiru ya hade fuska kana ganinsa kasan yana cike da bacin rai. Kusa da Mama Hamza yaje ya zauna ta riko hannunsa kawai sai ta soma kuka. Hajiya ta tashi zata bar falon Alhaji ya dakatar da ita. Hamza yace Alhaji barka da rana. Muryarsa har rawa take bata fita sosai. Alhaji yace Hamza.....toh fa yau duk su biyun sun kira shi da sunansa. Allah gani gareKa yace a zuci. Naam Alhaji. Alhaji yace dago kanka ka kalleni.

Kasawa Hamza yayi. Alhaji yace ashe kana da sauran kunya. Dubi yadda iyayenka suke kuka saboda bacin ran da suka kwaso a gidanka. Yau Mamanka ce a zaune ana mata gyaran gocewar da tayi a gidanka matarka tayi mata dariya. Wace irin rayuwar aure kuke yi kai da iyalinka? Me kake son nunawa duniya game da tarbiyar da muka baka? Ba don tsarewa ta Allah bace duk kannenka koyi zasuyi da irin dabiun da ka kwaso a turai. Alhaji ya cigaba da cewa duk irin abinda kuke yi babu wanda ban sani ba amma na kawar da kai saboda iyayenka basu tunkareni da maganar ba. Na basu damar su ta iyaye mata su saita ka a hanya kuma nasan sunyi iya kokarinsu. Amma yau saboda abin yayi yawa Halimatu da kanta ta sanar dani abinda yarinyar nan tayi musu. Wulakanci na karshe Izzatu tayiwa iyalina amma bazan umarceka da rabuwa da ita ba. Sai dai ka sani wallahi nayi maka rantsuwa ranar da duk kuka sake aro daga munanan al'adun wasu har kunnena ya jiye min ko ido ya gani zanyi maka hukuncin da baka taba tsammani ba.

Da sauri Hamza ya kalli mahaifinsa don Allah kuyi hakuri Alhaji. Nasan nayi kuskure tunda da goyon bayana komai ke faruwa. Amma in Sha Allah zan gyara kuma yanzu zan daukota tazo ta bada hakuri. Hajiya tayi saurin cewa ban yafe maka ba muddin kace mata tazo bada hakuri. Indai hankalinta da tarbiyarta basu nuna mata abinda ya kamata ba shikenan. Alhaji yace ina zaune kike irin wannan zancen Halimatu? Tace ayi hakuri. Hamza ya dubi Mama wadda kanta yake a kasa ki yafe min Mama don Allah. Abinda ya faru yau ko kadan bani da masaniya a kai. Alhaji yace halo me ma kuka ce sunan abin? Hajiya tace yo ni ina zan rike. Kamar ba kalmar turanci ba, yau na fara jinta ma. Hamza ya sake dukar da kai ko a da bama yin wannan ranar bansan dalilinta na yi ba yau. Alhaji yace dalilinta ya wuce ta tozarta min iyali ne? Ka tashi ka tafi Allah Ya kyauta.

Hamza dai kin tashi yayi ya kara matsawa jikin Mama yana rokon ta yafe masa. Murmushi kawai tayi tace masa ka tashi ka tafi ba komai. Duk yadda yaso Mama taki tsawaita magana. Hajiya tace ka tashi ka bamu waje magana ta kare. Idan ka fita ka turo min Adabiyya da Hamida. Jiki ba kwari ya fita ya turo su. Hajiya tasa Adabiyya sake gyara gadon Mama , ita da Hamida suka kamata suka kaita daki.

Zuwa dare su Ibrahim duk sun zo gidan da iyalansu. Kowa yayi bakin cikin jin abinda Izzatu tayi musamman dariyar. Ummahani matar Ibrahim tace ni Yaya tausayi yake bani. Jidda tace tausayin me? Ba fa auren hadi bane da kansa yaje ya kwaso mana ita. Mariya tace kuma dashi suke komai ba. Dama matsalar ka fara abu kenan. Sai kaso denawa mabiyanka suce basu san zance ba. Motoci hudu ne a gidan Yaya amma ko keke bai siyawa ko da Nura ba da yake karatu. Irin abinnan ka daukewa iyaye wani nauyi ko a jikinsa. Daga shi sai iyalinsa. 'Yan kwanakin baya ne ma naga abin ya dan canja. Mama dai tana daga kwance tace ku bar zancen nan haka.

A haka sai da Mama tayi sati uku a kwance saboda banda gocewar tayi ta fama da zazzabi. Kullum safe, rana da dare Hamza sai yazo. Da daddaren ma da su Khalifa yake zuwa. Izzatu kuwa tunda baice tazo suje dubiya ba itama ta share. A ganinta yan uwansa ne bazata masa shisshigi ba. Wani lokacin ya hadu da kannensa wadanda suka hade masa kai. Daga gaisuwa basa kara yi masa wata maganar. Su Hajiya suna amsa masa gaisuwa amma suma daga nan magana ta kare. Rashin kula shi da Mama keyi duk yafi komai tada masa hankali. Bashi da aiki sai bada hakuri sai dai tace masa babu komai.

A haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya har suka dan daidaita. Mama ce dai har yanzu bata yi masa kamar da. Shi kuwa bai kosa da yi mata siyayya ba kullum. Domin yanzu ya dauki irin abinda Ibrahim yake yi tun bayan yayi aure. Kullum sai yazo gidan ya gaishe da iyayensa ko da safe kafin yaje aiki ko bayan magariba.
[9/25, 3:34 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿16


Batul Mamman(Mrs)💖




Wata asabar da safe Izzatu ta nemi izinin Hamza tana son zuwa Abuja tunda su Junior na hutun makaranta wurin iyayenta. Ya amince har ya bata dubu hamsin ko zata yi siyayya sannan ya cika mota da mai yasa dreba ya kaisu. Ashe new year celebration taje gani. Sauran shekarun duk tare suke yi da Hamza, ganin yadda lokaci guda ya canja mata yasa bata sanar dashi gaskiya ba. Da yaran ta tafi suka je kallo tare da kannenta. Bayan sati daya suka dawo gida.

Zuhra ce take tafe da katuwar ghana must go shake da kayan sanyin da ta saka. Yanzu ta kware sosai don sanyin da ya wuce tayi ciniki sosai. Da yake farkon March ake gari ya soma zafi. Sai dai mijin Anti Faiza ya samar mata wata makarantar primary sun bata kwangilar sakar rigunan sanyin dalibai. Murna sosai su Baba suka yi. Ta gama na farko shine zata kai musu. A daidai wani lungu zata wuce bakin titi ta hango Anas da abokinsa Sani suna busa wiwi. Idonunta kyam a kansu, Anas ne ya fara hangota yayi saurin taba sani. Dukkansu kashe tabar suka yi suna murmushin yake. Fitowa suka yi daga lungun Sani yace kaga manyan yan mata. Zuhra ina zuwa haka da rana? Ta karkace kai tana kallonsu wai nan bagarar dani zakuyi. To nagani kuma sai na fada. Anas yace don Allah kada ki fadawa Baban yara. Kinga muje mu rakaki inda zakije ma. Sani ya karbi jakar zai daukar mata. Da sauri ya mayar ya ajiye...ke yanzu tun daga gida kika dauko jakar nan. Zuhra tace eh menene? Sani yace Anas dauki ka ji. Anas ma dagawa yayi ya mayar Zuhra haka kike da karfi. Wani murmushi ta saki da yasa duk munin kwalliyarta tayi kyau. Au ku da rainani kuke yi? Ai kada ku taba bari dambe ya hada mu don kasa zan kaiku. Sani yace ke dalla can wa ya fada miki maza na son mata karfafa. Ko ni naji nauyin jakar bare ke. Wallahi

Please Login or Register in order to submit comment