Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dole ta fara neman Zuhra tun kafin Hamza ya dawo kashinta ya bushe.

Daga bakin gate tayi parking ta fito ta tafi wajen masu karbar kudin shiga ta tambayesu ko sun ga wata mata da bata wuce shekara ashirin da daya ba sati biyu da suka wuce da daddare. Wanda ta tambaya yace ranar bashi bane da aiki amma bari a tambayi sojojin saboda yawanci a nan suke.

Da tafiyarta ta 'yan gayu ga takalmi mai tsini Izzatu tabi bayansa zuwa wurin sojojin. kafin su karaso yawanci duk sun taho wurinsu. Mutumin ne ya tambayesu abinda Izzatu tace ai kuwa wani gabjeje a cikinsu ya daka mata tsawa yace tayi kneel down a nan. Kamar ta saki fitsari don tsoro tayi abinda yace tana rarraba idanu. Ya kalleta sama da kasa yace...chege kaine ka bar kishiya a nan ko?


Izzatu tayi saurin girgiza kai alamun ba ita bace.

Wasu mutum biyu suka nunata da bindiga tayi saurin cewa nice, wallahi nice.

Katon yace dama kaine kawai zaka ki zuwa nemanta sai bayan two weeks. Mugu yau sai munci ubankaaaa. Ya fada yana wata irin dariya mai ban tsoro.

A take Izzatu taji saukowar fitsari daga mararta saboda tsabar kidima.
[10/23, 5:48 PM] +234 806 611 3313: AL'ADUN WASU 75

Batul Mamman(Mrs)






Wani soja musulmi wanda baiji dadin lokacin da suka sa Zuhra cire hijab ba, don babu yadda zaiyi ne saboda yadda ake amfani da hijabi ana cutar mana da addini da sauran musulmi. Muguwar harara ya dankarawa Izzatu sannan yace banda kneel down ta daga hannu sama. A dole tabi umarninsa babu inda baya rawa a jikinta. Tana daga hannu mayafinta yayi sama sai ga shatin fitsari a jikin zanin shaddarta. Kafin ta ankara ta rufe wurin sun gani suka rinka dariya. Sauran mazan dake gefe ma dariyar suke yi. Izzatu yau taga wulakanci irin wanda bata taba gani ba.

Daga nan suka rinka yi mata fada akan me zata bar yarinyar mutane a airport da tsakar dare. Ita dai Izzatu babu bakin magana bare ta tambayesu ina suka ga yarinyar tayi.

Su Khalifa ne suka hango mamansu daga cikin mota a wannan yanayi suka soma kuka. Wani soja da yaso sata tsallen kwado ya kula da yaran ya fadawa ogansu. Ogan yace to albarkacin yaran nan ta koma motarta da rarrafe sannan sun bata sati daya ta nemo kishiyarta ko su zo har gida su tafi da ita.

Abin tausayi haka Izzatu ta rinka rarrafe akan gwiwarta duk tsadar shaddar jikinta haka ta rinka jan jiki zuwa motarta. Khalifa da Junior sun sha kuka. Itama da kukan ta karasa wani soja yana binta a baya yana zungurinta da kasan bindiga.

Tana shiga motar Khalifa yace Mummy laifi kika yiwa Uncle dinku ya saka ki kneel down?

Idonta ta share tace a'a Khalifa takalmi na ya tsinke shine na gwada yadda muke yi da muna yara.

Motar ta tayar sai dai ga mamakinta sojoji biyu ne suka shiga wata motar a bayansu suka bi bayanta. Zuciyar Izzatu har bugawa take don tsoro tace yau na shiga uku. Maimakon ta tafi gida haka tayi ta yawo a titi. Tun su Nana na kukan yunwa har duk suka yi bacci don wahala. Man motar har kusan karewa yayi ta shiga gidan mai. Motoci wurin goma ne a gabanta amma bata damu ba. Burinta kawai wadannan sojojin su gaji su dena binta. Lokacin da ta fito daga gidan man tayi sa'a bata gansu ba. Sai biyar na yamma ta isa gida jikinta ya gama tsami. Har kusan faduwa tayi da ta fito daga mota ga yara sunyi bacci. Dole ta dauke su daya bayan daya ta shigar dasu gida. Wannan rana ta kafa tarihi mai girma a rayuwar Izzatu.

****
Bayan kwana hudu Zuhra na kwance a daki taji wayarta na ringing. Hamza ne ya kirata ta dauka tana murmushi. Har yanzu bai san halin da ake ciki ba. Idan ya kira hirarsu suke yi sosai. Wani lokacin suyi ta turawa juna hotuna. Gaishe shi tayi yace ni dai na gaji da gaisuwar nan Cutie. I miss you so much. Dan bakin nan na tsiwa yayi min nisa.

Tana jindadin kalaman Ya Hamzanta ta gyara kwanciya...saura wata daya da 'yan kwanaki kazo ka hadu da dan bakin. Ji nake kamar na jawo su Ya Hamza. Har rashin lafiya nake yi saboda rashinka.

Hamza yayi dariya yace ashe dai na siye zuciyarki...wayarsa ya dan cire ya kalla. Karo na uku kenan da Izzatu take kiransa tun bayan sunyi waya dazu. Ya rasa dalilin kiran ya danyi tsaki yace Cutie bani minti biyu zan sake kiranki. Ba jimawa ya kira Izzatu yana tambayarta ko lafiya.

Murya cike da kissa tace Baby dama ina son fita ne anjima to Zuhra ta fita dazu tace gidansu zata je. Ka kwatanta min gidan nasu idan na dawo sai na biya na daukota.

Har cire wayar yayi daga kunnensa ya sake kallo don ya tabbatar da Izzatu yake waya. Wai zata biya daukar Zuhra??? To ko sun fara zaman lafiya ne bai sani ba. Sake magana Izzatu tayi sai yayi mata kwatancen. Sai da yayi kuma ya fara tunanin ko wani abin zata je yi. Yace yaushe ta fita ban sani ba?

Izzatu tace to ai tunda ka tafi tana yawan fita nima bansan inda take zuwa ba. Matar taka gwanar yawo ce.

Shi dai hankalinsa bai kwanta ba har ya ajiye wayar.

Zuhra ya sake kira ya tambayeta yaushe ta fita bai sani ba.

Gabanta ne ya fadi da farko sannan ta dake tace ita tana gida. Yasan bazata masa karya ba shiyasa bai daga zancen ba. Amma sai da ya sake kiran Izzatu yace bai yarda taje dauko Zuhra ba. Idan har ta fita ta dawo da kafarta.

Tuni zancensa yabi iska. Lokacin da ya sake kira ma ta kusa fita daga unguwarsu.

****
Umma na kwashe kayan wanki Izzatu ta shigo da sallama tare da yaranta.

Tarba mai kyau Umma tayi mata sannan tace sai dai banganeki ba.

Izzatu sai yatsina fuska take. Gaskiya gidansu Zuhra basu da wani arzikin azo a gani. Tace sunana Izzatu matar Hamza.

Umma ta hade fuska tana dana sanin irin tarbar da tayiwa matar dake son kashe mata 'ya. Har zata fara fada ta tuna Alhaji yace kada su nuna sunsan abinda ya faru. A dole Umma ta kirkiri fara'a ta fara kiran su Khalifa tana tambayarsu sunayensu. Izzatu ta harare su suka koma suka zauna.

Umma ta dan waiga tace tare kuke da Zuhran? Ina fata dai lafiya.

Toh fa...Izzatu tayi tunanin samun Zuhra a nan gashi ga dukkan alamu iyayenta basu san abinda ke faruwa ba. Murmushi tayi ta mike dama hanya ce ta biyo damu shine nace bari nazo mu gaisa.

Umma tace Allah Sarki, kin kyauta. Nagode sosai zan fadawa Baban Zuhra idan ya dawo.

Kamar wadda ake kora haka Izzatu ta fita daga gidan tana tunanin daga nan kuma ina ta nufa. Kwanaki sai gaba suke yi, me zata fadawa Hamza idan ya dawo?

A bangaren Umma kuwa Izzatu na fita tayi dariya sannan ta kira Zuhra ta fada mata.

****
Bayan sayi biyu su Zuhra na cin abinci a falo ana dan taba hira. Hankalinsu yana ga labarin da Nura ke basu na sabuwar buduwarsa mai son kudi tunda iyayen nasu basa falo suka ji horn din mota.

Dariyar da suke yi duk suka dena Adabiyya ta fita waje da sauri. Murya suka ji ta daga da karfi tana cewa oyoyo Nana. Hamida ki fito ga su Junior da Khalifa. Jin haka Zuhra ta tashi ta shige ciki da gudu. Dakin Hajiya ta shige ta rufe kanta a toilet.

Izzatu ta shigo tare da su Khalifa. Ita da yaran duk sun rame. Ita damuwa da fargaba ke damunta su kuma rashin kula da basa samu daga gareta. A falon ta zaune jiki a sabule tana tararrabin abinda zai faru. Police station yafi goma taje duk ba'a tsinci Zuhra ba. Tayi zurfi a tunani bata ji sallamar su Mama ba sun dawo daga makota jaje.

Sai da Hamida ta taba ta tayi firgigit ta gyara zama. Har kasa ta durkusa ta gaishesu. Suma basu nuna komai ba suka amsa mata. Hajiya tace ina 'yar uwar taki?

Mama tace nima tambayar da zan mata kenan. Kwana biyu su Hamida sunce basa samunta ko a waya.

Cikin Izzatu har 'yar kara yayi sai kuma ga Alhaji ya shigo yace wayar waye ba'a samu?

Hamida ta amsa masa...wayar Anti Zuhra ce bama samu.

A ranta Izzatu tace munafukai wato har waya sukeyi da ita amma ita basa ko yi mata text. Junior ya tafi wurin kakansa ya rungume shi sannan yace nima bana ganin Maama tunda Daddy ya tafi.

Izzatu ce tayi saurin katse shi tace kai Junior ba tana bacci ba lokacin da muka fito. Har ka manta? Su Izzy an fara kwarewa a karya.

Khalifa yace nima dai bana ganinta maybe da Daddy suka shiga aeroplane.

Ji take inama bata zo gidan ba. Sai murmushi take kamar sabuwar shashasha tace Alhaji don't mind them. Tana gida. Bari mu tafi dama zuwa nayi mu gaisa.

Mama tace da sauri haka ko ruwa baku sha ba?

Izzatu tace babu komai ta tattara yaranta suka yi waje.

Tun kafin ta fita su Adabiyya ke dariya Hajiya tace bata son rashin hankali. Daki suka bi Zuhra suna bata labarin karyar Izzatu.

Washegari Tala ta dawo daga kauye. Izzatu kamar ta cinyeta da fada. Duk bakincikinta na wata daya da kwanaki akan Tala ta saukeshi banda tulin aikin gidan da ta tara mata. A haka har akayi azumi da sallah.

****

Sati daya ya rage Hamza ya dawo wanda yayi daidai da kwana sha daya azo kawo kudin auren Hamida da Adabiyya. Kannen Mama mata biyu ne suka zo daga Maiduguri. Mai binta Falmata sai autarsu a mata Yagana. Sun zo da wuri saboda akwai siyayyar da suke son yi na bikin sauran namijin gidansu da baiyi aure ba. Kwanansu daya da zuwa Mama ta kira Zuhra ta hadata da Yagana...ga 'yata nan Yagana so nake kafin ku nan da ranar da za'a kawo kudin nan ni kaina kada na ganeta. Ki hada min ita ciki da waje amma ayi min hankali da dan jikalle a cikin. Duk abinda kike bukata zan baki kudi kuje kasuwa a siyo.

Zuhra ta sunkuyar da kanta kasa cike da kunya. Yagana tace kwantar da hankalinki Ya Kaltume. Irin gyaran da zan mata ko Adabiyya da Hamida sai kin saki kudi zan musu irinsa. Tun jiya da kika bani labarinta na kudiri niyar sai na banbanta ta da wannan karan sigarin Izzatu. Mata tana tafe kamar an sawa taliya riga da zani.

Falmata ta kwashe da dariya. Yagana baki da dama wallahi. Kiyi aikin da aka saka ki kawai ki fito mana da 'ya.

Kafin sati aikin Yagana ya fara nunawa a jikin Zuhra. Dama ga hasken da ciki ya kara mata. Ita kanta tana jindadin gyaran don ma laulayi yasa ba komai ake yi mata ba.

Hamza ya koma kirgen kwanaki kuma a lissafinsa zai dawo lokacin da Zuhra ke da girki. Don murna har fada mata yayi yana sanar da ita irin tarbar da yake so da irin abincin da zata dafa masa. Har tausayi ya bata saboda tasan zai dawo ya tarar da sabanin abinda yake tsammani.

Izzatu dake gidan ta kasa nutsuwa tayi wani abu na murnar dawowar mijinta. Kwatakwata bata da nutsuwa. Kwanakin dawowarsa na matsowa tana kara firgicewa.

****
Karfe biyu da rabi jirgin su Hamza ya sauka a filin jirgi na Malam Aminu Kano. Da kansa yace kada Zuhra tazo saboda yasan da kyar idan zai iya hakuri da tabata indai ya ganta ko da a gaban mutane ne. Ibrahim ne yazo ya dauko shi. Ya kara haske yayi kyau kamar ba wanda yaje karatu ba. Farincikinsa baya misaltuwa.

Gidansa yace Ibrahim ya kaishi idan yayi wanka zuwa anjima zaije gidansu. Nan kuwa son ganin 'ya'yansa da Zuhra ne a ransa.

Motar Ibrahim na tsayawa maigadi ya soma kiransu Khalifa ga babansu ya dawo. Da gudu yaran suka fito suka dafe jikin babansu.

Yadda cikin Izzatu ya tsirga saboda tsabar tsoro da gudu ta shiga toilet. Gudawarta ta tara kenan tunda gari ya waye ko wanka bata yi ba.

Hamza ya shiga gidansa da murna ya ajiye Nana ya hau sama har yana tsallake bene uku uku don sauri. Dakin Izzatu ya fara shiga yaji alamun tana bandaki ya fita. Dama dai ba nan yafi damuwa da zuwa ba.

Cike da murna ya bude kofar dakin Zuhra yana tunanin me ya hanata fitowa tarbarsa a waje. Turus ya tsaya tun bai gama shiga ba, dakin yayi kura tamkar ya shekara babu shara. Da sauri ya fito ya koma dakin Izzatu wadda ke labe a jikin kofa. Zuciyarsa sai raya masa abubuwa take tun kafin ya tambayi ina Zuhra take.

Muryar Izzatu da kyar take fita saboda tsoro tace tun ranar da ka tafi ta bar gidan nan. Wani irin kallo ya bita dashi sannan ya dauki waya ya kira Zuhra. A kashe yaji wayar bayan ko da suka tsaya canjin jirgi sunyi waya. Nan take gaban [truncated by WhatsApp]
[10/24, 3:43 PM] +234 705 352 3457: AL'ADUN WASU 76

Batul Mamman(Mrs)





A yadda ya dago kai dole Izzatu ta kara tsorata ta shige daki ta kulle kofar da mukulli. Hamza bai kulata ba ya sauka ya tambayi Tala ina Zuhra take. Tala tace ita tun washegarin tafiyarsa rabon da ta ganta. Da ta dawo daga kauye ma bata gidan.

Wannan abu da daure kai yake. Maigadi ma irin amsar da ya bayar kenan. Murna da dokin dawowarsa gida duk suka bace a lokacin sai zulumin abinda ke faruwa.

Kofar dakin Izzatu ya koma yana bugawa iya karfinsa....Izzy ki bude kofar nan idan kina son kanki da arziki.

Daga ciki tace bazan bude ba Hamza. So kake ka taba lafiyar jikina akan abinda bani da masaniya akan sa.

Daurewa yayi yace ni ba dukanki zanyi ba. We need to talk. Ko kina da amsar da zaki bawa iyayenta ne?

Duk da haka Izzatu bata bude kofar ba sai da ya tabbatar mata babu abinda zaiyi mata.

Dakin nata duk a hargitse yake kamar ana wasan dambe aciki. Ko a mafarki bai taba tunanin akwai ranar da Izzy zata yi kazanta ba saboda ba halinta bane.

Kujerar gaban mudubi ya jawo ya zauna. Iyakar dauriya yake yi kada ya tsorata Izzatu taki bashi amsar da yake nema. A nutse ya fara magana.....Izzy kin tuna lokacin da muka fara haduwa?kunzo school dinmu ke da yayarki Zeenatu a Canada ko. Idan kin tuna ours was love at first sight. Daga haduwar farko bamu rabu ba sai da nasan gidanku da numbar wayarki. Kuma sanin kanki ne ko bayan aurenmu duk wata suka da ake kawo min game dake ban taba saurare ba saboda son da nake miki. Hatta iyayena basa son irin zaman da muke yi amma kullum ina supporting dinki. Haka ne???

A dan tsorace ta gyada kai.

Hamza yace good, ashe kenan duk ranar da kika ga na juya miki baya bai kamata kiga laifina ba. Kinfi kowa sanin da yadda na auri Zuhra. Kafin ba aureta na soma ganin sauyi a rayuwata wanda yasa dole na sake tunani akan yadda muke gudanar da rayuwarmu a matsayinmu na musulmi. Na rokeki da mu canja kika ki. Sai Allah Ya kawo matar da sanadiyarki ta shigo gidana amma sai ta dace da irin dabi'un da duk mai hankali yasan sune dabi'un da suka dace da al'adun mu. Bin al'adun wasu da muke yi tamkar mun saka mask(fuska)ne. Duk yadda muka so da nuna mu turawa ne hakan bazai taba tabbata ba saboda a karkashin fuskar nan mu na ainihin muna nan. Da ace kin dauki shawarata babu wani abu da Zuhra zata yi da zai dauke min hankali. Ke kika yi sake har yarinya kamarta ta zame min abin alfahari. Duk da haka kinsan a irin abubuwan da kike min kuma har yanzu kike gidan nan akwai sonki a zuciyata.

Duk tsarin zancen nan na Hamza hankalin Izzatu ba a kwance yake ba. Babu abinda take tsoro kamar yasan gaskiya ya saketa. Idan Hamza ya saketa tabbas zata iya rasa rayuwarta. Babu wani mutum da take so kamarsa.

A hankali yaje gabanta ya rike kafadunta. Idanunsa sunyi ja sosai...Izzy ki taimakeni ki fada min inda Zuhra take.

Hannunsa ta ture dama nasan duk wannan tsarin zancen kana yi ne don kawai kaji inda matarka take. To ni ban sani ba. Da zaka tafi ai ba ajiyarta ka bani ba. Tunda ka tafi bata sake kwana a gidan nan ba.

Kan Hamza ya daure...ranakun da kika ce tana dakinta ko ta fita duk karya ne kenan?

Izzatu tace karya ne. Nima nemanta nake yi saboda gudun rana irin wannan. Ka dawo ka fara blaming dina.

Shekaru sama da goma Hamza ya gama sanin Izzatu ya kuma san lokacin da zancenta yake karya...kisa mayafi ki fito ina jiranki, ki taho min da key din mota. Yana fadin haka ya fita daga dakin. Ji yake kamar ya shake Izzatu amma bazaiyi haka ba. Gara ya daure kila ta fadi gaskiya.

Sai da ya bita ciki har sau biyu tana kin fitowa karshe kusan janta yayi ya turata a mota. Gudu yake kamar motar zata tashi bai tsaya ko'ina ba sai gidansu.

Dama su Alhaji sun san hakan zai faru shiyasa aka hana Zuhra zaman falo. A dakin su Hamida ta zauna tayi tagumi. Ta rasa gane dalilin su Hajiya na kin sanar da Hamza inda take. Tana wannan zaman taji muryarsa a falo...gabanta ne ya fadi taji kamar ta fita. Ba karamin kewarsa takeyi ba. Domin ya dan wuce wata biyun kafin ya dawo.

*****
Hamida ya gani a falo tana masa sannu da zuwa ko amsawa baiyi ba yace ina Alhaji? Hanyar dakinsa ta nuna ya wuce yana jan hannun Izzatu.

Sallama ya rinka yi Mama ta fito da sauri. Itama Hajiya ta fito daga dakinta. Kana ganinsa kasan hankalinsa a tashe yake Mama tace Yaya lafiya?

Mama ina Alhaji?

Tace yana falonsa. Itama tausayi Hamza ya bata. Zata so a barshi yaga matarsa. Ta tabbatar ko zama baiyi ba ya fito.

Suna zazzaune a falon Alhajin Hamza ya gaishesu. Batare da ya jira sun amsa ba bare a tambayeshi ya hanya yace Zuhra ta bata.

Kamar gaske suka nuna mamakinsu. Alhaji yace wace irin magana ce wannan?

Hamza yace tunda na dawo banganta ba. Kuma kafin na taho kullum muna waya da ita amma yanzu na kasa samu. Na tambaya a gidan duk sunce tunda na tafi basu kara ganinta ba. Nayi tunanin zuwa gidansu amma ina tsoron ko bata can kada na tadawa su Baba hankali.

Alhaji ya kalli Izzatu yace ke kalle ni nan. Ai kuwa ta daga kai ta masa kiri da ido. Yayi murmushi irin na manya...tunda mijinku yayi tafiya kin fada mana baki ga Zuhra ba? Sai yau zaku zo nan kuna nemanta? Da kika zo gidan nan kwanaki ba cewa kika yi tana gida ba?

Hamza yace Alhaji duk karya take. Don Allah ku taimakeni....

Hajiya ta tashi zata bar falon. Tausayin danta take ji.

Maganar Izzatu ta dakatar da ita...Baby ina jin fa kauyensu ta koma. Kasan tun farko munyi shawarar zaka saketa bayan wata shida...
Ba kunya Hamza yasa hannu ya toshewa Izzatu baki a gaban iyayensa. Idan ya kyaleta zata baro masa matsala ne.

Alhaji yace sakar mata baki tayi magana.

Sakinta yayi yana harararta. Izzatu tace tunda aka yi auren ba sonta yake ba muka yanke shawarar bayan wata shida zai saketa. Ina jin saukaka masa tayi ta tafi kauye wurin 'yan uwansu.

Hamza ya dafe kai Izzatu kuwa tayi murmushi..ko ba komai yanzu ta fitar da kanta daga zargi.

Ran Alhaji a bace yace Yaya da gaske da girmanka da hankalinka ka taba fadar magana irin wannan?

Kai a kasa Hamza yace eh Alhaji, amma tuntuni maganar ta wuce.

Alhaji ya mike to ni babu ruwana. Tunda har yanzu bakayi hankali ba Allah Yasa a dace ka ganta. Kwana uku na baka ka nemo 'yar mutane ka bata takardarta. Na zata auren da nayi maka gata ne ashe kai tunanin mafita kawai kake yi.

Hamza ya fara bawa Alhaji hakuri. Wannan magana ta dade Alhaji. Don Allah kada kace na saketa wallahi ina sonta.

Idan ka iya nemota nan da kwana uku shikenan idan ba haka ba kuwa duk inda aka ganta zaka saketa ne. Ka tashi ka bani wuri.

Jiki ba kwari Hamza ya fita Izzatu na bin bayansa hankali ya dan kwanta ance zai saki Zuhra.

Suna fita Hajiya ta koma ta zauna. Alhaji yace kinga shirme irin na babana ko? Ni so nayi wannan mara kunyar ta fada da bakinta abinda tayiwa Zuhra yaji sai gashi ashe shima akwai nasa laifin. Ni kam da gaske idan auren nan bazai yiwu ba gara su rabu kada watarana su kashe 'yar mutane.

Mama tace anya Alhaji batun rabuwa bai taso ba. Yaran nan suna son junansu. Kayi hakuri ta koma dakinta. Tunda kace zaka hukunta Izzatu ai shikenan.

Shima Yayan sai na hukunta shi. Niyata a yau dinnan ya dauki matarsa. Amma tunda naji wannan zancen hukuncinsa shine ya tafi nemanta. Yadda suka kuntata mata a gidan nan suma su dandana.

****
Kwanaki biyu sun wuce a lokacin da Alhaji ya bawa Hamza. Police station din da yaje shi kanshi bai san adadinsu ba. Maganar bacci dama sai dai ya sace shi. Abinci ma rabonsa da abin kirki tun a jirgi. Lokaci guda duk ya zabge. Yana son bada cigiya a gidan rediyo da talabijin amma yana gudun kada su Umma su gani.

Da daddare ya bude jakar kayansa ya dauko tasu tsarabar. Babu wanda ya bawa komai sai a lokacin ya dauka ya tafi gidansu Zuhra.

Su Baba suna ta tambayarsa ya hanya amma hankalinsa na ga ta ina zai ga bullowar Zuhra. Sai da Umma tace tana fatan Zuhra lafiya kwana biyu basa samunta a waya ya tabbatar bata gidan. To shi yanzu ina zai duba kuma???

Da ya tafi Umma har kuka tayi tace ita wallahi zata fada masa inda Zuhra take....Haba Baban Zuhra ka duba kaga yadda ya rame duk ya fita hayyacinsa.

Baba yace nima ina tausayinsa amma ki bari muga iya gudun ruwan Alhaji. Mu bashi dama kamar yadda ya nemi alfarma.

****
Daga gidansu Zuhra gidan Ibrahim ya wuce ko Allah Yasa sun san inda take. Nan ma babu wani abun arziki da ya samu. Haka ya tafi gida jiki a sanyaye.

Izzatu ya tarar ta gyara jikinta sannan tayi masa girki mai kyau. Ita tunda laifin ya tashi daga kanta to babu matsala. Tana ji a ranta dai duk inda Zuhra take tana lafiya tunda har suna waya da Hamza kafin ya dawo. Idan taki bayyana kanta wannan matsalarta ce. Ko kallon abincin baiyi ba ya shige daki. Yana kwanciya Anti Faiza ta fado masa a rai ya sake daukar mukulli ya tafi gidanta. Har falo ta kaishi wurin mijinta suka gaisa itama ta nuna kamar bata san komai ba. A haka ya koma gida duk yadda Izzatu taso ya saurareta ko abinci ya ci abu ya gagara.

Washegari da safe ya bawa Tala umarnin ta gyara dakin Zuhra kafin ya dawo. Da murnarta tace an ganta ne?

Hamza yayi murmushi mai ciwo...a'a amma bana so ta dawo ta rasa wurin kwana. Yadda yayi magana yasa Tala hawaye. Me yasa iyayensa suka ki sanar dashi inda matarsa take. Sajensa duk yayi wani iri saboda rashin gyara wani gashin yafi wani tsaho.

Ruwan tea kawai yasha ya fita zuwa office din 'yan sanda da suka kirashi an tsinci wata mata. Yaje ya tarar ba Zuhra bace kafin ya fito Alhaji ya kirashi yana masa tuni gobe ne za'a kawo kudin Adabiyya da Hamida kuma za'a saka ranar aure. Shiru yayi na dan lokaci sannan yace yanzu Alhaji ni baza'a yafe min zuwa ba? Duk su Kawu basu isa ba sai nazo?

Alhaji yace kaine babba a gidan nan Yaya rashin zuwanka bazai nuna abu mai kyau ba. Kuma ina maganar Zuhra ta kwana? Har yanzu baka ce komai ba.

Ina kan dubawa Alhaji yanzu ma ina police station.

Tausayin dan nasa yaji yace ka koma gida haka gobe kuzo kai da matarka. Na sami labari ina tunanin an kusa ganinta. Bai jira amsar Hamza ba ya kashe wayar.

Cikin minti talatin Hamza ya iso gidan ya dami Alhaji sai ya fada masa labarin da yaji. Alhaji yace ya bari sai gobe idan ya tabbatar amma yazo tare da Izzatu idan an gama karbar kudin zasuyi magana.

***

Zuhra na daki tun shigowar Hamza tana kuka. A haka Mama ta shigo ta sameta sai

Please Login or Register in order to submit comment