Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafara takawa wanda hakan yasa dukkansu dake d'akin jin dadi kasan cewar tun dawowarsu basuga hakan daga garetaba,
a hankali suke tafiya Aliyu na rik'e da hannunta har suka fita daga d'akin,
da hannu taiwa Aliyu nuni da hanyar inda Hamma Umar ke zama dan duba marasa lafiya dake zuwa gida,
haka sukaita tafiya sanayi a hankali har suka isa gurin,
d'an juyowa tayi ta yafito ya Sadiq da suketa binsu a baya tunda suka fito ta nunamai carpet dake jingine agun da hannun ta,
shiko jiki na rawa yace, "in shimfid'a?".
Kai ta kad'a, aiko ya shimfida nan da nan, kwace hannunta tayi dagana Aliyu ta juya kamar tana neman wani abu, Ya Usman dake tsaye a bayanta kamar body guard' yace, "me kike so?".
itako Ummul Ammi ta nuna da hannu takuma nuna mata carpet da aka shimfid'a,
cikin sanyin jiki Ammi ta zauna kan carpet d'in, Ummul tasa hannu ta rik'o hannun Aliyu shiko yasa daya hannun yakuma rik'ota ya taimaka mata ta zauna sannan ta matsa kad'an ta jingina bayanta da jikin Ammi, ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta lumshe ido sannan ta kalli Ya Usman daya zuba mata ido tamai nuni da ya zauna.
zama yayi sannan taiwa Ya sadiq nuni shima ya zauna, ta kalli Aliyu tamai alama da hannunta daya yazo yazauna kusa da ita haka taiwa kowa nuni suka zauna harda Hajjajo,
Ya Adam yasa tafin hannunsa ya goge hawayansa a dai dai lokacin da Ummul taimai nuni daya zauna shima,
Haka suka zauna agun itako Ummul tanata kallon su da dai-dai kamar bata tab'a ganin suba saida aka kira magrib sannan suka koma cikin gida.


Kwanci tashi cikin Ummul ya isa haihuwa dan haka aka shirya komawa kasar egypt da taimakon adalin gwamnan gwamnoni, gwamna daya d'au rayuwar talakawan jahar shi da muhimmanci gwamnan jahar yobe.
Anyi tafiyar ne da Ammi, Abba da ya Usman sabida yanada buk'atar ganin likita akan yawan aman jinin da yake kowane lokaci, isar su da kwanaki uku
aka gama bincike kan zuciyar Usman inda cikin ikon Allah doctor ya shaida musu za'a cire na'urar dake tallafa zuciyar Usman domin sanadin wani tsoro da tsinkewar zuciya daya samu yasa zuciyar ta harba cikin tsoron to daga nan yanzu ita da kanta take aikin harba jinin kuma in anbar na'urar zata iya maida zuciyar ta cushe dan haka cirewa za'ayi,
abin ba k'aramin Al'ajabi ya bawa Ammi da Abba da Adam ba haka Abba da Ammi suka sa'a hannun,
ita kuwa Ummul bayan magun guna da allurai da likitoci keta bata ne akai shirin shiga yimata aiki saboda babu halin haihuwa dakanta sakamakon sanyin da zuciyar ta tayi dan bugun zuciyarta tayi k'asa sosai haka yasa rana d'aya za'ayiwa Usman da Ummul aiki
Abba kam da Ammi da Adam sai Addu'oi sukeyi Abba ya kira Daddy da Uncle dinsu Usman da sukaje saudi ya shaida musu su tayasu da Addu'a.



K'arfe 8:00 dai-dai babban likitan da zai jagoranci aikin yakira Abba da Adam a office din shi,
bayan yad'anyi rubuce rubucen shi ya d'ago kanshi ya sauke farin glass dinshi kasan hancin shi yace,
"Alh Hassan, zamu shiga aiki da yaranka muna kuma bukatar addu'ar ku kasancewar ita yarinyar aiki zamu me cike da hatsari domin kuwa bamuda tabbacin zuciyarta zata tsaya yanda muke bukata har mu gama aikin".
Abba yai ajiyar zuciya yace,
"to Allah ya bada sa'a". Likitan ya mik'o musu form da zasu saka hannu dan yin aikin, Abba yasa hannu ya janyo takardar ya juya ya kalli Adam da ya sunkuyar da kai k'asa ya dafa kafad'ar shi yace,
"Adamu kadaure kasa hannu aima k'anwarka aiki ni zansa hannu akan aikin Usman".
a razane ya Adam ya d'ago yana kallon Abba da takardar,
a hankali Abba yasake d'agamai kai da lumshe ido cikin sanyi Adam yasa hannu ya janyo takardar yad'auki biron sannan ya d'ago kai ya kalli likitan daya zubamai ido yana kallonshi, cikin tausayawa likitan yace, "Insha Allah zamuyi aiki cikin nasara".
shi kam Adam ido cike da k'ollah yasa hannu tsoro tab zuciyarshi yana jin tausayin Usman a ranshi yana jin tsoron kar wani abu ya faru da su kuma a zuriyar tasu,
hannu na rawa Adam yasa hannu a takardar yana zubar da kwallah, likitan yasa hannu yaja takardar yace, "good, be prayerful".
da haka yatashi yafita sukabi bayanshi jiki ba kwari, karfe 9:00 dai-dai aka shiga da Ummul d'akin tiyata ya Usman kuwa aka shiga dashi d'akin dashen zuciya,
akabar Abba da Ammi ,
tsaye suna karanto kowacce irin addu a da suka iya zuk'atan su cike da zulumi.




Har k'arfe 11:30 suna ta zirga-zirga bawanda yake magana kowanne da irin tuna ninda yake a ranshi, bude k'ofar dakin da akema Ummul aiki ya tattaro hankalinsu, ya Adam ya dafe kirjin shi da hannu yabi bayan likitan daya wucesu yanufi office d'inshi,
a lokacin kuma aka fito da ya Usman shi an gama aikin nashi,
Adam kuwa a office d'in doctor saida ya zauna a kujerar shi sannan yad'anyi murmushi yace,
"congratulation". Allah yayi ikon shi da taimakon y'an uwana likitoci anciro baby boy,
yaro yana cikin koshin lafiya sannan insha Allah itama zata farka babu wata matsala".
cikin jin sauk'in razanar Adam ya dago rinannun idanunshi dasukai jawur yace,
"Alhamdullah Masha Allah".
Sanna ya mike ya fito ya nufi d'akin da yaga Abban na shiga wanda ya haggo ana shigar da Usman,
suna shiga kuma sai ga ita Ummul an shigo da ita haka aka kontar dasu d'aki d'aya gadon Usman na gefen na Ummul Ammi kuwa waje ta fita ruggume da yaron tana kukan abubuwa da dama kukan tuno d'anta kukan fargabar halin da Ummul da Usman ke ciki kukan tausayin yaro maraya tun yana ciki an kashe mai uba haka tayita kuka gwanin ban tausayi.

Bayan awanni shida Ummul na kwance kan gadon hutu na asibitin, shiko Usman yana kwance kan d'ayan gadon dake kallon nata yasanya jinjirin gaba yanata kallo dan yariga ta farfad'owa,
yayinda Abba ke zaune a kan kujera a gaban gadon Usman kusa dashi kuwa Dr Bashir ne suna kallon yanda Ummul kedan motsa k'afarta a hankali,
Ammi ko tana zaune bakin gadon da ummul ke kwance tana rik'e da hannun ta idon ta ya na kanta,
yun kurin bude idonta tafarayi a hankali tanajin yamata nauyi,
da hannu Ammi taiwa Dr Bashir nuni aiko tare suka taso sukayo bakin gadon,
Tana bud'e idonta da kyar ta d'aga hannun ta da kyar ta shafi cikinta dan jin yayi mata wayam aiko saita d'an kara zaro idonta tabud'e baki da kyar murya nara voice a disashe a hankali tace,
"In in inaaaa cikin?". Hamdala suka rink'a jerawa cikin tsananin happy dan tunda Hamma Umar ya rasu sai yau Ummul ta iya magana,
ya Usman kuwa juya kanshi yayi a hankali wasu irin hawaye masu zafi suna bin fuskarsa,
Ammi ce ta mik'e da sauri ta d'auko babyn da yaketa bacci a gaba Usman shiko Usman sai kallon yaron yake cikin tsananin k'auna yana jin son yaro fiye da kowa a duniyar nan,
a hankali Ammi tace, "gashi nan Ummul, ga d'anki wanda Allah ya azurtaki dashi keda Faruoq na amman ke Allah ya nunawa shi shi kam Umar ya rasu da begen wannan rana ya rasu da kumfar rashin ganin d'anshi Ummul ga d'anki maraya zai tashi maraya kamar yadda iyayenshi suka tashi marayu".
Daga kwance tasa hannu ta d'ora akan yaron ta kuramai idanu tanajin k'aunar shi na ratsa zuciyar ta da dukkan jikinta sai kuma tayi kurui tana kallon Usman dake konce yana hawaye cikin sanyi yace,
"Ammi yaron nan bazaiyi maraiciba Insha Allah bazai yi kukan rashin mahaifiba Ammi da izinin Allah indai ina raye yaronan bazai zubda k'ollah".
sai kuma ya rink'a kuka yana rik'e da hannun Abba,
shima Abban kuka yake Ammi kuwa zuwa yanzu hawayenta sun fara k'agewa,
Adam ma gaba d'aya ya zama mai raguwar zuciya abu kad'an sai Kuka amman shi tausayi Usman ke addabar rayuwarshi,
haka Dr Bashir kuwa da sauran doctors din sukayi ta kula da Usman da Ummul da jaririnta k'ato fari tas kekyawa, sukaita kula dasu cikin ikon Allah kuwa Ummul da Usman duk Alhamdulillah jiki yayi kyau Ummul kuwa tun randa tayi magana bata kuma yiba.




Doctors sun bada tabbacin zuciyar Usman zata iya aikin da ake but'ata amman a guji b'acin ransa sosai sukayi kashedin gudun b'acin ran shi,
a gefen Ummul Kuwa sunce kar a damu da rashin maganarta sunce a koda yaushe maganarta zata iya dawowa amman kuma a duk randa suka tsinci Ummul na kuka toh karsuyi yunk'urin hanata a barta domin a cewarsu yin kukan zai iya maida tunaninta dai-dai har ta fara magana kuma sanyin da zuciyarta tayi harda rashin kukan.


Bayan kwanaki shida dayin aikin aka sallamesu da sharadin kulawa da bawa Ummul da Usman magunguna don cigaba da samarwa zuciyoyin su lafiya, da haka suka tattaro suka dungumo sai gida Nigeria.



Randa suka dawo gaba d'aya zuriyar Shuwa sun cika da farin ciki domin samun lafiyar Usman da Ummul ga jariri da ya zamo magajin Hamma Umar kowa zaizo da Happy amman abin fargaba har yanzu Ummul bata mgn,
Nenne takan buya tayi ta kuka,
Ummul kuwa in banda bawa yaro nono da da tasashi a gaba tayi ta kallo ba abinda takeyi da kanta sai an tasa a gaba wani lokacin sai ta wuni ta kwana bataci komaiba inko yaronta na kuka sai tai ta rawan jiki ta gigice,
in tak'i cin abinci da wonka Usman yakan zauna a gabanta yayi ta magiya har ya fara zubda k'ollah to da zaran taga yana kuka sai ta zauna ta fara cin abincin.

A haka rayuwa tayi ta juyawa har sukayi kwana 9 da dawowa,
yau asabar da safe bayan sun gama aiyu kansu,
Abba da kanshi ya shiga d'akin da Ammin ke zaune da Ummul a nan ya samu Usman da Nenne da Adam Ummul ruggume da yaron,
bayan sun gaisa cikin kula Abba ya kalli Usman yace,
"ni kam Usman me sunan yaron ne har yau baka gaya min
ba? ".
cikin mamaki Usman yace,
"Abba baka yiwa yoron huduba bane dama ni yamin ka gaya mai sunanshi ai".
a hankali Abba yace,
"A a Usman ya za'ayi haka yaro yau kwana 14 kuma ashe ba'a mai huduba ba".
Ammi ce ta kallesu a hankali tace,
"mahaifiyarshi ta mishi huduba tun randa yayi kwana uku amman har yau bata gaya min sunan shiba".
usman d'in ya zuba mata ido cikin sanyi yace,
"Ummul kiyi hak'uri mana ki ruggumi k'addararki ki rink'ayi mana magana yanzu tsakanin ki da Hamma kiyi mishi gatan Addu'a ki bawa d'anshi tarbiya to amman a hakan zakiyi wad'an nan abubuwan"?.
shiru tayi tana jinshi karo na forko da ida nunta suka ciwo da hawaye tab,
Abba ne ya kalleta a raunane yace,
"Me sunan yaron?".
murya can k'asa cikin rauni da tsananin k'una a zuciya tace,
"Washe garin za'a kashe Hamma na yace min in namiji na haifa ya bani dama nasa sunan wanda nafiso a duniya wanda duk duniya bani da kamarshi".
sai kuma ta saki wani irin kuka ta ruggumo yaron tana kallon shi,
Usman ma kukan ya fara a hankali yace,
"Ummul me sunan yaron?".
cikin tsananin kuka tazo ta durk'usa gaban Abba murya a disashe tace,
"Abba ina sonshi Abba ina sonshi ina sonshi Abba duk duniya bani da kamarshi Abba ina son Hamma Umar Abba ina zan ganshi Abba sun kashe min Hamma na a gabana Abba ina son Hamma Umar".
sai kuma ta kife kanta a cinyar mahaifin nata cikin rauni da tausayawa rayuwarta,
shiko Abba a hankali yace,
"Me sunan yaron kika saka? ".
cikin tsananin kuka tace,
"Sunan shi *Umar Faruoq*".
tana fad'in haka Usman ya........





*Sadaukarwa ga Umar Ibrahim Umar Hamma Umar*



By
*GARKUWAR FULANI*
[07:03, 12/9/2017] 😄😄💲ⓂℹLÂŖ®😀😀: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 3âƒŖ2âƒŖ

*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇





*MOH ALLAH WUJI FURD'ATA*

*Kin kid'i kankad'a damoni na damoni giddo mo fina laramo gaid'omo fina sukoyo ladde Allah yamad'u benduki yamete ki b'ib'b'e sammete joruki tenete ki d'oidi yalete*




*U*sman ya d'ago jajayen idanuwan shi yazuba matasu sannan ya mik'e yana layi yaje bakin gadon ya sa hannuwanshi biyu a d'auko Umar faruq ya rungume sosai a jikin shi yana zubda hawaye mai tsanani da zafi da k'una a zuciya yana shafa kan yaron dake cike da suma bak'ik'k'irin daya kwanta luf,
ita kuwa Ummul cikin kuka taci gaba da cewa,
"Hamma Umar ne rayuwa ta nafi sonshi a kan kowa a duniya, shikad'ai nakeso shine komai nawa na rasa a lokacin da nake tsananin buk'atarshi".
Tana magana ne cikin matsanan cin kuka, bakajin komai a gun sai shashshek'ar kuka da duk wanda kegun yakeyi,
shiko Usman yana k'ollah ne idanuwan shi na kan Umar faruq yana mai wani irin kallo kamar a lokacin yafara ganin halittar jariri,
Itakuwa Ummul cikin kuka taci gaba da cewa,
"Ammi wallahi ina sonshi,
bazan k'ara son wani mutum a duniyar nan bayan Hammana,
ina kaunar shi fiye da kaina Inamai matsanan cin so da duk duniya bamai iya fahimta".
sei ta kuma jan gwiwoyinta data zuba k'asa har gaban Ya Adam dake ta faman zubda k'ollah tace, "Yaya na kafi kowa yimin fad'a bakamin wasa amman na kasa ganewa,
kuma baka son damuwa ta, nasan kayi iya k'ok'arinka ka d'orani ka turbar gaskiya,
amman taurin kaina da rud'un shaid'an yasa nak'i gane abinda nasan gaskiya ne gashi hakan ya jazamin nadama ta har abadan na cutar da kaina da kaina naga illar rashin yiwa iyaye biyeyya, nagode dakaita k'ok'arin nunamin hanyar gaskiya".
Hannu yasa ya kama hanna yenta duka biyu ya d'an matsesu sannan yace,
"Ummul nasan kina son shi naga sonshi a idonki amma inaso ki nunamai soyayyar da kikemai inaso ya amfana da ita ta hanyar yimai addu a Ummu ki dena zubda mai hawaye".
kai ta rink'a gyad'awa cikin rauni da tsananin nadama,
saita kuma juya ta kalli Abba dake tsaye yana kallonsu ido cike da k'ollah,
sannan ta dawo da kallon ta ga Ya Adam dake murza yatsunta a hankali tace,
"Ya Adam Abbana yamin zab'i mafi al'khairi zab'i mai cike da al'kairai a rayuwata amma ina shaid'an ya hanani ganewa nayiwa iyayena taurin kai gashi zan dauwama cikin nadama da dana sanin rashin biyayya haka zan k'are rayuwata na kasa yiwa iyayenmu d'a'a kaitona Allah ya wadaran halina bani da wani abun koyi lallai duk yarda tayiwa iyayenta ba dai-daiba tana tare da nadama ya Adam na tsani kaina na cutar da Hamma na na b'ata ran mahaifanmu".
sai kuma ta kife kai wani irin matsanan cin kukane ya kwace mata wanda ya hanata k'arasa kalaman ta ta kife kanta a gwiwar Ya Adam jiki na rawa tana cewa,
"Wallahi ina son shi, inason Hamma Umar Yazanyi Hamma Umar yaga soyayya da kaunar da nakemai,
ya Adam kullum Hamma Umar yana cewa Ummul zaki soni, zakisoni lokacin da soyayyar bazata amfane muba ashe wannan lokacin ne Hamma na yake ganemin dana sani dana nuna mishi so da yake son in nuna mai lallai wannan shine kuskure mafi muni da yarinya tayi dan iyayenta sun mata auren dole".
kuka takeyi sosai tana cike da madama,
Aliyu ne yataho jiki ba kwari yasa hannu biyu ya d'agota ya durkusa gabanta a hankali yace,
"Aunty Ummul kiyi hak'uri, Hamma yace nine abokin shawararki abokin kukanki kuma me rarrashinki kiyi hak'uri kidena kukan nan kinga kinsa Ammi da Nanne kuka ga Abban mu shima yanayi kinga Hamma junior zaiji sautin kukan mu ki dena auntyna dan Allah".
Cikin galabaita da ajiyar zuciya ta kwantar da kanta a cinyar Aliyu tana sheshshe k'ar kuka tana nannad'e kafafun ta,
hannun Aliyu yasa yana shafa bayanta yana bubbugawa tare da share mata k'ollar cikin lallashi da haka bacci yayi gaba da ita,
su kuma Abba ya zauna yayi ta musu nasiha Usman kuma sai ajiyar zuciya yake sauk'ewa yana ruggume da farouq,
a haka rayuwa tayi ta juyawa rana d'ad'd'ayace
basa zama suyi kuka a hankali mutuwar ta fara shiga jikinsu,
lokaci yaja kwanaki sun tafi tuni Farouq ya cika kwana arba'in.


A bangaren Mustapha kuwa a kullum koda yaushe tunanin shi nakan Ummul da yaronta dan haka ranar Asabar suka shirya da umman shi suka nufo potiskum dan duba lfy Ummul da jaririnta, dai dai lokacin da motar Mustapha na shirin shiga harabar gidanne motar Dr Bashir ta sako kai dan fitowa wanda shima zuwa ganin Ummul da yaronta ya zame masa jiki a duk

4 Comments On RUBUTACCEN ALAMARI
avatar
shukra-sulaiman

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
shuraihu

1 year ago

Reply

Replying to shukra-sulaiman

Tnx too

avatar
fatima-idris

1 year ago

Reply

Nice novel

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fatima-idris

Aha tnx

Please Login or Register in order to submit comment