Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa sai kayi dawainiya. Dan sunkuyar da kansa yayi albarkarku muke nema Umma. Zuhra mamaki tayi wai dama yana zuwa gidansu. Kawai sai taji ya kara girma a idonta. Zata yi kokarin dena yi masa rashin kunya.

Hira sosai suka yi da Baba ita kuma suka shige daki da Umma. Duk dadi ya kama Umma taga kamar Zuhra ta nutsu. Zuhra tace sai bayan hutu zaki dauko Safara'u ne? Umma tace eh ance sun kusa fara jarabawa. Zuhra tace yace daga nan gidansu zamu je. To me zaki kaiwa surukan naki? Sai a lokacin tayi tunani ya kamata ace ta kai wani abu tunda yana yiwa nata iyayen. Umma bata jirata ba ta fita kitchen. Kayan kamshi da kayan kadin da kanwarta ta aiko mata da yawa ta zuba a leda ta bata. Da zasu tafi bayan sunyi sallar laasar Baba ya bata wani turare mai kyau yace ta kaiwa Alh Nasiru. [10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: [9/26, 12:31 AM] +234 803 244 1205: AL'ADUN WASU 46

Batul Mamman(Mrs)




Ba shiri ya saketa, yana yarfe hannu. sake bude baki tayi zata yi ihu a hankali yace ke nine....ajiyar zuciya tayi da karfi sannan tace da tsoratani kazo yi kake min sanda a daki? Kaima baka da fitila ne? Dukan da tayi masa ya kulle masa ciki gashi ta dame shi da surutu. Da waya na shigo karama bansan inda kika jefar min da ita ba. Yayi kokarin dukawa ya lalubi wayar yaji zafi a cikin....auchhhh. Zuhra tayi saurin matsawa kusa dashi menene ta tambaya a tsorace. A duhun ya harareta naushi na fa kikayi a ciki ga cizo sai kace wata yar dambe. Duk hanyar mugunta kin sani. A wahale take jin muryarsa na fita ta mika hannu tana sannu taji ta taba cikinsa....kamar wadda aka tsikara tayi saurin janye hannun tana cewa yi hakuri. Shima hakan yaji amma bai so ta dauke hannunta ba. Dakin yayi shiru na dan lokaci...Hamza ya kasa gane dalilin da yasa ko yaya jikinsa ya taba na Zuhra sai abin yayi affecting dinsa sosai. Dan gyaran murya yayi bazaki tayani neman wayar ba? Kamar jira take ta durkusa tana rarrafe tana shafa hannu a kasa. Abu taji ta taba tayi saurin janyowa ashe hannun Hamza ne shima yana duddubawa. Da yake da karfinta taja shi kuma baiyi tunanin hakan zai faru ba sai ya fada kanta. Bakon yanayi duka suka tsinci kansu a ciki. Kunya kamar Zuhra ta nutse a wurin, kamshi ne mai dadi yake fita daga jikin Hamza.

Yana fadawa ya gane daurin kirji ne a jikinta...a hankali ya soma yi mata magana. Nifa bana son daurin kirji don Allah ki dena. Wai ita yake hadawa da Allah....saurin dawowa tayi hayyacinta ta fara kokarin ture shi. Yana ji ya sakar mata nauyinsa yana mata dariya.....wai kema kina son jin dumin mijinki shine kika janyoni. To saboda ina tausayinki bazan miki fada ba mu kwana a haka. Wayyo Allah, karshen kunya Zuhra ta gama ji. Har wata in'inar karfi da yaji ta fara. Al'Quran....Al'Quran ba...ba haka bane. Ko kadan bashi da niyar tashi don ya soma jindadin tsokanarta yace to yaya ne? Abinda kika ga munayi da Izzy kike so nayi miki? Wani karfi ne yazowa Zuhra ta dage ta ture shi. Tana ji yana dariya ita kuwa sauran kadan ta soma kuka. Bata dade da matsawa ba yaga wayar ya dauka ya kunna tare da soma haska dakin.

Can bakin kofa ya ganta ta takure harda jan bargonta ta rufe jiki. Koda ya matso harda dan hawayenta. Kusa da ita ya koma me kuma nayi miki kike min kuka? Sai da ta dan matsa sannan tace ba kaine kace wai...wai...wai....kwafa tayi ta kasa karasa maganar. Dariya shagwabarta ke bashi, dazu fa aljani kika kirani banyi kuka ba sai kece mai arhar hawaye zaki min kuka daga wasa. Kin kallonsa tayi saboda kunyar ganinsa babu riga. Yace kinga fito daga bargon nan kisa rigar bacci bana son daurin kirji. Tana kumbura baki tace ni a haka zan kwana. Mikewa yayi to ya rage naki...wai ma kinyu wanka kuwa kafin ki kwanta. Tsami nake ji a dakin nan....dama zuciya na kusa ta fara kuka wallahi bana tsami. Yace to kinyi wankan..tsakaninki da Allah. Rufa tayi har ka sannan tace banyi ba. Rufe bakinta ke da wuya ya janye bargon gaba daya tana kuka ko kulata baiyi ba. Lokaci daya ya yankewa kansa shawarar abinda zaiyi ya taimaka mata kafin su rabu.

Kan gadonta ya jefa bargon sannan ya shiga toilet dinta. Babu komai sai sabulun wanka da omon wanki da wanke toilet. Ficewa yayi ya barta a duhun baiyi magana ba. Ga tsoro tana ji ita kadai amma bata son binsa.

Bayan kamar minti biyar ya dawo da wata fitila mai haske wadda tafi karamar wayar tasa. Shima a babbar bashi da chaji sosai. Wani abu ta gani a hannunsa kamar toothpaste tace ina da makilin fa. Wannan ba makilin bane yar kauye zo nan. Baya ta dan matsa tace yi hakuri. Fitilar ya ajiye a kan dressing mirror dinta sannan ya jawota ya zaunar da ita kamar ranar da yayi mata kwalliya. Duk ta tsargu da daurin kirjinta, shi kuwa ya saka kayan bacci marasa nauyi yanzu. Yana zaunar da ita ya kama hannunta duk da yadda yaji ya daga. Allah Sarki Zuhra sai hawaye...ashe dazu bata ga komai a kunyar da Hamza yake shirin bata ba. Kokarin sauke hannunta tayi ya sha kunu zan matseki idan baki tsaya ba. Kuma kinga mu kadai ne a gidan babu mai taimakonki. To me zaka yi min? Yace sa ido ki gani bana son surutu kuma ki hadiye kukan nan. A hankali take hawaye tana gani ya bude abinda ta zata makilin ne ya zuba a wani abu kamar cokali mai dan fadi ya soma shafa mata a hammata. Ji tayi kamar cakulkuli ta soma dariya....girgiza kai yayi kina da matsala, daga kuka sai dariya. Bata dena dariyar ba har ya gama yace ta bar hannunta a bude. Dayan hannun ya daga ya shafa a nan ma. Wurin minti biyu yana dube dubi a dakin har yaga inda ta ajiye turaruka da body spray din lefenta. Tace wai a haka zan zauna ne? Sai da ya dauko wurin kala biyar sannan ya dawo ya dauki yar robar da tisssue a hannunsa ya kwashe duka gashin. Zuhra ta wage baki ....lahhhh kaga gashin ya cire. Hamza murmushi kawai yayi..yar kauye bata san shaving cream ba. Fes ya share mata sannan ya mika mata shaving stick har uku. Shiga toilet kiyi shaving sannan kiyi wanka ina jiranki a nan. Ya Salam yau Hamza so yake ta tona rami ta boye kanta don kunya.

Kasa shiru tayi tace can kasa wai yau kunya kake son sani ji? Bata san yaji ba yace yes idan baki wuce ba zanzo nayi miki da kaina. Fitilar ta dauka da sauri ta shige harda murda key. Murmushi Hamza yayi ya dan matsa kofar toilet din...kada ki fito sai kinyi wanka sau uku. Ki tabbatar jikinki ya fita sosai don zan duba. Idan baki fita ba na iya yiwa kazamai irinki wanka. Kuma kiyi brush sosai. QTo an hada Zuhra da aiki, sai da tayi amfani da duka shaving sticks din wurin gyara jikinta sannan ta shiga dirzar jiki. Allah Ya kiyaye ta bari yayi mata wanka. Sau biyar ma tayi harda goge kafa da abin kaushi duk da kafar tata bata da matsala. Brush da toothpaste kuwa sun san Hamza na dakin don sun sha aiki. Katon tawul tasa ta goge jikinta sai taji wani dadi da iska na shigarta. A hankali tace na gama. Yana kwance akan gadon nata yace to fito mana. Lallai ma a hakan? Rigar bacci yake duba mata amma sai yace to meye ya rage da zaki boye min. Shiru yaji bata fito ba ya dan kwankwasa, bude ga riga ki saka.

Dan kadan ta bude kofar ta zura hannu. Wata rigar bacci ce mai kyau amma cotton mara nauyi ta wuce gwiwarta ma da karamin hannu. Yace ki goge jikinki sosai kafin ki saka. Dama ta goge ta saka ta yafa tawul din ta fito. A kan stool din yake zaune yace tunda yau akwai zafi sosai ba sai kin shafa mai ba. Har gabanta ya karasa ya cire mata tawul din sannan ya fesa mata body spray kala uku. Don Allah baki ji dadin jikinki ba yanzu ya tambayeta yana murmushi. Kanta a kasa tace naji...yace good, lesson one duk dare sai kinyi wanka kafin ki kwanta kinji ko. A hankali tace to. Wayarsa ya kunna yace to sai da safe ya fita ya bar mata fitilar.
Gado ta haye tayi addu'o'in kwanciya sai dai baccin yaki zuwa. Duk abinda Hamza yayi mata tun shigowarsa ta rinka tunawa tana murmushi......
[9/26, 12:32 AM] +234 803 244 1205: AL'ADUN WASU 45

Batul Mamman(Mrs)




Amma yarinyar nan bata da hankali. Rai a bace ya tashi ya zaki min haka? Don me bakiyi shawara dani ba kika fadawa maigadi kamar zamansa kike yi? Ni gidana babu aljanu. Dariya take kasa kasa, daga abin arziki sai kayi min fada. A take ta kwabe fuska tana shirin yin kuka....sau biyu suka ci min abinci. Wannan wace sabuwar rigimar ce kuma ya fada a zuci. Sannan ya dan rage murya ni kada kiyi min kuka. Kamar yace yi kukan kuwa hawaye ya wanke mata fuska. Sai dai bai sani ba hawayen dariyar da takeyi ne ta wayance kamar kuka take. Rannan sunci min kosai a kitchen sannan a gabanka ma suka ci min tuwo. Subhanallah.....da gaske wai ta zata aljanu ne? Muryarsa da kyar take fita yace ke banda jaraba meye na kirga kosai har kika san anci miki. Kuma ya akayi kika san anci tuwonki a gabana? Zuhra na kukan karya tace ka manta da suka ci tuwon har suka saki cokalin a kasa. Kawar da kansa yayi gefe, ni banji ba bana son sharri. Da dankwalinta ta share idanunta tace kosan zai kai goma wanda suka ci. Hamza bai san lokacin da yace kiji tsoron Allah uku ne zuwa hudu kawai.

Ai kuwa Zuhra ta kyalkyale da dariya sosai. Duk yadda yaso dakewa fuskarsa sai ta bawa mutum dariya. Har yayi hanyar fita ya fadawa maigadi kada a kira malam mai ruqiya sai kawai ya gano tsokanarsa take yi. Ya rufe bakinsa da hannunsa da ya tuna har adadin kosan da yaci ya fada mata. Yana juyowa suka hada ido Zuhra ta kwasa da gudu tayi sama. Binta yayi wato kin mayar dani abokin wasanki ko. Nine aljani me satar abinci.... bata jira ya iso ba ta shige daki ta rufo kofa. Duk yadda taso ta kasa murda key din ta rufe saboda tsoro gashi yana turo kofar. Karfinsu ma ba daya bane sai kawai ya tura kofar.

Hanyar toilet tayi yayi murmushi kina shiga zan rufeki a dakin nan sai kin kwana biyu. Can gefen gado ta tafi babu wurin buya....gabanta na dukan uku uku taga ya biyota. Sai kawai ta zauna a wurin ta boye fuskarta a cikin cinyoyinta. A hankali ya tako yazo gabanta yana murmushi sannan shima ya zauna suna fuskantar juna. Zaman nasu yayi kusa da yawa saboda wurin yayi musu kadan. Da wata irin murya mai dadi yace dago kanki. Sake tura kan tayi cikin cinyoyinta zuciyarta na bugawa da karfi. Bata ankara ba taji yasa hannu biyu ya daga kan nata. Babu inda baya rawa a jikinta don tsoro...shi kuwa wani irin yanayi na daban ya tsinci kansa. Kukan gaske yaga tana yi sai ya soma dariya har sai da tayi mamaki. Yayi ajiyar zuciya, kin iya tsokana amma kina tsoron hukunci ko. Shiru tayi yau babu rashin kunya su kadai a gida. Duk laifinki ne baki taba yimin tayin abinci ba, baki damu da inda mijinki yake samun abinda zaici ba. Kunnenta yaji da kyau kuwa? Miji fa yace. Bata iya kallonsa ba tace kai kace na rinka dafa na iya cikina. Kuma itama kafin ta tafi tace kada nayi girki da kai. Hannunta ya kama suka tashi muje na hukunta ki. Sake yin alamar kuka tayi yace kinga ni na dena yarda da kukan naki na karya.

Plates din ya dauka yace babu ruwa ne ko juice. Akwai ta amsa da mamakin me zaiyi. Ki dauko ki hado da wani spoon din. Falonsa ya shige da abincin. Sai a lokacin tayi ajiyar zuciya....wai amma ta tsorata. A tray ta dora jug cike da zobo mai sanyi da cup da kuma spoon din da yace ta dauko. Samunsa tayi a falonsa yana zaune a kasa yana cin abincin. Murmushin da tayi yayi masa kyau yace na dena satar abincin a bayan idonki. Gabansa ya nuna mata zauna muci.

Dawa??? Ta kwalalo idanu tana kallonsa. Tashi yayi ya zaunar da ita. Punishment dinki kenan na tsokanata kici abinci tare dani. Idan baki ci ba kuma nayi bakinki zan dalle. Don Allah kayi....hannu ya daga mata. Kada ki bata bakinki ki bani hakuri. Daga yau har Izzy ta dawo zaki rinka yin abinci dani. Tace to amma ni bazanci da kai ba. Harara ya sakar mata. Don ma kin samu Hamza zaici abinci plate daya dake...kuma wallahi bana son kazanta. Idan zakiyi na dare zan zo inspection naga yadda kike girkin don nasan halinki.

Ba yadda ta iya dole ta zauna suka ci. Sai dai bata iya sakin jiki ba don da ta diba zaice lomarta tayi girma ko kuma tayi kadan. Haka yayi ta mata har suka gama ta kwashe komai ya wanke. Zobon kuwa bayan ya shanye cewa yayi ta hada masa wani...zobo ma yana cikin abinba Izzy bata masa. Shima na masu karamin karfi ne.

Da daddare tuwon semovita yace tayi da duk miyar da ta ga dama. Su Hamza an sami sake Izzy bata nan. Miyar kuka ta kada taji wake da nama. Bai iya boye mata santinsa ba. Sai da ta gyara kitchen din tsaf ta tafi dakinta.

Wurin shadaya da rabi tana kallo aka dauke wuta. wayarta tayi saurin janyowa daga jikin chaja sai taga ashe bata yi chajin ba. Chajar bata shiga jikin socket din da kyau ba, ga wayar dama bata rikon chaji yanzu. A take ta fara jin tsoro ga zafi. Da bin bango ta janyo bargo daga gadonta da pillow tayi shimfida a gefen kofa. Bata son duhu ko kadan shiyasa take kwana da fitila a kunne ko ta kunna torch light din wayarta.

Hamza na fesa bodyspray ya fito daga wanka aka dauke wuta. Wurin minti biyar baiji maigadi ya tayar da inji ba sai ya sauka. Maigadi yayi yayi injin yaki karbar wuta kuma akwai mai a ciki. Dama irin babban nan ne da yake daukar har AC da fridge. Sunyi iya kokarinsu abu yaci tura Hamza ya kira mutumin dake masa gyara yace ko zaizo da safe. Mutumin yace yana kauyensu yaje karbar kudin auren kanwarsa amma jibi zai dawo. Hakan baiyiwa Hamza dadi ba ya yanke shawarar neman wani washegari domin zafin gari sai ya hana mutum bacci. Dakinsa ya koma sai ya tuna da Zuhra yace bari ya doba ko tayi bacci.

Tsoro yasa Zuhra ta dukunkune kanta cikin bargo duk zafin da akeyi. A hankali ya bude kofar dakin gudun kada ya tasheta idan baccin take yi.

Dishi dishi take ganin inuwar mutum da yayi hanyar gadonta. A ranta tace shikenan barawo ya fado dakinta. Tashi tayi da sauri zata gudu ko da bin bango ne taje dakin Hamza taji anyi saurin rungumota ta baya. Sandarewa tayi a wurin don tsoro kamar ta saki futsari, gumi ya rinka tsatstsafo mata. Hamza bai ankara ba yaji ta kai masa naushi a ciki ta soma ihu...Wayyo Allah barawo. Duk da zafin cikin bakinta ya samu ya toshe da hannunsa ai kuwa ta gantsara masa cizo iya karfinta.
[9/26, 8:58 AM] +234 815 728 4163: AL'ADUN WASU 47

Batul Mamman(Mrs)





Zuhra na idar da sallar asuba ta sauka zuwa kitchen. A zafin nan da rashin wuta tana tsoron kada naman cikin fridge din ya lalace. Fito dashi tayi tana wankewa Hamza ya dawo daga masallaci ya sameta. To acici me kike yi a kitchen da asubar fari. Muryarsa taji kamar hancinsa a toshe yake. Amma yau gabadaya kunyarsa take ji da ladabin musamman ta gaisheshi. Sannan tace nama zan tafasa na soya kada ya lalace saboda babu wuta. Ta sunkuyar da kanta, ya jiki naji kamar yau murar tafi ta jiya. Hamza yace eh amma da sauki. Yaji dadin yadda har ta fuskanci bashi da lafiya ta nuna damuwarta. Kallonta yake yadda take aiki ga hijab dan madaidaici a jikinta, hakan bai hanashi tuno surarta da ya gani ba daren jiya duk da duhun dakin. Ji tayi kamar ana kallonta ta dan juya suka hada ido. Murmushi kawai yayi mata ya tafi.

Flask ta dauko sabo na tea ta wanke sannan ta tafasa ruwan zafi da lipton, citta da kaninfari. Ta soya kwai guda uku da albasa yar kadan saboda bata sani ba ko Hamza na son kwai da albasa. A karamin plate ta zuba ta rufe shi da wani irinsa sannan ta dora mug na shan tea da teaspoon a tray. Bread daya ta bawa maigadi ya siyo musu jiya gashi bata da dankali ko doya. Duka bread din ta dora masa da kayan tea. Kasa shiga falon nasa tayi tana tunanin ko tayi masa karambani ne.

Sai da ta gaji da tsayuwa sannan tayi sallama ta shiga. A kwance ta ganshi kan doguwar kujera ya zurfafa a tunani. Ba komai ke damunsa ba kamar harkar office ga mura tayi masa kamu sosai. Sallamarta ce ta tashe shi ya zauna. Batayi magana ba ta ajiye masa tray din a gabansa sannan ta koma ta dauko flask din. Kallon kayan yakeyi har ta dawo...ta ajiye flask din tana dan sosa kai tace uhmm dama nasa citta da kaninfari a ruwan. Idan baka so sai na tafasa wani. Dago kansa yayi jikinsa duk babu kwari sosai yace me yasa kika dafa da cittar? Naga kana mura ne zai bude maka kirji. To nagode da kulawarki, taimaka ki hada min amma kada kisa sugar. Tausayi ya bata sosai bata yi masa musu ba ta hada masa sannan ta fita ta koma kitchen.

Kazar dama daya ce tayi mata saura ta wanketa sosai ta hada da kayan kamshi da jajjagen kayan miya tayi farfesu. Yana kan wuta ta wanke shinkafa ta baza a tray sannan ta shiga yanka su cabbage, albasa, attaruhu, karas da koren wake. Harda grating din tafarnuwa kadan. Duk bayan ta gama ta sake komawa falon ko ya gama cin abincin. Ya gama amma fa bread din da rage bazata iya raba musu ita da maigadi ba saboda dama ba wani babba bane. Duk yadda take jin yunwa da ta kwashe kayan kwai biyu ta soya ta hadawa maigadi tea da bread din. Tace idan ya gama zai kai mata nikan shinkafa. Talle maigadi yanzu duk gidan babu wanda yake ganin girmansa kamar Zuhra yace to Hajiya nagode. Kitchen ta koma ta kashe farfesun sannan ta fara soya sauran naman. Tana yi ta hada tea ta zauna a kan kujera tana sha don bazata iya cin kwai zalla ba.

Bayan yaci abinci yasha magani jikinsa yayi dan kwari. Shiru babu motsin Zuhra sai yaji babu dadi. Sama yazo hawa yaji alamun har yanzu tana kitchen. Tea ya hangota tana sha shi kadai. Shiga yayi yana kallonta tea kadai kike sha ba bread? A'a na cinye bread din ne. Yadda tayi magabar yasa bai yarda ba ya duba dustbin dinta ina ledar. A zuciyarta tace kaji mutum da bin kwaf. Shiru tayi ba amsa yace bakya jina ne? Na bawa maigadi....kin me? Dama bashi da yawa kika bani, kuma sauran kika bawa maigadi to ke me zaki ci. Baki da Indomie ne? Murmushi kawai tayi ai yanzu zan dora abincin rana bana jin yunwa ma. Mamakinta yake...yanzu kamar Zuhra tasan ta hakura da abinda take so domin wani. Ji yayi ta sami wani gurbi a zuciyarsa. Hannunta ya kama suka koma falo...meyasa baki fada min ba kika yi shiru zaki kwari kanki. Wasa ta soma yi da yatsunta taki kallonsa..ai naga baka da lafiya kuma zan iya jira. Lallai yau ya koyi darasi a wurin Zuhra...shi bai taba bata kudin siyan wani abu ba yasan da kudinta ta sayi bread din kuma ta bashi. Kallon da yake mata yasa duk ta kasa sakewa . Shi kuwa hannu yasa yana shafa gefen fuskarta har sai da tsigar jikinta ta tashi. Nagode kinji, Allah Ya baki lada, kin nuna damuwa da rashin lafiyata sannan kin iya hakura da abinci don wani yaji dadi. Amma daga yau ki rinka fadamin duk abinda kike bukata, tace to cike da kunya sannan ya saketa ta koma aikinta zuciyarta na bugawa da sauri. Sauran naman ta kwashe ta bawa maigadi nikan shinkafar sannan taje tayi wanka. Har ta dauko foundation sai ta tuna da kwalliyar da ya gyara mata ranar da suka fita. Irin yadda yayi mata haka tayi aka dauki deodorant da body spray aka fesa. Sannan kayanta ma suka sha turare mai kamshi.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 48

Batul Mamman(Mrs)




Hamza na falonsa ya gama waya da assistant director akan wasu ayyuka. Duk yayi musu bayanin yadda yake so ayi aikin da alkawarin idan yaji sauki anjima zai shiga office. Bayan ya gama Izzatu ya kira. Hira kadan suka yi ya gaisa da su Khalifa tace masa tana son wucewa Abuja idan an gama bikin. Dad dinta ne zai tafi Japan shine zata je yi masa sallama sai wata lahadin zata dawo. Ransa a bace yace Izzy ba haka muka yi dake ba. I need you here, bama ni da lafiya. Izzy tace kayi hakuri baby amma Dad zaiyi wata biyu kaga ya kamata naje muyi sallama. Idan yace bai amince bama yasan sai taje ko tasa mamanta ta kira shi a waya. Abin mamakin ma tsakaninsa da Allah rashin dawowar tata bai wani dameshi ba. Shi da baya iya nisa da ita...yace to su Khalifa kinsan zasuyi missing school da yawa ko. Eh zasu taho da Tala ranar lahadin amma da Nana zan tafi Abujan. Bye baby, love you. Dip ta ajiye wayar, rike tasa wayar yayi a hannu yana mamakin Izzatu. Ko sau daya bata yi masa sannu ba duk da muryarsa data canja ko bai fada ba za'a gane bashi da lafiya. Har tunani yake yi wai dama haka take masa ko yanzu ne dai saboda bikin da suke yi.

Zuhra na saukowa aka kawo wuta. Tsabar murna yasa tayi ihu har sai da Hamza yaji. Da sauri ya fito yaga abinda ya sameta sai yaga tana ta juyi a falo tana kiran nepa, nepa.... baki ya rike yana kallon ikon Allah, sai kace wata karamar yarinya sai tsalle take yi. Riga da skirt ta saka na yadi mai laushi. Dinkin ya kamata tsam ta daura dankwalinta. Duk da ba wata kwalliya tayi sosai ba amma tayi masa kyau. Gabadaya surar jikinta ta fito sai tuna masa daren jiya take. Sannu da aiki yar kauye ya fada yana tsaye a bakin koma.

Da farko tsoro taji har zata gudu sai kuma ta tsaya ta fara neman wuyan hijab dinta ta saka. Jira yayi ta saka din sannan ya karasa gabanta ya kama kasan hijabin. Hannunta tasa tana neman kwacewa ya janyota gabadaya jikinsa. A take ta fara rawar jiki tana cewa kayi hakuri na dena tsallen. Sosai ya rungumeta yana kallon fuskarta ya cire mata hijab din cikin nutsuwa sannan ya saketa. Kirjinta ta fara kokarin rufewa yace ke jiki ba jiki ba kiyi ta wani rufewa. Haushi taji ta dan tura baki sai ta fara juyi a gabansa tace a hakan? Wallahi ina da jiki, kaga fa...dariyar da yake mata yana cewa juya na gani da kyau yan mata yasa ta bar abinda take yi ta soma kokarin kwatar hijab dinta. Hannunsa ya daga sama tace to na bar maka bari na dauko wani. Baifi taku biyu tayi ba ya jawota jikinsa. Hannuwansa na gaban kirjinta ya dan rage tsaho daidai da kunnenta...ki hakura da hijab din kinga akwai zafi. Kuma naga ashe kina da jikin da zan kalla. Yana

Please Login or Register in order to submit comment