Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanan suka zamu guri suka zauna.

Taro yayi taro al'umma sun hallara taya Sabreen da Naufal murna,chan na hango wasu manyan mutane,tun isowar su aka fara buɗa musu hanya,Abin mamaki Sai na ga Aunty Nabeela ta tashi da murnar ta,guri na ta iso tana murmushi ta kalle ni ta ce"My batul zo muje ki ga waɗan da suka zo"

Kallonta nayi nai murmushi na ce"Toh muje my Aunty"

waiyo allah na wa zanga ni Sarah ce da alfaga da kuma mutumina Sul harda Ruƙaiya,nayi mamaki sosai ganin su gurin Bikin Sabreen.

Hhhh baku ga da Sarah da zauna kusa da Sabreen ba,kunga Sabreen kuwa sai tai wani irin mugun muni,to kyau na gaskiya ya baiyana a gabanta.

"Toh wai ko yarima mu'utasim ya zo kuwa?

hhhh to ya zan sani tunda ba ganinshi zanyi ba.

Ina cikin wanan tunanin Aunty nabeela ta ce min"My batul yarima mu'utasim yana gaisuwa"

A ruɗe na ce"My Aunty ya zo ne"

"Eh kin shiga ruɗani ne"

Wanan shine *Ruɗani* ,littafin Sarauniya beelat(My Aunty nabeela).

biki yayi biki Tunda manyan mutane suka hallara bikin harda su Yarima mu'utasim,na so ganin baba me gadi dan yaban dariya.
.
[12/16, 5:41 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: _ 🇵σѕт 🇧у 🇬яσυρ 🇴 🇫 🇭уρє 🇭αυѕα 🇳σνєℓѕ 🇧σσк 🇼нαтѕαρρ 08064400100_ 📚📚
[12/22, 5:26 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: 🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹


*By*
*fatima* *Batula*
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

Page 11
............................................................
_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{WANDA YA RUFE WA MUMINI WANI SIRRI(NA LAIFI) KAMAR YAYI CETO NE GA WANDA AKA BINNE DA RAI!.}*_

```[Sahihut Targib;2337]```
~~
_Duk wanda ya rufa ma mumini sirrinsa na laifi, bai ba mutane labarin abinda ya sani game da shi na sharri ba, to kamar an binne shi da rai ne sai ya ceceshi. Allaahu a'alam._

```Allah ta'ala yasa mudace```

_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_

....................................................................................

Ansha shagalin baki abun ba'a cewa komai, sai wanda ya gani kawai.

Kallon ta kawai Naufal yake yi yana mamaki gashi sai washe baki take yi ,maganar da ta gayamishi yake tunowa"Bana sonka ba zan iya rayuwa da kai ba,na aure ka ne dan ɗaukar fansa"

A haka taro ya watse hankalin shi baya tare da shi abubuwa sai yawo suke mishi kwakwalwa ,daga sun haɗa ido ya su harara juna suja tsaki.

Ƙarfe Tara taro ya watse,kowa ya kama gaban shi,su kum suka ɗau hanyar zuwa gidan su hajia.

Kallonta yayi rai a ɓace ya ce"Sabreen meyasa kika min haka kin san bana sonki kika ce zaki aure ni"

Ɗagowa tayi ita ma ranta a ɓace ta kalle "Hmm to kai me kake tunani ,ni Sabreen zan iya auran haka kawai allah ya kyautamin da auran....

yaji zafin maganar matuƙa ya janyo ta jikin shi da karfi ya rungumeta ɓacin ran da yake ciki bai bar shi ya saurara feelings ɗin da yaji ba "Ke ni tsaranki ne zaki gayamin irin wanan maganar,ni wllh ko banga dalilin da zai sa na aureki ba,dan banga abinda zanyi da ke ba,ko a jerin mata ban saka ki ba,balle ki xama class ɗina,ke kanki kinsan ke ba aji na ba ce,banda kaddara da wallahi ko kallan ki bazan yi ba"

Ran Sabreen kai ƙololuwa gurin ɓaci idanuwanta sunyi jajir dan takaici gashi ya matseta,cizo ta ganna mishi a hannu da ƙarfin gaske da sauri ya sake ta.

Har yakai hannu zai janyota farrah ta buɗe kofar

"Am. .. sorry"

Har zata maida kofar ta rufe Sabreen ta fito rai a ɓace,gaba tayi ta barshi a ciki.

Wani ƙululon takaici ya kama shi,idan har haka sabreen zata tunga mishi bai jin zai iya riƙe alƙawarin Dady,ya daɗe a cikin motor kafin ya fito.

Yana isa falon gaban shi yai mummunan faɗuwa ganin kowa da kowa yana falon,har ya samu wani guri gefe zai zauna Dady ya ce mishi"Naufal matso nan kusa da matarka."

Ba Naufal ba ita kan Sabreen zaida taji haushi.
Ba musu ya matsu kusa da ita ya ɗuka dan a kasa suke harda ita ɗin.

Dady yayi gyaran murya ya ce"Naufal mun gama magana da kai,ni yanzu ba abinda zan ce maka,illa na ƙara tunatar da kai haƙƙin aure wanda su ma kasan su."

Juyowa da kallon shi yayi gurin Sabreen ya kalleta duk da ƙarancin hasken da ke ɗakin amma yana hango fuskarta "Sabreen yanzu zaki shiga wata sabuwar rayuwa wacce baki saba yin irinta ba,abinda nake so da ke sabreen kinga Naufal ɗan uwanki ne,ki riƙe shi, ki mishi biyayya ki bi umarni shi wannan ce shine haƙƙin mata akan mijinta,nasan kina da hakuri amma sai kin ƙara,Sabreen ku riƙe junanku da amana,sanan duk abinda ya miki ki same ni ki faɗimin kina jina?

Ɗaga mishi kai tayi alamar taji.

Kallon hajia da Momy yayi ya ce"Toh baku da abin faɗi ne?

A hankali momy ta buɗe baki saida ta fara gabatar da addu'ar buɗe taro sanan ta ce"Naufal ba wata magana mai tsawo zanyi ba,kasan Sabreen marainiyace karka cutar da ita ka riƙe ta ƴar uwarka ce ,sanan wanan auren shi ne alkairi a gare mu da kai ma,bansan ko zaka fahimce abinda nake nufi ba,sabreena alkairi ce a gareka dan haka ka Naufal ka kula da Sabreen"

Tunda suka fara magana gaban shi ke faɗuwa,ya rasa wani irin tunani zai yi ma.

Hajiya kuwa kasa magana tayi sai kuka sabreen najin hajia ta fara kuka ita ma,ta fara yi,kusa da ita hajia ta zo ta rungumeta suna ta kuka ba wanda ya dakatar da su.

Naufal ma ji yake yi ina ma zai iya yin kukan da yayi ,dan shi ne abin kuka ba su ba.

Ganin basu da niyyar daina kukan Dady ya ce"Ya isa haka kuyi hakuri dole daman sai wanan ranar ta zo."

Kallon Naufal yayi ya ce"Naufal tashi ku tafi"

Gaban shi ya faɗi"Na tashi mu tafi"ya maimaita abinda Dadyn ya faɗa a hankali,shi kanshi zaida yaji wani iri wai yau zai bar gidan su ya kwana a wani gida daban.

Sabreen tana jin abinda Dady ya faɗa ta ƙara ƙanƙame hajia tana kuka mai tsuma zuciya.

Tashi momy tayi taje da riƙo Sabreen tana san ta rabata da jikin hajia.

"Waiyo hajia Momy dan Allah ,Hajia bazan tafi na barki ba,waiyo hajia ki riƙe ni,momy momy kiyi hakuri na fasa auran bana so Allah na fasa bana son ya naufal,hajiyata bazan tafi ba...

Duk da yanayin da suke ciki saida suka yi ƴar dariya,musamman Naufal da farrah A ran shi ya ce"Banza daman haka kike amma kika ce kina son aure n..

"Naufal zo ka jata"
Dady ya katse mishi tunani.
Hajiya ya fara ja dan baya son ya taɓa Sabreen.
"kai ita zaka ja", Dadyn ya taɗa.

Hannun shi yakai kan kafaɗar ta,ya fara janta ,ita kuma momy taja hajia.

"Yawwa kamata ku fita",cewar dadyn

Kuka Sabreen take yi tana ihu "Waiiyoo! wllh Dady na fasa bana so,dan allah ku barni,na zauna da hajia bana son auren,Yaya Naufal dan allah ka barni bana so waiyooo"

Dariya ta bashi sosai har ya kasa ɗaurewa zaida yayi,ita ma farrah dariya tai tayi.

"Karka sake ta Naufal."

"To Dady."

Har suka fito daga fallon tana kuka,gurin shiga motor ma,saida momy ta turata da ƙarfi tana shiga aka kulle kofar,hajia bata fito ba tana chan tana rusa kuka an rabata da ƴar aljanna.

shiga motor yayi direba yaja suka fita daga gidan,Su momy suna nan tsaye har motor ta fita,sanan suka dawo suyi ma hajia sallama su koma gidan su.

Dariya Naufal ya fara yi sosai da sosai wanda bai taɓa yin irinta ba.

Ƙara fashewa da kuka tayi mai sautin gaske.

"ke dare ne ki mana shiru baki son rabuwa da ita kika ce kina son aure."

ys ƙara fashewa da dariyar shi.

Kuka Sabreen ke yi sosai bata kuma kula shi ba har suka isa unguwarsu,wani katafaran gida ne,wanan kallo ɗaya zaka mishi kasan ankace dala,dan ya fituno da kyau abin zai wanda ya gani.

Suna isa harabar gidan direban ya tsaida motor,shi ya fara fitowa"Idan kin ga dama ki sauko idan baki ga dama ba ya maida ke gidan hajia."

Yana faɗa ya shige abinshi yana tafiyar kasaita da izza.

Kamar ta ce direban ya maida ta gurin hajia sai kuma ta fasa ,ta sauko ta bi bayan shi a falon ta isko shi,tana kuka ta karasa gurin shi ta ce"Idan na koma zance kaika kuro ni,ka ce na dawo."

A fusace ya miƙe har zaiyi wata magana ya fasa tuno halin Sabreen ba abinda ba zata iya ba,wani mugun kallo ya mata sanan ya juya ya haye sama.

Har lokacin bata daina kuka ba,kallon falon tayi ya mata kyau sosai,kan gujera ta hau,tana ta kuka har barci ya ɗauke ta.

Daman yasan gidan ya kuma zaɓa ɗakin shi,yana zuwa ya shige saida yayi wanka yayi sallah sanan ya kwanta,ya daɗe yana tunanin irin zaman da zasu yi da sabreen sanan shi ma barci ya ɗauke shi.

~~~~~~~~~~~~~

"mtseww!

"Wai ke wa kike ma wanan tsakin tun ɗazun."

Wani mugun kallo tayi mata sanan ta ce"Ban sani ba".

taɓe baki tayi ta cigaba da yin abinda take yi.

Kallon wayarta tayi ta ce"Naufal meke faruwa ne?

ƙanwarta wacce suke zaune a ɗakin ta kalleta a ƙaro na biyu ta ƙara cewa"Ai daman na sani"

"Kin san me,banson iskancin banza."

Tana rufe baki saƙo ta whatssap ya shigo wayarta,kamar ba zata duba ba,dan baƙowar number ce.

Sai ta duba, a tsorace ta miƙe tsaye haɗe da zaro idanowa,xuciyarta ta fara bugawa da ƙarfin gaske"Wa.i..y.."
Numfashin ta ya fara sarƙewa dushu-dushe ta fara gani.

"Aunty haulat lafiya mai ke faruwa? a ruɗe take tambayarta,ko kafin ta ƙarasa gurinta ta faɗi kasa zummama.

"Innalilahi! momy momy Aunty haulat mun shiga ukku.

~~~~~~~~~~~~~

kiran sallar farko a kunnan Sabreen a ruɗe ta fara tambayar kanta "Nayi Sallah jiya?
"Innalilahi ta faɗa da sauri ta miƙe tuno bata yiba,saman ta hau a ruɗe ,kasancewar bata san wani ɗaki ba ne tashi ta faɗa dakin shi,bata ma lura da yana kwance akan gadon ba tayi toilet da Sauri.

Jin ƙarar ruwa ya farkar da shi,kunna guluf mai hasken yayi,"waye a baya" ya faɗa a hankali saukowa yayi,sautin tafiya taji a tsorace ta ce"Waiyo Allah na waye"

"Ke meye ya kawoko ɗaki na?

"Bansan ɗakin ka ba ne"

"Bakin san ɗaki na ba ne".

"eh!

"To fito nima zan shiga ne".

"Waiyo karka shiga ya hakuri dan allah dan allah".

Dariya ta bashi a ranshi ya ce "Kamar wata wacce zan ga wani abu ƙwaila da ita"

Murmushi ya fara yi tuno hali irin na ta,mawuyacin abu ne ta ba mutum hakuri,amma yanzu harda wani haɗa shi da allah.

"To na baki minti biyar kafin na dawo ki fito"

Yana faɗa ya juya yana murmushi.

Tana jin ya fita ta fito da sauri,ta faɗa ɗayan dakin wanda ba tazara a tsakanin su da juna,tana shiga ɗakin ta kulle,kallon ɗakin ta tsaya yi,ganin zai shagaltar da ita yasa ta maida hankalinta akan abinda zata yi.

Yana dawowa yaga bata nan daman yasan ba ganinta zaiyi ba,shiga toilet ɗin yayi ,saida yayi wankar tsarki sanan ya fito ya gabatar da ibada.

Zaune yake kan sallayar yana hailala da tasbihi wa ubangijinki,tunanin Haulat ya shigo ranshi zumbur ya miƙe ya fara naiman layinta...

Ringin wayar tayi har ta katse ba'a ɗauka ba,tsoro ya kama shi,tunda yake da Haulat bata taɓa ƙin ɗaukar wayar shi,cikin hanzari da zaƙuwa ya ƙara kira,nan ma shiru ba'a ɗauka ba,saida yai kira biyar abinda bai taɓa yiba ,amma shiru ba'a ɗau wayar ba,jefar da wayar yayi akan gado ransh a ɓace,haɗe da hura hanci.

"Haulat Allah yasa kina lafiya?
"Taya zata kasance cikin lafiya bayan abinda ka mata."

Da kanshi yayi tambayar kuma ya ya ba kanshi amsar da ta ƙara ruɗa shi,yasan bai kyauta ma Haulat ba,ya kamata ya sanar da ita koma meye,yanzu idan taji a bakin wani fah.

Tashi yayi ya fara safa da marwa a tsakiyar ɗakin,lissafin shi duk ya dagule,kanshi yayi zafi tunanin halin da masoyiyar shi take ciki yake yi,wanda ya ɗaura laifin akan Sabreen ko kaɗan baya jin zai iya raga mata kan abinda da mishi,zumbur! kamar wanda aka tsungula ya fito da sauri,bibbiyu yake taka matalakar dan sauri,har ya iso cikin falon bai kula da mutanan dake ciki ba,ya fara ƙokarin fita.

"Ango Naufal ina kuma zaka je ka bar amarya ita kaɗai."

Tsayawa chikk yayi sakamakon jin muryar ko ta wacece,a hankali ya juyo dan ƙara tabbatarwa zaro ido yayi ganin ba ita kaɗai ba..

"Naufal saurin me kake yi,baka kula da mu ba."

Momyn shi ta katse mishi tunanin shi,kallon su yayi,Hajiaya ce ita da Momy da farrah sai Sabreen ɗin wacce ke manne a jikin Hajia, "Meye kuma ya kawo su da safe haka? taya zasu zo mana gida a irin wanan lokacin jiya ne fah muka tare", a ranshi yake wanan tambayar,"To meye wani abun zamu yi waɗan da ba son juna muke yiba",duk a zuciyar shi yake wanan tunanin,bai san lokacin da ya ƙaraso tsakiyar falon ba,sai jin shi yayi zaune a ƙasa,cikin harɗaɗiyar murya haɗe ta aro murmushi ya yafawa fuskar shi ya ce"Ina Kwana momy."

Bai tsaya jiran amsarta ba ya juyo da kallon shi ga hajia ya ce"Ina kwana Hajia ya gajiya."

yana kai aya hajia ta ɗauka"Lafiya lau Naufal ka barni da kewa shi ne ko tambayata baka yiba,au naga kamar ba baka so ganin mu yanzu ba."

Kallonta yayi ,yana tuhumar kanshi akan maganar da ta gayamishi ,a fili ya ce haɗe da ɗan guntun murmushi, "Ba haka bane hajia,ya kewa?

"Ba sauƙi jiya ban iya barci ba ,da zan iya da nayi kishi da kai"

Gaba ɗayan su sukai dariya banda Sabreen wacce ta murtike fuska.

"yi hakuri Naufal munzo kawo abinci ne da farrah zata kawo to sai hajia ta ce tana son zuwa."

Murmushi yayi ya ce"Ba komai Momy."

"Amma ina kake ƙokarin zuwa?

"Am..amm..da. amman daman zanje gurin hajia ne na samo mata abinci bata ci komai ba."

ya faɗa yana kallon Sabreen ɗin yana mata guntun murmushi.

Charab hajiar ta ce"Hm to na hutar da kai,amma naji daɗi da kake nuna kulawarka akan Sabreen na gode Naufal Allah ya biyaka da aljannar shi."

"Ba komai Hajia ko kin manta Sabrewn ƴar uwata ce,zan iya yin komai a matsayinta na ƴar uwata,sanan kuma matata! daidai gurin yji zuciyar shi ta buga ƙara maimaita kalmar yayi "Matata!

Wani irin kallo Sabreen ta mishi na mamaki,shi ma ɗago kai yayi suka haɗe ido mugun kallo suka yiwa junan,amma sai suka yi murmushi.

Wani irin daɗi ya mamaye Momy wanda ta kasa ɓoyewa sai yaƙar baki take yi,kamar Ango.

Ita kanta farrah dake gefe murmushi take yi,dan jin daɗin yadda naufal ya aminta da ita cikin ƙanƙanin lokaci haka.

Wai kuma kunsan farinciki gurin hajia ba sai ance komai ba.

Sun ɗan taɓa fira kaɗan,sanan momy ta kalli hajia ta ce"Hajia to mu tafi ko,yadda zasu sake su iya cin abincin da kyau."

Kallon momy yayi a ranshi ya ce"Hm wai mu sake kamar wasu masu cin amarshi."

Sabreen naji abinda momy ta ce,idanowan ta sukai jajir kwalla ta shika su famm,cikin murmuyar kuka ta ce"Hajia yanzu tafiya zaki yi."

Momy ta ce"Kinga idan kuka zaki dunga yi,xata daina zuwa,muma zamu daina zuwa,kina son gobe ta zo?

ɗaga mata kai tayi alamar eh.

"Toh idan kina so ta zo gobe,kiyi shiru."

"Tohhh! kawai ta faɗa.

Kallonta hajia tayi ita ma hawayen ne a idonta ta ce"Kiyi shiru kinji ga mijinki nan zai tayaki zama,kuma baga waya ba,sai ki kira ni mu gaisa."

"Ba zaki xo gobe ba."

"zan zo."

A tare suka fita fita har harabar gidan,suna kallo suka shiga motor,Sabreen sai hawaye shaaa kamar famfo,ko kallon inda take baiyiba ya juyo ɗakin,yana zuwa ya janyo kulolin abinci ya fara ɓuɗewa,kunon gyaɗa ne sha madara sai waina da miyar ita kanta wainar sai tashin ƙamshi take yi,miyar ma haka ga nama zaƙo-xaƙo,sai dangalin turawa soyayye da dafaffe wanda ya haɗe da hanta, sai kuma farfeson kaza,da soyayyan gwai harda lipton,kallon abincin yake yi yana yamutsa fuska kamar wanda yai arba da ɗanyan kashi.

Kunon gyaɗan da waina ya xuba ya fara ciki,yana cikin ci Sabreen ta shigo,kallon shi ta tsaya yi.

"Waya ce ka cimin abinci ai ba kai aka kawo mawa ba."

Bai ɗago ba balle ya tanka ta,saida ya gama ci ,tana kallon shi yana hura hanci kamar warin abincin yake ji.

Yana gamawa ya tashi saida ya fara goge hannunshi da hankey sanan ya tashi har lokacin bai kalla inda take ba.

"Ina zaka?

A fusace ya juyo gabanta ya ƙaraso dabb da ita har suna jin fitar numfashin juna,kallon ta yayi ido cikin ido ya"Momy ko Dady,kuyi hakuri dan allah zani gurin wacce nake so ne."

"Toh ban aminci ba."

Dariya ya fashe da ita sosai yana mamaki hali irin na Sabreen,a lokaci ɗaya kuma ya murtike fuska kamar ba taɓa dariya ba,rikiɗewa yayi ya dawo ainihin Naufal mara dariya ɗan gilibibi da iyayi da yatsine isa izza mulki.

kallon ta yayi ya ce"me zan miki idan na tsaya?

"Ai.. dan...

"Hm Sabreen dan kin aure ni,da ƙarfi ba ki da ikon juyani,kin gane yana maganar yana ƙarya harshe cikin iyayi.

Kallon ƙaramin bakin shi Sabreen ke yi,yadda yake fito da maganar take kallo.

Ƙara matsuwa yayi dabb ta ita ƙokarin haɗe bakin su ya fara yi,tureshi Sabreen ta fara ƙokarin yi,amma ina ta kasa.

"Yadai ba abinda kike so ba kenan."

"Allah ya kyauta ni ba ƴar iska ba ce."

"Ni kuma ɗan iskane,u know what Sabreen?i cant share anything with you,"

"Ni bana jin yaren india."

Haba me Naufal zaiyi dariya ya fashe da ita harda komawa baya ya zauna kan gujera.

Ta ƙule gurin takaici hararshi take yi ,shi baima san tana yiba,saida yayi me isarshi sanan ya tsaya ,ɗaure fuska yayi ya ce"u are very funny Sabreen."

Ko kaɗan Sabreen bata gane abinda yake faɗa,ko hausar ma ba ko wani lokaci take ganewa ba.

Fita yayi yabarta a tsaye tana jin hauci.

"Kai Anya banyi kuskure ba,gashi gurin Haulat zaije kuma sai ya gayamata abinda ya faru ni nace zan aure shi baya so na,waiyo allah na yanzu ya zanyi? ya zanyi???

Naime naime ta fara yi,chan ta hango abinda take naiman wayarta ce.
"To yanzu wa zan kira?
"Dady nace mishi me?
"Na kira Naufal yawwa shi ,to me zanje mishi ya dawo.

Cikin rashin abinda zata faɗa mishi ta kira shi,yana tafiya a cikin motor shi da tunanin yadda zai fusanci Haulat a ranshi,jaji ringin ɗin waya,baƙowar number ya gani dan bashi da number ta,kamar kar ya ɗauka sai kuma ya ɗauka,tana jin ya ɗauka tai shiru.

"Hello! waye?

"Ya Naufal ka dawo gida yanzu Dady ya zo yana son ganinka."

"Ohhh no! Am coming" yana faɗa ya katse wayar ya juyo da sauri a zuciyar shi yana tausayawa kanshi halin da zai shiga,ya kamata a kyaleshi ya sarara amma yaga alamar ba'a da niyyar barin nashi.

"To ni yanzu idan ya zo me zan ce mishi,ko na ƙara mishi wata ƙaryar ."

"Ah'ah ba zan kara mishi wata ƙaryar ba,gaskiya zan faɗa mishi."
"To idan yaji hauci fah?
"to sai me ba abinda ya isa ya miki"

Murmushi tayi haɗe da juyo kanta"Hm ni ce fah ƴar aljanna ƴar gata kuma shalelen Hajia da Dady,sai abinda na ce,baka da yarda zaka iya Ya Naufal zan juyoka"

🤕waiyo aka ce raahin sani yafi dare duhu Sabreen kina da ƙuruciya kuma kinyi kuskure.

Tana gaba faɗa ta haye sama tana jin daɗi,wanka tayi ta saka riga da sikit na atamfa shiff-shiff suka mata kamar dan jikinta aka yi kayan,ko mai bata shafa ba,ta fito falo ta zauna akan 1seater ta kunna tivi tana kallo hankali kwance.

********************

Kwance take akan gadan ta hannuta ɗauke da drip,barci take yi,tun jiya har yanxu bata farka ba.

Momynta ta kalli ƙanwarta salma ta ce"Kai salma lamarin Haulat yana ban tsoro ,ban taɓa tunanin akwai namijin da zata shiga wani hali akan shi ba,tun yaushe nake gaya muku,daga kun ga abinda yake son ya gagareku ,kuje gurin malam gajere zai warware muku komai amma kun ƙi jira kuke yi saina kama ku na kaiku".

"Ba haka ba ne momy,shi ma yana sonta dan ya sha matsa mata akan ta bashi izini ya turo."

"Yana sonta shi ne zai aura wata ke baki ga hoton ba,yadda suke wa juna kallon soyayya."

"Wllh momy yana sonta bansan yadda aka yiba,kuma ita ma tana da laifi tunda tun lokacin yake mata mita ya fito taƙi amcewa."

"Ni na kasa gane abinda kike son faɗi,kina nufin wanan zoƙeƙen saurayin ne zai tsaya a mishi auran dole,bari kiji yanzu ko wacce mace ba'a zaune take ba ,musamman ma shi wanda kowacce mace ke buri ,to da ƙyalla ido ta ganshi bazata bari ya ƙuɓuce mata ba,amma ita dayake bata da wayau shashace ta zauna haka ai gashi nan tana ji tana gani an ƙwace mata shi,ba yadda zata yi."

"Hm momy kenan ai ko ni kinsan ba hakura zanyi ba,balle Aunty Haulat kuma akan abinda tafi so a duniya ai wallahi zata iya yin komai akan shi,ba zata haƙura ba."

"To da dai yafi mata,ta ɗau mataki,akwai wani sabon malami wanda ƙawata tamin hanyarshi ya iya aiki,aikin shi kamar yankan wuƙa yake,idan ta tashi sai muje a san yadda za'ayi"

"Yawwa momyn mu shiyasa muke sonki kuma muke alfahari da ke allah yabar mana ke."

Murmushi tayi ya ce"Hm dole na so ku,ban yarda da rashin nasara ba,shiyasa zanyi komai akan nasararku.....

.
[12/22, 5:26 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: _ 🇵σѕт 🇧у 🇬яσυρ 🇴 🇫 🇭уρє 🇭αυѕα 🇳σνєℓѕ 🇧σσк 🇼нαтѕαρρ 08064400100_ 📚📚
[12/22, 5:28 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: 🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹


*By*
*fatima* *Batula*

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
Page 12

.............................................................................................

🌈 *FALALAR* *KWANCIYA* *DA* *AL* *-* *WALA* .

_Hadisi ya inganta daka *Annabi Sallallahu Alaihi wasallam* yace:_
*→(من بات طاهرا بات في شعاره ملك فلم يستيقظ إلا قال الملك :اللهم اغفر لعبدك فلان فإنه بات طهرا)*
...•
_( Wanda ya kwanta da alwala, mala'ika zai kwana acikin mayafinsa bazai gushe ba yana masa Addu'a yana cewa "Ya Allah ka gafartawa bawanka wane domin ya kwanta yana da tsarki (alwala)"_
...•
_*Abdullahi bin Mubarak yaruwaitoshi acikin littafinsa "azzuhudu" (64) ta hanyar hasan bin Zakwaan, Ibnu hibbaan ya fitar dashi acikin saheeh dinsa (1052).*_
...•
_Saidai isnadine mai rauni, domin Alhasan bin Zakwann imamu Ahmad ya raunatashi da ibnu ma'een da sauransu.._
...•
_*Duba Mizanul I'itidali (1/489),*_
...•
_Amma yanada wani hadisin dake mara masa baya wanda imamul dabarany yaruwaito acikin *Mu'ujamul kabeer (13620) da waninsa.*_
...•
_Hadisin dake goyawa wannan baya wanda imamu dabarani ya ruwaito daga Abdullahi bn Umar Allah ya kara masa yarda shine wanda manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace:_
*→"( طَهِّرُوا هَذِهِ الْأَجْسَادَ طَهَّرَكُمُ اللهُ، فَإِنَّهُ لَيْسَ عَبْدٌ يَبِيتُ طَاهِرًا إِلَّا بَاتَ مَعَهُ مَلَكٌ فِي شِعَارِهِ لَا يَنْقَلِبُ سَاعَةً مِنَ اللَّيْلِ إِلَّا قَالَ: اللهُمَّ اغْفِرْ لِعَبْدِكَ فَإِنَّهُ بَاتَ طَاهِرًا )*
...•
_Ma'ana"ku tsarkake jikinku Allah zai tsarkake ku, domin babu wani bawa da zai kwanta da alwala face mala'ika ya kwana tare dashi acikin mayafinsa babu wani lokaci a cikin dare da zai shude face wannan mala'ika yanai masa addu'a yana cewa: " ya Allah ka gafarta wa bawanka domin ya kwanta da alwala"._
...•
_Wasu malamai Suntafi akan hadisine kyakkyawa saboda wasu hadisan da suke mara masa baya._
...•
_Duba *"Attargeebu wattarheeb, na munziry (1/231) da muj'ma'ul zawa'id na haisami (1/226) da Sil-sila saheeha na Albany (2539), dabarani yaruwaitoshi acikin Ausaad (5087) daka ibn Abbas*_
...•
_isnadan hadisin dukkansu babu wacce ta kubuta daka wata tawaya saidai idan ka hadasu wani yana karfafa wani saboda haka Albani ya hukunta hadisin da cewa kyakkyawane idan ka hadashi da waninsa. *Saheehul Targeebu wattarheeb (599).*_
...•
_*Falalar karanta Suratul Mulk*_
_Falalar karanta Suratul Mulk (Tabarakallathi biyadihil Mulk) tazo adunqule sannan kuma Falalarta tazo kafin kwanciya bacci a kebance, *Imam *Tirmidhiy yaruwaito hadisi (2891) da Imam Ahmad a cikin musnad nasa hadisi na (7915) daga Abu huraira Allah ya kara yarda dashi* daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Akwai wata Sura mai aya talatin a cikin Alqur'ani, ta ceci wani mutum har aka gafarta masa, itace Suratu Tabarakallathi biyadihil Mulk), Sheikh Albani ya ingantashi a cikin sahihul Tirmidhiy "_
...•
_*Tirmidhiy ya ruwaito hadisi (2892) da Imam Ahmad (14249) daga Jabir Allah ya kara masa yarda"* Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya kasance baya barci har sai ya karanta Alif laam miim Tanzeel da kuma Tabarakallathi biyadihil "Sheikh Albani ya ingantashi a cikin sahih sunanul Tirmidhiy._
...•
_Abinda yafi shine mutum ya karanta Suratul Mulk kafin ya kwanta barci a kowane dare, saboda irin yadda Annabi tsira da amincin Allah su

Please Login or Register in order to submit comment