Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗaya a ƙirjin shi.

Saida tayi alwala sanan ta matso kan shi ta taɓa sanan ta ce,"Miji na ka tashi lokacin sallah."

Shiru barci yayi nisa ganin hakan yasa ta matso kusa da hunnan shi ta hura mishi iska,motsi yayi amma bai buɗe ido ba,hancin shi ta fara ja nan ma shiruu na koma gurin idon shi ta fara shafa batar idon nan ma shiruu,ganin hakan yasa takai hannunwan ta kan lips ɗin shi ruwan alwalan da bai bushe ba na hannunta shiyasa lips ɗin suka jiƙe,shafasu ta ke yi,ta shafa da ƙasa ta shafa na sama nan da nan ya fara juya su kamar me kokarin cin wani abu,ganin hakan yasa ta fashe da dariya,wacce tai nasara isa ga dodon kunnan shi.

Firgittt! ya tashi kallon ta ya ke yi cike da mamakin abinda ta ke ma dariya.

Cikin dariya ta ce,"Wai Halan yunwa kake ji."

Cikin rashin fahimta ya ce,"Me?

"zan tashe ka ne ka ƙi tashi shi ne ta hura ma kunne na jajja hancin ka ƙi tashi shi ne da na taɓa ma baki ka fara motsawa kamar zaka ji wani abun."

Murmushi yayi labarin sabreen yana bashi dariya ya kuma bashi mamaki.

"To meye na dariya."

Har ta buɗe baki zata yi magana akai kiran sallah,"Kai ka tashi."

Tana faɗa ita ma ta tashi ta shimfiɗa sallaya sanan ta fara sallar nafila kamar yadda ta saba.

Ganin hakan yasa shi ma ya tashi ya faɗa toile bai ɗau lokaci ba ya fito gurin saka kaya ba bai ɗau lokaci ba ya fita.

Bayan ta idar da sallah ta fara aikin gyara ɗakin saida ta ƙimsa komai sanan ta wuce ɗakin ta,tana zuwa ta gyara shi sanan ta nufi kicin.

Yau bai zauna dan barci bai ishe shi ba,yana shigowa falon yaji ƙamshin abinci yana tashi,kallon hanyar kicin ɗin yayi kamar ya shiga sai ya fasa ya wuce ɗakin shi bai yi mamaki ganin shi tsab ba dan yasan halin ta ne,ya kula da ita sosai tana da tsabta har ta kusa fin shi,kwanciya ya koma yayi.

Bayan ta gama haɗa komai ta koma ɗakin ta,tai wanka ta shirya cikin riga da siket na atamfa,Karuwan jiki sabreen gare ta,irin jikin da ko wani irin shiga yana amsar shi,irin shi ne ka kan kasa gane al-adar mutum idan ya kasance mai yawan shiga iri-iri.

Bayan ta gama shirin ta tsab,kai tsaye ɗakin shi ta nufa,a hankali ta buɗe kofar,ganin shi kwance yasa ta ƙarasa hawa tayi kan gadon,naniƙe shi tayi,shi kuwa bai sani ba yayi nisa yakai ziyara golden pen😃

Ita barcin ne ya ɗauke ta.🚶‍♀nidai nayi nan asha barci lafiya.

~~~~~~~~~~~~~

"Baki san waye mutumin nan ba,bashi da mutunci kar mu koma mu bani mu lalace dan mugu ne."

Cikin kukan mai sauti Haulat ta kalli momyn nata ta ce,"Haba momy gaskiya mu koma kina gani momy ya daina so ba,na shiga ukku momy ya zanyi."

"Ai tun farko shi ya kamata ayiwa asirin ba ita ba,da shi aka mawa ya isa ya daina sonki bai isa,amma me kika buɗe baki kika ce min,ke baki son a mishi asiri kin fi son irin son da yake mi ki,to ai gashi kin ga ni irin son da yake miki dai ko yanzu kin ganshi."

"Har da it..

"Harda ita ko,ke banza ce har yau baki gane avubuwa da dama an gaya miki namiji irin macce ce."

A sanyaye ta ce,"Momy yana so na ni ce nai bishi abinda yaji haushi."

"Koma meye da anyi asirin bazai ji haushin ki ba duk abinda kika mishi saida ya baki hakuri."

"Momy to muje dan allah mu je yanzun nan."

"Tashi to mu tafi."

Cikin gaggawa suka tashi ko shiri basu yiba mayafi kawai suka ɗauka,a harabar gidan suka haɗu da sakina ta dawo daga makaranta ko kallon banza ba su yi mata ba.

Ita kuwa tana kallon yanayin su tasan ba hanyar allah zasu bi ba,aran tai musu addu'ar gafara da shiriya ta wuce avin ta.

~~~~~~~~~~~~~

Sama-sama ya fara fuɗe idon ƙamshi ya fara ziyarta hancin shi,na hanzari ya buɗe su dan tabbatar da abin da yaji,a hankali zuciyarshi ta fara bugawa da ɗan ƙarfi,lumshe idanuwa yake yi,kallon hannuwanta yayi waɗan da gaba ɗayan su suna rungume a jikin shi,kafafuwan ta duk suna kan cinyar shi,fuskarta kuwa tana ƙirjin shi kasan cewar yafi ta tsawo.

A hankali yasa zame hannun shi da ga jikin ta ya tallafo fuskarta idanuwa ya zuba mata,numfashin ta yana dokan fuskar shi,a ran ya ce,"kamar mu kasance a haka,"

Ko kaɗan baya gajiya da kallon ta,wani irin yanayi ya shiga wanda bai san irin shi,bai kuma taɓa shiga ba,saida ya ƙarewa halitta fuskarta gaba ɗaya kallon,ɗan ƙaramin bakin ta shi yafi ɗaukar hankalin shi,gai gashin idanuwanta,tsarin fuskar ya mishi kyau,hannu ya kai kan lips ɗin,da sauri ta buɗe ido,sai cikin nashi kallon ƙuda suka fara yiwa juna,cikin muryar da batai yi tunanin zai ji abinda zata faɗa ba ta ce,"Kai ma zaka rama ne."

Bai ji sautin muryarta ba amma motsin bakin ta ya gani,murmusawa kai yayi.

"Yaushe ka tashi?

"Ɗazun."

Shiru tayi sanan ta ce,"Kai baku ƙarya ba."

Janye jikin ta tayi ,wani irin abu ya zake shi a heart ɗin shi,ko kaɗan bai ji daɗin janye jikin ta ɗin da tayi ba,lumshe ido yayi yana jin wani iri a ran shi.

Hannuwan shi ta yanyo,"Ka tashi rana tayi."

Wani irin yaji kallon hannu yayi sanan ya kalle ta shagwaɓe fuska tayi haɗe da rausaya kai alamar ya tashi.

Kai tsaye zuciyarshi ta amsa umarnin ta,tashi yayi ya banɗaki ya nufa,ita kuma ta fita.

Ƙarfe goma sha ɗaya da rabi agogon bangon dake manne a jikin bangon fallon ya nuna.

Gurin abincin ta nufa ya ɗan rage zafi amma bai yi sanyi ba zasu ci a haka.

Bayan ya fito daga bayin saida ya zuba kasaita gurin shiri,cikin ƙananan kaya ya shirya sun mishi kyau ainun navy blue rigar sai baƙin wando,saida ya gyara fuskar shi da gashin shi sanan ya fashe jikin shi da turare,sanan ya fito.

Tun daga saman benan ya hangota tsintar kan shi da yin murmushi yayi wanda bai san dalilin yin shi ba,kamar ance ɗago kai ta ɗago suka haɗa ido murmushi suka sakar wa juna,wanda ya fito ne daga ƙasan zuciya.

Zama yayi,ta fara zuba mishi waina ta fara zuba mishi sai lipton da kwai,ita ma shi ta zuba,ba wanda yace ba wani ƙalla saida idan sun haɗa ido su sakar wa juna murmushi.

Dukkan su suka tsince zuciyoyin su cikin natsuwa da jin daɗi da farin ciki da walwala,ita ta fara gaba ci yana jin ta tsaya shi ma ya tsaya kallon shi tayi wai murmushi,"Nima na ƙoshi."

"Ka ci dai ka ga ni ko ban ci ba,ina da qiba ta,amma kai kuwa idan baka ci ba sai yadda...

"Kin fi ni qiba ne?

"Kam wa zai haɗa ma."

Kauda zancen yayi ya kawo wani ta hanyar faɗin,"Gobe ne fa!

"Wai zuwa honeymoon ɗin mu."

"Kin shirya ne?

"ƙwari kuwa ,kai baka shirya ba ne?

"Hmm na shirya zaida ke nake tunanin anya kuwa."

"Na shirya ma komai da komai ka daina shakka."

"Komai da komai fa kika ce."

"Eh komai da komai."

"To amma kin koya kuwa."

"Me?

"Haƙƙin miji!

"Ka fasa koya min ne?

Murmushi yayi mai ƙunshe da abubuwa da yawan gaske.

Bai kai ga bata amsa ba ta ce,"Dady ya ce,wai da wuri zamu tafi goben yau sai muje muyi musu sallama,amma fa ina ɗan jin tsoro kar wani abu ya faru mara kyau a can,ko da yake tsoran me zan ji ina tare da mijina ɗan uwa na,nasan ba zaka bar wani abu ya cutar da ni ba."

Ta ƙare maganar tana kallon shi,yanayin shi kuma ya ɗan canza wanda zai iya alaƙanta wa da maganar da ta mishi.

"Wai zanga fararan muta ne,ai nima kuwa irin sabulon su zaka sai min nayi fari irin na su."

Dariya ya ɗan yi,"Ai ke zama abin kallo ce a gurin su."

Saida ta ɗan zare ido,"Wai saboda muni ko.?

Wanan karan saida sautin muryar shi ya fito,ita kuwa ya mutsa fuska tayi tana kallon shi.

🚶‍♀🚶‍♀Ina zan iya muku dan firar ku bata ƙarewa.

~~~~~~~~~~~~~

Banka gudu Momy ke yi,har suka isa garin katsina ba wanda ya ce da wani komai,wanan ƙaran tsoron Haulat ya ragu.

Kamar yadda suka yi farkon zuwa yanzu hakan suka yi,saidai shi yanayin shi ya ƙara canzawa ya ƙara muna,kuma bai yi dariya ba kamar wancen zuwan sai uban ihun ta yake yi.

Ya daɗe yana amvaton shi yana ihiuu yana yarfe-yarfe dukan su sun tsorata ainun ganin sun daɗe bai ce musu uffam ba gashi sun daɗe da zuwa.

Cikin mummana kuma kaussar muryar ya ce,"Hatsabibiyar yarinya ce,da ƙyar ƙaranjuug yasha ya kasa kusantar inda ta ke,ba nazara ba nazaraaa,ba zai iya zuwa inda take bahhh."

Wata razanannar ihuu yayi wacce dan tsoro har hantar cikin su saida ta juya,hatta kasar gurin da bukkar zai da ta girgisa.

Bayan wasu ƴan mintina sanan komai ya lafa shi ma ya tsagaita.

Cikin rawar murya momy ta ce,"Yaanzuu shiii yaaron f."

Ai kamar ta ƙara tunzura shi ya ƙara buga wani sabon ihhu na tsawon sakonni sanan ya murtuke fuska,ƴan karance karancen shi da kalle-kallen shi yayi sanan ya bushe da muguwar dariya saida yayi mai isar shi sanan ya ce,"Akwai nazarraa Nazara,me kuke da bukatar ai mishi?

Har momy ta buɗe baki zata yi magana haulat ta katse ta,"Ya so ni kamar ya mutu sanan sai abinda na ce zai yi magana ta kaɗai zai ji sai yadda nayi da shi."

Dariya ya bushe da ita ,sanan kuma ya murtuke fuskar,"Wanan ƙaramin aiki ne amma akwai sharaɗi bai tsauri...

Kallon Momy Haulat tayi a tsorace sai zare ido take yi.

"Hhhhh maganar tsoro babu ita tunda kuka kawo kan ku ƙaranjuuug ya amshi saƙon ku dole ku yarda da sharaɗin."

Tsuull! fitsari ya zubowa Haulat tsabar tsoro da farga ba,kallon momyn take yi wacce ba alamar tsoro da fargaba ko kaɗan a idon ta.

Kallon shi momy tayi ta ce,"Kasan ni indai akwai nazara to ina amincewa da ko wani irin sharaɗi."

Dariya ya ƙara fashe wa da ita,wanan karan saida na tsorata da gudu na fito ina haki ina naiman taimako duk na ruɗe na kasa gane hanyar da zan bi,kawai sai ga Aunty beelat janyo hannu na tayi muka fara gudu,kwatsam sai ga ommu deedat da motorta tayi fakin a gaban mu,ai tsorum muka taɗa,ina shiga ng bloody a ciki janyo ni jikinta tayi ta fara jijjiga ni tana ban baki nayi shiru cikin raɗa ta ce min,"Bloody na ki kwantar da hankalin ki kinji ga shadowwn ki tana jiran ki tun dazun."

Cikin hanzari na ɗago na kalle ta😅😅🚶‍♀🚶‍♀🚶‍♀🚶‍♀🚶‍♀kunga dole na kama ɗariqa shadow tayi kira💃💃.

.

Ina mugun -mugun son ku har raina,ba abinda zan ce saidai allah ya barni da ƙaunar ku a raina❤.
[12/23, 2:24 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: _ 🇵σѕт 🇧у 🇬яσυρ 🇴 🇫 🇭уρє 🇭αυѕα 🇳σνєℓѕ 🇧σσк 🇼нαтѕαρρ 08064400100_ 📚📚
[12/23, 2:25 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: 🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹


*By*
*fatima* *Batula*
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
Page 18
.......................................

_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{BABU WANI AIKI DA AKE 'DORAWA AKAN MIZANI YA SANYA MIZANI YAYI NAUYI KAMAR KYAWAWAN HALAYE DA 'DABI'U, KUMA LALLAI MAI KYAWUN HALI YANA SAMUN MATSAYIN MAI RAYA DARE DA IBADA, DA RANA YA RAYA DA AZUMI.}*_

```[Sahihut Tirmizy;2003,Sahihul Jaami'i;1620]```

_Shi kyawun hali yana dauke da dumbin alkhairi wanda mai yi zai amfana da shi Duniya da Lahira. Allaahu a'alam._

```Allah ta'ala yasa mudace```

_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_


_______________________________

Wata mahaukaciyar dariya yayi mai haɗe da ihuu sanan ya murtuke fuska ya kalle Momy ya ce,"Kin yi nisa! asiri zai kama shi amma kuma duk sanda ya ƙarye kan ki zai dawo zaki haukace ne."

Ya kara bushewa da dariya sanan ya ɗaura da faɗin,"Kuma asirin ba mai nisan zango ba ne,duk sanda ya tambaye kan shi akan naiman dalilin da yasa yake bin umarnin ki kamar raƙomi da akala to ranar zai ƙarye."

Haulat dan tsabar tsoron jin abinda ya faɗa saida fitsarin da yake zulluwa ya fito gaba ɗaya,zuciyarta ta shiga buguwa da karfin gaske zufa duk ta wanke ilahirin jikin ta,kallon Momy tayi wacce ita kan ta tana cikin tsoro da tashin hankali.

Murya na rawa Momy ta ce,"Mun amince!!

Ya kwarara uban ihuuu yana kallon ta yana tasar baki,"Duk sanda yaji muryarki asirin zai fara aiki."

Ita kuwa Haulat kamar gunki haka ta koma,saida ya ƙara kwanciya da su sanan suka tafi.

~~~~~~~~~~~~~

Bayan sun kama firar suka shiya gidan su hajia suka nufa a can suka tadda dukkan su momy da dady da farrah,fira suka yi sosai dan Naufal ma ya manta da wata haulat ni kuwa na ce daman ba son nata yake yi ba.

Har bayan maqrib sunan nan zaune a falo Dady wacce Sabreen ke zaune akan cinyar shi ya zaunar da ita kasa gaban shi,kiran Naufal yayi ya zo kusa da ita ya zauna.

Cikin dattijowar murya ya ce,"Naufal!

Naufal wanda ke zaune a kasa gaban Dadyn kusa da matar shi ɗukar da kan shi yayi ya ce,"Na'am Dady."

"Naufal ba zan iya misalta maka irin farincikin da na ke ciki ba,duk da nasan ka ji magana ta kuma ka bi umarni na ka amshe matarka da hannu biyyiyu,amma hakan ba zai hana na ƙara tunatar da kai akan amanar da ka ɗauka ba,Naufal Sabreen amana ce na danƙama, ka sani Naufal ko wani irin yanayi zaka tsinci kan ka a rayuwar nan idan har ka cutar da sabreen ban yafe ma ba ko bayan ba raina bani ba ka."

Zuciyar Naufal ta fara bugawa da mugun ƙarfin wanda faruwar hakan yai sillar haifar mishi da mutuwar jiki,bai yi tunanin zai iya magana va yai karan banin buɗe bakin shi,"Dady na ma alkawari ba zan cutar da ita ba komai rintse komai wuya zan rayuwa da ita zan kyautata mata."

"Yawwa Naufal Allah yai maka albarka."

Jin amsar da Dadyn ya bashi ne ya tabbatar mishi da ya faɗi abinda ke ran shi kenan.

"Naufal ka ga Sabreen ba sabawa da zuwa irin ƙasacen nan tayi ba ,dan haka sai ka kula da ita sosai,Sabreen matar ka ce nasan ka fi ni sanan yadda zaka kula da ita,tsananin son da na ke mata ne yake sawa naga kamar ba wanda zai iya kula da ita,Naufal karka cutar da sabreen dan ni zaka cutar ,idan ka kyautata mata ka kyautata min,ina son sabreen fiye da tunanin ka jinin jiki na ce,ka kula da ita k....

"Ya isa haka kamar yadda kake son ta shi ma yana son ta matar shi ce,"
Cewar hajia ,kallon Naufal ɗin tayi fuskar ta ɗauke da murmushi wanda shi har lokacin kan shi yana ƙasa,"Naufal ba abinda zan ce ma sai abu ɗaya ni ma na baka amanar Sabreen shi ne kawai abinda zan faɗa ma,matarka ce ka fi mu sanin yadda zaka kula da ita,allah ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya."

Dukkan su suka amsa da amin,sanan momy ta kalle shi ta ce," nima abu ɗayan zan faɗa ma ka riƙe amanar Sabreen Naufal allah ya kaiku lafiya."

Nan mu suka amsa da amin,sanan suka ɗan taɓa firar duk akan tafiyar su ɗin labarin garin su ke yi,da gidan ya zasu sauka.

Duk abinda ake yi jikin Naufal a mace,zuciyar shi ta cunkushe wanda hakan ya hana shi yin tunanin komai.

Sai ƙarfe takwas suka tashi zasu koma gidan su,Sabreen tayi kuka kamar ranar auran ta tunda goben tun biyar zasu bar gida ba haɗuwa zasu kuma yi ba,da ƙyar aka janye jikin ta gurin hajia.

"Kiyi hakuri ki daina kukan nan plss."

Kallon shi tayi cikin kukan ta ce,"Ji na ke kamar na tafi kenan bazan dawo ba."

Saida gaban shi ya faɗi taka burkin motor yayi da sauri ya juyo
ya kalle ta,janyo ta jikin shi yayi ,"Hava ƴar aljanna yaushe kika zama haka ne ban san ki da rauni ba fah,taya zaki ce haka zamu dawo cikin ƙushin lafiya."

"Ba zamu daɗe ba ne."

"Eh ai sai yadda kika ce,idan kina so a fasa zuwan ma za'a fasa."

"A'a ina son zuwa."

"Kina son cin amarci kenan."

Murmushi tayi ta ɗaga mishi kai alamar eh.

"To ai baki iya komai ba."

"To ba ka ce zaka koyamin ba."

Ɗago kanta yayi kasancewar akwai haske a motor yasa ya ga fuskarta da kyau lipa ɗin ta ya fara kallo,haɗa bakin shi da nata yayi sun ɗau lokaci suna abu ɗaya kafin ya fara fita haiyacin shi,ganin abin yafi ƙarfin ta yasa ta fara koƙarin zame jikin ta,amma ta kasa.

"Ya Naufal!

Yaya yayi nisa nishi ya fara yi,janye jikin ta tayi da ƙarfi ita ma haƙin ta fara yi.

Sun daɗe a haka suna nishi wanda kowa ke jin na kowa,can ya ja motor cikin ƙanƙanin lokaci ya isa gidan.

Tunda yayi fakin ɗin ya tsaya yaƙi saukowa,ganin hakan yasa ta ce,"ka zauko."

Tana gama faɗa ta sauko gaba tayi bata tsaya jiran shi ba.

"ke ce kaddara ta Sabreen dole na karɓe ki ba yadda na iya,nasan wata rana zan son ki."

Ya daɗe yana tunanin ya amincewa zuciyar shi yin rayuwa da ita cikin kulawa ga alƙawarin iyayen shi baya son ya saɓa musu,kuma ko da ba alƙawari Sabreen abin tausayi ce marainiya ta uwa da uba dole a tausaya mata,ya yaken wa zuciyar zai koyan son ta idan sun je turkey .

Ita kuwa kai tsaye ɗakin shi ta nufa saida yi ɗan gyare-gyare sanan ta shiga bayi tayi wanka ta tauro alwala,shafa'i da wutiri ta yi.

Tana cikin yi ya shigo murmushi yayi dan san tayi sallar isha'i zama yayi bakin gadon yana kallon yadda take sallar komai daidai cikin natsuwa,bayan ta gama ta fara addu'o'i duk yana jinta saida ta yi komai sanan ta tashi da nufi ɗauke sallayar ganin shi yasa tayi murmushi.

"Ka shigo? na haɗa ma coffee?

"Eh lipton ki matsa lemon tsami."

"To wai kana jin daɗin shi ne."

"Eh!

"Nima zan haɗa na sha."

Vata tsaya jin avin da zai ce mata va ta bar ɗakin,saida ta shiga ɗakin ta sanan ta sauko kicin ɗin ,cup biyu ta haɗa duk ta saka lemon tsamin sanan ta nufi ɗakin.

Da sallama a bakinta,ta isa ɗakin,can ƙasa ya amsa mata gaban shi ta je ta ajiye mishi sanan ta ɗau na ta.

"Kin saka ma naki lemon tsamin ne?

"Eh baka ce akwai daɗi va."

"Magani ne fah kuma bai kama ta ki sha ba."

"maganin me? ko ma na meye tunda kai kasha nima zan iya sha,oh yanzu gobe iwar haka muna can garin ƴan gayu."

Kallon ta kawai ya ke yi yadda ta ke jero zance wani kan wani,murmushi kawai yake yi,kuma taƙi dainawa zai yi ta ke yi.

Can ta gaji lokacin ta sanye lipton miƙa tayi da sauri yai ƙasa da kai dan baya son yaji wani abu.

Cikin muryar jin barci ta ce,"Ni barci na ke ji kar na makara gobe."

Tashi tayi ta hau akan gadon yana kallon ta,ta rufe da bargo,murmushi kawai yake yi yana jin wani irin baƙon yanayi yana kai wa zuciyar shi ziyara.

Bai tsaya wani tunani ba ya kwanta nan da nan barci yai awan gaba da shi.

>>>><<<<

Kamar dai kullum yau ma hakan ita ta fara tashi da jin kiran sallar farko na asuba,bata tsaya tashin shi ba ta fita ɗakinta,ta nufa na zuwa ta fara haɗa ƴan abubuwan da zata naima Dady ya ce gidan akwai kayan sakawa amma saboda tsoro zu ɗau abinda zasu bukata,haka ta haɗa abubuwan ta a cikin akwati duk abinda tasan zata buƙata,tana gamawa ta shiga bayi tai alwala,da ta fito saida tayi nafila sanan ta wuce ɗakin shi tashin shi tayi dan lokacin an kira sallah,yana tashi ya shiga yai wanka ya ɗauro alwala,ko kafin ya fito ta fara gyara ɗakin,yana fitowa ya tafi masallaci ,ita kuwa ta gyara ɗakin tsab.

Yana dawowa Dady ya iso dan shi zai kai su tashar jirgin,tara da hajia su ka zo dan ta ƙara yi musu sallama basu wani ɓata lokaci ba suka ɗau hanyar ,saura minti hudu jirgin ya tashi,hajia da Sabreen kuwa sun sha kuka.
🛫🛬Wai sai ƙasar turkey.

~~~~~~~~~~~~~

"Ke dan allah ki kwantar da hankalin ki wahalar da muka yi ba zata tafi a vanza ba,kawai dai yanzu kiyi ta kokari ki samu wayar shi yana jin muryar ki aiki zai fara,idan ya so zai ki bishi ƙasar ma."

Ita kuwa Haulat ɗin wacce ta zuba uban tagumi a gaban Momyn tana hawaye da wayar a hannun ta.

Dafa ta momy tayi,"Ki kwantar da hankalin ki idan sun sauka ki ƙara kira ,karki manta ba duk abinda kika faɗa shikenan to meye da damuwa."

"Kina ganin zai ɗau wayar kuwa."

"Dolen shi ba,ai ki fara shirin zuwa ƙasar turkey private zaki hau ya kai ki yau ɗinnan komai dare."

"Taya Momy."

"Wai yaushe kika zama banza ban sa ni ba,kuna yin waya ya turo miki kuɗi ki bishi."

"Je ki fara shiri ma,kuma idan jin je karki rama ma ƴar iskar matar ta shi,ku ƙuntata mata dan uban ta duk ita ce ta bamu matsala."

Wani irin farin ciki ya mamaye Haulat da rawar jiki ta tashi ta fara shiriii.

~~~~~~~~~~~~~

Ƙasar turkey kyakyyawar kasa ce mai abubuwan birgewa,yanayin tsarin garin da yadda al-adar mutanan garin ya ke shi yafi komai birgewa.

Tunda suka zauko Sabreen ta fara zare ido tana kallo riƙe shi tayi gamm kamar wani zai ƙwace shi.

Wata tsadaddiyar motor da wani ɗan afirka a cikin ta yazo tarbar su,cikin harshen turanci ya gaida su cikin girmamawa,suna shiga motor ta lafe a jikin shi.

"Lafiya ko garin bai miki ba ne?

gaɗa kai tayi alamar a'a,taɓa jikin ta yayi,dan ya lura yanayinta ya canza da zuwan su.

Cikin nuna kulawa ya ce,"Baki da lafiya ne?

"A'a lafiya lau,yaya karka barni plss."

Saida gaban shi yai mummunan faɗuwa,"Sabreen ba zan barki ba ki kwantar da hankalin ki ,amana ce a guri na,taya zan bar ki na je ina? kin san ban isa na ce gida babu ke ba,ke fa ƴar uwata ce ,zan kasance da ke har abada." cikin sigar lallashi ta tausasawa yayi magnar.

Ɗago da kanta tayi wanda ta kwantar da shi akan ka faɗar shi,ta kalle shi yaƙe tayi.

A zahirin gaskiya tunda suka zauko dga jirgin faɗuwar gaba ya kamata jikin ta ya mutu,wani irin yanayi mara daɗi ya shiga zuciyarta.

Sun daɗe zuna tafiya a motor bata ɗago ba balle ta kalla yanayin garin shi ma haka,wani irin abu mara daɗi ya ke ji a ranshi.

Wani hamshaƙin gida dan madaidaici direban ya nufa yana isa mai gadin wanda shi ma ɗan africa ne ya buɗe musu hamshaƙin get ɗin,karamin gida ne amm huɗuwar ta yi yawa,wanda idan kwatantawa zai ya ɗauke mu fiye da shafi biyar.

Yana tsayar da motorn ya fito da sauri ya buɗe musu,hannunwan ta ya riƙo su ka fito cikin su ba wanda ya tsaya kallon gidan sun bi bayan mutumin da ya kawo ne ,sun ɗanyi tafiya kafin suka isa cikin lafiyayyan falon suna isa ya tsaya,cikin harshen yar musu barka da zuwa ya juya.

Zaunar da ita yayi a kan kujerar da ke fallon kallon falon ya tsaya yi ,ya mishi kyau ainun,ita ma kallon falon tayi tai gutun murmushi ta ce,"Gidan yayi kyau sosai."

Kallon ta yayi ya sakar mata murmushi,"Nima yamin kyau,tashi mu je ɗaki muyi wanka muyi sallah sai mu fito mu kewa ya mu ƙara ganin gidan ko."

"Eh!

Hannunta ya riƙo suka nufi wata hanya wacce su ke tunanin ita zata sada su da ɗakin kwana,hakan kuwa ɗaku na ukku ne a jere,fuɗe wanda su ke kusa yayi suka shiga,ai nan suka yada ido dan haɗuwar ɗakin har yafi falon kyau gashi babba harda tavi da kujeru a ɗakin sai gadon ne ɗan ƙarami.

Basu wani tsaya ɓata lokaci ba,gurin ajiyar kaya ya nufa yana duvawa ya gane ɗakin ta ne,dan kayan mata ne.

"Ki shiga bayi kiyi wanka." ya faɗa haɗe da nuna mata bayin ,ba musu ta shiga,tana shiga ya fita ɗayan ɗakin ya shiga yana dubawa kowa yaga ɗakin shi ne,bayi ya shiga shi ba wani tsayawa kallon haɗuwar bayin yayi ba,dan ba yau ba ne farkon ganin gida irin shi ba.

ita kuwa ta zuba ƙauyanci kamar wacce ta fito a zaria ba abuja ba.

Da ta fito baya ɗakin sakin jikin ta tayi ta saka kaya duguwar riga cikin wacce ta tawo da ita,sallah ta fara yi.

Shi ma hakan sallah ya fara yi,tun yana sallah yake jin ringin ɗin wayar shi har ya idar ana kira,kafin ya idar anyi jira goma sha bakwai,yana idarwa ya nufi gurin wayar sabowar number

Please Login or Register in order to submit comment