Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah zai sa yayi
mata kwarjini amma ina don tsaki tayi tace
"banga uban da ya isa ya sa nayi girki
ba, dilla kalle ka wai kai har namiji ne
anan. Mtsww! An dai rako maza wallahi,
banda ba makwanci wahala ba abinda
mutum zai buga kirji ya ce ya iya. Ka
gayyato Halima daga inda take tayi maka"
Ta faɗi tana barin shi zaune a inda yake.
Kaninsa dama tun da ta fara masa masifa
suka fice daga wajen. Dafe kansa yayi da
hannu biyu yana tunanin wani irin hukunci
zai mata. Ashe dai haka take. Wasu
siraran hawaye ne suka fara zubo masa,
yana tausayin kansa. A haka ya fara tunanin
rayuwar sa, wanda ya sani da wanda aka
bashi labari.
ABDOULLAHI ABOUBAKAR
Asalin kakanninsa yan jihar Borno ne a
gabashin Nijeriya, sana'ar siyar da citta da
tafarnuwa ya kawo su Nijar inda suka sauka
a zindar.
Mahaifinsa Aboubakar ya taso ɗan dangi
kasancewarsa auta cikin yaran kakansu
talatin da shida. Yayi karatu zuwa sakandire
kafin ya faɗa harkan kasuwanci, tun yana
karkashin ubangidansa mommadou har ya
samu kantin kansa.
Amanarsa da gaskiyarsa yasa
ubangidansa masa tallar yarsa mafi soyuwa
a gareshi Safiyyah . Nan take kuwa don shi
ma ya daɗe yana sha'awar mallakarta a
matsayin mata sai dai tsoro ya hana masa
tunkararta.
Anyi biki amarya ta tare a nan cikin
gidansu tare da sauran yan uwansa maza.
Shekarar su ta farko ta haifi yarsu Aisha,
daga nan sai Abdoul wanda tsakanin sa da
Aisha shekara uku ne, daga nan kuma
Safiyyah tayi haihuwa bakwai wanda ya cika
su tara gaba ɗaya.
Duk abinda Alh Aboubakar ya tara akan
karatun Yaransu yake karewa, makaranta
mai kyau yake tura su, duk da kasancewar
daga shi har safiyyah ba suyi wani karatun
zamani ba hakan bai hana Yaransu samun
sakamako mai kyau ba don kullum suna
musu addu'ar samun nasara.
Abdoul na da rauni ɗaya 'yan uwansa,
baya son abinda zai ɓata musu, burinsa
farin cikinsu sannan yana hakuri da duk
wani mai son su. Wannan raunin da kuma
kalaman Halima ya hana shi ɗaukan
muguwar mataki akan Agaysha don duk
abinta bata wulakanta su sai da in shi ta
zage su a gabanshi ko tayi amfani da kissa
ta hana masa yi musu wani abin arziki.
Karar da wayarsa tayi yasa ya dawo
daga duniyar tunanin da yake. Share
hawayen da ya gangaro masa yayi sannan ya
ɗaga wayar.
"kun iso? Toh gani nan" Ya faɗi yana
ɗaukan mukullin mota.
Fita yayi dasu zuwa Assemblée, Auberge
Mourna ya tsaya inda ya kasance gidan
abinci mai lamba ɗaya.
" wannan rowan abinci har ina, salon
kada mu gaisa da Madam ne ko" faɗin
Ɗahiru ɗan jihar Kano. Dariya Abdoul yayi
yace
"kun san tayi nauyi. Muna gama waya
ɗazu sai ga kiranta. Wallahi oder nayi ɗazu
na kai masu" Ya karasa yana istigfari a
zuciyar sa.
Ya kashe musu kuɗi sun ci sun yi kat
sannan suka koma gidansa gaban sa na
faɗi. Ba laifi ta karɓe su da kyau kuma ta
chanza kaya zuwa shiga na kamala. Har
cikin ransa ya ji daɗi don har lemun abarba
da kankana ta basu mai sanyi.Tara
657 69 15
by Ummu-abdoul
Hira sosai sukayi da abokansa, sai da akayi
magariba sannan sukayi sallama. Ranar duk
sai ta wanke laifukanta saboda lafiyayyar
abinci tuwo da fakku (malohia murzazza) ta
kawo musu karfe shida na maraice.
"Ga fa fakku ku ci ku ba Yan Nijeriya
labarin daɗinsa" Ta faɗi tana dariya.
Kasancewar ta gwana a fannin girki yasa
basu so ya kare ba, tas suka tashi da shi
suna ci suna santi. Kudi suka aje mata dubu
hamsin na kuɗin Nijeriya, zo Kuga murna
wajen Agaysha saboda sanin da tayi in ta
juya su zuwa cepa zata samu kusan dubu
ɗari don ma darajar cepa ya faɗi. Da naira
dubu daya za'a baka cepa dubu uku, Yanzu
kuwa dubu da dari shida zaka samu.
Ko da ya dawo daga rakiyansu ya iske
har ta gyara wajen ta baɗe gidan da
kamshi. Har cikin ransa ya ji daɗi. Nan suka
baje hira bayan ya ja musu limancin isha'i.
***
"Yanzu Agaysha haka zamu dinga kallon su
Ummu Abieha da sadiya, shekarun Sadiya
and kusan talatin fa balle ayi maganar
Ummu. Wai bakya jin wani iri ganin su a
gida ba aure" faɗin Abdoul ransa ya kai
kololuwa a ɓaci. Ace Yaransu mata babu
wanda ya fito da niyyar aure.
"wallahi kuwa babansu, duk masu zuwa
kuma da matan su, da anyi maganar aure
matayensu su tada rigima, nima fa abin na
damu na." Ta faɗi tana gyara zama.
"kin san har Halima ta mutu bata yafe
min ba, kar ya zo alhakin ta ne ya ke kama
mu. Allah ka yafe mana yaranmu su samu
mazajen aure" Ya faɗi yana kwalla.
"Aameen ni ko na hudu ne in dai za'a
so su ba komi, " faɗin Agaysha
"Amma ke bakya son kishiya, kike fatan
ayi ma wasu don a auri yaranki. Lallai son
kai ya miki yawa" Ya faɗi yana mikewa, don
ya fara jin kiran sallah.
Kiran sallan ya ki karewa, tun yana Jinsa
daga nesa har yaji na bayan gidansu an
kira. Leman da ya ji yasa ya taɓa gadon da
yake kwance. Jike yake da zufa, da ma ana
mafarki mai tsawo ne haka, shi dai har ga
Allah bai taɓa ko jin labarin mafarki a
bayyane kuma mai tsawo hakaba, tun da ya
samu natsuwa da Agaysha, kalaci kawai yayi
barci ya kwashe shi kafin ya kai ga wanka.
Kallon agogo yayi karfe huɗu da minti
biyar, tabbas la'asar aka kira, shi kuwa
wani irin barci ne wannan tun karfe tara na
safe.
Abinda bai sani ba haka kawai Agaysha
taji bata aminta da shi ba, ta sa masa
maganin barcin da take ɗura ma yaranta in
suka ishe shi. Don kar ma ya nemo Halima
kafin ta dawo daga wajen bakanta. Abin
tambaya anan shin dama ana mafarki a
barcin da ba na Allah ba ko kuwa MAFARKIN
ABDOUL daban ne. Amsar na wajenku
masu karatu😜
Tashi yayi jiki babu kwari, yunwa yake ji
amma bayi ya fara isa yayi wanka, gami da
alwala. A zaune yayi sallah sannan ya shiga
kitchen ya iske tayi tuwo kafin ta fita. A nan
ya zauna ci hannu baka hannu akushi.
Sannan ya samu karfin gwiwan fita. Gidan
Yahai yaje don ya samu rakiyansa, nan ma
ba wani zama yayi ba suka ɗauki jiki zuwa
gidan iyayen Halima.
Bayan an musu iso, sun gaisa da
mahaifinta wanda murna ya hana shi
ɓoyewa. Baffa ya faɗa masa komi dangane
da alakar Halima da Abdoul banda
rabuwansu.
Nasiha sosai yayi musu musamman akan
aje mace fiye da ɗaya a gida, mahimmancin
hakuri da adalci. Sunyi murna kwarai da
karamcin dattijan arziki.
Tsoron Abdoul ɗaya yanda Halima zata
amshi Zancensa, hakan ya sa Yahai ya bashi
shawara da ya bi ta hannun iyaye kawai.
Yasan dai yana da fada a wajen iyayenta
maza shi yasa ya fara da mahaifinta.
Bayan tafiyar su Abdoul ya ɗaga waya ya
kira Baffa. Nan ya ke faɗa musu zuwan
Abdoul da kuma yanda suka kwashe.
"shi Abdoul ɗin ne yazo wajenka?" Ya
tambaya cike da mamaki. Dariya yayi
sannan ya bashi amsa da cewa
"shi fa, ko minti uku basu yi da fita ba.
Ga ma tsarabar da ya kawo ma yara nan.
Yace zuwa Asabar kaga jibi kenan zai shigo
wajenku".
"Allah ya kaimu, yanzu muka dawo
asibiti Halima har oxygen aka sa mata da
muka isa, mun aza ma rai yayi halinsa sai
mommansu ta nace akan Halima bata rasu
ba. Amma Alhamdulillah har drip ɗin da
akasa an cire kafin in dawo. Ban kira ku ba
don bana son hankalin ku ya tashi ne"
hawayen da suka zubo masa ya goge don ya
san da Ace Halima ta rasu ko iyayenta baza
su kai shi rashin ta ba, in bai yi karya ba ai
cewa zaiyi ya fisu sanin wacece Halima da
darajan da Allah ya bata. Samun irinta sai
an tona.
"Allah ya bata lafiya, gobe bayan
Jummu@ zamu zo mu duba ta, in kuma an
sallame ku shike nan" Ya faɗi bayan ya
gama tunanin anya a duniya akwai sauran
masu riko da zumunci irin yayansa.
"Toh shike nan, Allah ya baku iko, ya
sanya Alkhairi tsakanin ta Abdoul in babu ya
musanya mana" "kai baffa ba bu ko yar
kunyar nan. Yar farin ku ce fa kar ka bari a
ji kana kwararo addu'a fa" mahaifin Halima
ya tare shi da tsokana, nan sukayi dariya.
***
Ko da su Abdoul suka isa gida Agaysha ta
dawo tayi yan birne birnenta wanda aka
tabbatar mata da in har Abdoul ya shigo
gidan toh sai yanda tayi dashi. Suna gab da
shiga gidan Yahai ya ja shi gefe yace
"karanta addu'ar shiga gida haɗe da suratul
ahad, ba wani jinsi na shaiɗan da zai
kasance tare da kai. Kayi sallama kuma tun
daga bakin kofa kar ma Ace sun rako ka
zuwa bakin falo. Ire iren sakacin nan ke sa
tsafi yai tasiri a gidan mutum. Rashin yin
addu'ar fita gida da shigowa "
Ba musu ya karanta, suka shiga da
sallama. A ciki ta amsa tana yatsine
fuskanta kamar taga kashi. Cikin tsawa ta ce
" Daga ina kake na dawo baka nan" Ta
tambaya kamar wani ɗan ta da take shirin
mazga.
"Gida na ya zo fa gashi na kawo miki shi
har gida, dafatan banyi laifi ba" Yahai yai
saurin amsa mata don ya san kaidinta,
Allah kaɗai yasan tsafin da tayi.
"Auho! Kasan akwai wata karuwa da take
neman rusa mana zaman lafiya a gidanmu,
wallahi na aza wurinta ya je don yau da
asuba sunanta ya tashi da shi a baki, tsoron
zuwansa wajenta na bashi maganin barci a
tea, kasan abinda ya ban mamaki" Ta
karasa tana jefa ma Yahai tambaya, dama
ita haka take da son nuna isa, in tayi abu
gani take wayonta ne ya kaita ga hakan.
"Sai kin faɗa madam"
"ko da na fita kuka yake yana kiran
Halima ta rasu, tsakanin ka da Allah ko a
littafi ka taɓa karanta mutum na barci yana
mafarki Alhali barcin magani ne, nayi
Alkawari sai na hukunta yarinyar nan, duk
tsafinta sai na hukunta ta" Ta karasa tana
kara yamutsa fuska kamar Halima ne a
wajen.
"gaskiya shi yasa na gagara yarda da ita,
a sani na ke kaɗai ce aboki na ke so,
kwatsam ya zo min da zancen wata Halima.
Allah raba nagari da mugu, mtsw! Mata
basa kyautawa wai takan namiji su siya wuta
da hannunsu, sai ki ji suna malam malam
yoh ko da ayar Kur'ani akai lakani dashi ai
bazai tashi da ga shirka ba. Annabi ya faɗi
su zasu fi yawa a wuta. Kuma ba komi bane
zai kai matan zamanin nan wuta sai son
mallake ɗa namiji. Allah ya shirye ta da
sauran masu yi "
Fuuuuu! Ta shige ɗaki ba tare da ta
amsa aameen din ba. Nan ya ja Abdoul
kofar gida suka tsara yanda komi zai
kasance. Ya kara nanata masa kar ya yarda
tasan aikinta bai ci ba, tunda hutun sa ma
ya kare, ya lallaɓa ta kafin ya wuce.
What will you say about this chapter?
Hop u are happy dt Halima is still
alive....
Thnx for bn there happy reading as I will
b happy seeing u voting and
commenting...
Luff yhuuhhhhGoma Magogin Karfe
686 79 12
by Ummu-abdoul
Ranar Asabar tun da safe Abdoul ya shirya
ma tafiya. Karfe tara Yahai ya iso suka ɗauki
hanyar Niamey. Duk kayan marmarin da
suka gitta mawa sai sun tsaya sun siya.
Sannu a hankali suka isa, hiran da ya ɗau
hankalinsu yasa basu ga wani nisan tafiyar
ba.
Sun isa sun taradda an sallame Halima
har ta dan warware. A falon Baffa aka
sauke su inda shi ya fara tarbonsu kafin
kowa. Bayan sun gaisa ne ya kalle su yace
"ko zan san me ke tafe da ku?"
Duk da sunyi mamakin tarbon arziki da
suka samu, amma basu yi tunanin zai jefe
su da wannan tambayar ba. Sunkuyar da ka
Abdoul yayi sai Yahai ne ma da yayi karfin
halin tattaro natsuwarsa ya ce
"Baffa mun zo neman izinin ka ne, don
neman auren Halima"
Shiru ya sake ratsa wajen. Zukatansu nai
musu ki ɗan lugude don basu san ko zai
amince ba.
"Ba zan ce komi ba sai Halima ta faɗi
ra'ayin ta, in ka samu ta amince ka
gaggauta turo min waliyanka, in kuwa bata
amince ba ina rokon ka arziki kar ka sake
zuwa min gida, na barku lafiya" yana kai
aya ya tashi ya shige gida.
Sun zauna ma kamar minti goma sai ga
Halima ta shigo da kawarta Shamsiyya
Ummu A, fuskarta a sake, amma ko kallon
ɓarayin Abdoul bata yi ba. Hankalinta gaba
ɗaya ta ba Yahai. Sun gaishe shi, sai
shamsiyya ta kalli Abdoul ta ce
"ɗa na! Fatan dai kana lafiya" da
murmushi mai nuna tsantsan farin cikin an
san da zamansa ya ce
"Mommy ina fa lafiya, nayi zunubi mai
girma, don Allah ki sa baki a yafe min
kinji" Ya faɗi yana marairaice fuska.
Jin duk sunyi shiru ya sa ya fara basu
labarin duk abinda ya faru da ya koma gida
har zuwa mafarkansa da yayi masu ban
al'ajabi.
Shamsiyya dai da ka kalle ta kasan ta na
cike da tausayin sa yayin da Halima tayi ko
oho, ganin sun tsare ta da kallo ne alamun
suna son ji daga gareta ne ta muskuta ta ce
"Abdoul mafarki ba gaskiya bane, Allah ne
yake aikowa bawa wasu lamarika daga cikin
buwayarsa, domin ya haskaka masa wata
baiwa tashi wadda zai gane rayuwa da
abinda yake cikinta....
Idan bawa yayi mafarki mai dadi kona
ra'ayinsa sai yayi Sadaka kamar yadda yazo
a hadisi Majma'ul Bahraini cewar "Annabi
yace kunemi yayewar bakin ciki, da bacin
rai wajan yin Sadaka " hardai zuwa karshen
hadisin, shiyasa akeso bawa ya kasance mai
yawan addu'a aduk lokacin dazai kwanta
barci, sbd yanayin mafarkin dazai iyayi, idan
mai dadine sai yafadama mafi kusanci dashi
kuma abokin sirri agareshi amin domin
yatayashi rokon Allah nake alheri akan
mafarkin.
Idan kuma mafarkin abin tsorone kokuma
tashin hankali wanda zai haifar da bacin rai,
ana so kana farkawa ka nemi tsari ka tofa
ɓarayin hagu sannan ka chanza kwanciya,
shima dai mutum sai yayi Sadaka yanemi
tsari akan abinda yagani acikinsa, yanemi
kuma zabin Allah na alheri akan mafarkin,
yazama mai sirri akansa wajan barwa
cikinsa sirrin mafarkin, tosai Allah yaji
tausayinsa kuma yayi imani tare da
tawassali da Annabi wajan zabin alherinsa.
Wannan bayani kadan kenan daga cikin
abubuwan da Mafarki yakunsa, Allah yasa
mudace da rabo mai amfani adukkan
rayuwarmu Amin. " tana kaiwa nan ta tashi
tsam sai zuwa cikin gida. Dukkansu ba
wanda kansa bai ɗaure ba don a zahiri sun
ga tsantsan rashin bawa lamarin
mahimmanci.
Sunyi zugum na wasu yan mintoci chan
shamsiyya tayi karfin halin magana inda ta
ce
"Kun san ba lafiya ta cika ba, jiya aka
sallamo ta daga asibiti, mu ɗan ɗaga mata
kafa. Ɗa na kasan dai kai me laifi ne sai ka
san yanda zakayi ka wanke kanka" Duk
sukai dariya sannan suka tambaye ta jikin
Halima inda ta amsa musu da taji sauki
sosai. Sun ɗan taɓa hira kafin daga bisani
sukai sallama suka tafi.
Wasa wasa se da akayi wata biyu Abdoul
na zaryan neman sulhu amma Halima ta
kafe akan ba'a haifi namijin da zai
wulakanta ta ba, nan ta maida hankali a
aikinta ba ta saurari zancen ba.
Yanzu ma zaune take ya zo, momma ta
kora ta dole taje gare shi, tsayuwa tayi a
kan shi, bata ce masa komi ba. Kiran da
taga ya shigo wayarta ne ya hana mata cewa
komi don niyyar ta kwance masa rashin
mutunci . Ɗaga wayar tayi da sallama.
Maimakon a amsa sallama sai saukar ashar
taji, neman tsari take da ga sheɗan. Faɗin
da tayi "Abdoul yafi karfin ki jaka" nan ta
fahimci wacece kuma.
Shiru tayi ma wasu dakiku sannan ta ce
"kin kira a sa'a ma, tun ɗazu ya ke jira
na fitowar kenan se ga kiranki, gashi ku
gaisa" Ta karasa tana mai mika masa wayar
fuskarta cike da murmushi.
"macuci, azzalumi, annamimi, wallahi
in baka tuba ba wutan Allah sai ya ci ka" Ta
faɗi tana haki bayan muryarsa ya sauka a
dodon kunninta.
Murmushi kawai ya saki ya katse kiran
tare da kashe wayar gaba ɗaya.
"bani wayata, meye nufin ka na kashe
min wayar gaba ɗaya" Ta faɗi a tsiwace,
kallonta yake yana so idanuwar su su haɗu
amma fir ta ki.
"Ki zauna, magana nake so mu yi" Ya ce
yana nuna mata kujera. Zama tayi babu
gardama.
"Halima, L'erreur est humaine, (ko wani
mutum na tare da kuskure) ki yi hakuri s'il
vous plaît Il faut me pardonner. (don Allah
ki yafe min)" Ya faɗi yana rusunawa. Ganin
tayi shiru ya sa ya cigaba
"Nasan ba a son rai mafi yawa daga
cikin mata ke auren mijin aure ba, burin
kowacce mace ta kasance uwar gida, amma
ina zamu kai kaddarar rayukanmu. Allah ya
faɗi a cikin littafi mai tsarki LIKULLI AJALIN
KITAAB, wato ko wani kaddara a rubuce ta
ke.
Ba wai zan aure ki don in cikata giɓin da
nake da shi a gida na ba, kin san dai ina son
matata, toh ba wai zan aure ki don son
nata ya ragu bane, sonki da kaunarki yasa
nai sha'awar aurenki, don in yi bautan Allah
in nemi yardansa. Bayan wannan banda
wani dalili.
Bana so in miki karya shiyasa kika ga nayi
shiru akan zancen laifin da nayi Il faut me
pardonner." tsare ta yayi da idanu, burinsa
su haɗa ido amma fir ta ki yarda.
Shiru sukayi na kusan minti biyar,
zuciyar ta na rawa kamar pendulum, chan
dai ta tuna isa da mulki da Agaysha ke
Gwadawa akan Abdoul na ta ne ita kaɗai
yasa ta tsaida zuciyarta ta ce kamar bazata
magantu ba
"ka turo ayi magana" Ta na faɗi ta shige
cikin gida. Murna a tare da shi ba'a
magana, sai da ya kira baffanunsa suka
tsaida masa da ranar da zasu je sannan ya
bar falon da aka sauke sa.
Itama da ta shiga ciki ta faɗa ma
momma abinda ta yanke ta ji daɗi sosai.
Nan suka yi addu'ar Alkhairi amma
kowannensu zuciyar sa kal da murna.
***
Kamar yanda suka yi alkawari haka suka zo
da zancen neman aurenta. Iyayensa sun
yaba da karamci da halin girma iri na
iyayen Halima. An tsaida auren bayan wata
uku kamar yanda Halima ta roka sanda
momma ta tambaye ta.
Tun da lokacin wani sabon shaukin
kaunar juna ya shiga tsakaninsu. In baya
gari ko Kasar suna manne da juna a waya.
Agaysha tayi asirin, tayi tsafin amma
kullum lokacin bikin matsuwa yake duk da
bokanta ya tabbatar mata baza'a taɓa auren
ba.
Yau ma ta shirya zuwa maraɗi don ganin
wani boka, sarkarta da ammbasadan Nijar
a Saudiyya ya ba Abdoul ne ta siyar, tayi
karyan zuwa ta'aziyya ta ɗau hanyar maraɗi.
Sanda layi ya kai kanta ta shiga don ganin
sa. Kallo ɗaya yayi mata ya kwaɗaitu da
ita. Nan ya ce mata
"Halima ba ko mi bace face abin da zai
kawata MAFARKIN ABDOUL, yanzu dai ɗan
tsatsuba ya na son ya ji kalan ruwanki, da
shi zai halaka Halima"
" Ruwa kuma.! ya mai biyan bukatu" Ta
tambaya cikin rashin fahimta.
"eh! Kwaye min wannan zanin in ɗiba"
ba musu ta Kwaye, ta tsorata da ya cire
zanin da ya ɗaura a kugu amma zuciyar ta
da ta tuna mata shike nan kafin ta koma an
hallaka Halima da auren saura mako ɗaya
ya sa ta sakin jiki.
A wahale ta fito runbun boka ta sa mu
abin hawa, Gidan kawarta Taghayshuwane
ta je, nan ta huta washe gari ta koma
zindar.
Shiru! Shiru tana jiran a ce mata an fasa
aure amma sai shirye shirye ake, ta kira
boka yace shi dai yasan baza'a yi auren nan
ba, ta kwantar da hankalinta ko an taru za'a
fasa. Hakan yasa ta ji sakayau fatanta a
fasa ranar ɗaurin aure don zai fi musu zafi.
BIKI BIDIRI ....
Karfe goma na safen 13 ga watan febweru
2016 a Nijar, Nijeriya, Kamaru da Chadi
aka ɗaura Auren Abdoullah da Halima bisa
ga sadaki mafi karanci.
Anyi shagulgula sosai inda mawakiya Sa'a
Vocal ta wake ango da amarya. Hanifa
creations and couture suka fito da amarya
da ango da zafafan ɗinkuna inda mutane
sukai ta santi.
Ranar Lahadi da safe aka yi walima a
gidan ta da ya kama mata a nan Niamey.
Agaysha bata yarda da an ɗaura auren ba
sai da aka kai amarya gidan iyayen mijinsu
da maraice sannan taga sun dau hanyar
Niamey. Nan ta ɗau waya ta aika ma
Abdoul sako kamar haka
"Ango mijin Amarya, ina maka
murna, na ba ka wata uku kyauta kasha
amarci lafiya"
ko da ya karanta sai da yai dariya a ransa
cewa yake "wannan bata san abinda ke
damunta ba" nuna ma Yahai wayar yayi ya
karanta.
"mtswww ! Wasu matan fa na kwafsawa,
akan wani dalili zaki bar ma wata mijinki
wata kawai don ya auro ta da yaudaran kai
zata ginshe shi. In kaga an ginshi juna
amaryar bata iya takunta bane. Ai ta baku
daman fahimtar juna a ne amarya kuma ta
kafa gwamnatin ta da kyau. Aminina kasha
amarci lafiya" Ya karasa suna masu tafawa.
How una dey?
Op una dey enjoy am well well
May Allah albarkatize una eyes make
una read well nd ur hands make una
vote nd comment. Luv u wolla😍😙😘😚😗
Cikan Mafarki
800 58 20
by Ummu-abdoul
An watse taro Lafiya yan Uwa sun koma
gidajensu lafiya lau sai addu'an zaman
lafiya da aka bi maauratan dashi. Ɓangaren
Agaysha kuwa kawayenta na nuna mata
gara da tayi hakan kafin wata ukun ya wuce
za'a tura mata warin jaɓa da ɓallewan jini.
Haka dai sukayi ta shawara har dare ya
tsaga.
Washe gari ma haka sukai ta bata
shawaran da suke ganin zai fishe su, kafin
suka watse aka barta da kunan zuciya.
Mafarkin ido biyu ta yini tana yi, idonta na
hasko mata Abdoul ɗinta da Halima. Tayi
kuka kashi kashi, ta yini tana tsine ma
bokayen da sukayi mata aiki, barinma
wanda ta ba jikinta.
Kamar an muntsile ta, wayarta ta ɗauko
ta kira shi don ta ci masa mutunci. Ringing
biyu ya ɗaga.
"mace mai garɗi Uwargidan Abdoul kina
lafiya" Ya faɗa yana kasa da murya, hakan
bai hana ta jin kaurin muryar kamar saukar
aradu.
"kasan kuwa an ɗaura auren" abinda
bakinta ya iya furtawa kenan.
"Kinsa kokwanto, baki bada gaskiya akan
zan iya hana auren ba. Aiki da kokonto ai
ba zai taɓa karɓa ba." Ya faɗi daga chan
ɓarayin.
"Kokwanto kuma?" Ta tambaya tana
zare idanu kamar yana ganin ta.
"Eh! Ai da kin mika gaskiya, kin
amince zan iya yin komi duk da ba haka ba.
Amma bai yi latti ba, ki samu ki zo sai a
tura mata cuta wanda zai kar da ita har
lahira." jin hakan ya

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment