Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magana taji yasa hannunsa a kafadarta yana mayar mata da hannuwan breziyarta da suka fito. Daga daren jiya zuwa yau Hamza yasa Zuhra tsananin jin kunya. Yadda ya rufe mata jiki gabadaya ta baya yasa ta kasa motsi. Zuciyarta ce kawai take bugawa da sauri. Tana wannan yanayin har ya saketa bata sani ba. Ganinsa kawai tayi a gabanta yana murmushin da yanzu take yawan gani tare dashi. Hada ido suka yi ta kawar da kanta, a hankali tace duk kasa ni jin kunya. Sai ka rinka wayon taba min jiki. Kuma dai kasan babu kyau. Ya daga gira kina matar tawa. Tace to ba sakina zaka yi ba. Tana fada ta wuce kitchen ta barshi a tsaye. Maganar Zuhra tasa ya shiga damuwa sosai.

Dambun shinkafa ta hada mai rai da lafiya. Ta rinka yawo tsakanin falo da kitchen har abincin ya dahu. Daya da yan mintuna ta gama ta mikawa maigadi. Shi kam yana jindadin sauyin da ake samu na girki a gidan nan. Gashi harda ruwan sanyi tunda an kawo wuta. Na Hamza ma ta hada masa komai a tray ta shiga falonsa ta ajiye sai dai baya ciki. Yunwa take ji sosai domin yau tayi dauriya. Nata tayi niyar zuwa ta diba a kitchen sai taga wata kofa ta bude ashe da toilet a wurin. Tashi tayi zata gudu yace dawo ki zauna fita zanyi, da alama alwala yayi. Zan canja kaya naje office zaman gidan ya isheni. Ba komai ke damunsa ba sai maganar Zuhra ta saki. Ya rasa gane yana son zancen sakin nan yanzu ko kuwa. Da 'yar damuwa a fuskarta tace amma baka da lafiya, ka hakura mana. Yana jindadin yadda take kulawa dashi yace bazan dade ba in sha Allah. A gaban tray din ya tsuguna Me kika dafa mana ne...yar kazama ta iya girki. Tray din ta dauka tunda ni kazama ce ka nemi wani a waje. Yi hakuri ki kawo kinji, ai kinfi kowa tsafta a gidan nan. Bubbude flask din yayi yaga dambun shinkafa tayi da farfesun kaza. A take yawunsa ya tsinke. Wai me yake damunka ne Hamza da kaga abincin sai ka rude kamar wani mayunwaci. Kinsan abincin da Hajiya tafi so kenan dambu ko wane iri ne. Zuhra tace da gaske? tare da dauke flask din da ta zuba masa nasa. Bari naje na juye sauran ina ga zai kai cin mutum uku idan aka hada. Tana magana tana neman fita daga falon. Hamza yace ke dawo bangane me kike nufi ba? Ya daga kawo min abinci ko tasting banyi ba kin dauke. Buga kafa tayi irin ya ma zai ki ganewa...yanzu fa kace min Hajiya na son dambu. Zan hada da sauran sai ka kai mata. Bari nayi sauri ko taliya na dafa mana tunda kaima fita zaka yi.

Tashi yayi da sauri ya kamo wuyan rigarta ta baya ya dawo da ita...haba yar kauye daga magana sai ki dauke abincin. Ya dan yi mata kalar tausayi, nima ina son ci don Allah ki ajiye. Zuhra ta dan harare shi to Hajiyan fa? Flask din ya soma ja itama tana ja. Da taga yafi karfinta sai tace to bari na zuba maka kadan sai ka kai mata sauran. Kaga duk duniya ga namiji bashi da abinda yakai mahaifiyarsa daraja. Kafin na tafi in sha Allah idan kana so kullum duk abinda take ci ka fada min sai na dafa mata. Ummana tace idan nayi aure na taya mijina neman aljanna ta hanyar kyautatawa iyayensa da sauran ayyukan kirki. Kaga yanzu kafin ka sake ni ko dan yaya sai nayi abinda tace ko? Sai kuma ta rufe baki da hannu daya...ka ganni ko? Umma cewa tayi ba fada maka zanyi ba sai dai ka gani a aikace. Don Allah kada kace na fada. A shagwabe take masa maganar wadda tayi matukar tasiri a ransa. Har wani dan dukan bakinta take yi ita a dole tayi laifi. Allah kadai Yasan farincikin da Hamza yaji a wannan lokacin. Yau shine da matar da take nuna damuwa akan mahaifiyarsa fiye dashi. A wannan lokacin gani yake Zuhra tafi masa kowace mace. Bai yarda sonta yake ba amma a shirye yake ya kyautata mata iya karfinsa...a hankali take samun masauki mai daraja a zuciyarsa. Ido ya zuba mata kawai yana kallonta. Ita kuwa kuwa tana kare maganarta tayi gaba da flask din ba tare da ya tareta ba.

A dan plate ta zuba daidai yadda zaici ta hada sauran wuri daya. Takaici ma take bata sani da wuri ba ai da tayu mai yawa. Naman da ta soya ta diba ta zuba a kai saboda farfesun tayi shi da yaji tunda Hamza na mura.

Tunda Zuhra ta fita yake ta kai kawo....ya tsani ta tayar da maganar sakin. Shigowarta tasa ya sami wuri ya zauna ta mika masa plate din. Jan hannunta yayi ya zaunar da ita a gabansa. Nasan kin fini jin yunwa ki ci ni ga nawa abincin ya nuna mata farfesun....cikinta har wani kullewa yake ta yi murmushi da gaske ka bar min. Hamza yace eh...plate din ta janyo gabanta ta soma ci da sauri. Ya kama hannunta lesson two yar kauye, ki dena cin abinci da sauri kuma banda katuwar loma. Ta danji kunya sai tace to yaya zanyi? Dan madaidaici ya diba a spoon din ya nuna mata. Tace dama Babana yace kada nayi loma a gabanka...Allah Yasa na iya denawa dai. Amma meye kake cewa lesson one da two? Kallonta yake ya rasa me yake ji game da ita so nake ki zama yar gayu kafin lokacin rabuwarmu, yadda zan dena kiranki yar kauye. Washe baki tayi da gaske don Allah? To ai da ka fada min da wuri yadda zan kiyaye duk abinda ka gyara min. Rabin abincin taci ta ture plate din ni na koshi. Hamza yace don nace ki rage loma? Yamutsa fuska tayi a'a cikina ne ya kulle tea zan sake sha. Sannu yayi mata sannan yaja plate din ya ci sauran tare da shan farfesun. Kamar kullum yau ma abincin Zuhra yayi dadi. A zuciyarta kuwa dadi taji ta bashi dambun saboda tana ganin irin kallon da yake yiwa abincin tunda ta soma ci.

Yana gamawa ta hada masa wanda zai kaiwa Hajiya a wata yar jaka ta bashi. Yace to daga can zai biya office. Har ya isa gidansu ko na sakan daya bai dena tunanin Zuhran Baban yara ba.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 49

Batul Mamman(Mrs)






Da yake weekend ne a falo ya tarar da mutan gidan suna kallon wani shiri da akeyi a Sunna TV. Kannensa suka gaishe shi ys amsa da sakin fuska. Sannan ya gaishe da iyayensa. Mama tace Yaya yau ina office din? Zama ya fara yi sannan yace mura ke damuna amma tayi sauki. Yanzu ma can zan wuce, aiko ni aka yi wurin Hajiya. Hajiya tace ni kuma? Jakar hannunsa ya tura mata gabanta gashi inji Zuhra. Hajiya dai kunyar bude jakar tayi Mama tace kaga Yaya miko min nagani.

Kowa a falon zuba ido yayi yaga abinda ke jakar sai ga Mama ta fito da food flask mai kyau. Tana budewa dambun shinkafa ne ke kamshi mai dadi. Muryarta a shake kamar tayi kuka tace Adabiyya, Nura, Hamida ku shiga ciki. Ba musu suka tashi suka barsu su uku a falon. Mama ta turawa Hajiya flask. Kinga abinda ke ciki kice wani abu. Murmushi Hajiya tayi nagani Mama amma me zance? Ga mamakinsa duka su biyun hawaye sukeyi. Hankalin Hamza yayi matukar tashi ya fara basu hakuri. Mama tace Yaya ko kasan tunda kayi aure abincin gidanka bai taba shigowa gidan nan ba sai yau. Kasan gidan iyayenka babu yunwa amma a tamu al'adar lokaci zuwa lokaci mace takan yi girki na marmari ko da da sallah ne ta aika gidan surukanta. Irin haka yana sa iyayen miji su so matar musamman idan tana da tarbiyya. Shima mijin indai yasan kimar iyayensa dole matar ta sake samun wuri a zuciyarsa. Hannuwansa ta kama gam ta rike...Yaya yanzu kayi aure, nasan zaka ga kamar muna kin Izzatu amma ko kai shaida ne akan bambancinsu da Zuhra. Kwalla ce ta cika masa ido shima ya basu labarin yadda akayi ya kawo dambun. Hajiya dai kasa rike kukanta tayi ta tashi ta bar falon. Ashe tana da rabon ganin Hamza ya auri macen da zata saka shi a hanya..Allah Yayi mata albarka. Ko ba'a fada ba tasan shima ba karamin dadi yaji ba.

Tana tafiya Mama ta share hawayenta. Yaya ka rike Zuhra amana Alhaji bai maka zaben tumun dare ba. Idan ka cutar da 'yar mutane saboda dalilin da ya jawo aurenku Allah zai kamaka da hakkinta. Tana gama magana tace jirani ina zuwa. Kafin ta dawo Hamida tazo tace Yaya gobe bayan laasar zamu zo ni da Adabiyya muyi weekend. Yace to Allah Ya kaimu.....shikenan zasu zo su takura masa idan yana tare da Zuhra. Shima weekend din yake jira yini biyu a gida ba fita.

Mama dakinta ta tafi ta dauko dubu sababbin dari dari ta bawa Hamza ya kaiwa Zuhra tukwici. Tunda yake bai taba tunanin irin haka na faranta zuciyar iyaye ba sai yau. A hankali yace God bless the day I met you Fatima. Allah Yayi miki albarka. Ko flask din bai jira ba ya fita ya tafi office. Duk aikin baya masa dadi so yake yaji muryar Zuhra tana masa shirmenta ko shagwaba. Har mamakin kansa yake, ga babban abin kunya bashi da numbar wayarta ma. A lokacin ya tuna wayar tata tana da matsala, bayan sun gama cinikin filayensa da wani dillali ya tashi. Beirut road ya wuce ya siyo wata sabuwar waya kirar Samsung mai kyau. Nasa tukwicin kenan na abinda Zuhra tayi masa yau. Daga nan ya biya wani shago yayi yar siyayya ya tafi gidansa.

Yana ajiye mota ko gida bai shiga ba ya fita masallaci saboda a hanya yaji kira. Can ya zauna har aka yi sallar Isha sannan ya dawo ya shigo da kayan da ya siyo. Duhun da ya gani ya tuna masa bai nemi wani maigyaran injin ba gashi har dare yayi. Zuhra ce ta fado masa ita da ko wayar kirki bata da ita. Nemanta ya shiga yi daki daki baiji motsinta ba. Abin ya bashi mamaki ko bacci take yi ne? Yana hawa sama tana fitowa daga dakinsa da fitila a hannu daya, daya hannun kuma tsintsiya ce da abin kwasar shara. Har ajiyar zuciya yayi, ita ta fara magana tace sannu da zuwa. Murmushi yake yauwa yar kauye. Me kike yi da tsintsiya a duhun nan? Tsoro na rinka ji ni kadai sai kawai na fara shara da wankin bandaki. Amma dai ban bata maka rai ba da na shiga dakinka ko? Naga yanzu kana min kirki shine nace bari nima na gyara maka daki. Bai amsa mata ba sai da yazo gabanta...baki yi laifi ba yar kauye, nagode. Ki je kasa akwai kaya a falo ki kai kitchen dinki bari nayi wanka.

Bai shiga dakin ba sai da ta saukq kasa. Dadi yaji sosai har da turaren wuta ta saka. Ta gyara gadon tayi shara. Toilet din ma ta wanke shi tas har boxers dinsa da vests da suke cikin wani abin zuba kayan wanki duk ta wanke amma bata shanya ba saboda wurin shanyar yayi mata tsaho. Sau uku take niyar wankewa sai ta fasa wai kada yace bata da kunya. Sai daga baya ne ta daure zuciyarta ta wanke su harda kawar da fitilar gefe ita bata kalla ba bare ace mata 'yar iska.....

Ba jimawa ya sauko yace mata tayi girkin dare ne tace a'a amma zata dora yanzu. ki dafa mana indomie kawai akwai a cikin kayan da nazo dasu. Cikin 'yan mintuna ta gama ta kawo. A plates daban ta zuba musu. Maigadi kuwa dama ana magariba ta dafa masa taliya. Hamza na kallonta har ta zauna zata fara ci ya dauko nasa plate din ya dawo gabanta, tasa ya juye a cikin natan sannan ya soma ci batare da yace mata komai ba. Ido ta zuba masa ta kasa ci saboda tana gudun tsokanarsa. Ya dago kai suka hada ido....lesson three, yana da kyau mata da miji suci abinci tare. Yana kara musu shakuwa da son juna. Kyakkyawan murmushi tayi...Allah, to amma ba da kai ya kamata naci ba kada mu shaku gashi zamu rab....hannunsa yasa ya rufe mata baki ta daga ido tana kallonsa. Ki dena zancen rabuwarmu akwai sauran lokaci. Just eat. Babu abinda yaki jini yanzu kamar tayi zancen rabuwarsu, idan lokacin yayi sai asan abinyi amma for now so yake yayi enjoying moments dinsu tare.

Sai da Zuhra ta gyara kitchen sannan tace masa sai da safe Allah Ya kara sauki. Lokacin aiki yake da laptop a gabansa. Suma yan nepa kamar sunsan injinsu ya lalace suke kim basu wuta sosai.

Wanka ta dauki lokaci tayi don so take duk abinda ya koya mata ta rinka yi. Zafin yau da sauki akan na jiya shiyasa ta dan shafa mai kadan sannan ta shiga barnar bodyspray. Har humrarta da bata taba shafawa ba ta dauko kwalba daya mai kamshi ta rinka bin duk gabobinta tana shafawa. Rigar baccin da ta dauko yar karama mai siririn hannu har tafi ta jiya kankanta da rashin kauri. Wani dadi take ji ashe haka tsafta ke da dadi...gadonta ta haye ta ajiye fitilar a bedside drawer tayi kwanciyarta. Zafi baisa ta rufa ba amma ba bacci ma take ji ba. Tunani take ko me Hamza yake yi yanzu.......

Kusan rabin awa kenan da yayi wanka ya gama shirin kwanciya sai dai ko alama babu bacci a idanunsa. Zuhra yake son gani amma yana kokarin hana zuciyarsa sabawa da son kasancewa tare da ita. Sakon kudin da Mama ta bashi ya tuna yana wallet dinsa ga wayar da ya siyo mata duk bai bata ba. Murmushi yayi ya tashi don ya sami dalilin zuwa dakinta. [10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 51

Batul Mamman(Mrs)





Kiran farko na assalatu Hamza ya bude idonsa. Murmushi ne ya bayyana a kyakykyawar fuskarsa saboda jin har yanzu Zuhra na jikinsa. Hannunta ya zagaye cikinsa, ga kanta a wurin wuyansa. Yana jin lips dinta a wuyan nasa. Sake matseta yayi zuciyarsa na fada masa yayi a hankali kada ya fada soyayyar da zata iya zame masa rigima nan gaba. A hankali ya rinka shafa kanta yana kiranta da sabon sunan da ya rada mata. Cutie ki tashi asuba tayi. Sake makalewa tayi a jikinsa batare da tasan halin da hakan ke sake jefashi ba. Cikin dabara ya fara janye jikinsa sai itama ta bude ido. Ji yayi ta tashi da sauri Ya Hamza ba dai a haka muka kwana ba. Mikewa yayi ni bana son gulma kin gama makale min a jiki kamar babu pillow a kan gadon zaki wani wayance yanzu. Kunyarsa sosai take ji ta koma cikin bargo ta dukunkune kanta. Gudun kada ya makara sallah yasa yayi murmushi kawai ya fita. Sai da taji ya rufe mata kofa ta tashi ta shiga toilet. Har addua tayi bayan ta idar da sallah,kada yayi mata kallon mara kamun kai.

Tana idarwa dakinta ta gyara da toilet sannan ta sauka ta share falon tayi mopping. Falon ne da girma shiyasa taga gara tayi aikin da wuri. Tun dare ya fada mata bread kawai zaici da safe da tea, wani maidadi ya siyo a Grand square. Ruwan zafi ta dafa ta juye a flask ta hada da kayan tea ta kai dinning table ta ajiye. Ta sallami maigadi ma sannan ta koma daki ta tsefe kitson kanta ta kama gashin da ribbon. Wanka ta shiga ta bata lokaci a bandaki don yanzu an dena jika jika. Ta zauna gaban mudubi ta shafa mai sannan ta rinka feshe jikinta da turaruka. Ta kula Hamza na son kamshi sosai, yau so take ta burge shi yasan tana daukar karatun da yake mata. Wani dogon wando tight baki ta saka ta hada da riga pink wadda ta kusa gwiwarta mai hannu three quarter. Rigar da dan matseta daga sama sannan ta yi fadi kadan daga kasa. Da Hajara suka je kasuwa aka siyo kayan da kudin sakarta. Hoda tasa da kwalli sai dan janbaki kadan pink wanda tayi lining lips dinta da liner pink amma mai dan duhu. Har wani tsalle tayi da tafi ganin tayi kyau. Ta fesa turare a kayanta sannan ta dauko karamin pink da bakin mayafi ta daura irin yadda dai 'yan gayu suke yi. Kasa ta sauka har lokacin Hamza bai sauko ba gashi har takwas da rabi. Tana son zuwa ta duba ko bacci ya koma bayan ya dawo daga masallaci amma tana jin kunyar kayan jikinta.

Wayarta da ta dan sami chaji ta duba taga text din Hajara tana sanar da ita zata zo wurin shabiyu ta kira wayar tun jiya taji a kashe. Wayyo dadi, Zuhra sai murna. Kada Hamza yace wannan karon bata fada masa zata yi bakuwa ba ta yanke shawarar zuwa dakinsa.

A darare tayi sallama ta shiga falon sai taji ya amsa daga cikin daki. Kanta tsaye ta shiga ciki ta ganshi daure da tawul yana tsaye a gaban wardrobe dinsa yana neman kayan sawa. Kafin ya juyo ta runtse idonta tana cewa yayi hakuri. Dariya yaso yi sai dai shigarta ta matukar daukan hankalinsa. Ji yake kamar ya dauketa yayi hugging. Zata fita yace tsaya a nan ina zuwa. Kayan ya saka sannan ya taho gabanta da coat a hannunsa da necktie. Kamshin turarensa ya sanar da ita isowarsa. Cikin murya mai jan hankali yace bude idonki Cutie. A hankali ta budesu ta ganshi tsaye da shirt dinsa duk maballan a bude. Yace jiya na fada miki ana taimakawa miji yasa kaya ko? Kai ta gyada kawai tana kallon kasa. To balle min buttons dinnan naga ko kin koyi karatun. Ta dan zaro ido tana kallonsa. Come on Cutie ina da meeting kada na makara. Hannu na rawa ta soma ballewa daga kasa. Shi dariya take bashi ga tsoro ga baki. Har tazo na karshen wuyansa jikinta sai bari yake. Bayan ta balle ya bata tie din saura wannan. A sanyaye tace ban iya daurawa ba. Gwada mata yayi sannan ya ware ya bata ta daura masa. Kallon da yake mata yasa hannunta ya kasa tsayawa sosai. Nasa hannun ya saka ya taimaka mata har suka daura tare. Yau duk ta kasa kallon shi ya dago kanta da hannunsa sai kawai ta rufe ido tace Ya Hamza kunyarka nake ji ka barni na fita. Zagayeta yayi da hannuwansa sannan ya matso da ita gabansa. Cutie kinyi kyau. Ta danyi murmushi da gaske? Yace da wasa. Kafa ta buga a kasa cike da shagwaba tace haba Ya Hamza mana kace nayi kyau don Allah. Hancinta yaja sannan yace kinyi sosai shiyasa na saka miki Cutie. Muje muyi breakfast kada na makara. Dan tsayawa tayi yau ban gaisheka ba, sai ta durkusa ina kwana ya jiki? Tayar da ita yayi tsaye kinga irin wannan gaisuwar bata dacewa da miji da mata. Kinga yadda ake yi ko don gaba. Duka hannuwansa yasa a kafadunta yayi kissing din lips dinta lightly. A take taji wani abu yana yi mata yawo a ciki. Shi kuwa jan hannunta yayi suka sauka don yasan ko rabin minti suka kara a wurin abinda zai mata sai ya fi wannan.

Yau cin abinci nasu babu wata hira ake yi domin dukkansu tunani suke. Hamza sai tambayar kansa yake ko dai ya fara son Zuhra ne? Itama Zuhra tambayar da take yiwa kanta shin zata iya rabuwa da Ya Hamza. Suna gamawa ya tashi tace anjima Hajara zata zo kanwar Anti Faiza. Yace nima kinga na manta su Adabiyya zasu zo kwana. To da safen nan kuma naga text din Jidda ita da Mariya da matar Ibrahim kanina zasu zo. Inajin duk da yaransu zasu zo anya zaki iya da baki da yawa haka? Ga mamakinsa murna take yi sosai, zan iya mana in sha Allah. Gara na dora girki da wuri saboda yara ma. A dawo lafiya....bata saurare shi ba shige kitchen tana tunanin abinda zata dafawa bakin nata. A hadith na shabiyar a Arba'una Hadith Manzon Allah SAW yace duk wanda yayi imani da Allah da ranar karshe to ya karrama bakonsa. Kuma tarbiyar Ummanta da Baba kenan. Ita yanzu me zata dafa ta burgesu kuma kowa yaci ya koshi?

Hamza ya gaji da tsayuwar mamakin irin wannan murna da Zuhra keyi ya dauki jakarsa ya fita. Izzatu bata taba son 'yan uwansa su zo gidansa ba. Idan sunzo ma zasha ruwa ne da juice su koma gida. Zuhra daban take.... Sai da ya shiga mota ya tuna da sabuwar wayarta ya dawo ya dauko har lokacin tana kitchen. A tsaye ya ganta ta rike haba ita a dole tunani take. Tana ganinsa tace yauwa Ya Hamza dan bani shawarar abinda zan dafa mana. Yace naki din, nida kika tafi kika barni daga cewa zaki yi baki. Ta marairaice masa to yi hakuri kaji Ya Hamzaaaaa. Murmushi yayi Cutie kina abinda kike so. Tayi murmushi tana kallonsa. Shima yayi mata kyau. Zo ga wannan I hope you like it. Da dan murmushi tace ina fa dan gane turanci kalma me tsauri ce dai bana fahimta. Amma dan fassara min abinda kace yanzu turancinka ba irin na malamin English dinmu bane. Fassarawar yayi yana dariya ya mika mata wayar. Gashi nan na saka miki wani sim din sai ki saka na daya wayar tunda mai sim biyu ce. Bade baki kawai tayi tana kallonsa. Sai kuma hawaye Ya Hamza wannan tawa ce? Ya gyda kai, tace Allah Ya saka maka da alkhairi Ya baka ladan faranta min. Allah Ya kareka daga dukkan sharri. Nagode sosai. Wayar dubu ashirin Zuhra kewa kuka da wannan addua, Izzatu kuwa dubu dari ya bata da zata yi tafiya amma kirikiri ta nuna ta raina. Matsowa yayi gabanta ya goge mata hawayen da hannunsa sannan yace nagode da adduarki. Su kuma bakin kiyi musu danwake idan kin iya, a iya sanina dasu Mariya duk mayun danwake ne. Yana gama magana ya fita tabi bayansa. Sai da motarsa ta fita daga cikin gidan ta dena daga masa hannu.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 52

Batul Mamman(Mrs)





Zuhra aiki ya kankama. So take ta gama abincin kafin su iso yadda ba zasu zauna da yunwa ba. Katuwar roba ta samu ta dora danwake sai da tayi tukunya uku tana yi tana juyewa a wata roba mai dan girma. A kalla mutum goma sha biyu zasu ci su koshi sosai. A ranta tace idan bai isa ba sai ta kara. Bata san adadin yaransu ba ga maigadi. Bayan ta gama ta dafa kwai guda goma, ta wanke tumatir, albasa, koren tattasai da cucumber ta ajiye bazata yanka da wuri ba kada yayi tsami. Man da ta soya yasha albasa sannan ta duba bata da juice da yawa. Zobo tayi wanda ta dafa da citta da kaninfari. Ta tace ta saka sugar da lemon tsami sai ruwan cucumber da ta gurza ta tace. A leda ta kulla ta zuba a fridge saboda jug bazai shiga ba. Tana sauke mai ne ya tsallo mata a wuya har wuri biyu. Wani uban tsalle ta doka saboda zafin da taji ta soma karanta ALLAHUMMA AJIRNI MINANNAR saboda neman tsari daga azabar Allah. Allah Ya kiyayemu, amin. Sanda ta gama komai shadaya da rabi ta gyara kitchen sannan taje tayi wanka. Riga da zani ta saka tayi irin kwalliyar dazu mara yawa ta sauko kasa.

Sabuwar wayarta ta dauko sai dai ta kasa gane kan wayar. Tana ta tabe-tabenta taji sallamar Hajara. Kamar kananan yara haka suka rungume juna suna tsalle. Can Hajara tace ke dena jijjiga ni kada ki barar da danki ko 'ya. Zuhra ta zaro ido tana shafa cikin Hajara. Doke hannun tayi to yar duniya meye na shafa min ciki. Kema ina tunanin akwai fa, ji yadda kika yi haske kika kara cikowa. Zuhra ta kama hannunta zo ki zauna yau tattalinki zan taya Yaya Sahabi. Ah su Hajara daga aure sai ciki. Hajara tace ke bana son iskancinki fa. Kema naki yana

Please Login or Register in order to submit comment