Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kalli Hajiya Fatee.

“Lallai sai kin tashi tsaye, ta mallaki danki Mallaka bata wasa ba, kuma idan ba ki yi da gaske ba abu ne mai wahala ya sake yin aure ko da kuwa ta mutu”

“Ka ji irinta ba, shedaniyar yarinyar na sha wahalar yarinyar da can babu ruwansa da ni ma, sai da na tashi tsaye, dan abun da ubansa ya bar min duk a can ya kare, ba dan Allah yasa nasa gadon yayi albarka kuma ya samu babban aiki ba da yanzu mun kade”

“Toh lallai dai gata nan ko yanzu a tsaye take akan danki”

“Dan Allah a zaunar da ita, idan da dama ma a kwantar da ita a saka ta bacci ko a sumar da shegiya”

Malamin yayi dariya

“Ai tun da kika zo nan komai zai zama tarihi Hajiya, ki bada kudin karan alkamin kawai a saka aiki”

Da sauri ta bude jakarta ta dauko kudin da ba zai wuce 30k ba ta aje masa.

“Ga wannan ban zo da kudi mai yawa ba, amman dai a fara saka aiki da wannan idan zan dawo zan ciko jaka da yardar Allah”

“Toh shi ke nan ba matala idan na gama aiki na hada abubuwa zan kira na fada muku sai ku zo ku karba ko kuma ku aiko ko kuma ni da kaina na aiko muku”

A bisa wannan suka yi masa sallama suka fito suka dawo cikin motar. Direban ya a kama hanya, ba su yi nisa da garin ba suka rage gudu ganin an tsayar da motocin dake gabansu a zatonsu sojoji ne, hankalinsu be tashi ba sai da suka fara jin harbe harbe wasu na ihu.

“Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un Bandits ne”

Direban ya fada, da sauri Hajiya Fatee ta kalli Hajiya Kaltume da cikinta ya soma murdawa.

“Mun shiga uku mun lalace, ya zamu yi?”

“Shiyasa bana son shigowa dajin nan gari gaba daya ya lalace a yanzu”

Cewar Hajiya Kaltume ido na raina fata.

“Kai direba ya zamu yi?”

“Hajiya ni ba ku kuka kawo ni nan ba, kuma gashi motoci a bayanmu balle mu juya”

Maganar yake yana leken motocin dake bayansu ga karar bindigar sai matsosu take.

“Toh ko dai mu kira Malamin nan mu fada masa”

Hajiya Fatee da fitsari ya fara zubo mata ta kalli Hajiya Kaltume.

“Ya mana me? Soja ne shi ko dan sanda?”

“Ya turo aljannu su dauke mu mana, Hajiya mutanen nan suka kama mu ai mun shiga uku, kuma na cewa Alhaji me? Daga zuwa sulhun aure!”

Cikin tashin hankali Hajiya Fatee ta ce

“Aljannu suka dauke mu ai shikenan mun bar duniya kuma kara ma wadannan da aljannu dan su kai mu za su inda babu kowa su aje, ko su kai mu China aljanni ai ba zai dauke ka ya aje ka nan kusa ba sai wata duniyar”

Hajiya Kaltume ta fashe da kuka tana neman agajin Allah.

“Allah ka yafe mana Allah ka dube mu Allah Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, ni har na bata zane”

Direba ya bude kofar a hankali ya sulale ya yanki daji cikin ciyayi. Hajiya Kaltume ta saka kalma shada, Hajiya Fatee ta kama mata suka karasa suka kallon juna kowacce na kai hannu ta taba yar'uwarta. domin sun san yadda suka ci suka koshi nan ba za su iya gudu ba ko sa sun gwada hakan.








____________________


Hmmmmm masu karatu kun taba gani ko jin mugun kishi da bakar hassada irinta ta Hajiya Kaltume?
Ni dai Hurriya ta ba ni tausayi domin rayuwa gurin da baka bukatarka yana da wahala, musamman idan babu uwa a kusa.

Ta wani bangaren kuma Iyami tana da laifi daga zuwa aiki sai ki aure mijin mata? Ina laifi ki rumgume talaucinki ki shafawa kanki lafiya, yanzu wa gari ya waya...?

Mu hadu da ku page din gobe, amman kamin nan ina son na ga Comments baza-baza line by line in ji Bature...
[10/18, 5:35 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆
                 

𝐁𝐲   𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲


𝗣𝗮𝗴𝗲 7️⃣

Ana kiran sallah asuba ta sauko daga kan gadon ta nufi kofar dakinta ta bude ta fito, a hankali ta sauko downstairs, tana isa bakin kofar falon bata tsaya komai ba ta kai hannu zata bude kofar.

“Ina zaki je?”

Ta juyo da sauri domin bata yi tsammanin wani zai iya fitowa at this early ba.

“Fita zan yi”

Ta amsawa Namra. Cikin mamaki Namra ta wara ido.

“Asuba ne fa”

“Na sani, Hijab zan dauko na yi sallah”

“Haba Hurriya shiga dakina ki dauko nawa mana, saboda Hijab sai ki fita tun a asuba ki koma part dinku kamar wata bakuwa, ke a gida kike fa”

Hurriya ta dan sauke kai kasa daga barin kallon yayarta wadda ta bata shekara uku da haihuwa. Namra bata sake ce mata komai ta nufi kujerar da ta zauna a jiya ta dauki agogonta da assignment din da ta yi, sai da ta kusa hayewa  sannan Hurriya ta rufa mata baya, cikin ladabi da natsuwa ta shiga dakin Namra ta tsaya jikin kofa, haka Hurriya take bata sakewa da mutane tana da wahalar sabo, musamman idan ta san zaka tsangwame ta ko ka yi mata fada. Namra ta juyo ta jefo mata hijab din cikin hanzari Hurriya ta cafke.

“Akwai carpet din Sallah a can?”

“Aa babu”

Namra ta dauki nata ta jefa mata Hurriya ta sake cafkewa ta juya ta fice daga dakin zuwa dakinta. Bata shiga nata dakin ba sai da ta kwankwasa kofar dakin Hamad tana kiran sunansa.

“Na tashi”

Ya amsa mata daga can ciki, sannan ta wuce dakinta ta maida kofar ta rufe. Tun bayan da ta yi Sallah bata sake fitowa ba sai da ta auna lokacin makaranta yayi mata, sannan ta bude kofar a hankali kamar wata bakuwa ta rufe ta nufo hanyar saukowa kasa gabanta har faduwa yake kar ta hadu da Musib ko dan'uwansa Miwan balle kuma Momy da ta san bata ishe ta kallo ba. Sai dai ta yi rashin sa'a Momy da duka yaranta suna falon zaune, abun da bata saka tsammani ba domin Momy bata tashi da wuri sai idan tana bangaren Appa shi ma da zarar ta kai masa abun karyawa zata sake komawa bachi kuma babu mai tashinta sai gidan maigidan ne da kansa if not kowaye ya tasheta zai gane kurensa a ranar.

“Baka fada min zaka zo ba, ai da na saka an shirya mana abinci mai kyau”

Cewar Momy tana kallon kyakkyawan saurayin dake zaune a kujerar dake facing nata, kyakkyawan saurayin farin saurayin mai jini a jika ya girgiza mata kai yana duba agogo hannunsa.

“Noo Momy na gode tafiyar ta gaggawa ce, yanzu zan kama hanya, kawai na ce bari na biyo mu gaisa ne”

Momy ta yi murmushin kasaita irin na manya mata.

“Daman na sani, abinci idan ba na Hajiya Turai baka ci na kowa”

Ya dan fadada fuskarsa da murmushim da ya kara masa kyau da haiba yana daga kai ya kalli Hurriya dake saukowa. Momy ta dan juya ta kalleta kadan ta dauke kai irin ba ki isheni kallo ba din nan.

“Momy ina kwana”

Hurriya ta gaisheta cikin ladabi Momy har ta yi kamar ba zata amsa ba sai kuma ta ci albarkacin bakonta amsa ciki ciki kamar an mata dole.

“Yaya Musib ina?”

Ya amsa, ta juya gurin dan'uwansa shi ma ta gaishe shi, sai ya amsa mata fuska a sake kamar dan'uwansa, ta kalli Namra ta gaishe ta kamin ta rufe baki Namra ta amsa tana mata an tashi lafiya, daga karshe Hurriya ta cike gaisuwarta da bakon da take kyautata zaton yana da muhimmanci a gurin Momy da yaranta ganin yadda suke ta murna da ganinsa kuma suka fito dukansu da sanyin safiyar nan suka zauna a falo just because of him.

“Ina kwana”

Ya d'auki 'yan dak'ik'u kafin ya amsa gaisuwarta, shi ma kuma ba da baki ba kai kawai ya daga mata and light smile. Binta yayi da kallo har ta wuce ta gabansa ta nufi kofar fita.

“ƴar Mijina ce, kanenta ne ka ga ya fita dazun”

Momy ta fada masa domin ta san ba zai tambaya ba, ta san kallon da yake mata be wuce na neman sanin wacece ba, dan zuwan da yake gidan jefi jefi be taba ganinta ba, haka ma bata yi masa kama da masu aikin Momy ba balle yace ko yar aiki ce, ba zai ce ya san kowa a gidan ba, amman yadda ya san familynsu musamman Momy idan har ta bawa wani damar shiga ma a falonta to yana da muhimmanci a gareta, sai dai abun da be sani ba wannan shigar ta dole ce ta cilastawar Appa ba dan Hurriya tana da muhimmanci a gareta ba.

“Yaya ance an daga bikinka”

Miwan ya tambaya yana kallonsa. Mutumen da Miwan ya kira da Yaya ya juyo ya kalleshi.

“Ka aje wannan Yaya aside ka kira ni da real sunana Jamal”

Momy ta yi murmushi mai sauti.

“Haba dai Captain dukansu fa kanenka ne ta ina  za su iya kiranka da sunanka kai tsaye, dole sai da girmamawa”

“Wallahi na tsani wannan Yayan na fi son a kira ni da sunana na gaskiya”

Ya amsa mata da murmushi sannan ya mike tsaye sai zuba kamshi yake. Namra ta mike tsaye kamar sauran yan'uwanta tare da fadin.

“Tafiya nan da nan Yaya ba zaka dade ba”

Da hannu ya nunata.

“Yanzu na gama yi ma Miwan gargadi shi ne ke ma zaki ďana ko?”

Sai duk suka saka dariya ban da shi da ya nufi kofar fita yana yi ma Momy sallama. Momy ta mike tsaye ta rako shi har bakin kofar falon Miwan da Musib suka karasa gurin da ya faka motarsa suna masa a sauka lafiya, Momy da Namra kuma na tsaye jikin kofar har sai da ya shiga motarsa yayi musu horn ya fice sannan suka dawo cikin falon.

“Captain baka iya masa, Allah kadai ke masa daidai, komai ka yi sai yace ba haka ba ga zuciya abu kadan ya fusata shi”

“Ai gaskiya Ammy tana hakuri da shi”

Cewar Namra Momy ta ce.

“Toh ya zata yi haka Allah yayi shi, kuma shi kadai ya bata daga ita har Yayana magajin da suke da shi kenan”

“Kuma Allah ya hada jininsa da ke, duk ya zo garin nan sai ya zo nan”

“Kin ji Namra da wata magana, uwa daya uba daya ai ta wuce wasa, ko kin manta alakata da mahaifinsa ne, ga kuma Hajiya Turai a bata da kawa a familynmu sai ni”

“Duk da haka dai Momy, Wallahi idan baya ra'ayinki ba zai zo ba, ba ke kadai kuke uwa daya uba daya da mahaifinsa ba amman ke kadai ce yake zuwa gurinki, duk ya zo gurinsu Hajjo sai ya zo nan, waya ma akai akai yana yawan kiranki”

“Haka kuma da maganarki, je ki taso masu aikin nan yau muyi tashi dole su zo su fara aiki, ke kuma ki shirya ki wuce makaranta”

“Okay”

Ta amsa sannan ta nufi sama, Momy ta dasa hirar da su Miwan.

“Ku yaushe zaku koma hutu ne wai?”

“January nan zamu koma, ni ai gaba daya na samu na bar garin nan na huta”

Musib ya ce.

“Kai gari kake son bari, ni Wallahi kasar ce ya isheni, ba dan halin Appa ba kamar mu zai hana a fitar waje, maza ne mu fa kuma yawanci yayan sa'ainsa duk suna waje suna karatu amman ya hana a fitar da mu kuma shi ba zai fitar da mu ba”

“Jami'ar nan kawai zaku kare a nan, amman masters da duk wani abu da zai biyo baya a waje zaku yi shi, na gaji da halinsa shi har yanzu be gama jefar da wannan halin nasa na da can ba, kuma a yanzu tun da na fahimci baya bin ra'ayi toh kowa yayi nasa ra'ayin kawai, duba yadda ya daga mana hankali jiya saboda kawai Hurriya ta zauna a nan”

“Wai me yasa ba zata bi mahaifiyarta ba?”

“Kai kana ganin uwarta zata yarda ta bita su zauna a can? Ai ba zata yarda ba tana ganin ga gidan arziki”

“Toh ai ko da sun koma Appa zai mata komai”

Musib ya sake fada.

“Amman dai ba kamar idan tana gidan nan ba, kuma Kaltume ba zata yarda Alhaji ya yi haka ba, yadda ba ta bar shi ya kula da yarsa Sapna ba haka ba zata bar shi ya kula wadannan yaran ba matukar suka bar gidan nan”

Miwan ya ce.

“Wai Momy saki nawa yayi mata ne?”

“Ina ruwana? Balle na tambaya can ta matse musu idan uku ne sun hutu, idan daya ne ma ya dawo da ita duk ruwansu ne ba nawa ba, ni ta harkokin gabana nake shirya ba a kaina take zaune ba, daga ita Iyamin har Kaltume babu wadda zata nuna min komai gaba da baya, mu da talauci sai a baki shi ma dan ambata kawai, su ko babu wadda bata tashi a cikinsa ba, ni ko babu wadda be san ubana ba a garin nan ba”

“Ai shiyasa Hajiya take shakkarki, yadda take ma Amma da yayanta bata mana haka”

“Ai bata ga fuska ba ne, ita kanta ta san na fi karfinta ta ko'ina, kuma ni bana jiran abun Alhaji ita da Iyamin dai suka dogara gareshi”

Hira sosai suka yi ta yi Momy na koda kanta a garin gusau ma jin take ba ko wace matar mai kudi ce sa'ar yinta ba balle kuma cikin gidan Alhaji Haruna Mai Yadi.


HURRIYA POV.

Tana shiga part dinsu sai kewar Amma ya kara daduwa a ranta, ta san da a jiya ne da kwanakin baya da Amma take gidan sai dai ta fito daga dakinta ta sauko kasa ta yi breakfast ba dai taje wani bangaren ta kwana ba har tana fargabar arba da Momy. Kujera ta nufa ta zauna ta rike hannayenta hawayen dake idonta suka zubo mata.

“Huriyya...”

Ta kalli kofar kitchen din da sauri tana zabura domin ta tsorata ba yi zaton akwai mai kallonta ba. Da sauri ta cire gilashin idonta ta share hawayenta da hannu biyu ta mike tsaye.

“Ya Yasir yaushe ka shigo?”

“Tun dazu abun karyawa muke hadawa da Hamad”

Ta fara takawa ta nufi kofar kitchen din da yake tsaye.

“Kuka kika kwana kika yi jiya ko? Idonki har ya kumbura, kuma kin san matsalar idonki why zaki jawa kanki wata matsalar”

“Yaya idan na tuna Amma bata nan sai na ji babu dadi, kukan zo min yake”

“Addu'a zaki yi, kuma ki daina damuwa Amma zata dawo da yardar Allah”

“Haka Appa yace maka?”

Ta tambaya tana kallonsa wasu hawayen na sauko mata zuciyarta kuma cike da daukin ya amsa mata da eh zai haka yace.

“Aa haka dai nake sashe, kuma ni na san haka zai faru ko dan ku, baki ga yadda hankalinsa ya tashi ba jiya saboda fada miki da Khairi ta yi, karki so ganin fuskarta yau sai da na kumbura mata baki”

Hamad dake can cikin kitchen yana juya plantain yayi murmushin jindadi jin cewar an kumburawa Khairi fuska. Hurriya kuma zuciyarta ta cika da tausayinsa.

“Da baka doke ta ba Yaya ai gaskiya ta fada min”

“Ba haka ya kamata ta yi ba, kuma be kamata daga ke har ita ace kuna shiga maganar manya ba, dan haka ke ma ki kiyeye kar na cire miki ido”

Ta yi dariya tare da maida gilashinta bayan ta share hawayenta. Saboda ya dauke musu kewar Amma ya zo part din ya fara hada musu abun karyawa yana cikin hadin ne Hamad ya shigo sai ya kira shi suka cigaba da yi tare, bayan sun gama suka hadu a dinning har Hurriya suka soma karyawa tea kawai Hamad ya sha sai yankan bread daya ya ce ya koshi, Yasir ya kalleshi sai dai be ce masa komai ba domin ya fi kowa sanin ba a cilasta Hamad yin abun da be tashi yi ba a kwashe lafiya, zai iya cilasta masa kuma ya ci amman kuma za su yi fada su rabu da bacin rai.

“Jiya ma haka yayi be ci abinci ba”

Hurriya ta fada tana tauna bread din dake bakinta.

“Ya saka tunanin abun da ya faru ne a ransa, kina ganinsa kamar be damu ba ko? Ya fiki damuwa daman mu maza haka muke muna boye abu a ran mu babu mai sanin muna da damuwa sai idan an bincika ko kuma an saka mana ido”

Hurriya ta dan yi murmushi kadan.

“Amman mazan ba kowa yake da zuciya kamar Hamad ba, ya cika fushi”

“Akwai su, wasu sunada fushi sosai a mata ma ana samu balle kuma maza, baki dai taba haduwa da su ba ne, ai halitta ce za a iya samunta a gurin mace haka ma gurin namiji, shi ma Hamad zai daina idan ya kara girma yayi wayo”

Bata sake cewa komai ba har ta gama karyawa sannan ta tashi da sauri ta nufi upstairs.

“Bari na yi wanka na saka uniform”

“To sai ki yi sauri domin kusa latti”

Ya mike tsaye ya fice daga bangaren zuwa bangaren mahaifinsa domin gaishe, kamin ya isa bangaren mahaifinsa ya hango shi tsaye waya a hannunsa yana dannawa, hakan ya saka Yasir ya cira kafa ya karasa gurin mahaifinsa sai yaja ya tsaya yana sauraren wayar da Appa yake.

“Kamar da karfe goma dai, amman ina son a kwashe komai kamin yara su dawo daga makaranta”’

Yasir ya dan kalleshi zuciyarsa na raya masa kayan Amma za a kwashe. Ashe kuwa ya canka daidai domin a karshen zancen sai Appa ya karasa da fadin

“Zan turo address din da kuma number wayarta ko da ba ku gane gurin ba”

Ya sauke wayar ya shiga message dinsa ya fara rubutu location din. Yasir ya mika gaisuwa cikin girmamawa kamar yadda ya saba.

“Lafiya kalau an tashi lafiya”

“Lafiya kalau Appa”

Daga haka Appa be sake cewa komai ba shi ma kuma be ce ba, daman baya tunanin Appa yayi maganar Amma ko wani abun da ya shafe ta da shi idan dai ba umarni zai ba shi akan wani abun ba, shi kuma be isa ya daga kai ya kalli mahaifinsa yayi masa magana akan lamarin aurensa ko wani abun da ya shafi matansa ba.

“Hurriya sun tashi kuwa”

Appa ya tambaya, domin tun tashinsa zuciyarsa take son zuwa duba yaransa sai dai gudun kar ace ga nuna banbanci ko kuma su ya fi kaunarsu da sauran yara ya saka ya danne ya boye abun.

“Sun tashi tare muka karya ma, amman Hamad be ci wani abun kirki ba?”

“Ba shi da lafiya ne?”

“Lafiyarsa kalau Hurriya tace jiya ma be ci komai ba”

Appa ya sauke ajiyar zuciya a hankali ba tare da ya bari sautin saukar numfashin ya fito ba. Har lokacin kuma be kalli Yasir dake tsaye gefensa ba kamar mai jin kunyarsa. Suna tsaye gurin har yara suka fara zuwa karbar chocolate da juice din da ya saba raba musu idan za su tafi makaranta, Appa ya koma ciki sai Yasir ya bishi ya riko masa suka fito da kayan waje sannan ya zauna a one of kujerarun dake gurin, ya fara raba musu suna karba yaran Hajiya Kaltume ne a gaba, Khairi kam baki ya kumbura gashi ta turo shi gaba ita ala dole an mata ba daidai ba fushi take, sannan Namra ta zo ta karba, a da can Hurriya da zumudi da far'a take zuwa karba kuma a kullum Hamad sai ya rigata karba, domin shi baya bata lokaci a komai ba kamar ita ba sarkin latti, cin abinci ma sai kowa ya cinye ita bata cinye nata ba.

“Appa ina kwana”

“Lafiya kalau Hurriya an tashi lafiya?”

“Alhamdulillah”

Ta mika hannu biyu zata karba, Yasir ya rigata ya karbe yana dariya kamar yadda ya saba, kasancewar bata a cikin yanayin farinciki sai kawai ta yi murmushi ta hade hannayenta. Appa ya dauko wani ya mika mata.

“Karbi, ina Hamad?”

Ta saka hannu biyu ta karba taba ba shi amsa.

“Yana bus ya ce shi ba zai karba ba yau”

Appa ya ji babu dadi sai dai be nuna ba kuma be sake cewa komai ba, Hurriya har ta juya sai kuma ta juyo ta kalli Appa.

“Appa yaushe Amma zata dawo?”

Kallonta kawai mahaifinta yake, kamar yace me yasa kika min wannan tambayar domin be gama saka kalar amsar da zai ba su ita da Hamad, musamman ma ita da take da shakuwa da shi sosai wata kila Hamad zai bar abun a zuciyarsa dai dai yayi ta fushi da shi. Yasir ne yayi hanzarin tarewa Appa numfashin da ya rasa ina sauke shi.

“Hurriyya idan zaki yi magana mai tsada da Appa, daga ke sai shi ya kamata ku yi, ki daina yi a gaban mutane kin ji”

Ta amsa masa da kai, sannan ta kalli Appa

“Na gode Appa Allah ya saka da alheri”

Ta juya ta fara tafiya zuciyarta babu dadi. Godiya ce ta yi masa irin wadda ta saba masa a duk lokacin da ya bata chocolate din ko kuma yayi mata kyauta kasancewar abun da Amma ta koya musu kenan, amman a yau sai ya ji godiyarta a wata sigar ta dabam, yake jin kamar abun da ya aikatawa mahaifiyarsu ne take masa godiya a kai, gashi dan murmushi da far'a da kuzarin da yake gani a fuskar yarsa yau ya kau, dan'uwanta kuma ko ganinsa be yi ba.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un”

Shi ne abun da ya iya furtawa yana binta da kallo zuciyarsa na masa zafi, tunanin dama da hadu na kokarin hade masa su rikita masa kwakwalwa. Yasir ya kalleshi sai dai be ce komai ba.

“Idan sun dawo makaranta kai ko daya daga cikin direbobin gidan nan wani ya kai su gida su duba Amma”

“Toh Appa In Shaa Allah”

Appa ya juya ya koma ciki, Yasir na binsa da kallo kansa a daure yana mamaki wane kalar laifi Amma ta yi masa da har ya yanke wannan tsatsauran hukunci haka.



*** *** ***

Ruma ta turo kofar dakin ta tsaya daga jikin kofar ta kalli Khairi dake zaune gaban madubi tana shafawa bakinta magani ta ce

“Khairi wai Ina Hajiya tace miki zata tafi?”

“Ba ni ta fadawa ba, Maama ta ce gidan Hajiya Fatee zata tafi”

“Toh amman har yanzu zata dawo ba? Na kira wayarta be shiga”

“Maybe can zata wuni, ai dole dai idan dare yayi kin san zata dawo”

“Khairi karfe 6:30pm ake magana fa, kuma ta fita tun safe”

“Aa Ruma kin cika matsala, Hajiya ai ba yarinyar ba ce idan lokacin dawowa yayi ai ita zata dawo, kika san abun da ya saka ta dade? Kin san dai Hajiya Fatee aminiyar Hajiyarmu ce, waya san me taje yi a gidan”

Khairi ta amsa mata da kamar fada domin ta hana ta shafa maganin da take cikin salama sai damunta take da tambayoyi. Ruma ta tabe baki ta fito taja mata kofar tana sake gwada line Hajiya domin ita idan Hajiya bata a gidan duk jinsa take ya zama dabam wannan ya saka wani lokacin ma har bin Hajiya take idan zata fita, kusan duk kawayen Hajiya sun san yar autar Hajiya Ruma saboda yawan lake mata da take. Har ta isa dakinta gwada line take amman kiran yaki shiga baturiyar sai tabbatar mata take da ba a samun Hajiya.
[10/18, 5:35 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆
                 

𝐁𝐲   𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲


𝗣𝗮𝗴𝗲 8️⃣

Suna shigowa cikin gidan Gwaggo Hurriya ta shiga dakin da sauri tana neman Amma. Gwaggo ta yi dariya tana daurawa jikarta dankwali

“Maraba da Hurriya yanzu ake tafe”

“Eh Gwaggo ina wuni”

“Lafiya kalau ina Hamad?”

“Shiga nan shigowa, Gwaggo Ina Amma?”

“Tana dayan dakin dake kusa da na su Rukayya”

Da sauri Hurriya ta tashi ta fice daga dakin Kakarta zuwa dakin da Amma take, tana shiga dakin ta fada jikin Amma kamar bata san tana dauke da cikin kanensu ba, sai kuka ya biyo baya ta kankame Amma sosai kamar za a kwace nata ita. Cikin karfe hali da dauriya irin na uwar da bata son raunin yayanta ya kamata har ta yi kuka a gabansu ta shafa bayan Hurriya tana dariyar da sautinta yaki fitowa, hakan kuma ba karamin taimakawa idonta yayi ba gurin zubar da ruwan hawayen da a da su kwana a idonta. Kanwarta Rukayya ta bata fuska sosai kamar ta fasa kuka.


“Amma da baki nan gidan babu dadi, kuma Appa ya kwashe kayanki daga gidan”

“Na sani, ya aiko min da su nan ai, suna nan a zuba a gareji, wasu an saka a falon waje”

Hurriya ta dago tana kuka ta kalli Amma.

“Ba

1 Comments On HURRIYA Book 1
avatar
rahmat-2-8

1 year ago

Reply

Love it

Please Login or Register in order to submit comment