Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saukar mata da wani
farin ciki da bata san daga ina ya fito ba.
Haka dai yai shawo kanta da zantuka na
karfin gwiwa da tabbatar mata da Halima
mai karan kwana ce.
Tunani da kukan da ta yini tana yi ya
saukar mata da zazzaɓi, wasa wasa tana
zata ji sauki ta samu ta leqa maraɗi amma
ina sai da tayi sati kwance. Kullum Abdoul
kan kira su sau biyu ko uku a rana don ya ji
lafiyansu, amma tana ɗauka zata mika ma
su Ummu Abeyha wayar su yi masa
magana.
Auren na da sati biyu ya samu zuwa
duba su, nan ya iske duk ta rame tayi baki,
da ya tambayi dalili ne yaji ta yi ciwo, bai
tambayi dalilin ta na kin sanar da shi ba.
Dare na yi ta wuce ɗakin Yaransu ta kwanta
abin ya ɓata masa rai har ya tunkare ta da
zancen, buɗan bakinta kuwa sai cewa tayi
"Ni fa sai munje anyi maka gwaji zan
kara amincewa da kai, ba zaka auro min
raguwan sida sannan in amince maka ba"
tana faɗin haka ta juya baya. Bakin cikinsa
ya ninku amma sai bai nuna ba. A daddafe
ya karaci kwanakin da ya ɗiba zai yi on yazo
yayi ya kara gaba.
***
A Ɓangaren amarya da ango kuwa soyayya
suke gudanarwa mai tsafta. Tun da ya
amfana da sadakinsa ya kara jinjina ma
Halima, ya san ba karamin jihadi tayi ba na
tsare mutuncin ta. Ace mace yar shekara
ashirin da shida ai dole tana da sha'awa,
zata bukaci abokin ɗebe kewa tunda dai
mutum ce ba dutse ba. Amma yana da ga
cikin jihadi (jihadul nafs) wanda yafi
kowane nau'i na jihadi daraja fin karfin
zuciya. Yayinda mutum yai hakuri, ya
danne sha'awarsa har zuwa lokacin da ba
ma sha'awa hakkinsa zai kai ka ga aljanna
ne ba wuta ba shima babban nau'i ne na
jihadi mai babban daraja (ni safiyyah
Ummu Abdoul nace Allah ya kare mu da
zuriarmu daga aikata zina da sauran
Alkaba'ir, Aameen ya rabbi ).
Tun lokacin yake bata wani daraja na
musamman don ta karyata masu bahagon
tunanin duk yar da ta je jami'a har ta
kammala to lallai ta siyar da yan
matancinta. Wasu ma har kauɗin kiransu
karuwai suke yi, su kan manta babu
tsattsauran sheda a musulunci kamar
shedan zina.
"banga kaddarar da zai kaini ga auren yar
jami'a ba, balle a ce ta gama har tana aiki,
ai duk ba budurwa cikinsu sai dai budur-
budur" faɗin wani abokin aikinsa. Tsakin
da ya ja ne ya dawo da hankalin Halima
wajen shi.
"Sweetyna! Lafiya kake tsaki" Ta
tambaya fuskanta cike da damuwa.
Kallon cikin idonta yake zuciyarsa na
ayyana masa tsarkin da ke tattare da
dukkan lamuran ta,chan dai ya ce
"Ina mamaki ne, yanda wasu mazajen
musamman namu na Hausa Fulani ke jifan
matan da suka yi karatun boko da rashin
tsarki... " nan dai ya bata labarin yanda
sukayi da abokin aikinsa mai wancan
tunanin.
"ka ji ka dai sweetyna, wai me yasa
mazan hausa fulanin kuma suke ganin nasu
kalar tsarkin a matsayin ado. Amma fa
laifin matan ne, sakarkaru, su bari ko wani
gardi ya taso sai ya ba gaɓɓai huɗu wahala,
kuma su garadan ganin kansu suke a
tsarkaka yayin da matan najasa.
Duk namijin da kaji yana kiran matan
jami'a ko wa'inda suka Gama a Yan iska toh
Allah sweetyna ya san inda yake haɗuwa da
su. Sai ka ga namiji ya gama sheke ayarsa
wai shi a dole zai ma Allah wayau se ya
koma ma auren karamar yarinya. Hukuncin
mace da namiji a fagen shari'a dai ɗaya ne,
duk namijin da yayi saɓon Allah toh saɓo
ne dai dai da na mace, hukuncin su ɗaya
sweetyna" Ta karasa tana sakar masa wasu
sakonni mai gamsar da mai amsa.
"Allah ya bar min ke Amaryar
Abdoul" Ya faɗi yana sumbatarta a goshi.June 2016
Raywarsu na tafiya gunin ban sha'awa,
Abdoul yayi kiba sosai, haskensa ya fito
sosai. Da gani hankalinsa a kwance ne. Duk
sati biyu yana zuwa zindar yayi kwana biyar,
matukar yana kasan. Agaysha dai kiri kiri ta
ki amincewa da shi, akan sai an masa
gwajin sida, yayinda sai chushe chushe
takeyi a jikinta da birne birne duk don
Halima ta mutu.
Sau biyu yaranta na zuwa hutu wajen
Halima, duk suka dawo takan lura da
chanjin da take gani tattare da su, nan ta
fara rigimar baya adalci Halima daɗi ta ke
ci.
"Halima aiki takeyi ba ta jira sai na ɓata
kafin ta yi" Ya iya ce mata ya barta nan.
Kwatsam! Wata rana ta je fitsari sai ta ga
kyankyaso a cikin masan, kasancewar ta
matsoraciyar kyankyaso yasa ta tsuguna tayi
a kasa, ta tsorata ainun ganin kalar Fitsarin
kamar jini ga wasu fararen ababenan a ciki
wanda da ta kalla da kyau sai ta ga ashe
tsutsotsi ne.
Ta firgita ainun, kasancewa ya fi sati
take jin azaba yayin fitsari, kuma bata taɓa
tunanin in tayi ta duba ba, tana tsarki take
matsa wajen da zai flushing.
"kar dai Halima ce ta turo mata" wani
sashi na zuciyarta ya faɗa mata.
"ko kuma naki ne dawo miki ba" ɗayan
sa shin mai faɗin ya ce hakan. Shiru tayi
duk a tsorace. Wa za ta kira, gashi ana
azumi balle ta je wajen boka.
Wasa wasa ciwo ya cin magani,
tsutsotsin har fitowa suke, tunda aka je
asibiti likita ya ce sanadiyyar chushe chushe
ne ko kuma jima'i da mai ciwon ko duka ya
jawo hakan Abdoul ya sa ma ransa chushe
chushe ne, ya haɗa kan yaransa sai
Niamey, sai de ya turo mata kuɗin magani
in ya samu sarari ya leqo ta don cewa yake
"kinga ranar zuwa wajen boka"
Sai da su Halima suka je Zindar da sallah
sannan ta iske laluran Agaysha, kwarai ta
tausaya mata nan ta ɗauki alwashin
taimaka mata. Bata yi shawara da kowa ba
ta shirya komawa har da Agaysha
kasancewa Abdoul ya riga su komawa. Da
fari taki yarda su tafi tare sai da ta tambayi
kawayenta nan suka zuga ta akan taje sai ta
haɗa mata tuggun da zai fitar da ita.
Ko da Abdoul ya gansu bai ce uffan ba, don
yana shirin zuwa wani course a Spain. Ba
zai dawo ba sai Satumba.
Nan Halima tayi ta haɗa ta da likitocin
mata gwanaye masana makamin aiki,
sannan ita ce har sako tayi aka haɗa mata
magunguna daga Egypt duk ta haɗe ma
Agaysha.
Basa ko zaman hira, iyakansu gaisuwa sai
bayani akan magani in an kawo. Duk bidirin
nan daga aljihun Halima ne hakan ya kara
mata daraja a idon Abdoul.
September 2016....
Fari da kyawun Agaysha ya fito sosai,
lafiya ya samu tana son ta nemi gafaran
Halima amma sam bata ba ta fuska ba, don
ko aikin gida bata yarda ta sa mata hannu
ba. Ranar da Abdoul zai dawo ta ga abin
mamaki don shirin da tayi don tarbansa ko
ita da ya yi shekara a France bata yi masa
ba a lokacin.
Da ya shigo gidan kuwa taga abin
mamaki, ita da yara suka tarbo shi tun
daga gate, Agaysha na kallon su ta window,
yaran nan fa ba na Halima ba amma bata yi
son kan raba su da uban su ba. Nan tayi
mamakin kyawun hali irin na Halima.
Sai da ya kintsa ya zauna cin abinci
sannan ta fito tayi masa sannu da dawowa.
Ya amsa a hankali ya dago ya kalle ta, ya
girgiza da kyan da tayi. Sai ka ce kafin suyi
aure. Fitowan Halima ya kalle ta yace
"me kike ba my dear da ta chanza haka"
dariya Halima tayi ta ce
"kace kawai na fita iya kula, ai se Ka
biya kawai"
"Ai gidanki na nan a Aljanna mai babban
daraja" inji Agaysha. Duk sunyi mamaki
don Halima bata taɓa mata abu don ta ce ta
gode ba ma.
Nan ta dage ta roke su gafara, inda ta ke
faɗin ta ga illar boka da bokanci, ta ga illar
zalunci da mugunta. Nan duk suka yafe
mata tare da kara mata nasiha akan tsoron
Allah, wuta gaskiya ce haka Aljanna ma
gaskiya ce.
8th October, 2016
Tun a hanyarsu na dawowa asibiti Halima ke
tsokanar su
"Ya kamata ku je honeymoon fa, wata 9
kenan fa rabonku da juna, tab ni dai na
yafe har sai na haihu nayi arba'in" Ta faɗi
tana kallon Abdoul da ke harararta. Asibiti
suka je aka tabbatar da lafiyan Agaysha.
"wai ido kika sa mana ne haka, mu de
tsofai tsofai damu ina zamu kai
honeymoon" Ya faɗi yana kashe ma
Agaysha ido.
"meye na kashe mata ido " Halima ta
faɗi tana dariya.
"Halima ba fa rayuwar Abdoul kawai kika
haska ba, har na wa da yaranki. Allah ya
sauke ki lfy ya kara mana kaunar juna"
"Aaameeeen!" suka faɗi su duka...
And they live happily ever after....
Et il vécurent heureux pour l'éternité....
Godiya ta musamman ga Haj. Mas'ouda
Moulaye.
Thank you all for sticking around,
MAFARKIN ABDOUL is neva complete
without u. I Luv u all fisabillillahi.
Contact me via
Wattpad
Ummu-Abdoul
Www.ummu-abdoul.com
Www.soufjay.wordpress.com
Instagram
Ummu_Abdoul
Kaico Na....
775 50 2
by Ummu-abdoul
Assalamu Alaikum warahmatullah...
Da fatan kuna lfy and I hop u enjoyed
MAFARKIN ABDOUL... Special gaisuwa cikin
birnin Kano to those dat read without
comment balle votes..
Anyway kaico na is here for u, I wrote it
while I was a novice.. So pls neva mind d
errors nd kwafsis... Luv u
MAFARKIN ABDOUL
Na safiyya ummu abdoul
Ebook creator:- Shuraih Usman 99%
Post at:- www.shuraih.waphall.com

You can download more hausa novels ebook at www.shuraih.waphall.com

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment