Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke wanda zai so ki. Nasan idan da bakinki kika fadawa Alhaji ke kika nemi sakin bazai ga laifin Sweetyna ba. Sai ta kalli Hamza ta kalli Zuhra duk tunani suke yi. Dan gyaran murya Hamza yayi duka suka mayar da hankulansu gareshi. Idan kin amince da sakin bazan sake ki yanzu ba sai nan da kamar wata shida ko shekara daya saboda Alhaji bazai taba yarda ke kika nema ba. Izzatu ta bata fuska habaaaa Hamza, wata shida is too long. Hankalinsa yana ga Zuhra yana karantar yanayinta saboda ta zurfafa a tunani. Zaman gidan nan ba nata bane saboda babu mai kaunarta. Itama kuma ba son mijin take ba, son kyautatawa iyayenta da nunawa Izzatu kurenta yasa tun farko ta amince. To yanzu idan aka saketa yaya Baba da Umma zasu ji? Waye zai yarda ya aureta idan aka ji aurenta ya mutu bayan wata shida. A sanyaye ta dago kanta suka hada ido da Hamza, saurin kawar da kanta tayi kamar ba itace mai tsare mutane da ido ba. Na yarda amma don Allah kada ku bata min suna idan anyi sakin saboda iyayena....hawaye ne suka zubo mata tayi saurin rufe fuskarta da mayafinta ta fita. Tana jiyo ihun murnar Izzatu ta sake danewa jikin Hamza.

Shima duk jikinsa yayi sanyi don baiyi tunanin zata amince da wuri haka ba. Dole ya sami dalilin da zai fadawa iyayensu yadda baza'a ga laifin kowa cikinsu ba.

Izzatu yaji tana kokarin cire masa riga yasa hannu biyu ya rike abarsa. Meye haka? Dazu kinzo kinyi hugging dina a gaban yarinya. To meye ta fada tana jan rigarsa. Ai tasan abinda yafi haka ma munayi. Tana dariya tace Baby we need to celebrate bari na samo mana juice mai sanyi da cups muyi toasting. Duk da wata shida is a long time amma ba komai. Fita ta sake yi ta barshi yana tunani. Kamata yayi ya yi murna da amincewar Zuhra sai dai a kasan zuciyarsa yasan abinda suke niyar yi bai kamata ba.

Ba jimawa ta dawo da apple juice a wata roba mai kyau ta tsiyaya musu a glass cups. Hamza zai kai nashi baki ta rike hannun, I said lets toast ta kashe masa ido. Tare suka dan buga cups din suka yi yar kara. Izzatu tace TO FREEDOM.
[9/25, 3:53 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 37

Batul Mamman(Mrs)





Kwanaki biyu a tsakani Zuhra na zaune a falo don yanzu Izzatu tace ta rinka zama tana sakewa. Hatta su Khalifa tana bari su zauna da ita. Wurin karfe biyar na yamma Hamza ya shigo maigadi ya biyo shi da ledoji. Kofar inda ya kamata ya zama kitchen din Zuhra yace ya ajiye masa. Su Junior da Izzatu suna ta yi masa sannu da zuwa Zuhra ta mayar da idanunta ga kallon tv. Ita yanzu da tasan matsayinta a gidan tana ganin yi masa sannu da zuwa kamar shishshigi ne. Shima a nasa bangaren bai kulata ba suka tafi dakinsa shi da Izzatu. Ba jimawa ya fito da shirt mara nauyi da dogon wando, da gani wanka yayi.

Abinci ya zauna ci suna ta hira da Izzatu. Sai da ya gama ya tashi ya bude kitchen din Zuhra sannan yace ke zo. Da farko tayi niyar sharewa sai Izzatu tace mata jeki mana Zuhra kayan miya ya siyo miki. A hankali take tafiyar har sai da yaji haushi. Ya nuna mata kayan da hannu alamun ta dauko. Wato kace na dauka da bakinka ne kake ganin asara....Allah Ya sauwake ta fada a ranta. Dauka tayi gabadaya hudun ta shigar dasu kitchen din. Kallon mamakin da yayi mata yasa ta tuna maganarsu dasu Anas da suka ce mata maza basa son mata masu karfi. Sai kuma ta tunawa kanta ai Hamza ba mijin da zasu so juna bane.

Kwalin gas cooker dinta ya farke ya sake fita. Bai dade ba ya shigo dauke da karamar cylinder. Daga can gefe ya ajiyeta sannan ya hada mata gas din. Ya koma kan fridge din shima dan madaidaici ya jona mata. Ita dai tana gefe tana binsa da ido. Sai da ya gama tsaf yace ga kayan miya nan da nama sai ki saka a fridge kada su lalace. Daga yau ki rinka dafa iya abincin da zaki ci. Idan akwai abinda babu a cikin kayanki sai ki fada a siyo. Tsananin farinciki da taji yasa ta washe baki da gaske kake don Allah....daure fuska yayi, na taba wasa dake ne? Nagode, nagode, nagode ta rinka fada tana bude ledojin. Ji tayi yace kuma ki kula kada ki bata wurin nan kinga tun asali ba kitchen bane. Ya nuna mata sink shi kadai zan iya sawa idan kin tafi sai a cire amma bazan miki wani kitchen kabinet ba. Duk da haka ma nagode ta fada cike da murna. Yau zata dafa abinci son ranta taci ta koshi. Hango kanta take da kwano ba ma plate ba shake da abinci.

Wannan irin farinciki da take yi yasa shi jindadi. Ko ba komai yana ganin ya tsira daga laifin tauye mata hakki a ganinsa. Zuhra tana susar kai tace uhmmm....yes ya amsa don yasan akwai abinda take son fada. Dama...dama... gajiya yayi da inda indarta yace dama me? Uhmm nace shi gas din ya zan rinka kunnawa? Au dama baki iya kunnawa ba aka kawo ki dashi. Turo masa baki tayi to mu a gida ba da itace muke yi ba ko risho. Ganin ya daga hannu tasan a bakinta zai sauke shi tayi saurin ja da baya. Nufi na fa ban saba dashi ba amma cikin kayana akwai risho din sai na fito dashi. Hannu ya daga yana nunata, ki fito da me? Wallahi kada kuskura ki kunna min risho a wurin nan in ba so kike ki sake min sabon fenti ba. Kinji ko! Gyada kai ta rinka yi kamar kadangaruwa da taji ya fara daga murya. Sai kuma yace matso ki gani..kunnawa yayi sannan ya gwada ragewa da kashewa duk tana gani. Idan kin kasa ki kira Tala ta nuna miki don naga alama kin fita kauyanci. Ni ba yar kauye bace ta fada tana kara turo bakin nan nata. Biyota Hamza yayi zaiyi maganin rashin kunya ta juya da gudu. A bakin kofa suka ga Izzatu tana dariya. Ai tunda naji kana daga murya nasan kun fara fada shine nazo kallo. Ta kalli Zuhra bai dake ba ko...babu wanda ya bata amsa ta cigaba da dariyarta ta kama hannun Hamza suka fita.

Tuwo Zuhra tayi niyar yi Izzatu tace kada tayi girki an riga anyi abincin dare da ita. Har ranta bata ji dadi ba amma haka ta daure taci abincin.

Inuwa sakatare yana ta hada wasu files zai kaiwa Hamza saboda meeting din da zasu yi sai gashi ya fito daga office dinsa rike da waya da makullin mota. Inuwa yace ranka ya dade fita zaka yi ne? Akwai meeting fa biyu da rabi. Ba jimawa zanyi ba Inuwa in sha Allah. Zanje banki ne tun friday kaga yau alhamis banji alert ba na kudin da ka ciro. Inuwa yace to Allah Ya kiyaye adawo lafiya. Amma ranka ya dade yaushe Oscar yace zai dawo ne muna bukatar sa hannunsa a wasu takardu. Hamza yace nima duk na damu ko jikin mahaifiyar tasa ne sai dai ban same shi a waya ba. Bari nayi sauri na dawo sai muyi maganar dai. Koda ya fita jikin Inuwa sakatare yayi sanyi....Allah Yasa abinda zuciyarsa take kitsa masa ba gaskiya bane.

Manyan architects yau da kanka a office dina. Manaja ke magana yana tashi tsaye suka gaisa da Hamza. Kowa fuskarsa dauke da murmushi suka tambayi juna iyali. Manaja yace sai kuma naji kayi aure ba labari. Kai Hamza ya dan sosa yana tunanin yadda zance ke yawo a gari..kayi hakuri abin ne yazo a gaggauce. Babu komai Allah Ya sanya alkhairi. Yanzu dai how can I help you? Tashi Hamza yayi kada ka damu shigowa nayi mu gaisa na riga na sanar dasu a costumer care alert ne bana ji tun last friday. Kuma har a atm da na cire kudi still banji ba. Manaja yayi dariya ai dole ka damu ku masu harka da manyan kudi. Suna magana text ya shigowa Hamza. Yayi murmushi dadina da bankin nan saurin gyara abu. Gashi har alerts din sun shigo. Yanayin fuskarsa ne ya soma canjawa a take. Manaja ya naga alert na an cire ten million har sau biyu a ranar friday din? Manaja ma dena murmushi yayi ai sau biyun ne Architect. Ka turo sakatare dinka sannan ga mamakina ka turo wani Mr..Mr....mtsw na manta sunan amma dai na kira nayi confirming a wurinka kafin a sakar masa kudin.

Jiri ne ya soma dibar Hamza daga tsaye yayi saurin dafa tebur din manaja ya zauna. Da kyar ya iya cewa Mr Oscar? Eh shi kuwa manajan ya amsa. Ka tuna na kira na tambayeka kace eh kaine ka turo shi. Tabbas manaja ya kira amma a lokacin Izzatu ke faman daga murya tana masifa sai ya saki Zuhra baiji abinda manajan yace ba ya amsa masa. Wato shiyasa Oscar yace mamansa ba lafiya ya tafi garinsu gashi an kusa sati babu mai samunsa a waya. Allahumma ajirni fi musibati wa akhlufni khairan minha.
[9/25, 3:53 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 38

Batul Mamman(Mrs)





A rikice manaja ya fara tambayar Hamza ko sunyi kuskure ne. Numfashin Hamza da kyar yake fita ya dago idanunsa da suka yi nauyi lokaci guda yace babu abinda kayi manaja. Matsalar daga bangarena ne. Sau biyu yana yunkurin tashi amma kafafunsa sun kasa daukarsa. Manajan sai bashi baki yake yana rokonsa ya zauna har zuciyarsa ta daidaita amma sam yaki zama. Ko da ya shiga mota rasa wurin zuwa yayi. Gidansa zai tafi ko office zai koma. Yafi rabin awa a motar kafin ya tayar ya dauki hanya.

Lokacin da ya shiga gidan babu kowa sai Kande mai aikinsu. Da fara'arta ta tare shi tana masa sannu da zuwa. Jikinsa duk a sanyaye yake yace ina mutan gidan ne naji shiru. Nura yana daki su Adabiyya kuma sun tafi makatanta. Hajiya da Mama kuma sunje unguwa. To din ma da kyar ya iya fada sai ya tashi ya tafi dakin Hajiya. Babu abinda yake a lokacin kamar yaga mahaifiyasa. Yaji dadi a bude ta barshi kamar tasan zai zo. Gadonta ya nufa ya kwanta abinda ya dade baiyi ba. Yana rufe ido sai wasu zafafan hawaye suka sauko masa. Ji yake kamar komai nashi ya tsaya cak. Cheque din da Mr Oscar ya dauka hade da sauran da suke office dinsa idan an hada miliyan arbain kenan zai hada ya bawa su Mr Peter ya kawo karshen contract dinsu. A dalilin hada wannan kudin gabadaya maaikatansa suka amince da karban rabin albashinsu a wannan watan don kawai su tseratar da kamfanin. Yanzu gashi miliyan goma ta tafi a kudin bai san ta ina zai samu su ba. Ginin gidansa yaci kudi ba na wasa ba. Idan kuma ya tattara kudaden account dinsa tare da sayar da filayensa zai iya biyan kudin to amma rike iyalinsa zai zama da matsala domin kuwa akalla kafin kudin ayyukan da yake su fito zai dan dauki lokaci. Yana wannan tunanin bacci ya dauke shi.

Hajiya ta kira Mama ko sun taho daukarta daga tata unguwar Mama tace tun dazu nake kiranki ban samu ba. Gamu a garejin makanike ban je inda zani ba. Amma na fasa ana gamawa zamu biyo. Hajiya tace babu komai bari na bi adaidaita sahu kaina ke ciwo. To ki kira Nura mana yazo ya dauke ki. Hajiya tace babu komai shima yau da mura ya tashi. Sai kun dawo ni zan wuce gida. Tana gama wayar suka yi sallama da kawarta da taje dubawa ta fita ta hau adaidaita sahu.

Gabanta yayi mummunan faduwa ganin mutum a kwance a kan gadonta. Alhaji yana Kumo kuma ko shine da wuya ya kwanta a dakinta. Nura kuma sai da ta leka dakinsa ta dubashi sannan ta taho nata. Babu inda baya rawa a jikinta ta ja kafa ta je gefen gadon inda zata ga fuskar mai baccin. Sai da ta dan ja baya saboda wanda bata taba tsammani ba ta gani. A tsorace tace Yaya....shima kansa ke masifar ciwo ya bude idanunsa da kyar. Hawaye ne bushe a fuskarshi Hajiya ta matsa ta taba shi. Bakinta har rawa yake saboda tsoron abinda zai ce tace Yaya me ya faru? Tashi yayi ya gyara rigarsa da ta yamutse sannan ya mayar da hularsa. Yana dan murmushi yace Hajiya babu komai. Zuwa nayi mu gaisa duk bakwa gidan. Bari na koma office sai anjima. Hannunsa ta rike. Itama hawayen take yi....haba Yaya duk duniya idan akwai wanda zaka boyewa damuwarka kasan banda ni ko. Bar ganin ban fiye shiga harkarka ba duk yanayin da ka shiga nakan gane na farinciki ne ko akasinsa. Dawowa yayi yasa mata kuka kamar karamin yaro. Kai bakace Hamza bane dan shekara talatin da takwas mijin Izzatu da Zuhra. Akan kujera ta zauna tana rike da hannunsa ya zauna a gabanta. Kansa ta dora akan cinyarta yayi kukansa mai isarsa. Rabonsa da yi mata irin kukan nan tun ranar da zai tafi Canada. Duk ranar da yayi irinsa to ba karamar damuwa yake ciki ba. Babu wanda yasan yana yi sai ita mahaifiyarsa. Cike da tausayawa irin ta uwa ta rinka shafa kansa har yayi shiru. Ko da ya dago kansa murmushi ne a fuskarsa yace Hajiya na dade banyi miki kuka ba ko. Yau ma sha'awarsa nayi shine na taso daga office. Bari na koma ana jirana meeting karfe biyu da rabi. Lokacin biyu saura kwata. Tunaninsa bai wuce yadda ya mori kudinsa ba lokacin da yake dasu shi kadai. Sai da matsala ta tashi zaizo ya tayarwa da mahaifiyarsa rai. Ya santa bata da magana sosai, ba lallai ko Alhaji ta fadawa amma zata shiga damuwa. Hajiya tace tunda baka son fada min damuwarka zan tayaka addua kamar kullum. Allah Ya kawo sauki cikin dukkan al'amuranka. Ka yawaita ambaton Allah hakan yana yaye damuwa da bacin rai, sannan kayi kokarin sauke hakkin wadanda ke kanka Allah Yayi maka albarka. Wani hawayen ne ya sauko masa yayi saurin gogewa. Amin Hajiya nagode. Tana kallo ya fita ta shiga toilet tayi alwala. Tasan da kansa zaizo ya fada mata matsalar amma abinda yafi dacewa yanzu tayi zata masa. Addua ta dukufa yi masa sannan ta saka dukkan kannensa da iyalansu.

Waya yayiwa Inuwa meeting sai gobe baya jindadin jikinsa. Tunani ne fal a zuciyarsa. Sai yanzu yake tunawa cewa Allah SWT Ya na jarabtar bayinsa ta hanyoyi da dama. A irin rayuwar sakaci da addini da yayi ai dole watarana ya fuskanci irin wannan. Sai yanzu ya sake nadamar abubuwan da yayi a baya da wanda yake kanyi yanzu wato sake da hakkokin matarsa don a zahiri suna damunsa. Sonta kawai baya yi. Zaiyi kokarin kyautata alakarsa da Mahaliccinsa da sauran mutane. Itama Zuhra zaiyi kokari ya sake da ita zuwa lokacin da zai saketa. Tunda basa son juna rabuwar ce zata fi. ta yadda bazai cigaba da daukan hakkinta ba. Zai bari sai komai ya lafa masa a wurin aiki sai ya sanar da Alhaji zai saketa saboda gudun kada Allah Ya kamashi. A lokaci daya duk sai ya zama abin tausayi.
[9/25, 3:54 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 39

Batul Mamman(Mrs)




Karo na biyar kenan da Zuhra ke dandana ruwan miyarta. Yawunta duk ya tsinke saboda yadda kamshin daddawa ke tashi. Nana na biye da ita a kitchen din har ta gama. Tuwon shinkafa tayi malmala biyar yadda zai isheta taci da rana, da daddare sannan ta sami na dumame da safe. Plate ta dauko mai dan fadi da zurfi ta saka malmalar da tafi kowacce girma da miyar kukarta duk a hade. Manshanu kadan ta zuba ta goya Nana a bayanta ba zani ta dauki plate din da hannu biyu ta tafi falo. Tana tafiya tana cewa Nana rike wuyana sosai fa. Ita kuwa Nana sai murna take tace toh.

Sai da ta shimfida tabarma kusa ta dinning table sannan ta zauna cin tuwo. Loma take kaiwa kamar za'a kwace. Tana ci tana bawa Nana a baki. Sun kusa cin rabi Izzatu ta sauko...idanunta kan Zuhra tana bawa yarta tuwo a baki. Har da nan gudunta tayi saurin zuwa inda suke ta dauke Nana tana ta warin kuka da daddawa. Zuhra ya zaki bata abincinki ke da aka ce ki dafa naki ke kadai? Ni ban saba bata abinci da hannu ba kuma bama tuwo sosai saboda yayi mata nauyi. Bata nuna jin haushi ba tace kiyi hakuri ban sani ba. Ganin Izzatu tayi hanyar kitchen yasa Nana ihu tana cewa Mummy sauketa, sauketa abinci. Izzatu tace naji yunwa kike ji bari na wanke miki baki na zuba miki couscous. Bata ankara ba Nana ta galla mata cizo a kafada. Ba shiri ta sauketa tana sosa wurin. Ita kuwa da gudu ta koma gaban kwanon Zuhra. Hannu biyu tasa tana ci bata jira Zuhra ta bata ba. Sake komawa Izzatu tayi zata dauketa sai taji muryar Hamza yana sallama.

Yana shigowa Zuhra ta kai wata shirgegiyar loma bakinta. Ido suka hada ai kuwa ta kware saboda kunya. Ji yayi nauyin zuciyarsa ya ragu saboda yadda yaga tana cin tuwon cike da nishadi. Izzatu tace sweety kaga rigimar Nana wai sai taci abincin Zuhra. To ki kyaleta mana ya fada tare da wucewa sama. Ita kanta Zuhra tayi mamakin amsarsa. Bayansa Izzatu tabi tana masa sannu da zuwa.

Zuhra ji tayi jikinta yayi sanyi saboda yanayin da taga Hamza. Da gani yana cikin damuwa Allah Yasa ba wani laifin tayi masa ba. Plate din tuwo kuwa sai da suka sude shi tas ita da yarta Nana sannan aka tashi aka wanke hannu.

Bayan yayi wanka Izzatu ke tambayarsa ya aiki. A hankali yake magana yace Alhamdulillah. Tana zaune akan kujera tana masa kallon tuhuma tace Hamza ko ka fara sonta ne? Bangane ba shima a zaunen yake don baya jin zai iya cin abinci. Banda damuwar da yake ciki hannun Zuhra yake hangowa miya na binsa ta gefe tana kai lomar tuwo. Yarinyar ta fiye kazanta. Izzatu ta dan sha kunu Zuhra nake nufi. Lokacin da ka shigo ita ka fara kallo kuma ka danyi murmushi. Izzatu kenan,yanzu baki bani komai nasa a baki ba kike tuhumata. To idan naso ta laifi ne? Matata ce fa. Sosai ta daure fuska bana so, Hamza bana son irin wannan wasan. Nan da wata shida zata koma gidan iyayenta mu cigaba da zamanmu yadda muka saba. Daga nan sai kuma ta soma murmushi baka ga yadda take cin abinci ba dazu. Baka ce dan bakin nan tana zai dauki abinda take tura masa ba. Idan ka fita yau pizza zaka siyo mana Baby a matsayin dinner. Ko sau daya bata damu da rashin walwalarsa ba. Hmmm kina bani mamaki Izzy...me kuma nayi Babyna? Murmushi take masa tana kashe ido. Fada mata ma bata lokaci ne don karshenta ta fadi abinda zai kara bata masa rai. Babu komai bari na dan kwanta kaina na ciwo. Tashi tayi to bari na kawo maka magani. Amma kafin nan ga wannan....ta dauko cards har kala hudu na biki. Ni duk matsalar Zuhra yasa na manta next week za'a fara bikin Mardiya cousin dina ta kaduna. Yar Uncle Jibril kanin Dad dinmu. Wai matar da miji ya fadawa yana ciwon kai kenan. Ga naka na daurin aure, ni a son raina ranar saturday na tafi kadunan saboda muna da shirye shirye a gabanmu. Kasan dani suka dogara tunda na zauna a Canada suna son ayi abin da tsari sosai. Kije Allah Ya kiyaye hanya ya fada a takaice....bargo yaja ya rufa har kansa. Bashi da kwarin yi mata fada ko fada mata abinda ya kamata. Sai da ta gama yi masa lissafin kudin da take bukata sannan ta dauko masa magani da ruwa.

Sai la'asar ya tashi jikinsa ya danyi kwari sannan kan ya dena ciwo. Masallacin kusa da gidansa yaje yayi sallah ya dawo yaci abinci. Yana gama cin abincin ya dauki key din mota....Izzy ni zan fita ki fadawa yarinyar nan kada tayi abincin dare zan taho muku da pizza din in sha Allah. Duk maganar a sanyaye yake yinta, wani salihanci yake ji tunda Oscar ya dibga masa sata. Tace harda Zuhra kuma? Ba kayi mata siyayyar kayan abinci ba. Yace nasan nayi amma as long as tana gidan nan zanyi kokarin sauke nauyinta. Tabe baki Izzatu tayi to shikenan sai ka dawo. Har bakin mota ta rakashi ya tafi gidansu. Nan ya zauna suka sha hira da kannensa kamar bashi ba. Hajiya taji dadin ganin ya sake ba kamar dazu ba.
[9/25, 3:54 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 40

Batul Mamman(Mrs)




Takwas da rabi a gida tayi masa ya shigo da ledar pizza har hudu manya. Ya riga ya kudurce a ransa daga yau siyayyar abincin alhamis ta kare sai lokaci lokaci kuma. Itama Izzatu zai bata kudi taje bikin ta dawo sannan ya sanar da ita halin da yake ciki tunda bata tambaya da kanta ba. Ita da yara suna ta murna da ya dawo ta karba ta rarraba. Yanka biyu ta sakawa Zuhra a plate Hamza yace ta kara mata daya saboda big size ce. Tala ta kirawo ta kaiwa Zuhra daki saboda tun bayan magriba bata sauko ba. Tala ta fito daga kitchen hannunta duk kumfa tana gogewa da tsumma. Hamza ya mika hannu bari na kai mata saman zani. Plate din ta mika masa tana tambayarsa a ina zai ci tasa yace ta kai masa falonsa yau baya son hayaniya.

Zuhra na kwance akan doguwar kujerarta tana kallon wani film din Hausa na marigayi Rabilu Musa dan ibro tana ta dariya. Tun daga bakin kofar dakin Hamza yake jin dariyarta. Yarinyar nan bata da kamun kai ya fada a ransa. Ji yadda take dariya kamar ba mace ba. Sallama yayi ta tashi da gudu ta dora hijab a jikinta. Plate din kawai ya mika mata zai fita sai yaji tace ina wuni? Tunawa tayi dazu tana cin tuwo bata gaishe shi ba. Jiya kuwa dama basu hadu ba. Da ya juyo ya amsa sai yaga plate din take karewa kallo. Ta dan kalle shi....shi kuma wannan menene? Pizza ce, baki taba ganinta bane? Tace eh, Allah Yasa da dadi dai. Sai da yayi murmushi sannan yace ci ki ji mana. Yanka daya ta dauko gashi da girma ta dan lankwasa shi biyu ta tura a baki ta gutsiri rabi. Sai da Hamza yasa hannu a bakinsa don mamaki....tabdi! Ke bakinki zai iya yagewa idan kina katuwar loma haka. Dan gayun nan na mata ma baki iya ba. Wani irin dandano taji da bata taba ji ba. Abin dai bazata iya kwatantashi ba. Bata san lokacin da ta furzar da na cikin bakinta ba, wanda bai sauka a ko'ina ba sai kafar Hamza.

Wayyo Allah, Wayyo Allah, Wayyo Allah shine abinda yake ta nanatawa ya dage kafar tare da kawar da kansa gefe. Idan ya kalli kafarsa yasan dole ne yayi amai. Kamar yayi kuka saboda da takaici. Yana girgiza kai yace ke kuwa me nayi miki zaki tofa min abin baki. A tsorace ta dago kai zata bashi hakuri. Sauran ya gani a gefen bakinta da habarta. Dan danne fushin da yake yi ne ya gagara ya daka mata tsawa....Goge bakinki mana. Da hijab dinta tayi saurin gogewa sannan ta sake cewa kayi hakuri, shi kuwa sake hade fuska yayi yana ta yatsina hanci....kai so disgusting yace yana rike hanci.

Irin kallon bangane ba tayi masa sannan tace SO kuma? Ni yaushe kaji nace so? Ba cewa nayi ina sonka ba hakuri nake baka. A wane dalilin zan ce ina sonka? Mamaki ta bashi ya rasa daga ina taji kalmar. Sai daga baya ya tuna yace SO DISGUSTING. Dariya sosai abin ya bashi, yace anya kin taba shiga aji kuwa? Sosai ma kuwa, har SS3 na kai a sakandire. Tana magana ta durkusa zata goge masa na kafar tasa da hannunta. Saurin jan kafar yayi tare da yin tsaki...kazama da hannu kuma zaki goge, ni bani

Please Login or Register in order to submit comment