Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sha magani su ka cigaba da firar su cikin jin daɗi.

Yau kwanan Sabreen ukuu a asibiti tare da Naufal,yanzun kam jiki yayi sauƙi sosai da sosai,shaƙuwa ta shiga tsakanin su mai ƙarfi,musamman Naufal wanda ya gama tabbatar da ya kamo da ciwon son Sabreen,wanda yake jin duk wani fitar numfashin su tare su ke fita,ga wani irin mugun kishi.

Zaune ta ke kan kujera shi kuma yana zaune kan gado idanuwan shi duk sua kan ta,tunani ta ke yi a ran ta,"Ta ina zan fara mishi maganar su dady gashi yau za su zo gurin shi,yanzun ya zan yi," ɗago wa tayi haɗe ido su ka yi tai murmushi murmushi da ido yai mata magana da lafiya kuwa dan ya ga fuskar ta akwai abinda ta ke son faɗi.

Saida ta ja garuwar ajiya zuciya sanan ta ce,"Ɗazun su Dady sun zo kana barci,"idanuwan ta suna kan shi dan taga yanayin da zai shiga.

ƙasa yayi da kai wani abu yana bijiro mishi a rai,ganin hakan yasa ta kama hannuwan shi ,ta raunana murya ta ce,"Dan allah karka ji wani abu wllahi dady da momy duk sun yafe ma,kaddara ce,ka kwantar da hankalin ka."

Runtse idanuwan shi yayi abubuwan da suka faru suna dawo mishi,ahankali ya buɗe su,saida sabreen ta tsorata ganin yadda idanuwan su ka canza sukai jajir,rungume shi tayi,"Dan allah kayi hakuri kar wani abu ya same ka,ba wanda ke fushi da kai."

A hankali yaji zuciyar shi tana mai sanyi,amma yana jin nauyin iyayen shi harda sabreen ɗin,saidai ya kasa gane dalilin da yasa ya aikata irin wanan ɗayan aikin ki,ji ya ke kamar ba shi ba,taya zai yi zina abinda ya tsana a duniya,wasu zafaffan hawaye sukai nasarar zubu mishi,ƙokarin yin magana yake yi amma maganar taƙi fitowa.

Kuka Sabreen ta fashe da shi,saida yaji wani radaɗi a ran shi,cikin kukan ta ce,"Dan allah kayi hakuri nasan ba laifin ka ba ne laifi na ne,bana sun su dady su zo su ganka a haka,kayi shiru."

Shafa kan ta yayi yana jin zafin hawayen ta,tamkar shi ke yin su,janye ta yayi su ka fuskanci juna da ido yayi mata magana da tayi shiru,zuwa yanzu Sabreen ta iya magana da ido sosai ,ita ma da idon tayi mishi magana ta yayi hakuri ya natsu,share mata hawayen yayi,shiru su ka yi kowannen su yana ƙokarin samawar zuciyar shi.

Sun ɗau lokaci a haka suna kallon juna kafin sabreen ta janye jikin ta,kasa ce mata komai yayi duk da kasancewar ba ji daɗi ba,bayi ta shiga wa wanke fuska sanan ta fito,ta dawo ta zauna ɗan nisa da shi sanin su dady zasu iya zuwa any time,kallon ta kawai yake yi yana mamakin hali irin na ta,yasan ya mata mugun laifi amma bata nuna mishi ba ko kaɗan sanan har ta ke ɗaurawa kanta laifi,lallai yasan halin dady kuma ba xai manta kalaman shi ba,yanzu ya yafe mishi wanda ko shakka babu sabreen ɗin ta buƙaci haka,runtse idanuwan shi yayi yana ƙara jin wani irin mugun azababben son sabreen na ratsa zuciyar shi lallai ta haifu,shi kuma yaci amanar iyayen shi da marainiyar allah.
ganin yadda ya kulle ido yasa sabreen kiran sunan shi,"Ya Naufal!,kai tsaye zuciyar shi ta amsa saƙon muryarta,a hankali ya bude idon.
"Yah kayi hakuri dan all..
"Ke kin hakura."
"Na hakura ai baka min laifin komai ba,ni ka hakura duk abinda haulat tayi dan na ji haushi ne sann.....

Sallamar su dady ne ya katse ta,da sauri ta ƙarasa gurin shi,amma ta kasa rungume shi,shi ne ya rungumu ta,shi kuwa naufal yana jin su yai ƙasa da kai wata irin kunya ta mameshi musamman momy.

Kowannen su kallon su naga naufal wanda yai ƙasa da kai,farrah ce ta fara ƙarasawa gurin shi,fuska ɗauke da annuri ta ce,"Brother ya jikin?

kan shi a ƙasa ya ce,"Da sauƙi sosai."
"Allah ya kara sauki yaya.",yaji daɗin yadda yaji tana mishi magana wanda hakan yasa ya ɗan ji daɗi.

"mutum india ya jikin? kabar amarya da damuwa gaskiya kaji sauƙi kasan bana son ganin damuwar ta,gashi ka siye zuciyar mu," cikin dariya ta ƙasara maganar,dariya kowa yayi harda momy da dady wanda ba ƙaramin daɗin hakan yaji ba.

Kusa da shi kaɗan momy ta matso shi kuwa har lokacin kan shi na ƙasa bai hadda ido da kowa ba,duk sun fahimce kunyar su yake ji sai tausayin shi ya ƙara kama su.
"Naufal ya ƙarfin jikin."
Rawa bakin shi ya fara ji,"da saauƙƙii."
ganin ya fara daburewa yasa ta faɗin,"Sauƙi sosai,dan yau zamu koma da kai gida, gidan duk ba daɗi ",idanuwan ta na kan shi,ta ƙarasa maganar,lumshe ido yayi yana jin wani irin sanyi a ranshi momy ce ke mishi magana kamar yadda ta saba kenan batai fushi da laifin da ya aikata ba,ganin yanayin da ya shiga yasa dady ƙarasowa inda yake ya ce,"Naufal halan dai baka son zuwa gida ne."

Lokaci ɗaya yaji bugun zuciyar shi na ƙaruwa,koƙarin faɗa da numfashin shi ya fara yi wanda ke koƙarin ɗaukewa,ganin hakan ya ruɗa su dady sosai,zama yayi kusa da shi ya dafa kafaɗar shi ya ce,"Naufal gudun iyayen ka kake yi? kana tsoran mu ne? naufal ba ka da wasu bayan mu,ko meye ya faru mu iyayen ka ne,plss my son ka kwantar da hankalin ka,kaddara ce wanda,Allah da kan ce ya ce," *Idan* *yana* *son* *mutum* *da* *alkairi* *sai* *ya* *jarabce* *shi* ."

Saida ya numfasa sanan ya ɗaura da faɗin,"Naufal allah yana son ka da alkairi ya jarabce ka dan ka kiyaye gaba,ba lalai abinda ka aikata ɗabi'ar ka ba ce,ko kana da kuɗirin aikata hakan ba saidan kaddara ce jarabta,mun ƙara fahimtar abubuwa da yawa faruwar wanan abun,wanda ni kai na,na gane kuskure na,na gaya ma irin waɗan nan kalaman ,wanda yanzun allah ya nuna min,kuskure na duk sanadin faruwan hakan,sry my son mubar hakan a matsayin kaddara," jin hawaye na son fitowa daga fuskar shi yasa ya tsaida maganar badan ya gama ba.

Maganganun Dady sun yi tasiri sosai a jikin su,musamman naufal wanda yake jin shi wani iri tamkar an canza mishi duniya,rungume Dadyn yayi wasu zafafan hawaye su ka fara bin fuskar shi haɗe da kuka mai sauti,shi kan shi dadyn hawayen da yake makalewa su ka fito,haka zalika ko wanne da ke ɗakin saida ya kuka,sun daɗe a haka su na kuka ba wanda ya kalle wani balle yai kuƙarin ba da hakuri.

Shafa kan shi dady yayi yana faɗin,"Is okk kayi haba kai fa namiji ne."
ai kamar ƙarawa naufal kukan ya ke yi, daɗi ya haifar mishi da kukan,jin ya ƙara sautin kukan yasa sabreen ta kara fashe da matsanaicin kuka,da sauri hankalin su ya dawo gare ta,dariya su ka yi dukkan su har dady da naufal ɗin sanin abinda yasa ƙara kukan.

"Ka gani ko," dady ya faɗa yana kallon naufal ɗin wanda shi kuma idanuwan shi yana gurin sabreen.

"Ga gani ko,ni kai shiru dan allah dan ta samu tayi shiru ita ma," cewar hajia wacce idanuwanta ke kan naufal.
fashe wa da dariya su kara yi,ita kuwa sabreen gurin momy tayi tana kuka ta rungume ta.

"Kiyi hakuri kin ji,ƙyale su ba ruwan mu da su," cikin rarrashi tayi maganar su kuwa,dariya su ke kasa-kasa.

Sun sake jiki sosai kamar ba wani abun da ya fara,duk yadda su ka so naufal ya sake jiki ya kasa,dan ya kasa haɗa ido da kowa a cikin su,yana son kallon sabreen amma ya kasa dan tana jikim momy,yana dai ɗan taɓa fira kaɗan kaɗan,ba su damu ba dan sun san daman ba sai son mgn ba ne.

Tun daɗe suna fira jikin jin daɗi da nuna kulawa,wanda naufal yaji daɗi matuƙa wasai yake jin zuciyar shi sai wani daɗe ma ta jake ji mara misaltuwa,tun mantar da shi abinda ya faru,sun so a sallame su yau amma doctor zain ya ƙi,dole sai gobe shi kan shi naufal ɗin bai ji daɗi ba,ya so zuwa gida,amma ya nuna musu yau da gobe duk ɗaya ne a gurin allah,har gurin motor sabreen ta raka su farrah sai zolayarta ta ke yi bata kula ta,anan ma saida su ka rarrashe ta sanan ta ɗaurr bata yi kuka ba,tana tsaye har motor su ta bar asibitin sanan ta juya lokacin an kira sallar maqrib,tana zuwa ɗakin yana fitowa daga bayi,kallon juna su ka ji yayi kamar ya shekara bai ganta ba,murmushi su kai wa juna,da saure ya ɗauke kai tuno yayi alwala,sallaya ta shimfiɗa mishi ya hau,ita ma bayin ta shiga ta ɗauro alwala,baya da shi kaɗan ta tayi.

Tana zaune tana lazimi ya idar da sallar har ya gama lazimin ya juyo ƙura mata ido yayi yana jin wani abu yana tasar mishi,saida ya lumshe ido sanan ya ce cikin nakasassar muryar shi,"Me kika roƙar mana."
ɗagowa tayi ta kalle haɗe da sakar mishi murmushi,"Wa zan ma addu'a idan ba ku ba,kai Dady hajia momy farrah,ku ne duniyata rayuwata."
Tausin sabreen ya ƙara kama shi,"lallai bata waɗan da su ka fi mu,zan raini ki sabreen zan kula zan miki gata,kin min komai kin temaki ni kin min gata..
"Ya dai? ina kallon ka ɗazun kasa cin abinci ka yi."
Tashi yayi ya ɗauke sallayar ya koma ya zauna,da ido ya kira ta,kusa da shi ta zo janyota jikin shi yayi ya rungume ta tsamm,wata irin ajiyar zuciya ya fara sauke wa,zuwa wanan lokacin sabreen ta saba da runguma gurin naufal,saidai bata bari yai mata kiss duk yadda ya so.
"Ka ci abinci ka sha magani ",ta faɗa tana kokarin janye jikin ta.

"Meye sa ki kuka ɗazun?
saida ta gama janye jikin ta sanan ta ce, "ba komai."
Runtse ido yayi yana sauraran bugun zuciyar shi wanda ke buguwa da son sabreen,"Allah yasa ki amci da soyayyata sabreen ban san lokacin da zuciyata ta kamu da son ki ba,"a ran shi yai maganar.
Abincin ta zubo mishi kamar yadda ya saba ita ke bashi a baki,yaci sosai sanan ya sha magani,xama su ka yi su na jiran kiran sallar isha'i,ƙura mata idanuwan shi yayii,yana jin wani irin abu a ran shi kamar ya janyo ta ya haɗiye ta yake ji.

Jin kiran sallar yasa duk su ka tashi shi ya fara shiga yayi alwala sanan ita ma ta shiga,bayan sun idar da sallah,ya koma ya kwanta baya jin yin magana ita kuwa bata matsa mishi ba,dan ba wani damuwa tayi ba,kwanciya kawai su ka yi,kowa yana saƙar zuciya daga haka har barci yai awan gaba da su.

Kiran sallar farko ya tashi sabreen daga barci,tana tashi tayi addu'a sanan ta tashi gurin shi ta je dan tashin shi.
Shi kuwa a lokacin yana tsaka da mafarkin da ya saba yi,hannu ta kai ta taɓa shi,"Ka tashi lokacin sallah yayi."

Can cikin mafarkin yake jin maganar,ga shi a lokacin su na cikin love.
"Ka tashi! da ƙarfi ta faɗa wanda yasa ya tashi da sauri,yana haki yana nishi,a kan fuskarta idanuwan shi su ka sauka,janyo ta yayi jikin shi ya rungume ta yana wani irin nishi.
"Yah lafiya kuwa,ko jikin ne?
Daman ba'a cikin haiyacin shi ya ke ba,yasan dai yaji tana magana amma bai fahimtar abinda ta ke faɗi,hankalin shi baya jikin shi,gaba ɗaya ya ruɗe ya fita haiyacin shi,ta ko'ina a jikin ta yake kai hannuwan shi,ruɗewa tayi jin yana kokarin zura hannuwan shi cikin rigarta,gashi ta ƙwatar kan ta.

Cikin zaƙuwa yake wasa da halittar ƙirjin ta,zuwa yanzu Naufal ya ruɗe ya fita haiyacin shi,koƙarin yaga mata riga ya fara yi,kuka ta sake me ɗan ƙarfi shi be san ma tana yi ba,ganin yana ƙara kuƙarin raba ta da kayan jikin ta yasa ta ganna mishi cizo a kafaɗa,yaji zafi hakan yasa ya sake ta,yana sakin ta,ta faɗa bayi da gudu tana kuka.

Da ƙarfin gaske yake sauke ajiyar zuciya,ji yake kamar yayi hauka kwanciya yayi ya runtse ido,wani abu ke bijiro mishi a rai,ji yayi ba zai iya hakura ba,ko kaɗan bai taɓa tunanin haka sabreen ta ke ba,zumbur ya miƙe sai kuma ya dawo ys zauna,yana kuƙarin ba zuciyar shi hakuri,safa da marwa ya fara yi,duk dan yaji sauƙin abinda yake ji,da ƙyar ya isa sarrafa zuciyar shi ta hakura.

Ita kuwa tana faɗawa bayin ta fashe da kuka wanda bata san dalilin yin shi ba,saida tayi me isarta sanan ta tashi ta ɗaura alwala,kasa fitowa tayi dan tsoro da kunyar shi ta ke ji gashi lokacin sallah na tafiya.

Ganin bata da niyar fitowa gashi lokaci yana yi kuma sai yayi wanka yasa ya fita daga ɗakin,dan ba zai iya magana ba,balle da ita.
Jin shiruuu yasa ta ɗan leƙo ganin ba kowa yasa ta fito,ta fara sallah,tana cikin sallah ya shigo bayi ya shiga,yana fitowa ya fara sallar shi ma.

Gaba ɗaya kunyar shi ta ke ji,kan ta a ƙasa ta ɗan kimtsa ɗakin,bayan ya idar da sallar ya dawo ya kwanta,dariya yayi ganin yadda ta jin kunyar shi a ran shi ya ce,"Akwai aiki kuwa."

Ƙarfe bakwai daidai su Dady su ka iso asibitin ba su je office ɗin doc xain ba kai tsaye ɗakin suka nufo,suna zuwa sabreen ta washe baki tai kan su,cikin so da ƙaunar juna su ka gaisa,har naufal duk sun gaisa sosai cikin jin ɗaɗi,har lokacin naufal yana kula da sabreen bata yarda sun haɗa ido ba dariya ma ta ke bashi.

Basu tsaya ɓata lokaci ba,su ka tafi gurin doc xain dan ya basu takardar sallama,ya kuwa basu tare da musu fatan alkairi.
Har gurin motor doc zain ya raka su,yai musu sallama.
Naufal da Dady suna gama su kuma suna baya,har su ka isa gida,suna zuwa sabreen tai ɗakin farrah,shi ma ɗakin shi yayi,kowa ya watse.

"Yadai malama."
Kallon farrah sabreen tayi haɗe da taɓe baki,ta juyar da kan ta kawai.
Dariya farrah tayi ta ce,"Yarinya kenan ai ina kula da ke a asibiti ",cikin dariyar da zolaya ta ƙarasa maganar.

"ke fah ƴar iskace,ƴar sa ido kawai."
"Naji gayamin kun yi ne,kai lamarin ku sai ku asibitin ma."

Da sauri Sabreen ta tashi ta fita ɗaga ɗakin tana faɗin,"Idan na biye miki wuta zaki kai mu banza ƴar isaka kawai."

Dariya farrah tayi sosai,tana mmk hali irin n sabreen.

Tana fita tayi ɗakin hajia,saida hajia ta gama yi mata tsiya sanan ta barta,ta kwanta.

Shi ma yana zuwa ɗakin shi ya kwanta bayan yayi wanka da tunanin sabreen a ran shi,addu'a yake yi allah yasa dady ya barsu zu je gidan su.

Ita dai momy bata koma barci ba,abinci ta haɗa musu me rai da lafiya bayan ta gama ta koma ɗaki tayi wanka sanan ta fito,lokacin ƙarfe goma sha biyu da kwata,ɗakin Dady ta. shiga barci ta tarar yana yi tashin shi tayi,dan lokacin sallah yayi bayan ya tashi yayi wanka ya nufi ɗakin naufal dan su tafi masallaci tare,kafin naufal ya shirya an kira sallah,yana shiryawa su ka fita ya so ganin ta a falo .

Saida hajia ta idar da sallah sanan ta tashe ta,bayan tayi sallar ta koma ta kwanta hankali kwance ba tunanin komai a ranta.

Bayan sun dawo lokacin duk suna falo,ware idanuwa yake yi amma be hango ta ba,wani iri yaji yana marmarin ganin,"yanzun cikin nan mun dawo gida haka zaki tunda min,"ya faɗa a ran shi ,duk sai yaji da basu dawo ba.

Bayan sun zauna sun Dady ya tambaya ina sabreen,Hajia ta ce,"Barci ta ke yi."

"Ayyah ku barta ta huta tana buƙatar hutu,da nayi tunanin ko yau zaku tafi sabon gidan ku wanda na siya."

Wani irin daɗi ya kama naufal wanda saida ya kasa ɓoyewa kowa ya fahimce hakan.

"Amma ina jin ku ƙara hutawa bari dai sabreen ɗin ta tashi."

Nan ma saida labarin zuciyar shi ya isa fuska,"Ya dady zai yi haka",ya faɗa a ran shi,yanzu ba zai iya kayan wata mgn akan wanda dady yayi ba,da ya ce wani abu.

Har su ka gama cin abinci sabreen bata tashi ba,hankalin shiul baya gurin su,duk abinda su ka ce daga eh sai a'a ya ke cewa.

Tashi yayi ya shiga ɗaki,lokacin kowa ya tashi dady ya fita,wayar shi ya ɗauka,number farrah ya kira tana ginin kiran ta ɗauka da sauri.

"Ke turomin Number Sabreen yanzun nan",yana gama faɗa ya kashe wayar.

Dariya farrah tayi,"Hm su yaya manya,ko number matar ta ka baka da shi,tana mgnr tana tura mishi number.

Tunda ya katse wayar ya ƙura ma wayar ido yana jikin numberta,ganin soƙon ya shigo ya buɗe da sauri,kiran number yayi a ƙufule,ringin wayar ta fara yi ,ya ƙagara ta ɗauka.
Lokacin tana barci bata ji kiran ba ,har wayar ta katse,kira ya ƙara yi amma bata ɗauka ba,wani jin zafi yaji a zuciyar shi,gaba ɗaya sai yaji ya ruɗe taya zata mishi haka,idan ta guje shi a lokacin da yake fuƙatar ta,bai san yadda zai yi ba.

Kamar yaje ɗakin hajia yake ji,kwanciya yayi badan yana jin barci ma,"Taya zaki min haka ina son ki,"a file yake faɗin hakan

Karfe ukku da rabi sabreen ta tashi saida tayi wanka sanan ta dawo ta saka duguwar riga ƙirar dubai,kamar ance ta ɗauke wayarta ,tana ɗauka ta ga kiran"Ya Naufal" sunan da ta sa mishi kenan,kallon wayar tayi ta ce,"Lafiya kuwa",kiran wayar ta shiga yi.
Daman har lokacin be kwanta ba yana jin ringin ya ɗau wayar ganin kiranta yasa ya miƙe zumbur ya ɗau wayar.

"Sabreen",cikin sanyin murya ya faɗa.
A ruɗe ta ce,"Ba ka da lafiya ne jikin ne?
"Sabreen zuciyata ki zo ɗaki na."

A ruɗe ta jefar da wayar ta,tashi ɗakin shi ta nufa a ruɗe bata haɗu da kowa ba,tana shiga ɗakin ta gan shi a kwance da gudu ta ƙarasa,juyo da shi tayi duk ta ruɗe ta kasa magana ga bakin ta yana rawa.
"Sabreen zuciyata xata fashe!
A ruɗe ta taɓa zuciyar shi saida ta ƙara ruɗewa jin bugun zuciyar kuka ta fara yi rungume ta yayi.
"Sabreen zaki fasa min zuciya,son yi yayi min yawa dan allah ki cece ni sabreen."

Ta abai-abai ga ke fahimtar shi,ta kasa magana gashi ya haɗa ta da jikin shi,wanda tana jin dokan da zuciyar shi ke yi.
"Sabreen kimin alfarma ki zauna da ni,ki kula da ni ba zan iya rayuwa babu ke ba,plss sabreen ki amince da ni dan allah mu tafi gidan mu muyi rayuwar mu."

Ta kasa magana ta kasa fahimtar inda maganganun shi su ka nufa.
Shiruu dukkan su suka,sai zuciyoyin su da ke bugawa,sun daɗe rungume da juna,sanan ya ɗago ta suka fuskanci juna lauyin idanuwan shi duk sun canza wani irin yanayi ya tsinci kan shi,cikin dakusassar murya ya ce,"Sabreen pls ke amince da ni bazan cutar da ke ba."
kai kawai ta ɗaga mishi alamar eh,ƙara rungumota yayi,shiruu tayi tana jin yana kissin ɗin ta ko'ina.

"A'a yaya kayi hakuri dan allah,kar wani ya shigo fah."
danne zuciyar shi yayi ya sake ta,idanuwan shi a rufe,janye jikin ta tayi tana son fita daga ɗakin,hannuwan ta ya riƙo.
cikin muryar da bai yi tunanin zata ji abinda xai faɗa ba ya ce,"Stay with me sabreen i can't without u,ba zaki taimake ni ba."
maganganun shi sun kashe mishi jiki ainun,"me ye nufi yana son ta komai."
Cikin ƙarfin hali ta juyo ta ce lokacin hawaye sun fara zarya a idon ta,"Meyasa xan zauna da kai,bayan baka so na,Malama haulat keke so,ni saki na zaka yi."

Da ƙarfi zuciyar shi ta buga,kama zuciyar yayi ji yake yi kamar zata fashe dan yadda take mishi zafi,ganin halin da yake ciki yasa sabreen ta ruɗe riƙo shi tayi a ruɗe ta ce,"Waiyo Allah na! na shiga ukku! zan zauna da kai har ƙarshen rayuwata dan allah kar wani abu ya fara zan zau....
Haɗa bakin su yayi wanda hakan yasa tai shiruuu sai wasu hawaye da ke bin fuskarta wanda ba ta ce ga dalili ba,wanan karan dai shiruu tayi ta zubawa sarautar allah ido sai sarrafata ya ke yi yadda ya ke so.

Saida ya gama jagwalgwalata sanan ya ƙyale ta,badan komai ba sai dan tuno a inda su ke ,kallon ta yayi tana hawaye haushin kan shi ya kama shi.
"Dan allah kiyi hakuri kin ji na kasa sarrafa kai na ne,plss ki daina kuka,ya sa hannu ya share mata hawayen.

Rigarta ya fara gyara mata,daman bata saka komai ba sai rigar,idanowan ta a rufe tana hawaye.
Janyo tayi yayi,"Kiyi hakuri ba zan ƙara ba kin ji ki daina kuka,"lallashin ta yai tayi har ta daina kukan amma ta kasa buɗe ido ta kalle shi,gashi an kira sallar azahar.

"Sabreen ki buɗe ido kin ji Dady zai shigo yanzun kin son ya zo ya gan ki a..

Tun kafin ya rufe baki ta janye jikin ta,ta fita da gudu.

A lokacin Dady da momy sun fito,bata lura da su ba ta wuce da gudu,kallon kallon Su kai wa juna,murmushi momy su kai magana da ido wanda su kaɗai su ka fahimce inda su dosa,daman ɗakin naufal ɗin za shi har ya sa hannu zai buɗe sai kuma ya fasa ya juyo.

Ya daɗe anan inda ta barshi dan gaba ɗaya jikin shi ya mutu,sai can kuma yai ƙarfin hali ya tashi ya shiga bayi yayi wanka sanan ya fito yayi sallah.

Da gudu ta shiga ɗaki binta da kallo kawai hajia ke yi,kwanciya tayi tana kuka wanda ba ta ce ga dalili ba,ta kasa yin tunanin komai dan kwakwalwarta ta cushe.

Bayan sallar maqrib Dady ya tara su a falo,nasiha ya musu wacce ta ratsa ɗukkan jikin su,sanan kuma ya ce naufal ya ɗau matar shi su tafi,kuka sabreen kamar ranar farko da xata gidan naufal ,shi kuwa wani mugun daɗi ya maimaye shi saidai fuskar shi ta nuna,da ƙyar sabreen ta rabu da so,direba ne zai kai su gidan ,akwai ƴar tazara sosai dan unguwar ba ɗaya ba.

Kuka sabreen take yi sosai,kusa da ita ya matso duk da idanuwan ta a rufe su ke saida taji kunya amma ta kasa ko da motsi sai ƙara sautin kukan da tayi,riƙo ta yayi,cikin sanyin murya ya ce,"Sabreen baki so na?kina tsoro na ko?
Kamar bata san abinda ta ye faɗa ba tai banza da shi,ganin hakan yasa ya ce,"Sabreen plss ki daina kuka har cikin rai na nake ji,zan nuna miki so wanda ba wanda ya taɓa nuna miki irin shi,dan kiyi hakuri kin ji."
Anan ma shiruu tayi kamar bata jin shi.
"Ni dai ban taɓa ganin inda miji ke ba mata hakuri tai banza da shi ba,shiyasa Haulat ta fiki dan ta iya komai kuma duk abinda na ke so shi ta ke yi."
Kuka sabreen ta fashe da shi me ƙarfin gaske,rungumuta yayi,janye jikin ta tayi cikin kuka ta ce,"Daman baka manta da ita ba?
"Eh ita duk abinda na ke so shi take yi."
Kuka sabreen ta ƙara fashewa da shi.
"Yi hakuri kin ji Baby nah ke kaɗai na ke so a duniya a kan ki na san meye so,amma ban manta da haulat ba,dan ta iya soyayya idan kin so na manta da ita ki yi dukk abinda na ke so kin ji."
kalaman shi har ranta take jin su,ɗaga mishi kai wai tayi,wani irin mugun daɗi ya kama shi.

Gida ya haɗu yafi wance haɗuwa sau biyar,da koma da komai a cikin shi,ba su tsaya wani zagaye ba su ka shiga wani ɗaki,ya umarce ta da suyi sallah bayan sun idar ya kalle ta ya gane yanayin da ta ke ciki a ranshi ya ce,"Sorry Sabreen ba zan iya hakuri ba da na hakura amma ki kiyi hakuri da na."

Toh fah! an zo gurin ni dai ɗan abinda na sani kenan shi ma a book ɗin k/mashi na gani,nan gurin yafi ƙarfi na dan wllh ban san komai ba dan haka nayi nan🚶‍♀🚶‍♀

Cikin salo da wayau da dubara yabi da ita,amma sun sha kuka shi kuka ita kuka😅wai ni batool na kawo rahutan ƙarya.

~~~~~~~~~~~~~
Momyn haulat kuwa hauka tsuburan dan kulle ta a ɗaki ake yi,ita kuwa haulat gaba ɗaya ya sukurkunci kamar sabon kamon hauka haka ta koma,ga ɗaya rayuwar ta sauya musu daman momyn ke naiman kuɗin yanzun kuwa ba ta dan da ita da babu duk ɗaya.
Ba abinda su sakina ke yi banda addu'a dan basu ba je naiman magani ba,ita kuwa salma ta gane annabi ya fako,ita kan ta haulat ɗin

Please Login or Register in order to submit comment