Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba. Gashi abun da Appa ya fada cewar yaran Iyami za su karatu a waje ya daki zuciyarta mugun daka irin dakan da ace mashi ne, babu abun da zai hana ya bullo ta bayanta, yanayinta ma gaba daya sai ya sauya hankalinta yayi mugun tashi, ba dan ta yaki zuciyarta ba wata kila ma da ta rasa sukuninta har kowa ya gane halin da take ciki.

“Allah sarki dan'uwa mai kaunar yar'uwarsa, duk da fadan nan da kuke da rashin jituwa wannan soyayyar da kaunar tana nan a zuciyarsa, Allah ya kara hada kanku, ya shirya mana”

Kowa ya amsa addu'ar da Hajiya Binta ta yi da Ameen ban da Hajiya Kaltume da gume ma ya karye mata kamar wadda aka kwancewa zane a kasuwa. Daga bangaren Hajiya Kaltume Hajiya Binta ta fito ta shiga bangaren Momy suka gaisa sannan ta fito tana jin kewar Iyami. Sai addu'a take ma Appa idan dawowar Iyami alheri ce Allah ya daidaita tsakaninsu, ya kasa amsawa da ameen bayan kuma abun da yake nema kenan a zuciyarsa. Mota daya suka shiga Hurriya bayan ta dauko mayafinta, ita da Hajiya suka zauna a back seat, Appa da Hamad kuma suka shiga gaba, Appa yana jan motar suka fi daga gidan.

After mintuna goma da tafiyar Hajiya Binta, Momy ta fito tare da bakuwarta da kuma ɗanta da be ci komai ba a cikin abubuwan da Momy ta saka a shirya musu, Miwan na bayansu tare da dan'uwansa Musib sun yi ma bakuwar Momy da ďanta rakiya ban da Namra da har yanzu tana can bangaren Hajiya Kaltume.

“Captain ai yana yawan zuwa nan, duk lokacin da zai zo garin na ba ya tafiya sai ya shigo, ina jindadin haka Wallahi”

Hajiya Turai ta yi murmushi.

“Ai danki idan yana son mutum to ya huta, Allah ya hada jininku”

“Sosai kam, Allah dai ya nuna mana lokacin auren nan mu rakwashe”

Cewar Momy, Mutumen da aka ta maganar akansa be ce uffan ba ya fara sauko Entrance din hannu dafe a kirjinsa yana murza a hankali domin ba karamin zafi ya ji ba a lokacin da suka yi karo da Hurriya, taku daya biyu uku hudu yayi kamin ya ja ya tsaya yana kallon yadda tsaddadiyar motarsa ta yi ta kasa gaba daya, saboda tayun motar da aka succe duka hudu. Ya juyo ya kallesu.

“Waya taba motar nan?”

“Wace motar?”

Kusan a tare suka kalli motar Musib yayi sauri sauka ya karasa gurin motar da mamaki.

“Lafiya kalau kuka zo da ita?”

“Idan bata da lafiya zamu zo da ita ne? What kind of stupid question is this!”

“Subhanallahi, garin ya haka ta faru!”

Cewar Momy tana saukowa ta nufi gurin motar. Miwan ya ce

“Gaskiya wannan succe tayun aka yi”

“To waya aikata haka? Wannan dai rainin wayo ne da neman mutum yayi magana ace ya cika masifa”

Ya fada da karfi wani karin bacin dai na tunkarosa, cikin bakinciki ya sauka ta isa gurin motar. Momy ta kai hannu ta dafa karjikinsa.

“Kwantar da hankalinka Captain, a cikin yaran nan dai wani ba zai yi gigin yi maka haka ba, akwai dai matsalar da aka samu”

Momy na rufe Hajiya Turai ta miko masa hannu kamar wani karamin yaro dan yaye.

“Captain shigo ka zauna, sai mu shiga wata motar”

Ya sauke ajiyar zuciya tare da jan dagon numfashi ya fi sau goma, sannan ya shuri motar da kafarsa da karfi.

“Duk wanda yayi min haka da gangan yayi, saboda a bata min rai”

“Toh waye zai maka haka Captain? Dan Allah karka bata ranka, na gano, yanzu haka ba zai wuce bakar matar can ba Kaltume, domin na dade da lura da yar bakinciki ce ta karshe”

Momy tana maganar tana jin kamar ta yi tsalle taje ta shake wuyan Hajiya Kaltume.

“Oh kekam baki zaune cikin mutane kwarai Hajiya Nafisa, rayuwa a gidanku tana da wahala”

Momy ta amsawa Hajiya Turai tana kwafa.

“Barta na san yadda zan yi maganinta, da ni take zancen, Captain yi hakuri shigo ka huta sai ka dauki motata ku tafi da ita, idan an gyara wannan Musib zai kai maka ita gida”

Jameel ya juyo ya nufo hanyar falon, sai duk suka dugunzuma suka biyo bayansa, ban da Hajiya Turai da bata matsa daga inda take tsaye ba tun bayan da suka fito daga falon. Cikin natsuwa da kamala ya shiga falon, sai ka rantse ba shi ne ya gama bacin rai a waje ba, zaunawa yayi ya hade hannayensa ya sadda kai kasa ya rufe ido yana motsa bakinsa a hankali, kokari yake na ganin be bar bacin ransa ya ninku a zuciyarsa ba...
[10/20, 6:25 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆
                 

𝐁𝐲 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy

https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy


𝗣𝗮𝗴𝗲 1️⃣4️⃣


Namra ta dago ta dubi kofar shigowa falon tana amsa sallama, sai ta mike tsaye da sauri tana kallon Captain da mamaki, zuwansa a yanzu ya bata mamaki tsabanin baya da bata mamakin zuwansa domin ya saba zuwa gidan a duk lokacin aiki ya kawo shi ko ziya, tana mamakin zuwansa ne kasa da wata uku da faruwar abun da ya fusata shi, wato fasa masa tayun mota da Hamad yayi suke zaton Hajiya Kaltume ce ta saka aka aikata haka. Ba kasafai yake sake zuwa gurin da aka bata masa rai ba, idan ma zai sake komawa a gurin sai ya dauki lokaci mai tsawo har an manta da shi yake sake zuwa, wannan ya saka duk wani makusancinsa da yake son alaka da shi ta daure ko da iyayensa yake kokarin kiyaye duk wani abu da zai batawa dan gatan Ammy kuma ďa daya tilo ga Alhaji Aliyu Turaki. Wata kila haduwar jinin da Allah ya saka tsakanin Momy da ďan Yayanta ya wuce yayi mata haka. Fuska ba yabo ba fallasa ya shigo falon hannayensa duka biyu suna bayansa.

“Sannu da zuwa Ya... Captain”

Tunawa da ta yi baya son ace masa Yaya ya saka ta kasa karasa sai ta kiranshi da sunan da kowa yake kiransa.

“Yauwa hutawa kike?”

“Eh bari na kira Momy tana ciki”

Tana juyawa ya dakatar da ita.

“No Wait... Ina yarinyar nan take Namra?”

Ta juyo tana wara alamar bata fahimce wadda yake tambaya ba.

“Wata fara haka mai dan tsayi marar jiki, mai saka glasses”

“Oh Hurriya, tana bangaren Hajiya a kirata”

Ya daga mata kai, sai ta aje remote din hannunta ta nufi kofar fitar ta fice da sauri, da mamaki da tunanin dalilin kiran Hurriya ta isa bangaren Hajiya Kaltume, sai ta ci karo da Hurriya tana rike da tiyo tana watsawa motar Yasir ruwa, Hamad kuma na ta kada kumfa.

“Hurriya”

“Uhmm”

Ta juyo ta kalleta.

“Wai ki zo ana kiranki Captain...”

“Waye Captain...?”

“Ina wani wadda na ganku tsaye a bakin kofar Momy har na dauko miki glashinki da ya fashe? Kin tuna”

Hurriya ta yi shiru ta dan bata fuska, kuma ta kasa amsawa Namra da ta tuna ko ba ta tuna ba.

“Wanda ya mareki?”

Hamad ya tambaya, Hurriya ta daga masa kai Namra ta zaro ido domin bata saka ran marinta yayi ba, ta san dai akwai abun da yake faruwa.

“Au daman marinki yayi? Ikon Allah me kika masa?”

“Wucewa na zo yi ban gani ba muka yi karo shi ne ya mare ni har gilashina ya fashe”

“Ni kuma na fasa masa tayun mota duk biyu da wuka”

Namra ta rufe baki with mamaki. Hurriya ma masa kallon rashin jindadi fadar da yayi a yanzu.

“Daman kai ka fasa tayun nan? An kusan yaki a gidan nan fa saboda an fasa tayun Captain, Allah ya tsare ka Momy bata sani ba, da sai ka zama abun tausayi”

“Ni ina ruwana”

Ya fada yana turo baki.

“Captain akwai zafin zuciya ko shi zai iya maka hukunci babu ruwansa da alakarka a gidan nan, to yanzu dai shi ya ce a kiraki”

Hurriya ta ake tiyon kasa ta nufi fanfon ta kashe sannan ta bi bayan Namra, Hamad kuma ya cire hannayensa daga cikin kumfan da yake kadawa ya bi bayan Hurriya. Ita dai bata san ta masa laifi a yanzu ba balle ta yi zaton mari ne ko cin mutumci, sai idan kuma cewa za'ayi ta haifar masa da ciwon kirji saboda kanta ya bugi kirjinsa. Namra ce ta fara shiga sannan Hurriya sai kuma Hamad dake bayanta. Yana tsaye a gurin da Namra ta barshi sai dai wannan karon gefen kujerar da Namra ta tashi yake kallo ma'ana kofar falon ta koma gefensa na dama sabanin dazun da ya bata baya.

“Gata nan”

Namra ta fada, sannan ta zauna Hurriya ta karaso inda yake ta tsaya gabansa ta kalleshi sau daya ta sauke kai kasa, Hamad kuma yake tsaye kusa da kofar falon yana kallon ya ga abun da za'ayi ma yar'uwarsa. Captain ya maido ta hannayensa gaba ya mika mata box din da ke hannunsa da hannunsa na dama ba tare da ya ce komai ba. Ko be fada mata ba, ta san box din glasse ne domin shi dabam yake ta ka ganshi kana ganewa balle kuma ita da take 5&6 da glass. A hankali ta dago ta kalli fuskarsa bayan ta kalli gilashin sannan ta kalli Hamad ya watsa mata harara duk ya bi ya bata rai, domin har yanzu haushi Captain din yake ba shi, daman kuma shi be iya tsana ba idan ya tsane ka sai Allah ke kasa ku sake shiri da shi. Captain ya karkarata da kansa kadan ya kalli Hamad da sai a lokacin da ya san da shi tsaye a gurin sai kuma ya kalli Hurriya. Ita ma ta kalleshi ta dauke kai ta nufi kofar fita daga falon ba tare da ta ce masa Komai ba balle kuma har ta karba, sai da ta fara ficewa sannan Hamad ya bi bayanta yaja kofar falon ya rufe. Captain ya matse box din gilashin dake hannunsa da mugun karfi ya daga kansa sama ya rufe ido.

“Allah ya sassauta min kar na kashe yarinyar nan....”

‘Tab ka kasheta Wallahi kai ma sai an kashe ta dan gata be fi gata ba, ita ma yar gatan banbanta ce’

Namra ta fada a ranta a fili kuma sai ta ce.

“Glasse ne?”

Ya sauke kan ya kalleta.

“Wuka ce”

“Gilashin da Appa yake siya mata mai kyau ne daga waje ake kawo mata”

Ta fada a zahiri a badini kuma sai ta ce.

‘Captain dai kamar ka fi kowa iya bakar magana’

Kamar ta san zai kara mata.

“Wannan a bula na dauko shi”

“Tambaya ce kawai, daman ai na san Hamad ba zai bari ta karba ba, amman ka ba ni zan bata hakuri sai na bata daga baya”

Ya kai dayan hannunsa yana zagayen gilashin da shi.

“Waye Hamad?”

“Kanenta ne wanda ka ga ya tsaya jikin kofa har ta kalleshi, shi ne ya fasa maka tayun mota saboda ka mareta, ni ma ban sani ba sai yanzu yake fada”

Murmushi yayi mai sauti, ya dago ya kalleta ya sake yin murmushi mai cike da mamaki.

“Wow... Nice...”

“Haka ya kamata dan'uwa ya zama, mai kokarin kare yan'uwansa i like him”

Ya fada after yayi taking few seconds yana kallon wani bangare na falon, because he know yayi missing wani part na shi da be taba samu ba, wato yan'uwa da suka hada uwa ko uba ko ma uwa da uban gaba daya.

“Amman haka ba zai hana a hukunta shi ba, they have to pay for what they did”

Ya juya ya fice daga falon ba tare da ya nemi a kira masa Momy ba, daman kuma ba dan ita ya zo ba wannan karon, ya zo ne domin baya Hurriya gilashin da ya siyo Saudiya saboda ya fasa nata, and that slap da yayi mata ya tsaya masa after ya bar gidan saboda lura da yayi da bata gani sai da gilashin kamar yadda Namra ta tabbatar masa tun a wacan ranar. Namra ta san me yake nufi they instead of he, wato Hurriya saboda ta ki karbar gilashin Hamad kuma saboda ya fasa masa tayun mota. Sai da ta leka ta ga tashin motarsa sannan ta saki curtains din tana fadin.

“Ban da kai Captain ana kyauta dole ne, ko ni ce ai ba zan karba ba, ka yi zafin hannu ba wani uzuri da an maka abu sai zafin zuciya”

Ta nufi upstairs, sai da ta fara leka dakin Momy ta ga har lokacin bachi take sai ta ja mata kofar a hankali ta nufi dakinta.




HAJIYA KALTUME POV.

“Yanzu kina da number Salame?”

“Eh ina da ita, ai ko shekaran jiya ta zo gidan nan, har take min zancen Malamin ni dai ban tanka ta ba, domin damuwata ta isheni kar na yi abun kunya”

“Kunya Hajiya fatee? Tofar da yawu, har abada ba zamu taba kunyar duniya ba lahirar ma muna fatan nasara, saka number ki kirata ki ce ta turo miki number Malamin ko kuma idan ta samu lokaci ta shigo sai ku yi magana”

Hajiya Kaltume na rufe baki Hajja Fatee ta dauki waya ta shiga laleben number Salame. Knocking aka yi har sau biyu sannan Hajiya Fatee ta amsa.

“Waye?”

“Hajiya Yaron nan ne ya sake dawowa fa, kuma mai Baba mai gadi ya ce yayi yayi da shi amman ya ki tafiya shi sai ya ganki”

Hajiya Fatee ta hanye wayar ta rafka tagumi.

“Oh wannan fitinanne yaro ba zai bar ni da abun da ya ishe ni ba”

“Waye haka?”

“Wallahi wani yaro ne na dauka aikin ba fulawa ruwa, ashe barawo, ni ban sani ba, irin yaran nan yan sare sare, wata rana suka zo nemansa har da fasa mana gida aka ayi, tun daga lokacin sai na sallame shi, amman yaron nan ya ki ya rabu da ni, duk lokacin da wani abun ya same shi sai ya zo ya fada ko mai dadi ko marar dadi, ko kuma ya ce ya zo gaishe ni, yanzu ya bi ya fitine ni yau sati biyu kullum sai ya zo wai mahaifiyarsa bata da lafiya ni yake son gani”

“Ikon Allah toh ke Hajiya irin wadannan yaran ai suna da amfani wata rana”

“Hmmm baki san yadda suke fitinar mutum ba ne, ga su da shegen na ci idan sun ga samu”

“Bari na yi magana da shi, ki kira Salame yanzu”

Hajiya Kaltume ta mike tsaye tabur tabur ta fice daga dakin, Hajiya Fatee kuma ta shiga kiran Salame da wayarta.

“Ina yake?”

Hajiya Kaltume ta tambayi one of masu yi ma Hajiya Fatee aiki da ta zo sanar da Hajiya.

“Yana can gate”

“Muje na ganshi”

Mai aikin ta wuce gaba Hajiya ta sauko tana bin bayanta har suka fita falon suka isa gate ta tambayi mai gadin ina yake.

“Yana waje Hajiya kullum sai ya zo kuma ita Hajiya ta ce kar a barshi ya shigo”

Ya bude mata karamar kofar gate din ta leka waje ta ganshi zaune daf da gate din, a take gabanta ya yanke ya fadi domin ya tuna mata da lokacin da suke cikin daji hannun yan ta'adda, ga fuskarsa duk tambo alamar ya sha sara har ya gaji, bakinsa baki kirin ido kamar an daka tarugu tsabar ja, jiki a murda kamar gashin kansa, kana ganinsa ka ga rikakken dan ta'adda.

“Kai ne kake neman Hajiya Fatee?”

Hajiya Kaltume ta tambaya cikin karfi hali domin zuciyarta har wani zillo take.

“Ni ne Allah ya taimakeki, Hajiya Wallahi ina cikin matsala ne, su kuma wadan nan watsatsin masu aikin kullum na zo sai su hana ni shiga, ba dan ina ganin mutumcin Hajiya Fatee ba da yanzu na farka cikin mai gadin nan Wallahi, sai dai Hajiya tana da kima a idona kamar uwa take a gurina ba zan iya haka ba”

Magana yake da irin muryar mazan nan da shaye shaye ya gama canja kalar muryarsu ta koma mai ban tsoro. Hajiya Kaltume ta yi murmushin karfin hali.

“Ka kyauta haka ake so ai, ya sunan ka?”

“Sunana Isiyaku, amman dai wasu kan ce min Danja yan sunanayen nan dai na zamani Hajiya”

“Toh Amman me kake so gurin Hajiya?”

A take ya fara kuka kamar wani yaro ko wawa kukan da babu hawaye sai zallar iskanci.

“Hajiya Gyatuma aka kwatar a asibiti, kuma ba ni da ko sisin na magani, ita Hajiya Fatee ta sani ba na wani aiki bana sana'ar komai tun da na bar gidan nan ban sake samun wani aikin ba, ina cikin matsala bana da gata sai Allah sai Hajiya Fatee so nake ta taimaka min da kudin magani, kar gyatuma ta mutu Wallahi Allah akwai matsala idan ta mutu ba a taimaka min ba, duk mai hannu a ciki sai na ci uwatar...”

Yana fada yana hada hannu biyu ya buga, Hajiya Kaltume ta dan ja baya sannan ta kalli mai aikin ta ce.

“Zaki iya tafiya”

Sai da mai aikin ta yi nisa sannan ta taka kafarta ta fito daga cikin gidan ta taka nesa da gate din yadda mai gadin ba zai ji abun da zata fada ba. Sannan ta tsaya ta kalli Danja ta ce.

“Nawa ne kudin maganin?”

“Toh Hajiya dubu talatin ne, amman dai ko dubu biyu ko biyar aka taimaka min da su duk taimako ne”

“Kana da account”

“Akwai account Hajiya amman bana da shi aka Wallahi, kwanyar ce mun sha miyar kuka, daddawa duk ta kwashe basirar, tuwon dawa ma haka ake baza mana shi a ture, kai mun ci wuya Wallahi ga talaucin nan har yanzu be bar mu ba”

Hajiya Kaltume ta yi dariya har lokacin tsoro be fice ta ba, domin muryarsa ma abar tsoro ce balle kuma ka kalleshi.

“Kana da waya?”

Ya dan sosa kansa ya shafa aljihu.

“Wayar ce Hajiya ko an siya idan ka ji eh ya ne tana damun cikinka dole mu siyar mu siye abinci, line ma dari da hansi na siyar da shi shekaranjiya”

“Toh yanzu idan ina son magana da kai za mu yi kenan?”

“Ki fada min gidanki kawai zan zo na sameki har dakinki”

“Aa ni da Hajiya Fatee duk ba mu gama warkewa daga damuwar da muka shiga ba, baka san yan ta'adda suka kama mu ba?”

“Kai na ji Hajiya, zuwana talatin gidan nan sai ace min bata nan, wai wasu ne suka kamata, da an fada min ba za a biya sisi ba zan karbota ni sai a ba ni kudin, akwai mutanenmu fa masu harkar kuma ni Wallahi jan wuya ne, bana inda bana iya shiga, karfe be fasa ni bundiga bata kama ni sai dai ayi min tambo, danjar nan da kika ji ance Hajiya ni fa danja ne, uban fitina kuma bana tsoron kowa”

“Kai zaka iya aikata komai kenan Danja?”

“Zan iya komai Hajiya mun zubar da hannaye mun cire kafa, rai ma mun wulgar da shi barzahu, Allah dai ya shirya mu kawai”

“Shiyasa Hajiya take tsoron ka, ni ma ina gudun na janyo ka jiki na jawa kaina matsala”

“Kai... Kuturi”

Ya rike baki.

“Wai Hajja Fatee tsorona take? Ita din ai uwa ce ba za a mata komai ba, wani ma be isa ya mata ba balle kuma ni, ba dan ita ba da yanzu na barar da hanjin masu aikin nan nata, alkur'ane da yanzu ka ga hanta ya lilo shushushushushuuuuuuu”

Ya nuna yadda hantar zata rika raea idan ya sareta.

“Toh yanzu dai zan shiga gida, zan aiko mai aiki da number wayata idan ka samu waya sai ka kira ni mu yi magana, amman dan Allah ka daina damun Hajiya Fatee da yawan zuwa”

“An gama amman Hajiya yanzu akwai wani abu nan? Ina fatar ke ma kina da yan abubuwa yan timatinmai eh... Eh.. Kin dai gane”

“Zan aiko mai number tare da kudin da zaka hau babur ka koma”

Tana fadin haka ta yi gaba tana nufi gate zata koma ciki, shi kuma ya bita da kirari yana daga mata hannu.

“Chau chau chau chachachau lafiya lau ne Hajiya, Allah dai ya kara miki kwanciyar hankali ya kara miki ƙiba kai kana ganin Hajiyar nan ka san akwai manyan kaya, Allah ya kara sutura”

Cikin gidan Hajiya Kaltume ta koma ta shiga dakin Hajiya Fatee ta samu biro ta mikawa Hajiya Fatee domin ita bata iya rubutun ba.

“Rubuta masa number ta a nan”

“Numberki kuma? Me ya faru? Karki jawa kanki matsala fa irin wadannan ba su jin magana”

“Ke dai rubuta babu komai, ke na ke yi ma jihadin ai, wayo yake masa”

Hajiya Fatee ta karba ta rubuta mata number ta mika mata. Hajiya Kaltume ta bude jakarta ta dauko 3k ta hade ta takardar ta fita falo ta bawa mai aikin ta umarce ta da ta kai masa. Sannan ta juyo ta dawo dakin tana tambayar Hajiya Fatee ya aka karkare da Salame.

“Na kirata na mata bayani, ta ce ai ya canja line saboda rufe masa wacan da masu gidan line suka yi, amman yanzu zata turo min sabuwa numbersa kuma zata kira ta masa bayani”

“Haka nake son ji, to yanzu ki kwnatar da hankali ki kira ki fada masa ya shirya komai na sa ya zo garin nan zamu aika da mota a dauko shi a kawo mana har gida, daga nan sai mu gabatar masa da matsakarmu”

“Amman kina ganin zai yarda ya zo?”

“Hajiya Fatee miye kudi ba zai yi ba? Muradi dai abashi kudi shi kuma ya biya mana bukata kawai”

“Ni dai Allah yasa cikin nan ya tausu, idan ba haka na zan shiga uku ga shegiyar suruka zata ji dadi”

“Komai zai wuce Hajiya Fatee ki kwanatar da hankali”

Cewar Hajiya Kaltume ga aminiyarta tana murmushi.



IYAMI POV. .

“Iyami ba a zama haka, ke kanki kin san mijinki yana sonki, ga yaya yanzu kuma ga cikin nan da kika shiga watan haihuwa, kamata yayi ki nemi taimako idan ma wani asirin aka yi masa aka rabaku a karya shi, ki koma dakinki bana son ki haihu a gida Wallahi”

Amma ta yunkura da katon cikinta ta tashi zaune daker tana kallon Hindu dake maganar.

“Hindu, Wallahi ban taba yi ba, su kansu da suke ganin kamar asiri na yi ma Alhaji yake ta so na ko na malleke shi, ban taba bada naira biyar na ce a mallake min Alhaji ba, tsantsar biyayya ne kawai da kawar da kai da kuma jin maganar duk abun da ya fada, ni yanzu ko zaki dora wuka a wuyana ba zan iya fada miki sunan Malami daya da na sani ba a garin nan, ban taba yi ba, Gwaggo ma bata taba ta yi ba mu ba mu da kowa sai Allah”

“Na sani, to ai tambaya ake kin ga har na tsarin jikinki sai ki sha kuma ki bawa yayanki, domin su ma ba barinsu zata yi ba”

“Ni dai ba zan iya ba, na kai kukana ga Allah shi zai min magana, ko yanzu ai ba yadda suke so suka samu ba, duk wata sai ya aiko min da abinci da kudi saboda cikin nan, yanzu kuma kina ganin yadda aka cika harabar gidan nan da itace saboda na shiga watan haihuwar, na san idan ra'ayinsu za a bi ba zasu so haka ba, yarana kuma idan ya auna lokaci ya kan aiko da su su gan ni na gansu, an rabu ne kawai amman kamar ana tare, idan Allah yayi zan koma sai ki ga na koma kamar yadda ban saka ran auren Alhaji ba Allah yayi kuma aka yi auren”

“Toh Allah yasa haka shi ya fi alheri, amman dai da kin tafi ba a san inda za a dace ba”

“Allah ya hada mu da dacewar”

“Ameen”

Ta amsa ba dan ta jidadin yadda Iyami ta ki amincewa da zuwan ba.
[10/20, 6:26 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆
                 

𝐁𝐲 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

Pease ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy

https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy


𝗣𝗮𝗴𝗲 1️⃣5️⃣

Salame na turo number Malamin Hajiya Fatee ta kira shi a waya, suka gaisa ta fada masa abubuwan da suka faru ya jajanta mata, ya kara mata da cewar shi ma layinsa aka rufe shiyasa bata ji shi ba. Hajiya Kaltume ya karba suka gaisa sannan ta dora masa da banin abun da ya sami Hajiya Fatee, daga karshe suka yanke ranar da zai shigo garin. Sannan Hajiya Fatee ta iya fita dakinta ta samu ruwan tea ta sha domin bata iya cin komai. Hajiya Katume bata jima a gidan ba Fadeel ya shigo gaishe da mahaifiyar, da zai fita Hajiya Kaltume ta bukaci ya sauke ta gida.



*** *** ***

Ba kadan ran Momy ya ba ce ba, jin

1 Comments On HURRIYA Book 1
avatar
rahmat-2-8

1 year ago

Reply

Love it

Please Login or Register in order to submit comment