Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hamma Umar kaito na tunda ina raye ban iya k'anwar da duk wani abu da zai saka kuka a rana mafi daraja a gare kaba."
jin muryar d'an uwanshi yasa ya juyo ya rugume k'anin nashi,
suka rugume juna cikin rauni Hamma Umar yace.
"Usman Abban mu na tuna yau gashi ina bid'ar addu'arsa gashi kuma baya raye."

ganin yadda suke kukan ne jikin kowa yayi sanyi haka yasa Ya Adam ya jagoranci abokan Hamma Umar din suka koma cikin gida a gefen baki Anty Shuwa kuwa taja k'awayen Amarya suka tafi,
Anty Halima kuwa cikin kuka ta kamo hannun Ummul dake kuka kamar ranta zai fita sukayi cikin gida,
haka aka watse taron,
Ammi kuwa dama tuni tayi cikin gida kai tsaye d'akin Hajjajo ta wuce tana wani irin kuka mai karya zuciyar mutane,
Hamma Umar kuwa shida Usman suna tashi suma suka wuce d'akin Hajjajo, suna zuwa suka zauna gaban Ammin su ita kuwa Ammin ta k'asa magana sai kuka,
Hamma Umar ne ya matsota kanshi ya d'ora kan cinyarta cikin kuka da rauni ya jawo Usman kuma jikin shi ya rugume shi baki na rawa yace.
"Am! Ammi! Ammeee! ki dena kuka Ammi ki samin al'barka kimin Addu'a Allah ya bani ikon cika al'k'awarin dana d'aukar wa kaina,
bani da mai tayani Addu'a bayan ke da d'an uwana Ammi kibar kuka karki sa Usman a rud'ani."
Hannunta ta dafe kanshi...




*Kuyi hak'uri da Wannan Yau bak'in ciki kamar na d'aki kaina na gama typing 1 page mai Reed more 7 wlh garin gyara nayi delete nashi da ker nayi wannan*


By
*GARKUWA FULAni*
濠碘槅鍋撶徊浠嬪疮椤栫偛绠熸い鎰剁秶缁辨棃鏌涢幇鈺佸闁挎稒鎸歌灋闁挎繂鎳庨弳娆戠棯閹规劖鐝柨娑樺暣瀹曟﹢濡歌缁憋附淇婇顒傚埌闁哥噥鍋嗘竟鏇㈡惞椤愵剛纾鹃梺鍛婂姂閸斿酣鏁嶉幘婢勬盯鏁愰崨顓熸缂佺偓宕樺▍鏇㈡晬閸愵喖绀冮柕濞у秶澶勫┑鈽嗗亾缁蹭粙宕銈咁棜闁跨噦鎷�

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 1闂傚倷鐒﹂崜姘舵偂婢舵劕绠柨鐕傛嫹3闂傚倷鐒﹂崜姘舵偂婢舵劕绠柨鐕傛嫹

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

濠碘槅鍋撶徊浠嬪疮椤愩倕顥氶柧蹇e亾缁辨棃鏌涢幇鈺佸闁挎稒鎸歌灋闁挎繂鎳庨弳娆戠棯閹规劖鐝柨娑樺暣瀹曟﹢濡歌缁憋附淇婇顒傚埌闁哥噥鍋嗘竟鏇㈡惞椤愵剛纾鹃梺鍛婂姂閸斿酣鏁嶉幘婢勬盯鏁愰崨顓熸缂佺偓宕樺▍鏇㈡晬閸愵喖绀冮柕濞у秶澶勫┑鈽嗗亾缁蹭粙宕銈咁棜闁跨噦鎷�









*K*anshi ta dafe cikin muryar kuka tace.
"Farouq Allah yayi muku albarka kai da d'an uwanka Allahu rabbi ya jibanci lamuran ka hak'ik'a yau ina al'fahari da kai,
kuma na tabbatar yau da mahaifinku na raye zaiyi al'fahari da kai ,
domin ka cika d'a na gari d'a na hallas tabbas yau kasa farin ciki a zuk'atan iyayen rik'onku kai da d'an uwanka domin wannan abin da kayi zai sama musu nitsuwa a zuk'atan su ta yadda zasu samu k'arfin guiwar cewa ko bayan ransu zaka kula musu da y'ar su bisa amana da gaskiya,
naji dad'i da samun yara nagari Umar Farouq da Usmanu shehu Allah ya muku al'barka ya k'ara muku k'aunar juna Allah ya sanya al'khairi a rayuwar Ku."

Murmushi suka rink'a yi zuk'atan su cike da farin ciki da aminci jin irin addu'oin da mahaifi yarsu ke musu,
Hamma Umar kuwa k'ara jawo Usman yayi jikin shi ,
shi kuma kanshi ya kara kontarwa kan cinyar Ammin sun,
Hajjajo da Inna ma Addu'a sukayi tayi musu da sanya al'khairi da sa musu al'barka.

Anty Halima kuwa tunda ta kamo hannun Ummul suka koma cikin gida kai tsaye d'akin Nenne ta wuce da ita,
tana shiga ta saki hannun Ummul taje bak'in gado ta kifa guiwowin ta a k'asa kanta ta kife kan cinyar Nenne cikin kuka mai cike da tausayi murya a raunane baki na rawa tace.
"Nenne Hamma Umar ya bani tausayi Nenne kiga irin al'k'awarin da Hamma Umar ya d'auka a kan Ummul Nenne sai kinga yadda Hamma Umar yake kuka cur-cur da hawayen shi ya rugume ya Usman suna ta kuka sun bani tausayi Nenne sun tuno Abban su."

sai ta kuma d'ago kanta cikin zubda k'ollah ta kalli Ummul dake ta kuka tamkar zata amayo da ranta cikin sanyi tace.
"Ummul ke kukan dad'i kikayi naki kukan najin dad'i ne iyayen ki na raye gaba da baya,
bawan Allah Hamma Umar shiko kukan rashin uba yakeyi domin shi yasan zafin rashin Uba dan shi kam ya Usman Hamma Umar d'in ya meye mai gurbin mahaifin su,
Hamma Umar bawan Allah maraya duk da tarin k'iyeyyar da kike nuna masa bai hanashi yin al'k'awarin zai rike da amana ba."

Daga nan kuma sai ta mik'e ta fice ta nufi part d'in Abban ta,
ita kuwa Ummul kuka take da bak'in ciki mai yawa a ranta a fili take gani duk an tsaneta tunda babu ko mai lallashin ta inba Ya Usman ba kowa harara ke had'a su ganin yadda su Anty Shuwa ke cilla mata harara yasa ta mik'e cikin kukan ta nufi part d'in Hajjajo,
a parlour ta samu su Hamma Umar d'in da ya Usman dasu Hajjajon da Ammin su,
har yanzu Hamma Umar kanshi na kife kan cinyar Ammin yana kuka k'asa-k'asa dan gaba d'aya jikin shi da zuciyar shi Abban shi kawai suke tuno mishi a yau d'in,
shi kuwa Usman kukan Hamma Umar ne yake sashi kukan,
itama Ammi ta kasa d'aure zuciyar ta sai k'ollah dake ta bin fuskar ta,
itama Ummul nata kukan take ta wuce bedroom d'in Hajjajo kai tsaye kan gadon ta konta ta kife kanta cikin pillow taci gaba da kuka,
ita kuwa Anty Halima a baki k'ofar parlour Abba tayi sallama cikin muryar kuka,
cikin sanyi ta shiga bayan Abba ya amsa mata sallamar , Abban ta samu shida Daddy suna zaune sai fufun goro kusan guda 12 da katon-katon na sweet da k'oren dabino dake gaban su,
gefen Abban nata taje ta zauna cikin sanyi ta gaida su sai kuma ta fara magana cikin raunin murya tace.
"Abba Hamma Umar!
Abba Hamma Umar da ya Usman sunata kuka sun tuno Abban su,
Abba Hamma Umar ya bani tausayin Ammin suma sai kuka takeyi,
Daddy kuje ku rarrashe su,
Hamma Umar ya bani tausayin yanata kuka ya Usman ma yana kuka."
kusan a tare Abba da Daddy suka mik'e suka fita kai tsaye parlour mahaifi yarsu Hajjajo suka nufa Anty Halima na biye dasu a baya,
suna shiga parlour suka zauna gefen Ammi da yaranta Daddy ne ya jawo hannun Usman cikin kula yace.
"Ya isa kukan ya isa haka habba Usman k'afa san zuciyar ka bata da cikekken lafiya."
A hankali Usman ya kalli Daddy cikin sanyi yace.
"Daddy kalli yadda Hamma Umar yake kuka ,
hawaye na bazasu bar zuba ba muddin idanun Hamma Umar na zubda k'ollah."
Abba ne ya kalli Hamma Umar d'in cikin sanyi yace.
"Farouq Kaine nake ganin kana da k'arfin zuciya sai gashi ka k'asa iya daurewa ga yadda kake kuka kalli yadda kukanka yasa d'an uwanka yin kuka kalli mahaifiyarku yadda kuka sata a rud'ani,
shin ka manta zuciyar d'an uwanka ne?
Farouq a yanzu ba abinda mahafinku keso daga gareku da mu da mahaifiyar mu sai Addu'armu."
da sauri yasa hannu ya share hawaye shi cikin k'arfafa zuciyar shi yace.
"Abba na bari,
Usman kayi hak'uri ka koyi dauriya kajiko d'an uwana?."
Kai Usman ya rink'a juyawa tare da goge k'ollah,
daga nan su Abba sukayi ta musu nasiha sannan suka fita tare dasu dan jin an kira sallan maggariba,
har sun fita gaba d'ayan su ,
sai kuma ya Usman ya juyo cikin sanyi ya shiga d'akin Hajjajo kai tsaye bak'in gadon da Ummul ke zaune yaje ya zauna cikin sanyi ya zaro hankicif d'in shi ya mik'a mata,
bata karb'a ba sai d'ago kanta tayi ta zuba mishi ido cikin kuka tace.
"ya Usman shike nan Hamma Umar zai rabani da Mustapha har *Abadan* shike nan nayi ban kwana da farin cikina,
ya Usman kalli al'k'awarin da Hamma Umar yayi dan tsabar mugunta ya Usman shike nan Hamma Umar ya zame min k'arfen k'afa Ya Usman kasan ina son Mustapha gashi Hamma Umar ya rabamu gashi Abba na ya kwace woyata shike nan ya Usman ko muryar Mustapha baza a barni Mayo ba,
ya Usman Hamma Umar ya binne min rayuwa ba Mustapha ba karatu na."
sai kuma taci gaba da kuka,
shi kuwa Usman ido ya tsura mata ,
sannan ya d'ago hannun shi ya dafe kahon zuciyar shi cikin tsura mata ido yace.
"Ummul kece sanadin bugawar zuciyata zaki kasheni ki huta ki sani idan na mutu kece sila."
cikin tsoro da mamaki ta zaro ido woje baki na rawa tace.
"Ya Usman ni kuma? ni dai? in kasheka kuma? sabida me zan kasheka?."
Kai ya jinjina mata cikin sanyi yace.
"Ehh kasheni kike son yi tunda na lura bazaki bar koke-koken nan ba,
na kuma gaya miki bana son inji kina kuka,
Kukan ki nasa zuciya ta tayi nauyi bana son kina kira min sunan Mustapha in kina ki ranshi ji nake zuciya tana harbawa da k'arfi, kamar zata fashe."
da sauri tasa hannu ta karb'i hankicif d'in sannan ta goge k'ollah cikin rawan murya tace.
"Nayi shiru ya Usman na bar kukan ,
bana son ka mutu."
Murmushi yayi sannan yace.
"Allah ya d'aiyiba."
itama murmushi tayi sannan tace.
"Ina sonka ya Usman."
cije lips d'in shi yayi da k'arfi sannan ya juya cikin sauri yayi hanyar fita har yaje bak'in k'ofar fita sai kuma ya tsaya cikin sanyi yace.
"Allah ya d'aiyiba,
nima ina sooon ki k'anwata Ummul."
daga nan kuma sai ya fita,
part d'in su ya nufa yana zuwa ya samu abokan Hamma Umar d'in duk sunyi al'wala shima al'walan yayi sannan suka nufi masallaci,
bayan sunyi sallan maggariba basu dawo ba saida akayi sallan ishah sannan suka dawo gidan.

9:00 pm Hamma Umar ne da abo kanshi suke ta hira a parlour shi hira sukayi sosai cikin shak'uwa da sabo Abdallahn Maryam ne yayi murmushi cikin tsokana ya kalli Hamma Haiydar din Minali yace.
"Kai General Aliyu wai ina Hamma Yusuf d'in Aysha ne ban ganshi ba?."
Amadin Nadiya ne yayi murmushi tare da cewa.
"You ai Hamma Mahmoud d'in Khadija ma ban ganshi ba."
Salim d'in Tawa ne yayi murmushi tare da cewa.
"Toh sa idawa."
Abun batul kuwa murmushi yayi sannan yace.
"Mutun da matar sa ai sai adena sa musu ido."
Hamma Bashir d'in Rukayya ne yayi murmushi tare da nuna Hamma Hassan d'in Fateema yace.
"Kaima ko zaka zillene kayi gaba da matar ka?."
Hamma Haiydar d'in Meenarl ne ya d'an yi murmushi sannan yace.
"Kai Aisar d'in Bintu sai dariya kawai kake kuma kaima anjima za'a nemeka a rasa zaka tafi gun matar ka."
Al'ameen d'in Fauziyya ya mik'e cikin raha yace .
"Nima nayi gaba."
Ridwan d'in Zakiya kuwa shima sai murmushi yake yana woya da zakiyarsa Ahmad ana Muslim kuma shima dariya kawai yake.

Suna cikin hira da dariyar su Hamma Yusuf ya shigo hannun shi rik'e da robobin inabi dasu Apple da reke sai kwakwa da dibino,
ajiye su yayi a tsaki yarsu ya zauna gefen Abuturrab cikin murmushi ya kalli Aisar yace.
"Ga inabi nan kusha ,
Aysha ce ta kirani tace in seyo mata shine kuma na kawo muku ku d'ana."
dariya sosai Abban Rukky pinky yayi yace.
"Aysha ta kiraka ko kai ka kirata."
murmushi Hamma Umar d'in Ummul yayi tare da cewa,
" Ku dai kuci kar kuyi tone -tone."
dariya sukayi baki d'ayan su sannan sukaci gaba da hirarsu,
suna hira suna cin lodin fruits din da Hamma Yusuf ya kawo musu,
can sai kuma Hamma Umar d'in ya mike cikin sauri Key din motar Aisar ya zara sannan ya fice da sauri yana fita yaje ya lodowa Ummul fruits d'in da yacin gaba d'aya sannan ya dawo gida,
Parlour nashi ya shiga inda ya samu su Abu har yanzu suna hira,
Amadi ne ya kalleshi cikin tsokana yace.
"Kaima Ummul tayi kira ne kaje ko?."
murmushi kawai Hamma Umar d'in yayi tare da juya kai sannan ya zaro woyar shi auta Aliyu ya kira,
Jim kad'an Aliyu ya shigo rik'e da hannun Hannah yarin yar Hamma Haiydar da Meenarl,
robobin fruits d'in Hamma Umar ya mik'a wa Aliyu cikin yana yin aike yace.
"Gashi ka kaiwa Ummul kace abokin nane ya seyo mana mukaci shiyasa itama na seyo mata nata."
"Toh" Aliyu yace sannan ya karb'i robobin yayi cikin gida,
kai tsaye parlour Hajjajo ya nufa, yana zuwa ko ya samu Ummul d'in tana zaune fuska duk a jeme ,
a hankali ya ajiye mata fruits d'in cikin kula yace.
"Anty Ummul sarkin son zak'i gashi wai inji Hamma Umar wai abokin shi ne ya seyo sukaci shine kema ya seyo miki naki."
ido ta d'ago cikin tsuke fuska ta buga mishi harara sannan tace .
"Bana so ka meyar mai da abunshi."
Kallon ta yayi cikin sanyi yace.
"Kai Anty Ummul kinfa san ba kyau meda hannun kyauta."
K'afa tasa ta ture robobin,
Shi kuwa Aliyu hannu yasa ya d'auki robaa inabi guda d'aya ya fice tare da cewa.
" ni dai zanci."
Hajjajo kuwa tire ta d'auko ta tattara fruits d'in duka ta lodasu kan tiren cikin yin hamdala ,
ta rink'a nuna wa mutane tana cewa.
"Ku gani Ku shida Farouq ya fara cika al'k'awarin d'aya d'aukar wa kanshi."
suko sauran mata sai sunyi ta yabawa halin Hamma Umar d'in,
ita kuwa Ummul ji take kamar taje ta shak'e shi ya mutu ta huta da bak'in cikin sa,
kamar wasa Hajjajo ta dage tana bin d'aki-d'aki tana nuna musu abinda Umar ya aiko wa Ummul harsu abba sai da taje ta nuna musu,
Ummul kuwa haka ta kwana cikin k'unci shiko Hamma Umar yana tare da abokan shi..

Washe gari misalin k'arfe 11:00 Am dai-dai
dubban al'umma suka shaida daurin auren Umar Ibrahim Umar Shuwa tare da Rabi'atu Hassan Umar Shuwa Ummul kenan,
d'aurin auren d'aya samu halartan manya-manyan bak'i kama daga gwamnan Yobe Ibrahim gaidam dan Hamma Umar shine doctor dake duba lafiyar gwamnan nasu na jihar Yobe tare da sarkin su,
bayan an gama d'aurin auren ya Usman ne yazo ya rugume Hamma Umar d'in cikin happy yace.
"Ina cin farin ciki Yau Allah ya nuna min auren d'an uwana Allah ya tayaka rik'o."
murmushi Hamma Umar yayi tare da cewa.
" Amin."
daga nan abokan shi suka rink'a yi mishi musabaha suna tayashi murna,
cikin zugar mutanen dake tayashi muryar ne yaga Mustapha ya mik'a mai hannu cikin sanyi sukayi musabaha sannan Mustapha yace.
"Hamma Umar inayi maka fatan al'khairi a Rayuwar auren ka kaida Ummul ina taya ka farin ciki a matsayinna na d'an uwanka musulmi."
sai kuma muryar shi ta fara rawa sai hawaye cur-cur a fuskar Mustapha,
cikin tausayawa Hamma Umar ya rugume shi a hankali yace.
"Mustapha ka gafar ceni na shiga rayuwar ka kai da Ummul Amman bayina bane Mustapha wannan rubutaccen al'amari ne bani da niyar rabaku,
su Abba ne suka had'a aurena da Ummul,
ku gafar ceni Mustapha domin na zame muku bak'in jakada a Rayuwar ku Mustapha ka gafar ceni."
Cikin rawan murya Mustapha yace.
"Hamma Umar na yarda da kaddar ta fatana ka rik'e min Ummul bisa amana."
kara rugume shi yayi sannan ya sake shi cikin sanyi Mustapha ya juya ya tafi,
shiko Hamma Umar haka yayi ta sallama da abokan shi dan duk yaune zasu tafi tunda biki ya kare gashi kuma abokan duk y'an nesane,
Hamma Haiydar har Kaduna
zai koma Hamma Yusuf kuwa Taraba Hamma Mahmoud Adamawa Yola Hamma Hassan Gombe yayin da Hamma bashin kuwa zai koma kano,
haka Hamma Umar da ya Usman suka tsaya a harabar gidan nasu suna ta ban kwana da bak'on nasu,
bayan duk sun tafi ne,
saura baki matama dake cikin gida duk sun tattafi sai y'an kad'an da suka rege.


Da daddare bayan Anyi Sallan maggariba da ishah Abba ya Tara family d'in shi harda Ammi da Inna da sauran mutanen gidan bayan sun zazzauna Daddy ya bud'e musu taron da Addu'a ,
sannan daga nan Abba kuma yayita musu nasiha mai ratsa jiki da zuciya,
Ummul kuwa zuwa yanzu kuka ya zame mata jiki.

Bayan Abba ya gama musu nasihar ne ya mik'e tsawon sa gaban Ummul yaje ya tsaya cikin bada umurni yace.
"Ummul taso kizo."
mik'ewa tayi cikin zubda k'ollah,
shi kuwa Abba hannun ta ya kama yaja har gaman Hamma Umar d'in cikin kula ya kamo hannun Umar d'in ya tsaida shi sannan cikin girma da jagoranci yasa hannun Ummul cikin tafin hannun Umar d'in a hankali yace.
"Farouq ga matar ka rik'e hannun ta ku tafi gidan Ku."
kallon Abban yayi cikin sanyi sannan ya manner tafin hannun shi ya rumtse hannun Ummul d'in kamar yadda Abba ya umur ceshi,
shi kuwa Abba Ummul ya kalla cikin tsuke fuska yace.
"Kibi mijin ki ku tafi Allah ya baku zaman lafiya."
"Amin Amin." sauran mutanen dake wurin suka amsa,
shi kuwa Hamma Umar hannun Ummul d'in ya jawo cikin yin k'asa da guiwowin shi suka durk'usa gaban Abba a hankali yace.
"Abba nagode Allah ya k'ara zumunci."
"Amin Amin."
Abba yace tare da shafa Kansu ,
sannan shi kuma Hamma Umar ya sake jan hannun Ummul gaban Daddy ya mishi godiya a haka ya rink'a jan Ummul suna zagaya wa har suka iso gaban Ammi da Nenne kamar kullum Hamma Umar hannun shi d'aya yasa ya ciro hularshi sannan ya jawo ummul suka durk'usa a gaban su cikin sanyi yace.
"Ammi ! Nenne ! nagode Allah ya saka muku da al'khairi."
dafa kanshi Ammi tayi kamar ko yaushe sannan tace.
"Allah ya sanya haske a wannan Aure naku Allah ya taya ka rik'o Allah yayi muku al'barka."
haka tayi ta musu Addu'a sannan tayiwa Abba ma godiya da kyautar y'ar shi d'aya bawa d'an ta.

Shi kuwa Umar yana rik'e da hannun Ummul yaje ya rugume ya Usman cikin sanyi da k'aunar k'anin nashi murya na rawa yace.
"Kamin al'k'awarin zaka kula da kanka, kasha maganin ka karkaci duk wani abu green kaji B'iyaye na,
nanda kwana 5 Kaima zaka koma gidana inci gaba da kula da kai."
murmushi Usman yayi cikin yanayin shi na abin dariya yace.
"Nayi ma al'k'awarin zan kula da kaina kafin nima na auru matata taci gaba da kula dani,
kaima ka kula da matarka Allah ya d'aiyiba."

gaba d'ayansu dariya sukayi sannan Abba yace.
"Farouq ku tafi dare yanayi."
"toh" yace sannan suka rekosu harabar gidan Usman ne ya bud'e musu mota bayan sunyi saida safe sannan Hamma Umar yaja motar suka tafi.

Tunda suka shiga motar ummul taci gaba da kukan ta,
shi kuwa Hamma Umar tuk'in kawai yakeyi hankalin shi na kan titi haka sukayi tafiyar tasu Ummul daga Potiaskum har cikin Damaturu kuka take batayi shiru ba,
suna isa k'ofar gidan ba tare d'aya shiga cikin gidan ba yayi parking sannan ba tare d'aya kalleta ba ya fito gefen da take ya zagayo marfin motar ya bud'e sannan ya jawo hannun ta,
ita kuwa sai fizge hannun take tana k'ok'arin kwancewa,
shiko sai matse hannun yayi da k'arfi cikin sanyi ya jata zuwa bak'in gate d'in juyawa yayi ya kalleta cikin bada umurni yace.
"Ki nitsu kisan abinda kikeyi karki kuskura ki shigar min gida da k'afar hagu ,
sannan kiyi Addu'a kafin ki shigar min gida, dan na lura akwai shaid'anu a tsakiyar kanki,
so ki watsar dasu anan kan titi karki kuskura ki shigar min gidana da su."
kai ta sunkuyar cikin zubda k'ollah dan ta tuno Nenne tama ta horeta da tayi addu'ar kafin ta shiga gidan,
k'ollah ta zubda sannan a hankali ta d'aga k'afar ta dama wanda kusan a tare suka d'aga k'afafun nasu,
a hankali sukayi addu'ar shiga gida sannan suka shiga cikin gidan.


A gida kuwa bayan Hamma Umar yaja motar sun tafi,
Usman ne ya dafe k'ahon zuciyar shi da sauri jin yadda zuciyar shi ke bugawa da sauri-sauri idon shi ya rumtse da k'arfi lokaci d'aya yaga wani irin duhu cikin k'arfin hali ya juyo ya kalli Nenne sai yayi murmushi ya bud'e baki a hankali yace ,
"Shike nan yau kam ni kad'ai zan kwana ba Hamma Umar,
da safe kuma ba Ummul wazan tsokana?."
Dariya su Ammi sukayi mishi sannan suka juya zasuyi cikin gida kenan a dai-dai lokacin Usman yayi wani irin numfashi tare da dafe k'irjin shi yayi taggal-taggal ya fad'i kan kujerun jiki ba.....



By
*GARKUWAR FULANI*
婵犵妲呴崑鎾跺緤娴犲鐤い鏍仜缁犵喐銇勯幇鍓佺Ф缂佽鲸妫冮弻娑㈠箛閳轰礁顬嬮梺鎸庣⊕閹告瓕鐏嬮梺鎸庣箓閹冲酣寮冲▎鎴犳/闁硅鍔栭悵顏堟煥濞戞ê鏆g€规洘锕㈡俊姝岊檪缂佹唻闄勬穱濠囶敃椤掑倸鍩岄梺鍝ュ櫏閸嬪棙绔熼弴銏℃優妞ゆ劦鍓涚壕楣冩⒑閸涘﹤濮傞柛鏂块叄閺佸秹骞樺鍕洴閺佹劙宕ㄩ鐔割唲缂備胶鍋撳畷妯衡枍閺囥垺鏅柛鎰靛枛缁€鍐煏婵炑冪Ф婢跺嫬鈹戦埥鍡椾壕缂佽弓绮欏畷顖烆敃閵堝拋妫滈梺璺ㄥ櫐閹凤拷

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 1闂傚倸鍊烽悞锕傚礈濮樿埖鍋傚鑸靛姇缁狀垶鏌ㄩ悤鍌涘4闂傚倸鍊烽悞锕傚礈濮樿埖鍋傚鑸靛姇缁狀垶鏌ㄩ悤鍌涘

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

婵犵妲呴崑鎾跺緤娴犲鐤い鎰╁€曢ˉ姘舵煣韫囷絽浜剧紒杈ㄦ閺屾盯骞囬埡浣割瀷闂佹寧绋掗幐姝岀亱闂佹寧绻傞幊搴ㄥ汲濞嗘垹妫柟瑙勫姈閻濐亪鏌ㄥ☉妯烘殻鐎规洘锕㈡俊姝岊檪缂佹唻闄勬穱濠囶敃椤掑倸鍩岄梺鍝ュ櫏閸嬪棙绔熼弴銏℃優妞ゆ劦鍓涚壕楣冩⒑閸涘﹤濮傞柛鏂块叄閺佸秹骞樺鍕洴閺佹劙宕ㄩ鐔割唲缂備胶鍋撳畷妯衡枍閺囥垺鏅柛鎰靛枛缁€鍐煏婵炑冪Ф婢跺嫬鈹戦埥鍡椾壕缂佽弓绮欏畷顖烆敃閵堝拋妫滈梺璺ㄥ櫐閹凤拷





*Y'an uwa abokai k'awaye yayu k'anne yara manya maza da mata masoya na da sab'anin haka writers da reedars dan Allah don soyeyyar mu da Annabi ina barar addu'arku ga mahaifiyata bata da lafiya dan Allah kusa min ita a addu'arku da bakunanku masu albarka Allah ya bata lafiya rabbi ya tashi kafad'an ta Allah yasa zakkan jiki ne a wanan gab'ar kuma zan shaida muku ba tabbas kuci gaba da samun posting nan kullum in nasamu nayi fani'imal in ban yiba la'basa nasan zaku min uzuri, DEDDE Am Allah ya baki lafiya 婵犵妲呴崑鎾跺緤娴犲鐤い鏍ㄧ箓閳ь剙鐡ㄦ穱濠囶敃椤掑倸鍩岄梺鍝ュ櫏閸ㄨ泛鐣烽鐐参╅柨鏃囧亹绾鹃箖姊洪崨濠傚闁告柨楠搁埢鏃堟晸閿燂拷*




*A baya nace Usman Accounter ne so na batane Usman Lecturer ne a Yobe state university so daga yanzu a lecturer sa zamu tafi dan shine aikin sa na gaskiya*





*B*a numfashi ya konta kan kujarar ba inda yake motsi a jikin shi, gaba d'aya su Nenne da Abba dasu Hajjajo a tare suka juyo kanshi ya Adam ne yayi sauri ya tallabo shi jikin shi cikin tsananin firgici ya rink'a juya kanshi yana d'an tab'a fuskar shi cikin d'imuwa yana .
"Usman ! Usman ! Usmaaaaaaan! ka tashi ka tashi Usman , Abba Daddy ku gani Usman baya numfashi."

Sai kuma ya k'ara rugumoshi jikin shi cikin rawan jiki,
Abba ne yasa hannu ya jawo Usman d'in jikin shi cikin k'arfin hali irin na manya ya cewa Daddy.
"Hussaini kawo wuruwa."
jiki na rawa Daddy ya shiga cikin gidan,
Ammi kuwa tunda Usman ya fad'i gaba d'aya sai jikin ta ya fara rawa kar-kar ko ina na jikin ta ya sake k'afafun ta suka k'asa d'aukar nauyin ta zuciyar ta sai bugawa take tara-tara cikin wani irin rashin kuzari ta zame a wurin ta zauna ta jingina da kujaran da Usman yake kai cikin sanyi baki na rawa take cewa.
"Ya Allah ka rufa min asiri Allah ka dub'eni da idon rahama Allah ka hanani ganin mugun abu Allah ka jinkirtawa wannan bawa naka kabashi lafiya Usman Allah ya hanani ganin gawarka ganin na mahaifinku ma har yau bai bar idanuna ba."
Inna ce ta dafa ta cikin sanyi tace.
"Kiyi mishi Addu'a Amina addu'arki gare shi ba hijabi insha Allah karb'ebb'iya ce ."
jin haka sai zuciyar Ammi ta kara karaya cikin sanyi ta kontar da kanta a cin yar Innarta ta kamo hannun Usman ta rink'a wani irin kuka mai cike da fargabar faruwar wani abu,
Hajjajo ma sai kukan takeyi ya Sadip da Aliyu ma gaba d'aya sun k'asa saida hawaye su Anty Halima kuwa cikin gida ta shiga tana kuka cur-cur,
Daddy kuwa yana zuwa ya d'auko goran ruwan mai sanyi ya dawo Abba ya mik'a wa,
yana karb'a ya b'alle marfin gorar sannan ya tuttulo ruwan sanyin a tafin hannun shi da k'arfi ya watsa a fuskar Usman d'in,
a take sai yayi wani irin ajiyan zuciya mai k'arfi sai kuma yayi shiru numfashi sa na harbaqa ,
cikin kuka Ammi ta rik'o hannun shi tana.
"Usman ! Usman! Usmaaaan!." sai kuma ta fashe da kuka,
Shi kuwa can sama-sama yake jin sautin kukan mahaifiyar shi da sauran yan uwa,
cikin tsananin mutuwa jiki ya bud'e idanun shi kuma sai ya lumshe su ganin baya ganin su sosai ,
su kuwa ganin haka yasa Ya Adam ya zaro woyarshi da sauri yace.
"Abba bari in kira Hamma Umar yazo ya duba shi."
jin hakan yasa Usman d'in ya k'ara bud'e idanun shi cikin rawan. Murya yace.
"Ah,Ah a a Adam kar ka gayawa Hamma Umar komai ka barshi ,
naji sauk'i."
meda woyar Adama yayi cikin jin dad'i ya kamashi ya rugume murya na rawa yace.
"Usman meyasa kake wasa da lafiyar ka me kake tunawa me damuwarka a duniyar nan Usman?."
cikin k'arfin hali ya d'an ture Adam sannan ya d'an jingina da jikin kujerar ya kamo hannun Ammin shi ya kalli Hajjajo da inna dake ta zubda k'ollah yace.
"Kai da Allah ni ku dena min kuka lafiyata lau ji tsoffin nan fa aini ras na ke sai namu rakiya kafin nima a min rakiya zuwa gidana na gaskiya,
Abba kace su dena kuka ni na worke."
Sai kuma ya kalli Ammin shi cikin sanyi yace.
"Ammi shi komai da kika gani a duniyar nan toh Rubutaccen al'amari ne so karki damu ki sawa ranki dangana insha Allah ba zakiyi kuka ba matukar Hamma Umar na yana raye,
karki damu shi d'aya ne tamkar da mu biyu kinji ko Ammi na."
kanshi ta shafa cikin rawan murya tace.
"Ku duk ina fatan ku rayu har bayan rayuwa ta."
dariya ya d'an yi sannan ya kalli Abba da Daddy dake binshi da ido cikin fidda numfashi mai nauyi yace .
"Dan Allah Abba kar a gayawa Hamma na kunga kar hankalin shi ya tashi."
Nenne ce ta kalleshi a hankali tace,
"Kasha maganin ka yau?."
Kai ya gyad'a mata sannan yace.
"Hamma Umar ya bani kafin ya tafi."
so haka yayi ta basu k'arfin guiwa ya kuwa hanasu su gayawa Umar,
a haka sukayi ta mishi nasiha kan shan maganin shi, sannan Abba yace daga

4 Comments On RUBUTACCEN ALAMARI
avatar
shukra-sulaiman

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
shuraihu

1 year ago

Reply

Replying to shukra-sulaiman

Tnx too

avatar
fatima-idris

1 year ago

Reply

Nice novel

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fatima-idris

Aha tnx

Please Login or Register in order to submit comment