Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inci, Maama ta iya girki.

Izzatu tace haba ko da naji,ashe Zuhra ce ta dafa. Kaga irin abinda nake fada maka ko. Yarinyar nan bazata ta taba wayewa ba. Kamar kai Baby aci wake da shinkafa a gidanka sai kace wani talaka. Jikin Zuhra duk yayi sanyi.

Hamza yace Cutie ga key ku tafi mota da yaran ina zuwa. Tana fita ya zauna a gaban Izzatu ya warware mata halin da yake ciki da irin gudummawar da ta bayar wurin fadawarsa wanda yasa ta mugun mamaki. Ya mike tsaye...saboda haka Izzy ki kiyayeni domin ko banyi aure ba ina gab da sakinki wallahi saboda kin jefani cikin tashin hankali sannan dayake kinfi amara son biki kika tsallake kika barni. Izzatu tace don ka sami matsala sai kayi min sharri? A take ya tuna mata duk abubuwan da tayi wadanda sukayi sanadiyarsa fadawa wannan halin. Baki bude haka ya fita ya bar Izzatu da Raliya don ma bai fada musu yadda Zuhra ta taimaka masa ba. AL'ADUN WASU 69

Batul Mamman(Mrs)






Daga asibitin gidan 'yan uwansa mata suka wuce. Dukkaninsu sunyi farincikin ganin Zuhra kowacce tana janta a jiki. Daga nan suka je gidan Anti Faiza wadda ta rasa inda zata sa kanta don murnar ganin Zuhra da Hamza tare. Dabarun kula da miji ta sake karanta mata da kyau sannan na karshe suka je gidan Ibrahim. A nan suka ci abincin dare sannan suka taho bayan Hamza da Ibrahim sun dawo daga sallar isha.

Kafin suje gida su Khalifa duk sunyi bacci sai Hamza da Zuhra ke ta hira. Kayan da suka biya suka siyo Zuhra ta iya dauka yaran kuwa Hamza ne ya dauko su. Dama sauri take su iso gida gabadaya bata jindadin jikinta tun yamma daurewa kawai take yi tana tafiya.

A dakinsu ya kwantar dasu Zuhra ta fadawa Tala taje ta kwana dasu sannan ta hau sama. Tana tafiya Hamza na binta da ido, jan kafa kawai takeyi tana tafiya da kyar. Tun yamma ya kula da yadda tafiyarta ta canja amma idan taga mutane sai ta daure ta rinka tafiya daidai tana bata rai. Girgiza kai yayi saboda yasan meye matsalarta.

A dakinta ya sameta tana daura tawul zata yi wanka yace ta jira shi yana zuwa. Turo baki tayi ...Ya Hamza don Allah kada kace zaka yi min wanka yau ni bama ni da lafiya. Yace to Allah Ya sauwake, maganin ciwon naki zan baki. Idonta har ya fara kwalla tace kasan me ya sameni ne? Cike da tausayawa yace na sani Cutie, bari ki gani ina zuwa.

Toilet dinta ya shiga ya tara ruwa mai zafi sosai a katuwar roba ya sirka shi kadan sannan ya fito ya cire rigarsa ya bar singlet yace muje. Duk ta gama tsorata ta fara ja da baya. Bai tsaya sauraronta ba ya dagata tanata dukansa. Tawul din kawai ya zare ya sakata a cikin ruwan zafin. Ihun da tayi yana tsammanin har maigadi sai yaji domin ba wutar inji bace bare ya rage sautin karar.

Zuhra kuka take yi sosai tana kokarin tashi Hamza ya tsaya daga bayanta ya danna kafadunta. Ya Hamza akwai zafi sosai.

Na sani kiyi hakuri, son jiki irin naki yasa baki shiga ruwan zafin tun da safe ba. Yayi 'yar dariya... Yau duk mai hankali kin gama tona min asiri a wurinsa da wannan tafiyar taki.

Sharkaf haka fuskarta ta jike da hawaye tace na shiga ruwan zafin da asuba.

Hannuwanta ya rike da take neman tashi tsaye yace nasan kin shiga ruwan da kika gama sirkawa ba. Wannan idan kika haihu da kaina zan miki wankan jego don kada ki cuce ni.

Muryarta har ta soma dashewa tace cuta har ta wuce gasa ni da kake yi. Ta kai masa cizo a kirji ya kauce yana dariya. Zumbura baki tayi kuma na dena sonka.

Yana dariya yace babu komai Cutie son da nake miki ya ishemu ai.

Bata kula ba ya sake kara ruwan zafin saboda na robar ya fara hucewa. Kuka kala kala Hamza ya gani. Da kyar take magana don bakin ya mutu. A hankali tace to ka dawo ta gabana na rungumeka naji dadi.

Yadda tayi ya bashi tausayi amma yasan abinda yayi mata zaisa taji dadin jikinta. Zagayowa yayi ta rungumeshi tana kuka yana shafa bayanta. Bai kyaleta ba sai da tayi kusan minti talatin a cikin ruwan zafin sannan kamar jiya yayi mata wanka. Sai da ya shiryata sannan ya shiga wankan shima. Kafin ya fito tayi baccin wahala. Gyara mata kwanciya yayi ya rumgumeta cike da tausayawa. A haka suka yi bacci tana kwance a jikinsa.

Yau dai bata ji kunyar tashi da asuba ba har Hamza na tsokanarta. Da wuri ta kammala ayyukanta na gida saboda jiki yayi kwari ta dena tafiya da kyar. Da tayi zancen zuwa asibiti Hamza yace bazashi ba office zai tafi. Itama baiyi mata izinin taje ba. Ganin ya dauki zafi yasa bata matsa masa ba. Bata damuwa da bin kwaf akan matsalarsa da Izzatu. Tare ta gansu tasan idan fushin ya kare zasu daidaita. Kullum Tala ke kai abincin asibitin.

Cikin 'yan kwanakin nan Zuhra da Hamza sun kara shakuwa sosai. Soyayya yake nuna mata tamkar wata 'yar yarinya haka yake lallabata. Itama dai ta fara sakewa dashi amma har yanzu tana jin kunyarsa. Ko kayan bacci tasa sai yayi da gaske yake cire mata hijab. Ana tashi daga office gida yake tahowa su sha soyayyarsu. Ana haka Hajiya ta kirashi tana masa fadan kwana biyu bata ganinsa a asibiti meye dalili. Dama yasan ba son Izzatu suke yi ba, idan ya fadi abinda tayi kuma kara wutar abin zaiyi sai kawai ya bata hakuri yace ayyuka ne suka saka shi a gaba.

Kwanan Izzatu tara a asibitin sannan aka sallameta. Duk irin nasiha tagari Raliya tayi kokarin yi mata domin ta samu ta rike igiyar aurenta dake lilo a iska. Itama ta danyi karatun ta nutsu saboda bata taba tsammanin zai iya shareta haka ko waya babu ba. Tun safe akayi sallamar ta kira shi a waya yana can jikin Zuhra bai bi ta kai ba. Sai daga baya yaga missed call ya kira tace an sallameta ne tun safe. Hamza yace to sai ki tari adaidaita sahu ki taho gida ni motata jiya da kyar ta kawoni gida. Anjima kadan makanike zai zo ya dauka. Kamar ya kwada mata guduma haka taji maganar tasa. Adaidaita sahu kuma??? Ita ba don kada tayi karya ba sai ta iya cewa bata taba shigarsa ba. Motoci uku ne a gidansu kuma duk inda zata indai ba aiki ne yayi masa yawa ba Hamza da kansa yake kaita. Gashi ko zancen motarta da ta bari a Kaduna baya yi. A sanyaye tace Baby ko daga gidanku kasa azo a daukeni mana. Saboda yadda ta bashi haushi ko amsa bai bata ba ya ajiye wayar.

Zuhra na falo tana biyewa yara suna shirmensu Hamza ya fada mata an sallami Izzatu tayi abinci da ita. Tace Mamanta fa? Gidan kanwarta zata wuce, kisa Tala ta gyara mata daki kafin ta karaso. Yana gama magana ya shige falonsa. Sakonsa ta fadawa Tala sannan tabi bayansa dama ta riga tayi girkinta kuma zai isa indai cikin Izzatu ne ita kadai.

Kwance ta same shi akan doguwar kujera ya dafe kansa da hannu daya idonsa a rufe. A hankali ta rinka tafiya har tazo gabansa ta durkusa. Gashinta ta janyo daga cikin dankwali ta matso kusa dashi sosai sannan ta zira masa gashin a kunne tana wasa dashi. Da sauri ya bude ido ya dagota ta fado jikinsa. Kinci bashi Cutie ya fada yana karkade kunnensa. Tayi dariya kai dai kaji tsoro kawai zaka wayance. Hancinsa ya goga a jikin nata yana murmushi...Cutie I love you so much. Ganinki yana sa na manta damuwata. Mayar masa da murmushin tayi tace I love you too. Amma yanzu ka tashi muyi magana kaji. Ba haka yaso ba a yadda ta kwanta a jikinsa so yayi su zauna a haka. Yace idan na tashi kin min alkawarin zan sami duk abinda nake so. A kunyace tayi hada bakinta da nasa tace harma da kari.

Zama ya gyara ya dorata akan cinyarsa. Ina jinki Cutie. Har wani dan gyaran murya tayi sannan tace Ya Hamza nasan bani da wani iko akan duk matsalarka da mamansu Khalifa. To amma abinda yake faruwa yanzu yana iya shafarsu. Idan har iyaye na fushi da juna yara su kan gane idan sun fara wayo. Jiya Khalifa cewa yayi yanzu baka zuwa wurin Mummy dinsu saboda tayi maka laifi. Nayi kokarin yi masa wayo nace kana zuwa. Daga baya yazo yace yanzu nice mamansu ko, ita kuma zata koma Abuja su dena ganinta. Bansan ya akayi yake irin wannan tunanin ba amma ya kamata ka nuna masa ba haka bane. Yanzu yaro ne bazai kawo komai ba, amma nan gaba idan ya kara wayo zai ga kamar baka sonta ne. Daga nan ko kai ko ita zai goyi bayan daya ya bar dayan wanda hakan bai dace ba.

Hamza kallonta kawai yake yi har ta gama bayaninta. Fuskarsa dauke da murmushin jindadi, shi kam yaga ranar biyayya ga iyaye. Iska ta busa masa a ido da taga baya kiftawa. Ya shafa fuskarta, Zuhra ke dabance a mata. Lokacin da ya dace kiyi farinciki hankalin miji ya dawo gareki gabadaya sai kike tunanin kyautatawa wadda tayi sanadiyar jefaki cikin kunci.

Zuhra tayi saurin dora yatsanta a bakinsa...Ya Hamza ni bana cikin kunci. Na aureka ba don ina so ba amma yanzu bana fatan ganin ranar da zamu rabu. Yayi murmushi Allah Cutie? Kice karatun da na koya miki yayi aiki kenan. Kunya taji ta sunkuyar da kai, ni ba haka nake nufi ba. Yayi murmushi ni haka nake nufi. In Sha Allah zanyi kokarin gyarawa kuma. Sai dai sai kinyi min hakuri da kunnenki kika ji abinda tayi. Zuhra tace babu komai indai zaka gyara itama zatayi da yardar Allah. Hamza ya jinjina kai, Cutie fada min gaskiya ke bakya jin haushin duk abinda tayu miki? Zuhra tace tabdi, ya za'ayi naji haushi ta hadani da mijin da babu kamarsa. Tana fadar haka ta tashi ta gudu tana masa dariya.
******

Mai adaidaita sahu ga gaji da ihun da Izzatu take yi ko yaya suka shiga gargada. Dama da ganinsa ko ba'a buge yake ba to yana dan tabawa ya kallota ta mudubi idanunta wuri wuri. Ke Hajiya ya zaki rinka min ihu kamar yau kika fara shiga adaidaita? Izzatu ta kankame karfen gefen da take tana mai nadamar kin bin mamanta a wanda ta tafi...ban taba shiga ba wannan ne shigata ta farko. Dan matashin yayi dariya yace shegiyar karya kice daga turai jirginki ya sauka kawai. Kallon yadda yake kurdawa tsakanin motoci take yi baki na rawa tace wallahi ba karya nake yi ba a Canada na girma. Dreban ya kwashe da dariya yace bari na dan shillaki kiji kamar a jirgin Canadan kike.

Ai bata kara samun nutsuwa ba sai da ya tsaya a bakin gate din gidanta. Gudu yake yi da ita sosai har wani abokinsa na tambayarsa ina zuwa haka da suka tsaya a danja yace yau Canada ya nufa. Izzatu taga tashin hankali duk jikinta ya bugu. Kafarta kamar bazata dauketa ba da suka tsaya a kofar gida.

Maigadi ne ya kwaso mata kayanta ta shiga ciki tana jan kafa. Tana shiga falon idonta ya dire akan Zuhra zaune a kan ledar cin abinci ta dora Nana a cinyarta ga Junior da Khalifa duk sun zagaye tray suna cin abinci. Zuhra ta dago kanta a dan tsorace tace mata sannu da zuwa. Ko bi ta kanta bata yi ba tace where are your table manners kids? Yaushe kuka fara cin abinci a kasa kuma a tray? Khalifa yace zumunci yake karawa. Izzatu ta dakawa Tala tsawa, daukesu ki zubawa kowa plate dinsa su koma dinning table. Tala ta ruga kitchen a ranta tana cewa shikenan mun shiga uku.

Sai a lokacin Izzatu ta karewa abincin kallo tace meye wannan kuke ci a wulakance. Zuhra taji babu dadi. Farar shinkafa ta dafa sannan tayi miyar alaiyahu. Jajjagen attaru da albasa tayi sai tumatir kadan ta soya da manja ta zuba alaiyahu wanda ya tsane ruwansa sannan ta dafa kwai ta sakawa kowa. Tala na zuwa da plate din Hamza ya fito yace ta mayar ko kallon Izzatu baiyi ba ya koma falonsa rai a bace. Zamansa kenan wayarsa tayi kara ya dauka.

Mutumin yace shine sakataren ministan tsara birane. An turowa Hamza sakon email ana bukatar ya karanta ya turo reply kafin gobe. AL'ADUN WASU 70

Batul Mamman(Mrs)





Hamza.
Hamza..
Hamza....
Shigowar Izzatu falon nasa tana kwala masa kira yayi daidai da faduwar wayarsa daga hannunsa saboda yadda kiran nata ya dan razana shi. Ya fuskanci kamar da gayya Izzy ke zuwa a lokacin wani abu mai mahimmanci ta wargaza komai. Sunkuyawa yayi ya dauki wayar ya mayar da batir zai kunna tazo ta tsaya rai a bace. Yanzu Baby don kayi aure shikenan ni ban isa ba a gidan nan? Menene dalilin da zaisa ka hana Tala rabawa yara plates kamar yadda na saka ta?
Hamza ya fasa kunna wayar kada ya bude email din Izzatu tayi abinda zai kasa fahimta ya bayarda amsar da bata dace ba. Sai da ya zauna sannan yace...daga yanzu da kika shigo gidannan zaki ga changes wadanda suka sha bamban da abinda kika saba dasu. Duk wanda baiyi miki ba ki fara magana dani kafin kice zaki gyara shi. Maganar yara na cin abinci a tray nima jiya haka muka yi dasu duka. Once in a while dai family suyi sharing plate yana kara saka shakuwa a tsakaninsu. Yanzu ki taimaka ki tafi daki kiyi wanka ko abinda ranki yake so kafin nazo na sameki. Yana kaiwa nan ya fita ya wuce dakinsa.

Wayarsa ya kunna ya duba email din. Gayyatarsa akeyi zuwa workshop da za'ayi a Lagos na kwana hudu. Daga litinin zuwa alhamis, a ranar juma'a kuma za'ayi musu gwaji a fitar da mutum biyar da suka yi nasara a turasu Korea course na wata biyu. Jin abin yayi kamar a mafarki ya sake karantawa. Su goma aka zaba su halarci workshop din. Idan ya amince zashi akwai inda zai danna alamar ya amince sai su turo masa da kudin jirgi. Hatta hotel din da za'a sauke su a kwanakin da zasuyi duk an tanada. Hamza dai ya rasa bakin magana sai cewa yaje IKON ALLAH. Shi bazai iya tuna lokacin da ya tura application na halartar workshop din ba. Inuwa sakatare ne ya fado masa yayi saurin kiransa. Bayan sun gaisa yake sanar dashi abinda ke faruwa. Inuwa yace Alhamdulillah, ranka ya dade ai kusan wata biyu kenan da naga tallan abin a labaran NTA sai kawai na bude website dinsu na cike maka tunda naga abin na architects ne. Banyi tsammanin zamu sami nasara ba shiyasa nayi shiru da zancen.

Hamza yace Allah Mai iko da daukaka ni bansan me zance maka ba Inuwa. Allah Ya saka maka da mafificin alkhairi.

Inuwa yayi dariya ranka ya dade ai bazan taba biyanka alkhairin da kayi min ba a rayuwata. Ban gama karatu ba ka bani aiki kuma ka cigaba da biya min kudin makaranta har na kammala. Allah dai Ya sanya mana alkhairi a wannan aikin Ya bamu sa'a.

Amin Hamza yace sannan ya ajiye wayar. Addu'ar tsohuwar nan da suka hadu a kasuwa ya tuna yayi murmushi. Lallai Allah shine mai bayarwa ga wanda Yaso a lokacin da Yaso. Duk wannan abu a dalilin canjin ra'ayi da ya samu ne ya kyautatawa Zuhra. Hakika Allah Yayi gaskiya da Yace a suratul Rahman " Hal Jaza'ul Ihsani Illal Ihsan"...babu wani sakamako ga kyautatawa sai kyautatawa.
Hamza ya gyara alakarsa da matarsa wadda ya aura domin ya wulakanta. Ya bata damar zama wata jigo a rayuwarsa gashi tun ba'aje ko'ina ba yaga sakamako mai kyau a lokacin da yake cikin halin matsi da takura. Sai gashi komai yazo masa da sauki tunda ba'a taba rasa abinci a gidansa ba. Da duka mutane zasu zama masu kokarin kyautata alaka da sauran mutane da hakika zamu ga taimakon Allah a cikin dukkan al'amuranmu. Ya Allah Ka taimaki Nigeria da shuwagabaninta da dukkan kasashen da musulmi ke ciki. Amin

Sallah Hamza yayi raka'a biyu yayi godiya ga Allah SWT sannan yayi addu'ar samun nasara. Baiyi saurin fadawa kowa ba yana jira sai dare ya fara sanar da Zuhra amma kafin nan ya fita zuwa gidansu. A nan ya fadawa su Alhaji wayar da ya samu. Alh Nasiru yayi murna sosai tare da yi masa fatan alkhairi. Su Hajiya ma duk sunyi farinciki suka yi masa addua. Yana fitowa bai biya ko'ina ba sai gida.

*****
Izzatu ta sauko falo tana tafiya tana rangwada jiki. Tun daga sama take jin hirar Zuhra dasu Khalifa. Tana saukowa ta zauna daga can gefe ta fara kiran yaranta daya bayan daya. Abinka da da da uwa duk sai suka koma wurinta suna bata labaran abubuwan da suka yi lokacin da bata nan. Ko kadan Zuhra bata nuna damuwa ko bacin rai ba sai da ta tashi suka hada ido da Izzatu ta jefa mata muguwar harara. Bata tanka mata ba ta tashi ta shige kitchen zuciyarta babu dadi. Ita dai tana tsoron zaman da zatayi da Izzatu.

Da ta gama abinci ta zubawa su Junior a plates daban daban yadda taga Izzatu tana so sai dai bata same su a falo ba. Tala ta tura ta kirasu suzo suci abinci. Ko da taje dakin Izzatu ta fadi sakon Izzatu cewa tayi taje ta dafa musu indomie guda uku ita da yaran. Khalifa ya tashi Mummy ni dai abincin Maama zanci. Indomie uku bazamu koshi ba. Junior ya tashi nima haka Mummy kizo muje tare akwai dadi ya fada yana jan hannunta. Izzatu ta fizge hannu tace Zuhra ba mamanku bace nice mamanku. Ita bata sonku, so take Daddy ya koremu mu bar mata gidan ita kadai. Khalifa yayi shiru alamar tunani...ni dai Maama tana sona da gaske. Amma bari naje na tambayeta dama tace duk wanda yake fadar abu ba mai kyau ba akan wani idan baya nan jirgin aljannah a Kano zai barshi. Ran Izzatu ya baci tace idan ka sake min zancen jirgin aljannah sai jikinka ya gaya maka. Kuma duk ku sami wuri ku zauna ko na zane ku. Babu musu suka zauna suna mata kuka. Juyawa tayi taga me Nana take yi a gaban dressing mirror taga bata nan. Da sauri ta tashi ta fita, ta sama ta hangota Zuhra na bata abinci. Ta girgiza kai wannan yarinya da shegen cin abinci take, bata san lokacin da ta fice daga dakin ba. Dole ta kula da abinda Nanan take ci saboda kada tayi kiba sosai.

Tala ta kawo indomie haka su Khalifa suka ci ba don rai yana so ba. A dakin nata suka yi bacci Izzatu tasa Tala ta kaisu dakinsu.

Zuhra dai tasan duk neman rigima ne yasa Izzatu ta hana su Khalifa cin abincinta. Babu ruwanta tunda 'ya'yanta ne fatanta Allah Yasa sun koshi da indomie din da aka dafa musu. Wurin karfe tara ta tashi daga falon ta koma dakinta. Dama bata yi gangancin zuwa dakin Hamza ba don tasan ko ba'a fada ba Izzatu ya kamata taje ta kwana dashi. Abincinsa ta ajiye a dinning table sannan ta tafi.

****
Da murnarsa ya shigo gidan yau zaiyiwa Zuhra kyakkyawan albishir. Ganin bata falo yasa ya zauna ya ci abincinsa sannan ya tafi yayi wanka. Idan yayi tunanin Cutie dinsa sai yayi wani shu'umin murmushi. Yasan tana daki ana gyara jiki bata yarda tazo dakinsa ba wanka saboda sai ya yi mata fin karfi yayi mata da kansa. Air freshner ya fesa a dakin yana mamakin yadda akayi yau har ya dawo bata fesa ba. Shi da kullum idan ya dawo dakin sai sanyi da kamshi.

Wata hadaddiyar rigar bacci Izzatu ta saka mai kyau. Ta gyara jikinta tana zuba kamshi ta fito ta rufe daki. A ranta ta kudurce idan har Zuhra na dakin to sai dai su kwana su uku don bazata fita ba.

Duk abubuwan da yake kafin ya kwanta ya gama ya koma falonsa yana duba karin bayani game da workshop din da aka gayyace shi. Ba karamin project gwamnatin tarayya zata bawa wadanda suka yi nasara ba. Hankalinsa na kan aikinsa yaji an rufe masa idanu ta baya. Shiru yayi ya shaki kamshin wanda a take ya gane mai shi. Da sauri ya cire hannuwanta daga idonsa ya kalleta fuskarsa babu fara'a. Lafiya, kika shigo min daki a daren nan?

Murmushi tayi don tasan har yanzu Hamza na fushi da ita. A hankali zata karkato da hankalinsa gareta har ya gane abinda tayi domin inganta rayuwarsu ne ba don ta kuntata masa ba.
Ta sunkuyo zata yi kissing dinsa yayi saurin kawar da kansa gefe. Yanzu Izzatu bata burgeshi ko me zata yi abubuwan da tayi masa kawai yake tunawa.
Fuskarta kamar zata yi kuka tace Sweety ya kamata ka manta da dukkan abinda ya faru mu sake gina rayuwarmu kamar da. Nasan nayi maka laifi ina rokonka ka yafe min.

Wani irin kallo yake mata na rashin gamsuwa da abinda take fada....zancen na yafe miki kema kinsan ba abu bane da zai iya faruwa lokaci daya. Mu bar wannan zancen ma, na fada miki duk irin asarar da kika janyo min amma baki ce komai ba. Duk wata kadara da kika san ina da ita na sayar. Motata ce kawai ta rage da taki. Wace gudummawa zaki iya bani domin ganin mun cigaba da running din gidan nan kamar yadda muka saba?

Izzatu tayi saroro tana kallonsa. Ita bata dauki abin serious ba lokacin da ya fada mata. Tayi ajiyar zuciya...nima bani da wani kudi yanzu duk nayi amfani dasu a wurin biki. Amma zanyi kokarin taimaka maka da gyaran tawa motar. Sun kira maigyara yace zata ci kamar sixty thousand.

Hamza yayi murmushi tare da girgiza kai. Izzatu kenan, ita nata taimakon a kanta zai kare kenan. Yace to babu komai a hakan ma nagode.

Taji dadi ta sami wuri kusa dashi ta zauna...nasan wannan problem din is not permanent amma zanyi kokarin ganin mun rage kashe kudi sosai. Abinci da kake siyo mana every thursday sai ka rinka siyowa a wurin da bai kai na da tsada ba, sannan...

Bai bari ta karasa magana ba ya tashi..bari naje na rufe gidan ina zuwa. Ko sake kallonta baiyi ba ya fice ya barta zaune. Gani yayi idan ya cigaba da zama ransa ne zaiyi ta kuna a banza. Ita a irin nata hankalin duk abinda ta lissafa gani take yi ba karamin taimako tayi masa ba kenan.

Babu wani rufe gida da zaiyi domin ya rufe tunda ya dawo. Dakin Zuhra ya nufa yaji dalilinta na kin zuwa dakinsa yau.

*****
Kwance take a kan gado amma sam bacci yaki zuwa. Tunanin Ya Hamza take yi, yana can yau tare da Izzatu. Hawaye taji ya cika mata ido zuciyarta na zafi. Yanzu duk irin yadda yake bata kulawa haka zaiyiwa Izzatu? Gaskiya taga kokarin Izzatu sosai da ta bari Hamza ya aurota. Bata fatan ranar da Hamza zai nemi karin aure, gani take ciwon zuciya ne kawai zai kamata. Da wannan tunanin Zuhra ta rinka kuka wanda ta kasa gane dalilin yinsa.

A hankali Hamza ya bude kofar dakin ya shigo. Fitilar a kashe take amma yana iya jin sautin kukanta a hankali. Cikin sauri ya kunna fitilar ya karasa gefen gadon ya zauna. Zuhra na jinsa taki kulawa sai wani hawayen da yafi na da. Muryarsa a sanyaye yace to bari na tafi tunda baki so zuwan nawa ba.

Yana rufe baki ta tashi zumbur ta rungume kam tana kuka mai sauti. Shima rungumetan yayi tare da sauke ajiyar zuciya. Ashe dai ba shi kadai yake sonta sosai ba. Sun jima yana rarrashinta har ya samu tayi shiru tana mayar da numfashi. Dago kanta tayi ya shafa fuskar yana goge mata hawaye...Cutie haka kike da kishi? Ina da aiki a gabana kenan. Ni da nake so idan an tashi rabon kwana ya zama sati bibbiyu. Kyakkyawan mintsini yaji a hannunsa sakamakon maganar da yayi ya daga hannun yana yarfewa....banda kishi harda mugunta a lamarinki.

Zuhra ta harare shi...ni ka tashi ka tafi tunda abinda kazo fada min kenan. Dan bakin da take turowa ya kama

Please Login or Register in order to submit comment