Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi sai kaji kamar shirme. Ita kuwa sai ta dake, sai an bata amsa tace nasan ku ma kun karu. Malama Rabia tace ina jinki Fatima. Zuhra tace menene hukuncin macen da ke karin gashi ko bleaching a musulunci. Malama tayi dan murmushi ai hukuncinsu a bayyane yake, babu kyau. Zuhra tace ai nima nasan babu kyau ina nufin akwai wata aya ko hadisi da yayi nuni an hana ko kuwa fatawar malamai ce kawai. Malama Rabia tace to bari mu fara da maganar karin gashi tunda shi tabbas akwai ingantattun hadisai a Sahihul Bukhari da Sahihul Muslim da suka nuna anyi hani da yinsa.

Manzon Allah SAW yana cewa Allah SWT Ya tsinewa mai karawa wata gashi da wadda tace a kara mata. Ki duba hadisi na 5934 a Bukhari da 2122 a Muslim.

A wani hadisin kuwa, Asma'u bint Abubakar(RA) tace wata mata tazo wurin Annabi SAW tace masa ta aurar da yarta amma lalura tasa gashin kan yar ya zube. Shin zata iya saka mata gashi? Sai Annabi SAW yayi kashedi ga mai karin gashi da wadda aka karawa. Bukhari 5479, Muslim 3962.

Malamai sun dauki karin gashi a matsayin yaudara sannan suka yi hani dashi. Akwai hadisin Mu'awiyya RA wanda yace Annabi SAW yace karin gashi yaudara ce. Sahihul Bukhari 3229.

Ta koma ga sauran daliban gaba daya. Ku kanku a ma'aunin hankali kunsan cewa akwai ha'inci a karin gashi. Banda asarar kudi da kuma warin da yake yi a kan mai sawa. Sannan duk mai karin gashi bata taba rufe kanta gaba daya domin tayi ne don a gani. Asali ma a shekarun baya muna ganin mace da karin gashi mun san ba musulma bace. Sai gashi a hankali mun dauki al'adu da dabiun wasu muna yi. Allah Ya shirye mu baki daya.

Sai tambayarki ta biyu akan masu shafa mai su canja kalar fatarsu daga baka ta koma fara. Wasu masu zalamar ma fararen ne suke kara kode fatarsu. To duk wannan yana cikin nau'in canja halitta wanda Allah Ya hana. Shaykh Ibn Uthaymeen yayi bayanin canja kalar fata na dindindin kamar bleaching a matsayin laifi kamar masu yin tatoo(zane da wuta ko abu mai kaifi a jiki) da kankare hakori ayi wushirya. Irin wadannan laifukan Annabi SAW ya sanar damu tsinuwar Allah ta tabbata ga masu yinsu. A bangaren lafiya kuwa munsan cewa babu wani nauin bleaching wanda bashi da illa ta kusa ko ta nesa. Wanda munsan Allah Ya hana mu cutar da kawunanmu. Ga zubar da mutumci da kimar mai yi a idon wadanda suke da hankali suke amfani dashi. Ga asarar kudi da sauran abubuwa marasa kyau. Allah Shine mafi sani daga kurakuran da muke aikatawa. Allah Yasa duk abinda zamuyi mu tsaya a iyakar da Yayi mana. Laifukanmu kuma Ya Yafe mana.

Gabadaya ajin suka ce Amin. Jikin yan matan duk yayi sanyi saboda ba'a rasa masu dan shafe shafe da masu dora gashi ko da a jikin acuci ne irin na Hajara. Zuhra tayi godiya ga Malama Rabia sosai. Duk bayanan da tayi kuwa ta rubuce su a yar takarda wanda zata nunawa Hajara shaida. Ta so ace Hajarar na nan tayi tambayar.

Daga kofar daki 'yan matan biyu suka ce Mama mun tafi. Ba tare da ta dago kanta daga laptop din gabanta ba tace Allah Ya kiyaye hanya ku gaishe su. Shiru taji ba amsa...tana dagowa taga sun tafi. A ranta tace na rasa saurin me yaran nan suke yi haka.

Hajiya ta fito daga dakin Alhaji taji karar mota. Sauri tayi kada su tafi ta basu sako su siyo mata a hanya idan suna dawowa. Kayan da ta gani a jikin Adabiyya ne yasa ta kara sauri tana kwala musu kira. A tsorace Adabiyya mai shirin shiga mota ta juyo. Hamida tace shikenan mun gama yawo. Ko kadan ba haka suka so ba. Hajiya na dakin Alhaji suka ki zuwa yi mata sallama. Ita kuma Mama daga bakin kofa suka yi mata basu bari iyayen nasu sunga kayan jikinsu ba. Hajiya ta fito har wajen rai a bace tace duk su shigo ciki.

Mama ta fito daga daki tace Hajiya lafiya? Kafin ta bata amsa yaran suka shigo. Ya Salam...Hamida? Adabiyya? Meye hakan kuma? Hajiya tace kema basu ce miki zasu tafi ba ko. Nima karar mota naji na fito da sauri ashe rabon idona ya gane min ne.

Hamida yar shekara ashirin da biyu jeans ne a jikinta da top wadda ko rabin cinya bata rufe mata ba. Duk ta dameta sai tayi rolling da karamin mayafi. Adabiyya mai shekaru shatara kuwa skirt ne a jikinta amma itama ya matse har shatin pant dinta ake gani. Shima don tafi yayarta jiki ne ta saka. Sai riga matsatstsiya karama har da wata belt a samanta an kara tamketa. Da dan karamin mayafinta. Hajiya ta kalli yayansu Nura. Kai mahaukacin ina ne da kana ganin sun fito a haka kake shirin jan mota. Ku fada min gaskiya ina kuke shirin zuwa. A tare suka ce gidan Yaya.
[9/25, 2:39 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU🗿6


Batul Mamman (Mrs)💖



Mama tace ni na rasa gane me ake yi a gidan Yayan naku ne? Jiya kunje kun ce aiki zaku taya Izzatu yau ma kun ce aikin zaku kara yi. Ko packing suke yi ne zasu tashi bamu sani ba, ta zauna akan kujera kusa da Hajiya tace ni a iya lissafi na ma ai sai karshen August za'ayi birthday din Nana. Kuma ita ce ta rage anyi na yayyenta. Hajiya ta tabe baki kina ma kokarin rikewa. Sun mayar da birthday tamkar wata ibada. Duk shekara sai anyi sau uku a gidan. Allah Ya kyauta.

Mama ta ce Nura fada min gaskiya me ake yi. Indai birthday ne an saba yi mun kuma hakura mun zuba ido. Tunda shima Hamzan bai ji maganar mu su dena ba ai matarsa bazata ji ba. Shiru yayi har sai da Hajiya ta daka masa tsawa...baka ji ana tambayarka ne? Adabiyya ta soma kuka dama ita akwai tsoro tace Hajiya party din wedding anniversary zasu yi na shekara goma da aure. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun shine abinda su Mama ke fada. Hajiya ta mike tsaya tana magana a hankali...lalacewar Yayanku har ta kai nan? Allah Ya shirya. Daga nan dakin Alhaji ta koma ta cigaba da gyarawa.

Mama ta dubi yaran. Yanzu don Allah waye ya ce ku saka irin kayan nan? Yaushe ma kuka siya? Adabiyya tace jiya da muka je ne Anti Izzatu tace kananan kaya zamu saka yau. Shine muka ce bamu da masu kyau. Sai ta kaimu wani kanti ta siya mana. Mama tace eh lallai yarinyar nan bata nemawa kanta zaman lafiya a gidan miji. Shirun da taga munayi don bama son zama iyaye masu sa ido a lamarin gidan 'ya'yansu ne. Amma wallahi idan na bullo mata ta bayan gida sai ta gane karyar rayuwar turai take yi. An gayyaci su Mariya? Hamida tace eh duk su biyun. Har Yaya Ibrahim ma an gayyace shi da Anti Umma. Mama tace suma duk kananan kayan aka ce su saka? Hamida tace bamu sani ba. Mu da kannenta tace mu saka dai jiya.

Mama tace duk su je su canja kaya tana zuwa. Nura yace harda ni Mama? Ta harare shi ban sani ba. Dakin Alhaji ta shiga ta tarar da Hajiya a zaune a kan gado tana kuka. Mama tace haba Hajiya kukan iyaye ga 'ya'yansu bai taba zama alkhairi ba. Hajiya ta share hawaye da gefen dankwali. To ya zanyi Kaltume? Yaron nan ko kadan ban goyi bayan zuwansa Canada karatu ba amma Alhaji ya dage. Karshe yaje ya hadu da mata itama tashin can. Mama tace shekara hudu fa kawai suka yi da babanta yaje aiki. Hajiya tace to ai dai ta zauna ko. Gabadaya sun dauko wasu al'adu daban da namu. Wadanda basu dace da addinmu ba. Kina kallo duk shekara sai sunyi party nasu da na yaransu. Sati kusan uku da suka wuce ba ya kawo mana laces ba wai na Mother's day. Na Alhaji kuwa na Father's day ai kinga bamu taba gaya masa dalilin bayarwa ba kila da zaginsa zaiyi ma. Duk wata rana da turawa suke bawa mahimmanci Yaya da matarsa suna yi. Ko da ba kowanne muke gani ba amma munsan anayi. Su a dole rayuwar turawa sukeyi. Mama tace kiyi hakuri yanzu zan kira shi a waya yazo. Dole mu sake masa magana ko mu hadashi da Alhaji. Wannan karon sun wuce gona da iri tunda suna son batawa yaranmu tarbiya. Hajiya tace Allah Ya shirya mana. Amma don baki ji yadda raina ke baci ba idan su Khalifa na kirana Granny dinnan. Mama ta kwashe da dariya. Ai gara naki ma. Nida ake kira Grams fa. Yau da bamuyi boko ba ai da mun sha kunya tunda sai kiyi musu magana ma amma su amsa da turanci. A dole sai an bambanta su da 'ya'yan yan uwansu.

Sani masinja ya dauki wayar landline din office dinsu da aka kira. Muryar mace yaji tace matar Hamza ce. Ji yayi tana kuka tace ya fada masa Junior ya fado daga kan kujera ya karye a hannu. Sani ya tashi da sauri sai ya tuna meeting din da suke yi mai mahimmanci ne. Har ya koma ya zauna ta sake kira a fada masa yanzu ya taho gida. Ta kira wayarsa a kashe. Dole Sani masinja ya shiga hall din da ake meeting din.

Architect Hamza Nasir Hamza ya juyo a fusace yace meye haka Sani? Manyan baki gareshi turawa masu son hadin gwiwa da kamfaninsa na zane da ginin gidaje da hotels da sauran manyan gine gine. Sani masinja yace ranka ya dade uwargida ce ta bugo tace Jiniya ya fado daga kan kujera ya karye a hannu. Hamza ya tashi da sauri....what? Ya dubi bakinsa yace da turanci kuyi hakuri dana ne ya karye a hannu. Sun tausaya masa suka ce zasu dawo a karasa meeting din. Amma ya daure yasa hannu a takardar shaidar amincewarsa da sharudansu. A gaggauce ya karanta ba tare da ya fahimci kalma ko daya ba yasa hannu a duka biyun. Daya tasu dayar ta kamfaninsa. Sunji dadin amincewarsa sosai suka tashi. Yana ta sauri a hanya wayar Mama ta shigo. Ya dauka a gigice a zatonsa Izzatu ce. tace Yaya kana ina ne? Mama ke ce? ina hanyar zuwa gida. Tace to maza kazo ina son ganinka. Yace Mama Izzatu bata kiraku bane? Junior ne ya karye a hannu. Yana hango wani dan sanda ya nufo motarsa saboda yana amsa waya yana tuki da gudu yaja motar kafin a bada hannu har ya kusa karawa wani. Mutane suka bishi da zagi da bakaken maganganu.

Mama ta dubi Hajiya tace bamu ga ta zama ba wai Junior ya karye a hannu. A tare suka fito daga dakin suka kiran Nura yazo ya kaisu gidan Yaya. Hamida tace Mama me ya faru? Junior ne ya karye a hannu. Yanzu yayanku yake fada min. Adabiyya tace ba gaske bane. Jiya ne Anti Izzatu tace bata san da yadda zata sa Yaya ya baro office da wuri ba. Partyn surprise take son yi masa. Bai san komai game dashi ba. Ana haka wata makociyarsu da aka bawa aikin meatpie ta shigo take cewa danta ne ya karye kuma ya kwana da zazzabi shiyasa bata aiko ta karbi kayan yin meatpie din ba. tana fita ne shine Anti tace ta sami idea din abinda zata fada masa. Hajiya ranta ya kara baci. Mama kuwa ashar ta dannawa Izzatu saboda yadda zuciyarta ke mata zafi. Ta kalli su Hamida duk sun saka material ne da mayafansu manya tace Nura ya kaisu amma ya fadawa Yaya tana son ganinsa komai dare.

Sai bayan fitar bakin sakataran Hamza yana hada takardu ya duba wadda ya saka hannu a kai. Jikinsa ne ya fara rawa ya soma salati. Wani cikin yan office din yace menene. Inuwa Sakatare yace ai bana jin oga ya karanta takardar nan da kyau. Ta nuna ya amince ya karbi kudin da suka bashi saboda haka nan da wata shida duk ribar da aka samu tasu ce. Daga wani wata shidan kuma sai su rinka raba ribar gida uku. Su kaso biyu shi kuma daya.
[9/25, 2:41 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿7


Batul Mamman(Mrs)💖




Alhaji Nasiru Hamza dan kasuwa ne mazaunin Kano amma asalin iyayensa mutanen Kumo ne na garin Gombe. Sana'ar siyar da shanu da tumaki ya fara wadda a hankali har ya fara fitar da fatar dabbobin kasashen waje yana sayarwa. Shiyasa ma aka fi saninsa da Nasiru maifata. Halima wadda suke kira Hajiya ya fara aure yar kanwar babansa. Sun fara zama a Kumo kafin kasuwancinsa ya bunkasa ya dawo Kano. Lokacin ta haifi danta na fari Hamza suke kiransa da Yaya. Suna zamansu lafiya da mijinta. Kuma suna yawan zuwa gida ganin iyayensu. Hamza na da shekara biyu ta haifi Ibrahim sai Mariya. Alh Nasiru ba karamin soyayya yake nunawa yaransa ba. Yana da amini kuma abokin kasuwanci Alh Sabiu. Kowa ya sansu tare hatta iyalinsu suna mutunta juna. Matan Alh Sabiu biyu. Kaltume ce uwargida sai Sahura. Kaltume bata taba haihuwa ba a shekarun da sukayi da mijinta. Tana dai karatu a lokacin. Ita kuwa Sahura 'ya'yanta shida. Da kamar gaske suke zaman lafiya. Sai daga baya Sahura ta rinka daukar zigar yan uwa da kawaye ta fara yiwa Kaltume habaici da gorin haihuwa. Tun bata kulawa har dai ta fadawa mijinsu akan ya yiwa Sahura magana sai cewa yayi ai ba matsayinsu daya ba. Idan taji haushi ta haihu mana. Da kadan kadan suka juya mata baya. A lokacin tayi shawara ta sanar da Halima halin da take ciki lokacin tana da ciki na hudu. Ita kuma sai ta fadawa mijinta. Ko kadan Alh Nasiru baiji dadin faruwar hakan ba. Ya zaunar da abokinsa yayi masa nasiha. Sai dai duk a banza. Wata rana Kaltume zata tafi makaranta ta shirya ta rufe dakinta sannan ta leka dakin Sahura tace ta fita. Tana dawowa da yamma ta tarar da Alh Sabiu da Sahura har da wasu makota a kofar dakinta. wasu samari ne suke kokarin balle kofar. Kaltume duk ta rude ta tambayi abinda ke faruwa. A madadin amsa sai mari da duka da Alh Sabiu ya rinka kai mata. Sahura na kuka tace muguwa saboda baki haihu ba shine zaka kashe min nawa 'ya'yan. Tunda kika fita nake neman Ihsan banganta ba. Sai dazu kawai naji kukanta a dakinki. Ba yadda banyi ba na kasa budewa, tun tana kuka har muka ji shiru. Ta cigaba da kuka ina jin ma ta mutu Alhaji. Shi kuwa sai dukan Kaltume yake har sai da aka bude dakin. A kwance suka tarar da Ihsan yar wata takwas. Sahura tace ai kawai ta mutu ko ta suma. Alhaji Sabiu ya cire babbar rigarsa yana ta dukan Kaltume. Babu mai hanashi har Allah Ya kawo Alh Nasiru. Yayi ta rokon abokinsa amma sam yaki dena dukanta. Alh Nasiru ganin babu yadda zaiyi ya ja hannunta. Sahura tace shikenan Alhaji dama tunda yake kare mata kwartonta ne. Ji yadda yake rike mata hannu a gabanka. Alh Sabiu yace ko Sahura, to ke Kaltume na sakeki saki uku in kin gama idda ki auri kwarton naki. Kai kuma Nasiru bani ba kai. Da haka abokan suka rabo. Ashe mukulli Sahura ta sata na Kaltume ta durawa yarta maganin bacci ta kaita dakin.

Halima taji tausayin Kaltume sosai barin ma da aka rinka yadawa a gari abokin mijinta ne kwartonta. Gashi ya gujeta bayan aurenta ya mutu. shi kanshi sai da abin ya shafi kasuwancinsa. Sai da ta kai ko makaranta ta dena zuwa. Har yan uwanta wasu suna kyamarta. A wannan halin ne Halima ta bawa mijinta shawarar ya auri Kaltume domin ta tsira da mutumcinta. Da kyar Kaltume da Alh Nasiru suka yarda. Bayan anyi auren saboda Halima ta lura Kaltume na son 'ya'ya ta dauki Hamza da Mariya ta kayansu ta mayar dakin Kaltume. Wannan abu ya kara musu zaman lafiya sosai. Kaltume har kullum bata yiwa Halima kallon kishiya sai yar uwa. Haka suka zauna lafiya Halima ta haifi Jidda. Daga nan Kaltume ita ta sami ciki ta haifi Nura da Adabiyya. Sannan Halima ta haifi auta Hamida. Gidansu abin sha'awa saboda kan 'ya'yan a hade yake. Daga baya asirin Sahura ya tuno Alh Sabiu yaji tana bawa yarta labari. Har gida yazo bawa Kaltume hakuri domin ya gane bai kyauta ba. A yanzu ma dai komai ya sukurkuce musu shi da Sahura don yaran babu wani mai abin kirki gasu har su shadaya.

Tun daga farkon layin gidansa yake hango motoci. Hankalin Hamza ya sake tashi sosai. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun kawai yake fada. Shikenan Junior ya rasu.........jikinsa duk a mace yayi parking din motarsa daga can baya ya fito. Sai kawai ya kasa karasawa gidan. Kifa kansa yayi a saman motar. A wannan yanayin Ibrahim ya iso. Yana neman gurin parking don layin ya cika ya hango yayansa a tsaye ya kifa kai. Ibrahim ya fito da sauri da matarsa Ummahani da yaransu uku.

Hannu yasa ya taba Hamza a kafada. Hakan yasa ya juyo da sauri. Muryarsa a raunane yace ashe kuma kunji. Ummahani tana gaishe shi yace mata shiga ciki Umma ai dukkanmu mukayi rashin. Ibrahim yace rashi kuma Yaya? Nifa tun jiya Izzatu tace muzo da yara yau. Nayi tunanin irin partyn da kuka saba ne na kawo su don kada ace ina raba zumunci. Amma wallahi barnar kudin naka tayi yawa. Hamza yace ina maganar party Ibrahim. Junior ne ya rasu. Baka ga mutane da yawa ba. Ummahani na kokarin bude gate Junior ya bude tare da wasu yaran. Sun sha sababbin kaya. Hamza ya kura masa ido sannan ya dubi Ibrahim. Ibrahim yace kai wa ya fada maka ya rasu? Hamza a rikice yace Izzatu tayi waya Office tace a fada min ya karye a hannu. To ina zuwa naga motoci nayi tunanin ya rasu ne. Ibrahim yayi tsaki cike da bacin rai yace Allah Ya kyauta ni na tafi. Zuciyarsa na kuna yaja motarsa yayi gaba. Ace babban mutum kamar Yaya dan shekara talatin da bakwai ya bari mace na karanta masa yadda zasuyi rayuwa. Kodayake ba laifinta bane. Tare suke yin komai. Daga nan Ibrahim gidansu ya tafi.

A hankali Hamza ya tura karamar kofar gate din ya shiga. Kawai sai ji yayi mutanen wurin sun ce SURPRISE!!! farfajiyar gidan ya gani ya sha kwalliya an jera kujeru da tebura. Ga fitilu suna ta haskawa an kunna inji. Kida aka kunna yana tashi a hankali. Bai gama tantance abinda ke faruwa ba Izzatu taja hannunsa suka shige cikin gida. Muje ciki ka canja kaya. Suna shiga daki ta rungume shi. ....HAPPY ANNIVERSARY MY BABY.
[9/25, 2:51 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿8


Batul Mamman(Mrs)💖




Hamza ya yiwa Izzatu kallon rashin fahimta. Izzy me yake faruwa ne? Kince Junior ya karye but it seems lafiyarsa kalau. Fari tayi masa da ido irin yadda tasan yana kara dauke masa hankali, sai a lokacin ya kula da kayan jikinta. Wani irin yadi ne mai matukar santsi aka yi mata doguwar riga wadda ta dameta daga sama har gwiwa sannan ta bude sosai. Ga wani abu kalar takalminta da sarka anyi mata dauri. Tamkar wata amarya ta fito. Jikinta mai kyau ne ba kace ta haifi 'ya'ya uku ba. Tana lura da yadda yake binta da kallo tayi murmushi. Dama nayi ne kawai don ka dawo gida akan lokaci. Na gama komai na shirya mana anniversary dinmu na shekara goma. Ya shafi gefen fuskarta amma Izzy ba kya ganin abin ya danyi yawa. Ki ce dana ya karye kinsan zan tsorata. Kiss tayi masa a kumatu to yi hakuri daddyn Junior. Kaga ana jiranmu a waje.

Tare suka fito rike da hannun juna. Sunyi matukar kyau sosai ga yaransu suma sun sha ado. Babban shekararsa biyar suna kiransa Khalifa mai sunan Alhaji Nasiru. Sai Junior mai shekara uku sunan baban Izzatu gareshi Sunusi sai kuma Nana(Halima) mai neman shekara ta biyu. Sunan Mama yaso saka mata sai dai Maman taki saboda Ibrahim da Mariya duk sunyi mata takwarori.

Hajara tana ta binsu da ido duk inda suka yi ana ta gaisawa da daukar hotuna. Ga masu rabon abinci suna ta yi su ma. Tace kai Anti Faiza ina ma Zuhra tazo muci son ran mu. Ji kaji kamar su suke kiwonsu. muma dai Allah Ya bamu kudin nan muji dadin rayuwa mu rinka party duk shekara. Mariya tace ba amin ba kanwata. Anti Faiza da Hajara suka juya suna kallonta. Hajara tace kinji min mata da bakinciki. Faiza ta kai mata duka to shashasha baki san mutum ba zakiyi rashin kunya, yi hakuri baiwar Allah. Ko ba'a fada ba daga shigar Mariya an san tana da kudi. Murmushi Mariya tayi ba komai ke dai kiyi adduar arziki mai albarka ba na party ba. Daga nan ta tashi ta hada kan 'ya'yanta sukayi waje.

Haka aka cigaba da taro har wurin karfe takwas na dare. Nura ne suna shirin tafiya dasu Adabiyya yazo ya fadawa Hamza sakon Mama kan cewa tana son ganinsa a yau. Sai bayan fitarsu ya duba agogonsa. Subhanallah ya fada da karfi tare da mikewa. Izzatu tace yaya akayi? Ya nuna mata lokaci. Kinga har lokacin isha yayi bamuyi magriba ba. Ta dan tura baki idan an watse ba sai muyi ba. Bana son a fara shiga ciki ne azo a bata min toilets. Hamza yace ni dai bani key please. Ta dan daure fuska Allah bazan bayar ba. Kana shiga mutane zasu fara bin bayanka. Ya girgiza kai yana murmushi Izzy baki da dama. Wani famfo ya zagaya a bayan gidan yayi alwala sannan ya fita masallaci. Duk lalacewar lamarinsa bai tashi da tarbiyar sakaci da sallah da gangan ba.

Ana gyaran wurin jamaa sun watse sauran kadan Hamza ya fito zuwa gidansu. Izzatu ta bashi manyan kuloli cike da abinci, nama da snacks. Ga katon din juice da na ruwa ya kaiwa su Hajiya.

Kula daya ya dauko maigadi ya biyoshi da sauran. Da sallama ya shiga babban falon. Mama da Hajiya ne a wurin sai Jidda da ta biyo su Nura tana jiran mijinta. Duk suka amsa sallamarsa sannan Mama tace maraba da Mungo Park. Turus Hamza yayi ya kasa furta gaisuwar da yake shirin yi musu. Hajiya tace Jidda tashi mu shiga ciki uwa da danta zasu gana. Dama zamanta a wurin ta kara tunzura mama da bayanin abinda ya faru a wurin partyn. Hamza yayi murmshi da wuya kaga fuskarsa a hade sai dai idan yana cikin tashin hankali. Mama nasan nayi laifi ko baki fada ba. Amma wallahi nima bani da masaniyar wannan party din. Surprising dina tayi nima. Mama tace ai naga alama. Zaka ce iyayenta basu da labari ne? Ka hado kuloli ka kawo wa mayunwatan iyayenka abinci ko. To duk ka kwashe abinka bama so. Yace Mama ita da kanta ta bani na taho dashi. Tace kaga ni ba wannan ke gabana ba kaji ko. Yanzu don Allah Yaya yaushe zaka san ka girma? Wace irin rayuwa ce kuka daukarwa kanku kai da iyalinka. Kanka aka fara zuwa kasar waje karatu ne da zaka dauko al'adun da ba naka ba kayi ado da su. Sau nawa muna yi maka fada ni da Hajiya akan birthday partyn da kuke wa yaranku duk shekara amma ka share. Irinsu valentine dinnan ma duk kuna yi ko? Shiru Hamza yayi don yau kam ya san ya batawa Mama rai. Tace ba tambayarka nake ba. Yace munayi. Ta cigaba da fada....duk wani dan iskan day da yahudu da nasara ke girmamawa kaima ka girmama. Ka iya kashe kudi mai tsoka ka shiryawa yara party kawai don suji dadi. Irin sadakar nan ta abinci ko kudi kuwa sai karshen ramadan. Baka tunanin halin kuncin rayuwa da mutane ke ciki yanzu.
Alhamdulillah muna da rufin asiri ci, da sha da sutura babu wanda Alhaji baya saukewa amma ai ihsani yana da dadi ko. Ko kasan duk wata sai Ibrahim ya kawo buhun shinkafa gidannan sannan ya bamu dubu biyar biyar

Please Login or Register in order to submit comment