Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina sai ta
kai ga Agaysha tana huce kamar mai shirin
dambe.
"Zina kake min a kan gadonmu na
sunna" Ta faɗi hawaye na kwarara daga
idanunta.
"Zina kuma Agaysha" Ya faɗi a ruɗe, ko
dai abinda ya ke tunanin a mafarki ne a
gaske abin ya faru, amsar da ta bada ya
dawo da shi daga tunani.
"Ya zaka kwanta kana numfarfashi a cikin
barci, Allah ya isa tsakanina da Aljannar da
ke shiga gona ta. Don taga bana ganin ta,
kai kuma sai jin daɗi kake" Ta karasa tana
gunjin kuka.
Rungumo ta yayi yana tura mata sakonni
masu wuyan fassarawa, "mafarki nayi kina
shayar dani zumanki nefa ma femme
(matata)" da haka ya rufe bakinta. Bata
sake ɗaga zancen ba yayin da shi kuma ya
gagara cire shi a ransa.
* **
Zaune take tana kwalliya, murna ne fal a
cikinta don grand frère ɗinta Abdoul zai
kawo mata ziyara. Sanye take da riga da
skirt na material mai kaloli, ɗinkin ya fito
da surarta ya bayyana asirtaccen kyawun da
Allah ya mata.
Feshe jikinta tayi da turaruka fin kala
biyar, duk da kasancewarsu masu saukin
kuɗi sun fitar da kamshi mai daɗi da
kwantar da hankali.
Karfe biyu ya iso, kiranta yayi a waya
cewan ya iso, yayin da ita kuma ta zura
hijabinta purple kasancewar shine kala mafi
karanci a kayan.
Falon su tayi masa iso, wanda ke fitar
da sassanyar kamshin freshener irin na
Larabawa. Lumshe ido yayi sanda ya sa ka
fara guda a cikin falon. Kamshin da ya daki
hancinsa ya sa masa nishaɗi, se da ta kawo
masa abin tarba sannan ta samu waje ta
zauna.
"yan mata" Ya faɗi fuskarsa yalwace da
murmushi.
"yayan yan mata" Ta faɗi tana maida
masa da murmushi.
Tsare ta yayi da ido yana neman abinda
zai bambamta ta da halimar da ke zuwa
masa a mafarki, mafarkinsa na jiya ya
dawo masa inda yayi Wai Halima ta haihu
an samu Abubakar suna ce masa saadik .
Hure masa fuska tayi. Nan da nan yayi farka
daga duniyar tunanin da ya shiga.
"lafiya grand frère" Ta faɗi cikin yanayin
damuwa.
"Babu komi je pense à ton avenir (ina
tunanin future ɗinki ne) " Ya faɗi yana
murmushi wanda kallo ɗaya zaka masa
kasan iyakarsa fatan baki ne.
"wani abun ya faru ne?" Ta faɗa a ɗan
firgice, kallonsa take cikin kwayar idonsa
ko zata fahimci wani abun. Ganin bata
fahimci komi ba yasa ta saukar da idonta.
"abinda da Hammad ya miki mana, aka
ce miki baya damuna ne. Addu'a ta kullum
Allah baki miji na gari, shekaru ashirin da
biyu ai ba a ce da ke yarinya ba" Ya faɗi ya
na basar da damuwar da ta shiga kamar bai
san tayi ba.
"Au da ma Shine, ai mun shirya kasan
na faɗa maka wancan yarinyar bacin biyan
maza da take har da ɗaga wuya tana taɓa
wa, wai karamar yarinyar da aka rabu da ni
yar jami'a saboda ita kenan" Ta faɗi tana
dariya kasa kasa.
"don ta sha giya Shine me? Ba hakan ya
ganta ya ce yana so ba, in ita giya tasha ke
anya beyi gwajin takalmi da ke ba, wani
irin zuciya gare ki, kina tunanin zai chanza
ra'ayinsa ya aureki ne bayan tun farko ya
nuna miki shi ba mijin aure bane, haba
Halima da hankalinki da komi kina bari so
na sarrafa miki rayuwa, oh ku ne masu bin
na turawa da suke cewa 'everything is fair
in love and war' Ko? Toh ki sa ma ranki
cewa rien est juste dans l'amour et la
guerre (nothing is fair in love and war)" Ya
faɗi a fusace, tabbas ta san gaskiya ya faɗi
amma ya zatayi da son Hammad. Kuka take
mai hana sukuni ido ya sa mata duk da yana
jin kukan har kahon zuciyar sa. Sai da tayi
mai isarta sannan ya fara lallashinta.
"Kinsan rayuwarki na da mahimmanci
a tattare dani, kiyi hakuri kiyi tunani kinfi
karfin Hammad in aka dubi halayya da
kamala, ki hakura tun yanzu kafin ya kara
miki wani takaicin gaba. Ki kuma cigaba da
addu'a Shine maganin komi" haka yayi ta
bata kalaman karfin gwiwa har ta sake.
"Ana fa fama da zazzaɓin cizon sauro, da
typhoid ga tattalin arzikin duniya na cikin
ha'ula'" Ta faɗi tana mai sauya hiran.
"Eh wallahi, ko ina har fa Nijeriya kuma
rashin tsaftar muhalli duk ke kawo hakan
fa" Ya faɗi cikin halin ko in kula.
"Ta ya kenan?" Ta tambayeshi don bata
fahimce shi ba.
"sakacin mu yayi yawa, ba ma gyara
gwata a anguwanni, bola ko ina, ciyayi sun
fito jikin gidaje, amma son kai irin na
mutanen mu yanzu ba'a gyarawa. Sauraye
sun samu mafaka, in ka gyara cikin gidan
ka ai zaka fira waje, kinga dole zazzɓin
cizon sauro yayi yawa.
Typhoid kuwa yanzu kinga damina ne,
muna tara ruwan sama muna sha ba tare da
an tafasa shi ba. Tsakanin sama da inda ka
tara ruwa ai akwai germs da zasu shiga. Ko
rijiyoyi da suka cicciko kinga ai ko alam
mutum yasa dattin zai kwanta kafin a sha."
"wai yaushe ka fara aiki da asibiti ban
sani ba. Tunaninka sak abinda ya ke
faruwa. Allah dai ya kare mu da lafiya".
"Aameen ya rabbi"
Haka suka cigaba da hira yaje yai sallan
la'asar ya dawo, sai wajajen biyar na
yamma yai musu sallama suka rabu.
Yanda Abdoul ya tafi haka shawaran da ya
bata ya bi ta gefen kunnen ta don kuwa
sabon soyayya suka fara da Hammad, duk
tayi masa zancen aure yakan ba ta amsa da
cewa "ai kawancenmu yafi soyayya
mahimmanci kar ki bari zugin kewaye ya
zama katangar biyan bukatar zukatanmu"
a haka yake binta da daɗin baki har ta
saduda.
Ana cikin haka sai ya sauya salon soyayyar
su ya zama hiran da suke na batsa ne, tun
bata sakin jiki har ta kware a sarrafa kamai
da kan motsa sha'awar su wanda hakan yasa
yakan bata kula na musamman. Sukan
kashe awanni suna waya har sai sun kai ga
samun natsuwa, wata rana suna cikin irin
wayar se ya ce mata
"Baby ina so in na zo Niamey zaki ɗan
min wasu abubuwan da kike kwaɗaita min a
waya" Ya faɗi cikin sigar rarrashi.
"Anya sweetyna kana so na kuwa,
kasan dai bazan taɓa yin zina in saɓa ma
Mahalicci na ba don faranta ranka" Ta ce a
fusace
"wa ya ce miki zina za muyi ai kin wuce
ayi aron hannu da ke, wallahi iyakarmu
romance, ba zan taɓa keta haddinki ba."
haka yai ta faɗa mata kalamai masu nuna
aminci da yarda har ta amince.
Washegari kuwa sai gashi, ta shirya da
sunan zata shiga makaranta kamar yanda ya
raɗa mata ta faɗi sai ga Abdoul ya iso gidan
babu sanarwa ya zo mata sallama za shi
karatu Kasar Faransa.
"haka ba ko ɗan notice" Ta faɗi a
zolayance
"Na duba ne naga tabbas in ba wani
kwakkwaran abu zai kaiki skul ba toh kina
gida, shi yasa kawai na ga gara in zo yau
tunda tafiyanmu ta nuna zuwa France"
"aiko da ka taka zero, yanzu take shirin
shiga makarantar wai an kira ta" faɗin haj
Mas'ouda da ke shigowa falon.
Kallonta Abdoul yayi alamun rashin
yarda, murmushin yake ta sakar masa
wanda ya tabbatar masa da zarginsa.
"shin ina zata je tayi karya da makaranta"
Ya samu kansa da tambayar kansa hakan.
"Sai muje mu dawo kawai momma" Ya
faɗi ma Haj Mas'ouda yana murmushi
"Toh a dawo lfy, kaga sai kayi mata faɗan
rashin tsaida miji, ta lake ma Hammad
wanda sam ba aurenta a rayuwarsa." Ta ce
fuskanta na nuna alamun takaici.
"Momma lokaci ne..." gwaɓe mata baki
da akayi ne yasa ta yin shiru. Se dai a ranta
tai ta surutun an sa mata idanu.
Fita sukayi tana tunanin yanda zasuyi da
Abdoul don ya sauke ta a inda Hammad ke
jiran ta. Sake-sake kawai takeyi don har
sun kai ga gate ɗin makarantar su sai
wayarta ta ɗau kara. Kafin ta ɗauka yai
saurin ɗauka ya amsa wayar kana ya sa
wayar a handsfree
"baby ina jiran ki tun ɗazu, na matsu naji
ɗumin jikinki" aka faɗi a ɗayan ɓangaren.
Da ace zata iya nutsewa a kasa da tayi don
kunyar da ta shige.
"se dai kaji azaban wuta don ubanka, kai
rayuwar da ka zaɓa ma kanka kenan lalata
yaran mutane toh Halima tafi karfin ka
kuma ka fita hanyar ta ko in wulakanta
maka rayuwa" bai jira amsar Hammad ba
ya figi motar zuwa gida.
Haj Mas'ouda ya zayyana ma komi nan
ta fara kuka tana salalami
"Halima me yasa zaki ɓata rayuwar ki
haba nayi mamakin abin da yasa kika kasa
rabuwa dashi ashe, ancen mahaifiyarki gsky
ne da tace an gama kwakule ki. Tir wallahi
da halinki" Ta faɗi tana shirin tsallaketa ta
wuce.
Kafafunta ta riko tana rokon ta,
rantsuwa take mata akan ba abinda ya shiga
tsakanin su asali ma wannan ne na farko
nan dai ta kwashe yanda sukayi ta fada
musu.
"Toh da kika tashi zuwa ki isko shi aka ce
miki haka ne zai sa ya aureki? Sai ma ya
kara tsanar aurenki. Kinga dai ni namiji
ne, duk macen da na lagudata ta yarda ta
aure ni wahala zata sha, kuma haka duk
wani namiji yake, uwa uba ya sa ki a ɗiya
mace to babu sauran mutunci tsakani.
Zama ayi ta wayar batsa shi ke kai
matasa ga aikata, zina, kuma da yake ce
miki turmi da taɓarya ne kawai zina ina ya
bar ayar Allah da yace kada mu kusanci
zina, kinga kenan hatta karatun batsa,
zantuttukan batsa, kallon batsa ana iya
danganta su da kananun zina, kuma abin
nisantarwa. Halima ki ji tsoron Allah ki
tsoraci kwanciyar kabari, wuta gsky ne
kuma azaban Allah gaskiya ne. Momma na
wuce sai in na dawo" Ya karasa zancen yana
mai da akalar zancen zuwa ga haj
Mas'ouda.
Godiya ta bishi dashi da albarka da tayi ta
sanya masa. Nan ta bar Halima da bakin
ciki da kunya.Sauyin Rayuwa
771 74 9
by Ummu-abdoul
Da kyar ta iya tashi ta sallaci magriba da
isha'i sannan ta sa tuwon shinkafa da fakku
(malohia murzazza) don taci. Jinsa take
kamar maɗaci haka tai ta tutturawa har ta
cinye kaɗan ɗin da ta ci. Har zata kwanta ta
yi tunanin ta ba Abdoul hakuri don ta san
da wuya ya sake amincewa da ita.
Nan ta iske missed calls ɗin Hammad
fiye da talatin. Bayan ta tura sakon ban
hakuri ga Abdoul ta kwanta tana wasikar
jaki nan sai ga kiran Hammad ya sake
shigowa, kamar bazata ɗaga ba don yana
gab da tsinkewa ta ɗaga da sallamanta
"Ni zaki wulakanta Halima? Nasan hana
ki zuwa akayi amma ya akayi baki tsara su
yanda mukayi planing ba, kin ban mamaki
kuma ki rusa mana budget don wallahi
zancen aurenmu yasa naso haɗuwar mu ba
komi ba wallahi" Yayi shiru yana huci a
tunaninsa zata ce wani abu sai tayi shiru
wanda hakan ya kara harzuka shi.
"kin ma maida ni mahaukaci ne ko,
haka Allah ke abunsa, ya bani daman
mallakar ki a matsayin mata nai wasa da
wannan daman yanzu gashi kuma soyayyar
ta dawo min kina min wulakanci" Ya faɗi
kamar zeyi kuka.
"tsaya! tsaya! Hotel ne zakayi zancen
aure dani, ina in har haka ne gidanmu yafi
dacewa da muyi, ban taɓa haɗa makwanci
da namiji ba kuma bazan fara akanka don
kana min barazanar aure na zaka yi ba. Na
kara gode ma Allah da ban saɓa masa
saboda kai ba, wallahi kunyar da naji yau
yafi min sau dubu akan wanda zanji ranar
kiyama inda na cikata umurninka." Ta
karasa tana mai shessheka.
"haba Mon amour (masoyiyata) kin san
Allah ɗaya ko to Je t'aime de tout mon
Coeur (ina sonki da dukkan zuciyata. Kiyi
min rai ki sake bani lokaci mu tattauna
wallahi duk abinda zamu tattauna mai
mahimmanci ne, akan zancen aurenmu
ne. Ki taimaka min ba son ni ba" Ya faɗi
cikin sigar lallashi da ban hakuri.
"Na ji gobe ina gida kazo kawai" Ta faɗa
a takaice.
"wani irin kina gida, haba sweetyna kar
kiyi min haka, in zaki samu fitowa ki same
ni a hotel din. Don Allah ba don ni ba"
abinda ya samu kansa da faɗi kenan bayan
ya tattara natsuwarsa zuwa yanda bazai
bayyana fushinsa.
"bafa zan saɓa ma Mahalicci na don
faranta ma abinda ya halitta ba. Kayi
hakuri kawai kazo gida" itama ta faɗi kai
tsaye ba tare da shakka ko tsoro ba.
"lallai duniya juyi juyi yanzu duk son da
ake min an dena ne, sai ni kuma da Allah
ya jarabta da sonki. Wai ba kiyi mamaki ba
Halima, anya zan iya rayuwa babu ke, ki
taimaka. Mana don Allah" Ya karasa da
sumbatar iska, wanda yasan Halima na so
kwarai da gaske koda ranta a ɓace yake da
ya mata takan manta inda kanta yake. A
mamakinsa sai yaji tace
"Ni in bazaka zo ba muyi maganar anan
shike nan, banyi mamakin chanzawarka ba
don kana son gani na komi zaka iya"
"shike nan kin zaɓi rabuwarmu akan ki
zo, kin san dai babu abinda zan miki, just
tattaunawa zamuyi akan mafitanmu" Ya
nace akan son yardar da ita akan ra'ayin shi.
"se da safe don na ga baka da niyyar
gane annabi ya faku. Bazan saɓa ma
Mahalicci na bafa" bata jira cewarsa ba ta
kashe wayar.
Buɗe kofar da akayi yasa tayi saurin
share hawayen da ya gangaro mata. Har ga
Allah tana son Hammad amma ya ta iya.
Rungumarta Haj Mas'ouda tayi tana share
mata hawayen.
"kin cika yar hallak Halima, ubangiji ya
dubi hakurin ki ya baki mijin marainiya,
kar ki sa damuwa a ranki, wani baya auren
matar wani haka wata ba ta auren mijin
wata. Don haka mata masu cewa zasu bada
kansu don a auresu babban kuskure ne da
suke tafkawa, in Allah beyi shine mijin ba
sai dai bakin ciki ya kashe su don bayan
asaran mutuncin su har da asaran masoyi.
Kuma duk saurayin da kika ba shi kanki
walau karami ko babban zina wallahi ranar
da aka ɗaura aure duk son kan koma
kiyayya, hantara da wulakanci zaki kwasa
maimakon soyayya da tattali.
Halima bakya mamakin meyasa auren
yanzu babu karko wallahi maimakon mata
su gina soyayya a zukatan masoyan su
sukan gina sha'awa ne, tura ma samari
kalamai da hotonan batsa wai da sunan su
rike su har su aure su. Daga ranar da akayi
auren kuma ya kashe kishin shaawarsa se
ya fara gasa ta. Ki cigaba da addu'ar zaɓin
Allah ki aje son rai. Gara ki so mijin da
kika aura da ki auri mijin da kika so. Kar
kiyi gaggawa a aure, Allah ne mafi sani a
dukkan Al'amura, Allah ya miki Albarka "
Ta karasa tana lallashi ta, sannu a hankali
ranta ya in fara haske ta nemi bakin cikin ta
rasa. Hamdala tayi ta nanatawa a
zuciyarta akan gatan da Allah ya mata na
samun mai ɗaura ta a hanya.
***
Sannu a hankali ta fara farfaɗowa daga
cutar da ke addabarta, tun tana tuna
Hammad sau ba adadi har ya zama takan
kidaya su, tafiya tafiya har bai wuce ya faɗo
mata sau biyu ko uku a rana ba.
Kwatsam wata ɗaya da faruwa wannan
Al'amarin suna kallon tashar Dounia TV
(Radio Télévision Dounia) su duka har da
baffa, bayan Ummitr Bingel sa Gimbiya
Zuby sun gama shirin da sukanyi na mu
shakata sai aka sako tallan auren Hammad
da wata Amina. Shiru ya ratsa su a falon
har aka sa wani shirin. Se chan ne baffa ya
nisa ya musu nasiha mai ratsa zuciya, ya
nuna musu illar yaudara da kuma mata su
zubar da mutuncinsu. Tun daga ranar ta
tattara lamuran Hammad ta sa a bola
sannan ta kona.
Ta samu aiki a makarantar da ta gama
wato Université Abdou Moumouni bayan
ta kammala masters ɗin ta. Ba laifi tayi
kiba tayi kyau abinta yayinda maza suka sa
ta gaba, ita kuma bata basu uzuri daga sun
nemi raina hankalinta zata kora su,
tsoranta zuciyarta ta kamu da son wani ta
kara wahala.
***
2014 ...
Gari na wayewa dare na yi kwanaki na
tafiya har su isko watanni. An wayi gari
Halima kan manta Hammad in ba taji an
kira sunan shi ba ko taganshi kasancewar
yakan kawo matarsa makarantar da take
aiki. Bata da wani abokin ɗebe kewa da ya
wuce Abdoul sun shaku sosai, komi ta
samu in na yara ne takan siya ma yaransa
ne safiyyah da ta ci sunan mahaifiyarsa
hakan yasa suke ce mata Ummu abiha ,sai
biyun Halima kuma a hakan suke kiranta.
Agaysha ta san da zaman Halima kuma
tana kishi da ita amma bata ɗauka da gaske
bane don a cewarsa Halima kawarshi ce
kawai da ya ɗauka kanwarsa uwa ɗaya.
Hakan ya kwantar mata da hankali don
duniya in dai kawance kawai Abdoul ɗin ta
zeyi da koma wacece ba soyayya ba toh
babu abinda ya shafe ta. Kalmar budurwa
ne dai ta tsana don ko da wasa kace mata
"ga budurwan Abdoul" toh zaka shiga cikin
jerin makiyanta da bata da kamar su.
***
Wata rana cikin ranaku, Halima na zaune a
ofishinta da ke cikin Faculté des Sciences,
kira ya shigo wayarta wanda daga amon
kiɗan ta san yayanta ne. Da sallama ta amsa
wani farin ciki na ratsa ta, lumshe ido duk
sukayi a yayin da suka ji muryoyin
junansu, shiru sukayi na yan dakikai, su
kaɗai suka san mai zukatansu ke raya
musu.
"yan mata jiya nayi mafarki da ke wanda
naga ya chanchanci in isar miki shi ta
hanyar labarta miki". Ya katse masu shirun.
"wow! Allah sa alkhairi ne MAFARKIN
ABDOUL ɗin" Ta faɗi tana dariya. Shima
cikin dariyar ya caɓe
"Au wai har kin sa mai suna ne, tun kafin
kiji" tun kan ya dire tace
"kasan da ace ina da fikrar rubutu babu
abinda zai hana in mai da shi littafi har in sa
mai sunan MAFARKIN ABDOUL" Ta faɗi
cike da alamun iyakan gaskiyarta kenan.
"wai tsaya, in kuma mafarki nayi ana
nakaɗa miki duka, shima alfahari zakiyi
dashi" Ya faɗi yana mai cigaba da dariya,
wanda ta kasa bambantashi da na keta.
Cikin Alamun gundura da dariyarta tace
"Ni ba abinda ke cikin mafarkin ya sani
murna ba balle ka samu abin tsokanata da
shi, wanda yayi mafarkin ne ke da
mahimmanci Alaranma" dariyan ya cigaba
da yi ba tare da ya damu da fushin da ta
fara ba.
" Toh hajiya halimatu ai ba yau ne farau
ba, ina ga ba'a cike sati. Banyi sau biyu ba,
wannan dai kawai ya tafi da hankali na
sannan ya magance min matsalar da nayi
shekaru biyu ina fama. Shiyasa zan faɗa
miki in ba haka ba ai se kin biya. Ya sake
kara sawa yana dariya.
"yanzu kana da matsala shi ne baka taɓa
faɗa min ba, kuɗi ne ko ciwo ko har yanzu
mamansu Ummu abiha ba ta dena tozarta
ka bane." Ta faɗi kamar zatai kuka. Wannan
na ɗaya daga cikin dalilin da yasa take da
mahimmanci a gareshi. Takan nuna
damuwa ko farin ciki yayinda ɗaya ya same
shi.
"ba ko ɗaya, wato ke hajiya ko. Kina
kwasan. Albashi, toh cepa miliyan ɗari
nake so, karkaɗa kunni ki sha labari" Ya
faɗi. Yana dariya, itama ta tayashi
Gaisuwa da fatan Alkhairi gare ku duka.
Ubangiji Allah ya Haskaka rayuwarku ya
baku dukkan abinda yake Alkhairi a gare
ku. Keep voting nd commenting
pleaseeeeee.
MAFARKIN ABDOUL
729 62 2
by Ummu-abdoul
MAFARKI...
"Na ganni ne a wani lambu mai ban
sha'awa, bayan kayan marmari da ya
yalwatu a cikin lambun har da wasu furanni
masu fitar da daddaɗar kamshi wanda ya sa
na kara kishingiɗa a resting chair ɗin da
nake zaune a kai. Lumshe idanu nake farin
ciki na yalwatuwa a zuciyata.
Sallaman da kikayi ne yasa na buɗe idanu
ina mai sakin murmushi. Farantin hannunki
kika aje a gefe sannan kika fara shayar dani
salad ɗin kayan marmarin da kika zo da
shi. Wanda daɗin sa bai sa na ankara da ya
kusan karewa ba har se da kika daga Yankar
karshe na abarba sai na na riko hannunki
haɗe da spoon ɗin da ke baki na. Hakan
yasa kikai saurin ɗago idanu kika kalle ni,
idanunmu na haduwa kika kasa ɗauke idanu
na wasu dakiku. Muna cikin haka sai ga yara
biyu sun zo a guje suna kiran "Abbu!
Ummu!" kallo ɗaya nayi musu na san yan
biyu ne kuma daga tsatsonki suka fito
saboda tsabagen kaman da sukayi da ke.
Sun faɗo jiki na kenan suna haki kiran
sallah ya tada ni daga barci, faɗa min me
kika karanto a ido na da kika tsare ni da
kallo" Ya karasa yana mai tsokanarta,
"ka bari sai mun sake haduwa a
dreamland sai ka min tambayar, kasan
me?" Ta dakata ko zai amsa
"A'a se kin faɗi" Ya bata amsa
Se da tayi dariya son ranta sannan tace
"za ka yi kyau da rubuta labarin soyayya
fa. Wannan iya tsara lbr haka" ba ta dena
dariyar ba shi kuma kansa duk ya ɗaure,
"yanzu ba za ta ba MAFARKIN
mahimmanci ba bare ta kai ga fahimtar
abinda ya ke damuna game da ita b" Ya faɗi
a ranshi yayin da a bayyane shiru yayi mata
kawai. Jin ya kyale ta yasa T faɗin "hello!"
dariya kawai ya bi ta dashi kana sukai
sallama.
Shiru tayi tana tariyo labarin da ta sanya
ma MAFARKIN ABDOUL, bata san me ke
shiganta ba ta dai tsinci kanta cikin wani
yanayi daga tafin kafarta har Kirjinta wanda
salon bugun zuciyarta ya chanza nan take.
Amon muryar Abdoul take ji a kunninta
sa'ilin da yake bata labarin. Nan take wani
farin ciki ya mamaye ranta yayinda tsoro
kuma ya shige ta sanda ɓari guda na
zuciyarta yace da ita "in baya sonki fa". Nan
take sai ta shiga damuwa.
Sai sa su ka yi sati biyu babu wani
kwakkwaran magana da ta shiga tsakanin
su, iyaka sukan gaisa da ɗan hira sama
sama.
"Amarya a gidan Abdoul barka da yini"
Ya shigo WhatsApp ɗinta daga lambar
aminin Abdoul Yahai.
Aljani mai dariya kawai ta tura masa
sannan suka gaisa a mutunce.
"kina gara ɗan uwa na fa Halima shi
tsoransa ki yankuna shi wanda hakan zai
taba zumuntarku amma wallahi nasan duk
kuna sonjunanku, meye amfanin cutar da
kai, in shi ya kasa buɗe hanya ke baza kiyi
ba? Ya tura mata haɗe da aljani mai jan kai.
Bata ce komi ba sai aljani mai dariya da
hawaye ta tura masa, ganin bata da niyyar
bashi haɗin kai yasa ya kyale ta.
Daren ranar ta tsawaita hirarsu da
Abdoul har yake faɗi mata mafarkan da ya
keyi kusan kullum

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment