Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta shiga yiwa kanta tamabayoyin irin haka, duda hakanan ta kaleta ta ce" kina nufin karya tayi kenan da ta sheganta shi?

Aunty idan shegen nema shi sai me? Aunty a yau yannayin rayuwar gidannan zaki duba ki yarda cewa akoy tarbiya, akoy girmama juna da gannin mutuncin juna, aunty yau koda mijinki, wanda mahaifinmu ya zaba maki ya kasance shege ya zaki yi bayan ki karbe shi ki rungume shi , aunty koda shine mai tara shegun kina gannin kinada yanda zaki yi bayan adu.a da neman Allah subahanahu wata allah ya shirya? Ni na tabata koda sunnan da ta kieayeshi da shi hakane aunty kadara ce zata fadawa su Aban wanda mu din nan kai har mahaifiyarmu bata fi karfin Allah ya jarabceta da hakan ba, na san abin da tsoratarwa irin yanda ta baki labarin, aman aunty kin san wani abu? Yau koda harda yaya Jamail a haka ko, wly a lokacin zan rungumi abinna, dan nayi imanin nima ban fi karfin Allah ya jarabceni da hakan ba, sosai na yi mamakin yanda kika fada a tarkon wannan da kika zauna da ita kika ganne nufinta ta fitar da ke ne ita ta shiga aunty

Gaba daya jikin Wujdane yayi sanyi, wani sabon tunani nema ya darsu a zuciyarta, a can kasan ranta take ayana tabas ita yanzu nema ta ji ya fara birge ta, domin idan har haka ne rayuwarsu kusan iri daya ce, shi ana takura masa ana zaginsa dan kadara ta kasance a kansa, ita kuwa jama.a sun mayar da ita aljannah dan halitarta,
A hankali take hasasoshi a idannuwanta, ita kadai murmuahi ya kubce mata da ta tuna musanyar hararan da suke shi da ita

Nan ta zauna tana tsara abubuwan da ita kadai ta barwa ranta

Mom ce ta turo ta shigo dakin nasu da salama

A tare suka amsa mata suna kalonta

Mom ta ce" dakin naki na je bakya nan sai nace kawai kina nan, tashi ki shirya mi tafi wajen mijinki ashe a konce yake ba lafiya, tana gama fada ta juya ta fice a dakin

Tsai Wujdane ta yi bayan ta fito a wanka tana kalon kayan da Aisha ta fitar mata, Lesh ne kalar tsanwa ruwan shukoki da ratsin farifari a jikinsa, sai mayafi fari kar mai duwatsu sai takalmi mai dan tudu da sarka da dan kunaye masu kyan gaske

Da ido take binta, ta shiga gyara mata gashinta ta daure shi a tsakiya ta hade shi waje guda

Fuskar Wujdane ta gyara mata dan daidai ba wani makup bane, girarta ta bi da ja gira maroon sai gashin idannuwanta da ta caje mata da maskara sai dan jan baki ta dan goga mata kadan,

Wujdane bata yi yunkurin hanata ba, domin itama ta yi kudurta fara gabatar da nata kuduri,

Riga da sket ne, suka bi jikinta luf sket din ya kamata sosai ya fitar da kirar jikinta haka rigar irin mai babar wuyan nan ce sai kuma hannayen na salak ne

Bayan ta gama shiryawa Aisha ta kashe mata daurin dan kwali wanda ta dan ja shi baya kadan daga gaba ya fitar da kontacen gashin kanta sannan dunkulelen ya fito a tsakiya
Nan ne Wujdane tace aa, gaskiya a rufe mata ko.ina aman Aisha ta dage da magiyar dan Allah karta taba

Tafe take takalmin kafarta na bada dan kara kwas kwas kwas suka sauko da Aisha

Mom ce zaune da Khadija sai labari Khadijar ke bata

Gaban Khadija sai da ya yanke ya fadi tayi gagawar kawar da kanta a kallon Wujdane tana jin kanta ta muzanta, Mom kanta sai da ta yi mata adu.a a kasan zuciyarta

Mikewa Mom ta yi, suka yi daga da Aisha wace ta saka hijabinta dan ta raka su itama, Wujdane na karshe

Har zata fita ta dakata ta dawo wajen Khadija ta ce" ji mana

Khadija ta dago tana kallonta, Wujdane ta ci gaba" dole na gode maki, domin kin taimake ni sosai, na so tafka asara na kin karbar mijina a tafin hannuna , aman a yau maganar da kika fada min ta ainahin shi din wanene sai na ji du duniyar nan bani da wanda zuciyata ta aminta da shi da na so shi irin *Alaidine* wato ni wujdane koda Alaidine aljani ne ina sonsa πŸ€ͺ



Nafa yi yaji gaskiya, na yi yaji kila wa kala zan kamala πŸ˜πŸ™„πŸ™„πŸ™„πŸ™„πŸ™„, ance ❀😍 kadai nake da muradi? Ga na yau byby
[2/1, 2:29 PM] Ummi Tandama.: πŸ¦„πŸ¦„ *BANI DA ZABI*πŸ¦„πŸ¦„





*30*


WRINTING BY *SAJIDA*



Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*


MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*

................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....



I.m sorry plz wly biki muke


Jansu direba ke yi sun yi shiru , Aisha ce a gaba Mom da Wujdane a baya,

Tunani ne fal cikin zuciyar Wujdane na yanda zatana rama abubuwan da suke yi mata daga matar Alaidine har tsohuwar matarsa da shi din kansa,

Wani murmushi ne ya subuce mata da ta tuna yanda fuskar khadija ta nuna firgici da kalamanta, ita kanta sai da ta ji maganar da ta fada wani banbarakwai da ita wai tana son Alaidine,

Zata buga kwalon da suke bugawa ne, zata yi kokarin yin gem din, domin ta lura zama ne ake marar tsari, daga baya idan hankalin su innarta ya konta ta nemi sakinta a sawaka mata da irin rayuwar nan dan kuwa ita tun tana karama bata muradin cudanya da masu hannu da shuni dan ta rigaya ta hade su cewar basa kyautatawa talakawa basa mutunta talakawa

A haka suka karaso gidan Alaidine,
Ba aisha ba ita kanta sai da ta firgita, gaba daya ginnin irin ginnin nan ne na tsakiya shi ba a kasa ba shi ba a can sama ba, ana kiran gidan ne da gidan glasss, domin du rabin gidan glass ne, ta ko.ina kana iya kallon kanka dan kuwa ma.aikatan gidan suna yin aikinsu


Mom ce a gaba sai su Wujdane na biye da ita,

Jamail ne ya fito da gajeran wandonsa zai je gudu wajen motsa jiki na cikin gidan

Da murmushinsa ya nufo su yana mai murnar ganninsu harda Aisharsa,

Da Aisha da Wujdane gaba dayansu juya bayansu suka yi cike da tsoron ganninsa a haka domin kuwa su dai tunda suke basu taba gannin namiji baba haka da irin shigar nan, (zaku fada ne)

Murmushi Mom ta yi, ta ce" ka ga malan tafi ka saka sutura mana ka sakan yayana jin kunyarka a haka

Shima murmushin ya saki ya miko hannunsa wajen Aisha ya ce" madame zo mu tafi bangarena kafin su fito ko?
Ai da sauri Aisha ta labe a bayan Mom harda rike hijabinta gam kamar wani dodo zai kamata

Dariya yake sosai, ya koma bangarensa, a ransa shi dai yannayin tarbiyarsu na bashi sha.awa,

Da kalo Alawiya ta bi shi, yana daria ta shiga tambayar kanta shi kuwa wannan dariyar menene yake haka?
Kafin ta samu amsar tambayarta sai ga su mom din sun shigo gaba dayansu bayan sun yi salama

Da ido kawai take binsu, irin kallon nan na an takura maka, wanda ya kashe su Wujdane da mamaki, wai mahaifiyar mijinka ne zata yi salama ka yi mata shiru, ta shigo ciki ka bita da kallon raini haka?

Aa ya zaku shigo min gida har ku zarto min falo haka ba wani salama ba komai idan fa kuka tarar da abinda yafi kallon idannuwanku bayan kun san cikin gidana ne hakan na iya faruwa? Kamar an matseta ta shiga sakin zancen nan tana kallon Su Wujdane wato da su take banda Mom a tunaninta,

Mom ta kada kai, bata ce da ita komai ba domin sam ta lura yarinyar bata da girmama mutane, sannan ai ta san sarai wscece Wujdane, idanma ta nuna an takura mata da zuwa gida ai yanzu gidan ba na ita kadai bane

Wujdane wani malalacin murmushi ne ta sakar mata, bata da niyar tanka mata domin a gaban Mom suke, bata da niyar bata amsa a yanzu har sai ta karanci kalar nata rashin da.ar,

Bayan Mom suka bi wace ta umarce su da hakan suka kama haurawa samA

Da wata muguwar harara ta raka su, itama ta aniyar binsu saman wato bangaren Alaidine

A nanma sun wanke isannuwansu da kallo , a falonsa yake, yana kwonce nan kasa saman capet din dakin mai ruwan ash color da bakibaki a jikin mai gashin mage

Jikin dogon wando ne baki, irin na costume sai yar riga fara mai siririn hannu wace ta bayanar mai da damtsen hannunsa da rabi rabin fafadan kirjinsa , idan ka ganshi ba irin shigar nan sai ka sha mamakin irin yanda jikinsa yake

Gefensa Boy ne da dan wandonsa ba riga yana ta bacinsa hankali konce

Salamar Mom ce ta saka shi kokarin zaunawa yana amsa mata sannan ya mayar da hankalinsa kan kofar dan gannin Mom dinsa

Maimakun Mom ta fara shigowa sai ta umarci Wujdane da ta fara shiga (tun farko Alawiya, rashin girmama girman mijinta da na sarakuwarta ya saka har Mom idan ta zo takan takawa da kanta ta haura wajen danta, a yau kuwa ta ja tunga ta tsaya ta tura Wujdane ne dan abubuwa biyu, na farko dai ta nunawa Alawiya dake tare da su irin kusanci mata da miji wanda a lokacin da yaronka yayi aure ya dace du wani abin da ya,shafe shi kafin kowa ya shiga ke matarsa kece farko, domin a yanzu a yannayin nan mai yiwuwa suturar jikinsa bai dace su shiga su tarar da shi a hakan ba, sai abu na gaba tana son shakuwa ta shiga tsakanin Wujdane da Alaidine ne)
Fuska ta daure ta tsaya kan kofar danma kar Alawiyar ta shiga, domin a da can bata nuna damuwarta da hakan sai yanzu dan neman izgili

A hankali ta tura kofar ta shiga da salama a bakinta,
Dan dakatawa ta yi tana neman wanda ya amsa masu salamar sai dai bata ganshi ba domin sam bata kawo a ranta cewar zai konta a capet ba

Juyawa ta yi ta duka ta bayar da kanta wajen kofa dan cire takalmin kafarta mai yar igiya siririya,
Sai da ta gama cirewar ta mike a hankali ta juyo ta fara dan takawa tana mai kuma yin salama ta nufi capet dan ta zauna a tunaninta ko wani wajen ya shige ne?

Kallonta kawai yake, a kasan zuciyarsa yana aiyana ta faru ta kare, wato ya guje mata dan kar ya ganta , yana jinyar fitsarariyar zuciyarsa yayi ya warke ya koma sabgogin gabansa sai gata ta zo wajensa, sannan ita fitinana harda juyawa ta nuno masa duwaiya dan ya ga tana da su(a tunaninkaπŸ€”πŸ˜±?), shi a yau din nan, yarinyar nan ta gama firgita shi sannan ta bashi tsoro a lokacin da yake jin zuciyarsa na samun nutsuwa da alama daman itace damuwarsa wace take dauke masa baci yayi ta tunani a kan rayuwarta, wanda dalilin hakan ya je gidansu ya fi a kirga dan kawai ya san wacece ita? Me ta tagaza mai karfi haka da yake wargaza shi a hankali hankali?

Idannuwanta ne suka sauka tsai cikin nasa, gabanta sai da ya yanke ya fadi ta yi gagawar juyar da kanta gefe domin idannuwanwa sun sauka tas a kan fafadan kirjinsa dake huci shi kadai

Hannunta ta jimke dan kaduwar da ta yi, a ranta take ayana wai su basu da kunyar zama da kaya irin haka ne?

Cike da rashin kunya ta ce" da Allah malan ka tashi ka saka sutura a jikinka da su Mom a kofa suna jira kar su gaji da zaman jiranka kai kuwa kana wani zaune da wasu kaya sai kace karuwin namijiπŸ™†πŸ»β€β™€πŸ˜²πŸ˜³

Alaidine jin magangannun nata yake tamkar a mafarki, tabas ya yarda yau da irin maganar da ake fada cewa mafadaciya ce bata da kunya dan akoy wani saurayi sale da ya tambaya kawai inane gidan su Wujdane,? Ai da ya takarkare ya fara yi masa zuba, domin ta taba wanka masa mari suka dambatu kuma shi yafi shan wahala, ya kara da fadin Wujdane Mama, banda yawo da masifa ma abinda take yi a rayuwa , harda rantsuwar yanzu haka yayi imanin wanda ya aureta ya kwashi masifa ne da kansa domin watarana idan ya yarda ya bata mata rai sai tayi masa lilis dan kowa a anguwar yana fadin tabas aljannu ne da ita masu saka mata karfin doki a jikinta (toh fa)

Murmushi ya tsinci kansa da saki, ya mike a hankali yana takowa kusanta, du taku daya sai ya ayana irin kokarinta na ta kale shi ta tafka masa rashin kunya,

Sai da ya zo daf da ita daga bayanta, yar ficik da ita idan suka jera, aman dan kokari ta iya buda fitsararen bakinta ta yi masa fitsara haka ko ji take Jamail ne?

Wai karuwin namiji, bayan ita ce mai yawo?

Tsahonsa ya rage, ya dora habarsa a daidai wuyanta inda sajensa yayi masauki a wuyanta da gefen fuskarta, a hankali yake dan goga sajen nasa yana shakar wani fitinanen kanshi dake dukan hancinsa , hannunsa a zagaye da jikinta ya riketa aman ba sosai ba

Tsoro ne ya darsun mata lokaci guda jin wani abu na gugan fatar jikinta wanda bata taba jinsa haka tunda aka haifeta ba, da sauri ta kufce ta juyo da karfinta sai dai tana juyowar ta afka a cikin kirjinsa har sai da daurin dan kwalinta ya kufce ya fadi kasa, mayafinta daman ya jima da faduwa gashinta tufkar nan ta warware aman daurin mai kunce ba

A hankali ta furta" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, A.uzubilahi minna shaidanin rajim

Murmushi ya saki ya sasauta rikon da yayi mata, ai kuwa ta samu bakin magana ta dago kanta ido taf da kwala ta ce" meye wannan ? Me kake yi wannan?

Idannuwansa ya kankance ya ce" karuwancin ne wai zan gwada maki

Wujdane da ido ya raina fata ta janye jikinta a nasa ta ce" ka ga malan ni bana son salon iskancin nan.............

Kafin Wujdane ta karasa maganarta sai jin wani dumi dumi ta yi a lebenta, wanda ta ji shi har cikin bakinta,
Alaidine ne ya cafke bakinta da niyar ya hukunta yanda take kokarin yi masa rashin kunya gatsai gatsai haka , aman maimakun ya hukuntatan sai ya bige da bata wani zazafan kiss, wanda shi kansa bai taba sannin wai idan aka yi kissing din mace ana jin irin abinda yake ji a yanzu ba, bai taba kawowa ransa cewa just kissing zai hargitsa masa tunani ya rikita shi ba sai a yau, hannunsa na rawa ya saka ya talafe kanta , na damar kuwa ya rike bayanta ya matsota sosai jikinsa dan tana wutsil wutsil din kwatar kanta, a hankali ya........



😳😳😳😳😳😳 ku ga du anyi zuru a ji yayi mai🀣🀣🀣🀣, naki din😎🀣🀣🀣


Shin Alaidine na kokarin fice gona da iri ne bayan ko nomata bai soma ba?
Su Mom fa? Suna ina ne?
Hajiya Wujdane sarakan fitsara ina bakin ya tafi ne????????????
[2/1, 2:30 PM] Ummi Tandama.: πŸ¦„πŸ¦„ *BANI DA ZABI*πŸ¦„πŸ¦„





*32*


WRINTING BY *SAJIDA*



Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*


MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*

................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....

*ina barar adu.a bayin Allah , na gode*


Kalar baya son rainin nan yayi da fuskarsa ya ce" mu tafi ka aje ni gidan Mom, na gaisheta na ga Boy

Anwar ya mike ya shiga tatara kayan yayan nasa dangin su waya bai ce komai ba, can kasan zuciyarsa kuwa dariya na tukarsa yana ayana abubuwa da dama da ya ga sun canza a wajen yayan nasa a kasan ransa


Shigowarsu gidan Mom gabansa ya yanke ya fadi, domin ya ga wani sabon babur a ajiye a nan daga an shigo toh aman bai saka komai a ransa ba sai sa ya hango Wujdane ta fito da gudu gudu ta nufo tsakar gidan da wata doguwar riga baka mai santsi a jikinta, garin gudun da take ya saka dan kwalinta ya fadi aman bata tsaya damar daukansa ba


Lukman ne kamar yanda suka yi da Aba kan ya zo zai yi masa bayanin da zai saka shi kara gamsuwa ya yi amana da halin da yake ciki a yau ya shirya zuwan wanda ita bata san da zancen ba kwata kwata shi sin kansa bai san cewa wai a nan gidan take ba

Tana zaune ta ga shigowarsa kamar a mafarki hakan ya tunzura zuciyarta ta mike ta nufo shi dan ta yi masa tas irin wulakancin da yayi mata domin ita rabonta da ta saka shi a ido tun aurensu sauran kwana uku gashi yanzu ya zo ya saka haka ta faru ta auri mutumin da bai san darajarta ba

Shi dinma gidan yake karewa kalo, a kasan zuciyarsa yana aiyana lale Aisha ta shigo baban gida, yana kallon tsare tsaren gidan ya hangi budurwa na nufo wajensa da gudu gudu ko dan kwali babu a kanta hakan ya saka shi bada hankalinsa wajen daidai shigowar su Alaidine

Tana isowa ta ja ta tsaya dan nesa kadan sa shi auka shiga aikawa juna da kallo, ita kallon haushi da tambayar abunda ya kawo shi gidan take shi kuwa kallon mamaki , soyaya kai harma da kokonton anya Wujdane dinsa ce?

Hannunsa ya dago ya nunota cike da fara.a ya ce" WuWuWujdanena? Ke ce? Dan Allah ke ce? Daman Elhaj nan ya kawo min ke? Wujdane na daman kina raye? Daman ba.a yi maki aure ba yayanki yace na manta ki anyi maki aure? Daman na fada masa ko wa kike aure sai ya sake ki na auri abinna domin dan ni kadai aka halice ki Wujdane na, ni na san ba zaki taba mantawa da soyayarmu har ki auri wanina ba

Anwar da ya lura da yannayin yayansa yayi kokarin bude motar dan ya karasa ya babala wannan mahaukacin da yake yiwa kallon bashi da hankali sannan ya kora Wujdane da har ta tsaya sauraron wani kato da aurenta ko shigar kirki babu a jikinta, aman mai sai Alaidine ya dakatar da shi
Gaba daya jikinsa rawa yake, du irin sanyin ac din motar Anwar bai hana zufa karyo masa ba, a hankali ya bude motar ya fito ya dan matsa wajensu ya ja hannunsa ya harde a daidai kirjinsa ya tsurawa yannayin tsayuwarsu ido sannan yana iya jiyo abinda suke fada daga inda yake


Wujdane ki amsa ni mana? Ina rokonki ki amsa ni Wujdane, πŸ‘πŸ½ Lukman ya karasa da kalar tausayi yana kallon Wujdane da take jifansa da harara

Cikin wata murya mai cike da takaici ta ce" Lukman, mai nayi maka a ranar nan? Abinda kawai nake son sani mai yayi zafi da ka so zubawa iyayena kasa a ido? Yanzun bai isheka ba ka biyo ni nan? Mai ka zo yi min a nan?

Nan Lukman ya marairaicw murya ya ce" Wujdane ki gafarce ni, a wannan rana kadarata ce ta afka min, bani da sanin abinda zai faru sai ana sauran kwana biyu, an yi min aure da wata a gidanmu sannan an hana ni aurenki, ba yanda banyi ba dan su saurareni aman suka yi bilis da ni, Elhajin gidannan shi ya taushe ni harma na samu nutsuwa na tafi cike da kunyar malan, ashe ya kilace min ke a nan Wujdanena?


Wani kallon sama da kasa ta bi shi da shi, ta ja uban tsaki ta ce" haka ne, an tarda su an fada masu Wujdane yar iska ce ko? An gargade su kar su yarda ka auri mai sifar aljannu ko? Lukman ni nayi imanin dama da wuya yan gidanku su soni aman banyi tunanin zaka shiga jikina haka sannan ka wulakantani ba, sai dai ka sani a yanzu ba wani abin da zai iya shiga tsakanina da kai domin an yi min aure, an aura min dan gidan Elhajin gidan nan dalilin da ya saka ka ganni a gidan, an aura min mijin da a duniyar nan ina gannin ina cikin mutanen da ya tsana, an aura min mijin da aka yi masa dole baya ra.ayin ganina baya maraba da ni, banyi tunanin mijin da zan zauna da shi zai kyamace ni ba, na dai yi tunanin dangin mijina aman a rayuwana na yau ina cikin gidan mahaifiyar mijin da aka aura min take sona tamkar yarta, aba na kulawa da rayuwana yan uwansa na mutunta ni, Lukman ba komai ka je Allah ya baka zaman lafiya da jakar matar da ka aura

Tana gama fadan haka ta juya da nufin barin wajen, domin har ga Allah ita tana jin Lukman a ranta ko ba komai shine mutumin da ya jure haukanta harma ya saka tayi amana da shi


Taku yayi da sauri ya riko hannunta ta baya, wanda ya saka numfashin Alaidine kusan daukewa, daman ya gama hawa caji tun daga yannayin bayannan Wujdane wa Lukman, somin shi ba abinda ya fahimta sai tsantsar soyaya a tsakaninsu wanda take jin haushin anki aura mata wanda take so a fahimtarsa sai maganar da tayi a dungule cewar ya gama jiga jikinta shi a nashi fasarar ya gama sanninta a ya mace zai guje ta, hankalin Alaidine ya kai kololuwar tashi da bacin irin yanda wannan garjejen kato ya tsaya gaban matar da take tasa ta suna yanai mata maganar soyaya harma tana nuna yannayin tayi missing din hakan
Sai abinda ya tainke tunaninsa, ya tafi da lunfashinsa na seconni, ya rikita shi ya girgiza zuciyarsa , abinda idannuwansa suka gane masa Lukman ya riko hannun Wujdane a lokacin da take kokarin komawa ciki,


Kafafuwansa ya daga bisa umarnin zuciyarsa, taku ne na gagawa irin kana jefa kafa ne a bisa umarnin zuciyarka, isannuwansa kyam a kan hannun nan na Lukman sa ya zama bakikirin a jikin lalausar farar fatar Wujdane

Wujdane da mamaki da haushi haushi ta juyo ta daga hannunta na daman wanda ba shine Lukman ya rikw mata ba ta kawo hannun nata da zafin rai zata dauke Lukman da mari aman komai ya tsaya mata
Sanadiyar mutumin da yake sakata faduwar gaba, wanda yake tsayar mata da tunani idan ya bukaci hakan har sai ta gama nasa tunanin, wanda tun ranar da ya dora lalausan lebensa saman nata da niyar hukuntata ya saka ta a tashin hankali, domin ko baci take sai tayi firgigit ta farka tana sauke ajiyar zuciya, hakanma ta dora a kan haushin Lukman ta ayana shi ya jaza mata wannan tashin hankali da ta tsinci kanta a ciki

Aman a wannan lokaci ta kai iya kololuwar tsorata da yannayinsa, domin ido cikin ido yayi fixernta, da idannuwansa da suka yi jajajir tamkar gauta yake hukuntata, da tsatsauran kallon baki kyauta min ba, kin cuce ni, ni zaki kashe? Bakya tausaya min? Bakya sona? Wannan kazamin zai taba hannunki? Wani zaki saka a gonata? Mai ya fi ni? Yake jifanta da su wa.inda suka rufe da tsantsar soyayar da yake ji tun daga zuciyarsa tana watsa jini ko.ina tana gayatar balaki kala daban daban na tashin hankalin da zai zube masu, ta idannuwansa yake isar mata da sakon yau ta mutu ta lalace, ta idannuwansa ya gama kashe mata jiki da dukan wani inji mai aiki a cikin jikinta, tama kasa kwace hannun nata da ya rike sannan jikinta ya shiga saki kamar zata fadi a kan kafafuwanta, ta rasa kalon tsana take hange ko na tabacin zargin mazinaciyar da yake yi mata a kawayar idannuwansa

Rigarsa ta saman costume dinsa wace yakan dauketa ne kawai sai idan zai shiga meeting harkar kasuwancinsa yake dora su saman chemise dinsa mai dogon hannu ya cire daga jikinsa ya karasa wajensu ya cire idannuwansa a cikin na Wujdane ya dawo da su saman hannun Lukman da yayi karkadaf ya rike yana musa cewar wai tana da aure


Sai a lokacin Lukman ya lura da shi, gabansa ya yanke ya fadi , wannan ai Elhaji ne na sabon gari, wanda yake faman samun kayan wajensa tun bara har yanzu, sai dai yannayinsa ya tsoratar da shi, idannuwansa tamkar ba.a taba yin fari a cikinsu ba sannan gaba daya jijiyoyin jikinsa sun mimike ko ta jikin hannayen rigarsa ana gannin

Please Login or Register in order to submit comment