Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yau shi da Adam zasuke kwana tare,
haka kuwa akayi,
shi kuwa Usman,
suna shiga d'akin nasu ya zame ya shiga toilet k'ofar ya maida ya rufe cikin tarin takaici dajin haushin kanshi da zuciyar shi ya kife kanshi jikin gini ya rink'a wani irin kuka maicin rai kuka yake yana d'an dukan saitin kahon zuciyar shi cikin kukan yake cewa.
"Kai tona da Wannan zuciya tawa mai zuwa hurumin daba nataba."
haka yasha kuka har saida yaji kamar numfashi sa zai yanke sannan yayi al'wala ya fito ya shimfid'a sallaya ya fuskanci gabar,
Adam ne ya kalleshi cikin kula yace.
"Usman zaka iya tsayuwa ? ka konta mana ka d'an huta."
Murmushi yayi cin juya fuskar sa dan baya son Adam yaga idanuwan shi da sukayi jazir suka kumbura,
cikin yanayin wasa yace.
"Kai nafa fika lafiya kuma zanyi wa Hamma na da Ummul addu'ar Allah ya basu zaman lafiya dakuma 'yan biyu."
dariya Adam yayi tare da cewa.
"A a yan ukune ba yan biyu ba."

Toh hakafa rayuwa tayi ta juyawa Usman kullum yakan b'uya yasha kuka har sai yayi gyatsa ya kuma ji numfashi sa na carkewa sannan ya fito,
ba kuma wanda yasan halin da yake ciki.

*Gidan Hamma Umar da Ummul kuwa*

Bayan sun shiga cikin gida Hamma Umar na rik'e da Hannun Ummul d'in a haka ya jata har bak'in k'ofar shiga cikin asalin gidan bak'in k'ofar parlour ya tsaya key ya zaro a haljihun shi sannan ya bud'e k'ofar cikin bada umurni yace.
"Kiyi Addu'a ki kuma shiga da k'afar dama."
bata kulashi ba sai k'ollah da take zubda wa sannan tayi yadda yacen,
suna shiga cikin Parlour Ummul tayi fizge hannun ta cikin kallon yadda Abban ta ya binne mata dukiya a parlour fuska cike da k'ollah tayi cikin bedroom da gudu tana zuwa shiga ta maida kamar ta rufe kan gado ta fad'a cikin disashewar murya taci gaba da sana'arta,
shi kuwa Hamma Umar shiru yayi a parlour ya tsurawa k'ofar d'akin ido yana jin sautin kukan can k'asa-k'asa kai ya juya ya fito kai tsaye motar shi ya shigar cikin gida ya ajiye ta a harabar gidan sannan ya bud'e bayan motar ya d'auko lodojin da ya ciko da abubuwan cin da sha,
kai tsaye parlour ya shigo kan dinning table ya ajiye ledojin sannan ya bi d'an corridor dake gefen d'akin da Ummul ta shigan nan ma wani d'aki ne babba wanda yasha gyara da shimfid'u daga dukan alamu dama nanne d'akin da yake rayuwa in yazo Damaturun daga can d'aya b'arin kuma nan ma akwai wani bedroom d'in dan gidane mai yalwar d'akuna parlour ne guda d'aya babba wanda ke d'auke da dinning area mai girma da tsarina sai daga gefen shi wani d'an corridor ne da zai sadaka da kitchen sai sito dake manner a gefen shi,
ta bayan kitchen din kuwa d'an k'aramin wurine mai cike da tsirrai masu kyau ,
cikin parlour kuwa yana d'auke da 3 bedroom,
so yana shiga d'akin sa wonka yayi sannan ya fito yayi shirin baccin sa,
parlour ya fito cikin nitsuwa yana taku mai cike da haiba a hankali ya jawo kujara ya zauna a dinning table d'in kanshi ya jingina jikin kujerar sannan ya d'ora k'afafun shi kan table d'in yana d'an kad'a su a hankali ida nunshi ya lumshe tare da kamo lips d'in shi ya matse yana jin yadda Ummul ke yin kuka cikin sauti mai cike da rauni da wahala da alamun gajiya daga kuma jin sautin kukan da alamun zazzab'i a jikin ta,
ido ya k'ara rumtsewa dan yana jin kukan nata na ratsashi dan window d'akin ta yana ta saitin dinning area d'in,
cikin sanyi ya mik'e a hankali yaje bak'in k'ofar, cikin murya mai cike da tausayawa yace.
"Khairi kiyi hak'uri ki dena kukan nan ya isa kizo ki bud'e k'ofar kinji kibar kukan kar ya saki zazzab'i ki fito kici abinci kinji ko Khairi?."
kukan Ummul ta kuma k'ara yi cikin dishewar muryar tace.
"Bazan fito ba,
ka barni nayi kukana in banyi kukaba me zanyi ? bazanci abincin ba inya so yunwar ta kasheni kowa ya huta tunda dama ba,a sona."
Shiru yayi sannan ya d'an yi ajiyan zuciya tare da cewa.
"Khairi baki da lafiya fa ki bud'e kizo kici abinci kisha maganin inyaso kyaci gaba da kukan tunda shi kikeso ."
bata kuma kula shi ba haka tayi ta kukan ta yayi ta lallashin ta a banza,
haka ya hakura ya barta ya koma bedroom d'in shi ba tare da yaci abincin ba,
ita kuwa haka ta kwana kuka har Allah ya wayi gari.

Bayan Hamma Umar d'in ya dawo masallaci ne ya zauna a parlour tare da kunna TV ya kama tashar manara idan ya samu sun saka sautin karatu k'ura'ani tare da muryar Ahmad Sulaiman volume ya k'ara ta yadda sautin ya rink'a ratsa cikin gidan baki d'aya kan kujera ya konta ya lumshe ido yana bin sautin karatu hannun shi kuma rik'e da carbi,
itako Ummul tunda tayi salla ta konta kan sallayar cikin jin zazzab'i ga ciwon kai kuma ta k'asa barin kukan,
a haka tana kukan har bacci ya saceta,
shi kuwa bai bar parlour ba sai 9:00 am ya mik'e ya shige kitchen nasu gas ya kunna tare da d'an tafa musu ruwan tea sannan ya sake d'uma kajin daya seyo ajiyan ya had'a musu komai yazo ya ajiye kan dinning d'in ,
d'akin shi ya shige wonka yayi sannan ya shirya cikin kananan kayan ya fito ras sai k'amshi yake zubawa,
kai tsaye k'ofar d'akin ta yazo ya tsaya cikin sanyi yace.
"Khairi ! Khairi ! tashi kizo kiyi breakfast."
tana jinshi tayi shiru kamar bata jinshi ,
sai mik'e wa tayi ta zauna ta jingina jikin gado tana jin yadda yake kiranta tayi cib kamar bata d'akin,
shi kuwa sai komawa yayi ta jikin window ta ya bud'e glass d'in sannan yasa hannun ya bud'e labulen ido ya zuba bata,
itama idon ta zuba mishi cikin nuna kiyayyarsa a fili,
kai ya jinjina cikin jin tausayin ta yace.
"Khairi taso kizo kinji ko."
"Bazan zoba bazan cin abince ba,
Na mutuwa mane me ruwan ka?."
Kai ya juya tare da cewa.
"Meyasa bazaki ciba."
a kufule tace .
"Sabida na tsane kaa! bana son ka! bana son ganin ka! bana son ko jin muryar ka!."
ido ya zuba mata cikin tsananin mamaki da al'ajabi bai tab'a zaton k'iyayyar da Ummul take Mashi yakai matsayin da zata kalleshi ido da ido tace mishi bata sonshi bata k'aunar shiba,
muryar tace ta kuma katsemai tunani tana cewa .
"Na tsane ka tunda ko yaushe a sana dinka nake azabtuwa."
Kallon ta ya kumayi sannan a hankali yace.
"Kina son kanki ai?."
"Sosai ma dama ina son kaina kam mana."
murmushi ya d'an yi sannan yace.
"Toh ki fito kici abinci dan ki kula da kanki ni kuma nagode da k'iyayyarki gareni."

"Bazan ciba ! ba kuma zan fito ba!."

Haka Hamma Umar yake ta fama da Ummul Amman sam tak'i fitowa ,
zuwa yanzu kuwa kukan har ya gaji da ita dan ba itace ta gaji da kukan ba kukanne ya gaji da ita sai dai tayi ta diri ba hawaye shi kuwa duk kula da tattali yana had'a mata Amman ko fitowa tak'i tayi bataci komai sai ruwan da take sha da fari bata jin yuwar Amman zuwa yau da tayi kwana biyu a hakan sai take jin yunwar kamar zata kasheta inta tsaya sai jiri ,
tayi wonka kuwa yafi sau 3 wai duk ko zataji k'arfi Amman abin yaci tura a deren kwana na 3 ne ta k'asa bacci dan yunwar dake kwak'ularta.

Shi kuwa Hamma Umar gaba d'aya kewar d'an uwanshi ya cika mar jiki da zuciya haka yasa kullum sai sunyi magana a woya a kalla sau 5 zuwa sau 6 duk lokacin shan maganin Usman in yayi sai Umar ya kirashi yace mishi kasha maganin a b'aggaren Ummul kuwa yana damuwa da halin da take ciki.

A al'adun shuwa'arab d'in kuwa suna yin wata al'adarsu duk lokacin da akayi Aure aka kai Amariya gidan ta washe gari y'an uwanta zasuje karb'ar tukuici a gun aggo kuma Wannan tukuici ba'a badashi sai aggo ya kusanci matarshi so haka yasa wasu basa zuwa washe garin randa aka kai Amariya sukan bari sai randa tayi kwana 3 ko 7 kuma Wannan tukuici ba'a ba dashi ga amariyar da bata kai budurcin ta gidan mijin taba,
so Hamma Umar kuwa yasan da wannan al'dartasu,
so yau ya tashi da wuri ya kimtsa ko ina na gidan dan yana tsammanin y'an uwan Ummul zasu zo yau d'in tunda yau kwanan ta uku da zuwa gidan,
bayan ya gama komai yayi wonkan shi fes ya fito ya shirya cikin
wagamri mai kalar sararin samaniya ya fito ras sai k'amshi yakeyi.

kamar kullum yazo bak'in k'ofar d'akin nata cikin sanyi yace.
"Khairi ki zo ki bud'e k'ofar nan zakiyi bak'i su Anty Shuwa na zuwa."
A hankali cikin wahala da jiri ta mik'e tazo bak'in k'ofar ta bud'e sai kuma ta juya ta koma ta zauna gefen gado tana ta haki hannun ta rik'e da cikin ta,
shi kuwa Hamma Umar yana ganin haka ya koma parlour dinning area ya nufa yana zuwa,
ya d'auki cup tea ya had'a mata mai kauri sannan ya juyo ya dawo cikin d'akin yana shiga kiran Usman na shiga woyar shi gefen ta yaje ya zauna sannan ya mik'a mata cup d'in cikin kula yace.
"Karb'i kisha tea zakiji k'arfi."
kai ta juya tare da matse ido ta samu ta zubda k'ollah,
shi kuwa woyarshi ya zaro ya amsa kiran yana kallon fuskar ta,
gaisawa sukayi da Usman sannan yace .
"Kashe maganin ko?."
"Eh nasha tun d'azun ma."
sai kuma yayi shiru... can kuma yace .
"Hamma Umar Ummul fa?."
"Gata nan tana ta kuka tak'i cin komai kuma bata da lafiya ,
gata bari in bata woyar."
"Toh" yace sannan yayi shiru yana jin Hamma Umar d'in yana cewa.
"Ga Usman yana magana."
Karb'ar woyar tayi cikin rawan jiki murya na rawa tace.
"Hello ya Usman."
A hankali cikin sanyi yace.
"Na'ammmm Ummul."
Tana jin muryar shi sai kuma ta fashe da kuka cikin kukan tace.
"Ya Usman cikina ciwo , kaina ciwo jiri nake ji duhu nake gani ya Usman ni dai zan dawo gida."
sai kuwa ta fashe da kuka.
shi kuwa Hamma Umar shiru yayi ya zuba mata ido yana sauraron magarda takeyi,
shi kuwa Usman a hankali yace.
"Ummul kinfi son zuciyata ta fashe ko? Ummul bazaki bar kukan nan ba ko? Ummul kina son inyi fushi da ke ko?."
Kai ta rink'a juyawa kamar tana gaban shi sai kuma tasa tafin hannu ta share hawayen ta murya a sanyaye tace.
"Ah ah ya Usman bana so kayi hak'uri nayi shiru."
Ajiyar zuciya ya sauk'e sannan yace.
"Ban yarda ba nasan yanzu haka idanun ki na zubda hawaye kuma ba zakici abinci ba."
da sauri tace.
"Wallahi nayi shiru kuma na share hawayen kuma wallahi zanci abincin."

"Kin tabbata ?."

"Ehh wallahi."

"Na tabbayi Hamma Umar?."

"Ehh gashi ka tabbaye shi."

Sai kuma ta mik'awa Hamma Umar d'in woyar tana cewa.
"Bani zansha shayin."
Mik'a mata cup d'in yayi sannan ya karb'i woyar tashi,
yana kallon fuskar ta,
shi kuwa Usman dariya ya d'an yi cikin sanyi yace.
"Hamma na tayi shiru ko? ta karb'i tea d'in ? ta fara sha ne?"

Murmushi yayi tare da cewa.
"Ehh ."
Dariya Usman ya kumayi sannan yace.
"Hamma na kai baka saba lallashin wani d'an adam bayan ni a duniya ba shiyasa ka k'asa sata tayi shiru Hamma dole ka koyi lallashi fa tunda Allah ya had'a ka da Ummul."

murmushi kawai yayi sannan yace.
"Toh."

Bayan ya katse kiran ne ya juyo ya kalli Ummul da tuni ta shanye tea d'in sai zufa keta tsatstsafo mata tako ina sai damk'e cikin tayi tana murk'ususuwa,
mik'ewa yayi ya tsaida ta sannan ya rink'a jijjigata har saida yaji tayi gyatsa sannan ya meda ita kan gadon ya kontar da ita,
d'akin shi yaje jim kad'an ya dawo hannun shi rik'e da magani ,
shida kanshi ya bata tasha sannan ta koma ta konta,
shi kuwa rafan kud'i ya ajiye mata a gefen ta wanda zasu kai dubu 100 sai kuma wata y'ar counter near yar k'arama sarkace da y'an kunne sai zobe,
zoben ya zaro sannan ya kamo hannun ta ya zura zoben a yatsarta dake kusa da y'ar karamar yatsar ta sannan yace.
"Gashi insu Anty Shuwa sunzo ki basu wannan kud'in da sark'ar."
Harara tayi mishi k'asa-k'asa sannan ta zare zoben ta jefar gefe,
shi kuwa parlour ya koma ya zauna,
ya zauna kenan su Anty Shuwa suka iso bayan sun gaisa ne sai ya fita shida ya SADIK daya kawo su.

Su Anty Shuwa kam tunda suka samu Ummul a konce ba lafiya sai sukayi zaton ta zama cikekkiyar matar aure,
yayin da Usman ma tunda Hamma Umar yace mai Ummul bata da lafiya kuma tana ta kuka sai ya d'auka Hamman nashi ya zama oggone a daren jiyan,
so haka suma su Anty Shuwa amman Anty Halima ita ta gane sarai ba abinda Hamma Umar yayiwa Ummul kawai ya bada tukuicin ne.
haka suka wuni suka yi tayiwa Ummul nasiha ta kuma ci abinci so ta samu tayi k'arfi,
sai yamma lis suka tafi.

bayan sun tafi kuma ta wore ras ta fito parlour dan a cewarta yanzu lokaci yayi da zata fara gasa Hamma Umar d'in.

Da dere yayi Hamma Umar yana d'akin shi bayan ya yayi wonka ya fito yayi shirin bacci har ya konta sai kuma ya mik'e ya nufi d'akin ta yana zuwa ya zauna gefen ta a hankali ya....



*Dedde na Allah ya baki lafiya*


By
*GARKUWAR FUlANI*




📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 1⃣5⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇







*Alhamhadullih jikin Dedde na da sauk'i sosai ta samu lafiya nagode wa Allah daya bata lafiya kuma nagode muku masu kirana da masu turo min messages da yi mata addu'a a groups da masu bina pc, UWA uba wad'an da sukayi tattaki suka zo dubiya duk nagode da addu'oinku gareta ngd matuka Allah bar zumunci 🤝😘😍🤝*






*K*allon ta yayi cikin mamaki ganin yadda take konce duk ta duk'unk'une wuri d'aya gaba d'aya ta takura kanta ga kayan jikin ta duk ta konta dasu hatta hijabin kanta bata cireba ta nad'e guiwowin ta har suna tab'a k'irjin ta sai hannun ta data sa ta kame kafad'un ta sannan ta cusa kanta cikin pillow da kaga ganta kasan bacci takeyi amman cikin tsoro duk ta takure hatta numfashi ta da kalan tsoro take fidda sautin shi,
gyara zaman shi yayi yana fuskan tarta a hankali yasa hannu tare da kamo hijabin ya fara k'ok'arin zare mata shi a jikin ta,
ita kuwa cikin baccin tsoron da tunda tazo gidan a haka take rayuwa cikin tsoro dan ita bata tab'a kwana ita kad'ai a d'aki ba a rayuwar ta gata da tsoro amman kuma k'iyeyyar Hamma Umar d'in ta hanata kusantan inda yake ta gommace ta rayu cikin tsoro,
a hankali ta d'an motsa tare da k'ara jawo hijabin nata duk cikin bacci,
shi kuwa ganin ta d'an motsa ne yasa ya d'an janye hannunshi yayi shiru yana kallon fuskar ta,
can zuwa wani lokacin kuma ya d'an k'ara matsota sannan yasa hannun ya fara zaro hijabin har ya cire shi a kanta,
dai-dai sanda ya cire ita kuwa ta bud'e idonta,
gaba d'aya jikinta rawa yakeyi tamkar mazari sai wani irin zaro idanu tayi cikin tsoro ta mik'e tare da fizgewa tana tuttureshi,
shi kuwa Hamma Umar kamota yayi da k'arfi ya maidata kan gadon pillow ya jawo sannan ya kontar da ita kan pillow sai kuma yasa hannu a hankali ya fara zuge zip d'in rigarta,
ganin haka yasa ita kuwa tayi wani irin yunk'uri tare da sa hannu bibbiyu ta tureshi da k'arfi har saida kanshi ya bugi jikin gado da sauri ya dafe kanshi da hannun d'aya d'ayan kuma ya kamota ya rik'e gam,
cikin sanyi yace.
"Ina zaki je?
ki nitsu mana zakiji wa kanki ciwo fa zoki konta ba abinda zai sameki gani a kusa da ke."
hannu tasa tana ta kiciniyar b'amb'are yatsun hannu shi cikin tsiwa tace.
"Bana so ka sake min hannun na ka fita harkata ba ruwan ka da ni ka barni inje duk inda naga dama kar woni zo ka mak'ale ni kace zaka min dad'in baki ni bana sonka bana son ganin ka."
jawota yayi jikin shi cikin tsura mata ido yace.
"Bakya sona fa kikace khairi nifa d'an uwan kine."
"Eh bana sonka bana son ganin ka na tsanekaaa."
lips d'in shi na k'asa ya kamo ya rink'a tsotsa a hankali yana jin zafin kala manta ,
sai kuma ya k'ara matsota tare da zare rigar sannan yasa hannun yana kunce d'aurin da tayiwa zanin ta,
ita kuwa gaba d'aya sai wujijjigashi takeyi tana ta kici niyar kwace kanta amman ta kasa kawai sai ta sunkuyar da kanta tare da kafa bakinta a damtsen hannun shi ta datsa mishi cizo mai zafi dan gaba d'aya ta tsinke da Hamma Umar d'in,
yana jin yadda ta dasa hak'oran ta a damtsen hannun shi zafin yana ratsashi madadin ya saketa sai ya k'ara matsota jikin shi ido ya rumtse da k'arfi cikin wani irin yanayi yace.
"Zaki kasheni kike so? Ummu kiji tsoron Allah fa meyasa kika zab'i ki azabtar dani bayan kin san ni mijin kine."

Ita kam ganin bata da k'arfin kwatar kanta yasa ta saki kuka mai cike da tsoro murya a birkice tace.
"Ka sani wallahi ni bana sonka bana son ganin ka,
ka fita hanya ta."
Ido ya lumshe dan hak'ik'a yana jin ciwon yadda take cemai bata sonshi cikin sanyi yace.
" Khairi bakya sona ko ?"
"Ehh bana sonka."
Kai ya jinjina sannan yace .
"Kin dai san ni mijin kine ke kuma matata ce so kin san akwai hak'k'ina a kanki ko? kin kuwa san zaman aure mukeyi ni kuwa ba waliyi bane."
tureshi ta k'ara yi cikin kuka tana Jan hijabinta tana k'ok'arin rufe jikin ta murya na rawa tace.
"Ni bana sonka kuma ba zaman auren da zanyi dakai dan bazan karya al'k'awarin da nayiwa Mustapha ba ni ka sake ni."
ajiyan zuciya ya rink'a sauk'e wa cikin yanayin cushewar tunani ga yanayin canji daya tsinci kanshi a ciki shi da kanshi bai san yana da wannan halittar ba dan a zaton shi da zai iya rayuwa ko ba mace amman gaba d'aya tunda akayi auren yake jin bak'in al'amura a jikin shi,
saketa yayi cikin sanyi ya mik'e ya tsaya a bak'in gadon yana mai jin zafin kanshi data gwora da jikin gado da kuma cizon da tayi mishi,
hannun yasa ya kamo hannun ta a hankali yace.
"Ki dena kwana da bra a jikin ki yana haddasa ciwon k'irjin yana kuma iya jawo cancer ko ya sa miki toshewar numfashin,
ki dena kwana da kayan masu nauyi a jikin ki,
ki rink'a yin al'wala kafin ki kwanta ki kuma yi addu'ar bacci."
Baki ta tab'e cikin jin haushin sa tace.
"Nida jikina ba ruwan wani dani inyi yadda nike so kuma dole in kula da kaina tunda ina rayuwa da kai gida d'aya."
Murmushi yayi gano wai danshi take kwana a hakan,
hannun ta yaja har zuwa cikin bathroom a hankali yace.
"kiyi al'wala."
baki ta tura sannan tayi al'walar nan ma dan tasan hakan koyarwa ce ta annabi,
bayan tayi al'walan suna fitowa ta zauna bak'in gadon cikin tsiwa tace.
"Zanyi bacci fa."
Kai ya gyad'a sannan yasa hannu ya kontar da ita blanket ya jawo ya d'an rufeta ,
hannun shi na cikin blanket d'in ya sunkuye kanta a hankali yace.
"D'an d'ago bari in cire miki bra d'in."
harara tayi mishi k'asa-k'asa cikin tura baki tace.
"Ni ai ba karuwa bace."
sai ta kuma ture hannun shi sannan ta juyo ta konta ta a kife,
shi kuwa Addu'a yayi tare da shafe jikinta kamar yadda ya saba yiwa Usman ,
sannan ya kalleta ahankali ya juya ya fita,
a parlour ya konta tare da son jin d'umin ta Amman yasan hakan bazai samu ba,
haka ya kwana cikin halin takura.


Haka rayuwa taci gaba da juya musu duk wata kulawa da gata Hamma Umar yanayiwa khairn shi yayin da ita kuwa take ta azabtar dashi ,
ta yadda baya samun ko magana mai dad'i ma bare ya samu hakkin shi dake kanta duk da yana yawan zuwa inda take amman haka ba abinda yake sama mishi sai azaba da bak'in ciki ko tafin hannun ta bai isa ya murzaba sai yasha bak'ar magana.


Yau Monday kuma Yau kwanan su takwas da tarewa kenan,
yau tunda sassafe Hamma Umar ya shirya komai tsab kamar yadda yasaba sannan ya shiga wonka sauri sauri ya shirya dan yau zai fita zaije gidan governor dan duba lafiyar shi duk da dai bai gama hutun auren nashi ba amman zaije dan duba lafiyar shi ,
bayan ya gama shirin shi tsab sannan ya fesa turaren shi mai tarin k'amshi laptop nashi da phone dinshi ya d'auko sannan ya fito parlour kan dinning table ya ajiye su ,
sannan ya jawo cups guda biyu tea ya had'a ,
sannan ya d'an juya rik'e da cups d'in ya nufi cikin parlour gaban Ummul d'in ya d'an tsaya cikin sanyi yace.
"Khairi taso kisha tea sauri nake zan fita yanzu zan dawo."
kallon shi tayi sannan ta kalli yadda tea d'in yake ta tiriri da alamun ruwan yana da zafi sosai ido ta lumshe cikin jin dad'in shawarar da shaid'an ya kawo mata fuskar shi ta kuma kalla cikin mugunta ta mik'e ta tsaya a gaban shi,
hannu tasa ta karb'i cup d'in tare da tsura mishi ido,
shi kuwa kanshi ya sunkuyar tare da d'an juya tea spoon d'in dake cikin cup d'in,
itako murmushi mugunta tayi,
cup d'in ta d'ago tare da watsa mishi ruwan zafin a fuskarsa ,
ba zato ba tsammani yaji ta watsa mishi tea d'in a fuskar da jikin wani irin zafi da rad'a d'i yaji yana ratsashi,
jin zafin ruwan daya sauk'a a jikin shi yayi wani irin yunk'uri ya hankad'ata da k'arfi saida ta fad'i k'asa,
sai kuma cup d'in hannun shima ya sub'uce yayi k'asa,
hannun shi ya rink'a yarfawa yana d'an jujjuya kai yana jin zafin na ratsa fatarshi har cikin zuciyar shi yake jin zogin,
a take fuskar shi tayi jazir sai zufa keta keto mishi tako ina,
ita kuwa Ummul yana tureta tana fad'uwa ta kife kai tare da sakin kuka,
kuka ta saki da k'arfi shi kuwa jin kukan yayi sauri yayi kanta yana zuwa ya d'ago ta ya sa hannu biyu ya rik'e kafad'un ta ido ya zuba mata cikin wani irin yanayi ya lumshe ido murya a sanyaye yace.
"Kiyi hak'uri Ummulkhari bawai na tureki dan zafin ruwan da kika watsa min bane,
a a wallahi na tureki ne dan kar ruwan ya fantsalu ya dawo jikinki ya k'onaki ,
kiyi hak'uri."
Ido Ummul ta zuba mishi tare da k'ara sautin kukan nata tanayi tana mita,
a cikin zuciyar ta kuwa tabbas ta cika da mamaki har cikin ranta taji mamakin yanayin da Hamma Umar keyi mata magana a yanzu bayan k'onashi tayi sannan kuma shike bata hak'uri har kuma yana cewa ya tureta ne dan kar itama ta k'one,
kuma a zahiri da kaga fuskar shi kasan yana jin zafin k'unan amman bai bi ta kanshi ba ya tsaya bata hak'uri,
shi kuwa Hamma Umar har cikin ranshi bawai ya tureta dan ta watsa mishi ruwan zafin bane kuma yaji zafin yadda ya ture harta fad'i har takai da tana kuka,
a hankali ya kuma matsota yana kallon bakinta da take ta kuka da iya k'arfin ta ya lura so take ta tara mishi mak'otan su,
kuka take tana.
"Allah zai saka min ka rabani da kowa nawa kazo kana azabtar dani na tsane k...!"

a hankali ya sunkuyar da kanshi cikin sauri ya manne bakin shi da nata lips d'in ta yayiwa rik'on taushi ida nunshi ya lumshi tare dasa hannun shi d'aya ya zagayo k'ugunta ,
ita kuwa ido ta zazzaro woje cikin tsantsar firgita da tsoro ga tarin mamaki Hamma Umar ne ke manne bak'in shi da nata ,
gaba d'aya ya rufe bak'in manata ya hanata kukan bare rakin da takeyi da son tara mishi mutanen,
shi kuwa Hamma Umar idon shi a lumshe ya sab'ule lips d'in ta a bak'in shi cikin lumshe ido ya juya ya koma bedroom d'in shi ,
wonka ya sake yi sannan ya canza kaga ,
ya fito parlour kan dinning table yaje phone d'in shi ya d'auka kanshi a sunkuye yazo gefen ta ya tsaya yana jin yadda take yin kuka a hankali yace.
"Ayyah Khairi kiyi hak'uri kibar kukan nan kinji bari

4 Comments On RUBUTACCEN ALAMARI
avatar
shukra-sulaiman

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
shuraihu

1 year ago

Reply

Replying to shukra-sulaiman

Tnx too

avatar
fatima-idris

1 year ago

Reply

Nice novel

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fatima-idris

Aha tnx

Please Login or Register in order to submit comment