Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gigice ta yunk'uro cikin rawan jiki ta sa hannu ta dam k'o....





By
*GARKUWAR FULANI*
[6:47AM, 9/20/2017] ‪+234 706 196 7803‬: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL'AMARI*

Page 5⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇





*Wannan shafi naki ne k'awata ta gari Ngd da k'aunar ki gareni Hauwa Halliru (Mmn khairat) Allah bar zumunci da k'aunar Ngd Ngd Ngd 🤝😘😍*





Hannun shi cikin wahala da gala baita ta ture hannun taci gaba da murk'ususu tana yarfa hannu da juya kai,
duk da sanyin a/c dake ratsa d'akin ita zuface keta tsatstsafo mata duk ta inda hudan gashin jikin ta yake,
tsayuwa yayi tare da tsuke fuska kai ya jinjina ya fice abin shi,
Parlour Hajjajo ya nufa,
sallama yayi tare da shiga gefen Abba ya zauna kanshi a sunkuye yace.
"Abba tak'i ta tsaya in dubata sai kuka take yi."

Nenne ta kalli Abba tare da cewa
"Toh ai kunji ko mara lafiya da gardama,
yoh ba sai abarta da ciwon taba,
ai bai dameta bane da ita zata nemi maganin".
Daddy ne ya mik'e tare da Hajjajo Ya Usman da Ya Adam na biye da su a baya har sunje bak'in k'afar Daddy ya juyo ya kalli Dr Umar Farouq d'in cikin murmushi dan yasan Umar ya hatsala ne,
murmushi yayi kumayi sannan yace.
" Farouq zo muje ka dubata ko."

Kai ya kuma sunkuyar wa cikin yana yinshi na girmamawa ya mik'e yabi bayan su,
Nenne ma da Abba da Aliyu biyosu sukayi.

Suna zuwa Parlour Nenne Daddy ya zauna tare da d'an d'aga murya yace.
"Ummul kizo nan,
taso kizo ko mamana,
kizo Hamman ku ya dubaki."


Jin muryar Daddy ne yasa ta k'ara sakin kuka dan tasan Daddy yana matuk'ar k'aunar ta da lallab'ata,

Jin ta fashe da kukan ne Hamma Umar ya zauna kan carpet a gefen Daddy a hankali yayi tsaki,
Usman kuwa da Hajjajo cikin bedroom d'in suka wuce suna zuwa,
Hajjajo ta zauna gefen ta cikin sauri ganin yadda take kuka da juyi gaba d'aya fuskarta tayi jazazir sai zuba da ya mik'a jikinta kab sai numfashi take a wahalce,
da sauri ta rik'o ta cikin kid'ima take kiranta.
"Subahannalhai Ummul me yake damun ki haka? yaushe ya fara miki wannan ciwon ?."

Kanta ta kuma kifewa kam pillow cikin cije lips d'in ta ta junk'ura ta zauna gaba d'aya jikinta rawa yakeyi hannu ta rink'a damk'e wa baki na rawa tace.
"Marata zata b'alle jiri nakeji cikina k'uguna yana sarawa."

A kid'ime Hajjajo ta kamota tsayar da ita tayi tare da talla beta cikin tattaro k'arfinta tace.
"wannan wanne irin ciwone kamar maiyin nak'uda."

A haka suka nufi parlour Usman kuwa na biye dasu a baya gaba d'aya tausayin ta ya cika shi ya kasa komai sai.
sannu yake ce mata.

Kan 3 str Hajjajo ta kontar da ita .

Nenne kuwa gaba d'aya jikin ta sai ya kama rawa ganin yadda yartata ta birkice.
gaba d'aya sai sannu suke ce mata,
abu kamar nak'uda duk ta galabai ta,
Abba ne ya kalli Hamma Umar d'in tare da cewa.
"Farouq me haka kuma? meke damun ta.?"

Juyawa yayi gaban ta ya d'an taso ya tirk'usa kan giiwarsa sannan ya kalleta cikin tsura mata ido yace.
"Ki nitsu ki gaya min ina ke miki ciwo."

Kai ta jinjina a wahalce.

Shi kuwa kai ya d'an sunkuyar sannan yace.
"Meke damun ki?."

"Cikina da marata."

"Yaushe ya fara miki ciwon?."

"Tunda yamma."

Kallon ta ya d'an yi sannan yace.
"Cikin da matar kad'ai ne ke ciwon?."

Dafe k'ugunta tayi murya na rawa tace.
"Harda k'uguna yana sarawa kamar zai b'alle."

Harararta yayi k'asa-k'asa tare da tsuke fuska yace.
"Karki cika min kunne da kuka in zaki magana kimin yadda zan gane kin sani sarai bana son hayaniya."

Usman ne ya d'an matso tare dasa d'an kwalinta ya goge mata zufan ya kuma d'an kalli Hamman nashi a hankali yace.
"Hamma meke damun ta?."

Ya fad'a shima kamar zaiyi kuka

Shi kuwa fuska ya kuma tsukewa yace.

"Dama kina irin wannan ciwon ne?."

Kai ta gyad'a alamar ehh.

Juyawa ya d'an yi kanta sannan yace.
"Bak'in ki bazai iya magana bane? ko kuma kin zama kurma?."

"Ehh dama yana min."

Ta fad'a a hankali.

"Sau nawa ya tab'a yi miki hakan?."

Ido ta rumtse cikin jin kunya tace.
"Ko wanne wata sai yamin haka."

Baki ya tab'e dan gano matsalar ta,
Hajjajo ma da Nenne sun gano abin da ke sata hakan shiyasa sukayi shiru suna kallon ta.

Shi kuwa Hamma Umar kamar cikin mugunta yace.
"Allurai 3 za ayi miki."

Jin allurai har 3 yasa ta zaro ido woje cikin rawan murya tace.
"Ni dai a barni da ciwona zuwa gobe zai bari,
dan Allah Hamma kar kamin allura."

Daddy kuwa da Abba Umar suka ni da ido cikin yana yin tabbaya suka tsareshi da tabbayarki me yake sata ciwon .

Shi kuwa Hamma Umar mutun ne mai tsananin kunya hakan yasa gaba d'aya sai ya resa ya zaiyi musu baya min ciwon nata.


Sai ya kalli Ummul d'in cikin lumshe ido yace.
"Ke me yake saki ciwon? kinaji ana tabbaya kinyi shiru,
ko kina jiran ni zan amsa miki ne?."

Kai ta sunkuyar cikin tsananin kunya da wahala sai hawaye car-car a fuskarta.

Shi kuwa Hamma Umar ganin su Abba sun maida hankalin su kanta,
yasa yayi maza ya zille ya fita.

Part d'in su ya nufa yana zuwa ya had'a alluran da zai mata sannan ya ajiye cikin firij woyarshi ya zaro tare da kiran Nenne tana d'agawa yace.

"Nenne Ummul d'in tazo zan mata allurar,
tazo da sauri dan akwai masu jirana a woje zan fita gunsu."


toh Nenne tace.
sannan tasa Ummul d'in ta mik'e ta fita badon ta soba.

Shi kuwa zama yayi ya d'an jirata,
ganin shiru bata shigoba ya mik'e ya shiga toilet wonka yayi sannan ya fito daure da towel a k'ugunshi,
parlour ya fito da nufin ya d'aukam woyarshi ya sake kiran Nenne.

Ita kuwa Ummul a daddafe ta shigo parlour tana shiga yana shigowa shima.

Ganin ta a tsaye ya sashi juyawa da sauri ya koma cikin bedroom d'in,
tsaki yaja sannan ya kimtsa tare da fesa turare a jikin shi.

Parlour ya dawo yana watsa mata harara,
ita kuwa Ummul batama ganshi ba lokacin da ya fito d'in haka yasa bayan san abinda yakewa harara da tsakin ba.


Bayan ta ya zagaya rigar ta ya d'an nad'e sannan ya d'an yi k'asa da zanin ta,
ba tare da ya ture farin ondawunyan ta da pan d'in tabaya dire bakin alluran a kansu,
dan shi haka yake matukar zai yiwa mutun allura mace ko namiji ba tab'a yarfa ya kalli fatar jikin mutun dai-dai yayi alluran a kan gajeron wonddon mutun inko mave ce kan siket d da pan d'in yake d'aura allurar.

Tana jin yana murza bak'in alluran sai kuma ya tsaya cikin fad'a yace.
"Ke ki sake jikin ki uwar tsoro allurace ba mashi ba kike wani Kane jikin ki,
kuma d'aga yau karki sake shigo min d'aki tunda baki iya sallama ba,
ki bari sai randa kika koti sallama."

Ita dai kai kawai take gyad'awa da rumtse tafin hannun ta.

K'ara ta d'an saki tare dasa hannun ta ta baya ta kamo k'ugunshi ta rik'e da k'arfi ido ta rumtse jin yadda ya zirnik'a mata allurar,
k'ara damk'e shi tayi dan yadda taji zafin yadda ruwan allurar ke shiga jikin ta.

Shiko Hamma Umar da sauri ya zare allurar sannan ya janye hannun ta dake kan k'ugunshi kan mazaunanta ya dire mata hannayen nata sannan ya tura ta murya a fad'ace yace.
"B'acemin da gani,
sokuwa kawai ba abinda kika iya sai koke-koke banza kawai duk kin cika min kunne."

Ita kam Ummul tuni ta koma gefen ta jingina da jikin kujera dan jiri take ji ga wani irin suka da taji k'ugunta nayi lokaci d'aya kuma taji d'umin jini na bin k'afafun ta.

Ido Hamma Umar ya zaro mata tare da buga mata tsawa fuska a yatsine yace.
"Fice min a d'aki kina tsaya har saidakika zubar min da k'azan tarki ,
ubanwa zai goge miki wannan abin."

Ya fad'a yana nuna jinin dake bin k'afafun ta a take kuma rumtse ido yana yamutsa fuska cikin fad'a yayi kanta.

Dai-dai lokacin Usman kuma ya shigo.

Da sauri yaje gaban ta cikin kula ya kamo hannun ta kai ya lok'osa a kafad'an shi cikin sanyi yace.
"Hamma kayi hak'uri ni zan gyara wurin."

tsaki yaja sannan ya fice yana cewa.
"Wallahi ka gyara wurin kafin na dawo ita kuma ta bar nan."

Yana fita Usman ya kalleta a hankali yace .
"Kije cikin gida."

A kunyace ta fice ta nufi parlour Nenne .

Shi kuwa Usman gyara wurin yayi tsab sannan ya feffesa turare.

Yana gama wa Hamma Umar d'in ya shigo rik'e da magungunan shi,
kan kujera ya zauna sannan ya bashi maganin,
d'aga nan kuma suka yita hirarsu tare da Ya Adam da Sadik da suka shigo.

Ita kuwa Ummul kai tsaye toilet ta shige wonka tayi ta kimtsa jikin ta sannan tazo ta konta kusa da Nenne ta,
a hankali Nenne tace.
"Ummul yanzu duk wata haka like gama da wannan ciwon cikin?."

"Ehh " tace mata tare da lumshe ido dan kunya takeji.


A khana a tashi haka rayuwa tayi ta juyawa shak'uwa tsakanin Usman da Ummul kullum k'aruwa yake yi
zuroyarsu cike da farin ciki.

Nasu da wata matsala Sai matsalar ciwon Usman da Ummul,
wasa-wasa ko wanne wota Ummul sai ta galabai ta abin yaci tsura tasha magunguna da allurai har tagaji a banza.

Abba kuwa ya matsala Nenne da tabbayarshin dama haka ko wacce mace take fuskantar wannan matsalar ne yayin yin al'adarta.
Nenne takan ce mishi .
"Insha Allah in tayi aure zai bari."

A haka suka bar maganar.

Sai yau kuwa tunda gari ya waye Ummul ta tashi da. ciwon ciki da matar ga sarawar da k'ugunta keyi.

Kasan cewa Hamma Umar baya gida yana cikin Damaturu yasa Abba ya d'auketa shida Nenne suka kaita jama'a clinic kasan cewa doctor abokin Hamma Umar ne.

Gwajin forko da doctor yayi ya gane matsalar ta,
cikin girmamawa doctor yayiwa Abba baya nin ciwon nata ya kuma k'ara da cewa.
"Abba dama akan samu wasu matan da irin wannan larurar,
maganar gaskiya duk magungunan da za'a bata ko allurai duk aikin banza ne mafita d'ayace wacce zata rabata da ciwon nan da izinin Allah muddin akayi mata aure ta mu'amalantu da zaman takewar aure toh insha Allah zata rabu da ciwon nan."

Cikin kad'uwa Abba yace toh,
"Doctor menene mafita?."


Ajiyan zuciya ya sauk'e tare da cewa .
"Mafitar dai itace ayi mata aure kawai."

Da wannan shawarar Abba ya koma gida tare da Nenne Ita kuwa Ummul bata san abinda ke wakana ba.

Sai fama da takeyi da ciwon ta.

Bayan kwana biyu Abba ya kira Hussain shi suka zauna a d'akin Hajjajo suka tattauna kan maganar Ummul su yasu suka gama maganarsu
ba and a yasan abinda suka zantar.


Yau jumma'a tun safe Ummul keta gyare-gyare da girkr-girke dan yau Habeebin ta Mustapha yana kan hanyarshi ta zuwa,
4:15 pm Mustapha ya iso,
yana isowa Abba da Hamma Umar suka shigowa,
da sauri Mustapha yayi parking ya fito ya nufi su Abba yana zuwa kusa dasu,yayi sauri ya....




By
*GARKUWAR FULANI*














📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 6⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



Ya tsugana gaban Abba cikin girmamawa irin ta tsurkai ya yace.
"Barka da dawo Abba."

"Barka dai Mustapha ya hanya?."
"Alhamudulallah Abba."
"Masha Allah ,
taso ka isa daga ciki ko."
Mik'ewa yayi cikin kunya tare da d'an murmushi a fuskar sa,
gaban Hama Umar ya matso cikin sakin fuska ya mik'a mishi hannu.
Shima Hamma Umar d'in d'an gajeren murmushi yayi tare da mik'o hannunshi suka gaisa.
Abbanne ya kalli Hamma Umar d'in tare da cewa.
"Farouq isar dashi parlour ciki."

"Toh" yace sannan yayi gaba Mustapha na biye dashi a baya.

Shi kuwa Abba part d'in shi ya nufa.

Suna zuwa Umar ya kalli Mustapha a fakaice yace.
"Ka isa ni zanyi cikin gida."

"Toh nagode Hamma Umar Allah bar girma."
"Amin" yace a tak'aice sannan ya fita ,
cikin gida ya wuce parlour Hajjajo ya nufa,
yana zuwa yayi sallama jin shiru ba wanda ya amsa yasashi shigowa a hankali,
parlour ba kowa,
kan 2. str ya zauna tare da dan jingina jikin kujarar ido ya lumshe yana mai fidda numfashi a hankali,
Hajjajo ce ta fito parlour hannun ta rik'e da carbi ido ta d'an zare tare da cewa.
"Kai Umaru yashe ka shigo?."

"Yanzu."
ya bata amsa a gajarce,
gefen shi taje ta zauna ta d'an kalleshi tare da tab'e baki tace.
"Hmmm yau kuma halin ya motsone?."

bai kulata ba sai zamewa yayi ya konta kan kujeran,
ganin haka itama ta koma gefe ta zauna tana murmushi tana mamakin hali irin na Umar mutun ba'a gane inda ya dosa.

A parlour Nenne kuwa Usman ne zaune yana kallon yadda Ummul ke zuba shek'i tayi kolliya mai kyau tayi shigarsu na shuwa'arab ta tubke gashinta tayi ras da ita riga da siket ne a jikin ta sunyi d'as gwanin shawa sai laffaya da ta yane jikin ta dashi har zuwa sama tayi irin yanawar da y'an mata sukeyi,
ga wani irin k'amsi da take zubawa na turarukan humrarsu na shuwa,
fuska ya d'an tab'e ya kalleta a d'an gyatsine yace.
"Wai gasar kyau zaki je kike ta wannan kolliyar akan wannan Mustapha naki."
Murmushi tayi tare da d'an juya ido ta d'an tsuke bakinta lips d'inta tad'an had'e tayi taku d'aya zuwa biyu tace.
"Kai Ya Usman kaima da kanka kasan Mustapha da banne dole kuma komai nashi da banne."

Fuska ya kuma tsukewa ya kalli Anty Halima dake ta nad'a mata laffayar yace.
"Waike Halima me naki na zak'ewa kina shiryata kamar wata amarya."

Murmushi tayi sannan ta kalli Usman cikin fara'a tace.
"Ya Usman ai mace 'yar gyara ce."

Ya Adam ne ya kalli Ummul d'in da Halima cikin harara yace.
"Aiki ya same ku ai, ni wallahi sam Mustapha nan ba wani burgeni yake yiba kuma wallahi zan zuga su Abba a hanashi ma zuwa kawai ."

Lokaci d'aya fuskar Ummul ta canza gaba d'aya annurin ta ya gimtse.
Aliyu ne ya kalleta cikin tsokana yace.
"Ummul in an hanaki shi zaki mutu ko?
dan wallahi na lura jinshi kike kamar sarki."

Harara ta cillawa Aliyu fuska a tsuke tace.
"Mustapha yafi sarki a gareni shi shugaba zai zame min kuma shi tamkar jinina ne,
shine bugun zuciya ta duk randa na ratsashi na rasa farin cikina."

Ido Usman ya zuba mata yana mamakin yadda take son Mustapha,
Halima ko murmushi kawai tayi ,

Ya Sadik ne ya kalleta a tsokone yace.
"Kuma wallahi inaji a jikina bazaki auri Mustapha ba."

Juyawa tayi tana fita tare da cewa.
"Ashe ko duk wanda aka hanani Mustapha a dalilinshi toh tabbas yayi ban kwana da farin ciki a rayuwar sa zai fuskanci k'iyeyyar iya k'iyayya zai samu bak'in ciki mai isarsa."

Tana kaiwa nan ta fice,
Usman ne ya bita da sauri gaban ta ya tsaya cikin yin murmushi yace.
"Koda ko d'an uwanki ne?."

"Sosai ma ya Usman ko d'an uwa nane."

K'irjinshi ya dafe cikin lumshe ido yace.
"Koda ko nine ya Usman d'in ki?."

Dariya tayi cikin lumshe ido tace.
"Kai ai kai d'an uwa nane mai tayani son abin da nake so kai nasan bazaka zama silar bak'in cikina ba."

Tana fad'in haka ta wuce ta tafi,
shi ko Usman d'akin Hajjajo ya shiga yana murmushi gafen Hamma Umar d'in shi yaje ya zauna cikin sauk'e ajiyan zuciya yace.
"Hamma yau kuma k'irjina yana min nauyi."

Da sauri Hamma Umar ya mik'e tare da bud'e ido yana kallon Usman cikin tuhuma yace.
"Me kaci? kashe maganin ka ?."

Ido ya lumshe sannan yace .
"Allah ko Hamma na ba abin da naci,
maganin nedai ban shaba."

Hannu yasa ya d'an bugi k'eyarsa cikin mik'ewa tsaye ya fice .
Jim kad'an ya shigo hannushi rik'e da magungunan shi,
bashi yayi yasha sannan ya kalleshi a hankali yace.
"Jeka shirya kazo muje jama'a clinic na d'an dubaka sai mu biya,
baba aura chemist na d'auko ma magungunan ka d'an sun kusa k'arewa."

"Toh" yace sannan suka fito suka nufi part d'insu Usman ne ya fara wonka sannan yana fita Umar ya fitomai da kayan da zai saka,
shima ya shiga yayi wonkan yana fitowa ya shirya tsab,
shiga irin d'aya sukayi shigar shuwa'arab shigar da tafi kama da ta larabawa,
sun fito ras tamkar tagwaye komai nasu irin d'aya hatta tafiyar su farar fatarsu sajen fuskarsu kamace ta sak da sak suke sun fito ras tamkar taurari sai shek'i da k'amshi suke zubawa,
Suna fitowa Motar Umar suka shiga shi yake jan motar kai tsaye al'ameen restaurant suka nufa,
suna zuwa suka shiga can ciki,
lokaci d'aya aka had'a musu abinci dan sun saba zuwa wurin su maikatan har sunsan iya abincin da Usman ke iyaci so dama suna zuwa za'a kawo musu komai yadda ya kamata,
kamar yaro Umar ya tasa Usman a gaba saida yaci yayi tik sannan ya biya komai suka fito,
daga nan kuma clinic d'in suka wuce anan ya k'ara duba lafiyar d'an uwan nashi suna fitowa nan,
kai tasaye katafaren chemist d'inshi suka wuce,
ya had'a komai na maganin Usman d'in sannan,
suna fita Umar ya sake jansu sai dicency super market ,
suna zuwa Umar ya had'e musu duk wani abin buk'atan su sannan aka loda musu a mota suka fito suka nufi gida.


Ummul kuwa da Mustapha hirarsu sukayi sosai gaba d'aya sun susucewa juna hak'ik'a Mustapha yana son Ummul so na hak'ik'a haka itama take mishi so da iya gaskiyarta hirarsu suke basuma san maggariba tayiba saida suka ji kiran sallah,
Mustaphanne ya kalleta cikin tarin so ido ya lumshe tare da sauk'e ajiyan zuciya murya can k'asa yace.
"Ummul idanuna basa gajiya da ganin kekyawar fuskar ki! kunnuwana basa k'osawa da jin sautin ki mai zak'i ! hancina bayi da wani b'uri daya wuce shak'ar k'amshin ki,
Ummul ina sonki son da bana yiwa kaina."

Tafin hannun ta tasa ta rufe fuskar ta cikin jin dad'i da kunya tace.
"Habeebi dani da murya ta da fuskarta da k'amshi na duk naka ne."
Ido ya tsura mata tare da tasowa yazo gaban ta durk'usawa yayi a guiwowin shi a k'asa ido ya lumshe sannan ya bud'e su a hankali yace.
"Ina jin tsoro Ummul inajin tsoron karna rasaki Ummul har yanzu baki zama tawaba gashi ban san yaushe Allah zai mallaka min keba ina sonki inason mu kasance ma'aurata Ummul kimin al'k'awarin duk rinsi kina tare dani ki min tattalin kanki kada idon wani namiji ya dira a kanki."

Kallon shi tayi cikin murmushi tace.
"Ako da yaushe ina shaida maka kai Habeebi da'iman ne a gareni zuciya ta ba inda wani zai samu ma tsuguni."

Ajiyan zuciya ya sauk'e sannan ya mik'e yana kallon ta,
itama mik'ewa tayi ta d'an matsa gefen shi,
cikin sanyi tace.
"Sai yaushe zaka kuma zuwa?."

"Ko gobe in kina so zanzo, ina damaturu ina potiskum garin masoyi baya nida."

"Gobe kam ai baka huta bama tukun."

"Hutu kuma Ummul aini bani da wani hutu har sai na ganki cikin gida na."

Murmushi tayi sannan tace,
" toh muje kayi sallan maggariba sai ka tafi kar dare ya maka."
"Kin gaji da ganina ne?."
"Inko zangaji da kallon fuskar ka toh zan gaji da kallon tawa fuskar kenan."

Murmushi yayi ya mik'a mata hannu wai suyi musabaha,
kai ta sunkuyar a hankali tace.
"Da saura."

kai ya juya sannan ya had'e hannu a k'irjin yayi muryar tausayin yace.
"Haka ne toh da wacce Kalmar za'a sallameni?."

Juyawa tayi ta fara fita yana biye da ita a baya sunzo dai-dai inda zatayi cikin gida shiko zaiyi woje tace.
"Laisa Lee misluka abadan ya habeebi.
gareni bakada damka masoyina,
ina sonka so mai tsananin Habeebi zanyi maka tattalin kaina dan cika zuciyar ka da farin ciki."

Mustapha kam tamkar ya had'iye ta yakeji da tsabar k'aunar da da hali zai nuna mata sonta a fili amman ba dama,
sai murmushi yayi tare da cewa.
"Anti sururi,
kece cikon farin cikina."

Ya matsota zaiyi magana kenan yaga Hamma Umar dake zaune can gefen yana al'wala,
haka yasa ya sallama ta,
tayi cikin gida shiko yaje kusa da Hamma Umar d'in shima al'awalan yayi sannan suka tafi masallaci,
ana idar da sallan suka nufi gida a bak'in gate Mustapha ya tsayai da Aliyu ya fito da manyan lododi guda biyu ya bawa Aliyun yace,
ya kaiwa Ummul .

Shi kuwa ya kama hanyar komawa damaturu

A parlour suka baje tarkacen daya kawo mata kayan k'amshi ne sai atampopi guda 2 da les 2 sai shadda 2 sai yadukan laffaya masu kyau da taushi guda 3 ,
Anty Halima sai kallon Ummul take tana .
"Iyeeh manyan masoya."

Nenne kuma cewa tayi.
"Maza Ummul had'e kayayya kin nan ki adana ko turaren bazaki fesaba."

Fuska a marairaice tace.
"Ayyah Nenne am kullum Mustapha ya kawo min abu sai ki hanani amfani dashi ban san me yasa ba ko kema bakya sonshi ne Nenne?."

Murmushi Nenne tayi sannan tace.
"Me yasa ina son Mustapha ai yaron kirki ne kawai dai wannan Al',adarmu ce budurwa bata amfani da kayan saurayi sai in sunyi aure,
mu a gunmu in kiyi amfani da kayan saurayi kamar kasawa ce,
toh kinga ke kuma ba abinda muka regeki dashi."

Murmushi tayi ta tattara kayan,
sannan suka ci gaba da hira,
Abba da Umar da Usman dasu ya Adam kuma saida sukayi sallan ishah sannan suka dawo,
suna shigowa su Usman sukayi parlour Nenne Hamma Umar kuma Abba ya kirashi suka tafi parlour Hajjajo,
suna shiga suka samu Daddy ma yazo gun Hajjajon.

Su Usman ko suna shiga,
cikin halin girma Usman ya kalli Halima fuska a tsare yace.
"Ke Sadiya har yanzu baki tafi ba?."

Cikin girmamawa tace.
"Ya Usman yanzu zan tafi."

Mik'ewa yayi tare da cewa.
"Muje in maida ki kinzo kin wuni bai kamata ki kai dare ba."

Maza Ummul ta mik'e tare da cewa.
"Yauwa ya Usman muje in rakaku."

Kai ya gyad'a yace.
"Oga Mustapha ya barki ne?."
"Mustapha kuma ji ya Usman fa dama Mustapha ne ke hanani zuwa unguwa?."

Juyawa yayi ya fita Sadiya na biye dashi a baya ita kuma Ummul tana gefen shi,
kallon ta ya d'an yi sannan yace.
"Keda ki kace Mustapha ya fimu matsayi."

Murmushi tayi tare da rufe idon ta,
shi kuma Sadiya ya kalla cikin murmushi yace.
"Shiga baya kinsan Ummal da son zaman gaban mota kamar ba fullatana."

Dariya sukayi sannan suka tafi.

A parlour Hajjajo kuwa bayan su Abba sun d'anyi hira Abba yayi gyaran murya cikin kula ya kalli Daddy sannan ya kalli mahaifiyar su Hajjajo sai ya kuma kalli Hamma Umar cikin wani irin yanayi yace.
"Farouq ina maganar aure da mukayi da kai?."
Kai ya sunkuyar yayi shiru,
ido Daddy ya tsura mishi tare da cewa.
"Farouq shi fa aure dolene a gareka tunda Allah bai hanaka yadda zakayi ba,
shin a zatonka munajin dad'in zaman ka hakan ne,
Farouq ka sani duk girman mutun da darajarsa da matsayinsa matukar baiyi aure ba toh bai cika mutun ba."

har lau dai baiyi magana ba sai sunkuyar da kai ya k'ara yi,
a hankali Daddy yace.
"Farouq me kake jira ne? da har yanzu baka fara maganar aure ba."

Kanshi a sunkuye murya can k'asa a hankali yace.
"Daddy ina jiran......





By
*GARKUWAR FULANI*
















📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 7⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇




*"Abba* ina jiran Usman ne."
ido Abba da Daddy suka zuba mishi Hajjajo ko kai ta jinjina cikin mamaki tace.
"Usman kana jiran Usman kuma? toh ka jirashi a kan me? me zakayi mishi da kake jiran shi?."
shiru bai amsa mata ba bai kuma kalleta ba sai zaman shi da ya d'an gyara,
juyowa gaban shi Abba yayi cikin son fahimtar sa yace.
"Farouq!
Usman kake jira? meyasa kake jiran shi d'in? ko so kake kuyi aure rana d'aya?."
kanshi ya d'an d'ago cikin tok'k'oshi wuyanshi kan kafad'arsa cikin sanyi ya kalli Abba da Daddy murya a raunane yace.
"Abba ina jiran Usman ne ! Abba inaso inga Usman ya samu mai kula dashi kafin nayi nesa dashi ! Abba in nayi aure yanzu wazai kula da Usman kaga baya son shan maganin shi kuma baya son bin dokokin doctors kuma kaga inba ana samishi idoba komai ya samu zaici,
gashi ko yau saida yace min k'irjin shi na mishi nauyi."

Sai kuma yayi shiru dan muryarsa da ta fara rawa,
dan har cikin ranshi yake jin tausayin d'an uwanshi da yana da damar karb'awa Usman ciwon daya karb'a mishi.

Abban ma shiru yayi tausayin 'yay'an d'an uwan nashi na ratsashi yana son Usman da Umar a ranshi fiye da yaran shi.

Daddy ne ya d'an gyara zama cikin kallon Hajjajo da ta fara zubda k'ollah cikin k'arfin haki yace.
"Farouq aure rahama ne meyasa kake ganin aure zai nesan taka da d'an uwanka Allah shike kula da Usman ba wayon mu

4 Comments On RUBUTACCEN ALAMARI
avatar
shukra-sulaiman

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
shuraihu

1 year ago

Reply

Replying to shukra-sulaiman

Tnx too

avatar
fatima-idris

1 year ago

Reply

Nice novel

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fatima-idris

Aha tnx

Please Login or Register in order to submit comment