Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

da nashi yana kissing. Bata dade ba ta manta ta fushin ta biye masa. Bayan dan lokaci ta ture shi ya tambayeta dalili...ance babu kyau satar kwana.
Dariya yayi kafin yace wa ya fada miki satar kwana nazo yi? Sai gobe ya kamata muyi maganar rabon kwanan amma kawai sai naji ki shiru.

Zuhra tace naga ta dade bata gida ita ya kamata ta kwana. Nima bazan so ayi min haka ba. Ka tashi ka tafi.

Ya shafa lips dinta...sai da kika gama cinye min baki zaki ce na tafi.

Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi. Ya dago fuskata suka hada ido tayi saurin kawar da kanta....gobe akwai albishir da zanyi miki maidadi Cutie. Ki tanadi tukwicin da zaki bani. Ba a son ransa ya tashi zai barta ba.

Yana cikin tafiya yaji Zuhra tace..Ya Hamza I love you.

Iyakar karfin zuciyarsa ya tattaro ya fasa komawa wurinta. I love you more Cutie. Goodnight.

****
Izzatu ta cika fam kiris ya rage ta fashe. Hamza daga rufe kofa ina ya tsaya sama da minti goma. Zuciyarta tafi zargin yana dakin yarinyar da a yanzu ta tabbatar asirce mata miji tayi. Da sannu zata kama ta a hannu. Alkawari ne sai ta bar mata gidanta.

Da ya shigo dakin ko kallonsa bata yi ba ta tafi ta kwanta. Dama haka yake so, kwanciyarsa yayi ya juya mata baya yana tunanin Zuhransa. A haka bacci ya soma daukar shi. Hannun Izzatu yaji ta rungume shi...Baby ko goodnight kiss bazan samu ba? A goshinta yayi mata peck..goodnight Izzy. AL'ADUN WASU 71

Batul Mamman(Mrs)

A yadda Zuhra ta sani idan akace yau girkin mace ne to ita ke da alhakin ciyar da jama'ar gidanta. Sai gashi har tara da rabi Izzatu bata fito ba balle ta fadi me Tala zata dafa idan bazata yi da kanta ba. Su Nana tun wurin takwas suka tashi suka tafi dakin Zuhra. Dole ta farka daga bacci suka sauko kasa tare. Zaman jiran Izzatu suke yi amma shiru, karshe Zuhra ta tashi dama gudun rigima yasa bata dora komai ba tun farko. Kitchen ta shiga ta hada tea a wani jug din roba ta dauko bread guda da butter. A falo ta zauna tana ci tana bawa yaran ko kopi bata dauko ba. Suna haka Izzatu da Hamza suka sauko tare duk sunyi wanka. Tana ganin abinda Zuhra keyi ta soma fada don me zata hada breakfast bayan ba ita ke da girki ba. Zuhra ta dan ware ido ni fa ba girki nayi ba. Yunwa nake ji na hada tea shine naga suna so na basu a nawa.

Izzatu ta harareta, tea din cikinki ke kadai shine kika hada a jug?

Zuhra tace to ni haka na saba ki tambayi kowa a gidan nan. Tana gama magana ta tashi da jug din da suka shanye da ledar bread ita kuma kadan suka rage.

Sama ta wuce ko kallon wurin da Hamza yake bata yi ba saboda tsabar kishin da taji ganin sun sauko tare da Izzatu. Shima baiyi mata magana ba sai dariya da ta bashi. Zuhra daru, ita kuma irin nata kishin kenan. Dole ya koya mata ba'a kyale miji saboda kishi kada hankalinsa ya koma kan kishiya gabadaya. Sannan yadda ta ciyar masa da yara yaji dadi. Duk abin Izzatu bazata ce anyi mata karambani ba. Ya dade yana tashinta daga bacci amma taki tashi. Shi da su Tala ranar sun gasu don sai shadaya da rabi ta gama suyar pancake ta hada custard. Gudu biyu aka sakawa maigadi da custard a dan karamin kofin roba. Yana gani yasan cewa lokacin gashin kuma ya dawo.

*****
Sai bayan la'asar Hamza ya taso daga wurin aiki. Yana zuwa gida yayi wanka ya bukaci ganin Izzatu da Zuhra a falonsa. A jikinsa Izzatu ta zauna tana ta wani shige masa. A haka Zuhra ta shigo ta same su. Tamkar tasa ihu haka taji. Hamza yayi ta kokarin ture Izzatu tana kara manne masa. Karshe da yace ta dan matsa sai da tayi masa kiss a kumatu ta matsa gefe. Yana kallon sanda hawaye ya zubo daga idon Zuhra tayi saurin gogewa. A take yaji tausayinta ya kama shi kamar yaje ya dauketa. Gyaran murya yayi sannan ya fara da ambaton Allah kafin ya sanar dasu dalilin kiran.

Duk su biyun yake kallo yace...kamar yadda kuka sani duk wani magidanci yakan tara iyalinsa a lokacin da ya kara aure domin ya sanar dasu abinda yake bukata daga garesu na dangane da zaman lafiya a gidansa. Kowacce a cikinki sadaki na biya na aureta saboda haka babu wadda zan wulakanta kuma bazan yarda wata cikinku ta wulakanta ta ba. Abubuwa da dama sun faru tun kafin auren nan har zuwa yanzu amma ina fata mu manta da komai mu gina rayuwarmu bisa doron addini. Zaman lafiya da kwanciyar hankali nake bukata daga gareku ni kuma in sha Allah zanyi kokarin yin adalci a tsakaninku. Sai maganar rabon kwana....

Izzatu tayi saurin katse shi...rabon kwana ai ba sai anja zance ba a rinka yin sati sati...

Da sauri Zuhra ta dago suka hada ido da Hamza. Ko batayi magana ba yasan yadda ya hango shirme a shawarar Izzatu itama haka ta gani...Izzy sati daya yayi yawa,yadda muka saba ji anayi muma haka zamuyi wato kwana bibbiyu.

Izzatu tace to naji amma sai an rama min kwanakin da nayi da bana nan. Ga sati biyun zuwa Kaduna da Abuja sannan ga kwanakin zaman asibiti tara.

Hamza yace wannan sunansa lalura saboda haka ki manta dashi kawai. Gobe Cutie zata karbi girki and that is final. Sannan babu takura kowa zata yi girkinta. Wadda take da girki zata yi dani da su Khalifa da masu aiki. Abu na karshe dole mai girki tayi breakfast kafin tara ya zama ready, abin rana kada ya wuce azahar sannan na dare kada ya wuce magriba. Akwai mai tambaya?

Zuhra tace babu, ina iya tafiya?

Hamza yayi murmushi yana kallon rigima ta Zuhra. Ita da gaske fushi take yi dashi...to idan babu ni ina da abin fada. Nan ya sanar dasu sakon da ya samu daga wurin minister.

Wani ihun murna Izzatu tayi sannan ta haye cinyarsa ko la'akari da Zuhra bata yi ba....ni nasan abinda yafi wannan ma zaka iya Baby. Am so proud of you.

Tana ta kankame shi wani abin ma da gayya take yi Zuhra ta tashi don bazata juri kallon wannan kayan bacin ran ba. Tana fita Izzatu tayi dariya a ranta tace yarinya baki ga komai ba. Hamza dai tureta yayi yabi bayan Zuhra.

*****
A kan kujerar dakinta ya sameta tana kuka. Ya rufe kofar harda saka key ya dawo kusa da ita ya zauna. Jikinsa ya janyota ta ture shi. Hannuwanta ya kama yace kalle ni nan Cutie.

Bata iya masa musu ta dan daga kai amma bata kalli cikin idonsa ba.

Yace idan kina irin wannan kishin to kishiya ta gama dake. Wa ya fada miki ana share miji saboda kishi? Baki san sai nayi fushi ba nima na dena kulaki. Wadda tafi kulawa dani sai na tare a wurinta ke kuma sai lokacin da naga dama zan nemeki.

A dan tsorace Zuhra tace...Allah ko? To ya zanyi Ya Hamza?

Cike da tausayinta ya dorata a cinyarsa tare da rungumeta a jikinsa...kinsan wani abin yi za'ayi kawai don kiji haushi saboda haka ko anyi kiyi kamar baki gani ba. Sannan ki yawaita addua Allah Ya rage miki kishin da zai cutar dake. Ranar da nake tare dake kuma kema sai ki dage wurin kyautata kin yadda zanyi ta tunaninki koda bama tare.

Murmushin jindadi tayi...nagode Ya Hamzana..dazun ma kune kuke ta wasu abubuwa a gabana. Don Allah ai kaga dole naji babu dadi.

Fuskarta ta rike a tsakanin tafukan hannunsa...nasan fushin duk na meye bari kema na baki rabonki.

Matsowa taga yayi yana neman hade bakinsa da nata tayi saurin sa hannu ta tare. Ya Hamza babu kyau irin wannan fa. Yanzu idan gobe kayi min haka bansan irin kukan da zanyi ba...ta tashi tsaye ka koma wurinta amma gobe..sai ta kasa karasawa.

Dan bakinta ya shafa yace gobe zaki fanshe kwana biyun nan ko yana daga mata gira.

Ita dai bata ce komai ba ya fita. Tsalle tayi ta dire akan gado tana hango zuwan gobe. Tana juyinta cikin murna text din Hamza ya shigo wayarta. Sanar da ita yake ta fara shiri da ita zai tafi Lagos ranar litinin.

Kasa boye murnarta tayi wanda duk abinda Izzatu tayi mata ya dena tsaya mata a rai. Washegari da ta karbi girki kuwa banda sauran mutan gidan da suka san anyi canji Hamza yaga soyayya daga Zuhra irin wadda bata taba nuna masa ba. 'Yar kunyar nan da take hanata sakewa gefe ta ajiyeta na wannan lokacin. A wannan kwana biyun ko sabuwar amarya taga su Zuhra sai ta kara kallo.

An turowa Hamza kudin jirgi shiyasa da kudin hannunsa ya biyawa Zuhra. Tunda a hotel zasu zauna yasan dai zata sha kadaici idan ya fita amma duk yamma zuwa dare zasu kasance tare. Ana gobe zasu tafi ya bata kudi yace taje tayi kitso da kunshi. Unguwarsu tace zata je shiyasa ya kaita gida da kansa.

Bakin Umma ranar kamar gonar auduga. Zuhra tayi fes da ita kamar ba ita ba. Suna tare har Baba ya dawo. A tsakar gidansu aka kira mai kunshi tazo ta rangada mata mai kyau. Safara'u 'yar wan Baba da take zaune a gidan yanzu ita tayi mata kitso kanana mai kyau bayan ta wanke kan. Sai dare da Hamza yazo daukarta yake sanar da su Baba zancen tafiyar. Yasha addua da fatan alkhairi. Har gidansu Hajara sai da suka shiga dashi ya gaishe da su Mama sannan suka wuce gida.

Izzatu ta gama yanke shawarar biyawa kanta kudin jirgi ta bi Hamza. Har kaya ta gama hadawa ta ajiye kusa da jakar kayansa wadda Zuhra ta hada ranar da zata fita girki. Surprise zata yiwa Hamza idan ya dawo yau. Tasan dole yaji dadi tunda ya sauko ya dena fushin da ita. Bata san kokarin ya kamanta adalci tsakaninta da Zuhra yasa taga saurin shiryawarsu ba.

Da suka dawo kowa dakinsa ya nufa. Izzatu ta kawo masa abinci yaci sannan yake tambayarta game da jaka da ya gani kusa da kayansa. Da dan murmushinta tace kayana ne na tafiyarmu gobe.

Ba shiri ya tashi yana kallonta. Wane irin kayan tafiyarmu gobe? Ni nace zan tafi dake ne ko me?

Izzatu tace kwantar da hankalinka zan biyawa kaina kudin jirgi. Shiyasa ban fada maka ba saboda nasan zaka ji dadi idan na fada lokacin da baka tsammani.

Hamza ya hade rai...to kinyi kuskure da Zuhra zani....

A fusace ta tashi itama...wallahi baka isa ba Hamza. Ni zaka rinka wulakantawa akan wannan yarinyar. Shekararta ashirin da daya fa har zaka hada ta da mace kamar ni. Kuma meyasa baka fada min ba da wuri?

Girgiza kai yayi yana mamakin yadda take daga masa murya. Ban fada miki ba saboda gudun kada kizo ki tayar min da rigima kice sai kinje. Amma naga alama hakan ya zama kuskure. Ki zauna a gida ki karasa jinyar jikinki lafin mu dawo. Kuma bana son cigaba da maganar nan don banyi niya ba saboda haka idan wata tafiyarar tazo sai nayi dake idan naga dama.

Ficewa tayi daga dakin ta tafi dakin Zuhra rai a bace ta buga kofar da karfi tana masifa....Zuhra ki kiyayeni wallahi. Ki bar ganin na kyaleki lokaci na baki kafin na koreki daga gidan nan.

Hamza da yake bayanta yace tunda ki kike auranta ba. To kema ki kiyayeni wallahi ko gobe mu tafi airport tare ki koma gidanku. Kada ki kaini bango Izzy darajar 'ya'ya kawai kike ci kema kuma kin sani.

Zuhra dai kallonsu take daya bayan daya ta kasa magana. Tana kallo Hamza yaja hannun Izzatu suka fita. Ranar basuyi baccin arziki ba saboda yadda take ta fada. Sai da Hamza yace idan ta saki bude baki a bakin igiyar aurenta. Cikin masifa tace guda nawa? Yace sai kinyi maganar zan sanar dake ko nawa kika tsinke. Ba arziki ta yi shiru amma ta gama sikewa da Zuhra. Dole tasan yadda zata yi da ita kafin tayi sanadiyar kashe mata aure.

Tun bayan asuba Zuhra tayi wanka ta gama shiri saboda Hamza ya fada mata jirginsu karfe bakwai zai tashi.

Shima da wuri ya shirya ya shiga dakinta. Sai kai kawo take yi a tsakar daki. Tana ganinshi ta gaishe shi yace wannan tafiyar ta meye? Kinci abinci kuwa? Zuhra tace wane irin abinci Ya Hamza? Cikina sai kullewa yake saboda fargaba. Anya zan iya shiga jirgin kuwa. Yayi dariya idan bazaki iya ba sai na tafi da yayarki.

Jin haka Zuhra ta fita daga dakin da sauri har tana tuntube. Shi ya dauko mata akwatin kayanta yabi bayanta.

Da kyar ya samu tasha tea duk hankalinta baya jikinta. A tsorace kawai take da maganar shiga jirgi. Basu dade ba Nura yazo daukarsu shi zai kai su airport din. Har suka fita Izzatu ko kofar daki bata fito ba.

Ana shiga airport Zuhra na kara razana. Gabadaya a tsorace take. Hamza kuwa sai dariya yace yau ga 'yar kauye ga jirgi. Kamar tayi kuka tace Ya Hamza ko dai mu tafi tasha ne mu sami mota. Ya kama hannunta ya rike....Cutie kada ki damu babu inda zanje in barki kinji ko. A hankali ta gyada kai.

Cikin dan lokaci ya karbar mata ticket suka fita inda jirgin yake. Layi suka bi tare da wasu masu tafiyar. Zuhra sai kallo wai ita ce yau zata shiga jirgin sama. Ga wasu manyan jiragen da suka fi wanda zasu shiga ma. Tana rike da hannun Hamza tace kuma yanzu a iska dreban jirgin yake gane hanya ko akwai alama da ake sakawa yadda bazasu bata ba? Yace wurin tukin nasu ne yake aiki da na'ura mai kwakwalwa tana nuna musu hanya sannan daga can airport dinma ana yi musu bayani... Suna shiga ciki har suka zauna ya daura mata seat belt yana mata bayanin yadda jirgi ke tafiya a sama. Kusa da taga ya zaunar da ita shi kuma yana gefe. Sai da ya gama bayaninsa tace ni dai duk bangane ba. Hamza ya ja mata kunne,amma shine kika barni ina ta surutu ko?

A hankali jirgin ya fara tafiya a kasa cikin Zuhra ya murda don tsoro ta kankame Hamza. Ihu taso yi lokacin da ya fara tashi har ta bude baki yayi saurin rufe shi da nasa. Bai kyaleta ba sai da yaji sun daidaita a sama.

Da sauri da sauri take fitar da numfashi ta dan bata fuska Ya Hamza muna cikin wannan yanayin wa yake ta soyayya? Sai da ya ja hancinta sannan yace ai magana ta kare tunda soyayyar ta hana ki cikawa mutane kunne da ihu. Harda wani kara lafewa a jikina,kai wannan yarinya kin zama abinda kika zama. Kunya taji da kawar da kanta tana kallon waje.

Daga nan hirar ta koma ta abubuwan da take gani. Suna haka aka kawo abinci. Zuhra tace kaji fitina har mutum yana da nutsuwar cin abinci a nan. Hamza yayi dariya yau yaga shirme wurin Cutie kala kala. Har dan bacci tayi wanda ta farka lokacin da jirgin ya fara sauka kasa.

Taxi suka samu zuwa hotel din da aka ce suje ana ya hadu da wasu mutum biyu da suma basu dade da zuwa ba suka gaisa. Mukullan dakunansu aka basu sannan mutumin da aka turo wurinsu ya sanar dasu karfe goma mota zata zo daukarsu saboda a yau zasu fara abinda ya kawosu.

Sai da Hamza ya tabbatar Zuhra ta sami nutsuwa sannan yayi wanka ya shirya. Kashedi yayi mata kada ta bude kofar sai karfe daya lokacin da yayi magana da receptionist za'a kawo mata abincin rana. Kamar kada su rabu lokacin da zai fita. Tayi ta masa addua sannan suka yi sallama.

Hajiya Izzatu har karfe uku bata fito daga daki ba. Tala ce tayi komai. Wayar kawarta wata baturiya Laura ta kira ta sanar da ita halin kuncin da Hamza ya sakata a ciki. AL'ADUN WASU 71

Batul Mamman(Mrs)

A yadda Zuhra ta sani idan akace yau girkin mace ne to ita ke da alhakin ciyar da jama'ar gidanta. Sai gashi har tara da rabi Izzatu bata fito ba balle ta fadi me Tala zata dafa idan bazata yi da kanta ba. Su Nana tun wurin takwas suka tashi suka tafi dakin Zuhra. Dole ta farka daga bacci suka sauko kasa tare. Zaman jiran Izzatu suke yi amma shiru, karshe Zuhra ta tashi dama gudun rigima yasa bata dora komai ba tun farko. Kitchen ta shiga ta hada tea a wani jug din roba ta dauko bread guda da butter. A falo ta zauna tana ci tana bawa yaran ko kopi bata dauko ba. Suna haka Izzatu da Hamza suka sauko tare duk sunyi wanka. Tana ganin abinda Zuhra keyi ta soma fada don me zata hada breakfast bayan ba ita ke da girki ba. Zuhra ta dan ware ido ni fa ba girki nayi ba. Yunwa nake ji na hada tea shine naga suna so na basu a nawa.

Izzatu ta harareta, tea din cikinki ke kadai shine kika hada a jug?

Zuhra tace to ni haka na saba ki tambayi kowa a gidan nan. Tana gama magana ta tashi da jug din da suka shanye da ledar bread ita kuma kadan suka rage.

Sama ta wuce ko kallon wurin da Hamza yake bata yi ba saboda tsabar kishin da taji ganin sun sauko tare da Izzatu. Shima baiyi mata magana ba sai dariya da ta bashi. Zuhra daru, ita kuma irin nata kishin kenan. Dole ya koya mata ba'a kyale miji saboda kishi kada hankalinsa ya koma kan kishiya gabadaya. Sannan yadda ta ciyar masa da yara yaji dadi. Duk abin Izzatu bazata ce anyi mata karambani ba. Ya dade yana tashinta daga bacci amma taki tashi. Shi da su Tala ranar sun gasu don sai shadaya da rabi ta gama suyar pancake ta hada custard. Gudu biyu aka sakawa maigadi da custard a dan karamin kofin roba. Yana gani yasan cewa lokacin gashin kuma ya dawo.

*****
Sai bayan la'asar Hamza ya taso daga wurin aiki. Yana zuwa gida yayi wanka ya bukaci ganin Izzatu da Zuhra a falonsa. A jikinsa Izzatu ta zauna tana ta wani shige masa. A haka Zuhra ta shigo ta same su. Tamkar tasa ihu haka taji. Hamza yayi ta kokarin ture Izzatu tana kara manne masa. Karshe da yace ta dan matsa sai da tayi masa kiss a kumatu ta matsa gefe. Yana kallon sanda hawaye ya zubo daga idon Zuhra tayi saurin gogewa. A take yaji tausayinta ya kama shi kamar yaje ya dauketa. Gyaran murya yayi sannan ya fara da ambaton Allah kafin ya sanar dasu dalilin kiran.

Duk su biyun yake kallo yace...kamar yadda kuka sani duk wani magidanci yakan tara iyalinsa a lokacin da ya kara aure domin ya sanar dasu abinda yake bukata daga garesu na dangane da zaman lafiya a gidansa. Kowacce a cikinki sadaki na biya na aureta saboda haka babu wadda zan wulakanta kuma bazan yarda wata cikinku ta wulakanta ta ba. Abubuwa da dama sun faru tun kafin auren nan har zuwa yanzu amma ina fata mu manta da komai mu gina rayuwarmu bisa doron addini. Zaman lafiya da kwanciyar hankali nake bukata daga gareku ni kuma in sha Allah zanyi kokarin yin adalci a tsakaninku. Sai maganar rabon kwana....

Izzatu tayi saurin katse shi...rabon kwana ai ba sai anja zance ba a rinka yin sati sati...

Da sauri Zuhra ta dago suka hada ido da Hamza. Ko batayi magana ba yasan yadda ya hango shirme a shawarar Izzatu itama haka ta gani...Izzy sati daya yayi yawa,yadda muka saba ji anayi muma haka zamuyi wato kwana bibbiyu.

Izzatu tace to naji amma sai an rama min kwanakin da nayi da bana nan. Ga sati biyun zuwa Kaduna da Abuja sannan ga kwanakin zaman asibiti tara.

Hamza yace wannan sunansa lalura saboda haka ki manta dashi kawai. Gobe Cutie zata karbi girki and that is final. Sannan babu takura kowa zata yi girkinta. Wadda take da girki zata yi dani da su Khalifa da masu aiki. Abu na karshe dole mai girki tayi breakfast kafin tara ya zama ready, abin rana kada ya wuce azahar sannan na dare kada ya wuce magriba. Akwai mai tambaya?

Zuhra tace babu, ina iya tafiya?

Hamza yayi murmushi yana kallon rigima ta Zuhra. Ita da gaske fushi take yi dashi...to idan babu ni ina da abin fada. Nan ya sanar dasu sakon da ya samu daga wurin minister.

Wani ihun murna Izzatu tayi sannan ta haye cinyarsa ko la'akari da Zuhra bata yi ba....ni nasan abinda yafi wannan ma zaka iya Baby. Am so proud of you.

Tana ta kankame shi wani abin ma da gayya take yi Zuhra ta tashi don bazata juri kallon wannan kayan bacin ran ba. Tana fita Izzatu tayi dariya a ranta tace yarinya baki ga komai ba. Hamza dai tureta yayi yabi bayan Zuhra.

*****
A kan kujerar dakinta ya sameta tana kuka. Ya rufe kofar harda saka key ya dawo kusa da ita ya zauna. Jikinsa ya janyota ta ture shi. Hannuwanta ya kama yace kalle ni nan Cutie.

Bata iya masa musu ta dan daga kai amma bata kalli cikin idonsa ba.

Yace idan kina irin wannan kishin to kishiya ta gama dake. Wa ya fada miki ana share miji saboda kishi? Baki san sai nayi fushi ba nima na dena kulaki. Wadda tafi kulawa dani sai na tare a wurinta ke kuma sai lokacin da naga dama zan nemeki.

A dan tsorace Zuhra tace...Allah ko? To ya zanyi Ya Hamza?

Cike da tausayinta ya dorata a cinyarsa tare da rungumeta a jikinsa...kinsan wani abin yi za'ayi kawai don kiji haushi saboda haka ko anyi kiyi kamar baki gani ba. Sannan ki yawaita addua Allah Ya rage miki kishin da zai cutar dake. Ranar da nake tare dake kuma kema sai ki dage wurin kyautata kin yadda zanyi ta tunaninki koda bama tare.

Murmushin jindadi tayi...nagode Ya Hamzana..dazun ma kune kuke ta wasu abubuwa a gabana. Don Allah ai kaga dole naji babu dadi.

Fuskarta ta rike a tsakanin tafukan hannunsa...nasan fushin duk na meye bari kema na baki rabonki.

Matsowa taga yayi yana neman hade bakinsa da nata tayi saurin sa hannu ta tare. Ya Hamza babu kyau irin wannan fa. Yanzu idan gobe kayi min haka bansan irin kukan da zanyi ba...ta tashi tsaye ka koma wurinta amma gobe..sai ta kasa karasawa.

Dan bakinta ya shafa yace gobe zaki fanshe kwana biyun nan ko yana daga mata gira.

Ita dai bata ce komai ba ya fita. Tsalle tayi ta dire akan gado tana hango zuwan gobe. Tana juyinta cikin murna text din Hamza ya shigo wayarta. Sanar da ita yake ta fara shiri da ita zai tafi Lagos ranar litinin.

Kasa boye murnarta tayi wanda duk abinda Izzatu tayi mata ya dena tsaya mata a rai. Washegari da ta karbi girki kuwa banda sauran mutan gidan da suka san anyi canji Hamza yaga soyayya daga Zuhra irin wadda bata taba nuna masa ba. 'Yar kunyar nan da take hanata sakewa gefe ta ajiyeta na wannan lokacin. A wannan kwana biyun ko sabuwar amarya taga su Zuhra sai ta kara kallo.

An turowa Hamza kudin jirgi shiyasa da kudin hannunsa ya biyawa Zuhra. Tunda a hotel zasu zauna yasan dai zata sha kadaici idan ya fita amma duk yamma zuwa dare zasu kasance tare. Ana gobe zasu tafi ya bata kudi yace taje tayi kitso da kunshi. Unguwarsu tace zata je shiyasa ya kaita gida da kansa.

Bakin Umma ranar kamar gonar auduga. Zuhra tayi fes da ita kamar ba ita ba. Suna tare har Baba ya dawo. A tsakar gidansu aka kira mai kunshi tazo ta rangada mata mai kyau. Safara'u 'yar wan Baba da take zaune a gidan yanzu ita tayi mata kitso kanana mai kyau bayan ta wanke kan. Sai dare da Hamza yazo daukarta yake sanar da su Baba zancen tafiyar. Yasha addua da fatan alkhairi. Har gidansu Hajara sai da suka shiga dashi ya gaishe da su Mama sannan suka wuce gida.

Izzatu ta gama yanke shawarar biyawa kanta kudin jirgi ta bi Hamza. Har kaya ta gama hadawa ta ajiye kusa da jakar kayansa wadda Zuhra ta hada ranar da zata fita girki. Surprise zata yiwa Hamza idan ya dawo yau. Tasan dole yaji dadi tunda ya sauko ya dena fushin da ita. Bata san

Please Login or Register in order to submit comment