Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta dawo.

Har Tala ta juya zata koma ciki sai dai hankalinta bai kwanta ba. Da yake da waya ta fito sai ta gwada kiran Zuhra. Karar wayar suka ji daga cikin mota saboda a gefen motar suke a tsaye. Nan da nan Tala da maigadi suka shiga tashin hankali. Tace bari naje na tambayi Maman Khalifa ko ba a gida zata kwana ba.

Maigadi yace ashe baki da tunani ban sani ba? Tare ya kamata su dawo amma basu dawo ba kuma duk munsan ba da ita maigida zaiyi tafiya ba. Ni a tawa shawarar ki kira wani a gidansu Yallabai kiji ko a can zata kwana tunda ya fada min da bakinsa can zai fara zuwa kafin yaje iyafot din.

Da yake a rude take a take tace bata da numbar kowa. Har ta soma kuka tana tunanin ko wani mugun abin ne ya sami Zuhra. Daga baya ta tuna jiya da safe Hamida ta kira wayarta saboda bata sami ta Zuhra ba. Sai da suka rinka bin nambobin da aka kira a wayar wajen shida gashi babu kudi sosai sannan suka yi sa'ar samun ta Hamida.

****
Hamida da Adabiyya suna ta hira basu ji wayar da wuri ba. Tala har ta hakura sun kira wasu nambobin biyu sai ga kiran Hamida ya shigo. Ita duk ta tsorata ganin daga gidan Yaya aka kira da wannan daren. A tunaninta ko babu lafiya Zuhra ta kirata da numbar Tala. Jiki na rawa Tala ta dauka tace kiyi hakuri na kiraki a tsohon daren nan. Dama tambayarki zanyi ko a nan gidanku Maama zata kwana ko gidan iyayenta?

Hamida tace bangane ba Tala. Kina nufin Anti Zuhra bata dawo gida ba? To ina Anti Izzatu?

Tala tace tana dakinta munga ita kadai ta shigo kuma ga wayar Maaman a motar Yallabai an jona ta da wani abu. Sautin kukan Hamida Tala ta jiyo tasan lallai ba lafiya ba.

Ko ajiye wayar bata yi ba ta tafi dakin Mama ta tarar bata nan. Dama tasan Hajiya na falon Alhaji tun da suka dawo daga airport a nan suka gansu suna hira. Falon ta nufa da gudu tana yiwa Adabiyya bayanin abinda Tala tace. Sallama tayi ko amsawa basu jira anyi ba suka daga labulen suka shiga falon. Alhaji ne da matansa suke ta hira yau basu kwanta da wuri ba.

Hajiya ta daka musu tsawa tana son jin dalilinsu na shigowa a haka. Cikin kuka Hamida ta fada musu wayar da suka yi da Tala. Babu wanda hankalinsa bai tashi ba a wannan lokacin. Alh Nasiru ya dauki waya ya kira Ibrahim ya sanar dashi sannan ya tafi dakin Nura ya taso shi. Ko hula babu a kan Alhaji suka fita da Nura. Airport din zasu fara dubawa kafin suje gidan iyayenta.

*****
Hadari ne yake hadowa garin yayi duhu sosai sai fitilun cikin airport na gefen titi. Iska da kura sai kada Zuhra suke tana tafiya idonta sharkaf da hawaye. Banda Izzatu hatta Hamzan haushinsa take ji. Don me bai tabbatar da ta tafi ba ya shige ciki. Kullum Umma na fada mata maza basa son macen da tafi kawo kara amma wannan karon suna yin waya da Hamza idan har ta isa gidanta lafiya kenan zata fada masa. Dole ayi mata iyaka da Izzatu idan ba haka ba kuma lallai zasu daku. Ko a unguwarsu babu mai takalar Zuhra dambe don da gaske karfi gareta.

Ajiyar zuciya tayi da ta ga ta kusa isa bakin gate sai dai tun kafin ta isa ta fara jin ana daka mata tsawa. Nan take ta gigice ganin sojoji sunfi biyar a kanta da bindigogi.

*****
Sanarwar karshe akeyi cewa jirgi zai tashi kowa yasa seat belt kuma a kashe waya. Ran Hamza a bace ya kira Zuhra yafi sau ashirin bata dauka. Izzatu kuma da suka sake sallama tace Zuhran na dakinta. Ya tabbatar idan yace ta kai mata tata wayar kuma bazata kai ba. Dole ya hakura ya kashe wayar. Sauran mutum hudu da zasu tafi tare duk ta Abuja suka tashi da kyar ya sami alfarmar tashi ta Kano saboda iyalinsa. Yayi yunkurin kashe wayar sai ga text ya shigo. Da sauri ya bude ya zata Zuhra ce.
(Sir idan kana da lokaci gobe ka kirani.
Mr. Oscar)

Rasa abin yi yayi ba don yana cikin jirgi ba ai yanzu zai kirashi yaji abinda zai fada masa. Addu'ar abin hawa da ta tafiya Hamza yayi ya kashe wayarsa zuciyarsa tana tunanin me ya sami Cutie dinsa.

****
Kneel down sojojin suka saka Zuhra suna ta turancin da pidgin ta kasa gane abinda suke fada. Kuka take yi kamar ranta zai fita saboda tsabar fargaba. Wani cikin sojojin ya harare katon hijab dinta yace ta cire shi da Hausa. Zuhra ta sake kankame jiki tace bazata cire ba. Saita ta suka yi da bindigogi suna fada...ki cire hijab mu tabbatar babu komai a jikinki idan ba haka ba a wurin nan zamu harbe ki.

Wasu cikin sojojin har sun fara ja da baya saboda kin cirewa da tayi. Wani yace me ya kawoki nan? Bakinta har hardewa yake ta fada musu abinda tazo yi. Dariya suka yi suka karyata ta. Suka bata umarni na karshe ko ta cire hijab dinta ko a harbe ta. Can gefe wasu sojojin ke ta buga waya ga manyansu suna sanar dasu abinda ke faruwa.

A haka Zuhra tana kuka tana rokonsu ta kama hijab din ta cire gashi kanta ko dankwali babu dadinta ma doguwar riga ce ta atampa a jikinta. Rigar duk ta matse ta sama rabin kirjinta a waje. Idon wasu ya kai nan tayi saurin rufewa tana kuka sosai. Ta saddakar mutuwarta tazo amma har abada bazata taba yafewa Izzatu ba. Shi kanshi Hamza idan har wani dalili yasa ta tsira to ta bar gidansa kenan.

Motoci biyu ne suka iso kusan a tare sai ga motar 'yan sanda guda daya. Tun kafin su tsaya Alh Nasiru ya hango Zuhra a durkushe. Idanunsa suka kada suka yi ja saboda bacin rai. Wannan cin kashi da aka yi mata da me yayi kama, me zai fadawa Mal Bashir? Ibrahim ko kashe tasa motar baiyi ba ya fito da sauri amma da ya karaso sauke idonsa yayi saboda bazai iya kallon matar dan uwansa a wannan yanayin ba. Nura kuwa mai raunin zuciyar da tafi ta Hamza kuka yake yi kamar wani yaro.

Duk fitowa suka yi sojoji na tsayar dasu 'yan sandan suka taho suka fara yi musu bayanin report din da Ibrahim ya kai musu. Shaida suka nema domin gaskata zancen 'yan sandan. Nura ya duba wayarsa yayi sa'a akwai hoton ranar yinin Zuhra da suka je daukota daga Ajingi shine ya nuna musu. Duk da haka sai da suka bukaci washegari a kawo wani na'uin shaidar ko wacece Zuhra.

Alh Nasiru da kansa ya dauko hijab din da akayi wurgi dashi ya dora mata a kanta. Kasa tashi tayi ya dagata da kansa. Sai a lokacin ta kara sa kuka mai sauti. Ibrahim ya kalli sojojin yace mace mai hijab sunanta musulma ba 'yar ta'adda ba da zaku wulakanta ta haka.

A baya Alhaji ya zaunar da ita ya shiga gaba. Ibrahim ma binsu yayi a baya suka tafi gida.

Jugum jugum haka su Hajiya suka zauna a falo. Ana shigo da Zuhra Hajiya ta ajiye kunyarta taje ta rungumota. Zuhra ta kankameta tana kuka kamar mai ban tausayi. Cikin kuka tace Hajiya ai ba laifi bane idan ban yafewa Maman Khalifa ba ko? Kowa a wurin yaji tausayinta. Ga masu tayata kuka su Adabiyya suna yi.

Da kyar falon ya sami nutsuwa har ta fada musu abinda ya faru. Alhaji ya bata hakuri sannan yace ta kwantar da hankalinta zuwa gobe zasu san abin yi. Ruwa mai zafi Mama ta sa aka dafa mata tayi wanka amma taki cin komai. Dole suka kyaleta ta kwanta cike da tunani kala kala.

[10/22, 4:49 PM] +234 705 352 3457: AL'ADUN WASU 74

Batul Mamman(Mrs)






Gudu take yi a wani daji kafarta ko takalma babu ga gumi da ya wanke mata jiki. Sautin harbi take ji amma ta rasa daga ina yake fitowa. Tana cikin gudun ta hango wani gida a tsakiyar dajin ta tafi da sauri ta shiga ta rufe kofar harda saka kwado. Juyawar da zatayi idonta ya sauka akan sojoji da bata san iya adadinsu ba. Dariya suka fara yi mata kafin su saita ta da bindiga su fara harbi.

Hajiya tana idar da sallah ta juya gefen gado inda Zuhra ke kwance tana ta mutsu-mutsu duk ta hada gumi. Da sauri ta tashi ta tsaya a kanta ta fuskanci kowane irin mafarki take yi ba na lafiya bane. Kafadar Zuhra ta dafa da niyar tashinta Zuhran ta tashi a razane tare da kwalla kara. Ganin Hajiya yasa ta kankameta sai kuka ya kwace mata. Hajiyan tana rarrashinta tana kokarin mayar da hawayen da yake barazanar fitowa daga idonta. Tashin Zuhra na uku kenan tunda suka kwanta. Kamar ta sani ta hanata kwana dasu Hamida tace ta dawo dakinta. Sai da Zuhra tayi shiru sannan Hajiya tace...ki tashi kiyi sallah ba'a dade da kiran assalatu ba. Kuma ki yawaita addua nima zan cigaba da yi miki musamman na kwanciya saboda wannan mafarke mafarken da kike yi.
Jiki a mace Zuhra tace to Hajiya sannan ta tashi ta shiga toilet. Tun faruwar wannan al'amari 'yan awanni da suka wuce Zuhra da Hajiya suka manta da kunyar juna irin na surukai.

Bayan ta idar da sallah ne Mama ta shigo dakin da gani itama sallar tayi. Zuhra ta gaisheta ta amsa fuska a sake sannan ta tambayi Hajiya ya suka kwana...wallahi jiya Alhaji baiyi baccin kirki ba duk ya damu. Kusan a zaune muka kwana.

Hajiya tace to ai nima bamuyi baccin ba. Sau uku bacci na daukarta ta tashi a firgice. Allah Kaltume da sakin Izzatu a hannuna yake sai da yaron nan ya dawo ya tarar ta dade a gidansu.

Mama tayi murmushi, Hajiya Halima bata taba sanya kanta cikin lamuran 'ya'yanta musamman Hamza da ya kasance na fari. Wannan maganar tata ta kara tabbatar da cewa ba karamin bacin rai abinda Izzatu tayi ya sanyata ba. Haka suka zauna suna taba 'yar hira har gari ya karasa wayewa Mama ta tafi kitchen tare da Hamida wadda ita ce mai tayin abincin safe yau.

****
Dayake jirgin Emirate Hamza ya hau sun tsaya a Abu Dhabi canjin jirgin da hutun awa biyu. Wayar Zuhra ya rinka kira yanzu ko shiga ma bata yi. Hankalinsa yayi matukar tashi. Da ya kira Izzatu bayan sun gaisa lokacin karfe takwas na safe tace masa Zuhra bata fito daga daki ba. Hankalinsa gabadaya a tashe yake. Yace taje ta kwankwasa mata kofa tace yace ta kunna wayarta. Izzatu tace ita bazata je ba ta kashe wayarta ma a cewarta kada ya dameta ita babu ruwanta da matarsa. Haka ya hakura ya kira iyayensa suka amsa wayarsa kamar babu abinda ya faru. A hira ne ya sanar da Mama ya kasa samun Zuhra tun daren jiya bayan ya shiga jirgi. Mayar da zancen nasa wasa tayi har tana cewa ko zai biyata ne taje ta gano masa lafiyar amarya. Shi dai jikinsa duk babu dadi har ya sake shiga jirgin da zai kaisu Thailand wanda daga shi zasu shiga mai kaisu South Korea.

*****
Tunda Izzatu ta ajiye wayar Hamza jikinta yayi sanyi. Jiya dai lafiya kalau tayi bacci amma tunda ta fuskanci Zuhra bata dawo gida ba hankalinta ya kasa kwanciya. Ita fa a tata wautar ba niyarta wani mugun abin ya sami Zuhra ba. So tayi ta bata wahala karshe kila ta biyo motar haya a daren. Tunani tayi ko an saceta a hanya taji wani mugun tsoro ya shigeta. Sai yanzu take danasanin abinda tayi domin batan Zuhra ba karamin abu bane. Daga baya tayi tunanin ko gidansu Zuhran ta wuce sai tayi dariya. Karshen abin kenan kila ta koma gida ne tana son ta hadata da Hamza. Indai hakane kuwa ko a jikinta don tana da bakin kubutar da kanta. Tun daga wannan lokacin hankalinta ya kwanta.

Mama ce da kanta ta kira Tala wadda take ta hada kaya cikin kwanciyar hankali saboda Hamida ta tabbatar mata da anga Zuhra amma Alhaji yace kada ta kuskura ta fadawa kowa. Mama tace tasan yadda zatayi ta dauko wayar Zuhra a motar Hamza ta kawo mata gida. Wurin maigadi taje ta fada masa. Sai da rana ta fito yace Tala ta fada mata yace zai wanke mata motar yaga datti a ciki. Babu musu Izzatu ta leko ta tagar dakinta ta danna remote ta bude masa motar. Dama tana son zuwa shopping anjima.

Motar ya bude ya dauko wayar ya bawa Tala. Ita kuma bata dade ba tayi sallama da Izzatu ta dauki kayanta da sunan ta tafi kauye. Gidansu Hamza ta fara zuwa inda su Adabiyya suka labarta mata abinda ya sami Zuhra. Tala tayi kuka sosai sannan ta kawo wayar ta bawa Mama. Da aka kira Zuhra ta fito suka gaisa dukkansu sai da suka yi kuka. Tala tasan uwargidan nasu sai a hankali amma bata taba tsammanin abin nata yakai ta aikata wannan rashin imanin ba. Tayi musu sallama kuma su Hajiya suka kara mata guzuri ta tafi.

Wurin shabiyun rana Alhaji ya tara iyalinsa harda na gidan miji su Jidda da Mariya aka sake sanar dasu halin da ake ciki. A nan ya fada musu cewa bai yarda wata ta nuna tasan inda Zuhra take ba har Hamza ya dawo. Daga masu hawaye suna tausayin Zuhra sai masu zagin Izzatu da yi mata muguwar addua. Bayan sun tashi Alhaji ya wakilta Mama taje tasan da yadda zata yi ta daukowa Zuhra kayan sawa kafin ya dinka mata wasu. Bayan sun fita yace da Hajiya ta shirya ita da Zuhra zasu je unguwa.

Ibrahim ke jan motar har iya inda mota ke shiga a layin gidansu Zuhra. Yana tsayar da motar Zuhra ta fita da gudu ta shige gida.

Umma da Baba na zaune a falo suna jiran Safara'u ta gama girkin rana zasu je Ajingi barka maman Safara'un ta haihu.

Kamar an jehota Zuhra ta fada kan Baba tana kuka. Daga shi har Umma hankalinsu ya tashi suna tambayarta abinda ke faruwa ta kasa magana. Sallamar Hajiya ce ta katsesu Umma ta tashi ta tarota. Bayan sun gaisa ta fadawa Baba tare da Alhaji suke. Da kyar ya daga Zuhra daga jikinsa ya fita ya shigo dasu shi da Ibrahim.

Bayan sun zazzauna Hajiya ta kalli Zuhra da ta lafe jikin Umma, ita kuma Umman tana shafa mata baya tace...lallai Zuhra ke 'yar shagwaba ce ajin karshe. Umma taji kunya ta soma ture Zuhra. Baba yace dawo daga nan uwata nima ina da jikin da zaki tumurmusa. Kasa karasawa tayi ta sunkuyar da kanta saboda kunya. Ita ta manta ma da surukanta a wurin. Umma da Baba kuwa indai Zuhra zata yi kuka to basu da kwanciyar hankali.

Alh Nasiru yace nasan zakuyi mamakin zuwanmu a wannan lokacin kuma a irin wannan yanayin. Dole ce ta kawo haka domin bahaushe yace ranar wanka ba'a boyon cibi. Daga nan Alhaji ya warware musu gaskiyar lamari game da auren Hamza da Zuhra. Baba da Umma duk mamaki ya ishesu yadda Zuhra bata taba nuna musu ba auren soyayya tayi ba. Alhaji ya cigaba da cewa a yadda na fahimta Yaya da Zuhra suna son junansu yanzu duk da irin abinda ya faru kafin auren.

Baba ya rike hannun Zuhra yace kada ki cuci kanki kinfi karfin wulakanci muddin ina raye. Ki fada min gaskiya idan ba kya son auren sai a waraware. Kana ganin Baba kasan ba karamin bacin rai yaji ba game da labarin April fool da aka yiwa 'yarsa. Kanta a kasa Zuhra ta kasa magana sai kara rike hannun Baba da take yi. Hakan da tayi ya bashi tabbacin tana son mijinta. Da akasin haka ne kiri kiri zata masa da ido yadda tayi da ya taba cewa yaron shagonsa yana sonta. Ya dago kai ya kalli Alhaji...to yanzu menene yake faruwa kuka dawo da ita gida daga tafiyar Hamzan jiya?

Alh Nasiru bai damu da yadda Mal Bashir ya canja ba. Abinda yafi haka ma yana da ikon yi akan 'yarsa. Babu uban da zai zuba ido yaga ana wulakanta masa 'ya'ya komai talaucinsa. Alhaji ya sake fada musu abinda Izzatu tayiwa Zuhra a daren jiya. Kuka ne ya kwacewa Umma sosai ta rungumo Zuhra jikinta har rawa yake. Da da ajali a kusa babu abinda zai hana sojojin nan harbe Zuhra. Hajiya ma wani kukan take tayata. Hakika duk da rashin wadata sosai amma gidansu Zuhra gida ne mai cike da soyayya a tsakanin iyayen da tilon 'yarsu. Baba ma idanunsa ja suka yi sosai. Alhaji yace na zabi fada muku gaskiya saboda halin rayuwa. Ba don mai aikin gidansu ba da tayi tunanin sanar damu da karshenta yau labari yasha bamban. Mal Bashir ina mai baku hakuri da neman afuwarku. Wallahi idan Yaya ya dawo zan dauki mataki akan shegiyar yarinyar nan.

Mal Bashir ya kalli Zuhra yace babu wani abu da ya sameki ko? Tayi masa murmushi Allah babu komai. Yace to Alhamdulillahi sai mu jira Hamza ya dawo lafiya ya baki takardarki. Yau ko akuyar gidan nan kike bazan yarda ki koma inda akayi miki wannan diban albarkar ba, bare 'yata. Alhaji kuyi hakuri amma bazan bari ku koma da ita ba. Ita kadai Allah Ya bani idan ka duba da wuya idan bamuyi sa'anni da kai ba amma sai a kanta haihuwa ta tsaya tsaya mana. Wallahi duk kawaici irin na mutumin kauye bazan iya dauke kai ba idan abu ya shafi uwata. Gara na aurar da ita a kauye da ta fuskanci rayuwa irin wannan. Umma ta nuna ta goyi bayan mijinta.

Alhaji da Hajiya suka shiga bawa su Baba baki amma kememe Baba yace shi fa bazai yarda ba. Ibrahim yace Baba idan bazaka damu ba ka bani damar magana. Baba yace ina jinka amma bazan canja kudirina ba. Murmushi Ibrahim yayi sannan ya sanar dasu irin canje canjen da ya gani tattare da dan uwansa bayan aurensa da Zuhra. A takaice abinda iyayensu basu sani ba dangane da irin taimakon da tayi masa bayan durkushewar kamfaninsa a dalilin Izzatu duk sai da ya fada musu. Mamaki sosai suka yi Zuhra ta sake samun masauki a zuciyar surukanta. Ibrahim yace shekaranjiya yazo har office ya sameni ya sanar dani komai yace wasiyyace ya barmin saboda yanayin tafiya idan har bai dawo ba kada na taba bari ta wulakanta a duniya.

Wannan jawabi na Ibrahim ya sanyaya zuciyar iyayen Zuhra ita kumq yasata kuka sosai tare da dagewa wurin yin addua Allah Ya bashi sa'a kuma ya dawo dashi lafiya. Alhaji Nasiru yace bukatarsa daya a wurinsu kada su taba cewa sunsan inda Zuhra take domin Izzatu da hannunta zata girbe abinda ta shuka.

****
Mama da su Hamida ta tafi gidan Hamza. Ihun su Khalifa Izzatu ta ji suna murnar ganinsu ta fito daga kitchen a tsorace. Ba dai can Zuhra ta tafi ba. Ai kuwa tasan Alhaji sai ya bata mata rai. Ga Mama itama wata mara son nata. Gashi uwa uba bata san takaimaimai inda Zuhra ta tafi ba. Har wayarta ta gwada kira bata samu ba.

Da dan cokalin miya Izzatu ta fito tana murmushin da bai kai zuci ba tayi musu sannu da zuwa. Mama ta amsa fuskarta a sake tana tambayar ya suka kwana. Izzatu tace lafiya kalau Junior yace amma yau tun safe bamu ga Maama ba. Inata kiranta bata amsa ba. Izzatu ta make shi sannan tace tana dakinta kila bacci take yi. Mama tayi 'yar dariya tace su Hamida su duba mata. Dama da wata jaka mai dan girma da Adabiyya ta sako cikin hijab. A gaggauce suka debo mata kayan sawa, 'yan ciki da na bacci suka sauko. Hamida tace Mama da gaskiyar Junior Anti Zuhra fa bata dakinta..

Cokalin hannun Izzatu ya fadi don tsoro tace au na tuna tun safe ta tafi gidansu tace a can zata yini.

Adabiyya da Hamida suka kalli juna suna dariya kasakasa. Mama ta dauke kai kamar bata gansu ba tace to ga wannan dama Alhaji ne yace na duba ku. ..dubu biyar ta bawa Izzatu...idan Zuhran ta dawo ki gaidata. Daga nan suka fita suna mamakin karyar da Izzatu tayi musu.

Suna fita tayi ajiyar zuciya hankalinta ya kai karshen tashi. Yanzu idan Zuhra bata dawo ba ina zata fara nemanta? Dole ta kai cigiya wurin 'yan sanda tun kafin a kara dawowa nemanta.

****
A gidan Zuhra ta yini sai dare Nura ya dawo ya dauketa saboda washegari zasu tafi Ajingin da suka fasa zuwa a yau.

Tana zuwa gidan wayarta tayi chaji. Sakonnin text goma ta gani na Hamza masu nuna damuwarsa da rashin samunta a waya. Wurin shadayan dare ya sake kira lokacin suna masaukinsu a wani hotel. Ba karamin dadi yaji ba da ya sameta. Tayi ta bashi hakuri akan cewa wayar ce ta fada kasan kujera a motar bata ganta ba. Hirarsu suke ta masoya har Hamida da Adabiyya suka bar mata dakin suna tsokanarta don ta dage ita wurinsu zata rinka kwana. Alhaji yace kada ta nunawa Hamza komai yanzu saboda kada ya kasa yin abinda ya kaishi. Ta nuna masa tana gida kamar yadda yake tunani.

****
Haka rayuwa ta kasancewa Zuhra a gidan Alhaji babu irin gatan da su Hajiya basa nuna mata. Haka sauran 'yan uwan Hamza ma. Umma da Baba kullum sai sun kirata a waya. Lokacin da ta cika sati biyu ne suna kitchen ita da su Hamida suna aiki Zuhra tana wankin nama taji zuciyarta na tashi. Abu kamar wasa ta fara cewa naman yayi karni da yawa Adabiyya tace ai kuwa yana da kyau. Bata kara magana ba ta soma amai kamar kayan hanjinta zasu fita. Kofar kitchen din ta baya ta fita tayi aman tana yi tana kuka. Hajiya da Mama aka kirawo suka shigo kichen din. Ita dai Hajiya tana ganin aman da Zuhra take yi murmushi kawai tayi ta ja da baya, Mama ta wuceta ta taimakawa Zuhra. Yadda take aman har kirjinta na amsawa yasa take kuka. Mama tace oh ni Kaltume haka kike yiwa Yaya wannan kukan shagwabar? Gaskiya Umma Atine ta shagwaba mana 'ya. Hajiya na daga gefe tace don ba tare muka je gidan dake ba da kinsha kallo. Yadda kika san ta shige ciki. Zuhra duk kunya ta kamata ta tashi da gudu. Mama tabi bayanta da sauri tana dakatar da ita...haba Zuhra yanzu kuma ai lokacin tattalin jikinki ya kama sai kinbi a hankali. Bari na kira Nura a waya yazo ya kaimu asibiti don a tabbatar mana da abin alkhairi. Kan Zuhra a kasa ta kasa cewa komai. Itama tana zargin abinda Mama take fada saboda 'yan alamun da ta gani daga irin hirar 'yan mata da kawayensu. Da yamma suka je asibiti aka tabbatar tana da ciki wanda ke cikin watansa na biyu. Tun a hanya Mama ta kira Hajiya harda Alhaji tayi musu kyakkyawan albishir. Siyayyar 'yan kayan kwadayi tayiwa Zuhra wadda don kunya ta rufe fuskarta da mayafi.

Shima wannan labarin bata sanar da Hamza ba a lokacin da sukayi waya. Tafi son ya gani da idonsa. Sai dai suyi ta hira yana tambayarta me tayi yau. Kulawa kuwa a wurin 'yan gidansu sai godiyar Allah.

****
Izzatu sam bata da kwanciyar hankali a gidanta. Ga Tala ta tafi gida ga yara su dameta. Junior da Nana sunki yarda ta saka musu pampers ko ta saka musu sai sun cire. Dakinta har zarni yake saboda fitsarin da suke mata a kwance. Kafin ta gama girki kullum sai Nana tayi kuka saboda ta riga ta saba da kin dorawa da wuri. Idan ta zuba musu anjima kadan suce yunwa tunda bata zubawa da yawa. Duk wannan bai dameta ba kamar rashin sannin inda Zuhra take. Hamza dai ya dena tambayarta Zuhra shiyasa take mamaki. 'Yan kwanakin nan har mafarkinta take yi. Don tsananin tashin hankali ko shara bata yi a gidan ga uba wanke wanke ta tara. Tunani ne ya isheta wata rana bayan ta dauko su Khalifa daga makaranta ta wuce airport. Ya zama

Please Login or Register in order to submit comment