Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni da Hajiya. Ya san ba kudin ko abincin muka rasa ba. Amma yana neman albarkar iyaye. Mariya da Jidda suma suna nasu kokarin da dan abinda sukeyi. Duk cikinsu kafi kowa morar Alhaji kuma ka fisu kudi amma daga kai sai iyalinka. Kawaici kawai mahaifinka yake maka irin na bafillatani amma ko kadan baya jindadi. Shin ka taba zama ka tambayeshi a halin da kamfaninsa yake ciki? Ko ka tambayi Hajiya me take bukata ko da ba na kudi bane? Hamza ya girgiza kai a hankali. Mama bata san cewa tana fadan ma hawaye take yi ba. Tace to girma ya kama babanku. Ibrahim lecturer ne amma daga wurin aikinsa yana zuwa kamfanin taya shi aiki. Nura yanzu yake ajin karshe a jamia amma tun yana level one yake zuwa. Hamza yayi mamaki wai Nura har ya kai level four yanzu sai dai bai nuna ba kada fadan ya karu. Ita kuwa Mama cigaba tayi da fadanta. Yan uwanku na Kumo makusanta. Ina nufin yan uwan Hajiya da na Alhaji kasan halin da suke ciki? Ko kasan a rage maaikatan banki harda kanin Hajiya. Hamza ya dago kai wanne? Tace Nafiu. Gashi yana da mata biyu da 'ya'ya goma sha uku. Watansa kusan bakwai ba aiki. Akan Nafiu Hajiya ta soma kukan rashin taimakon da kake yi. Maganganun sun ratsa Hamza sosai. Ji yayi kamar wanda aka tasa daga bacci. Mama tace ni dai lahirarka nake duba maka Yaya. Rayuwarka nema take ta sauka daga turbar addini. Har yau ban manta yadda Izzatu tasha maganin hana haihuwa ba wai sai ta gama karatu. Allah ne ma Yaso kuna da rabon haihuwar daga baya. Ka tashi ka je ka bawa Hajiya hakuri ka tafi dare yayi. Hamza yayi godiya sosai tare da sake bata hakuri. Har ya kai bakin kofa tace Yaya....naam ya amsa. Nasan saura baifi sati biyu ba birthday din Nana. Kwana hudu kafin ranar ka dawo dasu nan. Wallahi ka sake celebrating birthday a gidanka zaka ga fushina sosai.. Allah Yayi muku albarka
[9/25, 2:51 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿10

Batul Mamman(Mrs)💖





Zuhra ta shigo layin gidan Anti Faiza sai ta hango mai tsamiyar biri yana turawa a baro. Tsallakawa tayi bangaren da yake zata siyo. Dama tana ta tunani yar tsarabar da zata kaiwa su Abba.

Hamza da Izzatu suna mota suna hira tana fada masa Inuwa sakatare ya kira yaji ya jikin Junior fa. Dariya sukayi yace kin mayar dani makaryaci dai. Khalifa ne ya hauro daga baya ya dawo gaba ya zauna kusa da Izzatu. Ta juya ta harari maiaikinta. Ke Tala garin yaya kika bari ya taso har ya dawo nan. Oya Khalifa koma wurin zamanka. Ko kulata baiyi ba yace daddy ka kawo na tayaka driving. Hamza yace not today Khalifa kaga anyi ruwa jiya titin babu kyau. Kuma akwai mutane a nan. Khalifa yace ko sau daya ka bari na dana. Izzatu ta kama shi zata mayar bayan mota yasa ihu tare ta riko wuyan Hamza. Iyakar karfinsa yasa yana jan babansa. Garin ya cire hannun Khalifan ya dan dauke ido daga kan hanya.

Tana tura ledar tsamiyar birin a jaka taga mota ta yo kanta. Hantar cikinta ta kada ta rasa ina zata yi ma. Gabadaya ta rude kafafunta sun kasa daukarta. Da kyar Hamza ya iya tsayar da motar bayan ya shigar da ita cikin wani ruwa da ya kwanta a gefen titi. Har fuska ruwan ya watso wa Zuhra sannan ta zame ta fadi a zaune cikin ruwan.

Karshen bacin rai kam taji shi a lokacin. Musamman da ta hango mai tukin da yaro suke kicikici da sitiyarin motar. Da sauri Hamza ya tura Khalifa wanda yake ta kuka cinyar Izzatu ya sauke glass din motar yana duban Zuhra. Leko da kansa yayi zai bata hakuri sai dai akayi rashin sa'a kwalliyar fuskarta ta bashi dariya. Izzatu da Tala ma da suke cikin motar sai da suka yi saboda yadda lebenta ke daukar ido. Ita kuwa Zuhra haushi ya kara kamata. Hamza ya dan daure amma fuskarsa dauke da murmushi yace don Allah kiyi hakuri kinji. Yaro ne ya rike sitiyarin Allah Ya kiyaye ban tabaki ba dai ko? Zuhra ta tsuke baki ban sani ba...don tsabar wulakanci kayi min wanka da kwatami sannan ka wani kame a mota kana tambayar ko ka tabani. Hamza ya dan sha kunu jin abinda ta fada yace to naji kiyi hakuri don Allah. Ya zaro kudi a aljihunsa ya mika mata dubu biyar. Gashi ki sayi sabulu. Ganin ya tayar da motar ta kama hannun gefen inda yake zaune ta soma masifa. Amma kai baka da mutumci wallahi...tana kallonsa tana kallon kudin. Kudinka me zasu min. Malam ka fito ka duba ko naji ciwo ka kaini asibiti. Izzatu ta dan leko kiyi hakuri kinji, kinga yaron da ya jawo, ta dungure Khalifa. Maganar Zuhra ta bawa Hamza haushi yace idan bazaki karbi kudin ba sauri nakeyi. Kin samu na tsaya zaki rinka yi kin rashin kunya. Zuhra tace anyi din, nace anyi din kuma Allah Ya isa abinda kayi min. Ka wani makale a mota kai mai kudi ko. Yadda take magana ya sake bawa Izzatu dariya. Haka kawai yarinyar ta burgeta. Hamza kuwa harararta yayi sannan cikin fushi ya fito daga motar. Tun kafin ya karaso tsoro ya cika mata zuciya. A gabanta ya tsaya ta daga kai ta kare masa kallo. Tabdijam...da kyar in kanta zai kai kafadarsa ma. Ta hadiyi yawu da kyar. Mutumin duk da bashi da kiba amma dai baya sahun masu rama, gashi da tsaho. Idanunta suka kawo ruwa don kallon da yake mata ba na wasa bane. Idan ya dake ta kuwa ya daki banza. Ya dan rage sautin muryarsa ke kinga nayi kama da sa'anki ne? Ta girgiza kai. Yace to ina baki hakuri sai ki rinka yimin rashin kunya. Izzatu ta dan bude kofa tace babyna ka taho mu tafi kawai. Zuhra ta zaro ido ta kara kallonsa....baby kuma? Katon gardi da kai a kiraka baby. Lallai an cuci kalmar nan al'quran. Ran Hamza ya sake baci ya daga hannu zai mareta. Tace kana tabani zanyi suman karya a wurin nan sai mazan can sun taru. Kuma in fada musu abinda kayi min. Daga kai yayi ya kalli kofar kantin da ta nuna yayi murmushi yace bismillah. Zuhra ta dan ja da baya da gaske nake fa...shima ya kara matsawa gabanta ai ban hanaki ba. Ta tabbatar dai ba wasa yake ba kawai sai tace Allah Ya isa da karfi ta kwasa da gudu.

Binta yayi da ido sannan yayi tsaki. Idan ya sake ganin yarinyar nan sai jikinta ya gaya mata. Shi zata yiwa Allah Ya isa har sau biyu. Yayi kwafa ya shiga mota. Izzatu sai dariya take. Yarinyar kamar wata clown. Ita fa gani take tayi kwalliya karshe ko? Hamza yayi tsaki yanzu duk abinda ta fada min bai dameki ba Izzy sai ki rinka dariya. Tace ai abin naku ne da ban dariya. tayar da motar yayi don idanun Izzatu suna ga yarinyar da ke gudu ba maganar da yake ba. Tana kallo har Zuhra ta fada gidan Faiza....
[9/25, 2:52 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿9


Batul Mamman(Mrs)💖




Tunani ne duk ya ishi Hamza har ya isa gida. Tabbas ko makaho yasan kasarmu tana cikin matsi a wannan yanayin da muke ciki. Sai fatan Allah Ya kawo mana sauki. Amma a haka duk shekara basa rasa dalilin yin taro a gidansu. Duk da hakan ba ra'ayinsa bane tun farko amma ya goyi bayan Izzatu akan duk abinda take yi. Dole ne kuma ya nuna mata kuskuren rayuwar da suka daukarwa kansu ko don inganta tarbiyar 'ya'yansu. Kila mutane suna ta zaginsa bai taba tunanin haka ba sai yau. A haka ya isa gida zuciyarsa duk ba dadi. Izzatu ta gama gyaran dakin yana ta kamshi ita kanta ta yi kyau sosai tace ya shiga yayi wanka.

Inuwa Sakatare ya karanta takardun gabansa yafi a kirga. Yana son sanar da ogansa amma yana tunanin kada ya zama ya nuna rashin damuwa akan lalurar Junior. Daga karshe dai text ya tura masa wanda ke dauke da cikakken bayani dangane da yarjejeniyar dake tsakaninsu da turawan. Kusan minti goma ba reply sai kawai ya kira wayarsa. A lokacin Hamza na wanka. Izzatu na kallo har wayar ta tsinke aka sake kira har sau hudu. Tayi tsaki ta dauka. Bata son abinda zai bata romantic night din da ta tsara musu ita da mijinta. Gashi baya yarda da kashe waya komai dare. Inuwa ya gaisheta ya tambayi jikin Junior tayi dariya kawai tace da sauki. Yace na turowa Oga sako ne nake son tambayarsa ko ya gani. Izzatu tace yana wanka amma zan sanar dashi. Inuwa yayi godiya yace sai da safe. Har ta ajiye wayar ta dawo ta dauka. Tasan halin Hamza kafin ya kwanta sai ya duba sakonnin wayoyinsa mai bukatar reply ya tura. Ita kuwa daren yau na tunawa da ranar aurensu ne. Bata bukatar duk abinda zai dauke masa hankali. Duba sakonnin mail dinsa tayi duk ta bude su a matsayin an karanta haka ma na whatsapp. Text kuwa banda na Inuwa duk sauran na etisalat ne da mtn. Gabadaya ta hada ta goge harda na Inuwan saboda daga farkonsa taga an rubut RANKA YA DADE YA JIKIN JUNIOR......iya nan ta gani ta goge ta saka masa wayoyin a chaji. A tunaninta text din dubiya ne. Da ya fito ya duba wayar babu wani abu mai mahimmanci sai kawai suka yi shirin kwanciya....

Zuhra ta dawo daga islamiyya tana ta zumbura baki. Sallamar ma a ciki ciki tayi. Umma tace waya taba uwar masu gida? Jakarta ta jefar a kan tabarma ta cire hijabin ta kwanta. Umma yunwa nake ji kamar naci babu. Baba ya fito daga bandaki da buta a hannu yace Allah Ya rabamu da babu. Shine zaki wani kwanta kina turo baki. Ji don Allah kamar ba mace ba. Kin wani kwanta a kasa. Ji gaban rigarki ma kamar manja. Ya taba kitsonta da tsagar har ta bace don tsufa...yanzu kan nan yaushe rabonsa da ki wanke shi? Wai wa zan samu ya aureki a haka? Ba kwakwalwar karatu ga rashin jure yunwa. Gaki ba wani kyan azo a gani ba. Da nayi kudi ne ma sai a aureki ko don nauyin aljihuna. Zuhra ta soma shura kafafu Umma kinji Baba ko? Ai dai kai na biyo wallahi. Yace wa? Ni? Haba yarinya don kinzo na fara tsufane. Tambayi Ummanki lokacin da nake matashi yadda mata ke bina. Umma tana wanke shinkafa tana musu dariya. Zuhra tace har tafiyarmu iri daya fa. Baba yasa dariya ai kuwa da kinji kunya ace budurwa kamarki tana tafiyar maza. Maganin farinjini zan nema miki. Tunda karatun yaki sai ayi auren. Maganarsa ta sake tunzura Zuhra har ta soma hawaye tace Umma ina kama dake ko? Umma ta rike baki tace ta ina? Ni duk gidanmu babu mai kyau na. Ke kuma da Babanki kike kama. Kaga Sima yar gidan Malam Basiru. Dariya sosai suke yi mata tana ta kuka. Ta tashi ta shige daki. Baba yace kinga kin batawa uwata rai ko. Umma tace don na tayaka?. Amma maganar gaskiya rashin saurayin Zuhra na damuna. Maikifin bakin layi ne kawai yake zuwa kuma tace bata son shi. Baba yace nima abin na damuna. Bata son kula da tsaftar jikinta ne kuma da laifinki. Umma tace akan ta tsefe kanta har dukanta nayi. Lokaci na bata zuwa wani satin tana bacci zan sa mata almakashi kowa ya huta. Baba yace wallahi ban yarda ba. Da nayi saa ta gado irin gashinki mai dan tsaho kuma sai ki aske. Ba gidan Faiza zata ba bayan azahar...Umma tace can zata je. Baba yace to kice ta tafi da kaya ko biyu ne ta kwana. Kinsan halin Faiza ko taki ko taso sai tayi tsifar nan. Zuhra na jinsu daga daki ta leko ta taga na fasa zuwa gidan Anti Faizar. Umma tace kunfi kusa ai.

Sai da ta gama cin abinci ta sha ruwa sannan ta dauko hijab ta saka da kullin kayanta a dankwali tace Umma zan tafi. Baba ya harareta a haka Zuhra... Islamiyya fa kika je ko wanka bakiyi ba ki ka saka kaya. Ji hijab din ko guga babu. Ke ko irin gayun mata baki iya ba. Ki dan saka kayanki a yar leda zaki kulle a dankwali. Yarinyar nan da a kauye muka tashi bana jin zaki taba wayewa. Gaskiya Umman Zuhra bakya kyauta min. Kin bar min yarinya ta zama borar karfi da yaji. Umma tace ai kana gidan kana ganin yadda nake fama da ita.

Baba yace zo ki zauna kinji Fadimatu. Ta zauna bakin nan kamar ya zunguri kofa saboda yadda ta turo shi gaba. Yace yanzu don Allah idan ke namiji ce kika ga mace irinki zaki so ta? Tace eh to ya danganta da namijin. Baba yace ni bance sai mai kudi ba amma dai Zuhra a sami rufin asiri. Ke kadai fa Allah Ya bani dole na so ki da alkhairi. Dazu kina cin abinci lomarki har tafi tawa. Itama dariya maganar ta bata. Ta sunkuyar da kai. Baba yunwa naji sosai a lokacin. Yace to abinda zai faru nayi miki alkawarin waya mai kyau harda kemara indai zaki rinka tsafa. Alhamdulillah Zuhra tace da karfi tare da fadawa jikin Baba tana godiya. Yace dagani duk gidannan kinfi kowa nauyi saboda cin ki. Ta mike tsaye tana tsalle daga yau zaka ga canji Baba. A wurin ta cire hijab da dankwali ta kama zanin zata kwance Baba yace shiga daga ciki dai yana kawar da kai. Ta wuce da tsallenta kamar karamar yarinya. Baba yace da Umma kin kula da hannun rigar mamanta kuwa? Dandakuwa..... Umma tace Baban Zuhra ka fiye gane gane kaima. Allah Yasa canjin ya dore dai. Kusan minti goma sai gata ta fito da daurin kirji da gashinta buzu buzu. Ta dauko kwandon wankanta da yar robar shampoo ta wuce bakin rijiya ta debi ruwa bokiti biyu. Suna nan zaune ta fito bayan kusan rabin awa tayi wanka da wanke kai. Umma tace har kin danyi haske kuwa. Bata ce komai ba ta shige daki.

Tasha wahalar taje kanta sosai saboda tsabar cikarsa. Ta shafa mai a ko ina ta raba biyu tayi kitso manya. Ta shafa mai a jikinta da body spray din da Baba ya siyo mata. Ba wani abu ke sawa bata amfani dasu ba, ita a tunaninta idan basu kare ba Baba zai ajiye kudinsa yayi wani abin dashi. Tana matukar tausayinsa saboda lalurar hannu da ta same shi.

Sai da akayi laasar ta fito fes da ita. fuska tasha hoda da janbaki orange, har girarta ta gyara. Baba kuwa baki yaki rufuwa da ya ganta bayan ya dawo daga masallaci yace ko ke fa. Allah Yasa ayi gamon alheri a hanya. Umma tace iyayen zamani ba kunya. Dari biyu ya bata kudin mota tayi godiya ta fita. Tafiyar ma kokarin daidaita kafarta ta rinka yi kada Baba yace tayi ta maza. Sai da ta fita Umma tace ba naga ka siyo wayar ba. Yace eh kyaleta muga zuwa kwana biyu sai na bata. Ki rinka sa ido tana gyara kanta. Ga iya zuwa islamiyya daukar karatu amma bata damu da tsafta ba.
[9/25, 3:23 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿11

Batul Mamman(Mrs)💖




Su Anti Faiza sun sha dariya da Zuhra ta basu labarin dalilin shigowarta a guje. Anti Faiza tace lamarinki sai addua Zuhra. Yanzu meye na rashin kunya bayan an baki hakuri? Zuhra tace yana daga mota fa yake bani hakurin. Ni dariyar da suka yi min ita yafi bani haushi. Hajara tace to ba dole suyi ba kin kama fuska kinyi mata zane. Ji girarki kamar an miki fenti. Zuhra tace wai haka Anti? Yau baki ga yadda Baba yayi murna ba har alkawarin waya yayi min. Daga nan suka cigaba da hira. Anti Faiza ta sako zancen bleaching tana musu fada. Zuhra tace nima hanata nayi har malama Rabia na tambaya hukuncin mai yi. Ta zauna tayi musu bayanin yadda suka yi da malama. Anti Faiza tace ato ni dai nasan kuna tare naji tsoro kada ta koya miki hali kinsan ance zama da madaukin kanwa.....

Bayan kwana biyu suna cin danmalele a falon Anti Faiza suka ji sallama. Zuhra ta kwaye zaninta har ana ganin cinyoyinta. Anti Faiza sai fada take mata basu ji sallamar ba. Abba ne ya amsa sai ga Izzatu ta shigo. Da yake Zuhra na fuskantar kofa tana shigowa suka hada ido. Sai da ta kware don tsoro sannan ta tashi da gudu ta shige daki. Anti Faiza cikin mamaki tace sannu da zuwa Maman Khalifa. Ganin Izzatu na kallon kofar dakin tana dariya tace wata kanwata ce mai shirmen tsiya. Izzatu tace ai mun taba haduwa. Ta baki labarin an kusa kadeta da mota shekaranjiya ko? Zuhra daga daki tana lasar hannunta da ya sha manja tace na gama yawo yau.

A falo Anti Faiza tace ba dai Alh Hamza ta yiwa rashin kunya ba? Ke Zuhra fito. Izzatu tace ba kararta na kawo ba. Ni ta burgeni ne ma. Don baki ga idanunta ba da ya fito daga mota. Yadda kika san ta saki fitsari a wajen amma duk da haka bata dena magana ba. Anti Faiza tace ai indai Zuhra ce ta wuce nan. Sai ki fito ki bata hakuri ta kira Zuhra daga daki.

A sanyaye ta fito ta gaishe da Izzatu sannan tace ku yi hakuri. Hajara tana gefe tana musu dariya. Izzatu tace ba damuwa. Ai ranar baki ga yadda yaji haushi ba. Har muka je muka dawo yana mita. Ni da zaki bini gidana ma ai da saka ku zanyi a gaba ina samun abin nishadi. Zuhra ta kalleta da mamaki. Yanzu nufinki baki ji haushin duk abinda na fada masa ba? Izzatu tace not at all. Zuhra dai bata gane dangantakar turancin da tambayarta ba, sai tace da nice wallahi fitowa zanyi daga motar in saita bakin mara kunya. Hajara ta dan taba Anti Faiza sannan ta kallo Zuhra alamun ayi mata magana. Izzatu ta ce ni bana son hayaniya nasan he will handle everything shiyasa na kyale ku.

Maganar ta bawa Zuhra mamaki sosai. Ace wata tayiwa mijinki rashin kunya kice baki damu ba. Gaskiya ke a mata daban ce....anti Faiza tayi saurin toshe mata baki. To sarkin shirme ance abinda kika yi babu komai kin dage sai neman jawo magana kike. Maman Khalifa don Allah kiyi hakuri. Izzatu tayi dariya ke babu komai fa.

Haka suka cigaba da hira Zuhra tana basu labarin Baba na son yi mata aure amma yace yafi son miji mai ilimi. Ni kuwa indai gida da abinci bani da damuwa. Hajara tace amma kika ki maikifi? Baki taba tsayawa gabansa bane shiyasa kike magana. Banda karni babu abinda yake. Anti Faiza tace wai kura ce zata ce da kare maye. Ke da ba kya minti uku kin gama wanka ai bai kamata ki guji dan uwanki kazami ba. Zuhra tace baki ji na fada miki Baba zai bani waya bane..ai daga yanzu zan rinka wanka sosai. Ita dai Izzatu har ranta shirmen Zuhra yana bata shaawa. Dalilinta kenan na zuwa gidan ranar don idan tana neman Faiza waya take yi mata.

Kwana hudu Zuhra ta yi a gidan suka koma tare da Hajara. Baba ya bata dubu shida yace ta kaiwa mai koya mata sakar. Cikin dan kankanin lokaci ta fara kwarewa saboda abu ne da take so. Ga tsafta an dore da wanka. Kwalliyar ce dai har yanzu da sauki. Baba ya cika alkawari ya bata wayar. Ranar murna ba'a magana. Haka ta rinka shiga makota tana nuna musu. Mamansu Hajara ma tayi murna. Don duk makotansu sunfi shakuwa sosai tamkar yan uwa. Tecno ce second hand ya siya a wurin wani dan layinsu. Da yake suna ganin girman Baban Yara kamar yadda suke kiransa ba karamin sauki mai wayar yayi masa ba.

Arch Hamza na zaune yana duba wasu takardu a office dinsa Inuwa sakatarensa yayi sallama ya shigo. Bayan sun gaisa yace ranka ya dade naji baka ce komai ba game da text da wayar da nayi maka. Hamza yace yi hakuri wasu abubuwan ne suka dauke min hankali. Izzatu ta fada min komai. Babu matsala nagode. Har kunya yake ji ace matarsa karya tayi. Inuwa yace ranka ya dade babu matsala? Hamza ya ajiye takardun ko dai akwai wani abu ne Inuwa? Shi a tunaninsa Inuwa ya gano Junior lafiya yake. A'a babu komai, dama wannan maganar ce kawai. Daga nan ya fita. Tunda Oga bai damu da yanayin contract din ba gara ya dena damun kansa kawai. [9/25, 3:29 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿12

Batul Mamman(Mrs)💖




Da daddare yana bacci yaji kamar ana taba shi. A tsorace ya tashi ya lalubi fitilar gefen gado. Zaune ya ganta ta dora pillow a cinyarta. Sweetheart ka tashi muyi magana game da birhtday din Nana. WHAT??? Shine abinda ya iya fada a hasale. Izzatu tace maganar birthday din Nana nace. Ya nuna mata agogo Izzy kinga time fa, uku saura na dare. Ta dan kwanta a jikinsa kullum ina son mu tsara komai baka dawowa gida da wuri. Jikinsa ya janye sannan yace saboda haka sai ki tasheni da tsakar dare? Haba Izzy! Tashin miji ayi magana a irin wannan lokacin ai sai a film. Indai maganar kirki ce ai ido biyu ake yinta. Ni naga irin haka is normal tsakanin couples. Idan abu na damun daya sai suyi discussing at night. Kasan kuwa na sake ganin yarinyar da kuka yi fada saboda ka watsa mata ruwa. Ashe kanwar Faiza ce. A wannan lokacin Hamza ji yayi tamkar ya saka ihu. Fuskarsa ko kadan babu annuri yace yanzu Izzy ki tasheni a tsohon daren nan saboda zancen birthday sannan ki ce kinga yarinyar nan? Did I ask you? Gobe meeting gareni da sassafe kuma na fada miki. amma sai kika zabi yanzu ki hanani bacci kuma ki bata min rai. Kallonsa kawai take yi....yau me ya sami baby dinta yake irin wannan fadan. Shi kuwa Hamza banda bacin ran gani yayi dama ta samu na bin umarnin Mama a soke maganar party. Yace ki manta da maganar wani party don an dena. Kina iya dafa abinci ki kawo a kai asibiti ko makarantar allo sadaka. Wannan karon ita ce nata ran ya baci. Wace irin magana kake yi ne? Yarinya duk na gama sa mata rai. Har kayan da zata saka ranar duk na gama siya. Hamza yace indai kaya ne ko gobe ma ki saka mata. Izzatu ta soma hawaye kada kayi min haka Hamza please. Yace meye na daga hankali, shekara biyu zata yi ai ba wayo gareta ba. Hawaye take sosai ya rungumeta yana rarrashi. Tace indai don na tasheka ne kayi hakuri amma kada kasa yan gidanmu suyi min dariya ko aga kamar baka da kudin ne. Bai san haka suka daukaki abin ba sai yanzu. Yace na gama magana Izzy no more parties. Ki duba a family dinku mai bukatar taimako sai mu bashi jari. Su Mama basa son abinda muke yi kuma nima na fahimci kuskurenmu. Ai ture shi tayi ta tashi tsaye. Dama nasan zugoka aka yi tunda ka fara magana. Na rasa meyasa 'yan gidanku basa sona. To wallahi sai anyi ko kana so ko baka so. Hamza yace ni kike fadawa haka Izzy? Yau daya don na hanaki abu shine zaki nuna min ban isa ba. Ba tare da ta bashi amsa ba ta fice daga dakin harda buga kofa.

Kansa ya rike ya zauna a bakin gado. Lallai yayi sakaci da har abin ya kai haka. Dole ya nemi yadda zai gyara gidansa don a zauna lafiya. Cikinsa ne ya murda alamun yunwa. Yau kamar sauran alhamis Izzatu batayi girkin dare ba. McDonald's tayi musu order. Soyayyan dankali aka kawo musu da kaza harda Tala da maigadi. Ko kadan Hamza bai koshi ba sai dai an saba irin haka wanda tun kafin suyi aure yayi mata alkawarin ware rana daya a sati kada tayi girkin dare zasu rinka ci a waje ko ayi order a kawo musu

Please Login or Register in order to submit comment