Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inda yake kara hura mata
wutan sonshi a ranta. Chan dai ta ɗaure ta
tura "inaama! Inaama!" Yana gani ya tashi
zaune, sannan ya kira ta. Ringing biyu ta
ɗaya da sallama.
"me kike cewa ne Halima ɗazu" addu'a
yake ta faɗi abinda ranshi ke son ji.
" cewa nayi inaama! Inaama MAFARKIN
ABDOUL zai tabbata. Da an samu maaurata
gwanaye da zasu sadaukar da rayuwar su
wajen faranta ma juna" Ta faɗa bil hakki
abinda ke ranta kenan. Ya daɗe da sanin
Halima irin mutanen da masana psychology
kan kirasu da extrovert ne, sam bata ɓoye
ra'ayinta akan abu, ya daɗe yana jinjina
mata ɓoye soyayyar sa dake zuciyarta, ko
da yake matantakanta ya taimaka mata
ainun wajen ɓoyewa.
"Halima kina da matukar mahimmanci a
rayuwata, in na koma zindar karshen sati,
zanyi magana da mama da Maman Ummu
akan auren mu, fata na kar su kawo
matsala, shekara mai kamawa zamu
tabbatar da MAFARKIN ABDOUL, sai in
kama miki gida a nan Niamey ko ya kika ce"
mamaki ya cikata, wannan sai kace jira
yake ta furta.
"Amma wannan assurance ɗin da kayi
min anya beyi wuri ba, bana son abinda zai
taɓa alakarmu fa, kasan ban iya son abu ba,
ina sonka da yawa Abdoul" Ta furta a
sanyaye wanda hakan yasa yaji tausayin ta
ya mamaye shi.
" kar ki damu ina tare da ke insha Allah
ba gudu ba ja da baya" da haka suka
dulmiya duniyar soyayya ba ji ba gani. Wasu
kalaman in ya furta mata har mamaki
takeyi da ma chan yana sonta ne. Da kyar
sukayi sallama bayan sun tsara yanda zai
nemi aurenta da kuma yanda aurensu zai
kasance.
Cikin watanni biyu sun shaku sosai fiye
da wanda sukayi a baya. Kulan da suke ba
junansu abin ba'a magana, ko da yaushe
suna nane da juna walau a Chat ko a waya.
Cikin tsarinsu ne bazata faɗa ma kowa ba
har se yaje yayi magana da iyayensa in sun
tashi zuwa neman aurenta. Duk yanda yaso
zuwa aiki ya hana shi motsi kasancewar ya
fara aiki da Ministère des Affaires
Étrangères et de la Coopération ( Nigerien
Ministry of Foreign Affairs and
Cooperation) hakan yasa ya kan bi tawagar
da ke zuwa duba République Niger
ambassade na sauran kasashe. Yanayin
rashin zama yasa bai tafi da Agaysha ba
amma wani sa'in musamman in yara na
hutu sukan je a tare.
Naso yafi haka but abeg pls ejor don
Allah kuyi hakuri da wannan. Thanx for
always bn there 😍
Mutuwa Karan Kwana
715 54 7
by Ummu-abdoul
Soyayya suke mai cike da tsafta, har yanda
aurensu zai kasance sunyi, wani zuwansu
Abuja a tarayyan Nigeria ya siya yadin
material ya bada a Hanifa boutique ya ba
da a ɗinka bridal gown a Hanifa creations &
couture da ke lamba ta 10, Gimbiya Street
area 11, garki Abuja. Tun da ya kai yake
manta santin ɗinkin. Don sai da ya ba mai
wajen haj. Hadiza shawara in da hali ta
buɗe musu a Nijar ko suma zasu ci romon
ɗinki hadaddu. Dariya tayi tace " me zai
hana, Nijar da Nijeriya ai duk ɗaya suke,
zamu duba se a buɗe a Niamey in de zaku
kawo ɗinki".
Yini yayi yana faɗa ma Halima karamcin
su tun daga siyan material har ɗinki
fatansa su cika masa alkawari. Halima bata
tabbatar da haɗuwan dinkin su ba sai da ta
leka shafinsu na Instagram, rudewa tayi
tana nuna ma momma haj mas'uda, faɗi
take "momma anya bazamu aika sauran
ɗinku nan ba, ɗinki sunyi kyau" itama dai
haj mas'uda ta yaba da kyawun dinkin har
tayi shaawar aika ma kawarta haj.
Maijidda dake birnin Kano in za'a samu
wanda ze kai tunda suna home delivery a
Nijeriya. Hakan kuwa sukayi sanda Abdoul
ya tabbatar masu da cika alkawarin su. Sai
akayi da Abdoul ya karbo tunda za'a
kammala kafin su dawo Nijar.
Bata tsaya ba sai da tayi booking
kwalliyar da za'a mata wajen ramat
makeover, sannan ta bada aikin waka wajen
mai zazzakar murya da amon muryarta yafi
zuma daɗi wato sa'a Vocal.
"wai ke iyayensa basu zo ba duk kun
gama shiri ko dai ku zaku aurar da kanku
ne," faɗin haj mas'uda da ta fada mata ta
yi booking wakar sa'a Vocal, da irin
karamcin da sa'a tayi mata da ta kira ta a
waya.
"momma kinsan yace January yake so
ayi, da sunzo za'a yi komi gaba ɗaya" Ta
faɗi tana rufe ido.
"Au! Wai dama kina da kunya, bayan
ina ganin kosawa a tare da ke." itama ta
faɗi tana dariya.
"momma shekaru na fa ashirin da biyar,
kinga kenan ai na tsufa, ko" dukan da aka
kai ma cinyarta yasa ta yin shiru.
"Toh shi ɗin kin tabbatar da ya isa da
iyalinsa? Kuma baza'a samu matsala ba,
kin san maza in har basu isa da matansu ba
aurensu matsala ne. Ki cigaba da addu'a
de, in Alkhairi ne Allah ya tabbatar, in
babu ya zaɓa miki abinda yafi alkhairi"
Jikinta yayi sanyi, yaushe rabon da tayi
addu'a, a ganinta ai shi ne alkhairi tunda ya
zo bayan rabuwanta da Hammad. Haka dai
ta fara istigfari tun daga zaune. Ranar itace
har da tsayuwar dare.
Dawowannan Abdoul ya sa ta farin ciki
da annashuwa, gani kawai aurensu ya zo.
Bayan ya aje musu sakon ɗinki ya dauki
hutu ya wuce zindar. Nan ma ya samu tarbo
mai kyau daga Agaysha.
Sai da ya kwana biyu sannan ya fara mata
Maganar wata rana suna hira
"Madam aure nake son yi, ba don bana
sonki ba sai don gazawarki wajen kula dani,
ina sonki, banda niyyar kara aure amma
yanda kike tafiyar dani yasa har shakuwar
mu tayi karfi da Halima tace tana so na,
kuma nayi niyyar aurenta" Ya faɗi kai
tsaye. Kuka sosai ta fara, ganin yayi shiru
yasa ta cakume masa wuyar rigarsa tana
ihu tana kuka
"kaci amanata, Halima ta munafunce ni,
tayi ta ban shawara ashe sonka takeyi toh
wallahi baka isa ba, zan kai karanka wajen
baba don wallahi bazan yarda ba, ka gama
zubar min da mutunci a idonta sannan kace
zaka aure ta" rungumar ta yayi yana bata
hakuri.
Rigima taki ci taki cinyewa, kuka
Agaysha takeyi ta ki cin wani abinci, tayi
baki ta rame, yaranta ko wanka bata
musu, ya bada hakurin taki, har sai da ta
tsare shi ya kira Halima.
Ringing yake Halima na kallo taki dagawa
don takaicin tunda ya koma ko WhatsApp
yaki hawa, bai dauki wayarta ba haka bai
kira ta ba..
Sai da yayi kira uku sannan ta ɗauka da
fara'arta ta gaisheshi, a dakile ya amsa
sannan yace
"Na kira ki ne in baki hakuri, sannan in
faɗa miki bazan iya aurenki ba, tunda na
faɗa ma Maman Ummu abiha zancen auren
gida na ya koma sansanin rigima, matsalar
gida na yasa nayi tunanin kara aure kuma ta
min alqawarin canzawa, kiyi hakuri ki
jingine zancen soyayya tsakaninmu".
Saurin tare shi tayi tana mai kuka "kar
ka min haka, ina sonka zan jira ka har zuwa
sanda zaka shirya amma don Allah kada ka
rabu da ni" kuka take Bil hakki.
"kinga Halima matata ta ishe ni bazan iya
ba nace, ko ana dole, mtswww" Ya
karashe da jan tsaki kana ya kashe wayar.
Tun daga ranar bai sake ɗaga wayar
Halima ba, Agaysha kuwa hadiye shi ne
batayi ba saboda kula. Tarairayan da yasa ya
manta wata Halima a doran duniya.
A ɓangaren Halima tun tana ganin abin
wasa, taga har anyi sati ba kiranshi ba
alamun shi yasa ta kira amininsa Yahai
Bayan sun gaisa ta faɗa masa duk
abinda ya faru ta kara da faɗin
"ka bashi hakuri in laifi na masa, duk
Dokan da zai sa min na yarda in dai zai aure
ni, don Allah ka taimaka min."
"shike nan Halima, yanzu haka yana
hanya munyi alkawari zamu haɗu, zan kira
ki yayinda nake masa maganar don ki ji
komi daga gareshi" godiya tayi ta zuba
masa kamar yai mata bishara da Aljanna.
Ba'a yi awa ɗaya ba kuwa sai ga kiran
Yahai, da saurinta ta ɗaga tayi shiru tana ji
Yahai yace
"wai ni Abdoul ina Halima ne ya
zancenku ya kwana"
"mtsw! Tana chan, ni bazan kara aure ba
ina son zaman lafiyan gida na, tunda na
faɗa mata ban sake neman ta ba"
" ko dai ka gano wani mugun halinta ne,
yanzu kake neman rabuwa da ita? " Yahai
ya sake tambaya
"kasan in da banyi aure ba babu abinda
zai hana aje Halima a matsayin mata,
rigima ce dai banso. In kana so kuma Allah
sanya Alkhairi".
Mamaki da takaici ya cika Halima, ta yi
saurin katse wayar kafin taji abinda zai ɓata
mata rai.
Tsam ta tashi ta je ta faɗa ma momma
abinda ke faruwa, mamaki ya cika ta kwarai
amma ta bata hakuri haɗe da nasiha akan
addu'ar su ya karɓu Abdoul ba Alkhairi
bane a gare ta.
***
A kwana a tashi Halima ta zama wata mara
fara'a, kallon ko wani namiji a matsayin
mayaudari take in akai mata magana tace
tunda Abdoul yayi kowa ma zeyi.
Wata rana kawarta faɗima ta zo gidan
momma kamar yanda ta saba kawo mata
ziyara. Suna cikin hira tace
"wai dama Agaysha Iggalher ce matar
Abdoul?"
"Eh! Ina kika Santa?" itama ta tambaya.
"kin san kanwar miji na ke auren
babanta, da kyar uwar ta yarda akayi, jiya
muka haɗu a gidan da yake ita ayshatou din
ta haihu, Shine fa take nuna hotonki wai
kin nace ma mijinta kina son shi har tana
muyi kafa kafa da mazajenmu kwacen miji
ki keyi " kukan da Halima ta fara yasa yin
shiru. Ta fara bata baki tana cewa
" bafa na faɗa miki don ki bata ranki bane,
ina so dai ki yi aurenki ki huta sa surutunta,
don ta ɗauki alwashin sai ta hukunta ki"
"Ta ya zata hukunta ni, asiri ko tsafi bazai
taɓa kama ni ba don na rike addu'ar da
manzo SAW yace mu rike ma kariya. Manta
da ita kinji yar uwa, jiya na dawo daga
zindar fa" haliman ta karasa tana mai
chanza hiran.
Bayan magriba ta dauki waya ta kira
Abdoul, sun gaisa kamar da ya tambaye ta
mutan gida, itama haka. Chan ta ce
"Na kira ka ne in ce ka ja ma matar ka
kunni, babu abinda zanyi da mijinta, tun
tana kira na tana zagi na ban tanka mata ba,
har ya kai zata dinga yawo da hoto na da
guntuwar wasikar da ban san da zamansa ba
wai na rubuto maka, ai laifin ba nawa bane
naka ne mijinta. Don Allah ku fita harkata
nima daga yau na fita naku"
"kinga bazaki zo ki ma mata na sharri ba,
kuma Allah ya saka mata, aure ne dai nace
banyi ko dole ne" Ya katse ta a fusace,
"in da ina bin ta da sharri kasan da tuni
na barka ka saketa ko, ko ka manta sirrin
gidan ka yayi zama hannuna, Allah bamu
Alkhairi" Ta kashe wayar gaba daya ta
sallaci isha'i wani farin ciki take ji ta rasa
na menene, hatta yan gidan sun kula don
sai da baffa ya ce mata
"Halima Albishir ɗin Aljanna akai miki?"
Tayi dariya tace
"kusan haka ne fa, kasan an ce budurwa in
bata taɓa zina ba ta rasu tayi shahada da
ladan jihadul Nafs. Ko dai zancen mutane
ne baffa? " Ta tambayeshi tana dariya.
" se kinga auren jikokinki Halima, Allah sa
jinkirinki alkhairi ne " momma ta katse
musu.
" Allah dai yasa in tafi a sa'a, momma bata
so in tafi, se hakuri in lokaci yayi" Ta faɗi
tana dariya
Haka sukai hira har goma da rabi sannan tai
musu sallama ta je kwanciya
Kwanciyar ta ke da wuya ta fara ciwon
ciki, da kyar ta daga waya ta kira momma,
a ruɗe ta shigo ta iske ta cikin amai cikin na
murɗa mata.
Cirko Cirko sukai akanta, bayan cikin ya
lafa, faɗi take "ku yafe min, kuce su mama
su yafe min, na yafe ma kowa"
"ciwo ba mutuwa ba ai kinji sauki, sannu
halima" kawai suke cewa.
Huɗu da minti arba'in cikin ya sake
motsawa, wannan karan tana wani irin mika
in ya rike ta. Ɗaukan ta sukai zuwa mota
don kaita asibiti basu san sun kai ta ga
ajalinta bane. Daidai kwanar fita
anguwansu tayi wani mika haɗe da salati,
shike nan ta amsa kiran ubangiji.
"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun" kawai
baffa ke faɗi. Hajiya mas'uda kuwa
mutuwar zaune tayi. Hawaye na gasar
tsere a fuskarta.
NADAMA
659 52 7
by Ummu-abdoul
NADAMA....
Tunda ya sauke wayar jikinsa yai masa
sanyi. Anya ya kyauta mata kuwa, yarinyar
da ke ɗaukan shi mai babban daraja ya
yankuna haka. Shiru yayi kalamanta na
dawo masa ɗaya bayan ɗaya.
"wai me yasa ake ɗaukan maza masu
mata mayaudara ne, duk wanda nace ma
kai zan aura sai sun ce Allah sa kar kayi min
halin, in dai aje wani spare, tunda soyayya
ba mota bace meye amfanin tara samari"
Ta faɗa masa wata rana suna waya.
"Ni dai ba yaudaranki zanyi ba. In kinga
ba mu yi auren nan ba mutuwa ce, kece fa
mafarki na kece tunani na a farke" sai da
yaji kunyar kansa da ya tuna alwashinsa
gare ta.
"momma cewa tayi ba komi ya sa maza
masu aure iya yaudara ba sai ganin suna da
matan su a gida, ba su da halin karin aure
amma su je suna kwadayin soyayya da
wasu, basa ko la'akari da suna da yaya mata
ana iya musu suma. Wasu kuma ba laifinsu
bane matan su ke hana su aure, su ma
basa tunanin mazajensu na iya mutuwa ko
su rabu wani mara matan ne zai aure su, ai
aure kanta wa'adi gareta ban ga abin tashin
hankali akai ba"
"lafiya ka zauna kana tunanu" Agaysha ta
katse masa tunaninsa nan de ya zauna
sukuku har lokacin barci yayi ya kwanta.
***
Sanye take cikin shiga mai kyau, kyallin da
tufan jikinta ke fitarwa kaɗai abin kashe ido
ne, babu wani al'auranta da ke waje,
fuskarta cike yake da murmushi.
"Abdoul kaga ɗaukakan da Allah yai min
ko, ka gafarce ni in na saɓa maka amma na
tafi bazan sake damunka ba" Ta na faɗin
haka ta fara tafiya, taurari sun kewaye ta,
haske ya bayyana, kamshi ta ko ina.
"Halima! Halimaaaa! Halimaaaa!" yake
faɗi iya karfinsa wanda ya tada Halima daga
barci. Kallon agogo yayi karfe biyar na
asuba ya tashi ya ɗauro alwala nan ya fara
jero nafilfili kasancewa biyar da rabi ake
kiran sallah.
Tunani yake dole ya je Niamey su
sasanta kansu bazai ma Halima haka ba,
bata chanchanci abinda yai mata ba, ai
Halima matar alfahari ce, wacce Burinta
tayi aure tayi Ibadan da zai zama sanadin
shigar ta Aljanna.
Yana fita Agaysha ta kira kawarta da ke
mata rakiya zuwa gidan malamin da ke
mata aiki akan zasu je, Abdoul ya tashi
cikin dare yana kiran sunan Halima.
Ko da ya dawo sallah yayi mamaki da
bata tsare shi da masifa ba, illa hillatarsa
da tayi ta yi har ya shagala. In bayan sun
samu nutsuwa take faɗa ma sa zai kai ta
gidan kawarta zasu je ta'aziyya, ba gardama
ya amince.
Karfe goma sha biyu suka bar gida ya
sauke ta sannan ya karasa share zamna don
ya samu sallar Jumma'a a Grande Mosque
de Zinder. Bayan an iddar da sallah ne aka
bada sanarwan za'ayi sallan jana'iza, na
wata baiwar Allah da ta rasu. Haka kawai
yaji tsoro ya shige shi. Bai gama jawo
natsuwa ba idonsa ya kai ga baffa, da
mahaifin Halima suna share kwalla. Kallon
zanin da aka rufe ta yayi in bai manta ba
yana daya daga cikin ɗinkunan da ya amso
masu har yana mata tsiyar tayi zani plane.
Se da ya sa ma zuciyar sa mahaifiyarta ce
ta rasu sannan ya samu natsuwar tashi ayi
sallan da shi. An idar haka yabi tawagar
farko, ya kula da yanda mahaifinta ya
rushe da kuka sanda suka yi ido hudu
dashi. A harabar masallacin aka shigo da
hillux aka shimfiɗe gawar. Yana ta kallon
mutane ɗai ɗai, ga yan uwanta mata daga
sashin mata na masallacin. Da kyar ya shiga
motarsa, inda wasu yan anguwan su
haliman suka cika motar. A hankali akai ta
tuka motar har makabarta inda an riga an
gine mata lahda ɗinta. Ko a nan sai da
mahaifin Halima ya jawo shi, yayin da ake
maida kasan da zai rufe ta.
Suna nan tsaye bayan an rufe ba ma
kusan minti arba'in suna mata addu'a
kamar yanda manzo SAW ya umurce mu
kar muyi saurin barin makabarta yayinda
muka rufe wani namu.
Har suka fito babu wanda yace uffan, ya
kula da Muguwar kallon da baffa ke jifan shi
da shi, yayin da mahaifin Halima ke masa
kallon tausayi. Sun fito gate din makabarta
kenan mahaifin Halima yace
"Abdoul ya hakurin mu, Halima kuma
wa'adi ya cika. Sai mu" be kai aya ba sai
ganinsa sukai a zube sumamme. Shafa
masa ruwa akai sannan aka sa shi a mota,
baffa ne ya ja motar suka dunguma zuwa
gida. Banda ajiyar zuciya babu abinda
Abdoul ke yi, ina ma zai farka daga barcin
nan.
Nasiha sosai suka haɗu sukai masa har
baffa da ke cike da jin haushin sa. Ya shiga
cikin gida yai musu ta'aziyya sannan ya
koma wajen maza. Shi dai zai kira kan shi
da mutum mutumi don motsin kirki
gagaransa yayi. Ya kasa yarda Halima ta
rasu.
***
Can su Agaysha sun gurfana gaban
malaminta, bayan duk surutanshi da shafe
shafensa yace
"Halima anyi ta ne kawai don ta kawata
MAFARKIN ABDOUL, sai de akwai wasu
yara a gaba da nake hange, kuma bana
tsammanin naki ne amma tabbas na Abdoul
ne, yanzu de za'a yanka bakin bunsuru ayi
rubutu dashi ki sha, kishiya sai ta abin
hawa ba dai mutum ba, " yana gama faɗi ta
aje masa cepa dubu talatin sannan suka
juya.
Ko da ta isa gida bata iske shi ba, nan
tsoro ya cika ta kardai ya je wajen Halima
ne.
Karfe tara da rabi ya shigo gidan da
sallama, a cikin ta amsa amma ganin
idanunsa jawur gashi yana jan kafafu wanda
shi ne abin da yafi tsana a rayuwa.
"lafiya abban ummu" Ta faɗi a firgice
tana taro shi, a zuciyarta fata take Ace an
ɗaura ma Halima aure amma se taji yace
"Allah yayi ma Halima rasuwa jiya da
dare"
"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, Allah
ya jikanta yasa ta huta. Wai hankali na
yanzu zai kwanta babu mai takurawa miji
na" dukan da ya fara mata ta ko ina ya sa
tayi shiru haɗe da shekawa ɗaki ta rufo
kofa don gani take mutuwar ta taɓa
kwakwalwar sa.
Nan shima ya zube yana mai sakin kuka,
abubuwa da dama yai ta dawo masa
dangane da soyayyar su da Halima.
Mai Hali
711 52 2
by Ummu-abdoul
Hey peeps! Here is ur share of my bday
cake. Ur wishes made my day so so
special.. Thnx once again 😍
I also appreciate ur votes and
comments, I hop u r enjoying every bit
of MAFARKIN ABDOUL. Ur votes always
make me feel special... Love u all 😍
Dashi akayi zaman makoki aka gama,
Agaysha ko a kwalar riganta don tunanin ta
Abdoul nata ne ita kaɗai. Duk da
walwalarsa ya zama tarihi ba don son da
yake ma Halima ko kuma don ya gagara
ɗaukan kaddara, A'a, ya kasa yafe ma
kansa rabuwa da Halima da yayi. Shin dama
bai shirya aure bane yaje ya fara neman
ta. Shi ma yana cikin jerin maza masu
yaudara kenan. Me yasa ya gaskata ma
Halima zancen da ake cewa maza masu
aure sun fi yaudara.
Mafi yawan lokutta ba laifinsu bane
tsoron fitina yake sawa su hakura, amma
ai Allah ya basu ikon yi me yasa ya biye ma
Agaysha har ya saɓa ma Halima, ya ci
amanar yardan da ta mishi, ya sa kafa ya ci
mata mutunci duk da girmama shi da take
yi. Me yasa tun farko ya amince zai aure ta
bayan yasan bai shirya kari ba. Anya
Halima ta yafe masa kuwa.
Da irin wannan tunanin ya shirya ya je
gidan baffa. Cikin sa'a ya same shi a gida.
Bayan sun gaisa sunyi ma juna ta'aziyya sai
kawai ya sa musu kuka, tun suna takaici har
ya dan soma basu tausayi. Basu hana shi ba
har sai da yayi mai isarwa sannan ya ce
"Halima ba ta yafe min ba ta tafi ta barni.
Na ɓata mata da yawa ban san da hakan ba
sai da lokaci ya kure min, fitinar Agaysha
ya sa na ki zuwa, ni kadai na san abinda na
fuskanta." Ya karasa yana sakin wani kukan
mai tsuma zuciyar mai saurare.
"Da ma chan ba sonta kake ba Abdoul
mu barshi a hakan kawai" faɗin momma
don ita da tana da hali zata murkushe shi
take ji.
"mu dai barshi a yana sonta ɗin, babu
sauran abinda za'a iyayi se dai hakuri.
Halima kafin ta rasu sai da ta furta yafiya
ga kowa. Muyi fatan inda take tafi nan da ta
bari, in da rabo ai ss ku kasance a
Aljanna," kuka dai Abdoul ya cigaba, nan
Baffa ya zauna yayi ta bashi baki, nasiha
yake masa mai shiga jiki sannan ya rufe da
addu'a.
***
2016...
A kwana a tashi ba wuya wajen Allah,
shekaran Halima ɗaya da rasuwa. Kullum
kwanan duniya sai Abdoul ya bi ta da addu'a
wani zubin har da sadaka da azumin nafila
da niyyar Allah ya kai ladan zuwa gareta.
Agaysha tun da ta buɗe idanu ta tabbatar
da gaske Halima ta rasu ta chanza salon
rayuwar aurenta duk wani nau'i na kula da
take ma Abdoul ta janye. Bata kyashin
zaginsa ko ci masa mutunci ko a gaban
wanene. Ta kanyi amfani da kuɗin da
dangin mahaifiyarta ke dashi tayi ma
danginsa gorin arziki.
Irin haka ne ya faru yau, ya shigo ya iske
tana hira da kanninshi. Duk suka gaisa da
shi ita kuma ta yi kamar bata ganshi ba.
Har ya shiga ɗaki ganin minti goma bata
biyo shi ba yasa ya dawo falon ya same su.
"Madam me kika girka, zanyi baki wasu
Diplomate yan Nijeriya zasu zo" Ya faɗi
zuciyarsa na bugawa ɓat! ɓat! Kar ta kwaye
masa baya.
Ilai kuwa buɗan bakinta sai cewa tayi "
Au nom de Dieu il partir au restaurant le
plus près pour nous acheter à manger
(kasan Allah ka je Restaurant mafi kusa ka
sayo muku abinci) , don ko naka na ba
kanninka, ni na gaji ba abinda zanyi tun
safe nake aikin girki Haba!" ta karasa tana
murguɗa bakin ta.
Kallonta yake yanda ta jinɓire waje
ɗaya. Rigar sa mai tambarin wajen aikin su
ne ta sanya da zaninta. Shike nan don tana
da ciki ba zata yi ma kanta faɗa ta dinga
kwaliya ba, ko yaya ne ta yi shiga mai
kyau.
"kin san Allah babu abinda zai hanaki
girkin nan in ba so kike rayuka su ɓaci ba"
Ya faɗi yana haɗa fuska ko

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment