Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da jarabar sa, tsuka yayi ya ce "mace har mace babu tattalin miji".
Maganar ta doke ta sosai, amma ko kallon shi batayi ba, tana ganin ya shige d'aki ta tashi ta zauna, memakon maganar ta bata haushi sai tafara dogon nazari akai, gaba d'aya jikinta yayi sanyi tafara tunanin anya ba gaskiya ya fad'a ba, can dai ganin zata sa kanta adamuwa tayi kwanciyar ta a falon tana tuna bak'in halayen Sabitu, da wannan tunanin tayi bacci zuciyarta far haushin sa.

Gogan naku kuwa ko ajikin sa, wayarsa ya d'auka ya danna k'ira wa Saleema sukasha hirarsu duk da baison jin muryar amma ta iya hirar dayake so, anan ta shaida masa gobe zata koma garinsu saboda acan za'a d'auko ta.


Da safe Sabitu ya shirya a gurguje saboda kada Saleema ta tafi basuyi sallama ba, dai dai k'ofar gidan Alhaji Ma'aruf yaga Drivern sa na fito da akwatinan lefen da yayi wa Saleema, yawancin kayan ciki Saleemar ne ta siya da kanta, akwatina 5 masu shegen kyau, yana gani aka zuba a but d'in motan Alhaji Ma'aruf, har zai k'arasa sai yayi turus.

Kyakkyawan Saurayi yagani ya fito daga cikin gidan, jikinsa sanye da k'ananun kaya amma kallo d'aya zaka masa kasan masu tsadane, gashin kanshi dake kwance luf irinna asalin bafulatani wanda yasha gyara sai shek'e yakeyi, hanunsa d'aure da agogo sunfarin Gucci, farine sol kamar katab'a jini ya fito, kallonshi Sabitu yakeyi ko kyaftawa babu, ga wani tsananin kamar da sukeyi da Saleemar sa harta b'aci, nan ya tabbatar yayan Saleema ne.

Da sassafar ya isa wajen amma yana isa saurayin yana shiga mota cike da wani irin taku na gayen da aji ya zauna masa.

Alhaji Ma'aruf ya matso kusa dashi da sauri ya ce "Sabitu kaine tafe da sassafe"?

Cikin jin kunya ya ce "dama nazo akwai sak'on da zan bawa Saleema ne".

Alhaji ya ce "Ashha, ai tun asuba ta tafi, taurin kunnene da ita ina Bauchi ina Gombe nace ta bari tabi d'an uwanta ma tak'i, amma ai gobe zuwa dare an kawo maka amaryar ka kada kasamu damuwa"!
Ya k'arasa maganar yana bubbuga kafad'an Sabitu, murmushi Sabitu yayi ya russuna ya ce "nagode oga, Allah ya k'ara girma".

Kada kadamu Saleema ai 'yata ce, idan kana buk'ar wani abu ka turomun ko ta text ne".
Godiya Sabitu yayi sannan yabar gidan.

Sanin gidansu acike da bak'i yasa ya koma gidanshi domin ya huta.


*GARIN GOMBE*

Innah tana tsince zogale duk kewar Elham ya dameta, idan ta tuna rigimarta takanyi dariya, lokacin k'arfe 12 na rana taji Sallamar almajirin ta dake zuwa mata aika, tana d'aga kai taga suna shigo da akwatina shida 'yan uwanshi, mik'ewa tayi ta ce "kai Garbati a ina ka samo wa'innan jakkunan".
Yana dariya ya ce "Alk'ur'an Yallab'oi ne ya dawo yana waje".
Tana jin haka ta gane Saleem yake nufi domin yallab'oi yake cemasa, washe baki tayi cike da d'oki na murnar ganinshi ta ce "A lallai muna da bak'o, zo kaje kafad'awa khairat tayi maza ta shirya Elham ka d'auko ta mutumin nata ya dawo".

Da gudu kuwa ya fice shima yanata murna domin suna mqtuk'ar son Saleem, mutum ne da bashi da girman kai kowa nashi ne, akwai zafi amma sai an tab'o shi ne, don haka babu wanda ya tab'a lura da zafin nashi, har fiye da minti 30 Bai shigoba yana can yana gaisawa da mutane, Innah sai lek'e takeyi domin ta matsu ta ganshi tayi kewarshi sosai.

Dak'yar yasamu ya shige gida harda d'an gudunsa, gun Innah yayi data kasa b'oye farincikin ta, ya rungumeta cike da kewa, dariya tayi ta ce "sakarni yanzu jikin ba k'wari idan ba nema kake ka k'arasa ni ba".
Saketa yayi amma yana rik'e da hanunta, kallon shi tayi k'asa da sama gaba d'aya ya canza sosai alamar jin dad'i yafito sosai ajikin sa.

"Mu shiga ciki kasha ruwa ka kwaso hanya, memakon kayi waya a tanadar maka abinci sai kayi durowan yesu"!
Maganar tabashi dariya ya ce "Ina sarkin kukan naki naji gidan yau shiru".

Ya fad'a yana d'an dube dube, baki ta tab'e ta ce "tanacan gidan Sameer kasanta bata son zama waje d'aya, duk inda tasan za'a rik'a biye mata toh akwai mannewa".
Dariya yayi kafin yayi magana sukaji Sallamar Khairat, tana goye da Elham sai cakulkuli take mata duk ta haukata ta, ai tana arba da Saleem ta diro da gudu ta fad'a jikinsa tana dariya, sai kuma ta saki kuka tana shure shure, dariya Khairat tayi ta ce "wlh Innah yarinyar akwai iskanci, bakiga yanda tasa nayi ta dariya a hanya kamar sabon hauka, idan nasauk'e ta kuma tayi ta kurma ihu".
Dungure kanta Innah tayi ta ce "Ja'ira bakya sake zuwa ko ina ba ae".
Saleem daya zuba mata ido yana dariya ganin dagaske take kukan, rungumeta yayi ya shiga rarrashin ta yana cewa idan kinyi shiru zan baki sweet".
Shiru tayi tafara jan ajiyar zuciya, Innah ta ce "Ohh ni Habiba, me aka miki kike kukanne".
Mele baki tayi ta ce "Bazan sake zamaba Uncle Saleem zanbi".

Khairat fita tayi ta shigo da basket d'in da suka zo dashi, a gaban Innah ta dire ta ce "gashi Innah a baiwa bak'o nasan baki dafa abinci dashi ba".

"yo inama nayi girkin yazo ba tsammani".

Dariya sukayi duka sannan aka shiga gaisawa.

Sameer ma anan ya wuni suka ta hiran bayan rabo, nanfa Saleem ya shirgo musu k'aryar aikin gwamnati wani ogansa ya samar mishi, duk wata yana d'aukar albashi me yawan gaske kasancewar yayi karatu sosai duk sai suka yarda, ya ce musu har gida ya siya a Bauchi, su kuwa sukayi ta murna Innah nasa mishi albarka.

Akwatinan daya zo dasu ya janyo yafara musu bayani, "wannan kayan ogana ne zai aurar da 'yarsa angama komi Allah yamata rasuwa, shine mijin ya ce bazai amshi komi ba don haka Ogana yabani yace nakawo wa k'anne na, gashi k'anwar tawa bata girma ba".
Ya gama maganar yana shafa kan Elham datayi bacci a cinyar sa, Sameer ya ce "Babban Yaya dama wlh jira muke kadawo kafito da mata 'kaga sai ka ajiye akwatinan kayi auren ka dashi".
Harara ya watsa mishi ya ce "malam ina fad'a maka na samu aiki kana maganar aure, ni gaskiya ba yanzu ba".
Inna ta sake baki ta ce "Haba Saleem, kana ganin k'anin ka tun yaushe yayi aure ace kai ba dama amaka magana sai rai ya b'aci"?

Susa kai yayi ya ce "Innah yanzu dai ki rabar da kayannan daga baya sai muyi magana, tunfa wancan shekarar kike cewa kin samar mun mata ko kin fasa ne"?
Dariya tayi ta ce "shak'iyyi tashi maza kaje ka huta, kaima Sameer kaga dare yayi kaje Allah ya muku albarka, da Ameen suka amsa sannan ta shigar da Elham d'aki dake bacci harda minshari.
2/1/20, 5:10 PM - imusamuhd(professor): πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯
*D'AN DAUDU KO D'AN LUWAD'I*
πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

Page 5

_*RUBUTAWA:*_
*AISHA BICHIKI*
_Princess Eshat Aysm_



_wallahi cmmnt d'inku yayi ta bani dariya🀣🀣 nidai ba ruwana idan Saleem yajiku kuna had'a shi da Saleema🀣_
_Sabitu yananan yana ja muku Allah isa da kuke had'ashi da aljana_🀣🀣🀣




https://m.facebook.com/AISHA-Bichiki-265061884086077/posts_to_page/?ref=opera_speed_dial



✍

Washe gari ta shiga hidimar raba akwatinan da Saleem yazo dashi, da kanshi ya kwasar wa Elham kayan kwalliya masu yawa, Innah sai tsiya take musu wai zata ga a fuskar da za'a shafa wannan tarkacen, dariya yayi ya ce "kedai Inna yi mata wanka kiga irin kwalliyar da za'ayi, Elham sai murna takeyi tana mak'ale da shi, duk cikin mutanen da tasani a rayuwarta tafi son Saleem, duk da kowa na k'ok'arin ganin farincikinta tafi k'aunar Saleem, idan baya nan ne kawai take mak'alewa Sameer.

Kusan rabin kayan wa Khairat aka d'ibarwa.

K'arfe 2 na rana Saleem na zaune gaban Innah yanata shirga mata k'arya wayarsa dake hanun Elham ta fara ruri, k'arb'a yayi yad'an saci kallon Innah, ganin hankalin ta baya kanshi yasa ya fice da sauri, yana gama amsa wayar ya dawo ya zauna a gaban Innah, akwatin gabanta wanda ya tara tarkacen Elham ya matsa dashi gefe ya ce "Innah k'iran gaggawa ne ya sameni yanzu".
Da sauri ta d'ago tana kallon shi, murmushi ya sakar mata ya ce "Innah kada ki wani d'aga hankalin ki, duk sati zan rik'a zuwa miki kinsan yanzu tunda nasamu aikinnan ba hutu kuma, yanzu haka Oga yace nayi maza nazo akwai takaddun da zan bayar nawa, inaga k'arin girma za'ayimun".
Ajiyar zuciya Innah ta sauke ta ce "Shikenan Saleem Allah ya tsare hanya, ka kula da aikin ka sosai banda wasa dashi, a zamaninnan ba kowa ke samun aiki ba, tunda kasamu sai ka rik'e shi hanu bibbiyu, sannan ka nutsu sosai ka samo wacce zaka aura domin nagaji da ganin ka haka".
Hannuwan shi ya sanya ya tallafo fuskarta ya manna mata kiss yana murmushi ya ce "Insha Allah Inna duk abunda kike so shi za'ayi, kada Kiyi kewata da yawa inanan tare dake a zuciyata, inaso wataran na gina miki k'aton gida yanda munafukannan zasuji haushi Innah".

Hawaye ne ya gangaro mata, da sauri ya shiga goge mata su yana fad'in "Menene haka Innah, kina so ki hanani tafiya ne"?
Murmushi ta k'wak'ulo ta ce "Farinciki ne Saleem".
Had'a fuskan su yayi yana dariya, Elham da tayi tsaye tana kallon su sai taji babu dad'i jin wai Saleem zai tafi, da sauri ta fad'a bayanshi ta fara kuka tana cewa "zanbika Uncle Saleem".
Juyowa yayi ya ce "haba sweet heart kema kinsan dole dake zan tafi, d'auko jakar kayanki kizo mutafi".
Cike da murna ta ce "na gidan Aunty Khairat".
D'agata yayi sama yafara juyata tana k'yalk'yale dariya ya ce "sako hijabi muje mu d'auko".
Da gudu ta fad'a d'aki tana murna, Inna sai murmushi takeyi.


Tundaga zauren gidan ta fara k'walawa Khairat k'ira tana ce wa "ki fitomun da kayana zamu tafi da "Cweet heart d'ina".
Dariya Khairat ta fito tanayi ta ce "ohh zanga randa zaki daina ce masa Cweet heart, wlh matarsa fasa bakin ki zatayi".
Dariya Elham tayi domin bata fahimci ina maganar ya dosa ba".
Shi kanshi Saleem dake bayansu dariya yakeyi.

Da wayo da dabara yabarta a gidan ya d'au hanyar Bauchi.

**************************************

Gidan Alhaji Ma'aruf ya cika da mutane anata shagalin biki, ni harna fara tunanin kodai dama akwai mutane a gidanne ban tab'a ganin su ba.

Dangin ango Sabitu ma biki sukeyi sosai suna masa fatan shiriya.


Bayan Isha aka d'auko amarya Saleema data k'udindine cikin mayafi, gida ya cika ana gud'a harda mak'wafta da yaran anguwa, kowa na lek'awa yaga amarya amma fuskarta a rufe sai k'awayen ta da suka kewaye ta.
K'arfe 10 kowa ya watse aka bar amarya ita kad'ai, yaye mayafin tayi tana murmushin da ita kad'ai tasan manufarshi.

Cikin Zumud'i Sabitu ya shigo gidan har yana hana abokan sa shiga saboda kishi, tana jin motsin shi ta janyo mayafin ta mayar kanta, ledan hanunshi ya ajiye a gabanta ya haura kan gadon, bakinshi a washe yafara mata kirari dake nuna farincikinsa, ace warsa sai yanzu yasan yayi aure, mayafin ya yaye yana lek'a fuskan ta, tasha kwalliya tayi kyau matuk'a, rungumota zaiyi ta shagwab'e fuska da muryarta mara dad'i ta ce "Masoyi saurin me kakeyi, ni wlh duk na gaji".
Gab'on naku ya washe baki ya d'auko ledar ya bud'e mata kazar amarcinta, cikin yanga ta rink'a ci, shi kuwa Sabitu zumud'in gurzar amarya ya hanashi zagewa yaci, duk da irin munafukin yunwar dake addabansa, Saleema dake ganin take takensa tayi murmushi kurum a ranta.

Tana gama ci tasha yogurt d'in tayi nak abunta, kallon Sabitu tayi ta ce "kaje d'akin ka kayi wanka zan shirya".
Hanunta dayasha lalle ya kamo ya manna mata kiss ya ce "kinsan munyi tanadi a wannan daren ki shiryamun sosai yanda zanji dad'i".
Itama sunbatar hanunshi tayi ta ce "to masoyi".

Yana fita ta sanya key a k'ofar ta d'ale gado tayi kwanciyar ta, nanda nan kuwa bacci ya d'auketa.

Wanka yayi sosai ya feshe jikin shi da turare tako ina ya sanya jallabiya ya tafi d'akin amarya, ko gajeren wando bai saba wai kada ya takura mishi domin a matse yake sosai, yana tura d'akin yaji a rufe, waro ido yayi yafara d'an bubbugawa yana k'iran sunan ta, jin shiru yasa ya koma falon yazauna ya ce hala wanka takeyi, remot ya d'auka ya kunna Tv yafara kallo amma hankalin shi naga amaryar sa, yananan zaune har hak'urin shi yafara gazawa domin wani irin matsanancin sha'awa ke damunshi, yayi k'ok'ari kwana 2 bai nemi mace ba yana tanadi wa amarya shiyasa gaba d'aya yafara fita a hankalinshi, jin mararsa ta fara k'ullewa yasa ya koma jikin k'ofar nata ya fara bugawa, Saleema baccin ta take sha don haka batama san yanayi ba, tun na bugawa a hankali har yafara bugawa da iya k'arfinsa kamar wani zararre, rik'e mararsa yayi dake ta neman agaji yashiga buga k'ofar baji ba gani.

Mak'wabcin su Alhaji Sammani ne yaji bugun yayi yawa kasancewar garun gidan nasu d'aya ne, matarshi ya kalla ya ce "kubra kinajin abunda nakeji kuwa"?

Kubra ta ce "tun d'azu nakeji duk tsoro yakamani".

Alhaji Sammani ya ce "Allah yasa ba b'arayi bane".

Kubra tace "Ameen, gari na wayewa zanje na duba nagani, inaga gidan da aka kawo amarya yau ne".

Janyota Sammani yayi ya ce "kiyi bacci duk kin wani birkice".

Sabitu ganin babu sarki sai Allah yasa ya koma d'akin nasa ya rink'a murk'ususu har asuba sannan bacci ya kwasheshi.
2/1/20, 5:10 PM - imusamuhd(professor): πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯
*D'AN DAUDU KO D'AN LUWAD'I*
πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

Page 6

_*RUBUTAWA:*_
*AISHA BICHIKI*
_Princess Eshat Aysm_



_Akwai mutane masu banzan d'abia, sai ka gama wahalar ka suyi Editn suna cire sunanka suna posting, wasu ma siyarwa sukeyi shiyasa zakuga munata maishe da novels d'in na kud'i, to wlh duk wanda ya juya mun ta ko wacce siga Allah ya isa ban yafe ba😭_





✍

Asuban fari Saleema ta tashi, tayi sallar asuba sannan tayi wanka, shigan less tayi wanda ya karb'eta matuk'a, tayi kyau sosai ta fito amarya rass abunta, sai lokacin ta bud'e k'ofarta ta nufi kitchen, ba komi a ciki sai Indomee, kayan aiki kuwa babu abunda babu aciki, guda 4 ta d'iba ta dafa, ta d'umama sauran kazarta na jiya ta d'aura akan indomi d'in, haka ya cika k'aton trey d'in don dama Saleema badai ci bafa kamar wani k'aton gardi🀣

Lokacin k'arfe 8 na safe, zama tayi a falo ta kunna Tv tafara cin abunta hankali kwance, motsinta ya fito da Sabitu wanda tashin sa kenan, tsaye yayi a gaban ta yana had'iye yawu, shigar tata tayi masifar tafiya dashi, ga mahaukacin yunwan da yakeji cikinsa harna kukan yunwa, da fushi ya tashi amma ya nemi fushin ya rasa.

Kai ta d'aga ta kashe masa ido ta ce "Masoyi ka tashi? bismillah zauna muci".

Haushin ta ya kamashi watau batama san halinda ta barshi jiya ba, basarwa yayi dake yana jin yunwa ya zauna sukaci tare, sai kallon k'aton hanunta yakeyi wanda yafi nashi sosai, ga wani gargasa na kwantaccen gashi a hanun, da sauri ya d'aga ido yana satan kallon ta, lomarta kawai takeyi har tana lumshe ido.

Kallon ta Sabitu yake tayi zuciyar shi na bugawa da baisan dalili ba, murmushi ta sakar mishi ta ce "kallon fa"?
Shima murmushi yayi wanda kana gani bai kai zuci ba, kallon ta yakeyi ya kasa daina wa, bai tab'a k'are mata kallo ba sai yau, wani bak'i bak'i yake gani wajen gashin bakin ta kamar gashi...

Ganin irin kallon nasa yasa Saleema ta tsargu, tashi tayi ta koma kan cinyarsa ta zauna amma bata sake nauyin ta akansa, tsikar jikin Sabitu ya tashi jin yanda hanun Saleema ke shafa fuskar shi, cikin siririyar murya wacce bai tab'a jin tayi ba ta ce "kayi hakuri jiya bacci ne ya tafi dani, amma yau tare zamu kwana koh".
Gaba d'aya kan Sabitu kuncewa ne kawai beyi ba, taushin hanun ta kad'ai ya isa ya susuta shi balle irin kallon da take jifansa dashi, d'an kwanto da ita jikinsa yayi yana sauke numfashi, murya a sark'e ya ce "zanje nayi wanka don Allah kada ki gudu"!
Murmusawa tayi ta ce "Toh Masoyi".

Yana shiga d'aki Kubra na doka Sallama a falon, mik'ewa Saleema tayi cike da mamaki ta nufi wajen tana tunanin waye da wannan sammako haka, tana bud'ewa tayi arba da Kubra dake zare ido, lokaci guda ta saki murmushi, itama Salima murmushin tayi ta ce "Bismillah shigo".
Kubra ta ce "A'a anjuma zan shigo mugaisa, dama nazo ne naji ko a gidannan ne b'arayi sukayi ta buga k'ofa"?
Waro manyan idanuwa Saleema tayi ta ce "b'arayi? Gaskiya banan bane don bamuji wani motsi ba, kuma akwai me gadi banji yace komi ba".
Kubra ta ce "Toh madallah, ni zan koma idan kina buk'atan d'an aika kiyi magana saina turo miki yaro na".

Saleema ta ce "ai kuwa nagode kituro mun shi yanzu, dama inata tunanin a ina zan samu yaro na aika".
Kubra ta washe baki baki ta ce "bari na turo miki shi, duk abunda kike buk'ata ki aikeshi, yaron kishiya ta ce, sam bayajin magana, idan yamiki kwab'a ki zaneshi".
Mamaki ya hana Saleema magana, ido ta zubawa kubra dake ta zuba kamar an tambaye ta, ganin ba shiru zatayi ba ta ce "toh nagode sai anjuma".


Zama Saleema tayi tana tunanin maganar Kubra, watau d'an kishiyarta ne, to ina Maman shi....

Sallamar yaron ya katse mata tunani, kyakkyawa ne yaron zai kai shekaru 10, wankan tarwad'a dashi, kayanshi duk a kod'e alamun dai bashi da sutura, murmushi me had'e da ma'anoni Saleema tayi sannan ta amsa gaisuwar da yake ta jifanta dashi, a take ta d'auko kud'i ta rubuta masa abunda take buk'ata ta mik'a masa.
Harda russunawan sa alamun yaron yanada hankali.


Yaron yana fita ta juya zatayi d'aki idanuwan ta suka sauk'a kan Sabitu, yana sanye da kayan shan iska, matsawa yayi daf da ita ya ce "Amarya baki laifi".
Murmushi tayi ta ce "anya kuwa".
Matsawa yayi sosai jikin ta ya ce "ke zaki bada wannan shaidar, ko baki gani akanki ba".
Fari tayi masa da ido ta ce "wannan ai ba laifi bane".
Washe baki yayi ya ce "muje nabaki amsa, don wlh a matse nake".
Cikin jan hankali ta ce "shknn masoyi, nidai amun afwa ina fashin Sallah".
Wani irin zabura Sabitu yayi ya ce "kada kimun haka zan iya shiga wani hali Saleema, idanma tsoro kikeyi zan miki a hankali"
Ture hanunshi a jikin ta tayi ta ce "nifa bana son fitina, ba'a takuramun, idan kana buk'atar kud'i kayi mun magana amma na fad'a maka halin da nake a yanzu".

Binta da kallo Sabitu yayi cike da tashin hankali yama kasa magana, yana gani ta shige d'aki zuciyarshi ta shiga harbawa da sauri yana tunanin abu 2 daya kasa fassarasu.

Tsuk'a yayi ya d'auko key d'in motar Saleema dake hanunshi ya fice a gidan, me gadi na bud'e masa yaron da Saleema ta aika na shigo wa, baiko tsaya bi takanshi ba ya hura wa motar wuta yayi gida abunshi cike da son kasancewa da Suwaiba, dama duk lokacin da ta k'ak'are masa ananta yake sauk'ewa...








*KUYI HAK'URI INA GANIN SAKONNIN KU KAINA KE CIWO SOSAI*....



_Allah yayi albarka wa iyayenmu_
2/1/20, 5:10 PM - imusamuhd(professor): πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯
*D'AN DAUDU KO D'AN LUWAD'I*
πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

Page 7


Kuyi hakuri najina shiru kwanaki da yawa...



_*RUBUTAWA:*_
*AISHA BICHIKI*
_Princess Eshat Aysm_



_Akwai mutane masu banzan d'abia, sai ka gama wahalar ka suyi Editn suna cire sunanka suna posting, wasu ma siyarwa sukeyi shiyasa zakuga mu'ata maishe da novels d'in na kud'i, to wlh duk wanda ya juya mun ta ko wacce siga Allah ya isa ban yafe ba😭_



✍

Kai tsaye yaron data aika ya shiga falon yana doka Sallama, jin shiru yasa yafara k'arewa falon kallo, jin motsin bud'e k'ofa yasa ya waiga da sauri, murmushi Saleema tayi ta ce "shigo mun dashi ciki".

Tana fad'a ta koma tayi zamanta akan gado.

Da Sallama ya shiga ya ajiye sannan ya mik'a mata canjin, girgiza kai tayi ta ce "ka sayi omo da canjin ka wanke kayan ka".
Dariyar jin dad'i yayi yafara jera mata godiya.

"menene sunanka"?

Tayi tambayar fuskanta nakan wayar hanunta.

"Ahmad".

Ya bata amsa.

d'an kallonshi tayi ta ce "ina mamarka"?
Ya ce "Mamana ta dad'e bata nan, ta tafi garinsu har yanzu bata dawo ba".
Ajiye wayar Saleema tayi ta zubawa Ahmad ido, can tayi ajiyar zuciya ta ce "kana zuwa makaranta"?
Ya ce "da ina zuwa amma yanzu bana zuwa, Babana ya ce bashi da kud'i, 'ya'yan Aunty ne kawai suke zuwa".
Murmushi Saleema tayi ta ce "zan baka kud'in makaranta ka koma kaji, sannan zaka rik'a zuwa kana tayani aiki, har kaya masu kyau zan siya maka".
Ahmad sai washe baki yakeyi yana murna, yaron yanason karatu sosai amma bai samu wannan damar ba, gashi har kaya masu kyau za'a siya mishi, zai zama kamar abokansa, don haka yayi ta murna yana mata godiya.

Yana fita yaje yasami abokanshi ya ce "Zai koma makaranta, suma sukayi ta murna don suna son Ahmad".

Da gudu yayi gida abunka ga yaro, ba ruwanshi da abunda Kubra ke mishi yaje yasameta da zancen, kama baki tayi tana kallon shi harya kai Aya, jawoshi tayi ta matse kunnenshi tace "Yanzu Ahmad harka barbad'a mata sirrin gidannan"?

Tsaban jin zafi har hawaye yafara yi, cikin azaba ya ce "Aunty wlh bance mata komi ba, kiyi hak'uri".
Rankwashi ta sakar mishi me zafi ta ce "zanje yanzu naji me kace mata, munafukin Allah kawai".
Hankad'ashi tayi ta zari mayafi ta nufi wajen Saleema.

Saleema na yanka Salad a kitchen taji shigowar Kubra tana karad'a Sallama, aranta tace "na shiga uku me kuma yadawo da wannan matar".

Hanunta ta d'auraye ta fito falon, a zaune ta same ta tana bin ko ina da kallo, Saleema ta washe baki ta ce "Auntyn Ahmad ko"?

Kubra ta gimtse fuska ta ce "naji wani magana ne abakin Ahmad, shine nakasa zama sai da nashigo, ace daga tarewarki jiya har Ahmad ya kawo miki gulmar bai zuwa makaranta, kumafa bakowa ya hanashi zuwa ba iskanci da rashin ji yakeyi aka koroshi, shine nazo nafad'a miki kada ki wahalar da kanki ba karatun yakeyi ba, zancen sutura kuwa yana dasu dai dai gwargwado wlh k'in sawa yakeyi".

Ta gama maganar tana k'ifi k'ifi da ido, Saleema ta gyara zama ta ce "kinsan yara sai hakuri, musamman idan bakai ka haifesu ba".
Kubra najin haka ta washe baki ta ce "wlh kuwa, sai aga kamar mugunta kake musu, yaronnan shekararsa 4 kenan a wajena amma mutane basu ganin wahalar danakeyi dashi, hakanan uwarsa ta d'auki kishin banza dani tak'i zama tabarmun masifa".
Murmushi Saleema tayi cike da mamakin Kubra.
Nan Kubra tabata labarin mahaifiyar Ahmad da bak'in kishinta har ya sa aka sake ta, shine ta tafi da 'yarta macen wai gudun kada ta lalace tabar namijin.

(Wannan shine babban kuskuren da mace take tafkawa, kibar d'anki sabod rashin tunani, lalacewar maza shi yafi komi sauk'i a yanzu, Namiji shike sata, shaye shaye, yayi garkuwa da mutane duk saboda rashin ingantacciyar rayuwa da tarbiya, dazaran kin haifafa

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

2 Comments On DAN DAUDU KO DAN LUWADI Book 1
avatar
hamidu

1 year ago

Reply

Wasu novels nakudine, idan nayi subscription naku zansamu complete na books dinne? Kosai nabiya a wurin marubuciya?

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to hamidu

Muddin Novel na kudi ne koda ace ka yi subscribtion na mu ba zaka samu complete na shi ba dole sai ka siya a wurin marubuciya, shi yasa ma novel na kudi su ana iya downloading na su koda ba a yi subscribtion ba

Please Login or Register in order to submit comment