Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin zufa ya keto mai daga tsakiyar kanshi har kan d'an babbar yatsar k'afarshi hatta cikin gashin kanshi sai d'igowa yake tol-tol,
Hajjajo kuwa wacce tun ihun da Aliyu yayi ta fito amman ganin Abba a sume Aliyu a sume ga Ummul jiki duk jini,
a take sai jijiyoyin ta suka sassake k'afafun ta suka kasa rik'e ta jiri ya rufeta cikin tashin hankali ta fad'i k'asa dirsham hawaye na bin fuskarta ta kasa tashi sai yanzu ta mik'e da kyar ganin halin da Usman ya shiga,
tana xuwa ta kamo hannun shi tana k'ok'arin zaunar dashi amman ina sai taji jikin shi kamar an dasashi ganin haka cikin muryar kuka tace,
"Usmanu! Usmanu! Usmanu ! ka ambaci Allah shi zai kawo mana agaji Usmanu kar kabar zuciyarka ta mance da Allah Usmanu wannan shine jarrabawarmu a wannan shekara a wannan wata a wannan rana muyi rashi mai girma ban sani ba waya kashe mana Umar".
sai kuma ta k'ara rik'o hannun Usman d'in sannan cikin kuka ta kalli Adam dake yayyafawa Abba da Aliyu ruwa,
a firgice Aliyu ya farfad'o cikin k'ara tare da rarumo Sadik dake gefen shi,
karan da Aliyu yayi ne yayi dai-dai da farfad'owar Abba a razane ya mik'e dai-dai lokacin kuma sojojin dake harabar gidan suka shigo dan jin k'aran da Aliyu keyi,
suna shiga Usman suka kama suka rik'e sabida ganin yadda yake tsaye,
zau nar dashi suke k'ok'arin ya,
cikin hard'ewar harce ya janye hannayen shi gaban Abba yaje ya tsaya hannun Abba ya kamo ya rik'e harce a nad'e maganarsa bata fita sosai kuma yadda bugun zuciyarshi tayi k'asa haka muryarshi numfashi a cushe ya nuna Ummul dake zaune ta zama mutum mutumi sai ida nun ta da sukayi jazir tamkar rushi sai lips nata da suka kumbura,
a hankali yace,
"A..! Ab...! Abb!...
Abba wai jinin Hamma nane a jikin Ummul Abba kace ta gaya ma inda ta barmin d'an uwana Abba kalli matar nan wai cewa take d'an Uwana ya resu Abba wai Hamma fa suke cewa ya rasu".
kife kai Abba yayi tamkar yaro ya rink'a kuka yana durk'ushe a gaban mahaifiyarshi,
Aliyu kuwa kuka yakeyi da shid'ewa Nenne ma kuka takeyi da tsananin k'una ya Sadik kuwa kanshi ya rink'a murzawa yana kuka cur-cur Adam kuwa ruggumo Usman yayi yana kuka tankar ranshi zai fita,
Umman Mustapha ma tuni kukan take,
ganin haka sojojin suka kama Abba suma kansu kuka suke dan tausayawa rayuwar wannan family,
cikin hikima sukayi wa Abba bayani,
suka k'ara da cewa,
"yanzu haka gawarshi tana gidan sarki ya kamata kuje ayi mishi sutura".
Abba jikin shi sai rawa yake cikin kuka yace ,
"Mu tafi".
juyawa sukayi har zasu fita Adam yaga yadda Usman yake tafiya numbfashin sa na yankewa ganin haka ya kamoshi da sauri a cikin kuka yace,
"Usman ka zauna a gida Abba kace Usman karya je".
Abba ya bud'i baki zaiyi Magna kenan Usman d'in ya d'ago ida nunshi da suka koma tamkar zasuyi aman wuta murya a nad'e yace,
"Gun Hamma na kuke cewa kar naje idan banje gunshi ba ina zan shiga a duniyar nan wai yau ni kuke cewa kar naje gun d'an Uwana idan banjeba me zanyi".
daga jin Maganar Usman an san baya hayyacin sa,
haka yasa Adam ya rik'eshi suka shiga motocin sannan sojojin suyi gaba suko suka bisu a baya dan an hana zirga-zirga a garin suma dan da sojojin ne,
Mustapha kuwa kai tsaye gida su Ammi ya nufa dan yasan gidan sun tab'a zuwa shida Hamma Umar d'in.

Ammi kuwa tunda garin wannan ranar ya waye ta kasa yin komai gaba d'aya jikin ta a mace yake,
a haka ta jawo radio ta kunna wanda yayi dai-dai da saka harbe-harben da yan BH sukayi a garin na damaturu sannan mai bayanin yaci gaba da fad'in uguwannin da suka fara shiga da kuma irin b'arnanr da sukayi,
jin an kira uguwarsu Hamma Umar ba k'aramin tashin hankali da firgici ya sawa Ammi ba a take taji wani irin sanyi yana ratsata har cikin hanjin cikinta tsoro mai tsanani ya rufeta ido cike da k'ollah tib ta kalli mahaigiyarta cikin muryar kuka tace,
"Inna ta uguwar su Farouq suka fara shiga Inna kinji sunfa kakkashe mutane".
Itama Inna gaba d'aya jikin ta rawa yake cikin hargitsi tace,
"Kira min wayar Umarun kira minshi maza Amina".
jiki na rawa tayi ta kiran Hamma Umar d'in amman tuni abinda Ammi bata saniba an kashe mata d'anta,
ganin Umar baya d'aga woyar sai kukanta ya k'aru sai kuma ta rink'a kiran Usman ina shima baya d'agawa hakan yasa hankalin ta ya tashi ta rink'a kiran mutanen gidan Abban amman duk basa d'agawa haka yasa ta koma ta zauna dirsham kan taburma a gaban Innarta d'in ta zauna kenan,
Mustapha yayi sallama,
shi kuwa Mustapha ganin tana kuka sai yayi zaton taji batun rasuwar Umar d'in sai ya tsuguna gefenta cikin kuka kamar yaro yace,
"Ammi kiyi hak'uri hak'ik'a munyi rashi mai zafi amman Hamma Umar yafi but'atar addu'armu a kan kuka Addu'a zakiyi mishin Insha Allah muna zatama mai rahama Allah ya karb'i shahadarsa".
Ita kam Ammi tunda taga Mustapha jikin ta ya rink'a b'ari kar-kar ta kasa tashi amman jin ya ambaci Hamma Umar yasa ta mik'e da sauri cikin razani a kid'ime zanin ta ta rink'a d'aurawa tana kuncewa tana sake d'aurawa sai karkarwa takeyi ganin haka cikin kuka Inna ta kamota ta rik'e tana cewa,
"Innalillahi WA innailaihi rajiun".
haka ta rink'a maimatawa har akayi sa'a itama Ammi cikin kukan daya kufce mata ta rink'a cewa,
"LA haulawala k'uwta illabillahi aliyul azim hasbunallahuwani'imam wakil Allahu Akbar Allah Akbar innalillahiwa Inna ilaihirajiun Allah mai girma yau kuma da k'unar dana wayi gari kenan Mustapha yau kuma Boko Haram sun yanke min naman jikina kenan Mustapha ina Usman Mustapha Usman yana cikin wanne irin hali?".
sai kuma ta kife kanta kan ciyar Innarta ta saki wani irin kuka mai cike da k'unci a zuciya,
itama Inna sai kuka shima Mustapha ya kasa barin kukan,
a haka Uncle ya shigo ya samesu wanda dama Abba ne ya kirashi ya gaya mishi,
abin tausayi shima Uncle sai yasa yar uwarshi a gaba suna kuka tamkar yara Ammi kam kuka take har numfashin ta na tafiya,
a hakan Uncle ya daukosu ya kawosu gidan Abban sannan shida Mustapha kuma da sauran abokan Hamma Umar dana ya Usman da abokan Adam Sadik da abokan Abba duk suka d'ugguma damaturun,
suko Inna da Ammi suka wuce cikin gidan.


A damaturu kuwa suna isa suka samu ana shirin yiwa mamacin wonka suna shiga Usman ya wuce kai tsaye inda yaga an mik'e gawar a shimfid'e ta a k'asa Adam ma da Abba da Sadik da Aliyu gaba d'aya sai sukasa gawar a tsakiyan su,
shiko Usman hannu yasa ya d'ago gawar fuskar ya tsurawa ido cikin wani irin yanayi mafi rauni da muni ya rink'a kallon wuyanshi da aka yanka, ruggume gawar yayi da k'arfi,
a hankali ya rink'a juya kanshi yana wani irin numfashi Adam kuwa kuka yake kukan tausayin Usman Sadik ma kukan yake Aliyu Kuwa a k'asa ya kife kanshi yana kuka,
Shiko Usman cikin hard'ewar murya da juya kai yace,
"Sun cuceni sun cuci rayuwata sun rabani da mutun mafi soyuwa a gareni ina ma ina wurin in fanshi ran Hamma na da nawa ran Ammi sun cuceki sun kashe miki lafiyayyen d'anki suka bar miki ni wanda zama danima larurace".
sai kuma ya kalli Abba cikin wani yanayi da yafi kama da wanda baya hayyacin sa yace,
"Ashe duk hirar da nike da Hamma na watsiyace ashe yana barmin abinda har in mutu bazan manta bane Abba Adam Sadik Aliyu ko jiya da dere Hamma na yace ince ku gafarceshi fad'an da yayi a kan Ummul".
sai kuma ya ruggume gawar ya fara magana kamar zai bashi amsa cikin bushewar zuciya yace,
"Hamma na ba jiya nake cema in na mutu zaka zama gatana na ko?".
sai ya kuma kallin fuskar Hamman nashi yace,
"Hamma na ka tuna kace min zaka zama gatana bazaka zubdamin hawaye ba zaka min wonka kamin sutura sannan zaka dauwama dimun wa da'imun kana min addu'a har sai randa kabar numfashi,
to Hamma na Insha Allah zanyi maka wannan gatan har zuwa lokacin da nima zan biyo bayan ka".
sai kuma ya kalli Adam yace,
"Adam taya ni in yiwa Hamma na wonkan k'arshe a duniya".
Adam yana kuka da majina suka kamo gawar suka matso inda aka tanadi abubuwan buk'ata dan yin wonkan gawar,
Abba kam da Sadik zama sukayi suna ganin duk ta inda aka juya kan Hamma Umar sai yayi lagwas shiko Aliyu kuwa kuka yake da zafin rabuwa da d'an uwa,
shiko Usman nad'e k'afafun wondonshi yayi cikin bushewar zuciya ya rink'a wonke wuyan nashi da sauran wuraren da jinin ya taba sannan yayi mishi wonka yadda addinin musulunci ya tanadar,
bayan sun gama ya shiryashi tsab cikin likkafanin shi aka kawo makara motor da babu taya motar da ta zame mana dole shigarta bayan an sashi a cikine aka fitar dashi akayi mishi sallah bisa koyarwar annabi sannan aka d'auki Hamma Umar aka nufi gidanshi na gaskiya da shi,
inda Usman da Adam su suka sashi a makoncin sa,
Allah Akbar ko wanne d'an adam k'arshen sa kenan,
an gama binne shi ne ya Usman ya d'aga hannu yayi ta karanto addu'oi bayan sun gama ne aka fara juya baya ana tafiya,
a dai-dai lokacin ne Usman yaji wani irin suka da zogi a kahon zuciyarshi wanda ya fara ganin duniyar tana juya mai,
da kyar yake d'aga k'afafun shi har suka fita cikin mak'abartan suka shishishiga motocin su suka nufi Potiskum.


A gida kuwa Ammi da Inna suna shiga suka samu Anty Halima da matar Daddy da sauran yan uwansu duk sun taru suna zaune a barandar Nenne,
Ammi na shiga Nenne ta ruggumota suka had'a kai wuri d'aya suna wani irin kuka,
Halima kuwa da Anty Shuwa gefen Ummul suke zaune wacce tunda tazo batayi magana ba sai idonta da yake a zazzare,
cikin kuka Halima tace,
"Allah sarki Ammi wayyo ya Usman Ummul tashi ki cire rigar nan Ummu kar kiyi Ammi taga wannan jinin zai iya kawar mata da hankalin ta".
shiru bata kula Halima ba sai kallon Nenne da Ammi take Hajjajo da Inna ma kuka suke kamar zasu shid'e,
Ammi kuwa da Nenne sunyi kuka har idanu su sun rufe,
sai can Ammin ta kalli Ummul dake gefensu tana ta zaro ido tamkar idanun zasu firfito,
a hankali Ammin ta kalli Ummul d'in da k'aton cikin ta wanda jikin ta duk Jini,
kife kai tayi ta kuma sakin kuka,
amman Ummul sai kallonta takeyi kamar bata santaba ganin haka cikin kuka Ammin tace,
"Nenne kuka rahama ne kuka wani sauk'ine a garemu kusa min Ummul tayi kuka inba haka ba zai zauna a zuciyarta ku samin yarinyar nan tayi Kuka Ummul ki zubda k'ollah".
amman ina Ummul Allah bai bata damar kukaba,
har Allah yasa su Abba da Usman dasu Adam Sadik da Aliyu suka dawo,
suna shigo wo gidan Usman yazo ya kife kanshi a jikin Ammin shi yana magagi harce a nad'e yace,
"Ammi sun kashe miki lafiyayye sun bar miki nakasheshshe wanda rayuwarsa bata da tabbas Ammi zan kai kararsu".
cikin kuka ta ruggumeshi tace,
"Usman ya zamuyi da *RUBUTACCEN AL, AMARI* wanda Allah ya tsara mana Usman ina zaka kai kararsu waya gansu".
harce na k'ara nad'ewa yace,
"Allah Ammi Allah ya gansu kuma zan kai k'ararsu gun adalin sarki Allah zan had'asu da Allah ya bimin hak'kin jinin yan uwana musulmai Allah zaiyi mana hisabi dasu zubarmin da jinin Hamma na da sukayi Ammi babu kotu ko lauya ko alkali da zaiyi wannan shariyar sai Allah dan haka zan dawwama ina kai kararsu gun Allah zasuga saka makon aiyu kansu a ranar da gabbansu zasuyi bayanin rayukan da suka kashe Allah ya isar mana ana cutar damu musulmai a k'asarnan ana kashemu tankar kiyashi Allah ya isa! Allah ya isa! Allah ya isa jinin d'an uwana".
gaba d'aya sai gidan ya kuma cika da tasbihai dan samun sanyin zuk'atansu ita kuwa Ummul sai binsu take da kallo,
Aliyu ne wanda tunda suka shigo yake kuka sai yanzu Sadik ya kamo hannunshi suka k'araso cikin gidan suna shiga Aliyun ya fad'a jikin Ummul d'in yana kuka mai tarin k'una shi kuwa Sadik cikin rawan murya yace,
"Ammi mun kai Hamma Umar gidanshi yanzu addu'arki yafi buk'ata".
daga wannan kalmar Ummul bata kuma sanin inda takeba ko a wanne halin takeba,
ta sume cit suma mafi munu domin harda k'ok'olwarta tayi sanyi,
daga nan aka kwasheta akayi asibiti da ita Dr Bashir shike duba lfyar ta,
yayin da Usman Kuwa yake ganin suma hutune a wannan halin da yake ciki ba kuka ba suma sai tarin k'unan zuciya ga fargabar halin da Ummul take ciki.


Har tsawon kwana uku Ummu bata farfad'o ba hakan yasa yan uwa cikin wani sabon tashin hankali ganin haka Dr Bashir ya bada shawaran a fiddata woje,
haka kuwa akayi cikin kwanaki aka shirya fita da ita k'ark'ashin d'aukar nauyin gwamnatin jihar tasu aka fidda ita,
Egypt inda aka kai tsaye suka wuce Magrib Medical Center Cairo,
ita da Ammin Hamma Umar sai ya Adam tare da jagorancin Dr Bashir,
koda suka je Ummul saida tayi kwana 8 a sume sannan ta farfad'o koda ta farfad'o d'in kuma bata magana sai kallon mutane kawai,
duk bincike anyi da magani amman ba magana a haka aka sallamesu dan doctors sunce a koda yaushe zata iya magana,
an sallamesu da sharadin watan haihuwar ta na tsayuwa su dawo dan bugun zuciyarta yayi k'asa sosai bazata iya haihuwa da kantan ba,
a haka suka dawo gida dan hankalin mutanen gida ya konta.


randa Hamma Umar ya cika sati uku da rasuwa a ranar suka dawo,
suna dawowa koma yazo yanawa Ummul magana amman ba amsa,
bata ko d'ago kanta ta kalli kowa sai in Ammi ce tayi magana,
haka gaba d'aya farin cikin su ya koma ciki.

A daren ranar ne bayan duk an shiga an konta Ammi na zaune da Usman a gefen Ummul da ta konta tana kallon su ba magana,
Usman ne ya kalli Ammin cikin rauni yace,
"Ammi cikin kam baida matsala ko? ".
Ammin ta bud'e baki kenan zatayi magana Ummul tayi wani irin gigitaccen......




*By*
*GARKUWAR FULANI*
[07:03, 12/9/2017] 😄😄💲ⓂℹL£®😀😀: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 3⃣1⃣

*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇





*MOH ALLAH WUJI FURD'ATA*


*DEDDE Na Ummu uwata ta kaina mahaifiyata abin k'aunata abin Al'faharina yau kuma kirarinki da kikemin na yarintata na tuno lallai bani da tamkarku kida Abba na domin a yau Kirarin da kikemin zai iya kasan cewa a horkon ko wani shafina na littafaina inada kike cemin*

*KIN KINI KAN KAD'A DAMONI NA DAMONI GID'D'O MO FINA LARA GAID'O MO FINA SUKOYO LADDE ALLAH YAMAD'UM! KI D'OIDI YALETE! KI B'IB'B'E SAMMMETE! B'ENDUKI YAMETE! YORIKI TENETE! DAMONI NA DAMONI GID'D'O MO FINA LARAMO GAID'OMO FINA SUKOYO LADDE ALLAH YAMAD'UM ALLAH WANNE BARKA BOD'D'I DEDDE Allah fintine ba seto arana*
*wata kalmar sai a bakin Fulani*
*Wani Abu sai Uwa da Uba wannan kirarin duk ni kadai Aisha Aliyu garkuwa mahaifiyata da mahaifina kemin da sanya min albarka tun ina karama har zuwa yau Ya Allah ka sakawa iyayena da mafi kyawun sakamako ya Allah ka yiwa iyayena jagoranci har cikin jannatul firdausi DEDDE NA DA ABBAN ina sonku fiye da kowo har kaina Allah ya barmin ku😍😘😍😘*



*T*ayi wani irin firgitaccen zabura cikin tsananin
razana ta yunkura da karfi zata tashi tana wani irin gurnani,
ganin haka cikin karfin hali da firgici Ammi da ya Usman sukai saurin rik'ota suna mata addu'a,
ita kuwa gaba d'aya jikinta rawa yake kar-kar hatta d'an cikin ta sai motsi yake da k'arfi ta zazzaro ido tana waige-waige kamar me neman wani abu,
dakyar ya Usman ya kamo kanta da hannu biyu ya kwantar da ita a kan cinyar shi dan yadda take fisge-fisge Ammi bazata iya control enta ba,
ita kuwa Ammin sai shafa bayanta takeyi a hankali kwalla cike a idon ta tana furta, "hasbunallahu wa ni'imal wakil".
Shiko ya Usman yana ruggume da ita a jikin shi gaba d'aya jikin nashi sai kerma yake a karo na forko da yaji rauni da tausayin kanshi da kanshi ga taussyin halin rayuwar da Ummul ke ciki a zahiri yasan kuka rahama ne in dai da k'una a zuci amman shi kuka ya k'aura cewa rayuwarsa tunda Hamma enshi ya bar duniya baya gane halin rayuwar da yake ciki dazaran k'unan rai da k'uncin rayuwar sun tokare mai zuciya sai yayi ta aman jini yana murza kai da k'irji inko dere yayi sai ya tashi ya kwana nafilfili da nemawa d'an uwanshi rahamar Allah a hakan ne Adam ya gano wani abu daya shiga rayuwar Usman da zaran ya kad'aice sai ya rink'a juya kai yana mirgina kan nashi kan kafad'un shi kamar yadda yayi tayi lokacin daya zauna gaban gawar Hamma Umar abin a hankali ya zamewa Usman wani narkarwa ciwo mai zafi a ranshi da rayuwarshi da zaran ya tuno yadda yaga gawar d'an uwanshi sai kawai yayi ta juya kai jiki na rawa hakan yasa yanzu da zaran hankalin shi ya tashi ko ranshi ya baci sai ya rink'a wannan abun,
so yanzuma da Ummul take ta fisge-fisge da gurnani yana ruggume da ita duk da ba wanda yake gane me take fad'a hakan yasa sai ya rink'a juya kai yana murza k'afafunshi dan zafin da zuciyarshi ke mishi,
ita kuwa Ummul sai gurnanin takeyi Ammi kuwa duk sai zuciyarta ta d'anyace ta tasasu a gaba ta kife kanta tana kuka mai cike da dafi a zuciya,
Ya Adam ne ya k'araso cikin d'akin da sauri ya d'ago Ya Usman wanda ya kife kai a kan bakin gado yana jan numfashi da a wahalce,
Abba da yanzu ya iso da su Nenne da Hajjajo da su ya Sadik sai Aliyu suka shigo saboda jiyo k'arar da Ummul tayine,
cikin karfin hali Abba yace,
"Adam, d'aukemin Usman daga nan".
Usman najin haka cikin rawar murya da juya kai ya fara magana,
"Abba ku kyaleni dan Allah kubarni inkula da amanar d'an uwana ku barni in kula da amanar da Hamma na ya barmin".
sai kuma yasa hannu biyu ya rik'e kanshi yana juya kan a wahale yana k'ollah murya na rawa yace,
"Nanne ina zankai Ummul ? mezan mata ta sami sauki? Ammi ina soro kar d'an d'an uwana ya cutu ya zanyi na kare mutunci da lafiyar Iyalan Hamma na?".
sai kuma ya kife kai ya saki wani irin kuka mai k'arya zuciyar mai sauraro kuka yake har numfashin sa na cizga duk jikin shi sai b'ari yakeyi tamkar mazari,
Aliyu ne ya dafa kafad'ar shi cikin matsanancin kuka yace, "ya Usman tashi muje muyi nafila muroka mata sauki,
Hamma Umar yace min duk damuwa tanada magani a gun Allah, kutashi muyi musu addu'a zata samu sauk'i kullum Hamma Umar nace min Aliyu duk tsanani yana tare da sauki,
nasha in sameshi yana kuka in nace mishi Hamma Umar me yasa ka kuka? sai yace min Aliyu Usman baida lfy ina kukane wa ubangijina ina nemawa Usman lafiya a gun mai bada lafiyar,
dan haka muma muje mu nemawa Ummul lafiya a gun mahaliccinmu".
Yana kaiwa nan yaja hannun ya Usman suka fice suka nufi part insu al'wala sukayi sannan su fara nafilfili tare da karatun qura'an,
haka kowa na gidan yai alwala suka dukufa nemawa Ummul sauki gurin Allah,
Ammi kuwa na rungume da Ummul tana shafa bayanta a hankali tana tofa mata addu'o 'i har tasami bacci wanda takan razana duk mintina kad'an.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya cikin rashin wal-wala da kuncin zuciya yayinda kowanne ke buya yayi kuka san ranshi daga Abba, Hajjajo, Nanne, Adam, Sadiq, Aliyu, wanda b'angaren Ya Usman kuwa abun sai rahamar Allah kullum yana cikin aman jini ba k'ak'k'autawa kuma yanzu ya samu sauk'i yana iya kuka hakan yasa da zaran ya fara kuka kuma sai tari sai aman,
Ammi kuwa tamik'a lamuran ga Allah tadage wajen kula da Ummul wadda tazamo tamkar mutum mutumi duk da ansami cigaba a yanayin ta takan d'an sha tea duk da sai Ammi tasha rarrashi wonka kuwa sai Usman ya zauna gabanta yayi ta lallashi wani lokacin ya kife kai yayi ta kuka kafin ta yarda Nenne ko Ammi su mata wonka abu kamar wasa a zahiri Ummul ta zama tamkar zaucecciya komai sai an sata kuma tun randa Hamma Umar ya rasu har yau Ummul Allah bai bata bakin manana ba kullum kuma in dere yayi toh tashin hankali ya tashi kab zuriyar tasu basu da konciyar hankali da zaran an shiga za'a konta sai Ummul tayi ta firgice-firgice tana razana tana son guduwa sai ta rink'a b'uya ko tana k'ok'arin shiga duk inda taga luggu,
Usman kuwa haka zai zauna yayi ta kuka yana ga ya kasa tallafawa iyalan d'an uwan nashi a haka ciwon zuciyarshi ya tashi.



Yau Jumma'a da yamma,
ya Usman ne zaune gefan Nanne ya Adam yana tsaye Aliyu kuwa yana durk'ushe gaban Ummul sai kuka yakeyi duk sun zubawa Ammi da take bawa Ummul ruwan zam-zam da aka tofawa addu'oi wanda yanzu shine ruwan shanta,
domin samun sauki da sassaucin kuncin zuciya,
d'an ture hannun Ammi tayi sai kuma ta rink'a binsu da kallo d'aya bayan d'aya kai ta sunkuyar tana kallon k'aton cikin ta da d'an yaketa wintsil-wuntsul a hankali ta mik'awa Aliyu dake zaune yasata gaba yana kuka,
hannu alamar ya d'agata da sauri fuskarshi cike da mamaki yace,
"In d'agaki?".
dakai tamai alamar eh, aiko cikin jin dadi yamike yasa hannu ya d'agota ta mike sannan yasa hannu yana gyara mata d'aurin zaninta yana mai zubda k'ollah,
Ya Usman kuwa cikin saurin ya je bayanta ganin tana tangad'i kamar zata fad'i,
cikin k'arfin hali

4 Comments On RUBUTACCEN ALAMARI
avatar
shukra-sulaiman

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
shuraihu

1 year ago

Reply

Replying to shukra-sulaiman

Tnx too

avatar
fatima-idris

1 year ago

Reply

Nice novel

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fatima-idris

Aha tnx

Please Login or Register in order to submit comment