Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rikece yake sanar damu"

Lantana ta faɗa tana ƙoƙarin barin wajan.

Abu tsoro ne ya kamata ta shiga furta innalillahi gaskiya gida zata koma ba zata su kasheta ba gwara Inna wuro tai mata duk abinda za tai mata, da haka ta koma gida.

Kan kace me labari ya kauraye rugar kowa hankalinsa a tashe, ba mai fita ba mai shiga.

Inna Wuro kuwa ta shiga banɗaki ba adadi tana zawo.

***
Sai bayan sallar asuba Daddy da Fareeda suka zo asibitin Fareeda riƙe da basket ta shirya kayan abincin a ciki.

Sallama su kai suka shiga ɗakin da Khaleed yake ciki.

A zaune suka sameshi yayin da Mommy ke zaune bakin gadon suna hira.

"Assalamu alaikum! Ah yaro ya samu"

Daddy yai sallama tare da faɗar haka.

Mommy tai murmushi.

Khaleed Ya ce"Wa alaikassalam, Daddy sannunku da zuwa"

Daddy ya samu waje ya zauna yana amsawa.

Ya ce"Sannu Khaleed ya jikin?"

Khaleed Ya ce"Da sauƙi Daddy aina warware"

Daddy yai murmushi yana, Ce wa"To Allah ya ƙara sauƙi"

Duk suka amsa da ameen.

Fareeda ta gaishe su sannan tai masa ya jiki.

Ya amsa yana dariya, Ya ce"Ai da kin rasani yau da naga irin kukan da zaki"

Farida tai dariya, Ta ce"Allah Yaya nima da mutuwa zanyi, wai ma Yaya meya sameka?"

"Sharrin Nafeesa mana zata kashe shi"

Mommy ta faɗa cikin ɓacin rai.

Da sauri Daddy ya taɓo Mommy kafin, Ya ce"Kawai fa maleria ne Auta"

Khaleed kuwa sunkuyar da kansa kawai yai, meyasa Mommy ke son fallasa sirrinsa, dan ya basar da maganar.

Ya ce"Am Mommy yunwa fa nake ji"

Da sauri Mommy ta miƙe tana amsa masa ta ɗauko kayan abincin ta shiga bubbuɗewa kafin ta zuba masa wanda zai fi masa daɗin ci, ta miƙa masa ya fara ci dan rabonsa da abinci tun safiyar jiya.

Ƙarfe 7:00AM aka sallameshi sun su su wuce dashi gida amma yace gidansa zai wuce dn haka suka sauke shi suma suka zauna dan taya shi hira kafin wani lokacin.

Wayarsa dake ajiye kan centre tv yasa aka ɗauko masa ya duba nan yaga kira yafi guda nawa na ogansa kafin kuma yaga message.

Da sauri ya buɗe messafe ɗin ya shiga karantawa.

*Khaleed ina ka shiga ne na kira wayarka ba a picking? To idan ka gani ka kira ni tafiya ta sameku*

Da sauri Khaleed ya kira number ogan nasu rings1-2 ya ɗaga.

Khaleed Ya ce"Yes sir"

General Abbas ya amsa sannan, Ya ce"Khaleed dama nace ko da yaushe zaka iya jin wayata to na kira ka ba picking"

"Oga bana kusa da wayar ne"

Khaleed ya faɗa cikin girmamawa.

General Abbas Ya ce"Ok to ka shigo ina son ganinka domin tafiyar ba wata mai jan lokacin bace zuwa gobe ne"

"Insha Allah sir zan shigo"

Khaleed ya faɗa.

General Abbas y amsa masa kafin suyi sallama.

Mommy da Daddy suka zuba masa ido harya gama wayar domin tunda suka ga yadda yake maganar sun san ko dawa yake wayar.

Mommy Ta ce"Lafiya dai ko?"

Khaleed Ya ce"Mommy General ne ya kira ni domin tafiya ta kama mu zamu koma bakin aiki"

Mommy fuskarta ta suya zuwa damuwa kafin, Ta ce"Amma Khaleed ai baka da lafiya mene yasa ba zaka gaya masa ba a fasa tafiyar da kai?"

"Mommy ya zama dole naje yana yin aiki na ne hakan"

Khaleed ya faɗa cike da nutsuwa.

Mommy zata kuma magana Daddy ya dakatar da ita da.

Ce wa"Kinga Mommyn Fareeda kin san fa aikinsa, yaro na Allah ya taimaka ya bada nasara"

Da ameen suka amsa kafin Mommy ta daɗa yi masa addu'oi.



*Sallu alan nabiyul kareem🥰🤲 (s.a.w)*





*MATAR MIJI NA*
*(RETURN)*


_Writing by_


*Zainab Muhammad (ndian Girl)*


*Karamci Writer's Association*

_Karamci tushen al'umma_



*GODIYA*
_*Godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata ala sarkin da ya bani ikon fara rubuta wannan labari lafiya kuma ina fatan yadda na fara lafiya Allah yasa na gama lafiya ameen*_


*GARGAƊI*
_*Ban yadda wani ko wata su yi amfani da wani sashi ko ɓangare na wannan labari ko ɗora shi akan youtube yin hakan ba tare da izinina ba kuskurene babba domin haƙƙina ne*_


*NOTE*
_*Wannan littafi na MATAR MIJI NA littafi ne daya ƙunshi abubuwa da dama ciki kuwa har da cin amana,yaudara,tausayi,ilmantarwa,faɗakarwa da nishaɗantarwa*_



Book 1

*Back page*

Ce wa"Kinga Mommyn Fareeda kin san fa aikinsa, yaro na Allah ya taimaka ya bada nasara"

Da ameen suka amsa kafin Mommy ta daɗa yi masa addu'oi.

Page 009

بسم الله ار حمن ار حیم

*_______________________*
Sai dare sannan su Mommy suka bar gidan har sannan Nafeesa bata dawo ba, da suka tambayeshi saiya kareta wai jikin Ummanta ne har yanzu.

Bayan yai sallar isha'i ne ya ɗauko wayarsa ya danna number Nafeesa ya tafi kira, tana ta rings ba a ɗag ba harta katse ya sake kira nan ma shiru.

A can kuwa Nafeesa tana ganin duk kiran da yake shigowa ita fa ta gaji da wannan auran duniyarta take so taci da tsinke.

****
Gari fa ya ɓaci domin abu ya ci tura kowa tsoran ya fito daga gida yake saboda tsoran ƴan boko haram.

Inna Wuro ce ta fito daga ɗaki tana hamma alamar yunwa take ji, ta dubi Baffajo da Abu dake zaune a tsakar gida kan tabarmar kaba tai tsaki kafin.

Ta ce"Nifa Malam gaskiya na gaji haba wannan masifa ace mutum yai kwana 2 bai ciba ɗan ruwan ma daya rage ya kusa ƙarewa"

Baffajo ya kalli Inna Wuro Ya ce"Habba Wuro kin san dai babu wanda yake fita saboda kowa tsoro yake ya fita waɗancan azzaluman su kashe shi"

"To wallahi ba zai saɓu ba haba so kake na mutu?"

Inna Wuro ta faɗa cikin masifa.

Baffajo Ya ce"Ai wallahi dana fita waɗan can su kashe ni gwara yunwar ta kashe mu duka"

Abu ta miƙe tsaye tana, Ce wa"Baffajo ni bari naje naga ko Allah zai sa na samo mana ko da ɗan wani abun ne"

"Ke karki sake ki fita daga gidan nan dan wallahi da ki fita su kashe ki gwara su kashe kaf jama'ar dake rugar nan"

Baffajo ya faɗa cike da tsoro.

Abu ta dawo ta zauna jin abinda Baffajo ya faɗa tana mamaki rai ɗaya yafi na rai ɗari da samti.

Inna Wuro ta riƙe baki da tafa hannu, Ta ce"Malam ran wannan banzar ƴar yafi na kowa fa kace, to wallahi kwa saita fita inga uwar da zai faru"

Miƙewa Baffajo yai kafin, Ya ce"Aikwa ba inda zata, kalmar dana faɗa zan sake mai maitawa ranta yafi min rai dubu domin ina son ta rayu"

Inna Wuro tai guɗa da, Ce wa"Aikwa yau zan ga rayayyar da ake so ta rayu ta zama matacciya idan ba haka ba kuwa a gidan nan ni zan kasheta"

Nan suka cigaba da kace nace kafin daga ƙarshe Baffajo ya umarci Abu data shiga ɗaki ta kulle har sai yace t buɗe sannan, hakan kuwa akai nan suka cigaba da bala'i da Inna Wuro.

***
Washe gari bayan ya gama shiryawarsa tsaff ya haɗa kayansa domin yasa tafiyar ba zata wuce yau ɗin nan ba.

Sanye yake cikin kayan aikinsa na sojoji sun matuƙar ƙara masa kyau.

Gidan ya kulle sannan ya shiga motarsa ya nufi gidansu, sallama yayi musu tare da neman addu'ar su dan yasan ba zasu sake haɗuwa a yau ba sai dai in Allah ya nufa ya dawo.

Sosai sukai masa addu'a kafin ya tafi.

Leemat ya kira a waya yace yana son su haɗa ya kira number Nafeesa taƙi ɗagawa.

Sosai Leemat taji daɗin wannan dama da ta zo mata dan haka ta gaggauta shiryawa ta tafi.

Bayan ta ƙaraso inda yace su haɗu suka gaisa, kallonsa take domin tunda take bata taɓa ganin yayi kyau irin na yau ba yau zata sanar dashi ƙudirinta.

Khaleed ya dubi Leemat, Ya ce"Haleema ƙawarki bata ji sannan na fahimci cewar ba ita take sona ba nine nake haukan sonta, Haleema tafiya zanyi kin san dai yana yin aikin namu koda yaushe idan tafiya ta kama sai anyi"

Leemat Ta ce"Hakane Khaleed gaskiya Nafeesa bata da tarbiya domin abinda take maka yayi yawa"

Khaleed bai kawo komai a ransa ba ganin yadda Nafeesa da Leemat suke tamkar uwa ɗaya uba ɗaya.

Ya ce"Haleema tafiyar da zanyi bana tunanin zan dawo ko bazan dawo ba domin inda zamu bamu taɓa shigarsa ba dan haka ina so ki sanar da Nafeesa tafiya ta"

Kwallar makirci ne ya gangarowa Leemat, Ta ce"Shikenan Khaleed zan faɗa mata kuma insha Allahu sai ka dawo munyi aure!"

Da mamaki Khaleed ya kalli Leemat kafin yai magana ta cigaba da.

Ce wa"Khaleed ba tun yanzu ba nake fama da dakon sonka, Khaleed dan Allah ka so ni ka aure ni wallahi ni zan kula da kai fiye da tunaninka"

Daskarewa Khaleed yai da jin kalaman Leemat cabɗijam mutum ba a iya masa.

"Bari na wuce sauri nake dan karna makara a jira ni"

Khaleed ya faɗa yana shigewa motarsa har sannan maganar Leemat tana masa yawo.

Leemar Ta ce"Shikenan Allah ya dawo daku lafiya ya bada nasara domin zf matuƙar farin ciki daga sannan kuma sai zan cem aure na da kai"

Bai ce mata komai ba yaja motarsa ya bar wajan.

Farin ciki Leemat take ji yau domin ta faɗawa Khaleed abinda ke ranta, ita ko da zai sanar da Nafeesa abinda ta faɗa masa a shirye take su gwabza dan fitar da raini, tana tunanin itama ta bar wajan.

***
"Sir!"

Khaleed ya furta lokacin daya shiga office ɗin General Abbas.

Murmushi kwance akan fuskar General, Ya ce"Khaleed gwarzo abin alfahari"

"Thank sir!"

Khaleed ya faɗa.

General Abbas ya umarce shi daya zaunan nan ya zauna kafin su gaisa ya shiga yi masa bayani.

"Khaleed na san kwazonka sosai ina so a wannan ma ka jajirce sosai domin waɗannan ance masu haɗari ne dan haka ga bayanan garin da rugar da suke"

General ya faɗa yana miƙawa Khaleed wasu takardu.

Khaleed ya ƙarɓa ya duba sannan ya jinjina kai.

Ya ce"Sir! Insha Allahu za muyi nasara akansu karkaji komai"

General ya san da haka yai murmushi, sannan suka cigaba da tattaunawa.

An shirya musu komai na aiki bindigu da harshashi da nakiya komai an haɗa musu, ƙarfe 10:00am suka ɗaga a jirgi.

Ƙarfe 2:00pm suka sauka daga jirgin kafin motocin su na soja su zo su ɗebe su zuwa cikin dajin.




*Rahamar Allah ta tabbata a gare mu baki ɗayan musulmi🤲*




*MATAR MIJI NA*
*(RETURN)*


_Writing by_


*Zainab Muhammad (ndian Girl)*


*Karamci Writer's Association*

_Karamci tushen al'umma_



*GODIYA*
_*Godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata ala sarkin da ya bani ikon fara rubuta wannan labari lafiya kuma ina fatan yadda na fara lafiya Allah yasa na gama lafiya ameen*_


*GARGAƊI*
_*Ban yadda wani ko wata su yi amfani da wani sashi ko ɓangare na wannan labari ko ɗora shi akan youtube yin hakan ba tare da izinina ba kuskurene babba domin haƙƙina ne*_


*NOTE*
_*Wannan littafi na MATAR MIJI NA littafi ne daya ƙunshi abubuwa da dama ciki kuwa har da cin amana,yaudara,tausayi,ilmantarwa,faɗakarwa da nishaɗantarwa*_


Book 1

*Back page*
Ƙarfe 2:00pm suka sauka daga jirgi kafin motocin su na soja su zo su ɗebe su zuwa cikin dajin.

Page 010

بسم الله ار حمن ار حیم

*_______________________*
Gaba ɗaya Inna Wuro ta haukata gidan sai bala'i take ita wallahi sai Baffajo ya samo mata abinda zata ci dan haƙƙin ciyarwarta a kansa take, daga ƙarshe wuƙa ta ɗauko wai gwara ta kashe shi itama ta kashe kanta kowa ma ya huta.

Abu dake jingine jikin ƙyaure ta zaro ido jin furucin Inna Wuro ga Baffajonta, dan haka ba tai wata wata ba ta buɗe ƙofar ta fito.

Baffajo ya kalleta kafin, Ya ce"Abu ba sai da nace karki fito ba saina baki umarni?"

"Baffajo haka kace amma ni bazan iya jurar ganin gawarka ba shiyasa na fito dan na tafi na samo mata abincin"

Abu ta faɗa kanta a ƙasa.

Baffajo yai shiru bai ce komai ba.

Ganin haka yasa Abu ta nufi hanyar fita.

Da sauri Baffajo ya dubi Inna Wuro, Ya ce"Haka kike so ta tafi su kashe ta ko? To bari kiji idan kinga wani abu ya samu Abu to bana raye ne"

Bai jira cewarta ba ya bi bayan Abu da har ta fice daga gidan.

Inna Wuro ta sheƙe da dariya tana tafa hannu, Ta ce"Aini dama so nake duk ku mutu kowa ma ya wuta haba wannan jaraba haka kun zaman ƙaya kai da ƴar taka"

Tafiya suke babu kowa a hanya duk gidaje a kulle saboda tsoran kar su fito ƴan ta'addan nan su kashe su.

"Baffajo yanzu a ina zamu samowa Inna Wuro abinci?"

Abu ta tambayi Baffajo.

Baffajo Ya ce"Abu nima ban sani ba amma mu cigaba da zagawa ko Allah zai sa a dace"

Abu Ta ce"To Allah yasa"

Baffajo Ya ce"To ameen"

Rufe bakin Baffajo ke da wuya suka ji ƙarar jiniyar motocin ƴan ta'adda da ƙarar bindigu, kafin kace kwabo sun zagaye su Baffajo.

Wasu kalar mutane ne marasa kyan gani gasu baƙiƙƙirin dasu tamkar gawayi.

Gaban Baffajo da Abu ne ya bada saurin dummm! Abu ta ruƙunƙume Baffajo cike da tsoro.

Tsafff Ƴan ta'addan nan suka ƙarewa su Baffajo kallo, kafin shugabn nasu ya sheƙe da wata arniyar dariya.

Cikin wata murya mai firgita wanda ya saurara shugaban nasu, Ya ce"Kai dama ashe akwai kyawawa a duniyar nan gaskiya wannan yarinyar ta haɗu ban taɓa ganin me kyauta ba tunda nake"

Ɗaya daga cikin yaran nasa shima, Ya ce"Ai oga nima dai haka, kace dai idan mun kammala abinda za muyi zamu samu ganima?"

Shugaban nasu, Ya ce"Sosai ma kam domin ma ai ni tun anan zan fara morewa kasan ni bana ɓoyewa idan har na gani"

Duk yaran nasa suka sheƙe da dariya.

Abu sake ruƙunƙume Baffajo tai wasu hawaye na zubo mata, Ta ce"Baffajo tsoro nake ji"

Baffajo ya kalleta cikin kwantar mata da hankali duk da shima a tsoracan yake domin waɗannan mutanan dole kaji tsoransu idan ka gansu.

Ya ce"Ki nutsu babu abinda za suyi miki kinji indai ina tare dake"

Ɗaga kai kawai Abu tai wasu kwallan na sake zubo mata.

Shuban nasu ne ya kalleta ya dka mata tsawa kafin, Ya ce"Ke mai kyau zo nan"

Sake ruƙunƙume Baffajo Abu tai, shima Baffajo ya riƙeta zuciyarsa na dukan uku uku.

Tsawa yaran nasa suka daka mata da, Ce wa"Zaki zo ko sai mun kashe wannan tsohon?"

Shugaban nasu ya daka musu tsawa da, Ce wa"Ku fara rabu da ita tukunna kuje ku fito da sauran jama'ar dake gidajan su domin a gabansu zan abinda nake so da ita"

Gama maganarsa ke da wuya suka wuce dan cika magabarsa.

Ita kuwa Abu da Baffajo sun sanƙame a wajan sun kasa ko da kwakwkwaran motsi.

Kaf mutanan dake cikin rugar sai da aka fito da su aka zo gaban shugaban dasu kowanne ido ya raina fata barin ma Inna Wuro data hango Baffajo da abu tsakiyar muggan mutanan nan.

Shugaban ya gyara zamansa saman mota sannan ya fara magana da babbar murya.

"Ina so kowanne ya fito da abinda yake dashi idan ba haka ku baƙunci lahira yanzun nan"

Gaban sune ya shiga dukun dam dam, kafin kowanne ya shiga fito da abinda Allah ya bashi cike da fargaba.

Bayan ya gama kwace komai nasu ya juya ga Baffajo da Abu yace a kamo masa ita a zo masa da ita inda yake.

Jama'ar ruga masu tausayi sun tausayawa Abu jin abinda shugaban ƴan ta'addan ya faɗa, wasu kuma daɗi suka ji duk da suna cikin fargaba ne ciki kuwa har da Inna Wuro.

Baffajo na riƙeta tana riƙe shi suka dinga ƙoƙarin janta da suka ga Baffajo zai basu matsala sai suka harbeshi a hannu zafin daya ziyarci hannunsa yasa ya saki Abu.

Ita kuwa Abu ihu ta saka ganin sun harbi Baffajo a hannu.

Gaban shugaban nasu suka kaita suka jefata kansa, aikwa ya cafeta yana shashshafata.

Runtse idanu Baffajo yai ganin mummunan abu nason ya faru da Abunsa amma baya iya yin komai.

Ƙoƙarin rabata da kayan jikinta shugaban nasu ya shiga yi can kamar yai wani tunani.

Ya ce"Ku duk ku tashi ku ɓace min da gani daga rugar nan karna sake ganin kowa a cikin rugar"

Bai gama rufe bakinsa ba suka dinga tashi suna gudu amma ina wasu ba suyi nasarar guduwar ba saboda harbin da ƴan ta'addan suka dinga yi wanda ya tsira ya tsira wanda aka harba kuma shiya mutu.

Bayan sun gama da wannan shugaban nasu ya cigaba da ƙoƙarin cire kayan dake jikin Abu amma taƙi bashi dama hakan yasa ya wanketa da mari wanda yasa ta ƙasa zata faɗi.

Da sauri ya riƙeta yama fasa cire kayan a haka zai abinda yake so, dan haka ya shiga ƙoƙarin afka mata gaba ɗaya.

Kukan kura Baffajo yai yai kan shugaban domin ba zai iya jurar ganin wannan mummunan cin mutuncin ba tunda da ransa, kafin ya isa wajan ne wani daga cikin ƴan ta'addan ga ƙara masa wani harbin ta baya hakan yasa Baffajo ya tafi ya faɗi cikin azaba da karaji ya furta.

"Allah ka kawowa wannan baiwa taka Abu ɗauki Allah ni da zan taimaketa na gaza Allah ka kawo mai kawo mata ɗauki"

Ita kuwa Abu kuka ta fashe dashi tana, Ce wa"Wayyo Allah na Baffajo sun kashe min kai wayyo Allah Baffajo kana gani zasu lalalatan rayuwa wayyo na shiga uku na lalace babu mai taimakona wayyo"

Shi kuwa shugaban ƴan daban ko takansu bai koma ba shi dai kawai yaga burinsa ya cika a kanta.


*Tofa tirƙashi ƙaƙa ƙara ƙaƙa hohoho yau ake yinta, Allah sarki Abu da Baffajo na tausaya muku har naji ina kuka😭*

*Shin ko wannan shegen ɗan ta'addan zai samu cikon burinsa akan Abu? Ban sani ba amma naga book 2*

*Ko sojojin nan zasu kawo musu ɗauki ko kuwa sai ƙudirinsu akan Abu ya cika? Ban sani ba amsa naga book 2*

*Ko Leemat zata samu nasarar auran Khaleed kenan taci amanar Nafeesa? Ban sani ba amsar naga book 2*

*Wane yanayi da mataki Nafeesa zata shiga/ta ɗauka akan Leemat idan taji nufinta na auran mijinta? Ban sani ba amsar na book 2*


*Tofa akwai badaƙala da cakwakiya a gaba nima kaina ban san mai zai faru ba sai munje book 2 maji kuma ma gani*


*Domin neman ƙarin bayani sai a tuntuɓen a numbobi kamar haka:-*

*09042626462 or 08143907733*


*Na fece saina jiku🏃♀️🙌*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment