Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ga aiki ta zo yi a gidan ta aure Alhaji Haruna, ba dan ma da kaddarar aure ta hana ba kuma yara sun shiga tsakani ba wata kila da ba zata iya hakurin sharing miji daya da yar aikin gida ba, kallon da take yi ma Amma bata da ajin da zata yi kishi da ita sai idan abun ya motsa.
Ita dai abun da ta fi tsana shi ne a shiga sabgarta, idan ta shiga sha'aninta na masu arziki har mantawa take da Hajiya Kaltume da Amma, a yanzu kuma kawo mata Hurriya da Hamad da Appa ya dage sai shi ne abun bacin ranta a yanzu, domin da su zauna a gurinta kara ya dawo da uwarsu ta rainin abunta, sam sam Momy bata son yayan kowa idan ba nata ba, bata mutanta kowa sai masu kumbar susa, idan baka da arziki har ganin take kamar baka cika mutum ba.
[10/18, 5:34 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: https://chat.whatsapp.com/GJ9hOtbWbfDKmq8NrKsDIG


☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆
                 

𝐁𝐲   𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲


𝗣𝗮𝗴𝗲 6️⃣

Da tunanin Amma Appa ya dawo apartment dinsa, tsansar biyayyarta da yadda take gujewa bacin ransa da nuna kulawa akan duk wani abu da ya shafe shi. Ya tabbatar da ita ce ba sai ya bukaci a bawa Hurriya abinci ba, matukar ta san uwar yaran bata gidan zata yi kokarin kwatantan kyautata musu kuma ta ja su a jiki, haka ma da ita ce ya zo mata da zancen dawowa ƴaƴan abokiyar zamanta a bangarenta zata yi marhabun ta karba da hannu biyu ko da kuwa bata son haka ba zata nuna har ya gani ba, duk wani abu da Amma ta san Appa yana son kokarin raya shi kaunar abun take ba ta bata masa rai ba.
Hannayensa hade a bayansa yake tafiyar fuskarsa a yanutse zuciyarsa a hargitse yana jin kamar ya fashe da kuka gaba daya ya rasa me ke samunsa ya rabu da matarsa rabuwar ta haifar masa da rashin kwanciyar hankali da bacin rai, zamanta a gidan kuma masifa ce a gidansa masifar da be san ta micece ba domin shi dai ya san matarsa bata masa laifi ba, be san dalilin da ya saka ya tsane ta ba. Kukan Hurriya ne abun da ya fara masa maraba da zuwa a lokacin da ya kunna kai cikin falonsa, kuka take sosai irin kukan nan da ya hana gilashin idonta tsaya saboda hawayen da ke cika shi, ta rike gilashin a hannu lipa dinta da jikinta sai rawa suke, dishe-dishe ta ga alamar shigowar mutum bata bukatar saka gilashi domin tantance waya shiga, ta san tsayinsa da yanayin tafiyarsa ta haddace komai. Shi ya taho da sauri ita ma ta nufo inda yake da sauri tana rike da gilashin dayan hannunta kuma yana lalabensa.

“Appa. ..apa... Appa... Appa wai ka rabu da Amma?... Sakin Amma ka yi?”

“A gurin wa kika ji wannan maganar Hurriya? Waya fada miki haka cikin daren nan?”

“Yaya Khairi.... Appa da gaske? Appa why? Yanzu mu kadai ne zamu rasa uwa a nan Appa! Me Amma ta yi?”

Tambaya take tana wani irin kuka numfashi na fitar mata da karfi kamar ranta zai fita. Idon Appa ya cika da hawaye

“Bata yi komai ba Hurriya, be kamata ki shiga cikin magana irin wannan ba, zauna a nan ina zuwa”

Ya nufi kujera da ita ya zaunar da ita, ya juya ya fita gaba daya abubuwa sun rike masa har ji yake wani abu na juya masa cikin kai, kamar za a haukata shi haka yake ji. Bangaren Hajiya Kaltume ya nufa tun a tsakar falon ya fara kiran Khairi rai a matukar bace daman ciwon sakin Amma da ya kama shi, ga bacin ran da Momy ta saka masa yanzu kuma Khairi ta kara masa wani ta hanyar batawa Hurriya. Umm Khairi ta fito daga dakin Hajiya tare da Maama Umm Ruman na biye da su a baya, Umm Salma da Yasir kuma suka fito a nasu dakuna duk suka sauko kasa.

“Alhaji Lafiya?”

Cewar Hajiya Kaltume da ta riga su saukowa gabanta har faduwa yake.

“Akan wane dalili Umm Khairi zata fadawa Hurriya sakin mahaifiyarta aka yi? Ita mahaifiyar bata fada ba sai ke yar iya? Wannan ba rashin hankali da rashin tarbiya ba ne? Ki shiga cikin maganar iyayenki?”

Ya juya gurin Hajiya Kaltume.

“Kin ga abun da kika hanyo ko? Kin maida yaran nan kawayenki da maganar da ya dace da wanda be dace ba duk fada kike a gabansu, har suna jin sun isa sun kai su saka baki a zaman takewar mahaifinsu, sai na koya miki hankali sai na koya miki hankali Ummul Khairi”

Jikinta ya dauki rawa domin ta san halin Appansu idan hau yana wuyar saukowa. Yasir ya karbawa Appa.

“Iskanci ne da rainin hankali, ta fi uban kowa baki da bakin iyayi a gidan nan kamar wata babbar mace, yau sai kin fadi wanda ya aike ki”

Hajiya Kaltume na jin haka ta yi saurin zunguje Khairi.

“Ba zaki bada hakuri ba yar iskar yarinya? Idan kuma ba haka ba ne sai ki fadi yadda aka yi ai ko?”

“Appa Wallahi karya take min, yarinyar nan munafukace sai dai idan labe ta yi, ko kuma so take ta hada min sheri”

Tana rufe baki Yasir ya fara dukan bakin nata ya saka hannnunsaya kama lips din ya jan sai da ta ti ihu sannan ya rufe ta da duka gaba daya, Hajiya Kaltume ta fara kokarin kwatar yarta Appa kuma ya fice daga falon ba tare da ya hana Yasir dukan Khairi ba.

“Ai fa an taba yar gata yar gaban goshi yar lasa da halshe, kai dan Allah karka kashe min ƴa saboda ƴar wasu da ba zata amfana maka komai ba”

Hajiya Kaltume na masifa tana kwatar Khairi dake ta rusar ihu, Maama da Salma sai haushi suke ji saboda ana dukan yar'uwarsu Ruma ce kadai take jin abun da yayarta ta yi bata yi daidai ba.

A bangaren Hurriya Appanta na fita sai ta tsagaita kukanta ta share hawayen da suka ki tsaya mata ta saka gilashin da zai bata ganin kofar fita dakin daidai ta mike tsaye ta fito daga bangaren mahaifinta ta dawo na su bangaren tana tafe tana hawaye har ta isa. Sai ta ta tura kofar falon ta bude sai kuma ta kasa shiga domin jin take kamar Amma ma mutuwa ta yi ba barin gidan ba bata taba sanin haka kewa take ba sai yau da ta yi kewar mahaifiyarta. Kusan da ita da wanda ba shi da lakka a jiki duk daya domin tun a yanayin tafiyarta zaka fahimci zuciyarta ta karaya salulu ta shigo falon ta zauna kan kujera har lokacin Hamad na zaune a inda ta barshi, sai dai a yanzu fuskarsa na nuna danuwar dake zuciyarsa domin ya bata rai sosai ba kamar dazun ba d ya bar abun a cikin zuciyarsa. Fashewa Hurriya ta yi da kuka tana girgiza kai ji take kamar ace mata ba gaske ba ne, da ace ta san sakin Amma Appanta yayi babu abun da zai hana ta binta, da ba zata yarda ta zauna a gidan ba, a yanzu kam ta yarda ita wawuya ce da bata yi saurin ganewa ba, domin tana da saurin yarda idan aka fada mata abu dauka take ko da kuwa ba gaskiya ba ne. Kukanta ne ya saka Hamad hawaye yana ta dantse baki yana boye cikarsa domin zuciyarsa kawowa take kamar wani zaki, amman sai duk da hakan sai ya gagara rike kansa shi ma ya fasa kuka, ita da shi suka zama kamar wadanda aka cewa Amma ta mutu ta bar su.

“Hurriya Hamad”

Kusan a tare suka dago suka kalli kofar gefen Dinning din kofar da Appa ke tsaye, kofar cikin falon Amma ce dake basu damar shiga bangaren Appansu. Hurriya ta tashi da sauri ta nufi inda yake tana kuka sosai Hamad kuma ya dauke ido alamar baya son ganin Appa.

“Wannan kuka sai kace an yi mutuwa? Haba karku saka kanku a damuwa tsakanin halshe ra hokora ma ana basawa balle kuma mutum da mutum, dan tsabani muka samu shi ne Amma ta tafi gida, amman da zarar al'amurra sun daidaita zata dawo”

Hurriya ta kasa magana sai kuka take, Hamad kuma ya mike tsaye ya share hawayensa ya nufi sama.

“Karka shiga, ba a nan zaku kwana ba, na yi magana da Momynku a can zaku kwana ku zo muje”

Be jira cewarsu ba ya kama hannun Hurriya zuciyarsa na masa babu dadi, daman can shu baya son kukan wani ko ganin wani a damuwa balle kuma yaransa, sanin cewar shi ne silar damuwar ya saka shi jin babu dadi gaba daya abubuwan sun zo masa ta yadda be yi zato ba. Ganin Appa ya nufi kofar fita falon tare da Hurriya ya saka Hamad ya bi bayansu, sai da suka fita harabar gidan gaba daya, sannan Appa ya tsaya ya tsayar da yarsa ya daga kanta ta kalleshi.

“Haka zamu shiga bangaren Momynki kina ta kuka Hurriya? Dan Allah ku yi hakuri idan ba so kuke ni ma na yi kukan nan ba, ba ku san abun da yake cikin zuciyata ba, ina cikin wani irin tashin hankali da rudani marar misaltuwa”

Kai kawai ta iya daga masa ta saka hannayensa ta share hawayenta tana ta aikin hade kukan dake neman ya gagari tsayawa a iya bakinta da idonta.

“Ammanku ba mutuwa tayi ba, zaku iya zuwa ku ganta a duk lokacin da kuke so, ita zata iya zuwa ta ganku, Hamad na san kai ne mai zuciya ka sakawa kanka hakuri dan Allah ko dan yar'uwarka”

Ko saitin gurin da Appa yake tsaye Hamad be kalla ba, yadda ya dauke kai yana kallon wani gurin sai ka rantse da Allah ba da shi Appa yake magana ba, domin a yau kam ba shi da abokin tsana kamar Appansa saboda sanin cewar ya rabu da Amma, ko da kuwa ba zai iya fadar abun da ya faru tsakaninsu ba, hausawa suka ce mai lalabe a duhu balle an haska masa, a banza yayi fushi balle an taba shi. Appa ya dauke kai ya rika hannun Hurriya suka cigaba da tafiyar, da kansa ya shiga falon, be zarce ko ko'ina ba sai Stairs kai tsaye ya nufi dakunan da suke gefen bedroom din Momy kamar yadda suke a kowane bangare, ya san dakin Namra da na Musib da Miwan dan haka be taba dakunansu ba ya nufi wani dakin ba dabam ya tura kofar dakin sannan ya saki hannun Hurriya daki ne dake dauke da furniture na mutum daya domin Appa ya saka an zuba furniture an gyara ko wane daki duk kuwa da kasancewar wasu dakunan babu kowa, ba dan komai ba sai dan irin haka ko kuma idan an yi baki ko ma idan yaransa sun yi sha'awar canja daki daga wani zuwa wani. Hurriya ta daga kafarta ta shiga cikin dakin ta isa bakin gadon da zai wadaci mutum daya ta juyo ta zauna ta a hankali tana kallon Appanta dake jan kofar dakin. Gam... Kofar na amsawa gabanta ya yanke ya fadi, gaba daya sai ta ji kamar wata duniyar aka kawo ta, sai ta ji kamar wani gidan da bata san kowa ba kuma bata da gatan kowa a ciki aka kawota. Rabon da ta shiga bangaren Momy ma an dade, babu ruwanta da bangare sai da dalili ita ma Momy bata shiga nasu bangaren ita ta ware kanta dabam a gidan. Dayan dakin dake kusa da na Hurriya Appa ya budewa Hamad

“Nan zai mana Hamad?”

Ya daga kai sannan ya saka kai ya shige dakin da kansa ya turo kofar dakin ba tare da ya jira mahaifinsa ya rufe masa ba. Appa ya sauke ajiyar zuciya ya juya ya sauka, Namra da Musib suka hada ido suna mamakin yadda Appa ya shigo da Hurriya be ma bari ta zo da kanta ba.

“Musib ina Miwan?”

“Ya fita da magariba nan Appa”

“Namra da Musib dan Allah a zauna lafiya, yaran nan kanenku ne, jini daya ne ku da su, bana son na ji wani tashin hankali ko fada, Hamad dai kun riga kun san halinsa ba sai an fada muku ba, duk wani abun da zai yi ku kawar da ido ni kaina da nake mahaifinsa hakuri nake da shi, Hurriya kuma kun san babu ruwanta da fita dan Allah a zauna lafiya”

Nasiha yake musu amman zuciyarsa cike take da kunci da damuwa narar misaltuwa. Appa ya amsa cike da ladabi

“In Shaa Allahu Appa”

Ya dan motsa kansa kadan alamar gamsuwa sannan ya nufi kofar fita.

“Sai da safe Appa mu kwana lafiya”

“Allah yasa”

Ya amsa sannan ya fice. Yana sakin kofar falon Musib yayi kwafa ya mike tsaye ya nufi stairs Namra ta bi bayansa, ita ta shige dakin Momy Musib kuma ya nufi dakin da zuciyarsa ta raya nasa Hurriyya na ciki. Ya tura kofar dakin kamar abun arziki ya tsaya daga bakin kofa yana kallonta idonta shar da hawaye.

“Yar gatan Appa, da kansa ya riko hannunsa ya kawo ki, kuma saboda ke yayi ta fada da Momy”

Uffan Hurriya bata ce masa ba, har ya gaji da tsayuwa ya bar mata kofar a bude yayi tafiyarsa. Runtse ido ta yi tana jin wani sabon kuka na zo mata, ta dawo a rakube gurin ta ta san cewar zata sha azaba da wahalar zama, da ma ace bangaren Hajiya Kaltume aka ajeta ko ba komai zata samu sauki ta wani bangaren saboda Yasir, amman a na bangaren ta san babu mai sonta, gaba daya sai ta ji ta zama wata marainiya ashe ba sai da rashin uwa da uba ake maraici ba. Musib na barin kofar dakin Hurriya ya nufi dakin Hamad ya tura, kwance ya hango shi saman gadon ya baya kofar baya, kuma budewar da Musib yayi be saka Hamad juyo dan ya duba ko waye ba. Wani mugun kallo da tsana irin ta yan uba Musib ya jefi kanensa da shi, sannan ya bar kofar dakin shi ma be rufe masa ba, Hamad na jin alamar an tafi ya juyo ya sauko saman gadon ya iso gurin kofar ya rufe ta da karfi ya saka key, Musib da be jima da barin bakin kofar ba ya juyo ya kalli kofar jin yadda aka bugata da karfi.

“Zaka sha wahala yaro”

Yayi kwafa ya nufi dakin Momy sai wani huci yake kamar mace, daman shi ne mai kishin da matan ubansa a gidan sai dai yana boye abun a zuciyarsa, yadda yake jin kiyayyar Iyami da Hajiya Kaltume ko Momynsa bata jin kiyayyarsu haka domin ita sai idan kishin ya motsa mata ne take kula su ko kula wani abu da ya shafesu.

Daren sai ya zamewa Hamad da Hurriya dabam, sanin cewar rabuwa mahaifiyarsu ta yi da mahaifinsu ya hana Hurriya rutsawa har safe, sai ta raya daren da kuka Hamad kuma bayan ya gama nasa fushin bachi ya sace shi. Ta bangaren Appa ma yadda ya ga rana haka ya ga dare, kwanan Hajiya Kaltume ta bangaren be kuranye masa damuwarsa ba, sai ma ya kasa kwantar daga karshe ya koma falo ya zauna ya kunna Tv sai dai kuma babu mafitarsa a cikin kallon kamar yadda babu shi a cikin bacci sai ma karin damuwa, me yasa ya aikata shi ne abun da ya tsaya masa a rai yake ta tambayar kansa, idan kuma ya tuna da abun da yake ji idan tana gidan sai ya ga kamar yin haka shi ne daidai.

Washe gari da wuri Hajiya Kaltume ta tashi, daman duk ranar girkinta da wuri take tashi ta shirya masa abun karyawa, kasancewar bata da mai aiki tun bayan da ta dauki Iyami aiki ta aure mata miji bata sake yarda ko mai sharar gida ta sake dauka ba, sai dai ta yi komai da kanta ba kamar Momy ba da masu aiki ne suke mata komai sai dai ta ci idan kuma ranar girkinta ne sai dai ta dauki na Appa ta kai masa.
Ko da bakwai ta yi ta gama hada masa ruwan zafin tea da gasa masa bread dan ya fada mata tea kawai zai sha baya son cin komai. Yana shan tea yana hamma saboda bachi da ya gagareshi da dare da alama yana neman fansa a yanzu da safiya.

“Wai dazun ina barin bangarenka Hajiya Fatee ta kira ni”

Ya dan juyo kadan yana kalleta alamar ina saurarenki.

“Wai danta Fadeel ya samu tsabani da matarsa shi ne take son na zo”

“Allah ya kyauta...”

Yadda ya amsa mata ya karantar da ita izinin zuwa ne, daman kuma ta san ba zai hanata ba.

“Ameen zaman auren ne na su, zaman lafiya ta gagara Allah ya shirya tsakaninsu”

Appa dai be sake cewa komai ba, har ya shaye tea ya aje cup be taba bread ba. Hakan kuma be yi ma Hajiya dadi ba domin ta san damuwar ba zata wuce ta ƴaƴan Iyami ba ko kuma ta Iyamin ma gaba daya. Ta dauke cup din ta fita ba tare da ta fada masa yanzu ta tafi ba da safen nan. Ta isa bangarenta rike da cup din. A dinning din da duka matansa suke fara cin karo da shi a kowane falo idan suka fito daga bangarensa ta aje cup din sannan ta nufi dakinta, tana shiga ta raba jikinta da tufafin da ta saka da safen nan ta daura tawul ta shiga bathroom, a gaggauce ta yi wanka gudun kar ta yi latti sanin cewar inda za su je kaune dake gaba daji baya daji. Ko da ta fito ta samu Khairi zaune akan gadonta fuska a kumbure musamman bakinta.

“Subhanallahi haka Yasir ya fasa miki baki saboda yar iskar yarinyar nan?”

“Ba laifin Ya Yasir ba ne Hajiya, laifin Appa ne yana mugun son yarinyar nan, ya fi kaunarta da duka sauran ƴaƴansa, dubi yadda ransa ya bace saboda na fada mata gaskiya bayan kuma gaskiyar ce”

“Hmmm ai ni ganin nake kamar ba banza uwar yaran nan ta bar Alhaji ba, ita kanta ai ba a banza ta aure min miji ba, yanzu kuma saboda yaran nan Allah kadai ya san ran mutun nawa zai ɓace a gidan nan”

“Wallahi sai na rama komai ta dade”

“Toh ki rama dai ta sigar lalama, in ba haka ba Alhaji ko Yasir su ci ubanki kin san jira kawai suke”

Ta tashi ta fice dakin tana wani zakuɗa ita ga balagaggiya. Hajiya ta shirya cikin koriyar Atamfa ta saka farin mayafi ta sauki jakarta mai kala daya da gyalen da kuma talkaminta ta saka sannan ta dauki wayarta ta kira daya daga cikin drivers din gidan ta sanar masa fitarta. Gurin da take aje kudi ta bude ta dauko kudi mai yawa ta zuba a jakarta sannan ta rufe ta rataya jakar ta fito rike da wayarta sai kamshi take zubawa irin na manyan matan masu kudi kuma masu miji da ikon gida.

“Hajiya fita zaki yi?”

Maama ta tambaya.

“Eh wani guri zamu je da Hajiya Fatee”

“Allah ya tsare, Hajiya kin ga yadda Ya Yasir ya fasa bakin Khairi”

“Na gani, ku ma sai kun yi taka tsantsan ai, ni ba dan ubansu daya ba ai sai na tsora ta na ce aurenta yake son yi”

“Lallai ya fi sonta da mu ma”

“Hmmm Allah dai ya kyauta, ki tashi sauran yan 'uwanki kar su yi latti makaranta, ni na fita”

Daga haka ta fice daga falon Maama na yi nata Allah ya tsare. Ko da ta fito direban har ya tashi motar ya juyata tana fuskantar gate domin ya san uwargidan Alhaji Haruna Mai Yadi bata daukar raini. Tana shiga motar be tsaya da ita ko'ina ba sai gidan aminiyarta Hajiya Fatee, yana aje ta ya juya a can ma ba su bata lokaci ba, Hajiya Fatee ta kira direban dake kai su kauyen ta sanar masa sun shirya, ba su yarda su tafi da motarsu ba saboda tsoron masu kidnapping da kuma tonon asiri, sai dai su dauki shatar motar kasuwa ta zo ta dauke su har gidan Hajiya Fatee ta kaisu inda za su je, kasancewarsa mijin Hajiya Fateen ya dade da rasuwa ita kadai ce a katon gidan sai yan matanta biyu da kuma masu aiki da danta Fadeel ya zuba mata.

Misalin karfe tara da rabi na safe suka kama hanyar kauyen gidan zalla dake cikin local government din Kwatarkwashi. Suna tafe suna hira Hajiya Fatee na kara fada mata yadda matar danta Afrah ke son mulkar mata ďa ta saka shi ya manta da ita. Idan ta kai aya sai Hajiya Kaltume ta dauko nata zancen na abun da ya faru tsakaninta da Alhaji a jiya. Sanar da shi da suka yi cewar suna nan tafe ya saukaka musu wucewa kai tsaye dakin da yake gabatar da tsiface-tsifacensa. Sai da ya fara yi musu maraba da zuwa sannan Hajiya Kaltume ta ciro kudi 300k ta aje masa tana masa godiya.

“Aiki yayi Malam, dan haka na zo da kaina na kawo maka goronka, kuma na yi maka godiya”

Malamin da hakoransa ke daskare da jan goro ya yi dariyar jindadi da farinciki ya jinjina kai.

“Hajiya ai na fada miki, indai muka yi aiki ba a dawo mana da shi, kuma kar tunanin kin yi kin yi baki dace ba yasa ki karaya a gurinmu, idan kin ji ana malam anjima da nisa ba ma gobe da nisa ba to kika zo nan kakarki ta yanke saka kawai”

“Na gani ai Malam Wallahi na gode, domin shekara da shekaru ina neman yadda matar nan zata bar min mijina amman abu ya garara sai an yi kamar za a rabu sai kuma ka ga ba rabuwar bace, sai yanzu Allah ya kawo karshen abun, sai dai ko yanzu ni ina jin tsoro domin na lura ya shiga damuwa matuka gaya saboda sakinta da yayi, ina jin kar ya ce zai dawo da ita domin saki daya yayi mata”

“Ina ko alama! Karki damu Hajiya, idan har mutum zai mutu ya dawo to kishiyarki zata dawo gidan, ai farraqu muka musu ita tana gabam yana yamma har abada ba zama a tsakaninsu”

Wani kalar dadi ya lullube Hajiya Kaltume.

“Haka nake so, kuma ina son a koya mata hankali so nake ka yi mata wani aikin da ba zata sake aure ba har abada, tun da ta zabi kishi da ni to ko bayan ta bar gidan mijina sai ta dandana bakincikin da nadanar auren Alhaji da ta yi, sannan be sake ta sai da ya damka mata kudi har miliyan asirin, Malam ina son a lalata duniyar da ya bata, har da gidan da ya mallaka mata idan akwai yadda za'ayi a ruguza gidan ko ma ya karbe abunsa, kuma a daureta ko kare kar ya sake sha'awarta balle har ta yi aure”

“Wato so kike a lalata duniyar da ya bata, ba wadda ya bata kawai ba, har tata duniyar da ta mallaka za a iya lalatawa idan kina so”

“Aiko idan ka yi min haka, ina mai tabbatar maka aikin Hajji bana da kai za'ayi, kuma zan maka kyautar kudi har naira miliyan daya”

Malamin ya sake yin dariya yana gyara babbar rigarsa.

“Hajiya na miki alkawari akaifa kishiyarki ba zata sake amfana da ita ba, ba duniyarta ko ta mijinki da ya bata ba, har dukiyar wani idan ya dauka ya bata ba zata taba amfanarta ba, ita da aure ko sai lahira idan ana yi, kuma yadda ba a mutuwa a dawo haka ba zata sake dawowa a gidan mijinki ba”

“Alhamdulillah”

Hajiya Kaltume ta fada tana daga hannu sama ta yi ma Allah godiya, sannan ta kalli Hajiya Fatee suka taba suna dariya. Daga bisani Hajiya Fatee ta kora masa da nata bayanin.

“Malam nima da tawa mtsalar na zo yau, suruka ce ta saka ni a gaba, ta mallake min ďan yaki ya kara aure kuma baya jin maganar kowa sai ta matarsa, ga kudi yana da shi amman ko kyauta zai yi sai abun da ta so yake bayarwa, ni so nake a raba su ya sake ta saki uku idan da dama”

Malamin ya amsa mata da kai.

“Ya sunanta, ya kuma sunan ďanki?”

“Afrah ake kiranta, shi kuma Fadeel”

Ya dauko kasa dake cikin farantin katako ya dora a cinyarsa yayi zane zane ya jinjina kai ya dago

1 Comments On HURRIYA Book 1
avatar
rahmat-2-8

1 year ago

Reply

Love it

Please Login or Register in order to submit comment