Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka kunyatasu tunda anriga andaura maka Aurs dasu.


Wasu zafafan hawaye yaji sun sauko masa akunci dama ashe haka aka shiryi yi masa lallai yau annuna masa rashin kauna kuma saiya nuna shi Abdallah ne

Yakalli mahaifinsa yana kuka kamar wani yaro karami yace "dady Amma wannan matakin da hukuncin naka sunyimin tsauri dayawa walh duka yaran bana sonsu araina kuma baxan iya zama dasu amatsyin matanaba kayiwa Allah dady kasa inwarware wannan Auren Akan nasu walh indai akan yarinyar can dana kawo maka zancen tane to na hkr kabani kowacce ackn "yan uwa amma banda wadancan


Dady yahade rai tamkar bai tab'ayin murmushi ko dariya ba yace da Abdallah

"Kuma ni dasu nake son kazauna kakuma basu babban matsayi ackn gidanka inkuma kanuna min ban isa ba insallama ka

Dan haka kaxaba koni ko ra,ayinka.

Abdallah yayi shiru yana jan ajiyar zuciya ransa na masa quna

Uncle yadafa shi yace masa "Abdallah kaxama namiji gwarxo jarumi mana kadauki wannan tamkar kaddararka knn kayi godiya da Allah dataka jarabawar ma taxo cikin sauki tunda kai da kanka zaka iya daidaita lamarinka wajen karbar taka jarabawar ahannunka manufata karike matanka batare da nunawa ubangijinka cewar baka son zabinsa ba domin zabin Allah ne su kuma zabin mahaifinka dan hk kada kaki amincewa sbd kada kasami sabani akan wannan kaida mahaifinka kaji,

Cikin sanyin jiki yahau gyada kansa da alamar yadauki maganarsa

Dady yadubi uncle da zafin rai da daga murya yace "kasan Allah Alh inhar bai bi wannan abinda na shirya masa ba bai karbi zabin danai masa ba to walh yasani bani bashi bakuma "yan,uwana bashi hakama dangin mahaifiyarsa kada yasa ran xuwansa gunsu dan zan hana su karbeka kuma tsinuwace zata biyo bayanka


Wani abu ne yatsaye axcyrsa lallai dady yadauka da xafi ba dashi xa.ai hakanba ckn kwantar da murya yace da dady


"Allah yahuci zuciyarsa dady na amince zan zauna dasu amatsayin matana

Uncle yace "to aikaji Alh saikasa masa Albarka tunda ya amince da abinda kayi masa.

Dady yasaki rai yace "to naji Allah yayi mk Albarka tashi kaje.

Yatashi asanyaye yafuta


Kai tsaye dakinsu yanufa yatarar da Abdulhakim yafito daga wanka yaxira jallabiya

Da bacin rai yatunkareshi yanunashi da hannu "kai tsohon munafuki ashe Aurena kukaje shine baka gaya minba kuke ta boyaemin kaketa kumbiya kumbiya to walh nasan ma akwai hadin bakinka ack



Abdulhakim yace "hhhmmm koma me zakace kace naji amma kasani cewar kai kaja komi tunda da ace kana daukar shawarata da hakan baxata faru dakai ba


Yanxun da akai hakan wa gari yawaya? Tokasani duk abinda yafaru dakai ka tuhumi kanka


Abdallah yakufula yace "Au haka kace ko?


Abdullhakim yaxuciyo shima yace "nafada din me zaka iya?


Abdallah ya buga masa tsaki yafuta yana xaginsa


Saida yafuta shikuma yaxauna gefen gado yadafe kansa domin yanajin tausayin abokinsa dan,uwansa sosai bayaso yanuna masa ne


Adaidai lokacin da abin duniya yaiwa Abdallah yawane ita kuma Amarya Ni,imah Abin duniya yai mata dadi domin Allah yacika mata burinta yabata wanda ta dade tana kauna

Bata taba zaton wannan rana zatazo mata kwana kusaba lallai angama mata komi da aka jajirce aka ga andaura mata aure da Abdallah


Abu dayane yatsaye mata arai bawai jin Abdallan baya son taba ko baya dokin Auran a,a jin cewar Tanada kishiya ashe su biyune amaren na Abdallahn.


Tabbas inta tuno kyanta da matsayinta na ita dangin arxikice saitaji bacin rai wai ace itace me kishiya "yar kauye


Abinda take yawan tunani shine shin itanma yar kauyen baya son tane? koko ita yakeso ba ita Ni,iman ba …… ????






*Auntyn Sayyada da Shahidah ce*[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:👌🏼
🐄 *"YAR FILLO* 🐄
_Dijen kauye_
🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕
🏕🏕
🏕







*True life Story*





*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S &S)






PG 25 - 30

Tamfatsetsen gida Dady yabaiwa Abdallah me part biyu

Sannan kowanne yazuba furnitures masu tsada da kayan kicin ack

Kowanne part yahadu iya haduwa babu banbancin kaya da akayi sai daga gidansu Ni,imane suka karayiwa amaryarsu wasu karin decoration din suka kuma kara zuba kayan kicin din amaryarsu akan na dady dayayo musu

Ga parking space daxaici motoci uku xuwa hudu agidan sai dakin me gadi akusa da get


Motoci biyu dady yabada aka tafi dauko amarya dije a kauyen rogo wacce suke ashirye suna jiran motocin domin suna da masaniyar aranar za.a xo daukar amarya


Iyayanta kannan uwa da yan,uwan uba da yan unguwa sunyi kara wajen son xuwa birni don suga kwakwaf

"yan rakiyar amarya sunsha kallo sunsha mamakin kyan gidan dady da kyan tsari tamkar Aljannar duniya dayake can suka fara kai amaryar domin saida aka kawo Ni,ima gidan kana aka hadasu akai musu fada da nasiha don su zauna lfy

Dady yayi musu Nasiha me tsima jiki tamkar yadda uba kanwa "yayansa dai


Dije tasha mamakin jin cewar wai ashe da kishiya zata zauna

Lallai data san da hakan baxata taba yarda tazo zaman aure birniba sbd tasan matsaltsalun zama da kishiya da yanda ake fadin kishiyoyin burni suke illata kishiyoyinsu ita kuwa batada gata saina Allah wazata kaiwa kokenta kenan in wata baraka ta sameta? Wata xuciyar tata tace mahaifinsa mana ai mutumin kirkine kuma yana sonki.


Kowaccensu kanta akasa anlullube kai da mayafi sai zabga kanshi suke amma turaran Ni,ima shine yafi daukar hankalin mutane domin bazaka bambance kanshinba ita kuwa Dije dakaji zaka tabbatar karamine



Abdulhakim yana daga can dakinsu yaji tashin motoci yai xumbur ya mike daga kan gadon dayake kai yabude labulen windon nasu yahango gwanon motoci sunyi biyar ta amare zata futa dg gidan


Saikawai yaji hawaye ya xubo akuncinsa yasa hannu yagoge yana tambayar kansa dalilin kukan sa da damuwar da yayi akan wannan Aure na dije da Abdallah


Me yasa ya damu da yawane yana tausayin dije kuma yanajin wani abu akanta murmushinta yana masa gixo yana hangota akayan sakinta taci ado


Yakwanta ruf da ciki akan gado ya rumgume filo akirjinsa yahau fadin "khadija ki yafemin halin dana sakaki nine silar zamowarki matar wanda kikafi tsana aduniya,nine nazama musabbabin kasancewar ki ckn damuwa Amma nayi alkawarin baxaki wulakanta ba khadija.


Tunda aka daura Auren khadija da Abdallah yaji abin yana damunsa abin ya tsaya masa gashi yana yawan tunaninta


Shiko ango Abdallah adaidai lokacin da aka shigar masa da amarensa cikin gidan nashi toshi adaidai lokacin yana can gidan Abokinsa Anwar su hudu sunata shan shisha da sigari

tabbas
Yaji garau aranar domin sigari kwali guda yasha saida ya tabbatar damuwarsa ta ragu kana yabar falon yakoma ckn d'aki kan doguwar kujera yafara bacci da tunanin babynsa lowerst yakwanta


Yaita mafarkin suna tare da babyn nasa suna gudanarda daddadar soyayyarsu


Wayarsa tayita kara baijiba bacci yayi dadi


Abdulhakim ne keta kiransa alokacin tara da rabi na dare


So yake yazo yai masa rakiya xuwa gidansa


Saida Anwar yashiga dakin yafarga domin su sunacan falone


Ya d'aka masa duka yace "abokina tashi ga kira daga gida.


Yafarka agigice yakarba yaduba dayaga kiran Abdulhakim ne sai yaja tsaki yaso k'in d'agawa amma kuma saiya fasa yadaga yana masa tsawa"ya akaine mallam meye na kirana awannan lokacin ??


Abdulhakim ya murmusa yace "kayi hkr ranka ya dade kana ina?

Abdallah yasha mur " meye damuwarka da inda nake?,

Abdulhakim yace "kayi hkr abokina so nake muhadu yanzun

Tsaki Abdallah yaja yace "to me zakaimin inmum hadun kai bana son duk wata takura ayanzu kabarni da abinda ke damuna


Abdulhakim yace "naji kayi hkr kazo muhadu yanxu ojanty plx


Abdallah yace "waime xakaimin ne? kabari sai gobe mana dan kwana xanyi a inda nake.

" Amma dai kasan kai angone ko!? Kasan dai yanzu haka amarenka suna gidanka kuma inhar bakaje garesuba to ubangiji saiya tuhumeka dan haka aduk inda kk kataho in rakaka muje gidan.


Abdallah yaji wani abu yatsaye aransa wato ma yaune za,akaisu gidan shine ba,a gaya masaba tabbas yanda ake masan nan akansu xai rama yanda aka wulakantashi shima saiya rama wulakancin nan da akai masa


Ahankali yabaiwa Abdulhakim amsa "to kajirani ganin.


Yana dire wayar yakalli Anwar daya daga kwalbar giya yana kurba yace "abokina kajifa wai ankai min amare inje arakani gidan


Anwar yahau tafawa yana jinjina masa "kaga angon mata biyu walh kagodewa Allah inama nine akaimin wannan gatan hakan.


"Kaga dakata ba zolaya nace kayimin ba " cewar Abdallah yafada yana kokarin tashi tsaye


Anwar yace "to muje ayi rakiyar tare dani mana.


Abdallah ya harareshi yace "ahakan kana tsamin giyar zaka rakani? Lallai kanaso asirina yatonu gun Abdulhakim knn domin inhar yagano kasha giya to dole xaiyi zargin nima inashane dan haka kaxauna zan tafi kawai duk yanda ake ciki zakaji gobe


To shikenan " nan suka sallama yafuta yashige .motarsa sai gida


Abdulhakim shine dan rakiya shida wani cousing dinsu dayaxo gidan me suna Nura


Suna tafe suna xolayarsa amma ko kulasu baiyiba har suka isa gidan horn yayi me gadin yataso da sauri ya wangale get suka shiga sukai parking suka futo

Abdulhakim yakalli ango yace "to ina muka nufa kenan first?

Harara ya maka masa "wannan kuma kai kajiyo.

Abdulhakim yace "Sashin Khadija zamu fara shiga domin itace nabaiwa shugabantar uwar gida.

Yana gama fadin hakan yayi bangaren khadijan suka mara masa baya.


Tana can kurya tsakiyar gado kanta da lullubi tana jin sallamarsu ma takara jan mayafin kan takara rufe fuskar


Dasallama suka shiga suka zami kan 3 siter suka zaxxauna


Gaban dije yafadi kirjinta ya buga jin kamshin turaren Abdulhakim data dade batajiba take taji abinda yatsaye a kirjinta yanarke yana malala ackn tsokarta yanabin jininta.


shiko Abdallah wani tsanarta ce takaru aranta yakura mata idanu dukda baya iya hango idonta ji yake kamar ya shaketa


Abdulhakim dayake jin wani abu shima aransa yai kokarin bude baki domin ya magantu

"Khadija bude fuskarki ga mijinki munkawo mikishi.


Tanaji amma tayi mindikiskis taki budewa domin hawayene yaxubo akuncinta jin muryar data kwan biyu batajiba yana kuma ambata mata sunan wani da mijinta


Nura yace cikin raha "ko sai munsai bakine amarya?


Abdulhakim yace "a,a wata qila angon nata takeso yabude mata dakansa.

Jin Abinda yace yasa tayi saurin budewa saidai kash! idanuwanta ackn na Abdallah ta saukesu ………



_Muje zuwa fans_


😂😅👍🏼


*Auntyn Sayyada da Shahida* 💘🐄 *YAR FILLO*🐄
_Dijen kauye_
🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕
🏕🏕
🏕






*True life story*






*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)






PG 30-35



Wani bakin cikine yaxiyarci ckn zuciyar Dije naganin Sunyi ido ckn ido itada Abdallah Bacin rai yai mata dirar mikiya taji wata tsanarsa ta karu aranta


Shima din makamancin abinda taji aranta hakan yaji amaimaikon yaji ta burgeshi sai yaji tabashi haushi kamar yace mata "inma danni kk wani boye boyen fuska gara ki bud'e domin fuskarki naki jinin gani balle kiyimin yanga da yauk'i da ita !" Hakan yadace yafurta mata kodon ya bata takaici to amma baya faraba tunda akwai "yan baka agun yasan ran Abdulhakim zai b'aci sai kawai yahade ransa yakauda fuska daga kallon dasukewa juna natsana.


Ta sunkui da kanta kas tana murza yatsunta


Abdulhakim yace "to amarya muxamu tafi Allah yasanya Alkairi. Yadubi ango yace masa "abokina kaxama me rike min amanar kanwa ka kumaji tsoron Allah ackn zamantakewarku sannan kayi adalci atsakanin matanka kasani cewa baxan bari inga kana kuntatawa khadija inyi shiru ba sbd yarinyace kuma bataa kowa agarin nan saimu kakuma fi kowa sanin yanda muke da ita na amintaka dole zan ringa kawo kafata gidannan sbd inga zamanku ya daidaita inkuma naga abinda baiminba daga gareka to walh da dady xanringa hadaka ato.


Wata harara Abdallah ya makawa Abdulhakim din

Nura yahau dariya yana fadin "ai gaskiya yafada gara ma ka kiyaye domin hakkin Aure wuyane dashi saika dage zaka tsallake


Suka mike tsaye "katashi muje muraka ka dakin daya amaryar taka muyi muku nasihar zaman aure inyaso saika dawo nan dakin uwar gida ka kwana. Abdulhakim yafada da raha da zolaya


Abdallah yace "kadafa ku takuramin don baxaku ringa juyani kamar waina atanda ba ato.

Nura yadafashi yace "kwantar da hankalinka dan,uwana abinda duk Abdul yafada daidai ne tunda har muka kawoka nan to dolene can ma mukaika don mu fita hakkinta itama.


A dole badan yaso ba yamike yabi bayansu


Dije tabi bayan Abdulhakim da kallo


Taji inama tabishi taji inama shine angon nata taji kuma kamar tace masa "yaushe zaka dawo.? Bakinta yai mata nauyi

Ranta yai fari jin cewar Abdul din yace zairinga kawo kafarsa gidan lallai zata ringa kasancewa ckn farin ciki tayi addu,a aranta Allah yasa Abdulhakim din yakamu da sonta shima.kamar yadda xuciyarta ta kamu da sonsa


Kujimu da shirme Fa na dije 😅



Amarya Ni ,ima najin angwaye sunshigo mata ta gyara zama akan three siter datake ta yaye rufin kan datayi idonta akan kofa

Har suka shigo bata dauke ganinta akan angon nataba

Abdallah yasha mur yahade rai ganin irin kallon kurullan da Ni,ima ke masa kamar wata mayya wannan ai babu aji saiyaji wani karin tsanar nata aransa


Shikansa Abdulhakim bata burgeshiba domin duk amarya da aji akasanta kamar dai yadda khadija tayi tanuna kunya da aji takuma nuna ita din amaryace ba kamar Ni,ima da taxo falo tazauna ba kuma ta tari ango da mayen kallonta kamar ta cinyeshi

Suka zazzauna Tareda zolayar amaryar "Amarya ansha kamshi ga ango munkawo miki.


Cewar Nura yafada yana dry

Shiko Abdulhakim cewa yayi "to agurguje nasiha xamuyi muku akan zaman Aure domin dai Aure dan hkr ne ballantana ke ni,ima da zaki zauna da kishiya kuma ma kishiyar me karancin shekaru don natabbatar xaki baiwa khadija fin shekara uku ko hudu don haka inaso kirike girmanki kada ku ringa fitina duk da ba haduwa zaku ringayiba inba da daliliba tunda kowa na nasa bangaren

Abdulhakim yanisa yaci gaba da cewa "inaso insanar mk cewa Khadija itace uwar gida bawai kuma dan nuna bambanci muka zabeta a uwargidan ba saidan cewar Auranta aka fara magana sannan nata Auren aka fara daurowa kiyi hkr da hakan kinga ke akwai danganataka ma atsakani natabbata baxa.a samu matsala kema dg bangaren kiba.


Ni,ima data shaqa ta murmusa ckn takaici tace "bakomi Allah yabamu xaman lfy.

"Amin. Cewar Abdallah suka mike tsaye su duka.


Saida yarakasu har gun motarsu suka tafi kana yadawo sashen dije kai tsaye dakinsa dake jikin nata yashige

Babban gadone adakin da yar drowarsa ajikin bango

Bandaki yashige bandaki yawatsa ruwa yaxira jallabiyar bacci yahaye gado tareda daukan wayarsa yakira babynsa lowerst suka fara hirarsu ta masoya har na tsahon awa guda


ya dade bacci bai ziyarci idonsa ba da suka gama wayr yanata tunanin yanda zai zauna da mata har biyu da kwata kwata baijin zai iya sonsu aransa

Tabbas kowaccensu saita kwashi takaicinsa domin saiyayi musu gashin kuma saisun gwammace rabu dashi da zama dashi …………



_muje zuwa_
🐄 *YAR FILLO* 🐄
_Dijen kauye_
🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕
🏕🏕
🏕






*Nabilancy Luv*💘
{Auntyn S&S}







PG -35-40


Washe garin Abdallah da wuri yafuce yabar gidan yatafi gidan Abokinsa Anwar sbd shi Anwar din baitaba Aureba yawancin abokansu nan suke taruwa suna badalarsu


Dije ta tashi tayi sallah takoma kan lintsimemiyar katifarta ta koma bacci


Taringa mafarkai masu dadi wai gata nan a gona itada Abdulhakim suna tadi na masoya

Yana gaya mata irin son da yake mata

Yanda taringa masa murmushi haka ta tashi da murmushin akan fuskarta saidai kuma da cikinta ya kulle najin yunwa tuni ta gimtse fuska tana hamma tareda shafa d'akalallen cikinta


Ta sauko daga kan gadon tana dibi dibin neman kicin ko zata sami madafi tayi girki

Tashiga kicin din saidai tsayawa tayi turus tana kallon gas din dake girke akan ma.ajiyarsa


Ta waiga koina taga ga kayan abinci nan hardasu indomie akwali ga mai nan fari da ja gasu magi nan da duk abinda xa.a bukata saidai baxata iya kunna gas dinba

Falo ta dawo tana tunanin mafita

Takalli dakin dake jikin nata ta raya aranta ko nan ne dakinsa

Ta tafi ahankali ta murda kofar taji ta bude

Ta kusa kai tashigo don tayi tsammanin ko yana ciki ta tasoshi ya kunna mata duk da tasan zata fuskanci wulakanci da toxarci amma ciki ba.a masa wasa xata shanye komi indai zata sami abin kari


Taga wayam bayanan amma da alamar ankwana acknsa ga zanin gado nan ya yamutse ga toilet a bude anshigeshi


Ta juya da tsaki takoma falon

Taxauna akan doguwar kujera ta takure guri guda


Kusan mintina goma daxamanta tajiyo sallama abakin kofa


Ta amsa ahankali

Yammata tagani su biyu sun shigo da kuloli ahannunsu


Babbar sai yatsina takeyi takalli dije shekeke tace "Hhhmmm Amaryar kauye sannu ko.


Dije ta amsa fuska ba fara.a don ta fahimci dame taxo

Karamar datake fara.a takalli dijen tace "Matar yaya Ina kwana.

Dije tace "lfy qalau.


"Sunana Mubina wannan kuma yaya tace Zunnura uwarmu daya ubanmu daya da yaya Abdallah momy ce ta aikomu mukawo muku abin kari.
Cewar mubina knn


Zannurat tace "kinga ni xan wuce gun Amaryar mu Ni,ima ke ki ajiye mata na hannunki ni bari nakai mata nata daidai cimar sbd ita yar birnice nasan tasaba da dan kalin turawa da kwai ita ajiye mata kunun gyadar da kosan nasan tafi sabo da kosai...mubina tace "amma dai yaya Zannura baikyautu ba hakan gaskiya wannan ai cin fuskane.

Zannura ta harari mubina tace "to uwar shishshigi gaya min gaskiya.

Taja tsaki ta juya "nikinga tafiyata ma gun Aunty Amaryarmu.


Da gayya tafadi hakan dan dije taji haushi

Aiko dai dijen ta shaqa saidai bata nuna ba

Mubina ta zauna tana fara,a tace "matar yaya zoki dauka ki karya kinji.

Murmushi dije tayi tace "to nagode ki mikan gaisuwata da godiya gun momyn.

Ta mike taje ta dauko flet da cuf a kicin taxo ta diba tafara zirawa

Mubina tana kallonta tana murmusawa itakam taji qaunar dije ta burgeta

Dije takalleta tace "ke baxakici bane ?

Mubina tace "nakoshi matar yaya naci nawa daxu.


Dije ta gyada kai tace "Amma kinsan sunana kuwa?

Mubina ta gyada kai tace "nasani mana.


Dije da dariyarta tace "to ainaji kinata cewa matar yaya, inhar kinsan sunana to fadi inji.

Mubina tayi dariya tace "Khadija sunanki


Dije ta girgixa kai tace "a.a babu me cemin wani khadija a kauye Kawai kice min Dijen kauye yafi don kada sunan nawa ya bace 🤔😂


Mubina ta tintsire da dariya tace "dije ai ba sunane me dadi ba kuma kema kince ta kauye kinga kuwa ai khadija shi sai yaxama na birni tunda abirnin kk ko?


Dije ta dire kofin ta dawo kusa da mubina tace "to kuma in dijen ya bace fa.


Mubina tace "ai gara ya bace tunda ko Nana khadija matar manzon Allah S.A.W ba dije akece mataba kuma kema ai yafi miki aji ace mk khadija ko?


Dije ckn sokonci ta kama hab'a tace "ni dijen gala ina naga wani aji,angaya mk nayi makarantane da zaki kiramin aji, tab!


Mubina ta sheke da dariya tace "ke ajin da nake nufi bafa na ajin da ake shiga ayi karatu ba aji na haduwa da kamun kai


Dije tayi dry tace "au na fahimta


Mubina tace "Aunty khadija kinada kyau fa dan Walh kinfi Aunty Ni,ima kyau.

Dije tace "wacece Ni,ima kuma.?


Mubina tace "Kishiyarki mana matar yayan namu Ai gunta Zannura ta tafi yanzu.


Dije tace "kada kiji haushina mubina yayarki batayi minba sbd naga kamar yar wulakancice naga wani gani gani takemin amma dai ba momy ce ta haifetaba ko?

Mubina tayi dry tace "momy ce ta haifeta mana kawai dai ita halinta ne haka injinin ku bai haduba to bata nunawa mutum kauna karara dan haka saikinyi hkr da ita sbd kada ma kiga ta nuna tafison Aunty Ni,ima kiji haushi dama kawar tace kuma jininsu ya hadu da Yaya Abdallah zasu iya nuna miki kishinsu afili dan haka kada ki damu da wannan kinga ni ina sonki momy da dady suna sonki gakuma Yaya Abdulhakim ko? Tafadi tana karyar dakai tana kallon Dije datayi sakato tanajinta

Dije tace mata "nasani mubina nakuma ji dadi, Yanzu ina yaya Abdulhakim din yake ?


Mubina tace "sunfita da dady kafin mufito sbd zasuje can wani kamfanin dadyn daya bude musu.

Dije ta gyada kanta tace "to inkinje ki gaidamin shi


Mubina tace "zaiji insha Allahu.

Dije takwashe kayan takai kicin ta dawo ta zauna kusa da mubina tana fadin "Amma dai ba yanzu zaki tafiba ko.

Mubina tace "a.a ba yanzu ba muna hirarmu me dadi ina zantafi momy ma tace intsaya muyi girkin rana da dare nidake in nunnuna mk abinda baki ganeba na electric.(Kayan wuta na gas)

Dije taji dadin hakan sosai

Nan ta sake da mubina sukaita hira abinsu
Dama sa,annine baifi shekara daya ko biyu Mubinan tabaiwa dije ba

********
Sati guda da dije tayi agidan kusan kullum mubina saitazo tayata hira kuma tun zuwanta bata saka idonta akan ango Abdallah ba hakan bai dame taba bama taso taganshi hatta Ni,ima babu abinda ya hadasu kowacce na part d'inta

Shakuwa sukai sosai da mubina da dije domin kullum intazo hirarsu suke tamkar yan,uwan juna ita mubina tayita bata labarirrikan birni na ban al,ajab ita kuma dije labarukan kauye na ban dariya take bata bayama labarinsu na fulani aiko mubina nashan dariya

Sau dayawa dije na tambayar mubina shin Ina Abdulhakim anya kuwa sakon gaisuwarta na isar masa?

Takan gaya mata cewar tana gaya masa mana yana dai busy ne sai uxuri don yafara xuwa kamfani shida Abdallahn

A bangaren Ni,ima akullum neman samun shiga takeyi agun Abdallah dataji yashigo part dinta zatayi saurin fitowa dg dakinta tayi masa sannu da zuwa wani zubin ma harda binsa da ruwa da lemo ckn dakinsa amma bata taba ganin fuskaba ahakan dai bata gajiya tasawa ranta cewar baxata taba gajiyawa ba harsai hakanta yacimma ruwa domin ita kama yanxu Abdallah ne agabanta ba dije ba don ta dije me saukine tunda tanada labarin abin duk dayane ma ashe itada da itan babu wacce yakeso Zannurace ta gaya mata hakan dayake zannun itace abokiyar hirar Abdallan

Itako mubina ta hannun daman Abdulhakim kullum tazo gun Dije saitayi mata tambayar cewa "Shin wai wacece budurwar Yaya Abdul hakim ne?yaushe shima zaiyi auren?

Mubina takan tabe baki tace mata "wuuuu!tabdijan ai yaya Abdulhakim baida budurwa bansan kuma ranar aurenba tunda bai tsayar ba baikuma kawo mana wacce zai Aureba kinga dai nice abokiyar hirarsa da da akwai zansani nidai nasan cewar Yaya Zannurat tana sonsa sosai Amma shi baya sonta yaki kulata suyi soyayyar


Ran dije yakara baci dajin hakan saitaji ta kara tsanar Zannuran aranta Amma kuma Abu dayane yatsaye mata arai shin tayaya Abdulhakim da Zannura zasuyi soyayya ta yayama cikinsu daya zatace tana sonsa?toko dai zannurar batada sanine a addinance yahamta ka Auri yayanka ciki daya? Lallai ta yarda zannu batada hankali bawan Allah yasan abin bame yiyuwa bane shiyasa yaki knn.

Tabbas tashiga duhu alamarin saidai ta kasa tambayar mubina komi wannan tambayar Abdulhakim zatayiwa kawai domin tasami gamsassiyar amsa.

Taringa kirga kwanakinta agidan ta shiga fushi da quncin rai narashin ganin Abdulhakim domin shifa yai mata alqawarin cewa zai ringa shigowa yadubata

Saida tayi sati biyu sai gashi kwatsam da yamma aranar dama mubina bata zoba

Ranar lahadi ranar takama babu aiki don haka aranar yasami sararin zuwa gidan kuma Abdallah baya nan amma yasanar masa zaizo ta waya.


Taji farin cikin ganinsa amma farko fushi tayi ta cika tayi fam taki kulashi saida yace mata "to tunda ba.ayi maraba dani ba bari nakoma inda nafito …… ta dauka da gaske yake ganin yajuya din ai dasauri ta taso ta riko hannunsa kamar zatayi kuka tana fadin "na huce zoka zauna abokin birni.

Yai saurin kwace hannunsa jin wani yanayi daya hudashi yaziyarci kwakwalwarsa

Yanemi guri yazauna taje kusa dashi daf ta zauna ya dan matsa nesa yace mata "meyasa kkai fushi da dan.uwanki haka?

Tayi dariya tace "to ainaga kamance dani ne yau kwana sha hudufa.tafada tana hada yatsunta alamar kirge

Yace mata "ina sane dake khadija nabar kune kusha amarci kafin....

Ta toshe masa baki da sauri "Allah yakiyaye min inyi amarci da

Please Login or Register in order to submit comment