Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da na sanya ran wankin ciki, in samu jar miya idan hali har da naman kaza amma in ga wake da shinkafa da mai da yaji, to Allah suturibuƙui inji kishiyar mai doro" Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma sai ta yi saurin gyara fuskar ganin kowa ya lura da ɓata ran da ta yi ta sanya hannu ta kai kyawawan lomomin guda biyu, hakan ya yi dai dai da buɗewar da Ashrof ta yiwa ɗaya daga cikin flask ɗin aikuwa Inna ta yi ido biyu da shinkafa da miya ga wani uban namomi a saman.


Tufff Inna ta tofa da duka lomar abincin da ta take bakinta taf da shi ta ce.


"Amma Asharofa baki da imani wallahi, akwai wannan abincin mai rai da lafiya amma kika bani wannan ci ka mutun?" Ta kai ƙarshen maganar tana ture flask ɗin gaban nata.

Gabaɗaya suka saki baki suna bin Inna da kallon mamaki.

"Inna abincin Aunty Sadiya ne fa da za ta ci idan ta falka"


"Ka ji ni da yarinya mai shegen iyayin tsiya yo Allah na tuba meye marabar dambe da faɗa? Abinda ya yi ni ai shi ya yi yarinyar nan, in kuma kin manta ne in tuna miki" Ta faɗa tana janyo kwanan gabanta.

"Ikon Allah na zaune ya faɗi, lallai in da rai da rabo" Cewar Inna lokacin da ta luntuma hannu cikin abincin ta cika hannu ta kai bakinta ko bismillah babu.

Mama dai kan ta na ƙasa dan ta rasa bakin magana, dama abincin Sadiya ne Hajiya Amina ta girka mata takanas ta koma gida ta iyo girki dan ta samu ta ci idan ta falka.


"Ya rabb, matar nan ta addabemu" Cewar Imran a zuciyarsa yana dafe goshinsa da hannu.

Loma ɗaya biyu, a ta uku sai kawa Inna ta saki kuka, kukan da ya sanya duk waɗanda ke kusa da su suka waigo suna kallonta, dan wasu ma zatonsu ko mutuwa aka yi.


"Inna lafiya?" Mama ta tambaya da mamaki.

"Haba Rakiya ba dole in yi kuka ba, yanzu a ce kuna cikin irin daular nan amma ko ki ce in zo in yi ko da shekara ne a marmarce ni ma in yi wankin ciki amma kika barni ina fama da karta kafura (Miyar kuka) Da tuwon masara wanda in Tasalla ta tuƙa da yake bata iya ba kana ci yana maka dariya" Ta faɗa tana ɗaukan cinyar kaza ta yagi tsokar har wani lumshe ido take.

"Na shiga aljanna na maƙale" Cewar Ashrof da bata san ma maganar ta fito ba.

"Yo waye zai shiga aljanna ya fito ɗiyar nan kowa ya shiga ai ya ga wajen zama" Ta faɗa tana suɗar hannunta da take jin daɗin miyar har tsakar kan ta.

Gabaɗaya mutanen wurin dariya suka saka, wani saurayi da ke tsaye yana kallon Inna daga can gefensu a ransa cewa yake.

"Tsohuwar nan da za ta yarda in ɗauketa vedeo in sanya a status na san duk wda ya gani sai ya ci dariya kamar me sannan na san kowa ya gani sai ya yi replay har na rasa saƙon wanda zan duba, wallahi za ta yi kyau da comedy sosai ma" Ya faɗa a ransa yana kallon Inna daga can inda yake yana ta dariya.

Imran kwa ganin hankulan mutane duk ya dawo kan su hakan ya sanya a fusace ya bar wurin.


Sai da ta cinye abincin tas duk da yawansa ta suɗe kwanan ta maida murfin ta rufe, ta ɗauki pure water biyu ta kora ta ce

"Kai garin daɗi ba kusa ba, Allah sarki Malam da ƴar Tasallar sa suna can ana fama da dambu ni kwa nan na samu abinci na ci na yi nak" Ta faɗa tana miƙa hannunta can gefen tabarmar ta tilla wani pure water ɗin ta wanke hannunta.


"Jama'a ina wuninku" Ta faɗa tana kallon Hajiya Amina da Mama.

Dariya Hajiya Amina ta yi dan wallahi sosai Inna ta bata dariya wato sai da ta ƙoshi ne ma za a gaisa, ita mamakinta ɗaya ma da Inna bata tambayi mai haihuwar ba bare ma abinda aka samu ba, sai ta abinci ma take.

"Lafiya ƙalaw Inna, kin zo lafiya" Ta faɗa har lokacin tana ƴar dariya dan wallahi ta kasa riƙe dariyar.

"Lafiya ƙalaw, wallahi" Ta faɗa tana maida kallonta kan Mama ta ce.

"Kin ji Rakiya yaushe kika koyi mugun hali ne, ace ke baki gaisheni ba ni na gaisheki amma kuma kin kasa amsawa sai ɓata rai kike kamar na miki mugun abu, yo in shinkafar da na ci da nama ne ai rabona ne ya tsaga, ita kuma wake da shinkafar shi ne rabon Halima haka Allah ya tsara tun fil azal ni Hajiya Amina ta girkawa abincin tun da rabona ya rantse sai na ci kin san rabon kwaɗo ba ya hawa sama"

"Ina wuni Inna" Mama ta faɗa kamar ta yi kuka dan wallahi yau dai Inna ta gama zubar musu da kima da mutuncin a idon siriki da uwar sirikin ma baki ɗaya.

"Yawwa ko ke fa, lafiya ƙalaw ya abin da aka samu, mai ta haifa Halimar?"

"Ƴan biyu ne duka maza?"



Salati Inna ta ɗauka tamkar an yi wani abu, sai da ta gama salallamewa ta ce.


"Amma wallahi kin cuceni Rakiya, yanzu a ce jikartawa ta haifi tagwaye duka maza amma tun zuwana wajen nan kika kasa faɗa min har sai da na ci na gwatse?" Ta faɗa tana sakin wata gyatsa.


"Ki yi haƙuri Inna dama jira nake na faɗa miki to kuma na ga kina ta ƙoƙarin ki ci abinci"

"A'a babu niyya ango ya kwana da wando, yo bana ci abinci ba, lafiya ce ta kawo haka, yanzu da za ki bi ɗakunan marassa lafiyar asibitin nan, za ki tarar ana ta fama da su a kan su ci abinci, to duk dan basu da lafiya mu kuma da muke da lafiya ai sai mu ci ba sai an faɗa mana ba"

"Allah bar mana Inna" Cewar Ashrof tana dariya dan ta m daina jin haushin abin da Innar ke yi kuma dama inda sabo sun saba da halinta kuma mai hali ai baya canjawa.

"Amin ƴar nan, in da gaske kike, dan na san wani so yake ma ka mutu y bar ganinka saboda ba ya son ganinka amma babu yadda zai yi da kai sai kallo" Ta faɗa tana kallon inda Imran yake amma sai ta ga wayam ba ya nan, baki ta taɓe ta kalli Mama ta ce.

"Wai ina mazajen nawa ne, ko sai na roƙa za a bani in gan su, kuma ita Halima da ake ta faman cewa bata falka ba, ragwanta ta yi a haihuwar har ta suma ake jiran falkowarta?"


"A'a allurar bacci suka mata, saboda tana buƙatar hutu" Cewar Mama tana miƙa mata yaron hannunta.

"Kai duniya inda ranka ka sha kallo, wato yaron ma yana hannunki amma baki bani ba, ni kuma ban lura ba ko dan an ce hankali ke gani ba ido" Ta faɗa tana karɓa yaron ta buɗe shi tana ta yaba kyansa.Babu wanda ya ce wani abu, sai da ta gama ganinsa ta ce


"Wai ina ɗayan ko ba za a bani su lokaci ɗaya ba dan kuna tsoron in gudu da su?" Ta faɗa tana kallonsu.

"Wannan tsohuwa da ɗaukan ƙafa take" Cewar Hajiya a ranta a fili kuma sai ta ce


."Kin ga ɗayan Inna, wannan Husaini ne, shi ne ƙaramin wannan kuma shi ne Hassan ɗin, an haifeshi da wata baiwa ne" Ta faɗa tana ɗorawa Inna a cinyarta daga gefe sai ya zamana gefe ɗaya Hassan ɗaya gefen Husaini.

"Allah sarki bawan Allah, ashe da baiwa aka haifeshi, yo banda abinki ai an fi son ƴan baiwa" Ta faɗa tana buɗe fuskarsa tana ta sakin murmushin farinciki.

Ashrof kwa dariya take dannewa dan ta san yanzun nan Inna za ta tsorata in ta ji baiwar da ke tare da yaron.



"Ai gabaɗaya fatar bayan Hassan ɗin ce kamar jikin miciji, kin san wasu ƴan biyun ma ana haifar ɗaya mutum ɗaya miciji saboda baiwa ce id...


"Jikin miciji fa kika ce Amina?" Inna Azumi ta faɗa tana zaro idanu jikinta gabaɗaga ya ɗauki karkarwa dan tsoro...


Next page.😂😂😂

Yanzu fa aka fara wasan 🤣🤣🤣

Masu son grp ɗin ƴar zaman wanka

09030283375



🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼

(KWANA ARBA'IN)


NA



MAMAN AFRAH


🅿️4️⃣


"Kai jama'a shi kuma irin tasa baiwar kenan?" Inna ta faɗa gabaɗaya jikinta ya ɗauki karkarwa, musamman da ta ji Hajiya Amina ta ce wai wasu maciji ake haifa ɗayan kuma mutum.

"Wallahi sai ma kin buɗe kin gani da idaonki kin san an ce gani ya kori ji"
Cewar Hajiya Amina.

Daidai nan Imran ya dawo riƙe da ledoji a hannunsa amma Inna ba wai ta ledojin take ba duk kwaɗayinta da son abin duniya sai ta ji duk bata cikin nutsuwarta.


"Ni Azumi barni in mutu maza su kai ni ba mata ba, ai in kin ganni a lahira kaini aka yi" Ta faɗa tana ɗaukan Husainin ta miƙawa Mama ta ɗauki Hassan ɗin hannunta na karkarwa har yaron ya so kuɓucewa ya faɗi.

"Haba Inna ya za kike garaje a kan jaririn da aka haifa yanzu" Imran ya faɗa a fusace dan yanayin da Innar ta miƙo yaron tamkar wacce ta riƙo kashi.

"Jakar uban nan kayya, ɗan malafar uba ka ce fa, ashe dai kana magana rainin hankali ne yasa kake maƙe murya kamar ka haɗiyi rariyar tankaɗe, to dukana za kayi fa da hayayyaƙo min, yo wa ma ya sani ko haka bayanka yake irin na miciji abu a duhu, wa ma ya sani ko kai yaron ya gado na san ko haka naka bayan yake wannan yarinya Halima ba faɗa za ta yi ba, dan mu kaf danginmu babu masu fatar macizai"


"Me kika ce" Imran ya tambaya yana kafeta da idanunsa da suka masa jajir dan da ace matar nan bata da haɗi da matarsa wallahi sai ya shuka mata tsiya tunda ita bata san annabi ya faku ba.


"Yo ni kwa mai na ce, abin da wancan ya ce shi na ce kirarin mai tsoro" Cewar Inna tana kawar da kai gefe.


Hajiya kwa ta kasa furta komai dan yadda Innar ta jangwaɓar da yaron tamkar ɗan mutuntumi ba ɗan mutum ba.


"Ina ƴan uwan Sadiya Abdussamad wacce ta haifi ƴan biyu ɗazu?" Wata nurse da ke tsaye ta faɗa tana daga tsaye kan barandar ɗakin haihuwar sai wani yatsina take tana taɓe baki.


"Gamu nan" Cewar Ashrof tana miƙewa tsaye.

"Haba Asharofa bakya barin in bata amsa dai dai da ita, to in banda raini ta kallemu duk mun haifi uwarta ma mun yi jika da ita ta wani mere baki, ina ƴan uwan Sa'adiyya" Inna ta faɗa tana gwada maganar matashiyar.

Wani kallo nurse ɗin ta watsawa Inna, ta ce


"Ta falka ana buƙatar mutum ɗaya ya zo, dan sallamarta ma za a yi dan babu matsala" Ta faɗa tana gyara hijabinta da yake iya kafaɗarta.


"Bismillahi ku bari ni in je tun da ni kaɗaice banganta ba, ku duk a nan na sameku" Inna ta faɗa tana miƙewa ta gyara ɗaurin zaninta tare da ɗankwali, ta daidaita mayafinta.


"Haba tsohuwa ya ana neman masu ɗan gwaɓi -gwaɓi za ki taso bayan ke ma da za a taimaka miki kina buƙatar taimakon, ta ya za ki taimakawa wani?" Ta faɗa tana kama tsantsa.

"Ke ki kiyayeni da ganinki ko auren fari baki da shi amma sai a ɗaukeku aiki saboda kun yi karatun masu jajayen kunne, ku ke karɓar haihuwa kafin ku je gidan miji kun gama haddace komai, kun san ta yaya ake haihuwa har kun ɗinkesu tamkar wata ƙwarya, to ni nan har gozomanci na yi a ƙauyenmu" Ta faɗa tana hawa kan barandar da za ta sadata da
ɗakin haihuwar.



"Inna dan Allah ki bari ko Mama ko Hajiya su je mana ke fa ko ɗakin baki sani ba" Ashrof ta faɗa tana marairaicewa.


"Ke rufe min baki matambayi ai baya ɓata, zan tambaya kuma ma Allah na tuba ko daga bacci na tashi ai bazan kasa shaida Halima ba, duddubawa zan yi har in ganta, ke ɗin da gulma ajali in ba a yi ba a mutu" Ta faɗa tana wani gatsinen gefen hanci.


"Ki bari Mama ta je" Cewar Imran lokacin da ya ajiye ledojin hannunsa ya nufo wajen Innar dan ya ɗan bata baki, dan shi a kan matarsa zai iya yin komai ko da ba ya so. Mama kuwa ranta in ya yi dubu ya ɓaci ji take dama bata sanar da Inna Sadiya na naƙuda ba da yanzu duk haka bata faru ba ta rasa bakin magana tana da kara, bare kuma ƴar fari ce Sadiya a wajenta, kuma Inna sirika ce a wajenta ko da kuwa ɗanta baya raye uwa ce a wurinta.

Bare kuma Hajiya ita mai za ta ce tun da ba daga ɓangarenta Inna take ba.

"Lallai Imirana to wallahi in kuma ganin bakinka a ƙunshe kamar wani balangu a takarda, tun da har kana magana, kai da kake da aiki jajawur a gabanka, wato an haifa maka ƴaƴa biyu ai yanzu kamata ya yi ace kana kasuwa siyo sadakin gado (Raguna) Sai ka tsaya kana shiga shari ba shanu" Ta faɗa tana yin gaba ta barshi tsaye baki sake, tana shigewa ɗakin nurse ɗin ta ce "Mutum ɗaya ta taho dan wannan babu abin da za ta yi in ba surutu ba"

"To mun gode ki yi haƙuri kin san tsofaffin nan sai a hankali" Hajiya da ta baiwa Ashrof Hassan ta faɗa tana tahowa dan zuwa wajen Sadiya ganin Mama tana yiwa Inna kara ba za ta bita ba.

Ashe Inna tsayawa ta yi bata tafi ba, dan haka nurse ɗin na shiga ɗakin ta ganta a tsaye a hanyar shiba ɗakin dan akwai ɗan tazarar zuwa inda masu haihuwad suke.

"Ƴar nan an buga an barmu" Inna ta faɗa tana ƴar dariya.

."Nonsense" Cewar matashiyar tana jan tsaki ta juya abinta.

"Uwaki ce nosi wallahi ba dai ni ba, ƴar kare kawai da kai tun na haihuwa, ai duk da ban san abin da kika faɗa ba yanayin yadda kika yi maganar da kuma yadda kika yi tsaki na san ba abin arziƙi bane, to aniyarki ta biki"

Ganin Hajiya ta taho ya sa ta yi shiru, haka ta bi bayan Hajiyar suka tafi har suka je ɗakin.




Suna shiga ɗakin gadaje ne sun kai talatin da yake ɗakin hutu ne inda ake ajiye masu haihuwa bayan sun haihu shi asalin cikin ɗakin da ake haihuwar yana daga ciki amma ana iya jiyo ihun masu haihuwar da ke naƙuda saboda kusa ne ƙofa ce ta raba.


"Ke rufewa mutane baki, lokacin da kika je kika karɓo cikin wa ya raka ki wajen mijin, to yanzu ma haka zaki sha wahalarki ke kaɗai" Cewar Inna cikin ɗaga murya, jin wata mai naƙuda ta daddage tana ihu tana cewa a kawo mata agaji.

Kowa bin ta yake da kallo kawai wasu na dariya.




"Sannunku kun ji, sannunku da ƙoƙari yau kowa ta san yadda ta zo duniya da irin rigiji gabjin da uwarta ta yi lokacin haihuwarta, da wanɗanda yau ne suka yi ta fari da kuma wanɗanda sakewa suka yi, sai a wasa haƙora kuma domin cin sadakin gado "Ragon suna" Cewar Inna da ta buɗe muryar tana ta faɗa wa matan da ke wurin su kwa mai za su yi in ba dariya ba. Hajiya kwa gadon Sadiya ta wuce, ta bar Inna tana ta yawan yi, kallon nurse ɗin nan Inna ta yi ta ɗazu ganin tana darawa kan maganar da Innar ta yi Inna ta mere baki ta ce


"To fa harda su kaza a cin danƙo?' Bata jira cewar nurse ɗin ba ta wuce gadon Sadiyar tun kafin ta ƙarasa ta fara rafka uban salati
tana cewa.

"Wayyo Allah sannu Halimatus Sa'adiyya, sannu kin ji"


Wani uban bugawa kirji Sadiya ya yi da ta ga Inna.

"Na shigesu mai Inna ta zo yi kuma daga haihuwar ba dai ta zo bane har suna, in kwa haka ne to tabbas akwai matsala dan ta san kafin ranar sunan nan sai ta ginshi kowa" Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma sai ta ce.

"Yawwa Inna" Ta faɗa a hankali kamar bata so.

"Ikon Allah ya wuce mamaki sai kallo, yanzu ke ma Halima halin mijin naki kika koya? Magana kamar mutum baya so ni na kasa ganewa gayu ne hakan ko kuwa rainin hankali ne, ace Allah ya tsaga maka baki dan kake magana amma kake tauyewa baki haƙƙinsa" Cewar Inna lokacin da ta ƙaraso ta samu gefen gadon ta zauna da yake Halimar ma a zaune take ta jingina da filo.

Shiru Sadiyar ta yi bata ce komai ba.

"To ni in baki so zuwana ba in tashi baki alekum in koma inda na fito, dama dan ke zan yi, dan ɗana kuma marigayi, ai dai yau kin ɗanɗana haihuwar kin ji kin banbance tsakanin aya da tsakuwa kin kuma ƙara sanin muhimmancin ƴaƴa a wajen iyayensu da na iyaye a wajen ƴaƴan ma baki ɗaya.

" Ni ban ce ba Inna"



"A'a to in ma bakya so ai ba faɗa za ki yi ba, dama abu ɗaya ya kawoni amma kuma yanzu ya zama biyu, zuwa na yi in miki barka in miki jaje duk a tare"

"Jaje kuma Inna?"

"Yo jaje mana, barkar Hussaini zan miki, sai kuma in miki jajen Hassa...

Ai Inna bata ƙarasa ba sai Sadiya ta fashe da wani kuka mai cin rai, dan ita zaton ta Hassan ɗin mutuwa ya yi.

"Haba Inna ya zaki sakata kuka?" Hajiya Amina da take haɗawa Sadiya shayi dan ta sha ta ji ƙarfin jikinta ta faɗa cikin fusata dan abin na Inna ya fara wuce gona da iri.

"Yo ba dole ba in mata jaje ba wannan yaro da fatar bayansa take ta miciji ai abin a jajanta ne, ko ba haka ba bayin Allah?" Ta faɗa tana kallon mutanen ɗakin da wasu hankakinsu ke kan su babu wanda ya ce wani abu wanda ta basu dariya dai sun ɗan dara a ɓoye wanda kuma ta basu haushi sun ji haushi.

Dafe kai Sadiya ta yi tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya jin ba mutuwa ya yi ba dan ita sosai take jin son Hassan ɗin har ya fi na Hussainin saboda baiwar da ke tare da shi.

"Shi yasa aka hanaki shigowa amma kika shigo dama na san in banda surutu babu abin da za ki zo ki yi" Nurse ɗin nan da ta taso daga kujerarta da aka tanada domin su ta faɗa lokacin da ta ƙaraso wajen gadon domin yiwa Sadiya allura.

Hajiya kwa jin abin da Inna ta ce sai ta ce

" Allah kyauta"

Tana ga shan shayin, aka mata allurar, Inna dai bata ƙara yin magana ba har Sadiyar ta tashi suka je wurin nurse ɗin ta rubuta musu sallama tare da magungunan da za a siya. Da yake basu da kaya a ɗakin sai kawai kayan shayin Hajiya ta ɗakko suka taho Inna na yiwa ƴan ɗakin sallama tana ɗaɗɗaga hannu masu dariya suna yi ita kwa ko a jikinta dan ita iya gaskiyarta take komai ba dan wani abu ba.



Tafiyar da Sadiyar ke yi ce Inna da ke bin su a baya ta lura da hakan ya sa ta ce.

"Halima wannan tafiyar tantatan da kike yi fa sai kace wata wacce aka yiwa shayi?"

"Haba Inna yo wanda ya haihu har a haɗashi da ɗan shayi, ai haihuwa tafi gaban wasa, bare ita da ta haifi tagwaye kuma ɗinki uku aka mata a waje daga ciki kuwa huɗu aka mata dan bayan an ƙarata ta sake ƙaruwa da kan ta shi ya sa take tafiya...

"Halima ɗinki bakwai kenan aka miki sai ka ce wata ƙwarya? Yo ki ce min Sa'adiyya babu bayani yanzu Imirana zai daina wannan rawar kan da rawar ƙafar, tun da duk an miki faci a mafitar ɗa, shi kwa namiji dama wannan wurin yake wa da an ce babu to ke kuwa mace kin kaɗe a wurinsa har ganyenki dan wata zai nema ya aura"

"Faci fa Inna sai kace wata tayar keke?" Hajiya Amina da ta dakata da tafiya ta faɗa tana kallon Inna.

"Yo meye marabar dambe da faɗa Amina? Da bakinki fa kika ce ɗinki har bakwai to aikuwa bagaruwa ma bata yi wannan aikin ba"

Kunya ce da haushi duk suka kama Sadiya abin da Inna ke mata a gaban sirikarta idanunta har ƙwalla suka kawo.

Har suka fito babu wanda ya ƙara magana Inna kwa sai taɓe baki take yi abinta.




Suna fitowa suka samu an sanya komai a motar abokin Imran da Imran ɗin ya kira domin ya maida su gida, Inna tana hango Imran a zuciyarta ta ce


"Wannan ai shi ne sauna kira mana shasha sha in ka ga sakarai ku taho tare, wato dai har yanzu bai tafi neman sadakin gado ba (Raguna) Kar dai a ce ba zai yiwa yaran nan yanka ba amma kwa in haka ne da Imirana ya cuceni ya jayo min abin faɗa a ƙauyenmu, dan yo mai zan ce idan na gama zaman wanka zan koma ƙauye ne babu naman suna son ayi dani cewar ba a yiwa jikata yanka ba, ni da nufi na in a ban kashina in sanya a cikin mai (Kakide) Dan kar ya lalace amma ni ban ga yaron nan yana da niyya ba" Ta faɗa a zuciyarta lokacin da suka ƙaraso wajen motar.

Mama riƙe da Husaini, a baya, da Sadiya, sai Hajiya riƙe da Hassan wanda ta karɓa yanzu a hannun Ashrof, suka shiga gaba ita da Ashrof ɗin, Imran kwa dama a machine ɗinsa zai tafi.

"Inna can zaki shiga fa" Hajiya ta faɗa ganin Inna tana wani kalle-kalle

."Haba Amina ai ban ce miki ban sani ba, ko kina nufin a ɗan sahu zan koma ai wallahi ko babu wuri sai dai ɗaya daga cikinku ta haƙura ni in shiga" Ta faɗa tana shiga bayan Imran ya rufe musu ƙofar yana jin haushin Inna. Abid kuwa abokin Imran sai dariya yake abinsa dan sosai yadda Inna ke magana ya bashi dariya ya daɗe yana jin labarinta wajen Imran idan ta zo gidansa wai baya son matar takura masa take sai kuma ɗazu da yake bashi labarin zuwanta a waya, sai yau dai Allah ya sa ya ga Inna da idonsa.



Tun da suka hau kan titi take ta kalle -kalle abinta babu wanda ya ce wani abu, zuwa can ta ce

"Oh yau ai na ga ta kaina da na biyo Imirana, ko kallon titi ban samu na yi ba, yo ni da lokacin ma ina zaman garin nan ko unguwa zani in ba wani nisan azo a gani gareta ba bana hawa abin hawa da ƙafata nake yawo, yo in a ƙafa ne sai ka gama kallon gidaje masu kyau da abubuwa a hanya amma in a abin hawa ne sai dai ka ke ganin wulgawarsu wul-wul" Ta faɗa tana taɓe baki babu wanda ya tanka ta sai Abid da ke tuƙi yana darawa abinsa.

" Ka ji yaro ya sunanka?" Ta tambaya tana ɗan ɗaga murya yadda zai ji ta.

"Abid" Ya faɗa yana ƙunshe dariyarsa yana kuma jiran mai zai biyo baya dan ya tabbata sai ta masa ƙwasƙwarima a sunan kamar yadda Imran ya ce ta jagwalgwala masa suna wai Imirana.

"Ikon Allah wai na kwance ya faɗi, Abid kuma ka dai ce Abida wato sunan mata ma kai aka saka maka"

Sosai Abid yake dariya.





"Ka yi dariya man ɗan nan a rasa sunan da za a saka maka sai sunan mata"

Har lokacin dariya yake. A haka suka gangara hanyar da za ta sada su da gidan Sadiya, a cikin tafiya aka zo gidan da Imran ya shiga wajen abokinsa, aikuwa

Please Login or Register in order to submit comment