Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan”

Iya ta fada yana runtse ido, ba karamin dadi Falmata ta ji ba, sai ta juya ta nufi hanyar shiga cikin gidan, sai da ta gaisa da mutane da yawa kamin ta samu isa bakin kofar farko ta falon Ammy. Haka ta ratsa falo kusan uku sannan ta isa gaban wata haraba tana kallon Hajiya karama dake tsaye a backyard tana kallon wani gurin dabam, Falmata ta kasa dauke mata ido, domin ta hadu iya haduwa tana da kyau sosai irin kyaun nan mai daukar hankali ga mayan ido sai dai ba manya can sosai ba, bayan tufafin jikinta mai kamada na turawa da ta saka wato English wears ta saki gashin kanta ya sauko sai tai kamar wata baturiya abun ka da Fulani.
Ba karamin burge Falmata Hajiya Karama tai ba, domin fari na daga cikin abunda Falmata ta rasa kuma yake burgeta iya burgewa idan ta ga wani da fari sai ta ji kamar ta cire ta sakawa kanta, ba dan tana da siffar Fulani ba da kuma yaren da take ji ba zaka ka taba kallonta kace ita Fulani ce saboda bakinta.

“Ko wacece? wata kila yar sarkin ce?”

Ta tambayi kanta tambayar da bata da amsa a gurinta. Wani abun mamaki tana kwankwasa kofar corridor Iya ta bude mata tana watsa mata wani kallo mai kama da harara. Falmata ta bata yarda ta yi ido hudu da ita ba ta sanda kai kasa ta shiga. Kato falo ne mai cike da kayan alatu ga sanyin ac da katon plasma, an jera wasu ɗakunan daga gafe, kai tsaye stairs din ta nufa ta fara takawa a hankali saboda tana gudun kar tsantsin gurin yaja ta ta zame kasa, sai da ta waiga taga babu kowa bayanta sannan ta risina kasa ta shafa tile din, sai a lokacin ta tabbatar ba ruwa ba ne kuma ba mai ba, a iya tunaninta yadda take jin tsantsin gurin da yadda take ganin yana shining a zatonta ruwa ne ko mai duk kuwa da kasancewar bata jin ta taka abu makamancin haka.
  Dan abun da aka nuna mata na jikin kofar ta danna wato door bell sannan ta ja ta tsaya sai rabon ido take, sai da ta danna shi sau kusan uku sannan aka bude mata kofar. Har kasa ta risina tana gaishe da Muhseen.

“Ina kwana?”

“Lafiya kalau”

Bayan ya amsa ya juya yana kallon Momy wacce ke tambayar waye a kofar.

“Wata ce ban santa ba dai shigo”

Ya matsa daga kofar wanda hakan ya bawa Falmata damar shigo cikin falon mai kama da aljannar duniya. Da sauri ta fadi ta kasa tana gaisar da Ammy, Ammy ta amsa mata ba yabo ba fallasa sannan ta cigaba da danna wayar da take.

“Ranki ya dade zan gyara dakinsu Yan uku ne”

Ta fada muryarta kana ji kasan tsoro ne ya cika mata ciki fal, tsoron irin amsar da za a bata tsoron kallon matar sarki tsoron mutane da suke falon duka suka taru sukai mata tsaye a kai, kamin Ammy ta bata amsa har idonta ya soma cika da kwalla cikinta har murdawa yake kamar wacce tai wani laifi.

“To ai kin san inda dakin yake”

Ta yi saurin mikewa tsaye ta nufi corridor da zai sadata da dakin yaran, a nan ma wasu hadiman ne suke ta aikinsu, Falmata sai gaishe su take kowa ta gani sai tace nasa ina kwana da wanda ya kamata da wanda be kamata ba, ta kasa daga ido ta kalli kowa.
Sai da tai Bismillah sannan ta kai hannu ta tura kofar dakin ta shiga har lokacin gabanta be daina faduwa ba, tsoron da take ji be gushe ba, haka take samun kanta a duk lokacin data shigo Masarautar, abun ka da wanda be saba shiga mutane sosai ba balle kuma manya kamar gidan Mai Martaba.
 
Wannan karon ba tai mamakin ganin Iya a dakin ba, daman ta saba ganinta a kullum idan ta shigo sai dai wani abun da yake bata mamaki yau kusan kwananta uku da fara aiki a gidan amman bata taba ganin yaran ba ko hotuna, a kullum kuma sai ta tararda Iya a dakin, haka ma a kullum sai Iya ta saka dogari yai mata gadin dakin har Falmata ta gama gyaranta ta fita.
 
“Ka sa ido, irin wadannan yaran ba abun yarda ba ne”

Iya da fadawa dogarin tana wani yawo da manyan idonta akan Falmata kamar zata ciro su.

“To ranki ya dade”

Ya amsa mata yana risinawa sannan ta fice tana ta wani shinshine². Falmata dai bata ce komai ba bayan gaisuwar da ta mikawa dogarin har da risina masa, sannan ta hau gyare gyaren dakin tana yi tana satar kallonsa domin gani take kamar wani abu zai mata.

Muhseen ne kadai zaune a dinning domin kowa ya karya a kama gabansa, wayar makkale a kunnensa yana ta fira da matarsa sai faman zuba murmushi yake kana ganinsa kasan yana cikin nishadi. Sai da ya gama breakfast din sannan ya yanke wayar ta taso ya nufo gurin Ammy yana fadin.

“Wai har sun wuce ne?”

Da kallo Ammy ta bishi tana murmushi har ya karaso kusa da ita ya zauna a kasa.

“Ka dade kana bachi ne shiyasa”

“Gajiyar jiya ce, gashi kuma yau zan kama hanya shiyasa na tsaya hutawa”

Shiru tai na yan mintuna kamin ta kalleshi ta ce.

“Yau zaka koma kenan?”

“Eh daman Mama Fulani kawai na kawo, ba dan ma yamma yayi ba ai da tun jiya zan koma dan ina da aiki yau”

“Ai ka kyauta shi Aliyu ya dauke mana kafa ko?”

Muhseen yayi murmushi kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya shafa kansa ya ce.

“Shi ma zai zo soon da Matarsa”

Ammy ta tabe baki.

“Shi dai ya sani, babu ruwansa da dangi daga Momy sai Fulani su kawai ya sani a rayuwarsa, ko da yakeba laifinsa ba ne laifin Fulani ne da bata nuna masa ba”

Ammy ta karasa maganar tana aje wayar hannunsa.

“Ko da yake ga Shattima ne nan muna fama da shi, idan na ce yaje gurin yan'uwa kamar na kira masa mutuwa, sai dai azo a iske shi, wani irin jin kansu suke kamar wasu Sarakuna”

“Ammy ai kara ma Shattima da Aliyu, tun da shi zai zauna ayi fira da shi kuma zai sakewa kanensa Fuska, Aliyu kuwa idan kika ga yana fira to da Mama Fulani ne ko matarsa ko Momy sai kuma Abba”

Ammy ta tabe baki.

“Uhm Abunda yai Aliyu shi yai Shattima idan ya ganka ne yake nuna shi na kwarai ne”

Har Muhseen ya bude baki zai yi magana sai ga Iya ta shigo falon fuska daure.

“Ranki ya dade wai yarinyar nan za a bari tai ta kula da dakin yan uku?”

Ammy ta mata wani kallo cike da kasaita.

“Akwai wata matsala ne?”

“Ranki ya dade ni kam sam ban yarda da ita ba, kuma yarinya ce karama ina zata iya wani abun kirki, yanzu ga masu aiki bila'adadin a gida amman ace sai an dauko wata daga can waje ta zo gyara dakin jikokin Mai Martaba?”

Kallonta kawai Ammy take na wasu yan dakiku kamin ya bude bakinta cike da kasaita ta ce.

“To yanzu challenge dina kike yi Iya? Ko umarni kike ba ni?”

Da sauri iya ta risinar da kai.

“Ba ko daya ranki ya dade Allah ya kara miki lafiya, shawara ce kawai ni kaina idan aka bar ni zan iya kula da su”

“To Mahaifinsu yace baya bukatar kowa ya kula masa da su a nan sai daga waje, kuma shi yace baya son tsohuwa ko mai ƴaƴa, sai ki same shi ki bashi shawara”

Kasa kasa Iya ta watsawa Ammy harara tana wani kashe ido.

“Rana na zuwa Zainabu”

Ta fada a ransa sannan ta juya ta fice bayan ta bawa Ammy hakuri. Sai da Iya ta fice sannan Ammy ta daga kai ta kalli Katuwar kofar ta dauke kai ta mike ta nufi hanyar dakinta.

Tsab Falmata ta gyara dakin yaran daman can ba datti yai ba sai dai kullum sai ta tisa gyaran ne ta goge ta saka turare ta canja sanin gadon yaran, tana gamawa ta fice ba tare da ta yi ma kowa sallama ba. Sai da ta fito daga Masarautar gaba daya sannan ta samu sallama da natsuwar zuciya domin a yanzu har numfashinta take jin ya daidaita tsabanin idan tana gida bata son yin numfashi da karfi wai kar su ji ace ta yi laifi. Ta mika kafa sai tafiya take ita kadai a titin da babu mutane sosai, idan ka cire kofar Masarautar da a kullum take cike da mutane sauran makotansa kowa yana cikin gidansa sai idan fitar ta kama, unguwar manyan mutane ce mai kama da GRA, ko'ina manyan gidaje ne gwanin sha'awa.
   Sai da ta shigo cikin gari sannan natsuwarta ta kara daidaita domin ta fi son unguwarsu fiye da wacan da take ganin kamar wata rana za a iya sace ta a can, da ganganta ta rage tafiyar da take ta soma tafiya kadakadan tana saurarin wakar Sirleem dake tashi a shagon wani mai charji, cikin zuciyarta take bin baitin wakar tana jin muryarsa na shiga har cikin kanta.
03/12/2021, 08:06 - 🤐🤐🤐🤐: *🐄🐄 FULANI 🐄🐄*


By Khadeeja Candy

*Fadime dabam ta kauyen Katsina ita ce take jin busar sarewa. Falmata dabam ita ce ta Yola mai aikin raino a gidan Sarki, sai dai dukansu ana musu inkiya da Fulani. Fatar kun gane za ku daina rudewa 😀*

*4*

SIRLEEM POV.

“Hajiya ina jin kamar ba zan iya jira har Nana ta kare Karatu na aureta ba....!”

Ba Hajiya kadai ba gaba daya kanensa kallonshi su kai. Da Mamaki Hajiya tace.

“Ban gane ba?”

Ya cika ma bakinsa iska ya busar sannan ya shiga murza hannunsa kamar mai shafa mai.

“Kawai dai bana iya jira, tana kula wasu bayan kuma kowa a Masarautar nan ya san ni zata aura, sannan ina ganin kamar yan gidansu basa son hadin nan nawa da ita idan abun ya kai wani lokacin za su iya lalata shi”

Ajiyar Hajiya ta sauke.

“Gaskiya ne, za su iya lalatawa amman zancen tana kula wasu kar ya dame ka kai auren a haka ai zata daina kuma idan ka gani ka rika magana”

“Na ganta da Deen din nan da yake zuwa duba yaran Shattima, na je har Part din su na yi magana babu wance komai karshe ma Hajiya Karama ta taso tana fada ni wai ina takurawa Nana kamar wani ubanta”

Hajiya ta yi murmushi mai kama da dariya.

“Kar hakan ya dame ka Sirleem kai dai ka aureta kawai komai zai wuce”

Ya kalleta cike da gajiyar jin abunda take yawan nanata masa idan yai mata complain akan Nana.

“But Hajiya miyasa dole sai Nana? Tsakanin da Allah neman auren nan na saka kaina ne kawai saboda kin tirsasa ni amman ni kaina yarinyar nan bata kwanta min ba, ni kuma na fara gajiya gaskiya ba zan jure daukar wulakanci a gurin kowa ba na fi karfi haka, dan kawai tana yar sarauta ubanta yana sarki mahaifiyarta tana matar sarki yayanta yana dan sarki ba zan dauki wannan wulakanci ba na fi karfin wulakanci a gurin kowa ni”

Ya fada yana daga kafadunsa, Rima ta tabe baki tana ture kofin tea dake gabanta tare da kallon yayan nata.

“Ni kaina ba son auren nan nake ba, dan dai kawai Hajiya ta matsa ne akan ayi, amman miye amfanin hada alaka da makiyi alakar ma ta aure haba dai...”

Murmushi Hajiya tai ta taso daga kujerar da take zaune ta dawo bayan Sirleem ta tsaya.

“M2 ba haka duniya ta sanka ba? Kai a yadda kake Celebrity sai kaje ka auri wacce bata kai ba? Ga yar sarauta yar masu naira kuma kyakkyawa yarinya mai kurciya a gidanku? Ba ka lura ba? Maran manyan mutane suna auren yar manyan mutane? A yadda kake sannen a duniya ai kamata yai ace ka auri yarinyar da ta isa gaba da baya, taya za a tashi maganar da kasan zata iya saka Mai Martaba a cikin wani hali bayan gashi kwance ba lafiya? Baka tunani ya takama mu sakawa Mai Martaba da irin hallacin da yai mana? Idan mahaifiyarta matar sarki ce kai ma taka uwar matar sarki ni da Zainabun Jirgi daya ya dauko mu domin dukanmu Mai Martaba muke aure. Ke kuma Rima da kike fadar hakan ai kyautatawa ce wanda yai maka sheri sai ka saka masa da alheri, ba ni da burin da ya wuce na ga Sirleem ya auri Nana a yanzu ku karfafawa dan'uwanku guiwa ba wai ku sare ba”

Ta karasa tana kallon Rima. Sirleem ya juyo yana kallon mahaifiyarsa tasa.

“Amman Hajiya ai ba Nana ce kadai yar sarauta ko yar masu arziki ba, akwai da yawa mi yasa ba zaki bar ni naje da kaina na zabi wacce tai min ba?”

“idan zaka auro yar sarkin Makka, dan arzikinsu da Sarauta ba ka cika min burina ba matukar baka auri Nana ba, idan kuma zaka auri yar sarkin talauci na duk duniya bayan ka auri Nana to ba zai tana damuna ba, ni dai burina Nana ta zama uwargidanka”

A hankali ya aje numfashi yana kallon kanensa wanda shi ma kallonsa yake suna mamakin furucin mahaifiyar tasu. Talba ya ce.

“Amman Hajiya miyasa?”

“Saboda ta wannan hanyar ce kawai zan iya sakawa mahaifinka da abunda yai mana”

Gaba daya kanensa mata su uku tashi sukai daga dinning, kaf a duniya basa da makiyiya irin Ammy wato uwargidan Mai Martaba, su kam ba su da dalilin na cewa ala dole sai yayansu Sirleem ya auri Nana ba bayan shi kansa ba sonta yake ba. Da kallo ta bisu tana murmushi kamin ta kalli Talba ta ce.

“Raheen a kira min Kulu”

Tana fadar hakan ta nufi hanyar dakinta cikin wani irin taku kamar wacce ba zata mutu a saka a kasar ba, tsadadar shaddar dake jikinta sai motsi take tana wani maiko. Tashi Talba yai ya fita domin zuwa kiran Kulu kamar yadda ta Umarta, Sirleem kuma ya ciro wayarsa daga aljihu yana kallon kiran Mansura da ke shigowa wayarsa.

Gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta fuska babu annuri kamar ba ita ce dazun ta gama dariya ba, a zahirin sarkar gold din dake wuyanta wacce ta sauko har saman kirjinta take kallo a badini kuma zuciyarta na can wani gurin tana wani tunani na dabam,  stool din madubin ta ja ta zauna tana cigaba da kallon kanta abubuwan da suka faru a baya take tunawa, ta dayan bangaren kuma tana kitsa yadda wasu abubuwa za su tafi a nan gaba. Yanayin yadda take motsa bakinta kadai ya isa ya sanar da cewar zance zuci take.

“Shigo”

Ta fada tana dauke kai bayan an kwankwasa dakin minti uku da suka wuce. Kulu ce ta shigo dakin tana sanye da doguwar riga ta atamfa an mata irin dinkinsu na tsohu kanta lullube da mayafi, gaban Hajiya Bilki taje ta zauna tana mika mata gaisuwa.

“Allah ya taimake ki ya kara miki lafiya, Sardauna yace kina nemana”

Tashi Hajiya tai daga kan Stool din ta koma saman shimfidarta da ke gefen gado ta kishingida tana kallon Jekadiyar ta ta.

“Kulu wane Likita ne yake zuwa duba yaran Shattima?”

“Wallahi ban san shi ba ranki ya dade”

Wani kallo Hajiya tai mata.

“Taya za'ayi kina cikin masarautar ace baki san masu shiga da fita a ciki ba?”

“Ranki ya dade na ga kamar bangaren Ammy ne, ni kuma na fi kula da abunda ya shafi bangarenki ne Allah kara miki lafiya”

“This is nonsense, Ammy da bangarenta ba a cikin masarautar nan suke ba?”

Hajiya ta fada a tsawace har tana tashi zaune fuska babu annuri.

“Ciki suke Allah ya baki yawan rai, tuba nake”

Cewar Kulu tana kara noce kai kasa.

“Kina da matsala Kulu, duk abunda ya kamata ki saka ido akai ba kya yi”

“Zan bincika ko waye shi Allah ya huci zuciyar ki ya kara miki lafiya”

“Kira min Jarma”

“An gama ranki ya dade”

Kulu ta mike da sauri ta fice daga dakin ganin yadda Hajiya ta hade rai kamar bata taba dariya ba. Ba a dauki dogon lokaci ba Jarma ya shigo dakin yana sanye da babban riga ga wani uban rawani a kansa, inda Kulu ta zauna ya zauna tana kallonta hankalinsa kwance sai dai har ya zauna ta kira shi ya amsa ta kora masa bayani bata kalleshi ba.

“Jarma”

“Hajiya”

“Akwai wanda ke son shiga tsakanin Sirleem da Nana”

“A cikin masarautar nan yake?”

Jarma ya tambaya cike da mamaki, sai a lokacin ta kalleshi.

“Bare ne, yaron da yake zuwa duba yaran Shattima”

Jarma yayi murmushi.

“Doc Deen? Kar hakan ya damu Salim, wayayyace kawai irin ta yan zamani ke kinsan ai ba zan bari wani ya dauki hankalin Nana ba”

“Idan ma ka ga zai kawo mana matsala ko wasa, aka yi masa sanadi da gidan nan”

“Baki da matsala da wannan Hajiya Salim ya cigaba da neman yarinya babu abunda za a fasa”

Ta dan yi murmushi tana kallon wata doguwar Fulawa dake gabanta.

UNCLE A A POV.

Ya yamutsa shinkafa da waken dake gabansa a kwano yana bata fuska.

“Anti Rabi sai ayi ta mana wake da shimkafa ba wani canji”

Anti Rabi dake aikin damawa dabbobinta kasari ta yi dariya.

“Hmm Unclen dinsu wani lokacin iskancin ka yawa yake, wani na can be samu kamar wannan ba amman kai ka raina, da alama dai kana da kudin cin wani abinci shiyasa”

Ya shafa kansa yana yar dariya.

“Wallahi kuwa wata yar marasa sanin darajar naira na samu nai mata na yan talakawa na ci kudinta”

“Ban gane yar marasa sanin darajar naira ba”

Yayi dariya a karo na biyu sannan ya labartawa Antinsa yadda ya yaudareta.

“Amman dai Uncle din yara baka da tausayi”

“Wane irin tausayi kina ganin yarinyar nan kin san yar masu abunce ce karamar yarinyar yar secondary school ta ciro kudi sun kusan 50k ta bani 5k ya maida saura, uwayensu ne barayin Jihar mu ai”

Ya mike tsaye yana ciro kudi, 2k ya cire a ciki ya mikawa Yayar tasa sannan ya maida sauran aljihu.

“Ni bari naje waje na ci abu mai kyau”

“Ni wannan aikin na ku yana bani mamaki kuma aiki a restaurant amman ba zaku iya cin abinci a ciki ba?”

“Ai wannan mutumen be da kirki ko ruwansa ka sha sai ka biya shi, zaka ci idan kana so amman zai cire a cikin albashinka”

“Allah dai kyauta ni kam ban taba gani ba”

“Ai ina samun wani aikin zan bar na shi Wallahi”

“Allah dai ya kawo rabo mai amfani”

Da amin ya amsa sannan ya fice daga gidan. Abun ka da unguwar mai mutane yana fita abokasa suka fara dago masa hannu.

“Sai Sardaunan samarin Yola”

Ya nufe su yana dariya.

“Amman na talakawa”

Ya karasa ya basu hannu suka gaisa sannan ya kara gaba ya siye alalen gwangwani gurin wata ya cika cikinsa a titi.

Washe gari ma fa yaje restaurant din sai da ya sake tararda Nana a inda ta saba zama, wannan karon ba bachi take ba idonta biyu suna hada ido ta watsa masa harara ta kawardar da kai, a iya ganinta da yake yi a yanzu kam ya tabbatar karya take da tace yayanta ne yake cewa ta jira a nan, ya lura idan ta ga mutane sai ta boye fuskarta kar a ganta haka yai ta aikin raba ma jama'ar da suke shigowa abinci yana kallonta zuciyarsa na karantarta tana tsara masa yadda zai sake samun wasu kudin a gurinta.
  Sai da ya koma gurin zamansa ya zauna sannan ya dauki biro da takaradar yai rubutu a kai ya dauki bottle water ya nufi inda take ya aje mata takardar a saman tebur din tare da ruwan ya koma ya zauna yana kallonta.
Tun da ya nufota take turo baki tana harararsa har ya karaso ya aje mata ruwan da takardar ya koma, a zatonta zai ce yau ma sai ta biya kudin zaman dana bachi amman bata ji yace mata komai ba, sai dai ta lura duk abunda yake idonsa na kanta.

“Ni nace ka kawo min ruwa ne”

Ya fada tana turo baki cikin sautin da ita kadai zata iya jin kanta, na kusa da ita ko kuma mai kallonta sai dai yaga bakinta na motsi sai hararar da take watsa masa ta isa ta sanar masa cewar da shi take. Hannu ta kai ta dauki takardar ta jefar a kasa tana cigaba da turo baki ita ala dole ga shagwa6a66iya.

“Ba za a karanta ba”

Daga can inda yake zaune ya gwalo mata ido ya hade rai yana mata alamu da ta dauki takardar ta karanta ko ya daketa, sai ta make masa kafada tana murguda masa baki, sai da ya unkura kamar zai taso ta karaso inda take sannan tai saurin kai hannu ta dauki takardar ta bude.

“Idan kina so zan iya kai ki wani guri inda zaki rika boyewa ba tare da kowa ya sani ba, amman nan ai public place ne kowa zai iya ganinki, idan kin aminta fita waje mu yi magana”

Da sauri ta dago ta kalleshi tana gyada masa kai alamar eh ta amince din, da ido yai mata alama da waje sai ta dauki school bag dinta ta nufi hanyar fita tana waigensa. Sai da tai kusan minti biyar da ita sannan Sardauna ya fakaici idon mutane ya tashi ya fita. Can gefe ya hangota ta juya baya dan kar a ganta sai boye boyen fuska take.

“Ke”

“Ni ba ke ba ni Nana Aisha”

“To ina ruwana da wani sunanki”

“To nima ina ruwana da kai”

Ita ta amsa masa ta shigar da yai mata maganar wato da fada fada, sai yai kwafa ya juya alamar zai tafi ya barta, da sauri ta riko hannun rigarsa.

“To akwai ruwana”

Ya sake yin kwafa sannan ya kalli security camera dake gurin ya kalleta.

“Idan kina so zan iya kai ki gidan ku sai ki boya a can idan lokacin da direban ki zai dauke ki yayi sai na dawo da ke”

“Ina zuwa”

Ta fada kai tsaye cike da jindadi, kallonta ya tsaya yi a ransa yana ayyana cewar idan shi barawo ne sai ya sace ta salon alon.

“To ai zamu aro babur da zamu je can unguwar”

“To aro”

“Zaki hau?”

Ya tambaya da mamaki dan be dauka zata yarda ba.

“Eh”

“To ai kudi ake biya kamin a bamu aron babur din”

“Nawa?”

Tunani ya tsaya yi kamin ya ce.

“2k kuma a can gidan da zaki zauna sai kin biya kudin zama”

Ta dan bata fuska.

“Nawa?”

“3k”

“Toh, ai dai ba zaka sace ni ba ko?”

“Eh shekararki nawa?”

“16”

“Amman dai ke wawuya ce”

Ya fada yana dariya a ransa sannan ya juya ta nufi cikin restaurant din, abokinsa Mu'az yai ma magana ya karbi makulin mashin dinsa sannan ya fito ya same ta a inda ya barta.

“Ki fita can titi sai na zo na dauke ki”

Ba musu ta kama hanya a ranta tana jin zafin wawuyar daya kira ta dazun, karasa yai gurin da suke aje abun hawan a gurin ya bude mashin din sannan yasa masa key yai tashi mashin din sannan ya fara tukawa ya fito da shi bakin titi can ya hangota ta boya a kusa da wani shago, karasa yai gurim ya faka mata ta hau yana fara tafiya ta rirrike shi gam ta boye fuskarta a bayansa, kusan sai ta rantse a rayuwarta bata taba hawan achaba ba, iyakarta keke shi ma tana yin wayo Ammy ta hana ta hawa saboda tana mace.

“Ke dallah sake ni kin wani rike ni kamar yar iska haka zan shiga da ke a unguwar mu kina tabani, ni ba dan iska ba ne ba a saba ganina da mace ba balle kuma ta rike ni”

“To ni ba tsoro nake ji ba ko kuma ni aka ce masa yar iska ce, ni yar iska ce kai ne dai dan iska mai sato yarinyar mutane kaje ka kaita wani guri ta boya”

Ta fada tana turo baki har lokacin bata yarda ta dago kanta ba. Tafiyar ba tai nisa ba ya faka mashin din gefen titi ya sauko ya fuskance.

“Ni ne ma dan iska mai sace yaran mutane? Ai ke ce stupid girl mai guduwa daga makaranta kina boya a wani guri, kuma ba zan kai ki din ba na fasa”

Ya karasa yana dangwararta da yatsansa.

“Ai Wallahi ba zan sauka ba, zan maka ihun ka yi satar mace”

Yadda ta daddage kan mashin din kamar na gidansu tana watsa masa wani kallo ya sani sarai zata iya iya masa ihun abunda ba halinsa

Please Login or Register in order to submit comment