Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kasance to ya kan yi iya ƙoƙarinsa ya shawo kan ta dan kar ya rasa biyan buƙatarsa dan bashi da haƙuri ko kaɗan a wannan harkar, sai ya samu matar tasa ita ma mai burin faranta masa bata so ko kaɗan ta hana shi kan ta.


Ya kusa ƙarasowa gidansa ya hango wata ƙatuwar jakar bakko a ƙofar gidan, cikin mamaki yake kallon jakar da kuma neman dalilin ajiyeta a ƙofar gidansa.




Cikin sauri da azama ya ƙaraso har yana neman faɗuwa a machine ɗin dan ba ya ƙaunar abin da zai haɗa shi da kayan wasu, dan shi akwai tsare gidan ko maƙota iyakarsu gaisuwa tsakaninsa da su dama shi ba wani yawan magana yake ba bare zaman majalissa in har ba wurin aiki ya tafi ba to yana gida tare da iyalansa, sai ko idan ya je gaishe da Hajiyarsa. Yana faka machine ɗin ya ƙanƙance idanu yana kallon jakar, kallon da ya mata ma sai ya ji yana tsantsaninta dan sai ya ga duk ta yi wani ƙura, ko kuwa dan bai yarda da jakar bane oho ya ɗago kai yana son gano yadda aka yi jakar ta zo ƙofar gidansa sai ya ji wata murya tamkar daga sama an ce.

"Shikenan ma na huta ga Imirana nan" Shiru ya yi tare da runtse idanunsa da ƙarfi, jin an kirashi da sunan da ba ya so kwata-kwata, kuma ma duk duniya ya san babu mai kiransa da sunan nan sai kakar Sadiya wato Inna Azumi ita kaɗai ke kiransa, kuma ya shaida muryarta dan ko daga bacci ya tashi ba zai kasa shaida muryarta ba.



Shi ya rasa me yasa matar nan take son takurawa rayuwarsa, sam ba ya son wannan nuna ƙoƙon usulin da take nuna masa dan yana auren jikarta, shi ko ƴarta yake aure ba ya son takurawa amma ita ta kasa ganewa, sannan duk miskilancinsa na ƙin son magana da mutane sai da ya daure ya faɗa mata cewa Imran ake kiransa dan idan ta kirasahi da Imirana nan ji yake kamar ta kwaɗa masa gudum a kan sa.

"Ashe ma kana kusa har nake bin gidan maƙotanku ka ganni nan saukar yanzu tsal ɗin nan" Ta ƙara faɗa tana ƙarasowa wajensa ba tare da ta jira ya ce wani abu ba, cije gefen lips ɗinsa ya yi yana ji da a ce wani ne da ban ba tsohuwa ba yake damunsa kamar yadda tsohuwar nan ke damunsa da sai ya ɗau mummunan mataki.

"Eh" Kawai ya ce hakan ma dan ta kasa kunne ne ta gane me ya ce amma da gungune ya yi maganar.

"Allahu akbar Imirana har yanzu dai kana nan da wannan mugun halin naka, kai wane irin mutum ne da baka sakewa da mutane ku yi magana ma ta fatar baki kawai ni fa kakar ka ce ba sirikar ka ba" Ta faɗa tana kallon fuskarsa da ya haɗe ta murtuk kamar zai saki kuka.


"Sauri nake" Shi ne kawai abin da ya ce, shi ma dai da ƙunƙunen ya faɗa.

"Oh Allah na shiga aljanna na maƙale, yanzu baka ce min Inna ina wuni an zo lafiya ba sai ka zauna kana min magana kamar mai ciwon haƙori, ko kallon arziƙi na kasa samu daga wajenka"

Banza ya mata ya fara ƙoƙarin buɗe ƙofar gidan.

Inna Azumi kuwa baki ta taɓe, dan ta lura in ta ce za ta ga yadda take so to zuciyarta sai ta yi bindiga bata samu yadda take son ba, gwara ta lallaɓashi a rabu lafiya, bare ita da ta zo dandalar arziƙi.

"Sa'adiyyar ta sauka ne?" Ta faɗa tana kallonsa yana cire kwaɗo daga jikin ƙofar gidan.

Bai bata amsa ba a take ta tuna da katoɓarar da ta yu, dan dama Sa'adiyya take kiran Sadiya amma saboda kwainane irin nasa ya ce wai ta fiya ɓatawa mutane suna ganin baya iya faɗar Sadiya sai Sa'adiyya sai take cewa Halima saboda jarabar Imran ɗin dan duk ranar da ta zo gidansa haka zai yi ta mita a ƙunƙunen nan har dai ta ɗan canja sannan ta samu salama.


"Na ce Halimar bata sauka bane?" Ta gyara sunan dan ta matsu ta ji halin da jikarta ke ciki.

" Ta sauka" Ya faɗa a takaice yana tura ƙofar gidan ya shige ya bar Inna Azumi a tsaye baki sake, da ya shige ma sai da ya ɗan turo ƙofar.


"Yau na ga abin da ya isheni, a haka zan yi har kwana hamsin ɗin, ana wannan zaman doya da manjan, taɓɗi aikiwa duk abin amarya sai an sha manta wallahi ko me za ka yi sai na zaina ZAMAN WANKAN nan dan ban ga abin da zai sanya na fasa ba dan kana wannan fisfigar" Ta faɗa a ranta tana tura ƙofar ita ma ta shiga gidan tare da jan jakarta ta shigar da ita dakyar saboda nauyi, Imran da ya dawo domin ya ɗakkowa Sadiya zani saboda zannuwan sun yi kaɗan yana cikin sanya zanin a leda ya jiyo ƙaran jakar Inna Azumi tana janta ƙiiiii.

"Me yasa matar nan ta shigo min da ƙazamar jakarta gidana" Ya faɗa a ransa, ya yi sauri ya fito daga ɗakin ya dawo falo ya sanya hannu ya fusgi labule da ƙarfi ya fito daga ɗakin tare da rufo ƙofar dan ma kar ta yi gigin shigar masa da jakarta ɗaki dan ba ya jin zai iya bacci ma idan jakar tana ɗakin saboda ƙyanƙyami.

Baki sake Inna Azumi ke kallonsa har ya gama kulle falon, yana wani ɗaɗɗaga kai kamar ya ga kashi ya ce.


"Asibiti zan koma" Sai da Inna Azumi ta saurara da kyau sannan ta gane me ya ce.


"Yo ni ma ina na ga ta zama, ai ba zama wai an ɗaurawa karya zani, mu tafi sabitin in je in gan su dan can ma gidansu na fara zuwa a rufe, na zo nan ɗin ma ashe dai basu dawo daga asibitin ba"


"Eh" Kawai ya ce dan shi kamar mai ciwon baki haka yake ba ya son magana ko Sadiya sai ita ta yi ta masa hira shi dai sai umm da um, um kawai ko da zai yi maganar ma to ba wata mai yawa ba sai dai kuma ranar da ya ga dama sai ya yi maganar amma ba sosai ba.

Yana fitowa ita ma ta fito ya rufe gidan, aikuwa sai ga wani mai napep zai wuce ya tsayar da shi ya ce ya ɗauketa sai ya biyo bayansa.


"Wannan yaro da mugun hali yake" Ta faɗa tana taɓe baki ta shiga napep ɗin suka bi bayansa. Maƙociyar Sadiya kuwa da ta leƙo ganin Innar bata dawo ba, ganin Imran ya sa ta juya ta koma gidanta dan ita ko gaishe shi ta yi banza yake yi in ma yana amsawa to ita bata ji, sai ma ta daina gaishe da shi ganin rainin wayo da rainin hankalinsa dan ita tana mamakin yadda Sadiya take zaune da mutum kamar gunki.


Tun da suka fara bin Imran yake zabga uban gudu kamar zai tashi sama, da yake kuma unguwar kwana -kwana ta yi yawa ga ƙurunƙusai sai ya zama na Inna Azumi tana ta tangal-tangal a cikin napep ɗin saboda yadda ɗan sahun shi ma ke zuga gudu abinsa. Inna Azumi hannu ta sanya ta kama ƙarfen napep hagu da dama ta ƙanƙame dan ji take gabaɗaya kamar juyata ma ake yi. Idanu ta ɗaga ta sauke a kan me napep ɗin fa bai wuce shekaru sha tara zuwa ashirin ba, ga wani uwar suma a kan gashin ya yi cibir-cibir har da matajin kai a soke a jikin gashi, ga wani uban kiɗa da ke tashi a napep ɗin tamkar ma kiɗan jijjiga napep ɗin yake.


"Wai ni kai kwa yaro bahaushe ne?" Inna Azumi da bakinta baya shiru ta tambaya tana mai ƙuga maganar da ƙarfi yadda zai ji..

"Ke tsohuwa da wane yare na miki kama"?" Ya faɗa yana sakin wani uban fito da duk ƙaran kiɗan amma bai hana fitowar fiton ba.


"Ai tambayrka na yi dan na ga alama hausa bara ganka ba"


"Inyamuri ne ni, ko na miki ne, kina ciki"

"Amma wannan yaro an yi shegen yaro yanzu ka dubeni tsofe-tsofe da ni ka ce ina sonka? Amma gidanku ba manya"


"Sun ƙare" Ya bata amsar yana sanya hannu ya ciro matajin ya ɗan taza kan ya mayar ya soke.

"Baby kin yi shiru"


"Uwarka ce baby, wallahi tsakani na da kai Allah ya isa, ni Azumi na ga ta kaina.

"Ba dai shaƙa kika yi ba Hajiya, ban da ƙauyanci dan na ce baby ba wai yarinya nake nufi ba, wasan kaka da jika ne fa"


"Ƙauyancin uban wa? Na ce ƙauyancin uban wa, to tun kafin a haifi uwar mai sabulu farfela take da farinta" Ta faɗa tana jin kamar ta saki fitsari dan gabaɗaya an dagula mata lissafi ga yunwa ga wani fitsari da ya cika mata mara ga wannan jijjigar da napep ɗin ke yi sai ta ji a ranta ta fara ɗan da na sani kaɗan ba da yawa ba na tahowa ZAMAN WANKA, da tana gidanta da yanzu ta ci ta ƙoshi tana bacci ko kuma tana kama ƴan kuɗaɗenta daga masu zuwa siyan mai da ƙuli amma wani ɓangaren na zuciyarta sai ya bata ƙwarin gwiwa.


"Kar ki karaya bayan wuya sai daɗi, daga yau ne fa wahala ta ƙare za ki fara cin kayan daɗi" Wani murmushi ne ya suɓuce mata har sai da ta ɗan rausaya kai.


"Ka daina zabga wutar nan haka gudun ya yi yawa"

"Bakya ganin yadda wanda muke bi yake gudu kamar zai tashi sama.





"Rabu da Imirana mugun hali ne da shi ka yi tafiyarka a hankali ka ji"

"In ya ɓace mana ke zaki kaimu wajen da za ku je?"

Shiru ta yi bata ƙara magana ba, wata kwana Imran ya shiga dai dai wani gida ya faka machine ɗin ya sauka ya faka machine ɗin ko kallon su Inna bai yi ba ya tura gidan ya shiga.

"To ki fito mana tun da mun zo ashe ma babu wani nisa sosai"


"Nan ne asibitin?"

"Asibiti kum?"

"Eh mana asibiti za mu je"

"Haba Hajiya nan ya miki kama da asibiti nan ai gida ne"

"Gida kuma, wai ni me ya sa Imirana ya raina mutane ne haka, ya za a yi ya shige wani gida ya bar ni ko bayani ba zai mini ba" Ta faɗa tana saurin sakkowa daga napep ɗin ta ce mai napep ɗin ya jira ta, a fusace ta tura ƙofar ita ma ta shige tana shiga ta ga wani ɗaki da ke a farkon shiga gidan, bata yi wata- wata ba ta bankaɗa labulen kawai sai ganinta suka yi bakam ta shigo kamar an jefo ta.

Wani kallo da Imran ya jefawa Inna Azumi shi ya sanya ta wayance ta ce


"Ikon Allah ashe ba mu zo asibitin ba, wallahi duk zatona ɗakim haihuwar ne nan" Ta faɗa tana saurin juyawa ta fito da sauri dan shi da wani da alama abokinsa ne ya miƙo wa Imran ɗin zamzam a robar zamzam. Abokin kuwa yadda Inna ta yi ya matuƙar bashi dariya, Imran kwa tsaki ya yi ya fito ya hau machine ɗin.

Inna kuwa mai napep ganin ta fito da sauri sai abin ya bashi mamaki har ya so bashi dariya.

"Kin masa magana?" Ya tambayeta lokacin da ta fito ta shiga napep ɗin.

Inna da gabaɗaya take a ruɗe ba wai kallon da Imran bane ya sa ta gigice ba, abokin nasa ne babu kaya a jikinsa daga shi sai ƙaramin wando wanda ake kira inpant, to har ga Allah bai san ya yi wawan zama ba ashe Inna ta hango abu ya leƙo ta ƙafar wandon wannan ne abin da ya ruɗa ta dan ita yaushe rabonta da ta yi ido huɗu da bananar ma ta manta, dan su yanzu an tsufa, ganin bananar abokin Imran ne ya ruɗa ta, hakan ne ya ruɗa ta ta dawo da sauri har tana neman yin tuntuɓe. Dan da alama ɓa abokin nasa gwauro ne dan ɗakin nasa a bakin ƙofar gidan ne daga ciki kuma tana jiyo hayaniyr mutane daga cikin gidan.




" Ashe ruwa zai kama" Ta faɗa dan ta waske amma a ranta sai salati take ko idanu ta rufe sai ta ga abu kawai. Da haka dai har suka iso asibitin bayan sun sha uban gosulo. A wurin da aka tanada dan ajiye napep a nan ya sauke Inna haka ya yanka mata uban kuɗi ta bashi, dan Imran ko tsayawa bai yi ba bare ta sa rai zai biya kuɗin napep ɗin.


Tana bawa mai napep ɗin kuɗi ta fara sauri-sauri gudu-gudu dan ta tarar da Imran dan machine ana iya zuwa da shi har ƙofar ɗakin da mutum zai je da ke asibitin na gwabnati ne, ashe da ɗan tazara zuwa ɗakin haihuwar dan haka kafin Inna ta kawo ta gama jigata dan ma tana iya hango Imran ɗin da yake wurin babu kwana bare ya ɓace mata.


"Oh ni da bani da kuɗi yau da na tagayyara, wannan yaro ko kaɗan bai san mutunci ba, uwarsa kwa ba haka take ba lallai albasa bata yi halin ruwa ba, na ɗauka shi zai biya min kuɗin tun da shi ya tsare ɗan sahun amma sai ni na biya, ko ma ya tsaya idan ma ba zai biya ba, sai ya ce Inna ki biya kuɗin amma shiru maƙatau babu niyya wai ango ya kwana da wando" Take ta zancen zuci har ta ƙaraso wurin ɗakin haihuwar.



🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼

(KWANA ARBA'IN)


NA



MAMAN AFRAH


🅿️3️⃣



Ƙarƙashin bishiyar da aka tanada dan zaman masu zaman jinya can ta nufa inda ta hango Imran ya yi, dakyar take iya ɗaga ƙafarta dan lokacin har an yi sallar la'asar amma Inna ba azahar ba la'asar dan wajen sha biyu ta baro ƙauyensu. Da jan ƙafa ta ƙaraso wajen da suke zaune a tabarma, dan tun daga nesa ta hango Hajiya Amina mahifiyar Imran, Ashrof ƙanwar Sadiya, sai kuma Ruƙayya mahaifiyar Sadiya, sai Imran da ke gefen mahifiyarsa da alama magana yake mata

"Wash Allah nah" Cewar Inna kamar an shaƙe mata wuya tana neman kan tabarmar ta zauna daɓas. Da mamaki suke kallonta su duka, Inna Azumi kwa saboda wahala ta ma manta da cewar ba a san da zuwanta ba.


"Inna!" Ashrof da Mama Ruƙayya suka faɗa da mamaki.


"Rakiya dan Allah ku taimaka min da ruwa wallahi maƙoshina duk ya bushe ƙamas ko yawu na haɗiye sai na ji wucewarsa wani garrrr yana cin birki saboda bushewar maƙoshin a maimakon na ji wucewarsa midik"


"Humm ai bari ba shegiya bace da ubanta" Cewar Imran a zuciyarsa dan yadda idanun Innar suka koma sun wani ƙanƙance kaɗai ya isa ya sanya ka dariya duk ta fita hayyacinta, ga gwaggwaron gaban goshin ya koma gefe har ɓangaren hagun ɗin ɗankwalin ya zamo ya ɗan rufe gefen idonta amma duk bata kawo a ka ba.


"Inna wai kin ganki kwa kamar wata maroƙiyar" Ashrof ta faɗa tana tuntsurewa da dariya.


Inna ji ta yi ba za ta iya magana ba, amma da sai ta ji amsa dai dai da tambayarta, amma ina! Babu hali. Hatta Mama Ruƙayya da Hajiya Amina dariyar suka ƙunshe ganin Innar a birkice sai wani faman nishi take kamar ta yi tseren gudu.


"Gashi Inna" Mama ta faɗa tana miƙa mata pure water guda ɗaya da ta ɗakko a cikin leda.


"Haba Rakiya kamar wata almajira, za ki bani ruwa ƙwalli ɗaya" Ta faɗa a fusace dan ita ba ma ruwan ɗaya bane ya ɓata mata rai, so ta yi Mamar ta ce mata ga abinci dan ta tabbatar yanzu idan ta sha ruwan nan cikinta ƙullewa zai yi.

Mama kwa faranti ta ɗauka ta ɗora ruwan har huɗu ta miƙa Innar, har lokacin tana mamakin zuwan na Inna Kano da ma yadda aka yi ta gane asibitin da suke.


Ruwan ta kalla guda huɗu ga cikon na biyar ɗin a hannunta,ta ce.


"Kai Allah na tuba wannan ruwa kamar wata saniya ina zan kai shi ma son in sha ya ƙulle min ƴaƴan hanji, mu wallahi zamanin da ba haka muke yiwa baƙo ba sai mun fara gabatarwa baƙo sanwa (Abinci) Kafin mu kai ga bashi ruwa, amma yanzu zamani ya banbanta halayya wani wurin ma sai ka je baƙunta ka tafi amma ko ruwan ma ba zaka samu ba to amma ke kin yi ƙoƙari ma da kika bada ruwa har biyar da babu gwara ba daɗi amma da ace ko kaɗan kuna haɗawa baƙi da abinci duk ƙanƙantarsa ai da hanau ƙwara mannau" Ta faɗa tana sauke idanunta a kan wasu food flaks har guda uku da ke ajiye a gefe.


"Wai Inna dai ko yunwa kike ji?" Ashrof ta tambaya tana kallon Inna da sheƙiyanci ganin duk idanunta ya faɗa bakin nan a bushe kamar mai azumin nafila.


"Yo Allah na tuba yunwa sai ta karni za a san ina jinta, cikin nan nawa kaɓar an yi shara ko motsin ɗiyan hanjina bana iya jiyowa duk sun yi likimo ko kuwa suma suka yi" Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce.

"Asharofa kar fa ki min fassara ato, ni ba wai ina roƙon a bani abinci bani kawai dai ina koyawa uwarki abinda ya dace ta yi ne, idan ta yi baƙi amma ba wai kaina nake yiwa tanadi ba"

"Wannan tsohuwa da shegen ɓatawa mutane suna take, wai asharofa sai ka ce wata tinkiya, ni ta ce min Imirana kamar wani gatari, sannan ko Sadiya ma Sa'adiyya ko kaɗan bata iya seta bakinta kamar wacce aka gutsirewa gefan harshe" Imran ya faɗa a ransa yana aika mata da harara a ɓoye.


Kunya ce ta rufe Mamar Sadiyar jin furucin da Innar ta yi, ga sirikinta ga Babar sirikin amma ko kaɗan Innar bata san kunya ba.


" To da yaushe ma ta zo, ko gaisawa fa ba a yi ba amma har ta ɗora min laifin rowa, ni ban taɓa ganin tsohuwa mai rangwangwan irinta ba" Mama ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce.

"Inna wallahi ina shirin baki abinci ne ka wai dai wani lokacin an fi fara gabatar da ruwa kafin abincin ne"


"A'a Rakiya a lokacin zafi ba amma a lokacin sanyin nan ai an fi jin yunwa a kan ƙishirwa, amma ba wai ina nufin ina cewa yunwa nake ji a bani abinci ba, kawai da ku ɗauka hira ne muke kowa yake faɗar abinda ya dace a yiwa baƙo idan ya kai ziyara " Ta faɗa tana bin su duka da kallo irin ko ba haka ba.

"Inna duk nan fa babu bare ko ma abinci kika ce a zubo miki ai baki yi laifi ba duba da irin nisan tafiyar da kika yi daga garinku zuwa nan" Hajiya Amina ta faɗa tana kallon Inna Azumi.



"Allah sarki ƴar nan,ko da na ji shi dama tunani ai baiwa ne, kin ga ke kin fi hango jirgina wallahi dama yunwa nake ji tamkar an mini sata a cikina, ayi maganar nisan ma, gashi na je gidan Rakiya a rufe daga nan na tafi gidan Halima can ma a rufe, haka dai na haɗu da taƙadarin yaron nan Imirana, ya ringa gudu da mai adaidata sahun da ya ɗakkoni na binsa yadda kika san a filin tsere haka ya ringa gudu, ko yanzu daga bakin babbar ƙofa (Get) Zuwa nan daƙer na ƙaraso a ƙafafuna, in da kara ai akuyar gidan sirika ma iya ce, ko ni ba uwar Halima bace ai Kakarta ce in banda dalili mai sa a leƙe gindin sirika mai zai kawoni gidan Imirana" Ta kwashe yadda aka yi ta faɗa tana kallon Hajiya Amina.


"Da me ya kai ki bin Imran yaron da ni ma addu'a nake binshi da ita a kan Allah shiryeshi wannan halin nasa tun yana yaro, kin yi sa'a ma da har ya yarda kika biyo shi asibitin bai tafi ya barki a ƙofar gidan ba, ko ya ɓace muku da ke har napep ɗin ku yi ta bulayi a titi ƙarshe mai napep ɗin a ajiyeki a inda kuɗinki suka ƙare"Cewar Hajiya a zuciyarta a fili kuma sai ta ce." Ta faɗa tana bin su duka da kallo irin ko ba haka ba.

"Inna duk nan fa babu bare ko ma abinci kika ce a zubo miki ai baki yi laifi ba duba da irin nisan tafiyar da kika yi daga garinku zuwa nan" Hajiya Amina ta faɗa tana kallon Inna Azumi.



"Allah sarki ƴar nan,ko da na ji shi dama tunani ai baiwa ne, kin ga ke kin fi hango jirgina wallahi dama yunwa nake ji tamkar an mini sata a cikina, ayi maganar nisan ma, gashi na je gidan Rakiya a rufe daga nan na tafi gidan Halima can ma a rufe, haka dai na haɗu da taƙadarin yaron nan Imirana, ya ringa gudu da mai adaidata sahun da ya ɗakkoni na binsa yadda kika san a filin tsere haka ya ringa gudu, ko yanzu daga bakin babbar ƙofa (Get) Zuwa nan daƙer na ƙaraso a ƙafafuna, in da kara ai akuyar gidan sirika ma iya ce, ko ni ba uwar Halima bace ai Kakarta ce in banda dalili mai sa a leƙe gindin sirika mai zai kawoni gidan Imirana" Ta kwashe yadda aka yi ta faɗa tana kallon Hajiya Amina.


" Humm Inna kenan, a nunawa na rigingine farin wata, ai ni sai dai na bada labarin Imran, dan ma ni yana raga min kasantuwata mahaifyarsa, kema da gangan ne ai, duk wanda ya sayi rariya ai ya san za ta zubda ruwa, me ya kai ki bin Imran yaron da, ni ma addu'a nake binshi da ita a kan Allah shiryeshi wannan halin nasa tun yana yaro, kin yi sa'a ma da har ya yarda kika biyo shi asibitin bai tafi ya barki a ƙofar gidan ba, ko ya ɓace muku daga ke har napep ɗin ku yi ta bulayi a titi ƙarshe mai napep ɗin a ajiyeki a inda kuɗinki suka ƙare"Cewar Hajiya a zuciyarta a fili kuma sai ta ce.

"Sannu Inna gaskiya kin yi ƙoƙari, wallahi kai kuma Imran ka kiyayeni a kan me za kake gudu baka ganin tsohuwa ce?" Hajiya Amina ta faɗa tana kallon Imran da ke wani haɗe rai yana kauda kai gefe irin bai yi laifin ba ma.

"Hajiya baki san yadda tsohuwar nan ta takura min bane, ta kasa fahimtar ni ko ganinta ban son yi" Cewar Imran a zuciyarsa a fili kuma sai ya ce.

"Sorry Hajiya" Ya faɗa yana sosa ƙeya.

"Au Allah, wato sorre, a soron gidanku na kwana, kai kenan taƙidarancin naka har uwarka bai baka bari ba to Allah wadaran naka ya lalace wallahi" Cewar Inna tana jijjiga kai irin na ga abinda ya fi ƙarfina.

Mama kanta ta kawar gefe tana jin wata irin kunya ganin gabaɗaya Inna tana kwance musu zani a kasuwa.

"Ina za a kai wannan abin kunyar? Ta faɗa a ranta.

"Haba Inna ki yi shiru dan Allah" Ashrof ta faɗa jin ɓaran-ɓaramar Inna ta yi yawa.



"Ashrof miƙo mata abincin" Mama ta faɗa dan ta kawo ƙarshen maganar.

Idanun Inna a kan kwanukan abincin wani mai jan murfi da ratsin yellow shi ya fi tafiya da hankalinta dan tana tunanin wataƙila a samu abinci mai daɗi a ciki, cikin ikon Allah kwa sai Ashrof ta miƙo mata shi, hannunta har karkarwa yake wajen karɓar tana washe baki.


"Yawwa Asharofa kamar kin san shi nake hari shi ne a raina" Cewar Inna a zuciyarta lokacin da ta kama kwanan da hannu biyu ta buɗe.


Fuskar Inna ce ta sauya har suka lura da hakan, ba komai ya sanya fuskar Inna sauyawa ba sai arba da ta yi da wake da shinkafa.

"Ni

Please Login or Register in order to submit comment