Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kokarin ya kamanta adalci tsakaninta da Zuhra yasa taga saurin shiryawarsu ba.

Da suka dawo kowa dakinsa ya nufa. Izzatu ta kawo masa abinci yaci sannan yake tambayarta game da jaka da ya gani kusa da kayansa. Da dan murmushinta tace kayana ne na tafiyarmu gobe.

Ba shiri ya tashi yana kallonta. Wane irin kayan tafiyarmu gobe? Ni nace zan tafi dake ne ko me?

Izzatu tace kwantar da hankalinka zan biyawa kaina kudin jirgi. Shiyasa ban fada maka ba saboda nasan zaka ji dadi idan na fada lokacin da baka tsammani.

Hamza ya hade rai...to kinyi kuskure da Zuhra zani....

A fusace ta tashi itama...wallahi baka isa ba Hamza. Ni zaka rinka wulakantawa akan wannan yarinyar. Shekararta ashirin da daya fa har zaka hada ta da mace kamar ni. Kuma meyasa baka fada min ba da wuri?

Girgiza kai yayi yana mamakin yadda take daga masa murya. Ban fada miki ba saboda gudun kada kizo ki tayar min da rigima kice sai kinje. Amma naga alama hakan ya zama kuskure. Ki zauna a gida ki karasa jinyar jikinki lafin mu dawo. Kuma bana son cigaba da maganar nan don banyi niya ba saboda haka idan wata tafiyarar tazo sai nayi dake idan naga dama.

Ficewa tayi daga dakin ta tafi dakin Zuhra rai a bace ta buga kofar da karfi tana masifa....Zuhra ki kiyayeni wallahi. Ki bar ganin na kyaleki lokaci na baki kafin na koreki daga gidan nan.

Hamza da yake bayanta yace tunda ki kike auranta ba. To kema ki kiyayeni wallahi ko gobe mu tafi airport tare ki koma gidanku. Kada ki kaini bango Izzy darajar 'ya'ya kawai kike ci kema kuma kin sani.

Zuhra dai kallonsu take daya bayan daya ta kasa magana. Tana kallo Hamza yaja hannun Izzatu suka fita. Ranar basuyi baccin arziki ba saboda yadda take ta fada. Sai da Hamza yace idan ta saki bude baki a bakin igiyar aurenta. Cikin masifa tace guda nawa? Yace sai kinyi maganar zan sanar dake ko nawa kika tsinke. Ba arziki ta yi shiru amma ta gama sikewa da Zuhra. Dole tasan yadda zata yi da ita kafin tayi sanadiyar kashe mata aure.

Tun bayan asuba Zuhra tayi wanka ta gama shiri saboda Hamza ya fada mata jirginsu karfe bakwai zai tashi.

Shima da wuri ya shirya ya shiga dakinta. Sai kai kawo take yi a tsakar daki. Tana ganinshi ta gaishe shi yace wannan tafiyar ta meye? Kinci abinci kuwa? Zuhra tace wane irin abinci Ya Hamza? Cikina sai kullewa yake saboda fargaba. Anya zan iya shiga jirgin kuwa. Yayi dariya idan bazaki iya ba sai na tafi da yayarki.

Jin haka Zuhra ta fita daga dakin da sauri har tana tuntube. Shi ya dauko mata akwatin kayanta yabi bayanta.

Da kyar ya samu tasha tea duk hankalinta baya jikinta. A tsorace kawai take da maganar shiga jirgi. Basu dade ba Nura yazo daukarsu shi zai kai su airport din. Har suka fita Izzatu ko kofar daki bata fito ba.

Ana shiga airport Zuhra na kara razana. Gabadaya a tsorace take. Hamza kuwa sai dariya yace yau ga 'yar kauye ga jirgi. Kamar tayi kuka tace Ya Hamza ko dai mu tafi tasha ne mu sami mota. Ya kama hannunta ya rike....Cutie kada ki damu babu inda zanje in barki kinji ko. A hankali ta gyada kai.

Cikin dan lokaci ya karbar mata ticket suka fita inda jirgin yake. Layi suka bi tare da wasu masu tafiyar. Zuhra sai kallo wai ita ce yau zata shiga jirgin sama. Ga wasu manyan jiragen da suka fi wanda zasu shiga ma. Tana rike da hannun Hamza tace kuma yanzu a iska dreban jirgin yake gane hanya ko akwai alama da ake sakawa yadda bazasu bata ba? Yace wurin tukin nasu ne yake aiki da na'ura mai kwakwalwa tana nuna musu hanya sannan daga can airport dinma ana yi musu bayani... Suna shiga ciki har suka zauna ya daura mata seat belt yana mata bayanin yadda jirgi ke tafiya a sama. Kusa da taga ya zaunar da ita shi kuma yana gefe. Sai da ya gama bayaninsa tace ni dai duk bangane ba. Hamza ya ja mata kunne,amma shine kika barni ina ta surutu ko?

A hankali jirgin ya fara tafiya a kasa cikin Zuhra ya murda don tsoro ta kankame Hamza. Ihu taso yi lokacin da ya fara tashi har ta bude baki yayi saurin rufe shi da nasa. Bai kyaleta ba sai da yaji sun daidaita a sama.

Da sauri da sauri take fitar da numfashi ta dan bata fuska Ya Hamza muna cikin wannan yanayin wa yake ta soyayya? Sai da ya ja hancinta sannan yace ai magana ta kare tunda soyayyar ta hana ki cikawa mutane kunne da ihu. Harda wani kara lafewa a jikina,kai wannan yarinya kin zama abinda kika zama. Kunya taji da kawar da kanta tana kallon waje.

Daga nan hirar ta koma ta abubuwan da take gani. Suna haka aka kawo abinci. Zuhra tace kaji fitina har mutum yana da nutsuwar cin abinci a nan. Hamza yayi dariya yau yaga shirme wurin Cutie kala kala. Har dan bacci tayi wanda ta farka lokacin da jirgin ya fara sauka kasa.

Taxi suka samu zuwa hotel din da aka ce suje ana ya hadu da wasu mutum biyu da suma basu dade da zuwa ba suka gaisa. Mukullan dakunansu aka basu sannan mutumin da aka turo wurinsu ya sanar dasu karfe goma mota zata zo daukarsu saboda a yau zasu fara abinda ya kawosu.

Sai da Hamza ya tabbatar Zuhra ta sami nutsuwa sannan yayi wanka ya shirya. Kashedi yayi mata kada ta bude kofar sai karfe daya lokacin da yayi magana da receptionist za'a kawo mata abincin rana. Kamar kada su rabu lokacin da zai fita. Tayi ta masa addua sannan suka yi sallama.

Hajiya Izzatu har karfe uku bata fito daga daki ba. Tala ce tayi komai. Wayar kawarta wata baturiya Laura ta kira ta sanar da ita halin kuncin da Hamza ya sakata a ciki. AL'ADUN WASU 72

Batul Mamman(Mrs)





Laura ta gama jin korafin Izzatu tayi tsaki tace....
Duk laifinku ne 'yan Nigeria. Kuna bawa iyayenku mahimmanci fiye da yadda ya kamata. Na tabbata duk abinda mijinki yake miki yanzu don ya faranta musu ne.

Izzatu tace hakane amma kinsan mu addininmu da al'ada duk basu yarda da rashin biyayya ga iyaye ba.

To ai kuwa bazaki dena ganin bacin rai ba Izzy...Laura ta fada tana kara jin haushin al'ada irin ta hausawa....idan baki manta ba sai da nace kada ki yarda kuyi aure. Ku zauna tare ku haihu kamar yadda nayi. Duk lokacin da kika gaji dashi ki tattara ki bar masa gidan amma kika ki. Shawara daya zan baki shine kice ya zaba ko ke ko iyayensa da wannan matar da ya auro. Ni kinga mahaifiyata ce bata son Phil kinga tuni na yakiceta. Sai karshen shekara muke haduwa a wurin anniversary din mutuwar babana.

Izzatu tayi kasake tana jin gurguwar shawarar Laura. A ranta tace duk ranar da ta bawa Hamza wannan zabin to ko minti biyar tasan bazata kara a gidan ba. Su turawa basu san al'adunmu akwai bambanci ba. A gurguje tayi sallama da Laura domin ta fuskanci shawararta tamkar ta kama kafar wala ne. Dole ta sake sabuwar shawara amma zaman Zuhra a gidan nan bazarana yake ga igiyar aurenta.

******
Kullum karfe goma Hamza yake fita sai takwas na dare yake dawowa. Kafin ya dawo Zuhra zata wuni bacci amma yana dawowa to fa sai a bude soyayya. Zamansu suke lafiya cike da kwanciyar hankali. Basu da wata damuwa sai ta junansu. Kullum dai zai kira Izzatu kuma zai gaisa da 'ya'yansa. Rashin lokaci yasa bai sami damar kai Zuhra ko'ina ba. Amma ita kasancewarsu tare ya isheta shiyasa bata damunsa da su fita.

Ranar da zasuyi jarabawa Zuhra tayi ta masa addua. Karfe uku ya dawo ranar ya dauketa suka sami taxi suka fita gari. Shine har bakin ruwa(beach)ya kaita. Suka dan zagaya kasuwa ya siyawa Zuhra kananan kaya masu kyau don yaga bata dasu sosai. Wata rigar idan ya dauko sai taji kunya.

Asabar da lahadi ma duk yawo ya kaita sai ranar litinin suka biyo jirgin safe suka koma Kano. Wannan karon kauyancin Zuhra ya ragu. Nura ne ya sake zuwa daukarsu amma sai da ya biya gida ya gaisa da iyayensa sannan suka wuce nasu gidan.

Tun asuba Izzatu tasa Tala guaran gida ita kuma aka shige kitchen girkin tarar maigida. Tana jin tsayuwar mota tun daga bakin kofa ta taresu ta kankame Hamza tana murna. Kiss take zuba masa ko ta ina a fuska ga Nura a bayansa dauke da jaka sai kawar da kai yake sannan ga Zuhra da ta hade rai. Izzatu tayi dariyar keta, ko babu komai tasan Zuhra bazata iya yin abinda tayi ba. Shi kanshi Hamzan yanzu sai da yaji kunya sabanin da da suke abinsu hankali kwance.

Ko zama baiyi ba taja hannunsa suka tafi daki tana fada masa yadda tayi missing dinsa. Zancen yaya aikin da ya kaishi kuwa ko a waya bata yi. Bata da zance sai na korafin ya tafi ya barta.

Haka rayuwa ta kasance musu kowacce ranar girkinta tana kokarin farantawa mijinta rai. Kwanansu biyar da dawowa Hamza ya sami sako cewa yayi na uku a jarabawarsu ana bukatar ya kai passport dinsa Abuja ofishin minister domin neman visa. Da farincikinsa ya sanar da Izzatu saboda ranar girkinta ne. Tana jin haka ta tashi ta nufi dakinta.

Hamza ya bi bayanta da sauri don ya zata wani abin ne ya faru...Izzy saurin me kike yi haka ko gama sauraron abinda nace bakiyi ba?

Wardrobe ta bude ta janyo wata jaka sannan ta fuskance shi...naji abinda kace mana. Sai dai Sweety nasan ba abin mamaki bane idan kayi nasara saboda I believe in you my darling. Kayana zan hada na tafiyarmu Abujan....ta daga jakar sama, kana ganin wannan zata isa ko tayi kankanta?

Rasa bakin magana yayi sai binta yake da ido kamar lokacin ya fara ganinta. Babu godewa Allah, babu taya shi murna sai jaka da ta dauko zata hada kaya bayan shi kanshi bai sami cikakken bayani game da tafiyar ba. A kalla jakar zata dauki kaya bakwai zuwa goma idan an cusa su sosai. Ko ya fada mata a Abuja zasu yi course din ne bai sani ba. Haka ya fita ya barta ba tare da ya bata amsa ba ya tafi dakin Zuhra.

Kulu ne tumuli guda a gabanta tana warewa saboda ya samar mata wata makarantar sun bada kwangilar sakar rigunan sanyin makaranta.

Da murmushi ta tarbe shi tace Ya Hamza ba na hanaka satar kwana ba? Shima murmushin yayi ai kece satar kwanan. Ace mutum bashi da ikon ganin matarsa sai ranar girkinta.

Kusa da ita yaje ya zauna ya kama hannunta ya rike.

Cutie albishirinki? Idonta a kan fuskarsa tace goro Ya Hamzana.

Me zaki bani idan na fada miki?

Duk abinda kake so indai baifi karfina ba.

Ya shafa lebenta da yake kyallin lip gloss da ta saka mai kyau...so nake ki soni har abada kuma kada ki taba rabuwa dani.

Maganarsa tasa jikinta yayi sanyi saboda ta lura kamar yana cikin damuwa. A hankali tace Ya Hamza har a aljanna ni matarka ce in sha Allah. Amma nan...ta nuna lebenta...kai dashi sai jibi. Tana magana tana masa dariya. A hankali ya rinka sakewa. Dama bacin ran abinda Izzy tayi masa ne.

Cutie nayi nasarar cin wannan jarabawar har ana bukatar ganina a Abuja. Da murna Zuhra ta rungumeshi tana cewa Alhamdulillah. Can sai ta sake shi ta durkusa tayi sujjadar godiya ga Allah SWT. Tayi kusan minti biyu tana hamdala da takbir. Ko da ta dago kanta wasu zafafan hawaye ne suka sauko daga idanun Hamza. Kullum Zuhra daban yake ganinta.

A tsorace ta tashi yana daga zaune ta rungumeshi a kirjinta. Murya a raunane tace Ya Hamza me yasa ka hawaye?

Muryarsa a can kasa yace Cutie ina sonki. Ina sonki. Ina sonki. Kuma nagode miki for being who you are.

Sake kankameshi tayi tace nima ina sonka Ya Hamza. Uhmm sai dai dan turancin nan na karshe kace who you are ko.. Toh, I am Fatima Bashir.

Mai Hamza zaiyi in ba dariya ba. Zuhra tayi kicin kicin da fuska ita tayi fushi. Hamza ya rike habarta haba my darling Zuhra? Kada kiyi fushi dani. In sha Allah idan komai ya daidaita na wannan course din da za'a turani zamu fara English lessons dake. Dole na ware lokaci na koya miki da kaina.

Zuhra ta turo baki ni bazan koya ba kuma ka tashi ka koma dakinka ni munyi fada. Cakulculi Hamza ya rinka yi mata har ta soma dariya sannan ya fita zuciyarsa fari kal.

Washegari da safe ya sami cikakken bayani game da zuwansa Abuja. Da yake abin na gwamnatin tarayya ne kuma da izininsu kwana biyu aka ce zasu yi a tantance su. Babu wani zancen masauki alamun kowa yayi ta kansa kenan. Harda dariyar mugunta ya fadawa Izzatu basu da masauki saboda haka bazai tafi da ita ba. Kila yaje gidan abokinsa ya kwana. Itama dariyar tayi tace ta riga ta sanar da iyayenta batun zuwansu har an gyara musu wurin kwana a gidansu. Baiji dadin wannan karambanin ba shiyasa yace mata baza shi ba. Ko minti ashirin basuyi da maganar ba Alh Sunusi mahaifin Izzatu ya kirashi da kansa yace lallai yazo gidan anyi masa masauki ko da shi kadai ne. To ta yaya zaije gidan shi kadai dole ya tafi da Izzatu. A haka suka rabu yayi shirin tafiya office.

Da rana da ya dawo a kitchen yaji motsin Zuhra. Yana shiga ya tarar da ita tana rabon abinci a cikin irin abin take away dinnan. Jallop din shinkafa tayi sai kwai da ta dafa ta yanka shi bibbiyu take sakawa a abincin. Hamza ya dan dauki lokaci yana kallonta bata kula ba saboda ta juyawa kofa baya. A hankali yaje ya rufe mata ido tayi murmushi tace Ya Hamza ka dawo?

Cikin wasa ya bata rai, ya akayi kika gane nine?

Tace da kamshin turarenka mana.

Jera abincin yaga tana yi a wasu manyan robobi yace abincin meye wannan Cutie?

Ta dan kalle shi tayi murmushi...ni banso ka dawo ka tarar ban gama ba. Abincin sadaka ne zan bawa maigadi yace akwai makarantar allo a nan baya. Nayi da niyyar Allah Ya baka sa'a kuma Yasa kayi karatun ka gama lafiya. Tana kaiwa nan idonta ya ciko da kwalla, tunanin rabuwarsu da Hamza na wata biyu ke damunta. Shi kuwa kasa magana yayi kamar kodayaushe idan tayi wani abin da yafi karfin tunaninsa. Har abincin sadaka take yi wanda yasan akan yi lokaci lokaci a gidan iyayensa. A take yayi wa kansa alkawari indai ya sami sarari da yardar Allah Hajji zai kai Zuhransa. A duniya dai shine kawai abinda zaiyi mata na karshen jindadi a matsayinta na musulma. Amma a nan kanta ya dafa ya rinka saka mata albarka. Sonta kuwa kullum karuwa yake a zuciyarsa saboda kyawun halayenta.

Kwanaki biyu a tsakani su shirya tafiya Abuja. Izzatu sai rawar kafa take kamar farin shiga a zuwa Abuja. A motar Hamza suka tafi da aka gyaro. Zuhra tasha kukanta a daki Hamza na rarrashi sannan ta fito ta rakasu.

Kwanansu uku suka dawo aka fara shirye shiryen tafiyar Hamza zuwa kasar South Korea. Kwanaki uku suka rage ya tafi idan kaga Zuhra duk tayi wani iri. Har rama ta danyi saboda zulumin tafiyar Ya Hamza. Dambun nama ta roki Umma tayi mata saboda ita idan tayi duk sai rabi ya kone. Ai kuwa Umma tayi mai dadi musamman da tasan na tafiyar Hamza ne. Da aka kawo yayi ta murna.

Izzatu ma a nata bangaren cake tayi masa kanana mai dadi ta jera a wata roba sannan ta liketa saboda kada ya bushe. Itama Hamza yayi mata godiya.

Da asuba ana saura kwana biyu ya tafi kuma ranar Zuhra zata fita girki. Tunda ta idar da sallah take masa kuka. Duk abinda zaiyi mata tayi shiru yayi amma minti kadan sai ta cigaba. Ya zuba mata ido kawai yana kallonta.

Cutie wai kukan nan na meye? Ba fa yau zan tafi ba.

Ta dago jajayen idanunta...to meye maraba Ya Hamza daga yau kai da ka sake kwana...sai tayi shiru kanta a kasa

Ya share mata hawaye kina tunanin zanyi wata biyu bamy hada shimfida ba ko? Gashi ke kuma kina son kwanciya a jikin mijinki.

Rufe ido tayi a kunyace...ni ba haka nake nufi ba.

Hamza yayi dariya yace ai ba sai kin fada ba na sani. Addua kawai nake bukata daga gareki. Kinga jiya munfi awa daya ina nuna miki yadda ake whatsap saboda haka zamuyi ta hira kullum kinji ko. Idan kika yi kwalliya kullum ki turo min hotonki na gani.

Ta gyada kai wani hawayen na taruwa a idonta...Ya Hamza yau kada kaje ko'ina har sai lokacin da zan fita girki. Don Allah ka zauna dani.

Hannunta ya kama ya tasheta daga kan gadon. Muje har breakfast tare yau zamuyi.

Manne jikin juna suka sauko saboda asabar ce su Khalifa basu da makaranta. Sai karfe goma zasu je islamiyyar safe.

Kayan kwabin fanke Zuhra ta debo ta fara kwabawa. Hamza taji ya tsaya a bayanta ya zira hannu a robar da take kwabin yana wasa da hannunta sannan yana bin wuyanta yana kissing. Gabadaya aikin gagararta yayi cikin kankanuwar murya tace Ya Hamza don Allah ka bari na gama. Koma can gefen ka tsaya.

Yi yayi kamar yayi fushi yace ba ke kika ce kada na barki ba yau. Ni babu inda zani ya fada yana sake rumgumarta ta baya. Muryar Junior ce tasa ya saketa ba shiri da ya shigo kitchen din yana murza ido.

Maama fanken zaki yi min don Allah?

Zuhra tayi murmushi tace kaga har na gama kwabawa sai mu dan jira ya tashi ko.

Rungumeta yayi daidai kafarta yace Maama kinfi sona akan Daddy shiyasa kike dafa abinda nake so.. nima idan na girma ke zan fara siyawa mota da jirgi kafin Mummy da Daddy.

Hamza ya bude baki
yana kallonsa. Lallai yaran zamani kun iya sa ido. Kai yanzu har kasan so? Ya fada yana daga Junior sama suna dariya.


***********

Wannan shafin naki ne Maman twins. Gaisuwarki ta riskeni ina fata nima tawa ta iso gareki. Godiya mai tarin yawa tare da fatan alkhairi. Allah Ya albarkaci zuria. AL'ADUN WASU 73

Batul Mamman(Mrs)






Jirginsu Hamza shabiyu da rabi na dare zai tashi shiyasa ya yanke shawarar barin gidan karfe goma domin ya sami damar zuwa gidan iyayensa yayi musu sallama.

Sai da ya dawo daga masallaci bayan sallar isha sannan yaci abinci kadan yaje yayi wanka. Gidan duk yayi wani iri saboda kowa na tunanin tafiyar Hamza. Ya shirya cikin kananan kaya yayi kyau sannan ya dauki rigar sanyi a hannu saboda banda sanyin jirgi ya bincika ana sanyi sosai a South Korea. Ya gama shirinsa tsaf suka sake wata sallamar da Izzatu sannan ya fito zaije dakin Zuhra. Gabansa Izzatu tayi saurin tarewa ta daure fuska....Baby ina zaka je kuma?

Shima tasa fuskar a daure saboda bata masa lokaci da yake ganin zata yi yace zanje sallama da Zuhra mana.

Yana soma tafiya ta rike masa hannu....bafa zan yarda ba. Yau girkina ne saboda haka bai kamata kace zaka wata sallama da Zuhra ba. Ba tare zamu airport din ba? Sai kuyi sallamar a can.

Dan rufe idonsa yayi sannan ya bude a hankali....Izzy kada kisa mu rabu da bacin ran juna. Zanyi tafiyar wata biyu har zancen wani girki zai taso? Kije ki fito min da jakar kayana, idan bazaki iya ba ki jirani a kasa ina fitowa zamu tafi.

Bai kara saurararta ba ya tafi dakin Zuhra. Zaune ya ganta akan kujera tana sharar hawaye. Ta gama shiryawa ta saka wani katon hijab tana jira Hamza ya fito su tafi. Tana ganin ya shigo tayi saurin goge hawayenta ta mike tsaye...Ya Hamza har ka fito?

Murmushi yake yi yana kallonta. Na fito Cutie, wato baki dena kukan ba ko?

Kamar yace yi wani kukan ta soma wani sabo. Ya dauki lokaci yana bata hakuri da rarrashi duk ta hanyar da yasan zai dauke mata hankali. Da kyar tayi shiru tana fada masa irin yadda zata yi kewarsa idan ya tafi. Wayarsa ya dauko yana daukarta hoto tana ta rufe fuska wai bata yi kyau ba.

Yace gara na dauki fuskar a haka nasan cewa idan na tafi kullum zaki tuna dani kamar yadda zan tuna dake.

Jin haka yasa ta dauke shi itama sannan suka yi wani tare. Suna cikin haka suka ji wani mahaukacin bugun kofa. Yasan aikin Izzatu ne dama yana sane ya kulle kofar dakin don ba karamin aikinta bane ta bude su. Sai da ya sake yiwa Zuhra kyakkyawar sallama sannan suka fito tare fuskokinsu dauke da murmushin da ya kona ran Izzatu.

A gida aka bar yaran wurin Tala saboda dare ne. Kowa yana fadar me Daddy zai siyo masa na tsaraba. Suna zuwa gaban mota Izzatu tayi saurin shiga gaba. Dama Zuhra bata yi tunanin shiga ba saboda tasan ba ita ke da girki ba. Kafin su je gidansu Hamza taga kayan takaici kala kala. Hannun Izzatu a cinyar Hamza yana tuki. Ko ta sakala hannun a wuyansa ta wani kwanta a jikinsa. Yayi mata magana har ya gaji. Baya son abinda zai batawa Zuhra rai. Da suka je gidan Izzatu ta zauna kwam sai Hamza ya bude mata kofa. Hakan ya bashi damar tsayawa bawa Zuhra da ta fito hakuri. Don bata son ya tafi da baccin rai shiyasa ta nuna masa babu komai. Izzatu ta gaji da jiransa ta bude ta fito suka shiga ciki.

Duk kannen Hamza sun zo yi masa sallama. Mota uku suka yi zuwa airport wasu a tasa wasu a ta Ibrahim da Nura.

Sai da zai shiga ciki Izzatu ta soma kuka duk ana jinta ta rungume shi tana cewa zatayi missing dinsa. Tamkar ya tona kasa ya rufe kansa saboda kunyar kannensa dake wurin. Ibrahim barin wurin yayi saboda bacin rai. Sai da Hamzan yayi mata tsawa sannan ta kyale shi tana kallon yanayin Zuhra wadda ranta ya gama baci. Abinda yake gudu dai sai da ya faru sun rabo da Cutie dinsa ranta babu dadi. Key din motarsa ya bawa Izzatu yace su tafi gida ita da Zuhra don yasan ta kware a tuki.

Bayan ya shige ciki motocin su Nura da Ibrahim ne suka fara yin gaba sannan Zuhra da Izzatu suka tafi wurin motar Hamza. Da Izzatu ta bude ta shiga sai tayi saurin danna central lock ta rufe Zuhra a waje. A take hankalin Zuhra ya soma tashi ga dare ta fara buga glass tana yiwa Izzatu alama da ta bude mata. Glass din ta sauke kadan tace....naga babu abinda baki iya ba shiyasa kullum Hamza yake yabonki to wannan yabon ya kaiki gida. Daga nan ta fige mota tayi gaba ta bar Zuhra a tsaye.

Wayarta ma Hamza ya jona mata chaji tana cikin motar. Zuciyarta ke wani irin bugu saboda tsananin bacin rai. A rayuwarta bazata taba mantawa da Izzatu da ire-iren wulakancin da take mata ba. Kukan ma ta kasa ita daga airport din ma bata san hanyar da zata bi taje gida ba gashi tasan ko ba'a fada ba shabiyun dare ta kusa. Wani irin tsoro ne ya ziyarci zuciyarta ta fara addu'o'i. Jiki a sanyaye ta fara tafiya hanyar da tasan zata kaita bakin gate ta fita. Motoci kadan ne suke wuceta tana tafiya a gefen titi. Ga irin yanayin da muke ciki na raunin tsaro babu wanda ya tsaya yayi yunkurin taimaka mata. Itama ko an tsaya bazata shiga ba saboda tsoro.

Shabiyu saura minti uku Izzatu ta shiga gida. Maigadi ya tareta yana mata sannu da zuwa. Cike da nishadi ta shige ciki saboda ta gama tsara abinda zata fadawa Hamza idan Zuhra ta kai kararta. Rantsewa zata yi motar Ibrahim ta ga ta shiga shiyasa ta taho. Dama shima Ibrahim din ta tsane shi saboda tun farkon aurenta ta kula baya sonta. Kai tsaye dakinta ta wuce ta tafi ta kwanta hankali kwance.

Shiru Tala bata ga shigowar Zuhra ba tana son bata canjin kudin kulu da ta aiketa saboda bayan asuba take son tafiya garinsu zata je tayi sati biyu kamar yadda Hamza ya bada umarnin ta je. Gajiya tayi da jira ta fita waje maigadi har ya kwanta ta buga masa kofa ya fito ta tambayeshi ko yaga shigar Zuhra ciki. Yace shima yayi mamaki amma Izzatu ita kadai

Please Login or Register in order to submit comment