Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta dube shi, Ta ce"Khaleed!"

Da sauri ya ɗaga kai ya kalleta domin tunda ya shigo falon ya gaisheta ya nemi waje ya zauna ya faɗa duniyar tunani.

Ya ce"Na'am Mommy"

Mommy Ta ce"Khaleed na fahimci kana cikin damuwa, me yake damunka?"

Shiru Khaleed yai yana ɗan sosa kai domin bai san me zai ce da Mommy ba.

Mommy ta sake, Ce wa"Khaleed tambayarka nake"

"Mommy babu komai kawai dai aiki ne ya shamin ka"

Ya faɗa cikin nuna da gaske ba abinda ke damun nasa.

Mommy tai ɗan murmushi, Ta ce"Haba Khaleed haifarka fa nayi kasan kuwa idan kana cikin damuwa zan gane"

Khaleed Ya ce"Hakane Mommy, amma da gaske ba komai"

"Ko dai kai da Nafeesa ne?"

Mommy ta tambayeshi.

Girgiza kai Khaleed yai da sauri, tabbas ya tabbatar da ake cewa idan har uwa ta damu da ɗanta to damuwarsa ma zata iya saninta.

Ya ce"Mommy babu komai wallahi ki yadda dani"

Mommy Ta ce"Shikenan, ai na yarda da kai sosai ɗari bisa ɗari"

Murmushin jin daɗi Khaleed yai kafin ya miƙe yaiwa Mommyn sallama ya fice.


****
Yau Inna Wuro bata nan ta tafi gidan ƴarta Wasila dake aure a can gaba da su, hakan ya bawa Baffajo damar sanar da Abu yadda su kai da headmaster na makaranta da yaje kafin ya ƙara da.

Ce wa"Damuwata ɗaya yanzu shine ta yaya zaki dinga zuwa makarantar ba tare da Wuro ta sani ba"

Abu Ta ce"Baffajo zan dinga dabara idan gari ya waye zan ce Inna Wuro ta dinga abincin siyarwa ina kai mata"

Baffajo yaji daɗin shawarar Abu,tabbas zai so tai karatu domin yana da yaƙinin wata rana ko baya raye zata zama wani abu a rayuwa.

Sosai suka dinga hira saboda yau sun samu sake Inna Wuro bata nan dan harta Baffajo tsoran Inna Wuro yake ji.

Sai magriba Inna Wuro ta dawo gidan.

Bayan ta huta taci abinci ne Abu ta jemata da maganar da su kai da Baffajo akan ta dinga mata abincin siyarwa, ta ara da.

Ce wa"Inna Wuro kinga za ai ciniki saboda babu masu kai abinci"

Taji daɗi da maganar Abu domin bata kawo komai a ranta ba ta amince zata dinga mata abincin.



*Allah ya sada mu da rahamarsa ameen🥰🥰🤲*







*MATAR MIJI NA*
*(RETURN)*


_Writing by_


*Zainab Muhammad (ndian Girl)*


*Karamci Writer's Association*

_Karamci tushen al'umma_



*GODIYA*
_*Godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata ala sarkin da ya bani ikon fara rubuta wannan labari lafiya kuma ina fatan yadda na fara lafiya Allah yasa na gama lafiya ameen*_


*GARGAƊI*
_*Ban yadda wani ko wata su yi amfani da wani sashi ko ɓangare na wannan labari ko ɗora shi akan youtube yin hakan ba tare da izinina ba kuskurene babba domin haƙƙina ne*_


*NOTE*
_*Wannan littafi na MATAR MIJI NA littafi ne daya ƙunshi abubuwa da dama ciki kuwa har da cin amana,yaudara,tausayi,ilmantarwa,faɗakarwa da nishaɗantarwa*_



Book 1

*Back page*

_Taji daɗin da maganar Abu domin bata kawo komai a ranta ba ta amince zata dinga mata abincin_

Page 006


بسم الله ار حمن ار حیم


*_______________________*
Yau tunda ya dawo gidan ya kasa samun kan Nafeesa domin yasan ya saba da halinta amma ba irin yau ba.

Bayan yayi wanka ya shiya ya fito ya sameta a falo sai cika da batsewa take wai ita a dole fushi take akan abinda ya faru jiya.

Waje ya samu ya zauna daf da ita sannan ya dubeta wanda ita hankalinta yana kan tv.

Ya ce"Nafeesa wai meyake damunki ne? Ko baki da lafiya?"

"Fatan cuta kake min iyye? Dama ai na fahimci inda ka dosa"

Nafeesa ta faɗa cikin hayayyaƙowa.

Mamakin yadda tai masa magana Khaleed ya shiga yi kafin, Ya ce"Gaskiya Nafeesa na gaji da abinda kike min haba, nafa auro kine dan kina sona ina sonki amma gaba ɗaya yanzu kin ɗauko wasu banzayan halaye da ban sanki da su ba"

Miƙewa tsaye Nafeesa tai tana tafa hannu, Ta ce"Gayawa duniya Khaleed, amma dai kasan ba wai masu sona na rasa na aure ka ba soyayya ce ta ɗebe ni amma yanzu zan nuna maka ƴar halak ce Nafeesa"

Tana gama faɗar haka fuuu tai ɗaki.

Sanyi jikin Khaleed yai yana jin haushin kansa akan meyasa yai mata wannan maganar.

Tana shiga ɗaki ta ɗauki akwati ta zuba kayanta a ciki ta ɗauki wayarta ta fito tana gyara zaman mayafin dake kafaɗarta.

Ko inda yake bata kalla ba ta doshi hanyar fita.

Da sauri Khaleed yasha gabanta yana, Ce wa"A'a ina kuma zaki Nafeesa?"

"Gidanmu zani ka bani hanya"

Nafeesa ta faɗa tana jan akwatinta tana ƙoƙarin kewayeshi.

Da sauri Khaleed ya sake tare hanya, Ya ce"Haba Nafeesa kin san fa ina sonki dan Allah dan annabi karki tafi ki barni wallahi bazan iya jurewa ba"

Harara Nafeesa ta gallawa Khaleed da, Ce wa"Wallahi Khaleed yau sai na bar gidanka na gaji da wahala, kullum sai ka sadu dani sannan ga tijara ma bata barni ba to wallahi na gaji dan ban zo gidanka dan na zagwanye ba"

Kan Khaleed ne ya sara a haka Nafeesa ta samu ta fice ba tare da yai wani ƙoƙarin hanata ba.

Kenan dama wasu matan haka suke? Dan me ke yin aure dan soyayya da raya sunnar ma'aiki (s.a.w) sannan dan aji daɗi, yanzu da neman mata yake da nunashi za a dinga yi ana ga mazinaci amma yayi auran bai tsiraba, yasan da cewa shi mabuƙaci ne sosai kuma ƙaddararsa ce haka Allah ne ya ɗora masa ba yadda zai yi.

Khaleed yake faɗar haka a zuciyarsa yayin da wasu hawaye masu ɗumi suka zubo masa, "Allah kai kasan yadda za kai dani" Ya faɗa yana ƙarasawa cikin falo ya samu kujera ya zauna yau ya tabbatar rayuwarsa tana cikin wani hali matuƙar Nafeesa bata tare da shi.

Ita kuwa Nafeesa motarta ta shiga ta ja ta bar gidan,a mota ta kira Leema take sanar da ita nan Leemat taji daɗin hukuncin da ƙawar tata ta yanke nan ta ƙara ɗorata.

Parking tai lokacin data iso ƙofar gidansu,bayan ta gama paking ɗin ta fito ta nufi cikin gida tana kukan munafurci wanda yana daga cikin abubuwan da Leemat ta faɗa mata.

Ummanta data fito daga ɗaki da buta a hannu zata banɗaki ta saki butar tana faɗin innalillahi.

"Wa nake gani da wannan daran kamar Nafeesa?"

Umma ta faɗa tana sake kyalla ido.

Nafeesa ba tace komai ba sai ƙara ƙaimin kukanta da tai ta ƙaraso inda Umman take ta faɗa jikinta, cikin kuka.

Ta ce"Umma Khaleed ne baya ganin abinda nake masa Umma kullum cikin kyara da hantara yake"

"Khaleed ɗin kuma?"

Umma ta tambaya domin iya saninta ta san Khaleed mutumin kirki ne.

Nafeesa Ta ce"Eh wallahi Umma"

Ta ƙarashe da sakin wani kuka.

Baban Nafeesa ne ya fito daga ɗaki jin kuka da maganganu na tashi, itama ƙanwar Nafeesa ta fito daga nata ɗakin jin hayaniya.

"Umman Nafeesa lafiya meke faru, a'a Nafeesa meya kawo ki gidan nan ko tafiya mijin naki yai domin nasan kalar aikin nasu? Amma ai da kin sani waya kikaiyo da sai Jidda ta zo"

Baba ya faɗa haka lokacin da ya ga Nafeesa.

Nafeesa cikin kuka Ta ce"Baba babu tafiyar da yayi na gaji ne kawai da abinda yake min, Baba Khaleed kullum ina kyautata masa amma baya gani!"

Ta ƙarashe da wani kukan mai taɓa zuciya.

Ita kuwa Jidda shiru tai tana sauraransu,ita iya saninta Khaleed mutumin kirkine kuma a kwanakin baya data je gidan tai kwana biyu taga yadda Yayar tata take masa kyara da hantara amma baya ganin laifinta koda ace dan ganin idonta ne yasa baya damuwa ya rama abinda tai masa ɗin amma abinda take masa bai dace ba.

Baba Ya ce"Ok Khaleed ɗin ne yake duk wannan, to yanzu ya akai kika tawo gida?"

Nafeesa ta share hawayanta, Ta ce"Baba cewa yai wai in tawo gida saiya nemeni kuma karna sake na kira shi ko ku ku kirashi"

"Shi Khaleed ɗin duk yace haka? Kai amma mutum ba a iya masa yazo ringiɗi ringiɗi shi ga mai ɗa'a ya ya aureki duj da mun nuna masa cewar mu talakawa ne amma ya amince shine yanzu da abinda zai saka mana kenan, shikenan wuce ciki zai ga ƴan halak"

Nan Nafeesa ta wuce Jidda dake tsaye yanayinta duk alamun tambaya ta shige ciki, itama Jiddan ta bi bayanta.

Umma ta dubi Baba, Ta ce"Ni wallahi Baban Nafeesa gani nake kamar yaron nan ba zai aikata haka ba"

Baba Ya ce"Ramatu kenan baki san mutum ba yana iya canzawa koda yaushe bare shi da yake ganin yana da abun hannu shida iyayansa"

Umma ta riƙe baki kafin, Ta ce"Hakane kuma to Allah ya kyauta"

Baba ya amsa da ameen ya koma ɗaki ita kuma ta ɗauki butarta ta shiga banɗakin.

A ɗaki Nafeesa ta maze kamar ba ita ta zo tana ta wannan uban kukan ta ɗauki wayarta sai danne danne take tana dariya alamar chatting take.

Jidda da ta kasa samun sukuni ta gyara kwanciyarta kafin, Ta ce"Yaya Nafeesa"

Nafeesa ta ɗago ta kalli Jidda fuskarta a ɗaure domin tasan halin Jidda sosai.

Ta ce"Ya akai?"

Jidda Ta ce"Yaya Nafeesa wai dan Allah da gaske kike abinda kika faɗa Yaya Khaleed yai miki?"

Mamaki Nafeesa tai kafin, Ta ce"A'a ƙarya nake Jidda, nafa fahimceki baki da kunya wallahi to ki fita ido na shashasha kawai wadda bata san ciwon kanta ba"

"Allah ya baki haƙuri amma ni ba haka nake…"

Jidda ta faɗa.

Da sauri Nafeesa ta katseta da, Ce wa"Dallah ni rufe min baki banza wawuya"

Jidda bata sake cewa komai ba ta gyara kwanciyarta amma zuciyarta nata mata saƙe saƙe zuciyarta na ce mata tabbas abinda Yaya Nafeesa tai ba gaskiya bane.

***
Misalin ƙarfe 2:30pm na dare.

Gidan yaji yai masa faɗi ya rasa ina zai zauna yaji sanyi,yana nan zaune akan kujera yaji mararsa ta murɗa wanda dama yasan hakan zata iya faruwa dashi domin yau jinsa yake sha'awarsa tafi ta kullum gashi babu Nafeesa balle yai dabarar da zai ya samu ya gana da ita.

Abu kamar wasa amma ina sai yaji ciwon yana gaba tamkar wanda akawa caccaka a marar,dafe marar yai yana ambatar sunan Allah, yau shikenan mutuwarsa zata riske shi shi ɗaya a gida.

Yunƙurawa yau zau miƙe amma yaji mararsa ta amsa da sauri ya koma ya zauna yayin da idanunsa sukai jajur tamkar garwashi.

Tun yana iya daurewa har abu yaci tura ya hau murƙususu, kalmar shahada kawai yake ambata domin yasan yau mutuwa zaiyi idan har bai samu abinda yake so ba.


***
Tashinsa ta shiga yi cikin firgici sakamakon wani mafarki da tai ya bata tsoro, "Daddyn Fareeda! Daddyn Fareeda!! Daddyn Fareeda dan Allah ka tashi"

Buɗe idanunsa Daddy yai yana kallon Mommy da fuskarta cike da damuwa.

Ya ce"Mommyn Fareeda lafiya meke damunki?"

Hawayene suka zubowa Mommy cikin karaya, Ta ce"Daddyn Fareeda wani mafarki nai kuma wallahi mafarkin ya bani tsoro"

Daddy ya tashi zaune, Ya ce"Wane kalar mafarki kikai haka Khadija?"

Mommy ta goge hawayen kafin, Ta ce"Daddyn Fareeda mafarki nai Khaleed bashi da lafiya yana fa murƙususu mararsa na ciwo yana ambaton mutuwa zai yi"

Ajiyar zuciya Daddy ya sauke kafin, Ya ce"Haba Khadija ai mafarki ba gaskiya bane, sannan kuma kika sani ko ci yai ya ƙoshi"

Girgiza kai Mommy tai da, Ce wa"A'a Daddyn Fareeda zuciyata ta gasgata mafarkin nan dan haka wallahi ni hankalina a tashe yake"

Daddy yai ɗan shiru kafin, Ya ce"Shikenan kwantar da hankalinki bari na kirashi kiji muryarsa sai hankalinki ya kwanta"

"Gaskiya kwa hakan yafi dan wallahi ba zan iya samun nutsuwa ba"

Mommy ta faɗa tana kallon Daddy.

Nan Daddy ya ɗauki waya ya shiga kiran number Khaleed amma shiru tanata ringa ba a picking har sai da ya kira wajan sau 5.

Kuka Mommy ta saka tana saukowa daga kan gadon, Ta ce"Ka gani ko na faɗa maka ba lafiya ba ni dai bari naje gidan na gani"

Daddy Ya ce"Kinga Nafeesan ma na kirata wayarta a kashe bari na tashi muje mu gani tunda kin san in kika tafi nima hankalina ba zai kwanta ba"

Haka suka fice daga gidan ba tare da kowa ga sani ba suka nufi gidan Khaleed yayin da Daddy yake tuƙi, horn yaiwa maigadi bayan sun isa.

Maigadi ya tambayi wane sannan ya buɗe suka shiga yana mamakin abinda ya kawo su da wannan daran koda yake ai yaga Hajiyan gidan ta fita yanzu haka akan hakane.


"Innalillahi wa inna ilahirraju'un Daddyn Fareeda ka gani ko abinda na faɗa maka shikenan Khaleed ya mutu!"

Da sauri Daddy ya ƙarasa inda Khaleed ɗin yake kwance tsakiyar falo ya durƙusa shima yana tattaɓashi amma ina babu wani alamar rai a tare dashi…



*Allah ya nuna mana Annabi Munammad (s.a.w) a baccinmu da zahiri Ameen*




*MATAR MIJI NA*
*(RETURN)*


_Writing by_


*Zainab Muhammad (ndian Girl)*


*Karamci Writer's Association*

_Karamci tushen al'umma_



*GODIYA*
_*Godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata ala sarkin da ya bani ikon fara rubuta wannan labari lafiya kuma ina fatan yadda na fara lafiya Allah yasa na gama lafiya ameen*_


*GARGAƊI*
_*Ban yadda wani ko wata su yi amfani da wani sashi ko ɓangare na wannan labari ko ɗora shi akan youtube yin hakan ba tare da izinina ba kuskurene babba domin haƙƙina ne*_


*NOTE*
_*Wannan littafi na MATAR MIJI NA littafi ne daya ƙunshi abubuwa da dama ciki kuwa har da cin amana,yaudara,tausayi,ilmantarwa,faɗakarwa da nishaɗantarwa*_



Book 1

*Back page*

Da sauri Daddy ya ƙarasa inda Khaleed ɗin yake kwance tsakiyar falo ya durƙusa shima yana tattaɓashi amma ina babu wani alamar rai a tare dashi…

Page 007

بسم الله ار حمن ار حیم

*_______________________*
Jijjigashi ya shiga yi, ita kuwa Mommy ba abinda take sai kuka.

"Maza tashi ki taimaka mu kaishi asibiti da ragowar rai a tare dashi"

Daddy ya faɗa lokacin daya taɓa saitin zuciyar Khaleed yaji tana harbawa.

Da sauri Mommy ta miƙe ta shiga taimakawa Daddy suka fita da Khaleed zuwa cikin mota, sannan Daddy ya koma ya rufe gidan ya dawo yaja motar suka nufi asibiti.

Kuka Mommy take kan Khaleed na kan cinyarta dake a baya ta zauna.

Gudu sosai Daddy ya dinga yi har suka isa asibitin,kafin su ƙarasa yaiwa Doctor ɗinsu waya dan haka suna isa aka kawo gadon ɗaukan marasa lafiya.

Likitoci ne suka duƙufa a kansa domin ƙoƙarin ceto ransa dake barazanar barin jikinsa.

Sun shafe fin awa ɗaya kafin suyi nasarar dai daita numfashin nasa, sannan suka fito kowa na sauke ajiyar zuciya.

Da sauri Daddy ya ƙarasa wajan likita daya fito daga ɗakin.

"Doctor lafiya dai ko? Kunyi nasarar ceto ransa?"

Duk ya jerowa Doctor waɗannan tambayoyin.

Ita kuwa Mommy cak ta tsaya tana sauraran abinda likitan zai ce.

Nan Doctor ya umarce su da suje office yai musu bayani.

***
Ajiye kayan abincin tayi a bayan ɗakin malamai sannan ta shiga office ɗin headmaster cikin rashin sakin jiki.

"Shigo mana yarinya kike ta wani raɓe raɓe?"

Headmaster ya faɗa lokacin daya ga Abu ta shigo tana ta raɓe raɓe.

Cikin sanɗa Abu ta ƙarasa gaban tebur ɗin headmastern kanta a ƙasa.

Abu Ta ce"Malam ina wuni?"

Headmaster ya amsa.

Abu Ta ce"Malam nice wadda Baffajo na yazo kan zantan makaranta"

Headmaster yai murmushi, Ya ce"Ok! Ok!! kece kenan? Eh ai naga kama gatanan"

Abu ba tace komai ba.

Headmaster Ya ce"Yanzu zan baki hinifam ki saka muga wanne ne zai miki"

"To" Abu ta amsa sannan Headmaster ya miƙe ya shiga wani ɗaki ya fito da hinifom blue da fari a hannunsa ya miƙawa Abu.

Karɓa Abu tai tana kallon Headmaster.

Cikin inda inda Ta ce"In…In…In…"

Headmaster ya kalleta kafin, Ya ce"Lafiya ne ki magana mana"

"Malam a ina zan gwada kayan?"

Abu ta faɗa.

Headmaster ya ɗanyi murmushi kafin, Ya ce"Hhhhh! Banda abinki yarinya guda nawa kike da zaki nemi wajan saka kaya ki saka anan mana"

Abu ta kalli Headmaster fuskarta a ɗan tsorace.

Headmaster Ya ce"Ok na fahimta ajiye min kayan anan tunda bakyason karatun"

Da sauri Abu ta kalleshi, Ta ce"Malam ina so"

"To ai banga hakan ba, idan kina so ki saka kayan na gani mana"

Headmaster ya faɗa.

Abu Ta ce"Wallahi Malam ina so zan saka"

Headmaster Ya ce"To ki saka domin bake kaɗai bace wadda muke da lokacin da zaki ƙarar mana a haka"

Abu ba tace komai ba ta shiga ƙoƙarin saka kayan tana ɓoye jikinta.

Idanun Headmaster ƙirrr akanta musamman ma boobs ɗinta masu tsini duk da ta kare su da rigar amma hakan bai hana su bayyana ba.

Nan ta saka kayan ta juya ta dubi Headmaster, Ta ce"Malam na saka"

Da sauri Headmaster ya juya ganin Abu ta juyo tana magana.

Ya ce"A'a waɗannan kayan sun miki yawa cire na kawo maki wasu"

Abu ta amsa da to.

Headmaster ya koma ɗakin ya ɗauko wasu kayan ya leƙo yana, Ce wa"Zo nan ki karɓa ki saka domin kar wasu su shigo su ganki haka"

Abu bata kawo komai a ranta ba, Ta ce"To" sannan ta nufi ɗakin.

Headmaster ya miƙa mata kayan ta karɓa tana ƙoƙarin sawa.

Nan abu ta saka kayan ta fito ta samu Headmaster akan kujerarsa.

"Na gama Malam"

Abu ta faɗa tana riƙe da kayan data cire a hannunta.

Ƴan rubuce rubuce Headmaster yai a wata takarda sannan ya miƙe yace da abu suje.

Ajin da zatai karatu ya kaita sannan yaiwa malamin da yake kula dasu bayani sanna ya koma.

Abu ta shiga ajin ta nemi waje ta zauna.

Bayan an fito break ne ta fito da abincinta ta shiga siyarwa.

***
"Alhaji Khaleed ba yayi aure bane?"

Doctor ya tambayi Daddy yana kallonsa.

Da sauri Daddy Ya ce"Eh likita yana da aure"

Doctor ya jinjina kai sannan, Ya ce"To gaskiya ya tsallake rijiya da baya domin matsalarsa gwarama ace baya da auran"

"Kamar ya Doctor ban gane ba"

Daddy ya faɗa, ita kuwa Mommy ta kasa magana zuciyarta tunani ta shiga yi to ina Nafeesa ta shiga da suka je suka tarar gida ba kowa sai shi kaɗai cikin wannan halin? Ko tana ɗaki tana bacci? Amma kuma ta barshi cikin wannan halin tana bacci?.

Doctor Ya ce"Alhaji Khaleed tun kafin yai aure nasha faɗa muku irin matsalar da yake ciki hakan yasa yai auran amma sai gashi koda yai auran matsalar bata rabu dashi ba"

Doctor ya ɗanyi shiru sannan ya cigaba.

"Alhaji cikin kaso 100 na cutar dake jikinsa kaso 60 yaci ƙarfinsa sakamakon rashin saduwa da baya samun yi da matarsa"

Dammm! Ƙirjin Mommy ya buga.

Daddy Ya ce"Subhanallahi! Doctor ai na zata tunda yai aure aka rabu da wannan matsalar?"

Doctor Ya ce"Hakane Daddy, amma aure bai daɗeshi da komai ba domin memakon a ragu sai daɗuwa da akai domin da matsalar bai fi 35 ba amma yanzu gashi ya daɗu"

"Innalillahi wa inna ilaihirraju'un! Nafeesa yanzu abinda zata saka mana dashi kenan? Amma kuma shi Khaleed ɗin ya zauna da matsalar bai sanar da kowa ba"

Daddy ya faɗa cikin damuwa.

Mommy cikin kuka, Ta ce"Amma Nafeesa ta cutar damu taci amanar yarda"

Doctor Ya ce"Haƙuri za kuyi Alhaji domin Allah ya taimakeshi tunda har ya tsallake rijiya da ka"

Daddy Ya ce"Hakane, to amma Doctor yanzu mene abin yi?"

Doctor Ya ce"Gaskiya dole sai anyi maganin matsalar tasa, kuma hanya ɗaya da za a bi shine ya ƙara aure ko kuma matar tasa ta sauya halinta"

Nan dai Doctor ya ƙara masu bayanai kafin ya sallamesu.

Godiya su kai masa sannan suka fice, ɗakin da aka kwantar da Khaleed suka shiga.

Yana kwance idanunsa a rufe fuskarsa tai haske ya ɗan rame ciwon lokaci ɗaya, ko da yake ciwon ciki masifa ne balle ma na ɗa namiji.


*Allah ya jiƙanmu da rahma🤲*



*MATAR MIJI NA*
*(RETURN)*


_Writing by_


*Zainab Muhammad (ndian Girl)*


*Karamci Writer's Association*

_Karamci tushen al'umma_



*GODIYA*
_*Godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata ala sarkin da ya bani ikon fara rubuta wannan labari lafiya kuma ina fatan yadda na fara lafiya Allah yasa na gama lafiya ameen*_


*GARGAƊI*
_*Ban yadda wani ko wata su yi amfani da wani sashi ko ɓangare na wannan labari ko ɗora shi akan youtube yin hakan ba tare da izinina ba kuskurene babba domin haƙƙina ne*_


*NOTE*
_*Wannan littafi na MATAR MIJI NA littafi ne daya ƙunshi abubuwa da dama ciki kuwa har da cin amana,yaudara,tausayi,ilmantarwa,faɗakarwa da nishaɗantarwa*_



Book 1

*Back page*

Yana kwance idanunsa a rufe fuskarsa tai haske ya ɗan rame ciwon lokaci ɗaya, ko da yake ciwon ciki masifa ne balle ma na ɗa namiji.

Page 008

بسم الله ار حمن ار حیم

*_______________________*
Ƙarasawa ciki su kai suka nemi kujera suka zauna suna jiran farkawarsa.

Daddy ne ya dubi Mommy, Ya ce"Ya kamata a sama masa abinda zai ci idan ya farka"

Mommy Ta ce"To Daddyn Fareeda ko kai zaka koma gida sai ka faɗawa Fareeda ta girka in tayi sai a kawo masa"

Daddy ya amsa dan ya san Mommy ba zata taɓa yarda ta tafi ta bar Khaleed ba.

Bayan fitar Daddy Mommy ta zubawa Khaleed idanu tana kallonsa.

"Tunda na ganka na tabbatar da kana cikin matsala Khaleed amma dana tambayeka sai baka faɗa min ba, meyasa kake ƙoƙarin cutar da kanka dani ma kaina Khaleed?"

Magana take tana hawaye.

A hankali Khaleed ya buɗe idanunsa yana mai ambatar sunan Allah.

Da sauri Mommy ta miƙe daga kan kujerar da take ta nufi bakin gadon.

"Sannu Khaleed ka farka?"

Mommy ta faɗa tana kallonsa.

Khaleed ya ɗaga kai ya kalli Mommy kafin wasu siraran hawaye su biyo kuncinsa.

Ya ce"Mommy please ki yafe min"

Mommy tasa hannu tana goge masa hawayen, Ta ce"Na yafe maka Khaleed dama ba kai min komai ba, amma Khaleed meyasa dana tambayeka baka faɗan ba?"

"Mommy bana son ki shiga damuwa shine yasa"

Khaleed ya faɗa yana rufe idonsa da buɗewa.

Mommy Ta ce"To karka sake min irin wannan Khaleed"

Khaleed Ya ce"Insha Allah Mommy ba zan sake ba, amma Mommy ya akai kuka san banda lafiya?"

Mommy Ta ce"Mafarki nai kana rashin lafiya kana kiran mutuwa za kai shine na ce da Daddynku sai mun zo na ganka bayan an kira wayarka data Nafeesa ba a samu ba, wai ma nikam ina Nafeesan ne?"

Khaleed ya jinjina kai a ransa yana cewa'gaskiya uwa uwa ce kum daban take' kafin, Ya ce"Mommy ta tafi gidansu"

"Gida kuma to meya haɗaku ta tafi ta barka cikin wannan halin? Ko dama ba sonka take ba?"

Mommy ta faɗa cikin damuwa.

Khaleed Ya ce"A'a Mommy tun safe ta tafi wai Ummanta ba lafiya tace min zata kwana"

"To baka sanar da ita halin da kake ciki ba balle ta zo ta sameka?"

Mommy ta tambayeshi.

Khaleed Ya ce"Ai Mommy ba muyi waya ba sannan kuma idan na sanar da ita zata iya tawowa gashi sannan dare yayi"

Mommy Ta ce"Khaleed! Likita fa yace matsalarka ta tun kafin kai aure tana nan sai ma abinda yai gaba"

Juyar da kansa gefe Khaleed yai yana mai nazari baya son Mommy ta gane abinda suke ciki da Nafeesa.

"Magana fa nake Khaleed"

Mommy ta faɗa.

Khaleed ya juyo ya kalli Mommy kafin, Ya ce"Mommy Nafeesa tana iya ƙoƙarinta akaina, Mommy yadda nake Nafeesa yarinya ce ba zata iya ɗauka ba"

Mommy za tai magana likita ya turo ƙofar ɗakin ya shigo dan sake duba jikin Khaleed ɗin yaga koya farka.

"Au ashe ya ma farka Hajiya?"

Likitan ya tambaya.

Mommy Ta ce"Eh likita ya farka"

Likitan bai ce komai ba ya ƙarasa gadon ya shiga duba Khaleed, bayan ya gama gwaje gwajensa ya dubi Mommy.

Ya ce"Alhamdulillah Hajiya yanzu komai normal zuwa gari ya waye insha Allah zamu sallameshi, amma zamu bashi magungunan da zasu dinga taimaka masa"

Mommy Ta ce"To likita mun gode sosai Allah ya taimaka"

Da ameen likitan ya amsa sannan ya miƙawa Mommy wata takarda.

Ya ce"Hajiya ga magungunan a siyo su"

Mommy Ta ce"Insha Allah Likita za a siyo"

Likita ya amsa sannn ya fice.

****
Tasss Abu ta siyar da abincin kafin a tashi daga makarantar, bayan an tashi ta cire hinifom ɗin ta mayar da kayanta da tazo dasu ta saka waɗancan a leda ta ɓoye su a cikin makarantar ta nufi gida ita da ƴan rigarsu.

Inna Wuro taji daɗin ganin an siyar da abincin tasss hakan yasa tace gobe ƙarawa za tai.

Abu tafe take a hanyar rafi zata ɗebo ruwa.

"Abu! Abu!! Abu!!"

Da sauri ta juya tana dan ganin me kiran nata.

Da sauri Lantana ta ƙaraso tana haki, Ta ce"Abu wallahi karki je rafin nan ki koma gida"

"Meyake faruwa?"

Abu ta tambaya.

Lantana Ta ce"Wallahi azzalumai sun shigo rugarnan suna can kusa da garin nan kuma kisa suke"

Abu ta zaro ido da, Ce wa"Lantana ya akai kika sani?"

"Nima yanzu Jafaru ya dawo a

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment