Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


"Halima ashe dai mijinki bashi da kunya?"

"Me kuma ya yi Inna kin ce ya koma falo ya koma to me kuma kike so ya miki?.

"Ana ga yaƙi kina ga ƙura yo ai na ga yana so ya min kora da hali, in ba kora da hali ba ya za a yi ya san ba ku kaɗai bane a gidan, kawai ina zaune sai ganin mutum na yi sangamgam ya shigo falon babu neman izini gandaƙai-gandaƙai ko suturar kirki babu, da da sanyin nan ma amma ya zauna da kayan banza"



Sai lokacin Sadiya ta gane abin da Innar take nufi, ba tare da ta tanka ta ba ta ɗauki wayar Imran tanjuya za ta fita Inna ta ce.

"Ki taho min da bargona a kan kujera, ki haɗo min da wannan sauran maltinar guda ɗaya ta ɗazu"


Tafiya Sadiya ta yi ba tare da ta ce komai ba, tana fita daga ɗakin Inna ta rafka uban tagumi, idanunta a kan gadon Hassan.

"Ni Azumi da zan yi kwana Hamsin amma tun ban kwana ɗaya ba na fara fuskantar abubuwa, ga yaro mai bayan miciji ga ubansa yana yawo da jiki babu maraba fa tsirara, haka kawai lokacin fatarar nan fa ake rashin kuɗi ya je ya sa in gamo da ganin al'aurarsa, ni Azumi in shiga uku in ma ban makance ba" Ta faɗa a zuciyarta dai dai nan Sadiya ta dawo ɗauke da bargon da maltinar, ta miƙa mata dama ta buɗe mata kwalbar maltinar. Haka ta kafa kai ta shanye tas ta miƙa kwalbar kan mudubi ta ajiye, lokacin Sadiya tana shan magungunanta.

"Ni da nake ta shan maltina kayan ruwa, ko ya zanyi da fitsari, dama ya lafiyar kura bare ta yi hauka, ni mai yawan fita fitsari cikin dare, bare na cika cikina da kayan ruwa, wannan kurman mutumi falo" Ta faɗa tana kallon Sadiya.


"Shi da yake gefe ɗaya a kwance kuma ina ke ina shi"

"A'a Halima nake ƙetara mutum ina fita wa ya san fita nawa zan yi"

Sadiya dai bata kulata ba ta yi shirin kwanciya ta hau gadon ta kwanta.


"Inna ki kwanta mana, na ga dai gani gaki gani kuma menene zai hanaki kwanciya?"


"Hankalina a kwance yake, kawai dai ina jin kunyar gadon ne, yo na kwanta a gadon yara"

"Sai ki kwanta mana, ai babu komai ke da jikokin ki"

Wannan kalaman da Sadiya ta mata yasa ta ji ƙwarin gwaiwa ta kwanta ta rufa da bargonta, ita ma Sadiya gadon yaran ta tashi ta maido gefen gadonta kusa da ita dan ma haɗe yake da net ɗinsa sauro ba zai cije yaran ba.



~DARE~


Wajen ƙarfe biyu na dare Imran ya tashi zaune, dan dama ya ji tashin Sadiya wajen ɗaya saura yaran sun motsa, ya basu ruwansu yana dai ji har ta kwantar da su, bai sani ba ko sun sha nono ko kuma nonon bai zo ba, sa'a ma aka yi yaran ba wasu masu rigima bane. Ɗakin tsit baka jin komai sai ƙaran minsharin Inna tun da ta kwanta bata motsa ba, haka ya tashi cikin sanɗa ya leƙa bedroom ɗin sai da ta tabbatar bacci suke sannan cikin sanɗa ya shiga ɗakin drower ɗinsa ya buɗe ya ɗakko farar jallabiyarsa, tare da wata farar rigar sanyi mai haɗe da hula, haka ya lallaɓa ya rufe drower ya fita ba tare da sanin su ba, dan Inna kamar wata gawa haka kawai sai sakin munshari take.

A ransa ya ce

"Kina wannan munsharin koma me mutum zai yi da matarsa sai ya yi baki sani ba, ya faɗa yana jan tsaki tare da yin ƙwafar ganin Inna ta maye gurbin makwancinsa. Jallabiyar ya sanya sannan ya ɗora rigar sanyi a ka sai ya bar zip ɗin a buɗe, haka ya fita ya je bayin nasu ya cire ƙwan fitilar ya dawo ya kwanta.Zuwa can ya ji motsin Inna ta tashi tana cewa.

"Dama na san dole na tashi fitsarin nan duk ya cika min mara"

Da hanzari ya ɗakko filillikan kujera, ya jera a kan katifarsa ya dai daita su kamar mutum ya rufe da bargo, yana gamawa ya lallaɓa ba takalmi
ya tafi banɗakin.




_INNA_


Haka ta tashi ta kunna fitilar ɗakin, ta kalli Sadiya da ke baccinta cikin kwanciyar hankali ta ce a fili.


"Allah da hikima yake, shi yasa ya sanya mata ke zubar da jini bayan sun haihu (Jinin haihuwa) Amma ba dan haka ba Allah kaɗai ya san yawan matan da matansu za su ke maida musu mahaifa nan da nan (Su yi tarayya da su) Musamman in aka samu kudurarru masu jaraba, tuni za su haƙƙewa mai jegon saboda basu san wahalar naƙuda ba, shikenan mata su ringa haihuwar kwenika" Ta faɗa tana gyaran ɗaurin ɗankwalinta ta taso ta fito. A hankali ta leƙa falon dan tabbatar da Imran ɗin yana bacci, ganin filon da ya jera sai ta ɗauka shi ne ke bacci da yake ma fitilar falon ma a kashe take bata kunna ba dan bata so ma ya tashi.

Haka ta nufi bayin gadan-gadan har tana haɗawa da sauri jin fitsarin ya matseta. Imran da ke cikin bayin jin takun Inna yasa ya ƙara jingina a jikin bangon da ke kallon ƙofar bayin ya baza hannu ya sanya hular sai ya sunkuyar da kai. Inna jin fitsarin na nema zubo mata ganin fitilar a kashe sai bata kunna ba kawai ta shige bayin. Sai da ta je tsakiyar bayin kawai sai ganin abu ta yi fari ƙal,kallon abun ta yi da kyau ta ga mutum ne a take ta ji ƙafafunta sun fara karkarwa, hannu ta miƙa ta dafe jikin bango tana cewa.


"Innahu min sulaimana wa innahu bismillahir rahmanir rahim, ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba" Ta faɗa har lokacin tana karkarwa, so take ta gudu amma ƙafafunta sun ƙi bata dama, ji take kamar a wurin aka dasa ta.




Imran ganin tarkonsa ya kama tsuntsu ya ce a ransa.

"Mu zuba ni da ke mu gani, ba dai kin ce ke ZAMAN WANKA za ki yi ba ai ga wurin nan"


A hankali ya fara takowa yana nufota, dama ƙafarsa ko takalmi babu, Inna ganin aljani ya doso ta a nata tunanin kenan, sai haƙoranta suka fara haɗuwa da juna kafkafkaf, gaba ɗaya ta tsure ji take aljanin nan yana dafa ta mutuwa za ta yi, ji ta yi kawai fitsarin nan ya ƙwace mata, yana bin ƙafafunta, aljanin na matsowa a hankali ita kuma faɗuwar gabanta na tsananta. Imran kwa duk nufotan da yake bai ɗago kan sa ba, jib Inna ta zame ta zauna ƙafafunta sun kasa ɗaukanta, ganin dai da gaske aljanin na miƙo hannu hakan yasa ta fara rarrafe domin ƙwatar kan ta, tana rarrafawa yana ƙara matsota har suka fito daga bayin, dan Imran rage tsawo ya yi sai ta ga ɗan guduldili ne aljanin, tana rarrafe tana salati dan so take ta yi ihu amma ta kasa gabaɗaya bata da karazana.





Ta fito daga bayin yana biye da ita tana rarrafawa duk ta zubar da takalmanta, suna fitowa ta juya tana rarrafe dan rarrfenma dakyar take yi sai Imran ya yi saurin juyawa cikin sanɗa ya koma cikin bayin, Inna sai da ta kusa shiga falon da rarrafe ta waiga aikuwa sai ta ga babu aljanin hakan ya sa ta ɗauka ɓacewa ya yi.



Hakan ya sanya ta cigaba da rarrafen duk da tana jin kamar aljanin zai rafkota ya maidata bayin. A haka ta shigo falon, kallon katifar Imran ta yi ganinsa lulluɓe yasa ta cigaba da rarrafe dan ba za ta tsaya a falo ba tashinsa sosai take jin tsoro, haka ta wuce cikin ɗakin tana jin rigarta jigif da lemar fitsarin da ta saki.



```Imran```

Tun da ta waiwaya ta ga baya nan, sai ya laɓe daga bayin ya cire kayana ya bar singlet da gajeran wandonsa, sai da ya dai dai ci Inna ta kai bedroom cikin sanɗa ya dawo falo ya ɗauke filillikan ya mayar da su mazauninsu ya sanya kayan da ya cire a ƙasan filo ya koma ya kwanta ya rufa.



```INNA```


Gadon ta kama hannunta nankarkarwa so take ta hau amma ta kasa hawa ga bakinta ya kasa magana, hannu ta kai ta kamo ƙafar Sadiya ta kama babban yatsan Sadiya take ja, dan bakinta ba zai iya kiran sunan Sadiyar ba.


Sadiya da gabaɗaya ta yi nisa da bacci bata san Inna na jan yatsanta ba. Imran ya tabbatar yanzu Inna taa cikin halin ƙaƙanika yi dan haka ya miƙa ƙafarsa ya bugi jikin kujera, ai Inna na jin ƙaran sai ta ɗauka aljanin ne ya biyo ta, ganin Sadiya ko motsi bata yi kamar gawa hakan ya sanya Inna ta lallaɓa ta shige ƙasan gado...




Masu son shiga grp zaman wanka 09030283375



🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼

(KWANA ARBA'IN)


NA



MAMAN AFRAH


🅿️8️⃣


Inna sai numfarfashi take, nishinta na fita ta kwanta lifet da ribda ciki, kawai jiran tsammani take, dan duk tunaninta aljanin ne ya shigo kawai neman inda take yake yi.

"Allah ka gani ZAMAN WANKA na zo, hanyar zumunci ne, idan kuma ba aljani bane mala'ikan mutuwa ne Allah ka yafe min kura-kuraina, ka haɗa mu a aljanna da Malam, ka sa ni kaɗai ce matarsa a can ban da Tasalla" Cewar Inna a zuciyarta.


Gabaɗaya ta sanya hannunta ta riƙe ƙafar gadon, duka hannayenta a jikin katakon suke, dan gudun kar aljanin ya ɓanɓarota daga ƙasan gadon. Har aka fara kiran assalatu Inna tana ƙasan gado Sadiya kwa bata falka ba, saboda kwana da ta yi ta waye tana gwagwarmayar naƙuda hakan ya sanya ta gaji bare haka nan ma nauyin bacci gareta.


```IMRAN```


Tun da ya buga ƙafarsa a jikin kujera ya ƙara razana Inna, jin ɗif a ɗakin babu motsinta hakan ya sanya ya gane ta mugun tsorata dan haka bai ma san lokacin da bacci ya ɗaukesa ba. Sai dai lokacin sallah ya yi alerm ɗin wayarsa ya fara masa sallama, tashi ya yi ya kunna fitalar falon ya fara kiran Sadiya sau boyu kawai ya kirata dama ba dan ya tasheta ya yi kiran ba dan Inna ta jiyo muryarsa ya san tana nan har lokacin a tsorace dan haka ɗakin ya nufo ya zo ɗaukan kayansa dan ya yi shirin tafoya masallaci. Daga setin da Inna take a ƙasan gado daga nan drower kayansa take, haka ya buɗe ya sanya kayan da ya yi amfani da su wajen tsorata Inna ya ɗora musu wasu kayan ya ɓoye su yadda ba za a gani ba ya ɗakko wami yadi riga da wando, ya juyo ya fito daga ɗakin sai dai ya yi matuƙar mamaki da Inna ta ji shigowarsa amma bata fito ba, kuma ya tabbatar idonta biyu, dan babu yadda za a yi bacci ya ɗauketa dan bata cikin kwanciyar hankalin da bacci zai ɗauketa.Sosai abin ma ɗaure masa kai da ya ga bata kan gadon, yana tunanin inda za ta ɓuya a ɗakin sai da ya je zai buɗe drower ne ya hangi rigarta a ƙasan gadon aikuwa kamar dai ya yi ta ƙyaƙyata dariya.


"Ashe ma abin naki tsoro ne ba dai ke MAI ZAMAN WANKAN da za ta addabi mutane ba ma ji ma gani wai an rufe tsohuwa da ranta" Ya faɗa a zuciyarsa ya fito falo ya sanya yadin da ya ɗakko ya fita domin yin alwala ya tadi masallaci.


```INNA```


Tun da Inna ta hangi hasken fitilar falo gabanta ya shiga faɗuwa dan duk tunaninta aljanin ne.


"Ya Allah ka makantar da aljanin nan kar ya ganni, idan kuma shi ba aljani bane mala'ikan mutuwa ne ka sa in cika da imani, ka haɗa ni a aljanna da Malam Allah ka sa ni kaɗai ce matarsa a can ban da Tasalla" Ta faɗa hawaye na gangarowa daga idanunta.



Har sai da ta ji Imran ɗin yana ƙwalawa Sadiya kira hakan ya tabbatar mata ba aljanin bane Imran ne ya tashi. Ta san jin Sadiya bata amsa ane ya taho ɗakin. Amma sai ta ƙyaleshi har ya gama uzurinsa ya fice.


"Babu abin da zai sa na faɗa maka akwai aljani a bayi, sai ka je kaima kun yi ido huɗu da shi ka gan shi ra'ayal aini, sannan in ga ƙarshen kurmanci dan na san yau in ka rinƙa ƙwanzama uban ihu sai duk maƙota sun ji ka sai ka gwammace kiɗa da karatu, dan yaro bai san wuta ba sai ya taka, yau za mu ga ƙaryar rainin wayo" Inna ta faɗa a ranta tana hasashen yadda Imran ɗin zai yi idan ya ga aljanin.


Shiru -shiru bata ji ihun Imran ba, abin ya bata mamaki dan ita mugunta ce ta sa ba za ta faɗa ba ma bare ya fs zuwa bayin, tana a haka sai ƙaran buɗe ƙofar gida ta ji ya fita masallaci, sosai ta girgiza da hakan.

"To ko dai aljanun gidan ne basa yiwa masu gidan komai si baƙi, ko dai tun da ya ɓace lokacin da na waiwaya bai ƙara fitowa ba shi sa Imran ɗin bai ganshi ba?" Ta rinƙa saƙa-da warwara zuciyarta.


Har sai da gari ya ɗan fara haske sannan ta ji ƙaran ƙofar gida alamar Imran ya dawo daga masallaci, kamar jiran dawowarsa yaran ke yi, uka tashi suka fara kuka a tare. Hakan ma ya yi dai dai da shigowarsa ɗakin ya fara tashin Sadiya daga bacci, haka ta tashi tana ɗan yatsina fuska tare sa murza idanu irin na wanda ya tashi daga bacci.Haka ta ɗauki Hassan ta yi bismillah ta sanya shi a nono, shi kuma Imran ya ɗauki Husainin yana jijjigashi a kafaɗarsa. Sai bayan yaran sun ɗan yi shiru ta lura Inna bata kan gadon.


"Inna har ta tashi sallah kenan" Ta tambaya tana kallon Imran.

"Sa'adiyya, Sa'adiyya" Inna da ke ƙasan gado ta shiga kiran sunan Sadiya.

"Ikon Allah daga ina nake jiyo muryar Innar ne?" Ta faɗa tana ɗan waiwaye -waiwayen ɗakin dan ta ni muryar a ɗakin ne.

"Halima kin ganni nan" Cewar Inn jin bayanta ya tokare da jikin katako ta ma kasa ko da yinƙurin fitowa daga ƙasan gadon dan ta san dai yanzu aljanin ko yana nan dai, ba zai zo a tun ba ga masu gidan a nan kuma gari ya waye shi kuma zuwan dare ya yi jiya.


"Ina kike Inna?"

"Ko a cikin drower take" Cewar Imran a fili a ransa kuwa sai dariyar ƙeta yake yiwa Inna.

Hannu Inna ta ɗauke daga riƙon da ta yiwa katakon, ta sanya a jikin filankin gadon ta shiga bugawa da hannunta.


"Ƙasan gado kuma, Inna?" Sadiya ta faɗa da mamaki, ta miƙa Hassan kan gadonsa ta kwantar dashi ta tashi cikin sauri dan ta san tun da Inna har ta shiga ƙasan gado to ba lafiya ba lallai akwai lauje cikin naɗi.


"Wai kina nufin daga ƙarƙashin gado muryar ke fitowa?" Imran ya tambaya da nuna alamun mamaki.


Cikin sauri Sadiya ta gewaya ta leƙa aikuwa idanunta suka sauka a kan kakarta da ke kance magashiyan da rubda ciki ta kama katakwaye ta rirriƙe kamar wanda za a ƙwace mata su.

"Inna garin yaya kika shiga bakya ganin ma wurin ya yi matsi, ya miki kaɗan gabaɗaya a takure kike" Sadiya ta ce tana durƙusaw dan taya Innar fitowa.

"Taimaka mata mana, ko a magagin bacci ta shiga" Ya faɗa yana jin tamkar ya kwanta ya yi ta dariya tsabar yadda dariyar ke cinsa.

"Haba ɗan nan kamar wata ɓera zan shiga ƙasan gado, kuma ko a sume nake ba bacci ba ai ba na shiga ƙarƙashin gado ba" Inna da ke ta nishi ta faɗa a fili dan bakinta bai mutu ba, da ta ga gari ya waye. A zuciya kuma ta ce.


"Kai dai da Allah ya tsallakar da kai baka yi angamo ba amma ba haka na so ba na so ka ganshi muraran yadda na ganshi ai ni na ga ta kaina yau"

dashi ta tashi cikin sauri dan ta san tun da Inna har ta shiga ƙasan gado to ba lafiya ba lallai akwai lauje cikin naɗi.


"Wai kina nufin daga ƙarƙashin gado muryar ke fitowa?" Imran ya tambaya da nuna alamun mamaki.


Cikin sauri Sadiya ta gewaya ta leƙa aikuwa idanunta suka sauka a kan kakarta da ke kance magashiyan da rubda ciki ta kama katakwaye ta rirriƙe kamar wanda za a ƙwace mata su.

"Inna garin yaya kika shiga bakya ganin ma wurin ya yi matsi, ya miki kaɗan gabaɗaya a takure kike" Sadiya ta ce tana durƙusaw dan taya Innar fitowa.

"Taimaka mata mana, ko a magagin bacci ta shiga" Ya faɗa yana jin tamkar ya kwanta ya yi ta dariya tsabar yadda dariyar ke cinsa.

"Haba ɗan nan kamar wata ɓera zan shiga ƙasan gado, kuma ko a sume nake ba bacci ba ai ba na shiga ƙarƙashin gado ba" Inna da ke ta nishi ta faɗa a fili dan bakinta bai mutu ba, da ta ga gari ya waye. A zuciya kuma ta ce.


"Kai dai da Allah ya tsallakar da kai baka yi angamo ba amma ba haka na so ba na so ka ganshi muraran yadda na ganshi ai ni na ga ta kaina yau.


"

Imran ganin Sadiya ta kamo hannunta tana janyowa amma ta kasa taimakawa Innar, hakan ya sanya ya kwantar da Husainin jin ya yi shiru ya nufi wurin ya durƙusa ya leƙa, da idanun Inna ya ci karo sun yi wani ƙwala -ƙwala, ga bayanta tokare da saman jikin ƙasan gadon.

"Wa ya ga ido ya ƙwallin wake, sai rarraba ido take ya na mujiya" Ya faɗa a ransa yana dariyar zuci.

Hannu ya sanya ya kamo ƙafar Inna ya riƙe wajen idon sawun ya ja.

"Haba Imirana, baka ganin yadda ka riƙe min ƙafar da ƙarfi kamar ka riƙe ƙafar raƙumi, son dai ka karya min ƙwauri ko ka girɗa ni" Cewar Inna tana sauke numfashi dan da ɗan ƙarfi ya janyo ƙarfar.



Ai jin ta kira shi da Imirana nan da take kiransa hajan ya sa wani haushi ya ƙara turnuƙeshi, a haɗa ƙafar duka biyu ya shiga janyosu.

"Wayyo Allah, ashe Halima kina ganin rashin imanin da mijinki ke min sai ja min ƙafafu yake kamar mai ɗakko ruwa a rijiya, ni ba guga mai igiya ba a ce ana jana ta ƙarfin tsiya"

"Bari in ɗauke katifar sai a ɗauke filanki sai ta fito" Cewar Sadiya dan ita ma ta tausayawa Innar amma har yanzu tana mamakin dalilin shigar Inna ƙasan gadon. Jin abinda Sadiya ta faɗa yasa Imran sakin ƙafar Innar amma ba a hankali ya saki ba jaɓas ya yiwa ƙafafun.


"Ta Allah ba taka ba Imirana, in Allah ya yarda da ƙafafuna zan mutu, in ma taƙamarka ka gurgunta ni"

"Ga aljani nan mai fararen kaya, na ciki bayi yana tsaye a samanki" Imran ya faɗa a ransa.

Sai da aka fitar da duka filanki Inna Azumi ta lallaɓa ta fito tana jin jikinta gabaɗaya yana mata ciwo kamar wanda aka mata dukan tsiya.


"Ubangijn mutane da aljannu, Allah saka m..."Inna da ta fara ƙoƙarin neman sakayya ta ja bakinta ta yi shirun gudu ko aljanin na wurin ma dan su b ganinsu ake ba.



Sharaf ta zauna a tsakiyar ɗakin tana sauke numfashi.


"Inna wai mai ya kai ki shiga surƙuƙin ƙasan gadon nan, ko duk kunyar gadon ce ta sa kika ƙi kwana a ka, kuma sai ki shiga ƙasan gado san ki jiwa kan ki ciwo" Sadiya ta faɗa cikin jin tausayin Innar ganin ta yi wujig-wujiga, ji yadda rigarki ta jiƙe jigif"

"Haba Halima yo in har kunyar gado nake ai bana shiga ƙasan sa ba, sai in kwanta a tsakiyar ɗaki"

"To mai ya ki ki shiga ƙasan gadon?" Imran jin an jefowa Inna wannan tambaya sai ya yi saurin barin ɗakin ya koma falo dan ya yi dariyarsa ta ishe shi.


"Wai na ce Halima bayi nawa gareku a gidan nan?"

"Inna ana ga yaƙi kina ga ƙura, bayin me kuma amma dai na ga ba yau kika fara zuwa gidan nan ba bare ki ce baki sani ba"

"Ke kar fa ki min rashin kunya ki bani amsa kawai"

"Guda ɗaya ne"

"Mara ta gabaɗaya a cike take ina zuwa" Ta faɗa tana miƙewa ta fito daga ɗakin, gabanta na ɗan faɗuwa, tana zuwa falo ta ga Imran zaune a kujera ya ɗora ɗaya kan ɗaya baki ta taɓe ta ce

"To Allah ya yi dare gari ya waye" Ta faɗa tana yin gaba ta fita daga falon.

"Gata nan aljani" Cewar Imran zuciyarsa ya fara dariya har da riƙe ciki yana mamakin ƙarfin hali irin na tsohuwar nan wai ita ala dole ba za ta nuna karayarta ba. " Amma dai mu je zuwa" Ya faɗa yana sake sakin wata dariyar.




Dai dai nan Sadiya ta leƙo, ganin Imran na dariya sai abin ya bata mamaki mutumin da ganin dariyarsa m aiki ne sai ya ga dama amma yake dariya haka har da riƙe ciki amma dariyar ba mai sauti ba.

"Inna a ƙasan gado" Ya yi saurin faɗa dan Sadiya ta ɗauka ganin Inna a ƙasan gado ne ya sanya shi dariya, dan kar ta yi zaton akwai wani abu a ƙasa ta yi saurin harbo jirginsa.


"Haba kuma menene abin dariyar ni wallahi tausayi ta bani na san haka kawai ba za ta shiga ƙarƙashin gado ba"

"Hakane amma ki tuntuɓeta"

"To" Ta faɗa tana juyawa ta koma cikin ɗakin.



```INNA```


Tana fitowa gabanta na daɗa tsananta bugu, gani take kamar za ta sake ganin aljanin nan, hango takalmanta a wajen hanyar bayin kowanne ya kama gabansa, hakan ya sa ta nufesu ta ɗakko ta sanya a tsorace dan gani take kamar aljanin ya sa takalmin.

"Wallahi dama da ba takalmina bane na ado, da ba zan ɗauka ba in je in saka kofato ya fito min"



Haka dai a tsorace ta sanya takalmin ta je wurin wanke -wanke ta kunna famfo ta yi fitsarinta ta yi tsarki, ta wanke cinyoyinta zuwa ƙafafunta da fitsarin daren na ganin aljani ya ɓata mata, haka ta ɗaura alwala cikin sauri ta baro tsakar gidan, sai gata bidik ta faɗo falon kamar an jefo ta, duk da Imran ya san dalilin saurin nata sai da ya kalleta da mamaki. Amma Inna ta wayance ta fara tafiya a hankaliyadda take tafiyarta, ta buɗe jakarta ta ɗauki abin sallah da wasu kayana ta wuce bedroo.

Sadiya na kallonta ta ce

"Inna akwai ruwan ɗumi fa kika yi dana sanyi" Banza Innar ta mata har ta gama canja kayan ta tada sallah ita kuma lokacin tana baiwa Husaini ruwam zam-zam ɗinsa.


Sai da ta idar ta kalli Sadiya ta ce

"Ni Halima baku da mansileta ko roob, ko ma aboniki ne ki bani"

"Me kuma za ki yi da su Inna


"Ni na ji yarinya da neman dalili in da akwai ki bani mana , yo ni da na ƙarasa kwana na a ƙasan gado tamkar wacce take a ƙasan gadar legos har a tambayeni mai zan yi da man zafi, jikin nan nawa ban da ciwo babu abin da yake, ga wani wurin ma duk na kuje wallahi, kai in da ranka ka sha kallo"


"Akwai kin gan su can a kan mudubi, amma Inna wai dan Allah me ya kai ki kika shiga ƙasan gado?"

Har za ta faɗawa Sadiya

Please Login or Register in order to submit comment