Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da niyar zai jawo laptop d'in shi daya bari a wurin,
lalubawa yakeyi aman baiji inda laptop d'in yakeba dan d'akin yana da duhu gashi kan gadone mai rumfa duk yasha gyara da shimfid'a da labulaye sai ya k'ara duhun,
Ita kuwa Ummul tana ganin shi dan ita ta dad'e a d'akin so duhun yabi idonta shi kuma yanzu ya shigo d'akin shiyasa yake ganin duhun sosai,
tab'e fuska tayi cikin ko in kula tasa hannu ta turo laptop d'in nashi k'asa dai-dai sautin kan yatsunshi ta turo shi,
shi ko da sauri ya sunkuya da nufin yasa hannu ya taro laptop d'in kar ya kai k'asa gudun karta lalace,
amman ina cikin rashin sa'a ta fad'o kan yatsunshi tsinin aggil d'in jikin marfinta ya caki kan farcen babbar yatsarsa,
cakar da a take farcen ya tsage lokaci d'aya jini ya fara zuba a take k'afar ta fara wani irin b'ari dan azabar daya ratsashi gaba d'aya yatsar kuma sai motsi take kamar zata fice a jikin shi,
cikin wani irin azaba dayaji ya ziyarci k'ahon zuciyarshi ya dafe kanshi da k'arfi hannun shi sai rawa suke gaba d'aya jijiyoyin kanshi suka taso ida nunshi sukayi jazir ya kasa magana sai harshen shi ya d'an zaro ya rink'a d'an kad'awa yana furza numfashi tuni zufa ta keto mai ta sashoshin jikin sa,
harshen yake d'an kad'awa yana fidda sautin.
"Shihhhhhhhh ahhhhshhhhhh."
Sai kuma k'afar tashi daya d'an d'ago yana yarfawa,
Ita kuwa Ummul sai murmushi mugunta ta rink'a yi tanaji dariya nason kufce mata murmushin takeyi tuk'uru cikin jin dad'in azabtar dashi da tayi sai wani kad'a kai takeyi tana magana a ranta.
"Kad'an ma kaji Hamma Umar wannan shine makullin wahalar da zakasha a hannun na,
kaida azabtuwa kun kullah,
Sai kayi kuka cur-cur da hawaye ka sai ka gommace kid'i da karatu sai ka sakeni saki mafi muni wanda zan haramta maka har sai inna nasake wani auren an sakeni."

Kai ta jinjina taci gaba da maganar zuciyar da bata saniba na yanzun ya fito fili cewa take.
"Tabbacin da nake dashi ko ince yak'ini na sani Mustapha bazai sakeni ba har Abadan zamu rayu tare."

Da sauri Hamma Umar d'in ya bud'e idanun shi daya rumtse jin sautin Ummul d'in kan gadon ya tsurawa ido cikin wore idanun shi ,
fuskar ta ya tsare da ido cikin zafin nama ya mik'a hannushi kan gadon,
ita kuwa ganin haka tayi wani irin dira daga kan gadon a guje tayi woje a parlour ta samu ya Usman da su Hajjajo da Inna tare da Anty Halima da Anty Shuwa k'anwar Nenne,
cikin rawan jiki ta koma gefen ya Usman ta zauna cikin tura baki da tsuke fuska,
Anty Halima ce ta kalleta cikin tuhuma tace.
"Me kika aikata? kika fito a guje haka?."
fuska ta k'ara tsukewa sannan ta kalli Anty Shuwa dake ta danna mata harara cikin son yin kuka tace.
"Nayi ai ban sani bane."
Hajjajo ta bud'e baki zatayi magana kenan sai kuma tayi shiru ganin Hamma Umar d'in d'aya fito cikin d'akin nata ,
tafiya yake yana d'ingisa k'afar tashi duk inda ya taka sai jini dake zuba gaba d'aya jijiyoyin kanshi sun taso kanshi a k'asa yake tafiya hannushi rik'e da laptop d'in nashi yayinda d'aya hannun kuma yake rik'e da iPhone d'in shi,
Ya Usman ne da Anty Halima sukayi kanshi da sauri cikin rawan baki Ya Usman yace.
"Hamma Umar me ya fasama yatsa yaushe ya fashe kalli yadda jiki ke zubafa."
Anty Halima kuwa gaba d'aya jikin ta rawa yake ganin duk jini ya wonke mai k'afarsa cikin sanyi murya na rawa tace
"Hamma Umar a tsaida jinin nan mana ya dena zuba."

kai ya gyad'a musu cikin jarumta da dauriya ya nufi hanyar fita yana ce musu .
"Ba komai fa."
har yake bak'in k'ofar fita,
Hajjajo da Inna sukayi kanshi da sauri cikin kula da tsananin k'aunar jikan nasu suka kalleshi,
kusan a tare suke magana.
"Kai Farouq me ya fasama k'afar?
kayi magana kayi shiru ?."
kai ya jinjina a hankali yace.
"Tuntub'e nayi."
fad'in haka da yayi ne yasa suka rink'a jeromai "sannu-sannu Amman kaji azaba kam ai abinda ya fasa farce ba k'ara min abu bane."

Su tsoppin sun yarda Amman Anty Halima da Anty Shuwa kam sun gane sarai Ummul ce taji mai ciwon dan ganin yadda take zare ido da alamun rashin gaskiya Ita,
kuwa Ummul har cikin ranta take jin dad'in ciwon da taji mishi,
a wani sashin zuciyar ta kuwa tana mamakin yadda Hamma Umar d'in ya rufa mata asiri yak'i cewa Ita ta fasa mishi k'afar,
dan ta tabbaya d'aya fad'a Ita kuwa da ta shiga 9 nema ba 3 ba.

shi kuwa Hamma Umar ko inda take bai kallah ba ya fice yana d'ingisa k'afar,
ya Usman kuwa karb'a laptop d'in Hamman nashi yayi ya rik'e cikin raunin fuskar sa kamar zaiyi kuka dan tausayawa d'an uwan nashi,
har zasu fita ya juyo ya kalli Ummul d'in cikin raunin da yanayin tuhuma dan ya gane itace silar ciwon Hamman nashi,
itama kallon shi takeyi cikin sanyi ta rumtse idonta,
shi kuwa juyawa sukayi suka tafi.

Suna zuwa part d'in su Hamm Umar d'in yayiwa yatsar tashi dressing sannan yawa kanshi allurar ya kuma sha magani.

Ita kuwa Ummul suna fita Anty Shuwa da Anty Halima suka jata d'akin dake gefen na Hajjajo suka rink'a yi mata gyare-gyare tare da tsumata da irin tsumukansu na shuwa'arab ,
Anty Shuwa ce ta b'alle marfin wani roba sannan ta jijjiga tare da mik'ewa Ummul d'in cikin tsuke fuska tace.
"Karb'a ki shanye yanzu ki bani robar."

Kai Ummul d'in ta karya cikin kuka da gajiya da d'ure-d'uren da suke mata tace.
"Ni dai amai nakeji dan Allah a barni hakanan."

A fad'ace Anty Shuwa tace .
"Sai kinsha muguwar banza yadda kike mishi mugunta haka zai rama kiji tsoron mutumin da baya magana inya tashi ramawa zaki yabbawa aya zakinta."
kai Halima ta jinjina sannan tace .
"Gaya mata dai Anty wallahi wata rana zakiyi nadama abinda kikewa Hamma Umar d'in."

Haka suka rink'a yi mata fad'a da nasiha sunayi suna tsumata tare da dilketa da murjeta.

Haka nan kullum Sai sun murjeta sun tsumata,
ta fito tayi rasa sai wani shek'i take tamkar tarwad'a fatar jikinta kuma tamkar auduga komai nata yasha gyara sai wani k'amshin mai sanyi take fiddawa ko wucewa tayi k'amshin ta sai ya ratsa wurin
gashin kanta kuwa ba'a maganar gyaran d'aya sha, an gyareshi gyara na mussamman k'afafun ta da hannayen ta kuwa an musu zanen Lalle na mu samman komai na Ummul ya fito rasa ta fito a shuwa'arab d'in sak.


A gefen ago Hamma Umar kuwa ,
komai Ya Usman ne yake gudanarwa gaba d'aya ya gayyato abokon Hamma Umar d'in nashi ...

Yau ta kama Jumma haji babbar rana Wanda ya kasance gobe asabar ne za'ayi d'aurin aure Ummul da Hamma Umar .

Toh a rayuwar shuwa'arab akwai wata al'adar da sukeyi a duk lokacin da zasuyi bikin su ,
suna yin wannan al'adar tasune kamar gone za'a d'aura aure ,
kuma wannan al'adar tasu tana kunshe da wata al'adar kuwa Wanda a halin gaskiya a yanzu haka gaba d'aya shuwa'arab sunbar yin wannan al'adar ta biyun na farin dai sunyi Amman na biyun kam ,
a shuwa'arab d'in ma na zamanin yanzu da yawa basuma san al'adar ba dan tuni anbar yin al'adar duk da dai a zamanin da d'in ma a cikin aggwaye 100 da wuya a samu aggwaye 5 masu yin wannan al'adar domain al'adace mai nuni da d'auka alk'awari da kuma rik'o da amana suna kiran al'adar da sunan *Nad'in uwar gida*

So shiyasa aggwayen yanzu basa wannan al'adar ta biyun kenan fa,
Amman na farin kam har yanzu shuwa'arab sunyi kuma in an gama na farinne akeyin na biyun,
so Yau jumma'a tun safe aketa shirin wannan al'adar tasu na. farin wanda dama asan dashi shi kuwa na biyu ba wanda yake da tabbacin za'ayishi a cikin shuwanma wasu basu san da wannan ba,
tun safe aka k'afa tantuna a harabar gidan nasu aka shimfid'a kilisai na al'farma aka ajiye kujera na gani na fad'a kujera masu taushi gaba d'aya an zagaye wurin da kolliyoyin zamani tare dana al'adun shuwa'arab d'in,
cikin kujerun kuwa a tsakiyar kujerun akwai na aggo da amarya wanda sunayen su ke rubuce a Kansu sai na k'awayen Amarya da abokin aggo suma duk sunayen su na rubuce akan kujerun nasu.

Yadda ake al'adar tasu kuwa bayan an gama kimtsa wurin aggo zai fara zuwaya zauna da zugar abokan shi sai bayan ya zauna da mintuna kad'an sai a fito da amarya,
fito da amaryarna kuma 'Yar uwar amaryar ce ta jini zata fito da amariyar rik'e da hannun ta ,
sai ta mik'a hannun amariyar ga hannun y'ar uwar aggo ko d'an uwan aggon,
daga nan sai shiko d'an uwanshi ago yaja hannun Amarya ya kaita kusa da aggon ya ajiyeta,
so y'an uwa da abokin arzik'i zasu tashi sunyi ta yiwa Amarya lik'in kud'i da gudumowowinsu,
bayan duk an gama lik'inne sai shi kuwa aggo ya tashi yayi nashi lik'in,
shike nan itace al'adar su ta farin .


So haka aka tsaba wannan al'adar bayan an sauk'o sallan jumma'a Hamma Umar da abokanshi duk suka dawo gidan suka d'an huta sannan matayen su kuwa suna cikin gida ,
bayan anyi sallan la'asarne sannan aka fara shirin fita wurin taron,
abokon Hamma Umar manyane masu cikar kamala abokai ne daku masu karatu kun sansu haka kuwa matayen su,
haka sukayi shiga ta al'farma shiga irin ta shuwa'arab d'in sukayi baki d'ayan su suka fito rasa tamkar larabawa,
Suma matayen su da k'awayen Amarya Ummul shiga sukayi ta shuwa'arab d'in gaba d'ayan su laffaya suka yane jikin su dashi suma dama gasu kyawawa. Haka yasa wurin taron ya zama tamkar a k'asar larabane ,
wani abin burgewa kuwa duk woni sak'o da luggu har cikin fulawowi na gidan an ajiye kaskon turaren wuta sai wani irin k'amshin ke tashi hakan yasa nishad'i a zuk'atan duk wani bani adam dake zaune a wurin.


5:00 pm zugar ago da abokanshi suka ido farfajiyar gidan Ya Usman ne a gaba yayinda sauran abokon ke binshi a baya ,
Hamma Umar kuwa yana tsakiyar su yasha sutura ta al'farma ya fito cikin haiba da cikar zati sajenshi sai wani irin shek'i yakeyi farar fatarshi ta fito ras tamkar balarabe sumar kanshi kuwa. yayi luf gwanin sha'awa ya murza hula a kan nashi yayinda gashin nashi yabi k'eyarshi da zagayen fuskar shi,
idanun shi kuwa wani d'an siririn glass ne mai haske irin na Doctors ke manner a fuskar sa.

dai-dai lokacin da suka fito a dai-dai lokacin kuma matayen abokan aggon suna suka fito ,
gaba d'aya wani taku suke a jere kamar yadda kujerun ke Jere kowa da matarsa a gefen Hamma Umar ne ya fara zama sai babban abokin shi ,
Hamma Yusuf da Ayshar sa sai Hamma Hassan da Fateemar shi sai kuma. Hamma Bashir da Ruk'ayyar shi
Sai Hamma Mahmoud da Khadija shi sai kuma Hamma Aliyu Haydar tare da Minalin shi,
A d'aya gefen kuwa
wasu manyan abokan Hamma Umar d'in na gani da matayen su, Amadi da Nadiyar shi,
sai Abuturrab da Batul d'in shi sai kuma Salim da Tawa
Sai Abdullahi tare da Maryam d'in shi,
daga gefen su kuwa Fauziyya ce da Al'ameen sai Aisar tare da
Bintun shi
sai kuma Abbah da Ruky pinkyn shi,
ga kuma Ridwan da Zakiyya
can kuma kusa dasu Ahmad Ana Muslim ne tare da khadijan shi
sai kuma Assadiq da Safiyyar shi tare Hibbah da Faheem.

Gaba d'aya sun zauna cikin nitsuwa da al'farma suna zaune cikin cikar haiba sun fito tamkar taurari sai shek'i sukeyi da wani irin k'amshin da suke zubawa zamane sukayi na masoyan gaske.

Bayan sun zauna da kamar minti 5 Dangi da k'awayen Amarya da sauran mutane sukazo suka zauna,
cikin nitsuwa da lumana,
Jim kad'an,
suka fara jiyo wani irin k'amshin na k'ara ratsa hancin su gaba d'aya sai wani irin shauk'i ya ziyar cesu ido suka lumshe tare da jin dad'in k'amshin dake k'ara bud'e su wanda Anty shuwace ke rik'e da kaskon turaren wuta,
Anty Halima kuwa na biye da Ita a baya tana rik'e da hannun Ummul wacce tasha gyara iya gyara an yaneta cikin laffaya mai tsadar gaske ta fito a shuwa'arab d'in sak ta fito tamkar tauraruwar zarah dake kusa da wata,
Anty Halima na rik'e da hannun ta suka iso farfajiyar gidan yayinda ita kuwa Ummul kanta ke sunkuye idanun ta na zubda wasu irin wahaye masu zafi da tafasa zuciya tafiya takeyi tamkar hawainiya,
suna isowa Ya Usman ya mik'e cikin happy yaje gabansu ya tsaya cikin wani irin salon al'darsu ya d'an kife guiwarsa d'aya a k'asa sannan ya d'an d'ago hannunsh sama kad'an ya ware tafin hannushi cikin sanyi yace.
"Halima samin hannun matar Hamma na cikin tafin hannuna ni zan kaiwa Hamman matarsa kusa dashi."

murmushi Anty Halima tayi tare da kamo hannun Ummul d'in ta d'aura cikin tafin hannushi,
wani irin nanauyan ajiyan zuciya ya sauk'e tare da
rumtse idonshi da k'arfin,
yatsun hannushi ya cusa cikin nata ya rik'o hannun ta sannan ya mik'e tsaye ya fara taku a hankali itama Ummul takun takeyi tamkar hawainiya a haka har suka isa gaban kujerar da zai zaunar da ita suna zuwa ya kamo kafad'unta ya juyota tana fuskantar shi yayinda ta bawa kujerar baya,
cikin sanyi ya zaunar da Ita kan kujerar dake manne data Hamma Umar,
a hankali ya fara tasowa daga sunkuye da yayi a kanta,
Ita kuwa Ummul kanta ta kuma sunkuyarwa tare da sakin wani narkekken sautin kuka can k'asa,
Sai kuma tayi shiru cikin sauri ta d'ago kanta tana kallon Ya Usman d'in nata jin kamar y'an watsa mata ruwa,
abin mamaki da Ummul ta gani ba ruwan bane ya Usman ke watsa mata ,
Hawaye ne ke bin fuskar sa har yana diga cikin tafin hannun ta ,
ido ta zuba mai cikin yanayin tabbaya da tsantsar. mamaki a fuskar ta,
shi kuwa cikin jarumta yasa tafin hannushi ya goge k'ollah dake zuba a idanun shi,
murya na rawa yayi murmushin da yafi kuka k'una a zuciya murya can k'asa yace mata.
"Allah ya d'aiyiba."
itama murmushi tayi cikin zubda k'olloh murya a disashe tace.
"Ya Usman ina son ka".
ido ya lumshe da sauri cikin raunin murya yace.
" Ummul nima ina sooonki."
Ido Ummul kam ta kuma rumtsewa dan tasan ba haka suka saba cewa juna ba,
Ita tasan in tace mai ya Usman ina sonka shiko sai yace Allah ya d'aiyiba Amman Yau kuma shima sai yace mata "Ummul nima ina sooonki " a madadin yace Allah ya d'aiyiba Sannan ga hawaye dake bin fuskarsa,
tana cikin nazarin ne taji ya fara yi mata lik'in da Sabin kud'i na gudan dubu-dubu'
gaba d'aya wuri aka fara tafi marok'a na .
"Kaji k'anin aggo Usman d'an Maliki mai ruwan nare."
lik'in sosai Ya Usman yayi mata yanayi yana zubda k'olloh cur-cur sai yasa tafin hannushi yana gogewa ganin haka yasa Ummul tayi murmushi cikin d'an d'aga murya kad'an yadda zai iya jinta tace.
"Allah ya d'aiyiba min ya Usman dina."
jin haka sai ya rink'a murmushi tare da kallon fuskar ta,
a haka ya gama yi mata lik'in sannan Ya Adam da ya Sadik tare da Aliyu auta suma suka shigo sukayi mata lik'in ,
daga nan manyan abokan Aggo kuma jarumai suma suka fito sukayi lik'in ban girma,
daga nan y'an uwa da abokan arzik'i sukayi nasu. lik'in,
bayan duk an gama kowa ya koma mazaunin shi wuri yayi haske,
cikin wani irin yanayi Hamma Umar d'in ya mik'e tare da juyowa gaban Ummul d'in sannan kanshi a sunkuye cikin sanyin muryar shi ya kalli marok'an yace.
"Ku shaidawa Jama'a yanzu zanyiwa Ummul lik'in ne a matsayina,
na babban Yayanta d'an uwanta."
aiko a take marok'an nan suka rink'a shela suna fad'in.
"Aggo yace a shaida muku yanzu zaiyi lik'in ga Amarya a matsayin shi na babban yayanta kuma d'an uwanta."
gaba d'aya sai wuri ya ciki da shauk'i ,
abokan Hamma Umar da matan su sai murmushi suke,
shi kuwa Hamma Umar lik'in kawai yake mata da rafa-rafa na dubu-dubu,
haka ya rink'a zubawa Ummul kud'i tamkar ruwan sama,
bayan ya gama ne sai ya kuma komawa kan kujera ya zauna,
sannan k'awayen Amarya suka rink'a tattara kud'ad'en.

Bayan sun gama ne Hamma Umar d'in ya sake tashi tsaye cikin cikar haiba da kamala gaban Ummul d'in ya kuma tsayawa cikin k'asaita yace.
"Yanzu a matsayin aggo zanyi lik'in."
marok'an ko tuni suka cika wurin da kirari suna.
"Ummaru sand'a babuga mai nera Ummaru mai ado da zinari Ummaru Farouq mai K'amshin al'miski
kunji Umaru Farouq babban adali doctor mai tausayi da jink'ai."

Shi kuwa Hamma Umar Dolas ya zaro ya rink'a yiwa Ummul b'arinsu a kanta,
Ya Usman kuma na tsaye a gefen shi rik'e da turaren mai suna *du'a'ul jannarh* mai tsananin k'amshin,
bayan Hamma Umar ya gama lik'in sai ya kuma mik'a hannu ya karb'i turaren dake hannun Ya Usman,
sannan ya d'an sunkuyo kan Ummul d'in ciki kallon fuskar ta ya fara fesa mata turaren yanayi yana k'ara matsota har ya isa gab da Ita sannan ya mik'ewa Usman turaren ,
a hankali ya rokk'fo gaban ta sannan ya sunkuye dai-dai kanta,
mutanen wurin kuwa gaba dayasun maida hankalin su sukayi kan Hamma Umar d'in domin son ganin me zai aika ta,
Hajjajo kuwa da Inna tuni sun fara mamakin abinda Umar d'in yake shirin aika tawa,
sauran mutane kuma gaba d'aya kallon shi suke cikin tarin mamaki dan gano abinda yake shirin aika tawa,
Ammin kuwa lokaci d'aya taji wasu siraran hawaye na bin fuskata tana kallon Abin da Babban d'an nata zaiyi,
Abokan Hamma Umar kuwa ido suka zuba mai cikin mamaki su Hamma Yusuf duk an cika da mamaki sai k'ara rik'e hannun Ayshan sa yake.


Itako Ummul gaba d'aya jikin ta sai kerma yake ido kawai ta zubawa Hamma Umar d'in fuskar ta cike da k'olloh,
Nenne ma ido ta zuba mishi dan gano abinda zaiyi.

Shi kuwa Hamma Umar cikin wani irin yanayi yasa hannushi ya cire hular kanshi sannan ya k'ara sunku yowa kan Ummul d'in tare da manna....





By
*GARKUWAR FULANI*
婵☆偓绲介崯顖炲箟椤愶綇绱旈柛鎰╁妿閿涙挸螞閿濆懎鏆欑痪鎹愭珪閿涘啴宕橀妸褝绱︽俊顐到閸燁偆澹曢搹顐磾闁告劑鍔庨敍鎾澄涢敐鍛殭缁炬崘娅曢敍鍐礃閵娧嶇处婵☆偓绲介崯顐ゅ閿燂拷

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 1闂備焦鍓氶悡澶愬箯閿燂拷2闂備焦鍓氶悡澶愬箯閿燂拷

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

婵☆偓绲介崯顐ゅ閾忣偓绱旈柛鎰╁妿閿涙挸螞閿濆懎鏆欑痪鎹愭珪閿涘啴宕橀妸褝绱︽俊顐到閸燁偆澹曢搹顐磾闁告劑鍔庨敍鎾澄涢敐鍛殭缁炬崘娅曢敍鍐礃閵娧嶇处婵☆偓绲介崯顐ゅ閿燂拷









*H*ularshi ya cire daga kanshi sannan ya kuma sunkuyowa kanta,
yayin da gaba d'aya mutanen wurin kuwa suka zuba mai idanu,
shi kuwa Hamma Umar kanshi a sunkuye cikin lumshe ido ya manna mata hular tashi a kanta sannan yasa hannu biyu ya dai-dai ta zaman hular a kan Ummul d'in hular tayi ras,
ita ko Ummul ido ta zaro cikin tarin firgici gano cewa Hamma Umar al'adarsu ta biyun zaiyi a take zuciyarta ta rink'a buga wa a saba'in,
Ammin shi kuwa sai murmushi take a ranta tana al'fahari da d'an nata,
Abokan Hamma Umar kuwa kallon shi suke cikin sha'awa da burgewa,
Ya Usman kuwa k'irjin shi ya dafe da k'arfi sannan yasa hannun shi d'aya ya damk'o hannun abokin shi Nuru dake zaune kusa dashi a sashin zuciyar sa kuwa yana al'fahari da hallaci irin na Hamma Umar d'in nashi yana jin dad'in yadda a gaban dubban al'ummah zaiyi al'k'awarin da d'aukar amana,
Shi kuwa Hamma Umar bayan ya gyara zaman hulan nashi a kanta sai ya kuma sa yatsunsa biyu ya zaro siririn gilashin dake manne a fuskarsa cikin lumshe ido ya kuma mannawa Ummul gilashin tare da ajiyeshi ras a fuskarta ,
ita ko Ummul zuwa yanzu hawayen ta tuni suke d'iga kan tafin hannun ta tol-tol,
ganin haka yasa cikin furza sassauk'an numfashi Hamma Umar d'in ya d'an rok'k'ofo ya zauna gabanta suna fuskantar juna zama yayi dirsham a gabanta ya tok'k'oshe k'afafun shi sannan ya had'e guiwowin sa,
A hankali ya sunkuyo kanshi yana kallon k'afafun ta da su kasha zane ,
hannun shi yasa a hankali ya d'ago k'afafun nata sannan ya zare takal manta ya ajiye gefe cikin kula ya tallab'o k'afafun nata da tafin hannun shi cikin tabbacin abinda zaiyi ya d'ago k'afafun nata ya diresu kan guiwowin shi sannan ya had'a yatsun k'afafun ya rik'e yana d'an matsawa kamar mayi mata tausa sai kuma ya sunkuyar da kanshi cikin yanayin bugawar zuciya dan tabbas yasan hakan da yayi d'aukan babban al'k'awarine firgincin dake ranshi shin ko zai iya cika al'k'awarin da ya d'auka?,
mutanen wurin kuwa gaba d'aya aka kaure da tafi maroka na gud'a cikin yin kirari ga aggo Umar Farouq,
dan ba wanda yayi tunanin Hamma Umar zaiyi wannan abun,
Hajjajo kuwa hamadala ta rinkayi cikin jin dad'i Inna kuwa sai k'ollah dake bin fuskata a fili tace.
"Farouq na Allah
Umar Farouq adon gari Farouq mai zuciyar taimako Allah ya baka ikon cika wannan al'k'awarin da ka daukarwa kanka."

Anty Halima kuwa da Anty Shuwa
farin cikin su baya fad'uwa ita kuwa Nenne kuka takeyi sosai a ranta tana ganin al'barkacin sune ita da Abba Ummul ta samu wannan karramawar a gun Hamma Umar d'in,
Matar yayan Ammin Anty Nafeesat ce ta kalli Hajjajo dake gefen ta cikin mamaki tace.
" Hajjajo me Wannan abinda Umar yayi yake nufi?."
Murmushi Hajjajo tayi cikin al'fahari da jikan nata, ta kalli Anty Nafeesat tace.
"Anty Nafeesat Wannan abin da Farouq yayi shi muke kira da nad'in uwar gida sannan mutu ka raba ,
Anty Nafeesat wannan abin da yayi d'aukar al'k'awarine mai k'arfin gaske na rik'e mace da amana da gaskiya."
Numfa sawa Hajjajo tayi tare da ciga da cewa.
"Anty Nafeesat idan namiji yayi wannan abin toh ya d'aukarwa kansa indan zai kashewa kansa dubu 50 toh zai kashewa matarsa dubu 100 ninkin ba nashi kenan kuma ba abinda zaici ba tare d'aya ciyar da matarsa ba kodako tsagin dabino ne sannan ya bata matsayin sarauniya shin ki kalli yadda yake zaune a gabanta mana kuma ya d'ora k'afafun ta a kashi tamkar itace sarauniyar shi."
Kai Anty Nafeesat ta jinjina cikin jin dad'in abin tace.
"Allah ya bashi ikon cika alkhairi."
"Amin Amin."
Hajjajo da Inna suka amsa.

Tafi da sowan da mutane keyi da al'k'awarin da Hamma Umar ya d'auka su suka kara cushe zuciyar Ummul dan ganin duk Hamma Umar ya saye zuk'atan mutanen wurin ita kuwa zuciyar ta tamkar ta fashe dan tsabar tsanar Hamma Umar d'in sai wani irin kuka ta saki mai cin rai,
shi kuwa Hamma Umar ba abin da ya fad'o mishi a ranshi sai tunanin mahaifinshi dan al'adarta su ana gamawa aggo zai wuce gun maihaifin shine dan ya samishi albarka da addu'ar Allah ya tayashi rik'o,
tunanin shi a yanzu shi gashi yayi al'k'awarin Amman bayida mahaifi a duniya bare ya samishi albarka ya kuma tayashi Addu'ar Allah ya taya shi rik'o,
tuno hakan ne yasa rauni a zuciyar Hamma Umar ta yadda lokaci d'aya hawaye ya b'allo a fuskarsa hawaye ne ke zuba cur-cur dan tuno mahaifinshi ,
zuba hawaye suke har kan k'afafun Ummul dake kan guiwowin sa,
kuka yake cikin raunin sautin da ba wanda ke jinshi sai ita Ummul d'in da yake zaune a gabanta sai kuma Ya Usman da ya haggo hawaye na bin fuskar B'iyayen nashi,
Ammi ma dake zaune gefen a lokacin tunanin mijinta ya dawo mata yau gashi ana bikin babban dansu amman ba mahaifin su Allah bai nuna mishi ba sai ita kad'ai,
itama sai kuka,
Ya Adam kuwa dake tsaye gefen Hamma Umar ya fara jin sheshshek'ar Hamman nasu tuni shima hawaye ya fara bin fuskarsa,
Abokan Hamma Umar kuwa tasowa sukayi suka rink'a yi mishi liki,
Ya Usman kuwa tuni zuciyar shi take harbawa hakan yasa ya sake hannun Nuru ya nufi gun Hamma Umar d'in nashi,
shiko Nuru da sauri ya mik'e yabi bayan Usman din yana.
"Usman anya kuwa yau kasha maganin ka kuwa? jikin ka ko?
Usman kana wasa da lafiyar ka fa wato yau Hamma Umar yana cikin baki bai samu ya baka maganin kaba shine kai kuma bazaka iya shaba sai ya baka?."
cikin rawan murya fuska cike da k'ollah Ya Usman yace.
"A a Nuru a,a Hamma na ya bani maganin nasha ,
Hama Umar baya manta bani maganin duk hidamar da yake ciki,
Nuru kalli Hamma Umar na yana kuka da hawaye Nuru sake ni naje kusa da B'iyaye na,
Nuru Hamma Umar baya barin hawaye ya zuba a idanuna ,.Nuru ya za'ayi niko na k'asa tsaida nashi hawaye ?."

cikin tausayin su Nuru ya sake mishi hannun shi,
shi kuwa Usman kutsawa yayi cikin mutane yana zuwa ya durk'usa gefen Hamma Umar d'in daketa kuka hannun Usman yasa ya rik'o na Umar d'in cikin kuka yace.
"Kai tona

4 Comments On RUBUTACCEN ALAMARI
avatar
shukra-sulaiman

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
shuraihu

1 year ago

Reply

Replying to shukra-sulaiman

Tnx too

avatar
fatima-idris

1 year ago

Reply

Nice novel

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fatima-idris

Aha tnx

Please Login or Register in order to submit comment