Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taba mantawa da wannar ranar ba. You hold a special place in my heart. Hamza yana godiya da dukkan abinda kike masa na kyautatawa. Ita dai bata iya magana ba ta dauki jug din ruwa ta haye sama ta barshi yana murmushi.

**********

Kwayoyin guda hudu ne a hannunta da kofin ruwa. Zuciyarta tana dan yi mata wasiwasi sai dai gaskiya bazata iya yarda ta kara haihuwa ba. Wadannan ukun sun ishesu. Tun kafin ta hadu da Hamza take da ra'ayin 'ya'ya biyu kawai. Rufe ido tayi ta watsasu gabadaya daya. Idan cikin ya zube sai ta fadawa Hamza da iyayenta bata ma san dashi ba. Tana sha ta dauki waya ta kira shi. Lokacin Zuhra bata dade da barin falon ba. Hira sosai suka yi yana fada mata yadda yayi missing dinta. Har zuciyarta Izzatu tasan bata kyauta masa ba amma tasan idan ya gane da cikin nan tilasta mata zaiyi sai ta haifa. Sai da suka gama hirarsu ta masoya ta gyara kwanciya tayi bacci. Karfe biyar da rabi wani matsanancin ciwon ciki ya tasheta. Tana kunna fitila taji danshi a inda take kwance. Hannu na rawa ta bude bargon taga jini ne sosai a wurin. A razane ta kwalla ihu MUMMMMM.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 61

Batul Mamman(Mrs)





Kamar daga sama Raliya da Dad dinsu Izzatu suka ji ihunta. Kafin su karasa dakin kaninta Walid ya rigasu. Kokarin dagata suka tarar yana yi ga jini ya jika zanin gadon. Kuka Raliya ta saka ta soma jijjiga Izzatu sai dai ta suma bata san waye a kanta ba. Dad dinsu yayi saurin dauko makullin mota shi kuma Walid ya ciccibota ya sakata a ciki. Hankalinsu a tashe suka tafi asibiti mafi kusa dasu. Raliya sai kuka takeyi tana kiran sunan Izzatu.

A yanayin da likitoci suka ganta theatre akayi gaggawar kaita ana kokarin ceto ranta. Sai kai kawo suke yi a kofar theatre din har gari ya karasa wayewa. Suna kallo nurse zata fito da gudu wata ta shiga. Tsahon lokacin nan babu irin tunanin da iyayenta basuyi ba. Suna nan tsaye jugum jugum Raliya tace idan ka taho da waya ya kamata a sanar da Hamza. Alh Sunusi yace haba Raliya, ya za'ayi mu kirashi a wannan lokacin bayan muma bamu san aininhin abinda ke damunta ba. Ko kin sani? Cike da damuwa Raliya tace ni bansani ba kuma banga wata alama ta rashin lafiya a tare da ita ba. Likitoci biyun dake kan Izzatu ne suka fito a tare bayan fiye da awa daya da sukayi a ciki. Daya daga cikinsu ya dubi Alh Sunusi yace ku biyo ni office. Raliya tace Doctor kawai ka fada mana a nan idan ta cika. Yayi murmushi noooo Madam, ki kwantar da hankalinki. She is stable now.

Duk su biyun sun tsirawa liktan ido suna jiran bayaninsa. Glass din idonsa ya cire ya goge fuskarsa da hankice....duk motsinsa Raliya kamar ana tsikarinta take ji. So take kawai tasan abinda ya sami Izzatu. Likita yace "yallabai menene matsayin patient dinnan a wurin ka?"

" 'Yata ce" Alh Sunusi ya amsa masa.

"Tana da aure ko budurwa ce?"

Raliya ta kagu ya fadi abinda ke faruwa tace "matar aure ce harda 'ya'ya uku. Mijinta yana Kano".

Sai da yayi 'yan rubuce rubuce sannan yace "patient dinnan tasha maganin zubar da ciki overdose. A ka'idar wanda tasha ma guda daya ake sha amma da kyar ta iya fada mana hudu tasha a lokaci daya".

Cikin rashin fahimta Alh Sunusi yake tambayar Raliya dama Izzatu nada ciki tace itama bata da labari.

Likita yace to a gaskiya ba karamin ganganci tayi da rayuwarta ba domin da kyar muka iya ceto rayuwarta da ta abinda ke cikinta. Tunda yana da lafiya bamu ga dalilin zubar dashi ba. Sai dai ya zama dole a kula da ita sosai har ta haihu domin mahaifar a yanzu bata da kwari. A takaice ma dai sai dai ayi mata aiki a cire baby din idan ya cika watannin haihuwa sannan ita kanta mahaifar dole a cireta. Dalilin haka yasa muka tabbatar munyi kokari wurin ceto abinda ke cikin."

Raliya ta dora hannu a ka tana kuka tunda taji yace za'a cire mahaifa. Alh Sunusi rai duk babu dadi yace muna iya ganinta? Doctor yace su bari ta huta domin ta wahala.

Bayan awa uku Alh Sunusi da Raliya ke zaune a dakin da Izzatu take. Farkawarta kenan tace Mum me nake yi a nan? A fusace Raliya tace ubanki kike yi Izzatu. Nace ubanki kike yi. Shashashar banza mara hankali, iliminki da shekarunki basu kara miki komai ba sai hauka. Alh Sunusi yace haba Raliya ya zakiyi mata magana irin haka bayan kinsan halin da take ciki. Tun dazu kike kuka kina addu'ar ta farfado. Ta tashi kuma kin bita da zagi.
Raliya tace to ya zanyi da yarinyar nan? Ta hade rai ta kalli Izzatu...har kin iya zubar da ciki ko? To Allah bai nufa ba wannan dai sai kin haife shi. Izzatu ta zaro ido...Mum kina nufin bai zube ba? Meyasa basu yi min wankin ciki ba? Ni wallahi bana son sake haihuwa. Su Khalifa sun isheni.

Maganarta sam bata yiwa iyayenta dadi ba. Raliya tace kaji da kunnenka ko? Ni kam nayi nadamar kyaleku da mukayi kuka zama turawan karfi da yaji. Zeenatu ta auri mijin da dabi'unsa tamkar wani bayahude har yau ban taba sonsa ba. Amma saboda mun baku damar yin yadda kuke so a dole muka barta da zabinta. Ke da Allah Ya rufawa asiri kuma kina neman tonawa kanki. Idan Hamza yaji abinda kika yi ya sakeki zaki yi bayani.
Izzatu ta daure fuska Mum bana son irin haka. Hamza bazai taba iya rayuwa batare dani ba. Muna son juna kuma ai nayi kokari da na haifa masa har 'ya'ya uku.

Alh Sunusi ya daka mata tsawa. Ashe abinda Mamanki take fada gaskiya ne baki da hankali. Duk laifinmu ne da muka baku irin wannan tarbiyar amma wallahi idan kika kuskura kika kara yunkurin zubar da cikin nan sai ranki ya baci. Kuma ni dai bazan kira Hamza na sanar dashi abinda kika yi ba, ai da kunya. Raliya tace nima ai ba fada zanyi ba. Dama karya tayi masa ta taho shine muma zaki ha'incemu ki zubar da ciki bamu sani ba.

Izzatu ta soma kuka ni duk kun tsaneni. Kawai don nayi aure shikenan kuma bani da 'yanci na zabarwa kaina abinda ya dace? Tana magana iyayenta suka fice ta cije lebe. Ita bata ga aibun abinda tayi ba. Haihuwa ce ta isheta haka. Tunanin abinda Hamza zaiyi idan yaji zancen nan tayi gara tayi shiru tunda idan ya sani fada zaiyi mata shima. Za dai ta kirashi ya aiko mata da kudi na hannunta sun kusa karewa.

*********
Kwanaki biyu da maganar Hamza da Zuhra ya dukufa nema mata makaranta saboda yadda ta dame shi. Da samples biyu data bashi yake yawo. Cikin ikon Allah a rana da uku wadda ta kama Juma'a ya sami wasu makarantu har biyu. Ba karamin farinciki yayi ba da hakan. Har mamaki yake yi yadda yake kwantar da kai a gaban Principal ko Headmaster yana neman alfarmar a bashi wannan kwangilar. Da gaske ba karamin matsi zasu shiga ba shi kuma baya son taba kudin kamfani ayyukansu su durkushe.

Tun a hanya ya kira Zuhra ya sanar da ita. Makaranta daya bangaren nursery za'ayiwa dayar kuma secondary ce ma. Har wani tsalle take yi ta tambayeshi kalolin da aka zaba ya fada mata. Kafin ya iso gida a cikin kudinta ta aiki Tala kasuwa ta siyo mata kulu da maballai. Bai dawo gida ba ranar sai tara saura. Bayan yaci abinci yace gobe zan duba sai a siyo kayan da zaki bukata. Inda zai samo kudin yake tunani. Zuhra tayi 'yar dariya tace ai har Tala ta siyo min tun dazu. Wani daki kusa da na Tala a kasan ta nuna masa kayan. Yace wa ya baki kudin? Ya Hamza akwai 'yan kudi a hannuna. Yanzu dai ka huta sai ka nuna min irin yadda kayan nasu suke na fara aiki. Sai wani farinciki take yi zata sami damar taimakonsa. Murmushi yayi yace nagode Cutie Allah Ya baki lada, tace amin.

Jikinsa a sanyaye ya tafi daki. Bayan dan lokaci Zuhra ta bi bayansa saboda ta kula da yanayinsa. Rashin kudi a wurin wanda ya saba rike su da tausayi. A bude ta tarar da kofar falon amma baya ciki. Tana kokarin shiga dakin taji muryarsa yana waya muryarsa a raunane. Maganar karshe kafin ya ajiye wayar taji yace " Inuwa kafi kowa sanin halin da nake ciki, idan baku maida hankali sosai akan aikin nan ba karshenta yarana idan anyi hutu bazasu koma school ba.".

Izzatu ta kirashi tayi masa karya tace tana bukatar kudi zata asibiti tana zazzabi tun kwanaki biyu da suka wuce ya fada mata bashi dasu ta ranta a nata zai biyata . Tun daga ranar tayi fushi ta kashe waya baya samunta. Ita a tunaninta kuntata mata kawai ya koyi yi saboda iyayensa. Gashi tana son biyan kudin asibiti bata son tambayar iyayenta tunda fushi suke da ita. Banda ita yana tunanin yadda zai biya kudin makarantar yara boko da islamiyya duka masu tsada suke zuwa.

Komawa da baya Zuhra tayi tana kuka cike da tausayin Hamza. Inda ta ajiye kudin da Baba ya bata da sauran na hannunta ta duba. Abinda yayi mata saura dubu saba'in da uku har dan kudin sakar da ta taho dashi. Dubu hamsin ta dauko har ta kai bakin kofar dakinta sai ta dawo tana tunani. Idan ta kaiwa Hamza kudin nan bazai taba yarda ya karba ba. A take tayi murmushi da dabara tazo mata. A cikin rigarta ta boye kudin ta koma dakinsa.

Kwance ta same shi akan gafo ko kaya bai cire ba bare yayi wanka. Ta karasa kusa da gadon, Ya Hamza ba lafiya ne? Murmushin dole ya kirkiro ya tashi gajiya ce kawai Cutie ke kuma ko tausa baki taba yi min ba. Kodayake nine ban koya miki wannan karatun ba. Tace to yi wankan sai nayi maka. Amma sai ka kawo cin hanci. Dariya take tana maganar domin ta rage masa damuwa. Yace to ki jira na fito zan baki.

Shigarsa toilet keda wuya Zuhra ta bude wardrobe dinsa duk ya hargitse ta fito da kayan. Har ya fito daga wanka tana gyara masa kayansa. Yayi murmushi yau Cutie abin kirki ake ji ne. To nagode ki gyara da kyau. Ita dai bata juyo ba don tasan daga shi sai tawul. A hankali ta juya taga ba ita yake kallo ba sai ta fito da kudin dake boye a jikinta harda dariyarta ta juyo, nayi tsintuwa ba sata ba. Hamza yace kinyi satar kenan. Ai ba'a tsintuwa a cikin daki. Kudin ta nuna masa da fara'a a fuskarta. Ya Hamza har a cikin kaya kake boye kudi? Jin abinda tace ya taho wurin da sauri. Mu gani ya fada yana mika hannu. Mika masa tayi tana cewa sai ka bani ladan tsintuwa. Yanayin farincikinsa bazai misaltu ba. Ba karamin dadi yaji ba wanda hakan da Zuhra ta gani yasa wani hawaye kokarin fito mata tayi saurin mayarwa. Hamza yana ta juya kudin yace ni bazan iya tuna lokacin da na ajiyesu ba. Tace a nan gefen na gansu. Kuka ke neman kwace mata saboda yadda taga yana farinciki don ya tsinci dubu hamsin abinda yafi karfi a da. Ta dan wayance bari na duba su Khalifa na dawo. Tana fita nasa hawayen suka sakko..bai yi kokarin mayar dasu ba sai ma sujjada da yayi ta godiya ga Allah da Ya bashi Zuhra. Tunda ya fito daga toilet ya kula da yadda take yawan juyowa ta kalle shi shiyasa a na karshen yayi saurin kawar da kai. Yana kallon lokacin da ta daga rigarta ta zaro kudin. Wai shi zata yiwa wayo kada yace ta bashi kyauta yaki karba. Zuhra ta cancanci duk wata soyayya da kauna daga gareshi kuma wannan dubu hamsin din yana fata Allah Ya bashi ikon biyanta da abinda ya fisu daraja. A hankali ya furta I love you Zuhra.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 62

Batul Mamman(Mrs)





Washegari tun da Zuhra ta tashi sallar asuba bata koma bacci ba. Tana idarwa ta sauka ta shiga kitchen. Breakfast ta fara hadawa sannan ta dora miyar abincin rana, sannan ta yanka dankali 'yan madaidaita ta dafa da kwai. Bayan ta gama ta hadasu wuri daya ta yanka cucumber da koren tattasai ta gurza caras ta saka mayonnaise. Cikin kankanin lokaci potato salad dinta ya hadu ta saka a fridge inda bazaiyi sanyi sosai ba, idan tayi sallar azahar taliya kawai zata dafa. Duk wannan saurin so take ta fara sakarta ne da wuri. Tana gamawa ta tafi daki zata yi wanka ta tarar yaran duk sun tashi. Bata sami nutsuwa ba sai da ta shiryasu har suka gama cin abinci, ta barsu wurin Tala ta shige dakin da ta ajiye kayan sakar.

Duba kayan da Hamza ya kawo tayi da irin tsarin da makarantun suka bashi. Cikin dan kankanin lokaci ta soma sakarta hankali kwance. Dayake abu ne da take so ta kware a sarrafa injin sakar. Na 'yan nursery din ta fara wanda zata yi musu guda dari da hamsin a dubu daya da dari bibbiyu su kuma su sayar a dubu da dari biyar. Kokarinta ta gama ko na makaranta daya ne kafin litinin ya fara kai musu. Idan aka biya tasan kudin zaiyi masa amfani sosai.

Wayar Izzatu ce ta tashi Hamza tana sanar dashi zata dawo washegari zata biyo jirgin safe. Hamza yace to Allah Ya kawoki lafiya. Tace Amin tunda kaki aiko min da kudi wannan ma Dad dina ne ya bani. Hamza yace to Allah Ya saka masa da alkhairi ya ajiye wayar. Ace ko sau daya zata ce bata kula da yanayinsa da ya canja ba bare ta tambayeshi meye damuwarsa. Tsaki yayi ya tashi ya shiga wanka. Yana fitowa yaci karo da breakfast dinsa a falonsa. Murmushi yayi ya zauna yaci ya koshi. Aiki yake son yi amma yau ko motsin Zuhra baiji ba shiyasa ya fasa ya sauka. Su Nana kawai ya gani a falon suna ta kiriniya yace ina Maama? Junior ya nuna masa dakin da take, kuma Daddy tace kada wanda ya shiga aiki zata yi. Sai a lokacin Hamza ya tuna da zancen saka yace to ku zauna bari naje nace mata sannu da aiki na dawo.

Zuhra na kan riga ta bakwai Hamza ya shigo dakin da sallamarsa. Kafadarta ce ta dan rike saboda kwana biyu bata sakar ta dan tsaya tana dukan wurin. Ganin Hamza ya shigo yasa ta murmushi. Ya Hamza har ka tashi? Nayi tunanin sai ka kai karfe daya. Yace saboda ga kasa sarkin bacci ko. Murmushi tayi tace ni dai bance ba, naga yau asabar ya kamata ka huta. Maimakon yayi magana zagayawa yayi ya tsaya a bayanta sai ji tayi yasa hannuwansa yana mata tausa a kafadunta. Da farko kunya taji sai kuma ta soma dariya saboda ji take yi kamar yana mata cakulkuli. Sosai take dariya har ta fara kokarin tashi ta gudu yace ke dai kina da matsala. Kiyi ta dariya kamar shashashan madina. Da kyar take mayar da numfashi tace to ai kaine kasa ni dariya.

Daga yi miki tausa sai kice na sakaki dariya? To ajiye ki huta ya fada tare da daukan riga guda daya. Yayi murmushi Cutie ashe dai ba cika baki kike yi ba kin iya sakar. Kanta a kasa tana cigaba da aikinta tace kaima zanyi maka kafin na tafi. Amma dai yanzu ka fita idan na ganka bana iya aikin sosai. Ya dan durkusa a gaban injin yana dariya da gaske Cutie? Ko dai kin fara sona ne? Ta dago idonu a bude ni di??? Rufa min asiri Ya Hamza ina ni ina kai. Nifa har na yanke shawarar wanda zan aura idan ka sakeni.

Kamar saukar mari yaji maganarta. Harara ya watsa mata ya fice ba tare da ya sake magana ba. Da taji ya rufe kofar tayi dariya, ita tsokanarsa kawai tayi amma tunda ta ga yaji haushi ta daga hannu sama. Ya Allah Kasa shima yana sona ko dan kadan ne. Ba ita ta fito daga dakin ba sai azahar ta dafa taliya tayi sallah. Har ta idar su Khalifa basu dawo daga masallaci da Hamza ba. Ajiye musu abinci tayi ta kai masa nasa falo ta koma ta cigaba da aiki.

Bayan sallar magariba Inuwa sakatare yazo, Hamza ya sanar da ita zasu fita tayi masa adawo lafiya. Ranar gabadaya Zuhra a saka ta tafi sai sallah da girki da take tashi tayi. Wurin karfe goma ta fito saboda yunwa. Su Khalifa duk sunyi bacci Tala ta kaisu dakinsu ganin Zuhra na aiki. Abinci ta diba da ruwa ta tafi dakinta dashi saboda ko sallar isha bata yi ba. Sai da ta zauna zata ci abincin taga babu cokali. Wanko hannunta kawai tayi a toilet ta zauna taci. A gajiye take sosai ga kafadunta da baya duk suna ciwo. Gajiya da bacci ne suka tarar mata a kan doguwar kujerar da taci abincin ta dan kashingida sai bacci ko hannu bata wanke ba.

Hamza ya dawo gida bayan ya ajiye Inuwa a nasu gidan. Unguwar su Mr Oscar suka je ko akwai wanda yake da labarin inda ya tafi basu samu ba. Dakin da Zuhra ke saka ya duba ya tarar da riguna birjik a kasa ga fitila bata kashe ba ga dukkan alamu zata dawo ta cigaba da aikin ne. Bashi da niyar barinta ta cigaba a ranar saboda yasan ta gaji. Dakinta yaje ya tarar da ita tana bacci a zaune ga plate din abinci a gefenta a kan kujera. Ya duka zai tasheta ya kula da hannunta duk miya har ta soma bushewa. Da gani tana jindadin baccin sai yaki tashinta. A hankali yace Allah Sarki Cutie yasan ba karamar gajiya tayi ba. Tissue ya samo ya goge mata hannun, ya sauke plate din ya gyara mata kwanciya ya fita. Tausayi ta bashi sosai yadda ta dage tana saka ga girki tana yi akan lokaci.

Kusan minti talatin da fitarsa yaji kamar ihu daga dakin Zuhra. Lokacin bai dade da kwanciya ba. Da sauri ya fito ya ganta a tsaye ta rike hannunta na dama tana kuka sosai. Saurin matsowa yayi kusa da ita Cutie me ya same ki? Kara matsawa tayi baya tana kuka tace kada ka matso Ya Hamza ni tawa ta kare. Bai fahimci inda zancen nata ya dosa ba yace taki ta kare kamar yaya? Ki dena kukan kiyi min bayani.

Murya a shake tace abinci naci a wurin nan, ta nuna kujerar...sai bacci ya daukeni amma na tabbatar ban wanke hannu ba. Ina farkawa yanzu naga alamun an lashe hannun amma dai da saura kadan. Hannun damanta ta daga ta nuna masa. Yayi murmushi zai fada mata shi ya goge mata da tissue ta cigaba da magana. Ashe ni kuma a haka zan tafi Ya Hamza, Allah ma Ya sa mutuwa a dalilin annoba ana sakata cikin shahada. Ta sake barkewa da kuka, bera ya lashe min hannu Ya Hamza, ya saka min zazzabin lassa. Yadda Zuhra take kuka da gaske ya bashi dariya sosai. Yace banda sharrinki Cutie kin taba ganin bera a gidan nan. Tace shi bera ina ne baya shiga. A yadda naji a rediyo mutum ba wani dadewa yake ba idan ya kamu da ita.

Dariya Hamza yake son yi amma ya gimtse. Zuhra bata da dama ya fada a ransa. Hannu ya mika mata zo kinji Cutie dina, babu wani bera ki kwantar da hankalinki. Can karshen dakin ta koma kada ka tabani ka kwasa kaima. Ka barni kawai anan har lokacina ya cika. Kodayake naji ance gwamnati na bayar da magani ka sanar dasu akwai mara lafiya a nan sai suzo su daukeni. Ta sunkuyar da kai, nasan ma dakyar zan kai labari. Shi dai Hamza dramar Zuhra nishadi ma ta saka shi ya zauna akan kujerar da ta tashi tace tashi kada ka dauka anan na kwanta. Yana kallo tasa hannun hagunta ta dan tattaba wuyanta. Kaga har na fara jin zazzabin kuwa. Yace Allah ko Dr Zuhra yana murmushi. Sake taban wuyan tayi tace inajin ba zazzabin bane amma shima nasan yana kusa.

Hamza ya taso ya taho wurin da take tsaye ni zan zauna dake ko wane irin ciwo kike dashi kinji. Hannu ta daga masa alamun kada ya matso fuska duk hawaye tace Allah Sarki Ya Hamza shiyasa nake SON ka wallahi saboda kana da kirki da tausayi. Cak Hamza ya tsaya maganarta ta sauka a zuciyarsa. A hankali ya daga kai ya kalleta. Da gaske kina sona Cutie? Kunya taji har ta soma girgiza kai sai ta dena ta dago tana kallonsa. Ya Hamza idan mutum zai mutu ai babu zancen kunya da karya ko? Gara ma na fadi gaskiya na sami lada. Hamza yace wannan gaskiya ne. Zuhra harda gyaran murya tace nasan munyi daku zaka sakeni bayan wata shida to Allah Ya gani wallahi ni bansan ya akayi ba sai naji ina sonka. Ba a matsayin Yayana ba fa. Dadi Hamza yake ji sosai sai ya dan basar to a matsayin me? Sunkuyar da kanta tayi tana magana a hankali. Wallahi Ya Hamza irin na soyayya nake maka jiya har mafarki nayi ka kaini asibiti zan haihu. Amma kada kace min mara kunya wallahi ina zaman zamana tunanin yake zuwa. Kuma in fada maka wata gaskiyar ma duk sallah a sujjada sai nayi addua'a idan da alkhairi Allah Yasa kada ka sake ni. Tamkar ya zuba ruwa a kasa yasha haka Hamza yake ji a wannan lokacin. Ashe ba shi kadai yake sonta ba suka yi shiru da zasu kwari kawunansu. Ya dan bata rai dazu kika ce bakya sona kuma har kin tsayar da mijin aure. Tace wallahi karya nake, irin abin nan ne na mata zan maka ashe ma bani da rabon dadewa a gidan aure.

Ko kanta ta kasa dagawa saboda yadda take jin kunya gashi zata mutu ko soyayyar basu fara ba. Takun Hamza taji ya matso gabanta yasa hannu ya bude bargon da ta rufe kanta dashi. Kuka take tana rokonsa zai kamu da zazzabin lassa. Hamza yayi mata kyakkyawan murmushi sannan ya dauketa tamkar ya dauki karamar yarinya. Da wata bakuwar murya mai dadi yace Cutie ni na goge miki hannun da tissue, ta ware masa idanunta da yake son kallo tace da gaske? Ya gyada kai. A take kunya mai tsanani ta lullube Zuhra. Hamza yayi murmushi yace bari na karasa lada na nayi miki wanka, sai na fara koya miki lesson din soyayya. Irin soyayyar da zata sa mafarkinki na jiya ya tabbata nan da wata tara. Kanta ta tura a kirjinsa don kunya ta kankameshi. Zuciyarsa cike take da son Zuhra yace kinsan wani abu? Girgiza kai tayi batare da ta dago ba...I love you too Cutie. Nima bansan yadda akayi ba sai kawai naji ina matukar sonki. Dadi ne ya mamaye zuciyarta wai ita Hamza mijin Izzatu yake furtawa so. Tafiya taji ya fara yi da ita hanyar toilet ta soma kokarin zillewa.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 63

Batul Mamman(Mrs)





A kofa toilet ya ajiyeta ya fara juyata a gabansa yana karewa kayan jikinta kallo. Kokarin rufe jikinta ta soma yi yace wai ni ta ina kika saka rigar nan? Duk na duba na rasa maballi ko zip. Ajiyar zuciya tayi mai karfi tana murna da bai gani ba. A tsorace take da Ya Hamza. Janyota yayi jikinsa ya zagayeta da hannuwansa. Daga gefen kafadarta ta dama taji ya kama zip din wanda yake boye a jikin riga ya soma sauke mata shi kasa. Duk yadda tayi ta gudu abu ya gagara. Jiki na rawa tace Ya Hamza don Allah banda wanka. Yace kin manta sunnah ne? A'a amma akwai wasu dayawa. Idan nayi wankan da kaina duk abinda kake so zanyi maka. Wani murmushi yayi mata wanda shi kadai yasan ma'anarsa yace to amaryata. Zan jiraki a daki. Sai da ya manna mata kiss a goshi sannan ya tafi.

Sai yanzu take jin tsoron Ya Hamza kuma. Wanka zatayi kawai tayi kwanciyarta. Ta dade tana kalkale jiki ta

Please Login or Register in order to submit comment