Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bin hanyoyin da nafad'a insha Allah very soon everything will be going okay"



"Uhunm nagode"

"Amm....... dana inason namiki wata tanbaya inbadamuwa."



Gyara zamanta tayi Dan haka kawai takejin dad'in fira dashi


"Inajinka Dr"



"Ammmmm fatan bakida miji tsayayye"?




Jimmmmm tad'anyi shuru kafin cikin sanyi Tace.


"Amma Wannan tanbayar fa Dr"?



"Hunmmmm kedai Ansa kawai Kuma gaskiya zaki fad'a mun,"



Tabbas idan tace tanada miji ko saurayi to tayi k'arya Amma bazaiyu tinyanzu tabada Mata ba dole taja Aji kodan gano yawan sonda yake Mata Dan tagano Yana sonta ne...





"Kinyi shuru Zeeyat kifad'a mun Mana"




"Uhunmm inada mijina kusan yayi tafiya ne Yana dawowa za'a d'aura Auren mu Amma kayi hak'uri sai Anjima Dr"


Kit takashe kiran,




Kasa motsi yayi tare da kafe Wayar da idanuwan sa da tantake Suka sauya launi zuwa ja zuciyar sa saibugun tara Tara take masa,

Dafe kansa yayi dake Sara masa Komai ya tsaya yadaina masa tafiya A k'wak'walwarsa,




Salif ne ya shigo Office d'in da sallama Harya zauna Zayyan baigansa ba domun hankalinsa gaba d'aya yana kan Abunda tafad'a masa,



Bubbuga table d'in Salif yayi

Sai A sannan Zayyan yad'an firgita had'i da dawowa duniyar da ya fad'a



Salif yace"Wai meke damunka haka nashigo nayi sallama na zauna but dik bakama cikin hankalinka meke damunka ne Zayyan,"?




Cikin damuwa yace,"Bata Sona, tanada mijinta"



"Wai wacece Ni nakasa ganewa kamun yarda zangane Dr"



"Hunmmmm Salif ina magana Akan Zeeyat wallahi inason ta kataimaka kabani shawara insamu Zeeyat Dan Allah"



Ganin dik yafiwani firgice masa yace,"Okay shikenan, itace tace Batasonka"




"Eh yanzuma tafad'a mun Kuma wallahi inason ta sonda ya zomun Abazata,"




"Shikenan yi hak'uri bakasan gidansu ba,"


"Nine likitan kakar Tama"


"To ai komai yazo da sauk'i kawai gun grandma ma zamu nufa kaga Acan zamu gano gaskiyar komai" ............ .........




_BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_



WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948



*ZAYYAN ZEEYAT PAID BOOK*





_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱..._



```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book....... And others now ZAYYAN ZEEYAT PAID BOOK Is loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🀱```




*FREE PAGE 35 TO 40*


............................... "Kana da Wannan Idea muke zaune Abanza Raina Yana b'aci? Mutafi kawai Salif daga Nan saican nasani ai"

Mik'ewa yayi Yana gyara zaman glass d'in Idanuwansa,.



"Kaga dakata Zayyan mubi Abin A sannu Mana kana kan Aiki Nima haka Kuma saimu bar patient's mutafi"





"To mezai hanamu tafiya bayan koda yaushe Ina Basu Lokaci na, Salif kagane Ana magana ne Akan Rayuwa ta fa,"




Jinjina Kai kawai Salif yayi tare da Mik'ewa suka fice,




Salif ke drive d'in, har Bakin gida suka Isa



Fitowa sukayi bisa sa'a saiga wani yaro yabiya Zayyan Yace"Kashiga gidan nan kasan kace ga likitan grandma yazo"



"To" kawai yaron yace ya shige gidan


Bajimawa saigashi yafito, yace"Wai Ance kashigo"


"To Abokina nagode gashi kasiye Alawa"


"Nagode"


Shiga gidan sukayi Atare,


K'atuwar tabarma ke shinfid'e tsakar gidan tana zaune sanye da glass d'in da ya Mata na idanuwan, gaisawa sukayi,



Tana d'an gani bawai sosai ba tace"Zayyanu ku zauna Mana yanzu kuke tafe? Lafiya daiko,"?



"Eh lafiya k'alau grandma munzo duba kine kinji sauk'i ko,"




"Eh Alhamdulillah tinda kaban wannan madubin nafara gani Allah dai ya maka Albarka ya baka zuri'a tagari,"



"Ameen ya Allah granma"



"Ina mama fa,"




"Yanzu tad'an shiga mak'ota Ana bikin suna ne,"



"Wannan Abokin ka ne,"? Tana nuna Salif,




Sake gaidata yayi

Zayyan ya Ansa da "Eh Abokina ne Kuma gun Aikin mu d'aya,"



"Masha Allah to Allah yayi Albarka,"




"Ameen"





Salif ya gyara Zama yace," grandma dama fa gunki mukazo, Muna da wata tanbaya konace rok'o,"



"To Allah yasa lafiya inajinku"




"Dama bawani Abubane Wai jikarki Zayyan tanan gidan Kun Mata mijine,"




Dariya grandma tayi"wannan jikar tawa maisunan Maza irin na likita A'a mudai bamuda labarin tanada shi koda Akwai Amma dai babu shine nawai"





Ajiyar zuciya Zayyan ya sauke maik'arfi Saida grandma taji tace"lafiya dai likita,"




Kafin ya Ansa Salif ya k'arb'e zance dacewa " Ya fad'a komar soyayya Grandma Naga yamiki gaskiya bawani dubaki yazo kawai yazo yaji idan Zeeyat bata da manemi shiyafara, A tak'aice dai Likita Zayyan yaga Zeeyat yana so Kuma idan babu matsala basai And'au lokaci ba muje muturo manya Ayi magana,"




Ayiriiriiiiii "kai natsufa ba hancin gud'a yanzu danayi Amma zantaka rawa idan Wannan had'in yayi, Ai Likita kana da mutunci tin yarda ka k'arb'e mu ranarmu tafarko nagane hakan, kada kaji komai indai jika tace to Anbaka insha Allah, kawai kabari muzauna muyi magana da sauran Ahli Amma komai zaiyi daidai insha Allah"





"Masha Allah grandma mungode sosai Allah ya tabbatar muna da Alheri, yanzu zamu tafi inyaso Nan da kwana 2 zamu dawo muji koma mene,"




Zayyan kuwa tsabar farin ciki yakasa cewa komai murmushi kawai yake,



"To babu damuwa Nima nagode Allah yayi Albarka, kaga ja'iri shi ko magana ya kasa wato nazama sirika kenan,"?



Dariya sukayi Salif yace"kodai kishiya kika Zama ba,"



Dariya suka sakeyi sunjima suna fira kafin suyi sallama suka rabu,..




Bayan tafiyar su saiga mama tadawo Zama tayi kusada grandma tana fad'in"wayazo gidan da Wannan turaren maikama wuri haka,"?



"Hunmmmm kedai Bari Jamila wannan likitan ne maiduba Idanuwana shine Kuma sunzo neman Auren Zeeyat kum na Basu"




"Kin Basu mama? Bayan bamuwani San Komai game dashi ba,"




"Kinfi Ni hangen nesa ne? Nace kinfini hangen nesa ne Jamila? Ko a'a nunamin zakiyi Ni banice nake da iko daku ba tinda bani nahaife ki ba," kuka tafashe dashi tana fyace majina tana cigaba da mita"taya zankai d'ayan ku inda zaicutu, bayan inason ku sannan ai ban Hana Ayi bincike kansaba,"




Matsowa kusa da ita tayi had'ida rik'o hannuwanta tana goge mata hawayen"mama kidaina cewa haka dake da Wadda ta Haifan bakuda banbanci Kuma komai kikayi daidai ne Allah yasa hakan Alheri ne,"



Murmushi tayi"Ameen kinji magana Kam Jamila dama ai da gangan nace haka nasan inban Miki haka ba basauka zakiyi ba, ai Ina Alfari daku Jamila Allah yamuku Albarka"





"Ameen Mama"






Cikin farin ciki suka rabu kowa yakama gabansa,


Zayyan baisake Kiran Zeeyat ba dik da hakan nadamunsa Amma ya daure,



Nata b'angaren ma ganin baisan kiranta ba saidik tadamu tanajin haushin kanta na masa k'aryar da tayi Allah yasa dai ba hak'ura yayi ba,



Aunty tashigo tasame Ad'aki tabugu tagumi,


Zama kusa da ita tayi tace"Zeeyat meke damunki haka,"



"Ba Komai Aunty" tafad'a tana neman wayance wa




"Hunmmmm Zeeyat kenan kinzata Akwai Abunda Zaki b'oyemun nakasa gano kinada matsala? Oya gayamin meke faruwa Ni k'ad'ai gareki sister so fad'amun"



Bata b'oye Mata komai ba tafad'a Mata,


Dariya sosai Aunty tayi sannan tabata labarin zuwansa har gida dama yarda sukayi da grandma,



Bud'e baki tayi tace............................







(Wash nagaji ga Ciwon Idanuwa Ina fama kutayani Addu'a Allah yaban lafiyar idona)





_BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_




Whatsapp number 07064904617 or call 07031012948




*ZAYYAN ZEEYAT PAID BOOK*





_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱..._



```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book....... And others now ZAYYAN ZEEYAT PAID BOOK Is loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🀱```






_(((((Second to the last Page insha,. Littafin na k'ud'i ne 300 ne kawai idan kin biya saiki Sami duka complete d'in sa,.. Ammafa idan kinsan Dan kifiddamun Abu waje Zaki siya Dan Allah kibarmun kayana kada siya, idan kika fitar bayan kunsiya kuda Allah......))))_






*Page 45 to 50*



Cike da mamaki tace"Aunty yazo gida fa kikace? Kuma neman Aure na, Amma taya hakan tafaru bayan bansani ba,"





"To uwar tanbaya idan labarin kike so ai sai kije gun grandma Acan Zaki Sami labarina Komai,'




"Haba my Aunty ki gayamin Mana kinsan da kunya naje musu da maganar ba"



"Oh nice bakya kunya ta ba, Ai mama tace Bata yarda ba Wai bamai Miki Auren Dole tana can tana damuwa Wai za'a miki Auren Dole, batasan kinjima da sonshi ba"



Hmmmmmmm Aunty dai



........................................







Palourn cike suna ta fira saboda daddy yadawo,


Daddy yace"Wannan karon fa bazan d'aga maka k'afa ba Son Aure zakayi ko Kuma ni na sama maka koma wacece da kaina"



"Haba Daddy yanzu fa Anwuce stage d'in Auren Dole but Ni Zayyan Akeson ma,"





Dariya k'anwar sa Nawal tayi had'i da cewa"Allah Daddy kama sa inba haka ba, bamusan wadda zata masa ba, kowacce yace baya so why"





"Zan doke bakin fa, Nawal,"



"Ah Agaban nawa Zayyan Matar tawa guda,''?





Dariya su mommy sukayi kawai,.




Daddy Yace"ko Hiddat Zamu baka ne"



"Dama kuwa tana sonshi wllh kwana biyu kawai batazo gidan ba neman sa, inaga basa k'asar ne,"




Dariya sosai Nawal ta tintsire da ita, sanin ko ganin Hiddat bayaso yanzu ma maganar ta kawai da Akayi har Mood d'in sa ya sauya, shi kanshi Nawar sheda ne kan hakan idan bazai manta ba Akwai randa saboda ita kawai ya fasa Attending meeting d'insu dik da ko irin mahimmancinsa Amma saboda kawai tashiga motarsa ya wuce da ita yasa zuwa gaba d'aya yabar motar ya koma gida,





"Ya haka ku kunsamu gaba sai dariya shikuwa yawani d'aure fuska haka ita Hiddat d'in ce Abun dariya gunku shikuma Abun Haushi,"?




"Daddy Dan Allah kadaina mun maganar ta wallahi inada wadda nakeso Kuma har gidansu nayi magana sunce ma sunason ganin manya na Ni ita kawai nakeso daddy"


Mik'ewa yayi Yana wani cin magani zaibar gurin


"Zonan son yimin bayani wacece ita,"?




"Sunan ta Zeeyat, Kuma mahaifinta yarasu suna tare da mahaifiyar su ne, wallahi inason ta daddy sosai"




"Hunmmmm badamuwa son kafa d'amusu gobe zamuje"



"Dan Allah Daddy,"?




"Ina wasa dakai ne,"?



"A'a daddy kayi hak'uri, inason ka Daddy I love too," kiss yakaiwa Daddy Ahannu sannan yabar wurin cike da Murna





" Hunmm kunga Sai farinciki yake lalle son Yana son yarinya" cewar Mommy




"Allah dai ya kaimu gobe komai zai wuce, Allah yasa hakan ne mafi Alheri"



"Ameen"





Yana komawa d'aki ya kirata tana kusa kuwa tad'aga da sallama




Gaisawa sukayi


Kafin yace"Abar Sona,? Albishir zanmiki Mai dad'i Daddy na yadawo sannan yace zasuzo neman Auren ki gobe"




"To bana fad'a maka inada miji ba"


Cike da zolaya tayi maganar,



Dariya yayi"kinason kashe Zayyan d'in naki tinkan yaga yaranmu da jikokinsa"




"Bakajin kunya ta ko Dr,"




"Hunm Ni banason Dr d'in nan wani sunan masoya zaki ban,"




"Goben da yaushe,"




"Yeeee kindai yarda yarda kizama mallakar Zayyan I'm so happy today, wannan shine Rana mafi dad'i gareni saiko randa zamu kasance Dani dake Ad'aki d'aya gado d'aya shinfid'a d'aya da..."


Kit takashe kiran Dan talura Zayyan ba k'aramin D'an soyayya bane, tana mallakarshi tagama sa'a gaskiya,

Cike da farinci ta fad'awa Aunty cewar iyayen Zayyan zasu zo gobe,




Zayyan kuwa dariya yayi " Zaki shigo hannu yarinya nayi maganin kunyar duka,"




..................



Yayan Zeeyat yadawo Angaya masa Komai game da Zayyan shida mijin Aunty salma Kuma Susan Dr farin sani mutumin kirki ne,


Ayanzu hankalin Mama yaya kwanata Kuma ita kanta ta Aminta dashi sosai,



Washe gari iyayen Zayyan Suka zo kawun Zeeyat da mijin Aunty salma zuwa yayanta sune Suka tarbesu komai cikin mutunci daddy yaji dad'in hakan Dan haka daddy Yace suna buk'atar Nan da sati 2 kawai Ayi bikin Kuma sun d'auke wahalar komai kawai Kai Amarya sai Abinda ba'a rasa ba ko riyar biki zuwa bidi'a dik Basu buk'ata,

Haka yama kowa dad'i.





Murna gun *ZAYYAN ZEEYAT* Ba'a magana ga soyayya Mai k'arfi da sukewa juna.




Rana Bata k'arya Saidai uwar D'iya taji kunya inji hauwasawa wannan Karin maganar ai tamuceπŸ’ͺπŸ’ͺ🀩



Yaune dubban nin mutanen masallaci A sallan jumu'ah suka shaida d'aurin Auren MASOYAN biyu *ZAYYAN DAKUMA ZEEYAT* Akan sadaki naira dubu 1000.000,

Bakin Ango Ranar yak'i rufuwa hakama Amaryar yaudai komai ya k'are *ZAYYAN ZEEYAT* Sunzama ma Aurata.........................





(Nagaji zanhuta..........)




_BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_




WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948




*ZAYYAN ZEEYAT PAID BOOK*





_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱..._



```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book....... And others now ZAYYAN ZEEYAT PAID BOOK Is loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🀱```





_Last Free page daga wannan Free page ya k'are idan kana kina buk'ata complete d'insa ko son kasancewa Dani koma littafin *ZAYYAN πŸ’ž ZEEYAT* to kibiya kabiya k'ud'in ka 300 ne kawai,......... Saturday 17/12/2022 December_



*Last Free page 51 to 55*




Sosai suka Mata fad'a had'i da nasiha Akan Rayuwa dama Abubuwan yau da gobe da zata iya fuskanta,.




Sosai tasha kuka, Ahaka dai Aka turo motocin D'aukar Amarya mota 5 Aka kaita gidan ta tsararre Wanda yasha kyau, Zayyan ya kashe dukiya Agida hatta iyayensa basusan shine yayi wasu daga cikin kayan gidan ba kawai yabar su Akan danginta suka kawo mata Abunta,



"Kaga Salif wallahi idan Baku fito ba nida kaina zan Kai kaina, haba tind'azu Ace Ni Ango nashirya sai ku y'an raki zaku tsaya min delay Allah zankai kaina kuwa"



Hahhhhhhhh"lalle Zayyan yanzu sai ka Kai Kanka kunji Ango mairawar Kai ba Wanda yafi Amarya ma" cewar Nawar




"Ai baka sani ba Nawar Ni harna fita rawar kan, kunga naku wasa ne kusa meni mota, ba zaiyu kusa Amarya ta guda d'aya tall zaman jira A gidan nan ita d'aya ba,"



"Kamar kasan dik sun watse Dan k'awar ta Nafy ta gayamin sunwuce Wai basa irin wannan zaman Dan ba Addini yazo dashi ba,"




"Kaji ba ai Matar tawa kamila Kuma malama ce, shiyasa nake sonta wllh Ai macce Mai lilimi duniya ce wallahi bazaka fahimce hakan ba saika mallake ta, nidai natafi"

Baijira Ansarsu ba ya fice , ganin ya fita sukabi bayanshi suna dariya.



Gidan ya tsit ba kowa dika sunkama gabansu, itace kawai tsakiyar gado A zaune lokaci lokaci takan share hawayen ta ga tsoro dake damunta Dan gidan babba ne sosai




Shigowa sukayi Palourn suka zauna kan k'asaitattun kujerun dake palourn,

"To Kun rakoni ai saiku juya ku koma ba," Zayyanu ya fad'a Yana k'okarin cire babbar rigar jikinsa




"Au wato Aci moriyar ganga Ayada goronta bayan munkawo ka saimu juya,"



"To idan Baku koma yanzu ba yaushe zaku koma nifa nagaji kutafi Kona samu nahuta wallahi"



"Amma ai kabari muga Amaryar sannan muyi muku Addu'a ba,"




"Ah mungode Addu'a basai kunga Amarya zaku iya yintaba nifa kishi gareni wallahi haka kawai bazan Bari yau dare na nafarko Abokaina su kalle min Mata ba A'a wallahi kutafi nagode Saida safe, kujamin k'ofa,"

Yana Gama maganar ya haye step-step d'in da zai sadaku da d'akuna 4, 2 nata 1 d'aya nashi saiko d'ayan d'aya Bari Dan yaransu masu zuwa Nan gaba.



"Awo lalle mutumin nan da gaske take to kadaima y'ar mutane sannu da Bata Saba ba," cewar Salif



Dika sukayi dariya sannan Suka fice.





Da sallama ya Shiga d'akin bayan yayi nocking





Asanyaye ta Ansa masa sallamar



Tsayawa inda yayi inda yake saboda daddad'an turaren ta daya masa Mara ba, lumshe Idanuwansa yayi,



Ahankali ya k'araso bakin gadon Yana fad'in"Amaryar Zayyan yau Allah yayi *ZAYYANπŸ’ž ZEEYAT* sun mallake juna tahanya mafi tsarki Mata dakuma miji, farin cikin da nake ciki sam bakina bazai iya fad'ar Saba inasonki fiye da yarda zuciya ta take bugawa Ina fatan kada ranar rabuwar mu tazo ZEEYAT"




Ahankali tad'ago Karo nafarko da ta k'are masa kallo,


"Dik Abunda kakeji game Dani Zayyan Nima Ina jinsa kawai Ina tsoron watarana kamun halin naku na maza narashin Tabbas randa zanbu k'ace taimako daga wurinka Amma bazan samu ba saboda Lokacin banice gaban ka ba kana...,"




Shiiiiiiiiiiiiiiiii d'aura yatsan sa yayi kan bakinta had'i da girgiza Mata kai,


"A'a ZEEYAT kada kiyi wannan mummunan tunanin mara tushe da kinsan yarda nake jinki ko Alama bazaki furta hakan ba, maza dika maza ne nayarda Kuma nasan da mayaudara Amma Ahankali Zaki fahimce Zayyan dinki ya banbanta da sauran domin *ZAYYAN πŸ’ž ZEEYAT* Masoyan da Aka halitta Dan juna ne ruwa ko iska bazasu rabamu ba I love you Zeeyat with All Hart and soul, Kinga kukan ya Isa saikace Auren dole kodai yanzu fa Andaina kuka yarinya Kinga dik yunwa takamani ga Ciwon Kai, kema kinajin yunwa ba, Bari nasamo Muna Abinda zamuci,"



Yana Gama fad'in hakan yafice, da kallon so da k'auna tabishi harya fice Ajiyar zuciya ta sauke tabbas Zayyan ya sace zuciyar ta dayawa,.




Ba'awani jima ba saigashi yadawo d'auke da plate da k'aramar wuka da k'atuwar leda hannunsa,




Kasan grass carpet ya zauna Yana nannad'e hannun rigarsa, fidda Mayan kaji 2 yayi ya zuba kan plate din da tare da tsiyaya jus cikin kofin,


Juyawa yayi yaga still tana zaune inda yabar ta ko motsawa batayi ba,


"Kinga Madam ki sauke kicika cikin ki kada kisa kan tarihi kice gidan Dr Zayyan ba Abinci sanda nafara zuwa da yunwa yabarni to sauko,"



Da sigar Zolaya yayi maganar had'ida wani karya murya Kamar macce,


Dariya Sosai yabata kafin ta sauko tazauna nesa dashi k'ad'an


Tura Mata k'atuwar zakar yayi had'ida yagar d'aya yafara ci Abinsa Yana Kora lemunsa Mai sanyi,



Kallonsa kawai take Yana da barkwance cikin k'ank'anen lokaci harta sake dashi,



Kallon ta yayi yaga Batama tab'a kazar ba Kuma gatanan Wai k'udundune cikin mayafi,

"Inaga saina bar d'akin Nan nafita waje sannan Zaki Samu kisake kici Abinci, Amma kisani gidan Zayyan ba'a kunya" Yana Gama fad'ar hakan yaja plate d'insa yayi waje,



Sai A sannan tasamu taci sosai




Koda yadawo harta Gama tana zaune tayi shuru


Sallama yayi ta Ansa


"Kingama bakima ci sosai ba ko haryanzu bak'unta ce oho? To kije kiyi Alwala muyi salla mu k'ara godewa Allah dama rok'ar Allah kariya Daga masifa ko wacce iri,"


"To kawai tace tamik'e tashiga toilet d'in



D'akinsa yakoma ya watsa ruwa had'ida sanya farar jallabiyar sa yafito,


Harta shinfid'a musu sallaya tana tsaye tana jiransa.




"Yi hak'uri nabarki kinata jirana ko Amarya ta"





Tada sallar sukayi Kamar yarda Addini ya tanada haka sukayi tare da Addu'o'i dafa kanta yayi ya mata Addu'a sannan ya Mata tanbayoyi dik tabashi Ansa,


"Kinajin bacci ba,"



D'aga masa Kai tayi Alamar eh



Ya lura dik tawani tsorata dashi Kuma zahirin gaskiya bazai iya hak'uri yau ba Amma kuma yana Jin tausayin ta.

"To jeki kwanata Saida safe"



Hawa kan gadon tayi takwanta cen k'arshen gadon tawani takure guri d'aya.



Murmushi kawai yayi ya Maida hankalin sa kan Alqur'ani dake gabansa yaci gaba da karantawa,.

Saida ya d'au tsawon lokaci sannan ya dakata mik'ewa yayi tare da maida Komai mazaunin sa sannan yadawo kan gadon tini tayi bacci saboda gajiyar biki,.




Cikin dabara yaka hannunsa ya zaremata hijab d'in, Ahankali ya soma sarrafata, cikin mafalki tasomajin sabon yanayi saita basar Azaton ta mafalki ne kawai, Amma Jin manyan Abubuwan yasa ta farka, tabbas ba mafalki bane zahiri ne Dan Zayyan ne ke sarrafata kuka tasoma masa tana matsawa baya



Cikin wahalalliyar murya yace"Dan Allah kiyi hak'uri ZEEYAT kamar yarda Baki tab'a yi ba haka Nima naki k.g please kitausa min kibar Ni nakusance ba zafi Zeeyat,"



Tausayi yanata ganin Yana ta lallab'ata hakan yasa talafe tabashi damar yin Aikinsa yarda yaso, Saida kashe Mata jiki da Zafafan sak'wannin sa sannan yaraba ta da kayan jikinta ya nufe hanyarsa gadan gadan...






*Nidai Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🀱 ficewa nayi waje Dan ban iya ganin k'wanba, Kuma bazan gano Haramun ba, E Mana Haramun Kam Sirrin wasu ai Haramun ne ni nagano, Allah ka hanamu kallon Haramun da idanuwanmu, Kuma Allah katsera tar da hannayena daga rubuta Haram ko batsa,.... Idan saina saka batsa da miyagun Abubuwa zaisa ku k'aunace littafaina to Saidai karku k'aunace su Dani Baki d'aya, kusani dik Abunda Marubu ya rubutu to gobe k'iyama za'a tayar damu had'ida tanbayar me muka rubutu? Mutum nawa ya fad'a halaka Saboda littafanki? Mutum nawa suka shiryu suka gyaru Saboda littafanki? Idan babu Kisha kulki Kuma tinda ganan Azaba zatayi ta bibiyar kabarinki nadik sanda wata ta Aikata mugun Abu saboda littafin naki, ki daure ke mairubuta b'ata Kan littafan ki kidaina domun Wllh bayada Amfani.... Saiwata hujjar banza da zaku bayar Wai Ai Kuna bada styles na kwanciyar Aure, Hunmmm styles ba ? Ke sauna ce da Zaki zauna sai wata takoyar dake? To kiyi k'okari kirik'a kauda idanuwan ki daga karanta littafan batsa Haramun ne wllh kema kiyi k'okarin daina ruguza tarbiyar y'ay'an mutane tahanyar rubutun banza Dan neman kud'i ko suna ko d'aukaka wllh Haramun ne baida kyau..... KIJI TSORON ALLAH NAJI TSORON ALLAH SUJI TSORON ALLAH, ZAN MUTU ZAKU MUTU ZASU MUTU ZAMU MUTU DIKANMU BAWANDA YASAN RANA AMMA MUNSAN DIK ABUNDA MUKA SHUKA ZAMU GIRBA TO K'OK'ARIN SHUKA ALKAIRI ALLAH YASA MUDACE.. MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🀱 NI MAI WA'AZANTARWA CE ZUWA BADA SHAWARA KAWAI ALLAH YABAMU IKON D'AUKA NAGODE...............*




_WASHE GARI_



Tinda safe nalek'a gidan hangosu nayi manne da juna duka Rabin jikinta na kansa ya rik'ota tafito daga wanka sai wani b'ata fuska take, tana yarfa hannu,




"Sannu yi hak'uri nine ko, kik'ara daure zauna bara na d'auko Miki magani sannu my Honey"



Zaunar da ita bakin gadon yayi ya d'auko Vaseline da kansa ya Mata dik wani shiri ya d'auko Kaya zai samata saiwani sunkuyar dakai take



Rik'e hannun sa tayi Tace,"kawai kaje kad'auko min maganin zan shirya dakaina,"




Murmushi yayi"Kinga Bafa Abinda bansani ba dama kindaina wani kame kame ko kin manta jiya face to face Akayi da....,"



Jifarsa tayi da pillow gadon tana kukan shagwab'a"banaso kadaina banaso,"



Dariya yasa had'ida cafe pillow Yana mik'ewa "to nadaina kada kiyi kukan zanfita shirya"


Ficewa yayi yana dariya,

Itama murmushi tabisa dashi, mik'ewa tayi tashirya,




Yana fita saiga driver yakawo sak'on Abinci inji Mommy, k'arb'a yayi bayan sungaisa yawuce.




D'aukar basket d'in yayi yashi ga dashi ciki, harta Gama shiryawa ,



"Dear zokici Abinci nasan nasaki Jin yunwa Daren jiya ko,"? Yana matse dariyarsa,







Kamota yayi ya d'aura ta kan cinyarsa ya Fara bata Abincin Abaki tintana nok'ewa harta gaji tabada Kai, Dan talura Zayyan D'an soyayya ne, sai shagwab'a take ta zuba masa Yana biyeta.....





*************""**********


"What? Kinko San me kike fad'amun Ayshat? Aure fa kikace Zayyan d'in nawa,"?




"Hunmmmmm na Zeeyat dai ingaya Miki inma kina tantama Kinga zahiri," cewar Ayshat tana nuna mata pic d'insu da tasamo yanzu A Media wata k'awar ta zina tasa,




Kallon photon tayi tare da jefar da wayar tace"Bala'i wallahi Akwai tashin hankali Zayyan d'in nawa zai Aure wata bani ba Kuma Banda labari, wallahi Akwai rigima da tashin hankali na rantse

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment