Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan zai yabi umarnin ƙaranjuuu,kuna ɓata ma ƙaranjuuu lokaci ."

"Na shiga ukku yanzu wanan mummunan kazamin zai kwanta da ni."

Idanuwan ta har sun ciki taff da kwalla,har lokacin idon ta yana kan momy

Cikin raɗa momy ta ce mata,"Minti nawa ne ki ɗaure kawai kar ran ƙaranjuu ya ɓace ya fasa aikin kuma ya hukunta mu." tana gaba faɗa ta bar ɗakin kamar yadda ta shigo da baya-da baya.

Waiyo ni tirrrr da irin wanan ƙazamar rawuyar ya allah ka kare mu ka tsare imanin mu ba mu da wayau ba mu da dubara ya allah.

Ko da momy ta koma ɗakin ita ma haulat ta fito cike da ɓacin rai.

Ita ma momyn kwanciya yayi da ita sanan ya basu umarnin wuce wa...

.
[12/23, 2:17 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: _ 🇵σѕт 🇧у 🇬яσυρ 🇴 🇫 🇭уρє 🇭αυѕα 🇳σνєℓѕ 🇧σσк 🇼нαтѕαρρ 08064400100_ 📚📚
[12/23, 2:19 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: 🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹


*By*
*fatima* *Batula*

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
Page 15
..........................................

Addu'ar Saduwa Da Iyali:
بِسْمِ اللهِ اللّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا.
Bismil-lah, allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana.

Da sunan Allah. Ya Allah! Ka nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da shaidan daga abin da Ka azurta mu da shi.

__________________

Kallon Haulat Momy tayi sanan ta maida hankalin ta gurin tuƙi ta ce,"To baga shi ba mun wuce gurin minti nawa ne?yanzu wa yasan munyi ,ko shi bai sani ba tunda umarnin ƙanjuung ne,kuma yanzu zaki ga aiki cikin gaggawa."

Duk yadda Momy ta ke ba Haulat baki abin yaƙi dan jikin ta ya mutu,ranta bai so ba,ta so ta hakura amma tsoran abinda zai yi musu idan suka ƙi yarda yasa ta amce amma har ranta ta so hakura.

~~~~~~~~~~~~~
Kiran Sallar farko Sabreen ta miƙe,haɗe da addu'a a bakin ta,sanan ta dirgo daga kan gadon bayi ta shiga ta ɗauro al-wala sanan ta fito,har lokacin yana kwance yana sharar barci abin shi,kusa da shi ta matsa daff hannunta saka a kan shi tana shafa kwantacciyar zumar shi,a hankali kamar mai raɗa ta ce,"Miji na!ka tashi lokacin sallah."

Kamar daga sama yake jin muryarta cikin kunnan shi,a hankali ya fara buɗe ido,har ya ware su kan fuskarta idanuwan suka sauka,sun daɗe suna kallon s
juna,har wani lumshe ido yake yi,ta shi tayi zubur tabar inda ya ke.

"Ka tashi kar a tada sallah ka rasa jam'i."

Lumshe ido kawai yake yi,yana son macce mai riƙon addini tana ɗaya daga cikin ra'ayin shi.

Sallaya ta shimfiɗa ta tada iƙama raka'atanin fijjir zata yi,yana kallon ta birge shi ta ƙara yi,dan yasan ba'a tada sallah ba nafila ta ke yi,ganin ta fara yi yasa ya tashi ya shiga bayin,saida yayi kwankan tsarki kamar yadda ya saba yi ko wacce safiya.

Lokacin da ya fito da idar tana zaune akan sallayar yana kallon bakin ta yasan tasbihi ta ke yi ,bai ɗau lokaci gurin kallon ta ba,dan karya rasa sallah kamar yadda ta faɗa mishi,farar jallabiya ya saka ya ɗaura hula akan shi sanan ya fice.

Bayan sun idar da sallar saida ya zauna jin huɗuba,abinda bai taɓa yiba kenan tun dawowar shi daga india,ya rage abubuwa da yawa, a rayuwar shi wanda da ba hakan ya ke ba.

Tun yana falo ya fara jin sautin karatun al-qur'ani yana tashi,mamaki ya gama shi jin muryar sabreen,kasa yarda yayi har saida ya shiga ɗakin ya ganta tana karantawa,zama yayi yana sauraran yadda ta ke karantun cikin natsuwa kamar wata balarabiya.

"Kai daman yarinyar nan ta iya karatun haka mai daɗin gaske,to a ina ta koya?,a garin su,tun tana shekara tara dady ya gayamishi ta sauke al-qur'ani kuma tun a lokacin tana da hadda izufi goma,amma ban taɓa jin tana yi ba? to a gaban ka zata yi,yadda ta ke da rawar kai da ƙiriniya ba zaka ɗauka haka ta ke da ilimi ba."

Duk shi da zuciyar shi su ke wanan zancen ya tambayi kan shi sanan kuma yaba kanshi amsa.

Ya daɗe yana sauraran zazzaƙar muryarta,wanda bai san lokacin da barci ɓarayo ya ɗauke shi ba.

Saida ta haɗa izufi biyar sanan ta rufe al-qurnin ta yi addu'o'in naiman tsari kamar yadda addinin ya zo mana da su sanan ta tashi ,ganin yayi barci yasa ta fita a ɗakin ,ɗakin ta,ta wuce wanka tayi dogowar riga ita ce kayan da tafi so a rayuwarta,ta atamfa da saka orange colour da ɗan ratsin brown sai fari,kayan sun mata kyau ainun ɗauren gwaggwaro tayi ganin kicin zata shiga yasa ba tai komai a fuskarta.

Karin kumallo ta haɗa musu kunon gyaɗa sai soyayyan danganin turawa sai ferfesu hanta,sai ta soya indomi da kwai da sayayyan kwan sai lipton.

Bayan ta haɗa komai sanan ta koma ɗakinta,ta ƙara yin wani wankan dugowar riga ta ƙara saka wa,ƙirar dubai pink ne kalar rigari sai akai adon rigar da blue ɗin stone,rigar ba irin me kama jiki ba ce,amma duk da haka ta amshi jikin ta kuma kirarta ta baiya na,ɗan ƙaramin gyalen rigar ta yafa sanan ta feshe jikin ta da turaren da shi ne turaren da ta saba saka wa,light makeup tayi sai plat shoe kalar blue,tayi kyau ainun.

Safa da marwa yake yi a cikin bedroom ɗin shi ,"Me ya kamata nayi? Savreen zaɓin iyaye na ce,kuma bata da matsala ko kaɗan nabi umarnin mahaifana na zauna da mata ta,to amma ba ra'ayina bace,meye matslar hakan zan iya rayuwa da ita,inah da kamar wuya ita Haulat fa? ba da aure ta ke so na ba,na ƙyale ta kawai,a'a taya bayan ina son ta,ita ma tana so na,soyayyar ƙarya tunda ba auran ka ta ke son yi ba."

da ɗan ƙarfe yake maganar yana girgisa kai,"Taya? ba zan iya rayuwa da ita ba,to ya zanyi."

Marar shi tai wani irin murɗawa dafe ta yayi ,ya dawo ya zauna,"Ina bukatar macce,wata zuciyar ta ce mishi,"To ai kana da ita halal ɗin ka ce,ba zaka sha wahala gurin shawo kan ta ba."

"Zata raina ni."

Wata zuciyar ta ce mishi,"Wani raini mutuni na sai girman ka da zata ƙara gani,kayi tunani mai kyau."

"Assalamu alaika!

Bai tsaya tantance muryar ta ba ya amsa sallamar.

ƙarasowa ciki tayi saida ya lumshe ido dan wani irin asirtaccen ƙamshi da ya doki hancin shi,a hankali ya buɗe idannuwan shi ya sauke su akan ta,wani irin baƙon yanayi ya siyar shi zuciyar shi.

Ita kuwa ganin hakan yasa ta ƙara faɗaɗa fara'arta harda fari da fararan idanuwan tayi,ƙara takowa tayi daff da inda yake zaune ,ta duƙa cikin wata irin muryar ta ce," Ka tashi lafiya? ya gajiya?

Har lokacin bai ɗauke idanuwan shi a kan ta ba,wani irin abu zuciyar shi ke mishi.

jin yayi shiru yssa da ɗago kai wani murmushin ta ƙara sakar mishi,bai san lokacin daya maida mata martani ba.

"Tana gama kwarin kumallo ka sauko mu ci."

Ɗaga mata kai kawai yayi,ta tashi ta fara gyara ɗakin har lokacin yana nan ya kafe ta da ido,duk inda ta je binta da ido yake yi.

"Kayi wanka ne?

"A'a." ya faɗa a taƙai ce.

"Ba zaka yi yanzu ba ne."

"Zanyi."

"To ka tashi dan Dady ya kira ni wai muje yana naiman mu."

Tana rufe baki ya tashi,gyara gadon tayi sanan ta fita.

Bayan ya fito daga bayin yaji wani irin ƙamahi wanda duk lokacin daya ji shi yakan ji wani iri a ranshi.

Wanan shi ne sirran turare Naufal hatta so yana tsufa komai yana tsofa kuma yana gundura amma turare baya tsofa baya gundura kullum ka ji ƙamshin shi sabo ya ke zuwa kamar baka taba ji ba.

Kallon ɗakin yayi tsaf komai a kimtse yadda yake ganin sabreen da sakuwa bai taɓa tunanin zata iya aiki ba,yana son tsafta a rayuwar shi.

Tuno zasu je gida yasa ya saka shadda blue tasha aikin sama ,ta mishi kyau ainun da hula ita ma blue takalmi blue saida ya gyara fuskar shi sosai da kayan kwalliyar maza san ya feshe jikin shi da turarruka ma su ƙamahin gaske,zai yanzu ya tuno da wayar shi naiman ta yayi bai gane,bai damu ba dan yasan sabreen zata san inda ta ke tunda ita ke gyara ɗakin.

ƙasa ya sauko tun daga kan matattakalar ya hango ta,har ya iso cikin falon idan shi yana kan ta.

Jin ƙamshin turaran shi yasa ta waigo haɗa ido suka yi ,ta sakar mishi wani amintaccen murmushi shi ma sakar mata yayi.

"yawwa muyi sauri kar ya gaji da jiran mu."

Bai ce mata komai ba,gurin abincin ya wuce ya ja kujera ya zauna,ita ta zuba mishi gunun gyaɗa ta zuba mishi har saida ta kusa shika cup ɗin dan tasan yana son gunun gyaɗa sosai.

"Sabreen!

Saida ta ɗago ta kalle shi sanan ta ce,"Na'am miji na!

"Kin dafa lipton?

"Eh gashi nan shi zaka sha?

"Eh plss ki matsamin lemon tsami a ciki."

"Baka da matsala."

Kicin ɗin ta koma ta matsu ruwan sanan ta dawo,ta haɗa mishi da lipton ɗin.

"gashi sai me zaka ci?

Dan galin turawa da kwai su kama kaɗan ya iya ci.

"Sabreen ina waya ta?

"Wayarka tana ɗaki."

"Ki ɗauko min ban ganta ba."

Tashi kawai tayi ta dufi ɗakin nashi inda ta ajiye nan ta ɗauko,kunna wayar ta,pic ɗin shi ne wanda ya ɗauka a india a gaban wayar saida ta kalli pic ɗin sosai sannan ta taɓe vaki,"Ko kyau ina farin namji ya ga kyau kamar wani macce,dariya tayi ta ƙara cewa,"Uban yan iyayi zaka ga aikin Sabreen lokacin da ka ji ka manta wata haulat a rayuwar ka."

Number Haulat ɗin ta shiga naima,"My dear", ta ga an rubutu blocking ɗin number tayi.

Tai murmushin mugun ta sanan ta ce,"Hm malama ta nasan ke wacece,amma ke baki san ko ni wacce ba,ba taƙamar yana son ki ba idan ya manta da ke zanga tsiyar da zaki iya yi."

A falon ta same shi,miƙa mishi wayar tayi,"Gashi!.

Amsa kawai yayi,"Muje ko."

"Eh.

Kamar wasu masoyan gaskiya haka suka jeru sun yi kyau gashi kayan su iri ɗaya.

~~~~~~~~~~~~~

Tun a hanya Haulat ke kiran number shi wayar a kashe kamar tayi kuka.

"Momy tun jiya wayar shi a kashe ya zanyi momy?

"Ki kwantar da hankalin ki,ai na daɗe ina gaya miki kaidin mata da yawa,halan ma duk ita ce,amma yanzu za'ayi maganin ta dan uban ta shege idan ta fara bin bola sai mu ka tsiyar abun."

Duk yadda Momy ke kokarin kwantar mata da hankali ta ƙasa,dan hankalin ta ya kasa natsuwa duk wani iri ta ke ji a ranta,wanda bata san ko meye ba.

~~~~~~~~~~~~~

Cikin ƙanƙanin lokaci suka isa gidan su Dady,cikin natsuwa da sallama a bakin su ,su ka isa cikin falon.

Suna isa dady ya taso da kan shi ya tarbo Sabreen riƙo hannun ta yayi su ka dawo inda ya ke zaune kan cinyar shi ya zaunar da ita,ba yau ba ne ranar farko da dady ya taɓa zaunar da ita kan cinyar shi ba,amma ba ta taɓa jin kunya irin na yau ba,kasa gaida shi tayi dan kunya.

"Sabreen ya kike? ina fatan komai lafiya,idan yana miki wani abu da baki so ki gaya min karki ji komai,kinji Sabreen."

Saida ta ɗago kai ta kalle shi,shi ma kallon ta yayi yana son jin amsar da zata gayawa dady.

Ƙasa tayi da kan ta,"Ba komai dady."

"Kin tabbatar."

"Eh!

Ajiyar zuciya ya sauke sanan ya ce,"Masha allah komai daɗi,haka ne ke,kallon Naufal dady yayi,ƙasa naufal ɗin yayi da kai yana shirin gaida shi ya tari hanzarin shi.

"Naufal ka haifu,Lallai ka nuna min kai ɗa ne,na gari mai tarbiyar,naji daɗi Naufal na gode ma ka,da ka riƙe min Sabreen da kyau allah ya biya ka na god...

"Dadyn dan allah ka daina godiya,ni ya kamata nayi godiyae."

Farinciki da jin daɗi ya ƙara mamaye dady,ƙarara fuskar shi ta nuna irin farincikin da yake ciki.

Duk wanan abun da ake yi Momy da Farrah suna zaune a ɗakin.

"Nima zan ma godiya Naufal ka cika min burina,Jibe insha allahu za ku tafi honeymoon kasar turkey..

.
[12/23, 2:19 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: _ 🇵σѕт 🇧у 🇬яσυρ 🇴 🇫 🇭уρє 🇭αυѕα 🇳σνєℓѕ 🇧σσк 🇼нαтѕαρρ 08064400100_ 📚📚
[12/23, 2:22 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: 🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹


*By*
*fatima* *Batula*

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

Page 16
_________________________

*_السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته_*
_*بسم الله الرحمن الرحيم*_

_*Sayyiduna Aliyu yace; Manzon Allaah(ﷺ)* *yace min; KA RI'KA (ADDU'A KA NA) CEWA; {YA ALLAAH KA SHIRYENI, KUMA KA DAIDAITA NI (A KAN HALAYEN 'KWARAI.}*_
°

```[Sahihu Muslim;2725]```
~~
_Muma sai mu dage da yin wannan addu'ar neman shirya da kuma hali na kwarai. Allaahu a'alam._

```Allah ta'ala yasa mudace```

_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_

........................................................................

Gaba ɗaya jikin Naufal yayi sanyi tunanin halin da zuciyar shi ta ke ciki yake yi.

Ganin yayi shiru yasa Dady ya ce mishi, "Naufal ko ƙasar ce ba ka son zuwa?

Murmushi yayi sanan ya ce,"A'a ina so sai dai ban san ko Sabreen ba."

Kallon Sabreen Dady yayi wacce har yanzu tana kan cinyar shi,cikin murmuahi mai ɗauke da farincike dady ya ce,"Sabreen ba ki son zuwa ƙasar ne?

"Ina so."

Ai nasan ba zaki ƙi ba my Sabreen."

Haba Alhaji ka barsu mu gaisa mana,tun zuwan ta ka janyo ta jikin ka,ka hana ta zuwa guri na,Sabreen ta so kin ji."

Dariya dadyn yayi ya ce,"ba gwara ke ba kuna haɗuwa ni fa tun bikin sai yau ba abin ki ce ta zauna a guri na ba ne."

"Ah...Momyn zata yi magana ya katse ta.

"Sabreen ta shi ki je gurin momy ko."

A kunyace ta miƙe ta isa inda momyn ta ke,jikin jin kunya ta gaida ita.

Bayan zun gaisa ta koma inda farrah ta,cikin raɗa ta ce mata,"Oh su Aunty Sabreen manya,to ki tabbatar kin dawo min da baby a cikin ki." Cikin dariya da zolaya tayi maganar.

Muntsinin ta Sabreen tayi har saida tayi yar ƙara sanan ta gyale ta,taja bikin ta tai shiru kamar ruwa ya ci ta.

Dady ya ce,"Sai kun dawo ne za'a yi maganar makarantar Sabreen ko kuwa,"ya faɗa yana kallon Naufal.

"Eh a bari mu dawo kamar zai fi,amma yadda ka gani dai."

Sai da Dady ya ɗan murmusa sanan ya ce,"Naufal kai fa mijin ta ne,ka fi ni iko a kan ta yadda ka ce ɗin hakan za'a yi."

Fira sosai suka yi harda Naufal ɗin dan tunda su ka zo basu fita ko ina ba har Dady ,sai lokacin sallah su fita su dawo har la'asar sanan suka fito,sai sun biya gurin hajia kafin su wuce.

Kafin su tafi saida Momy ta bata magangunan mata kala-kala tun daga zamfara da sokoto ta saka aka siyo mata,ta kuma ce mata kar ta yi amfani da su sai sun je honeymoon sanan ta sha.

~~~~~~~~~~~~~

"Kin san meye honeymoon kuwa? bai kalle ta ba yayi maganar.

Saida ta kalle shi sanan ta ce,"Eh ba shi ne mata da miji ke zuwa wata ƙasa ba,cin amarci."

"Shi fa zamu je."wanan ƙaran ya kalle ta.

"Eh ko baka so ne,ni fa matarka ce ta sunna."

Ta taɓo mishi idan yake mishi kaikayi,zuciyar shi ta fara dan bugawa zuciyar shi ta mishi ce,"Tsoran me kake ji Naufal wanan ne gaskiyar lamari ita matar ka ce ta sunnah."

Da sauri ta riƙe hannuwan shi,ta ce a ɗan ruɗe,"Yaya ka manta ne zaka wuce gidan hajia ko ba ka so na je ne?

Taka birkin motor yayi da sauri,kallon ta yayi ido cikin ido sanan ya ce,"Yanzu idan na ce bana so ki je ba zaki je ba?

"Eh Momy da hajia duk sun gaya min duk abinda miji na ya ce baya so kar nayi kuma idan ya hanani yin abu kar nayi,idan ka ce baka son zuwa ba zan je ba."

Lumshe ido yake yi yana kallon lips ɗin ta yadda ta ke maganar,idanuwan shi har sun canza kala bugun zuciyar shi ya ƙaro,cikin izza da zafin nama ya janyo ta jikin shi ya haɗa bakin shi da tana ya fara kissing ɗin ta,abin mamaki yau bata yi koƙin ƙwatar kan ta ba,cikk ta tsaya yana juya harshen shi cikin bakin ta,shi kuma jin ta natsu ya saka ya ƙara zaƙewa,lalubarta ya fara yi ,jin ya fara taɓa jikin ta yasa ta ja jikin ta da sauri tana sauke ajiyar zuciya.

shi kuwa gogan kife kan shi yayi akan sitiyarin motor yana sauke nannauyar ajiyar zuciya,zuciyar shi kamar ta fasa ƙirjin shi ta fito dan bugawan da ta ke yi.

Bata ce mishi komai ba,har tsawon lokaci ba wanda ya iya yin magana a cikin su.

Ganin bashi da niyar magana gashi yamma na yi,ya saka ta mishi magana,"Yamma tana yi mu tafi."

Bai yi tsammanin jin wanan maganar daga bakin ta ba,yayi tunanin ɗan iska zata ce mishi,ɗagowa yayi yana so su haɗa ido taƙi bari.

"Sabreen! da ƙyar maganar ta fito dan ma ta saba da jin maganar shi da ,da ne ba zata ji abinda ya faɗa ba.

Kan ta a ƙasa ta ce,"Na'am."

Har lokacin idon shi yana kan fuskarta,yana son fahimtar yanayin ta,ganin yana ƙara shiga wani hali dan kallon ta yasa ya ja motor da gudu baya ya juya ,ya kai ta gidan hajiyar.

Sun isa harabar gidan yayi farkin ,yana yin farkin ɗin ta fito da gudu tai cikin gidan.

Kallon yadda tayi gudun yayi,yasan irin yadda ta ke son hajia a fili ya ce,"Ke nan Savreen zata iya zama da ni a matsayin mijin ta,hakan yana nufin ta aminta da ni,an ya kuwa ,koma me nene zan gano."

Shi kaɗai ya ɗinga saƙa yana warwara.

Ita kuwa tana isa falon ta dunga kwala ma hajia kira.

"Hajia ta! Hajiata!

Hajiyar tana ɗakin ta da sauri ta fiton falon jin muryar Sabreen Rungume juna suka yi suna ihun jin daɗin ganin juna.

Saida suka gaji da tsayuwar sanan suka zauna sanan suka gaisa cikin farin ciki da jin daɗi.

Bayan sun gama gaisawa d daɗewa sanan ya shigo da sallama a bakin shi.

Hajia tana amsawa ta ce tun kafin yakai ga zama,"Da ba zaka shigo ba ne,ko baka so ta zo ba ne."

Saida ya zauna sanan ya kalle ta yana murmushi ya,"Na isa na hana ta zuwa gurin bugun zuciyarta muradin ranta."

Dariya suka yi su dukkan su kuwannan su yana cikin yanayin jin daɗi,bayan sun gaisa da shi suka fara fira.

Kallon Naufal hajia tayi fuska ɗauke da annuri ta ce,"Naufal na gode,na gode lallai ka haifu,duk da Sabreen jikin ka ce dole akwai so a tsanin ku amma dole mu jin ji na ma dan abinda kayi ba ko wanne ɗa ba."

"Haba hajia ni kashe min jiki kuke idan kuna min godiyar ne."

Amma can ƙarƙashin zuciyar shi tunanin abinda ta ce yake yi,"Akwai so a tsananin ku" yana son ya gane wani irin so ne wanan.

Kallon ta yake yi yana son su haɗa ido amma taƙi yarda da hakan ta faru.

A zuciyarta ta ce,"Ba wani so wanan ne zai so ni, tabb kin saɓa number hajia."

Suna gidan aka kira sallar maqrib ya fita yayi su ma,su ka tashi zuka yi,bayan ya dawo saida suka ci abinci sanan suka tafi.

Saida hajia ta bata garin magarya da sabon magarya sanan suka tafi.

Har suka isa gida ba wanda yai ma wani magana,ɗakin shi ya tafi ita ma ɗakinta ta wuce dan ta chanza kaya.

Dan samon tayi wanka ta saka riga dugowa mara nauyi ba kwalliya a jikin rigar sai da ta fashe jikin ta da tararen da ta saba amfani na shi sanan ta fara gyara ɗakin ta duk da kafin su tafi ta gyara.

Yana isa ɗakin shi ya faɗa kan gadon kan shi na kallon saman ɗakin,sauraran bugun zuciyar shi ya tsaya yi,ya daɗe a haka sanan ya tashi yai toilet.

~~~~~~~~~~~~~

Kuka sosai haulat ke yi,"kin gani momy har yanzu ba wani labari tun muna kan hanya kika sa a fara saka ido amma ba wani labari sai ganin su ma da aka ce anyi suna jin daɗi har da kiss fah aka ce ya mata."

Dafa ta momy tayi,"Ki kwantar da hankalin ki,na gaya miki aikin shi a ranar ya ke yi,kuma yanzu baki ga gobe tayi ba ance bata hauka ce ba,yau komai dare sai aikin mu yayi ki kwantar da hankalin ki."

"Hankali na ba zai iya kwanciya ba momy."

"Na gaya miki ki kwantar da hankalin ki idan wani abu bai faru ba sai mu koma goven."

Duk wanan abun da suke yi sakina tana jin ,idanuwan ta sunji ja kwalla dam a idon ta.

Cikin raguwar murya ta ce,"Momy ba kyau kuyi tsoran allah,dan.....

"keeeeee dan uban ki ,ki ɓace daga nan kafin na buɗe ido na."

Gaba ɗaya jikin sakina rawa ya fara yi,da ƙyar ta iya jan ƙafar ta,ta bar gurin.

Ita kuwa momy taita vamvami kamar karamar mahaukaciya sai kwace ma sakina albarka ta ke yi.

~~~~~~~~~~~~~

Da sallama ya shiga ɗakin yana tashin ƙamshi,ganin kamar hankalin shi baya jikin shi yasa,ta lallaɓa ta vayan shi ta rufe mishi ido da hannuwan ta.

Mai da idanuwan yayi ya rufe su,dan yasan ita ce,a hankali zuciyar shi ta fara bugawa hannayen shi ya ɗauka kan na ta,sai da yaji wani irin jin lallasar fatar mai.

Cikin wata irin siga wacce shi kan shi ba zai iya bambance yanayin ba ya ce,Sabreen!

"Maimaita."

"Sabreen!

"Waw na baka kyautar Abuja harda kaduna ba,kasan me? ta sake shi ta dawo inda ya ke zaune taff da shi ta zauna,har suna gogan jikin juna.

Kallon ta yayi ya sake mata wani irin kyakyyawan murmushi sanan ya ce," taya zan sani."

"Ka bala'in iya kiran sunan da indiyanci kike kira gaji daɗi ku....

Dariya ta fashe da ita sosai ya dara ita kuwa bin shi da kallo kawai ta ke yi dan bata ji abin dariyar da ta faɗa ba.

Saida yayi me isar shi sanan ya tsaya bai ɗaure fuska ba ce kalle ta ya ce,"Wai da indiyanci,kai sabreen kina da abin dariya."

"Toh ai gaskiya na faɗa wa gaji yana kira na irin yadda kake kira na?

"Hajia da Dady."

"A'a su da hausa su ke kira."

Murmushi yayi mai ɗauke da annuri,"Hm kina da abin dariya,na tambaye ki."

"Uhum!

"Wai lokacin nan da na zo gurin hajia a lokacin ban daɗe da dawo wa ba,har na same ki a falo kina kallo kika banza da,naga kina da dariya a lokacin me ya sa ki dariyar?

Yana kai ayaa ta fashe da dariya,kallon ta ya ke yi tana dariya kamar irin wancen lokacin,taya da yayi.

Saida suka yi me isar su sanan su ka tsaya,suna kallon juna,wani irin abu ke ta so mishi a rai.

Cikin yanayin jin barci ta ce,"Barci na ke,bari na kwanta."

Bata jira cewar shi ba ta,tashi saida ta shiga bayi nayi al-awla sanan da tayi nafila tayi addu'o'i iri iri sannan kwanta,duk yana kallon ta,tana kuma ƙara birge shi,addu'o'in da yaji tana yi yayi magana dan wasu mai iya ba,wasu ya manta su.

"Na hakura nayi rayuwata da ita,bata da matsala ko kuma hakan zai saka iyaye na su ji daɗi sosai."

Nannauyan numfashi yayi sanan ya ƙara faɗin,"kai abin is not easy taya? to daman ai matsalar tawa ce," dafa kan shi yayi wanda ya ɗau zafi,wata zuciyar tana tausar shi akan ta zaduda kawai wata kuma na bijiro mishi da abubuwa marasa amfani.

Safa da marwa ya kw yi a tsakiyar ɗakin yana kuma kallon ta ,ta duƙunƙune guri daya tana varcin.

Tausayin kanshi ya kama shi tabbas yana da buƙatar macce,kuma yasan idan har mai samu yadda yake so ba,har wani ɗan lokaci zai iya samun matsala.

Kamar wanda aka ba umarnin ya zauna can kuma ya tashi tsaye,hura hanci ya fara, a fili ya ce,"Ba zan iya cutar da kai ba,bayan allah ya ƙubutar da ni."

Murmushi yayi me ƙyayatarwa har da lumshe ido da hura hanci,"Ban san ta yadda zaki ji al'amarin ba amma dole zanyi Sabreen, ba yadda..

.
[12/23, 2:22 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: _ 🇵σѕт 🇧у 🇬яσυρ 🇴 🇫 🇭уρє 🇭αυѕα 🇳σνєℓѕ 🇧σσк 🇼нαтѕαρρ 08064400100_ 📚📚
[12/23, 2:24 PM] 🅰° 🅰 D°🅱⭕Y🔛🔝: 🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹


*By*
*fatima* *Batula*

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

Page 17
......................................................

Kwanciya yayi ɗan nesa da ita kaɗan,ya daɗe yana saƙa da warwara, yana jin tana barcin ta hankali kwance,shi kuwa sai juye yake yi sai ƙarfe ɗaya saura sanan barci ya ɗauke shi.

Kamar dai kullum kiran sallar farko ke tada ita yau ma hakan ne,tana tashi da kunna hasken ɗakin kallon inda yake tayi saida tayi murmushi ganin yadda yake barcin hannayen shi gaba

Please Login or Register in order to submit comment