Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kare kansu ko maida martani amman Iyami bata cewa idan yana fada har yayi ya gama, ko daga kai ba zata yi ta kalleshi ba, wannan ta saka suke yawan yi mata kallon munafuka, hawaye shar Momy take yi daman kuma bata gama hucewa daga bacin ran abun da aka yi ma Captain ba.

“Eh sai Iyami, abar kaunarka, yanzu gashi nan ka rufe da fada akan yayanta, matarka Kaltume kuma ta takura min ta takurawa bakina, yanzu Captain ne ya zo, ka san dai yadda nake da Captain amman haka matar nan ta saka aka fasa mata tayun mota saboda bakin ciki, ban gama huce wannan haushin ba gashi nan kai kuma ka zo ka rufe ni da wani, toh Wallahi ka jawa yayanka kunne su daina munafurci, kuma ka jawa matarka matarka kunne ta fita safgata da ta bakina babu ruwanta da ni idan ba haka ba Wallahi za 'ayi tashin hankali da ba taba yi ba ko a lokacin da ka auro karamar yarinyar can Iyami”

“Ni dai na fada miki, karki sake banbanta min to ƴaƴa duk daya suke a gurina, babu wanda ya fi wani, zan iya canja mata ban canja ƴaƴa ba bana ni da kamar ƴaƴana!”

Yana kawai nan ya juya ya fice, cikin motarsa ya koma yaja ta zuwa bangare ya ajeta ya fito ya taka da kafa ya nufi bangaren Hajiya Kaltume yana shiga ita ma ya salllami yaranta suka haura sama ban da Yasir da baya gidan ma a lokacin ya fita gurin safgoginsa, Namra kuma ta fita zuwa bangarensu. Fada yayi mata sosai yana ja mata kunne akan abun da ta saka aka yi ma Momy.

“La'ilaha Illallahu ni Ummul Kultoon, yaushe kuma aka yi haka? Ni miye ruwana da Nafisa balle kuma bakinta, yanzu Fisabillahi na rasa me zan saka ayi mata sai fashe tayar baki? Abu dai kamar karamar yarinyar? Ni da nake ta kaina ma? Yaushe na fito daga daji? Kofar daki ma bana sha'awar fita balle kuma har na saka ayi wani abun, shigowar nan da ka yi ma hankalina sai da ya tashi”

“Ni dai na gargadeku, bana son wani tashin hankali kowa ya zauna lafiya kuma ya tsaya a iya matsayinsa, ku bar ni da abun da yake damuna, kullum ni ne cikin fitina kamar akaina aka fara mata aure da mata biyu”

“Mata uku dai Alhaji, yaushe ka saki yarinyar can Iyami da har zaka dawo kanmu nu kadai, musamman ni, taya za a ce na fasa tayar mota? Yara ma wa zan saka yayi wannan aiki? So take ta zugaka ka koreni a gidan kamar yadda ka kori Iyami, to Wallahi ni kam zama daram dam dam dam sai mutuwa, kuma Alhaji dan Allah ka rika bincike kamin ka fara fada, Wallahi sheri ne kawai na kishiya da neman hada mata da miji, abun da ba ayi ba da kurci ayi shi yanzu”

“Na dai ja muku kune, kowa ya tsaya iya matsayinsa bana son sake jin wata fitar”

Har Appa ya fice Hajiya Kaltume bata gama mamakin jin irin kagen da Momy ta yi mata ba, Salma ce ta fara saukowa sannan Khairi suna tambayar me ya faru domin sun lura da yadda mahaifinsu ya shigo cikin fushi.

“Wai munafurci matar nan ta hada, wai na tura an fashewa bakinta tayun mota, shi kuma babu tsayawa bincike da yake ta mallake shi komai ta fada masa shi yake yi kawai ya zo ya rufe ni da fada, ai bari Wallahi ita ma sai ta bar gidan nan Kamar yadda Iyami ta fitar da ni, waya sani ko gurin tsafinta ta tafi aka bata wani asirin ace ta zo ta hada mu, gaba daya ta mallake Alhaji ta juye masa kai komai ta fada sai ya hau ya zauna”

“Tab Lallai Momy ta yi nisa, wane irin fasa tayun mota kuma?”

Hajiya Kaltume ta kalli Salma dake maganar.

“Sheri ne kawai a samu yadda za a hada ni fada da Alhaji sai ya sake ni”

Haka Hajiya ta yi ta jininin maganar tana ta masifar har yamma.




*** *** ***


Hajiya Binta dake gidan baya tana shafa kan Hurriya dake kwance jikinta ta ce.

“Tsoho kamin ka kai ni gida, ina son ka biya da ni gidansu Iyami na dubata yaranta ma su ganta”

Kamar wadda aka cewa ya shiga ramen wuta haka Appa yaji, ko kadan be son abun da zai kusantashi da Iyami gashi kuma be isa ya musawa Hajiya ba.

“Toh Hajiya amman idan na aje ki Yasir zai zo ya dauke ki ya maida ke gida su kuma yara ya dawo da su”

“Toh zamu tafi gidan makiyiyarka ba, Allah ya kyauta”

“Haba Hajiya irin wannan maganar be dace ba a gaban yara ban da alheri me iyami ta yi min da zan dauki kiyaya na bita da ita”

Hajiya dai bata sake cewa komai ba har Appa ya canja hanya ya dauki hanyar gidansu Iyami. A bakin gate din ya faka, ya fito ya budewa Hajiya ta fito tare da Hurriya sannan Hamad ya bude front door ya fito.

“Ba zaka tsaya ta fito ku gaisa ba?”

“A gaishe ta dai Hajiya”

Ya amsa yana kin hada ido da Hajiya Binta, girgiza kai kawai Hajiya ta yi ta cira kafa suka karasa bakin madaidaicin gate din da tuni Hamad ya bude har ya shiga ciki. Yanayin yadda Hajiya Binta ta tararda Iyami be mata dadi ba, daman kuma ta san za'a rine wai an saci zanen mahauciya, mai ciki ba a rabata da laulayi balle kuma ita da take cikin damuwa, sai dai ganin Hajiya Binta ya saka ta ji kamar an dauke mata ciwo, suka ta yi hira kamar yadda suka saba.

“Jiya muke zancenki da Gwaggo na ce ina tuna haihuwar Hurriya da irin hidimar da kika yi”

Hajiya Binta ta yi murmushi.

“Abu kamar jiya, yanzu Hurriya ta cika sha shida cif”

Hurriya ta wara ido tana mamaki yadda ta manta birthday dinta.

“Eh fa Hajiya amman ai sai October 10”

“To October ba ya kusa ba? Miye rage yan kwanaki ne kawai”

“Hajiya zaki yi ma Appa magana yayi min celebration please”

Iyami ta ce.

“Kin san halin Appanki ba son irin abubuwan nan yake ba, shi gaba daya rayuwarsa irin ta mutanen da ne”

“Zan masa magana da kaina, maybe zai yi min gashi ma dazun ya fada mana a falon Hajiya ya ce ni da Hamad a waje zamu yi karatu”

Mamaki ya cika Amma har sai da ta bude baki ta kalli Hajiya dake murmushi.

“Shi da kansa?”

“Shi da kansa fa, sai dai ki yi ta addu'a kuma ki yi musu, ai maso uwa ya so yayanta, abu dai ne idan ya zo babu yadda za'ayi sai hakuri kawai, amman sakin nan ba karamin mamaki ya ba ni ba”

Amma ta sauke kai kasa tana jin wani rashin dadi yana ziyartar zuciyarta. Hurriya ta tashi ta fice zuwa dakin Anty Rukayya haka take jjnta kamar wata sa'arta saboda tana wasa da ita sosai kamar yaya da kanwa, wannan ya saka Hurriya bata kallon Rukayya a matsayin kanwar Amma sai idan babin girmamawa ne, ba ita ba ko Hamad wasa yake da ita, daman kuma hausawa sun ce karamar uwa madaukar zunubi. Amma ta ce

“Haka Allah ya so Hajiya komai Allah ne yake tsarawa Allah dai ya ba mu ikon cinye jarrabawar wannan jarabarwar”

“Toh Ameen ina nan ina ta addu'a, da yardar Allah Iyami sai kin koma dakin domin sakin nan naki har hawan jini yake son tasar min, Allah ya sauke ki lafiya, da na shiga gidan ma sai na ji duk yayi min dabam”

“Ameen”

Amma ta amsa tana jin zafin barin gidan Appa da ta yi, ba tare da laifin komai ba. Gwaggo ce ta shigo suka suka ta hiran kowa yana fadin abun da ya fahimta game da lamarin, Amma kuma tana fadar yadda Appa ya canja mata tun kamin sakin. Cikar da cikin Hajiya Binta yayi a gidan danta be hana ta cin abinci a gidan Amma ba, saboda tana son Amma kuma ta san idan bata ci ba Amma zata ji babu dadi domin abinci Amma take fara ci kamin ta ci na kowa wani lokacin ma bata taba abincinsu sai ta ce ta koshi. Bayan sallah la'asar Yasir ya iso gidan daukar Hajiya Binta kamar yadda mahaifinsa ya umarce shi, cikin gidan ya shigo suka gaisa da sannan ya fito tare da su Hurriya a daidai lokacin da Rukayya ta sallami bakonta ta nufo karamar kofar shiga tsakar gidan da suka fito.

“Yasir ya gida”

Ya sake mika masa gaisuwa a karo na biyu bayan gaisuwar farko da suka yi a lokacin da ya shigo.

“Mutumen da na gani saurayinki ne?”

Wani kallo ta yi masa jin yadda yayi mata tambayar kai tsaye kamar da zolaya kuma kamar gaske, domin murmushin dake fuskarsa ya hanata fahimtar komai.

“Dan makarantar mu”

“Dan makarantarku har cikin gida? Lallai yana da matsayi da alama”

Murmushi kawai ta yi ta maida dubanta gurin Hajiya da Amma ta rakota suna tafiya suna hira.

“Allah ya kiyaye hanya, Hurriya sai kun dawo”

“uhmmm za a shiga a cigaba da karatun ko? Ko last time da na zo har na fita baki sani ba tsabar karatun littafan soyayya, to aje a karasa kar a manta page din da ake”

Ta girgiza kai still tana murmushi.

“Yasir ka cika shiga min hanci fa... Haka kemin idan na je gidanku ko zama na yi sai ka ce ba daidai na zauna ba”

“Toh ki fyato ni mana idan kin isa”

A nan ma murmushi ta yi ta shige ciki, shi ma ya bita da kallo yana murmushi Hurriya da Hamad kam tuni sun kai cikin mota, inda sabo sun saba da ganin tsokanar yayansu akan kanwar Mamansu ba sabon abu ba ne a gurinsu Amma ma ta saba gani balle kuma su. Amma da kanta ta budewa Hajiya mota ta shiga ta rufe sannan ta juya ta koma ciki Yasir ya shiga ya fara jan motar.

“Yasir na ce ko a fara sabunta kayan dakina ne na kusa samun kishiya?”

Hurriya ta saka dariya Hamad kuma yayi murmushi tare da cewa

“Hajiya yanzu kuma kin fasa aurena?”

“Eh ga babba me zan yi da yaro! Yasir ya ishe ni gashi har yana nema min kishiya, ko da yake Kaltume ai ba zata yarda ka dauki wannan ba sai dai wata”

“Ke tsohuwa waya fada miki har yanzu ana irin zamaninku da ake yi ma mutane auren dole? Ni zan zabo wadda nake so na yi aurena”

“To Allah ya nuna mana, kuma ya bada ta gari”

“Ameen”

Ya amsa yana cigaba da jan motar. Sai da ya fara isa gidan Hajiya ya sauketa sannan ya juyo ya kama hanyar gidansu, a harabar Hajiya Kaltume ya faka motarsa ya bude ya fito Hamad ma ya fito tare da Hurriya gaba dayansu suka nufi hanyar falon Hajiya Kaltume.

“Hurriya me ya samu gilashinki?”

Yasir ya tambaya domin tun zuwansa daukarsu ya lura da fashewar gilashin nata. Ta kai hannu ta taba gilashin.

“Faduwa na yi”

Karaf Hamad yayi ya ce.

“Karya take wani bakon Momy ne ya mareta ni kuma ya na fasa masa tayun mota gaba daya”

Daga Huriyyar har Yasir tsayawa suka yi kallonsa da mamakin furucinsa.

“How?”

“Wuka na saka wukar Momy ta yanka ƙashi na yi ta cakawa ina yanka har da sai da na fashe duka tayun”

Maganar yake yana nuna yadda yana yana cize baki alamar ƙeta. Cikin mamaki Yasir yayi dariya ya bugo kan Hamad.

“Baka da kyau yaron nan bura'uba”

Hurriya ta yi murmushi for the second time ta sake jin Hamad ya burge ta a yau, bayan da ya fadi cewar zai zama likita saboda yayi mata aikin ido yanzu kuma ya fasa tayun wani saboda ya mareta, ita dai ta san bata jituwa da Hamad suna yawan yin fada da samun tsabanin amman kuma yana nuna damuwarsa da kulawa a duk wani abu da ya shafeta, idan wani ya taba ta yana jin zafi fiye da yadda shi idan aka masa yake ji. Yasir ya shiga tambayar me ta yi ma bakon yayi mata marin da ya saka gilashinta fashewa.

“By Misteke na fito... ”

Shi kansa be ji dadin jin karami dalili da be taka kara ya karya ba ya saka bakon marinta marin kuma mai zafi.

“Mutane ba su da hakuri kuma ba su da hakuri...”

Ya rufe baki yayinda yake tura kofar falon ya shiga.

“Toh Wallahi ba zan dauka ba, wannan wulakanci da rainin wayon da Nafisa take min yayi yawa”

“Me ya faru?”

Yasir ya tambaya domin shi kadai ne be san wainar da ake toyawa ba. A take ta amaye masa cikinta tana wani cika domin ba karamin cin mutunci ne a gareta ba Momy ta zargeta da haka duk kuwa da irin rashin zama lafiyar da suke. Yasir ya kalli Hamad, Hurriya ma ta kalli Hamad Hamad ya kalleta kowa yayi shiru, shi dai Hamad ba zai yi laifi yace shi yayi ba, kuma idan an gano shi yayi hakan ba zai dame shi ba, Hurriya kuma ba zata tonawa dan'uwanta asiri ba, balle kuma Yasir da ko da yaushe yake kashe wutar fitina.

“Toh Hajiya Ki yi hakuri, dan Allah ku daina wannan fadan, bana jin dadi haka Appa ma ba dadi yake ji ba, kuma dai ba yara kuke ba be kamata ace kuna biye zuciya ba”

Hajiya ta daki cinyarta

“Wallahi ba zan hakura ba, sai ta dandana kudarta, kuma Wallahi na fi karfinta bokanta yayi karya Wallahi, Iyami ma ta kara da ni ta bar ni balle ita bukkar banza, mai karyar arziki sai ka ce kanta farau arziki duk ta fi ta cikawa mutane gida da bakin kuri da iyayi ita diyar mai kudi, mun ji karuna duk arzikin ubanta be kai karuna ba, ni kuwa sai na zame mata fir'auna a cikin gidan nan”

“Subhanallahi Hajiya dan Allah ki daina irin maganar nan haba”

Yasir ya fada cike da damuwa, domin baya jin yadda matan ubansa suke samun tsabani a gidan.

“Babu ruwanka babu ruwanka idan ba zaka taya ni yaki ba karka sake shiga tsakanina da kowa, dan iya. Ke kuma yar gadon munafurci bace min da gani”

Ta karasa tana watsawa Hurriya dake tsaye tare da Hamad harara, babu bata lokaci Hurriya ta juya ta fice daga falon, Hamad kuma ya tsaya a gurin kamar ba zai tafi ba, irin yadda yara masu fama da rashin kunya suke yi, sannan ya fice yana wani tukuki saboda saka sunan uwarsa a fadan da Hajiya Kaltume ta yi kuma ta kira Hurriya da yar gadon munafurci.




____________________

Masu karatun suna hango abun da nake hangowa? 😳
Akwai Bomb fa ba karami ba? Fatan dai kun shiryawa tafiyar? 😁

Idan kun karanta ku yi sharing 🥰
[10/18, 6:16 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆
                 

𝐁𝐲 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

Hello Habibaties 😍🥰
Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy

https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy


𝗣𝗮𝗴𝗲 1️⃣1️⃣

Hanya Hurriya ta hadu da Hamad ya zo zai kirata domin ita Hajiya Binta ta fara tambaya daga isowarta gidan.

“Me ya same ki? Hajiya na kiranki tana bangaren Appa”

Ya tambaya kamar irin hankalinsa be tashi ba dan ya ga hawayenta.

“Momy ce ta yi baki shi ne namijin ya mare ni”

“Me kika masa?”

“Ban masa komai ba, kawai saboda na je fitowa da sauri shi kuma zai shiga na buge shi, shi kuma ya mare ni gilashina har ya fashe, da jikinki kamar itace mugu kawai”

Ta farasa tana kuka ita ma kanta ciwo yake an karon da suka yi, balle kuma shi da bata san yadda ya ji ba.

“Ina yake?”

“Yana bangaren Momy”

Ta bashi amsa ta bar shi a gurin tsaye yana kallon apartment din Momy kamar mai tunani tafiya, ita dai ta yi gaba abinta, har Namra ma ta zo ta wuce Hamad na tsaye a gurin yana kallon part din. Hurriya na shiga bangaren Mahaifinta ta rungume Hajiya ta fashe da kuka. Hajiya Binta da tsayi ke neman gagararta sakamakon rikon da Hurriya ta yi mata kalli Alhaji Haruna.

“Kalli abun da ka yi”

Appa ya sauke kansa kasa ba tare da ya ce komai ba.

“Allah ya kyauta”

Hajiya Binta ta fada sannan ta taka a haka ta isa gurin kujera ta zauna Hurriya na rike da ita, har jikokinta da matar ďanta Momy suka shigo suka gaisheta, suka fita Hurriya bata dago daga jikinta domin ji take kamar Amman ce ta rumgume, wani gatan ma da kakanin suke mata Hajiya Binta da Gwaggo Amma bata mata irinshi.

“Kullum idan na zo gidan nan bangaren Iyami nake sauka, amman yau ka raba wannan a dole na sauka a nan, mace mai hankali da girmamawa, wannan matar ta san kimata, har abada ba zaka taba samu mace mai irin tarbiyarta ba tsoho”

Appa ya sauke ajiyar zuciya domin ya san gaskiya Hajiyarsa take fada, iri irin Iyami masu son iyayen miji da girmamasu kadan ne a duniya ba su da yawa.

“Hajiya ga abinci ki bari na zuba miki”

“Aa Hurriya zata zuba sai mu ci tare ai kasan da ita na saba cin abinci idan na zo”

Appa yayi murmushi.

“Hurriya dago haka Hajiya ta ci abinci mana”

Hurriya ta dago ta bude kulolin ta dauki plate ta fara zubawa. Sai a lokacin Appa ya lura da fashewar da gilashinta yayi.

“Me ya sami gilashinki Hurriya?”

“Faduwa na yi”

Ta yi karya kai tsaye. Hajiya ta kalli Hurriya sannan ta kalli Appa ta ce

“Kana da dai jin abun da Hamad ya fada min a mota, idan ba zaka dauki mataki ba ni zan zo da kaina na dauke yaran nan na maida su gidana, domin ba zan bari a rika wulakanta kamar wasu bare ba”

Appa ya shiga mata rantsuwa domin kare kansa.

“Wallahi Hajiya, ban san da duk wannan ba, ai kin san idan na sani ba zan bari ba, ni kaina sai a yanzu nake ji a gurin Hamad din, kuma In Shaa Allahu zan dauki mataki, Hurriya me yasa baki fada min abubuwan da suke faruwa ba?”

Hurriya ta kalli Appanta ta sauke kai ta cigaba da zuba abinci, daman ta sani ko da Hamad be yi ikirari ba zai iya fada balle ma har yayi.

“Wallahi ban sani ba, amman zan dauki mataki yanzu da yardar Allah”

“Na dai fada maka, dan ba zaka saki uwarsu ba, kuma ka barsu ana musguna musu kamar wasu ba yi, har dokoki ake saka musu a gida, kuma duk tarin masu aikin gidan nan ace Hurriya sai ta share dakinta da na Hamad su sauran yaran ai ba haka take musu ba, shiyasa tun a lokacin da na ji ka saki Iyami na kira Nafisa da Kaltume na ja musu kunne akan yaran nan ashe na yi a banza, da Iyami ce ko ba zata jefar da magana ta ba”

“Za a gyara Hajiya, amman dan Allah ki aje maganar daukarsu ko maida su gurinki, tun da Iyami ta bar gudan nan yaran nan kawai nake gani ina jin sanyi, idan kika dauke su karin wata damuwar ne a gareni”

Hamad ne ya shigo falon rike da karamar wuka a hannu ya zauna kusa da Hajiya Binta ya aje wukar gefe.

“Me ya hadaka da wuka Hamad?”

“Apple na yanka”

Ya amsa tare da daukar spoon ya saka a abinci da Hurriya ta zuba.

“Hamad abinci Hajiya ne fa kana ganin na saka nama da yawa shi ne kuma zaka saka spoon”

A take ya daka mata tsawa.

“Toh ina ruwanki da ni, ba zaki daina shiga min hanci ba ko? Hajiyar ta ki ce ke kadai”

Hurriya ta kalli Hajiya tana turo baki alamar ta fusata.

“Hajiya kin gani ko?”

“Kyale shi zuba mana wani”

Hamad yayi kwafa, Hurriya ma ta yi kwafa daman tana da haushin marin da aka yi mata zuginsa be gama wucewa a kuncinta ba. Ai a take Hamad ya daga hannu zai kai mata duka Appa yayi saurin rikewa.

“Kai Kai Kai Kul daga magana sai ka ce zaka duketa, ita ce yayarka fa, ba zan daukar maka wannan ba Hamad, haka Iyami ke ta fama da kai kai baka san ka ragawa kowa ba?”

“Amman Appa ai ita ta fara”

“Yi mata hakuri kyaleta ai yar'uwarka ce baka da kamar ta, kyaleta”

Ba dan kakarsa Hajiya Binta ta saka baki ba zai bar Hurriya ta zauna lafiya ba, hakan kuma be hana shi sake yin kwafa ba sannan ya fara cin abinci.

“Ni wannan zuciya ta Hamad ban san gun da daukota ba, fushinsa har tsoro yake ba ni”

Appa ya fada yana shafa kan dansa, Hajiya ta ce.

“Zai daina kurciya ce, da zarar ya girma ya mallaki hankalin kansa zai daina, wani lokacin yara idan suna jin tashin balaga haka suke jin kamar daidai suke da kowa, ka bar shi ya cike 20 ko 18 fushin nan duk zai hauka”

“Allah yasa, ya shirya mana”

Hajiya ta amsa da Ameen. Sai da suka gama cin abinci sannan Hajiya ta tashi tare da jikokinta Hamad da Hurriya Appa na gafenta suka fito daga bangaren na Appa zuwa bangaren Hajiya Kaltume domin yi mata jaja da kuma barka da kubuta. Ko da suka shigo falon na Hajiya Kaltume yana cike da yayanta da kuma yayan yan'uwanta da ma ita kanta sai hira ake har da Namra. Kamar ta Allah haka Hajiya Kaltume ta washe baki tana maraba da zuwan Hajiya Binta.

“Sannu da zuwa Hajiya, ai da ma baki zo ba, ga kafafuwa suna ciwo ni kaina idan na warware ai sai na zo na gaishe ki, kuma ai kin kira waya haka ma ya wadatar”

“Aa kara dai na zo, fatar na same ku lafiya”

“Lafiya Kalau Alhamdulillah, ya ciwon kafafuwan yayi sauki?”

“Alhamdulillah”

Sama sama dai suka yi ta gaisawa Appa na zaune kusa da Hajiyarsa daga kasa, Hajiya Kaltume kuma na daga kan kujera ita da duka yaranta, Hurriya da Hamad ne kadai a kasa domin haka Amma ta koya musu idan babba yana kan gado ko kujera to su kuma su zauna a kasa, kar su zauna tare da shi ko kuma a yadda yake zaune. Da hira ta yi hira ne Hajiya Kaltume ta dauko zancen wahalar da suka sha a dajin tana fadar yadda aka rika mistreated dinsu kamar wasu dabbobi.

“Shiyasa ake son a samu soji masu kishin kasa da za su iya yakarsu idan ba haka ba, kasar nan da wahala ta gyaru domin Shugabannin ma sun zama sai a hankali”

Cewar Yasir. Cikin murmushi Hajiya Binta ta kalli Hamad ta ce.

“Da yardar Allah Hamad soja zai yi, wannan fushi da zuciyar ta soja ce”

Hamad ya girgiza kai.

“Aa ba soja nake so ba?”

Namra ta ce.

“To me kake so? Wannan zuciyar taka Hamad ai soja ya dace da kai”

“Aa ni Likitan idanu nake son zama, idan na kware zan yi ma Hurriya aiki ta, ita ma ta rika gani kamar kowa”

Tsit katon falon na Hajiya Kaltume yayi domin babu wanda ya za ci abun da zai fito daga bakin Hamad kenan. Hurriya ta yi murmushi tana masa kallo irin na so da kaunar dan'uwa, ita kanta ba yi zaton Hamad yana sonta kuma ya kula da damuwarta har haka ba.

“Come here my friend”

Yasir ya mika masa hannu, sai ya taso ya iso gurin Yasir din Yasir ya rumgume yana buga bayansa.

“Yayi kyau babban mutum”


Cikin jindadi da alfahari Appa ya kalli Hamad ya ce.

“Da yardar Allah da yardar Allah, Hamad ba zaka yi karatu a kasar nan ba, waje zan kai ka ka sha ilmin akan idanuwa har ka gaji, da ikon Allah wannan kudirin naka sai ya cika ko da bana raye”

Hajiya Kaltume da ta rasa abun da zata yi ta kalli Appa da murmushin dole.

“Za a karya dokar fitar da yara waje karatu kenan Alhaji akan Hamad?”

“In Shaa Allah, ba shi kadai ba Hurriya ma ba zata yi karatu a kasar nan ba, yadda take da kokarin nan waje ya kamata ta yi karatu, kuma ko ba ni ba Principal dinsu ya fada min suna sa ran da zarar ta gama secondary school zata samu scholarship mai kyau a manya kasasshe saboda kokarinta da yadda take cin gasa ta bangaren lissafi”

“Maa Sha Allahu, Allah ya nuna mana yara masu albarka Allahu akbar Allah dai yayi albar....ya bar zumunci”

Sai ta kasa karasa da Allah yayi albarka ta canja zuwa Allah ya bar zumunci, domin ta san hausawa sun ce addu'ar makiyi karɓaɓɓiya ce, ita ko ba zata so su yi albarka

1 Comments On HURRIYA Book 1
avatar
rahmat-2-8

1 year ago

Reply

Love it

Please Login or Register in order to submit comment