Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

juyo suna kallonsu, hakan ba karamin dadi ya musu ba barinma yanda suka dace sosai tun kafin su karaso fawwaz yafara musu hoto tare da videos batare da sun sani ba, mutsu_mutsu tafarayi da hannunta tana son kwacewa sake rike hannun yayi kam yaki sakewa kunya ne ya cikata kamar ta nitse akasa haka takeji su abba,ummi , fawwaz,areef duk suna falon banda zeenat da zata kwana a gidan anty amina. Dukkansu murmushi ne dauke akan fuskokinsu yanda fanan ke kokarin kwace hannunta gashi Mr azaad yake sakin hannun abin yaso basu dariya sesuka danne, sallama suka musu suka fita tasowa securities sukayi dan rakashi hannu yadaga musu kawai packing space yaje yafito da motar kirar BMW baka, shiga tayi me gadi yabude musu gate harsuka iso babu wanda yayiwa dan uwansa magana. Yana yin packing akofar gidan tafito da gudu tundaga bakin gate take kwala kiran " mama!mama!mama" duk suna zaune afalo suna hira kamar daga sama sukaji muryanta ya karade gidan tagumi baba yayi Yana kallon mama yace " ohhh mamansu nikam yaushe fanan zata girmane" duka dariya sukasa fitowa ya Usman,ya al ameen sukayi , ya Usman ne yafara fitowa aikuwa tana ganinshi taje da gudu ta rungumeshi tana dariya, dariyar shima yakeyi na farin cikin ganin yar kanwar tashi.
Mr azaad na tsaye abakin gate yashigo yana harde da hannunshi akirji yazuba musu ido fuskan nan ahade kamar wanda akawa mutuwa hada ido sukayi da ya usman dake rungume da fanan ganin yanayin Mr azaad abin yabashi dariya domin babu abinda yake hangowa a kwayar idon Mr azaad daya wuce wutan kishi , kamar ancewa fanan ta kalli bakin gate aikuwa karaff suka hada ido dashi mugun kallo kawai yake watsa mata ba shiri ta raba jikinta dana ya usman, kwafa yayi yawucesu yashiga falon suka gaisa da mama da baba cikin girmamawa sosai suke alfaharin kasancewar Mr azaad a sirkinsu da suna tunanin wani rayuwa yarsu zatayi tare dashi saboda ko fuskanshi kadai mutum ya kalla yasan mutum ne me tsatsauran raayi da rashin magana amma bayan aurensu da kwana biyu yazo gidan kusan duk bayan kwana biyu se yazo gidan gaishesu amma betaba fadawa fanan yaje gidansu ba.
Rungume auta tayi sosai , haka ya al ameen ma sosai yayi murna da ganinta yana tsokananta " yar kanwa wato seyau kikayi niyar zuwa ko ?" " Ah ah fah ya al ameen" dariya kawai yayi, sake auta tayi ta cigaba da kwalawa mama kira harta shiga falon fadawa jikin mama tayi ta rungumeta sosai tana fadin " mama na nayi missing dinki sosai" " kai!kai fanan kede bazaki taba girma ba mutum kullum ace baya girma dagani karki karya ni" shagwabe fuska tayi ta daga maman tana " yanzu mama bakiyi kewata ba " ganin yanzu seta farawa mutane kuka yasa mama tace " ah nikuwa nayi kewarki shagwababbiyata" dariya tayi ta sake rungumeta yau wani irin annashuwa take cikj na ganin iyayenta, haka taje gun baba tagama mishi shagwaba dariya kawai yaitayi yana kallonta yana jin wani irin daci aranshi babu yanda suka iya dolene seta tafi inde bata tafi ba sede wani ikon Allah shafa kanta yayi yace" Allah yamiki albarka ya kare mana ke da karewarsa " duka suka amsa da abin. haka suketa hiransu dukda Mr azaad ba wani gwanin magana bane amma yau yadan sake wani yabada amsa wani kuma yayi shuru tashi tayi tashige dakinta dan tasan suhaima na ciki tana wayar jaraba kilama batasan tazo ba , aikuwa kamar yanda tayi hasashe tana ciki tashige bargo ta kashe murya tana waya da masoyinta , tsalle tayi tadira akanta afirgice suhaima tamike ganin fanan yasa tasa ihu suka rungume juna. cire wayar fawwaz yayi daga kunnenshi dan yaji muryan fanan murmushi yayi kasa_kasa yace " kai matar babban yaya da baby se adduah" lura da yayi suhaima tamanta da suna waya sun baje da hira yasa yakatse kiran.
Shuru_shuru fanan bata fito ba se zuba ido yakeyi yana jiran tafito duk cikin abubuwan tabawa da mama ta kawo mishi drinks da fruit kawai yataba, suma yar hira sukeyi sama_sama da ya usman da ya al ameen kirane yashigo wayar ya usman ya mike yayi waje , picking yayi yanata hello hello bayajin me maganar network ya hana bude gate yayi yafita waje .

Magana yakeyi da yaron shagonshi idonshi ne ya sauka akan khairatyyy dake tsaye ta bashi baya iska se kada kayan jikinta yakeyi da dogon gashinta dayake sharan kasa, yanayin de abin tsoro in bil adama yagani amma ya usman de kara burgeshi tayi babu wani fargaba ko tsoro ya nufeta yatsaya abayanta tun fitowarshi a gida take sane dashi awajen amma batayi tsammanin har yanada karfin guiwan tunkaranta ba domin duk wani bil adama dayayi gamo da ita mugun firgita yakeyi amma shi meya taka haka , batare da ta juyo da gangan jikinta ba tajuyo da kanta kadai fuskanta ba alamun dariya ko wasa idon nan manya_manya dasu tace " meya kawo ka nan kazo ka tsareni da ido babu ko tsoro a tattare dakai " dariya ya usman yayi ganin tadage ita adole seta tsoratar dashi bata san son dayake mata ya kore duk wani tsoro da firgici ba , ganin yaki ce mata komai yakafeta da ido yana murmushi ne yasa ta murguda mishi baki tace " kabari banaso kadena kallona kokuma in hukuntaka" shi komai tayi kyau take mishi dakara burgeshi " kin taba kallon wanda yaji tsoron abinda yakeso ?" yamata tambayar yana kallon cikin manyan idonta dasuka zarce na bil adama, kara zaro su waje tayi tajuya ta kalli gaba daya arean dan tabbatar da babu wani jinni kana nan yaran aljanune kawai suke wajan suna wasa , kasa kasa tayi da murya tace " baka da hankali ne? kokayi hauka ne? kode bakasan nidin wacece bace kakemin irin wannan banzan maganar to koda wasa kar kasake insake jin irin wannan maganar abakinka in bahaka kuwa ze iya yuwa inyi ajalinka " tunda tafara magana yake kallonta sake matsowa daff da ita yayi yace" to aini hakan zezamo abin alfahari agareni ace wacce nakeso ce ta kasheni! balle ma nasan ke ba muguwa me cutarwa bace khairatyyy kiji tausayina kisoni kamar yanda nake sanki dan Allah " yafada yana hade hannunshi duka biyu yana rokonta , dafe kai khairaty tayi yau taga takanta duk iya yanda zatayi ta fahimtar da ya usman kancewa babu maganar soyayya tsakaninsu saboda sudin ba jinsi daya bane amma yaki fahimtarta .
Sosai yabata tausayi tabbas ta yarda da irin son da yake mata amma dolene tunkafin yayi nisar da bazeji kira ba ta dakatar dashi , godiyarta daya tasan duk abinda suka tattauna sarauniya taji.
_____ zuruf fanan dake hira da suhaima tamike domin duk maganganun da ya usman da khairaty suka tattauna akan kunnenta tana jinsu fitowa tayi daga dakin ganin haka yasa suhaima tabi bayanta ,suna zaune afalo sukaga tafito da mugun sauri kamar zata tashi sama hannu daya Mr azaad yasa yariko ta dan sun lura ba lafiya ba irin yanda tafiton nan duk tunanin su wani abunne yake faruwa, Mr azaad ne yafara magana " lafiya fanannnn ina zakije kike wannan saurin haka?" Ajiyar zuciya tasauke seyanzu ta lura a irin yanayin da tafito ko dankwali babu akanta gashi sun fara tunanin wani abu rike hannunshi tayi suka zauna akan kujera batare da tace musu komai ba ta daga kai ta kalli sama tace " khairat kizo keda ya usman yanzun nan " gaba daya lamarin yadaure mata kai taya akayi har ya usman yafada soyayya da jinsin daba tashi ba, ana haka yayi sallama yashigo yazauna kallonshi kawai fanan takeyi tama rasa mezata ce mishi " kallon bakin kofa tayi tace" kishigo kema " bayyana khairaty tayi taxube akan guiwowinta tagaida sarauniya,umarni fanan tabata data zauna itama, zama khairaty tayi tana satan kallon sarauniya sude da basu san meke faruwa ba sun kasa kunne da sunji abinda fanan zata fada.
Gyara murya tayi kafin tace " khairat meye hadinki da ya usman danaji zancen soyayya natashi " dafe kirji mama tayi tace " so me? Kamar de kunne na ne beji dede bako?" alama baba yamata da tayi shuru su gama jin me fanan zata fada sukansu abinda yabasu mamaki amma banda ya al ameen daya san dama zaa rina.
______ kanta na kallon kasa tace" yake sarauniya bantaba sanin da wannan labarin ba se dazun yake sanar dani babu irin fahimtar dashi da banyi ba amma yakasa fahimtar babu wani soyayya atsakanin mu saboda mun kasance jinsi daban daban" sun gamsu da maganar khairatyyy . maida kallonta fanan tayi kan ya usman da har time din idonshi na akan habibiyarshi khairaty " ya usman kabar wannan maganar saboda babu aure tsakaninka da khairaty kai bil adama ne itakuma jinnu ce hakan baze taba yiwuwa ba " hararanta yayi yace" fanan wallahi inasonta ni ahakan na amince zan aureta " daka mishi tsawa baba yayi kafin yadaura da " usman ina maka kallon me hankali ashe babu taya zaka fara tunanin fara son abinda kasan bazaka taba samuba ko so kake ka lalata rayuwarka yar uwarka tafada maka illan hakan amma kai har kana wani cewa zaka aureta ahaka " " nooooo bazeyuba ba Ina san khairaty babu abinda ze rabani da ita se mutuwa! wallahi ba ni na daurawa kaina son taba Allah ne yadaura min bazan iya rayuwa ba in babu ita aciki dan Allah kutaimakamin ku auramin ita " ............




Tofa ana wata ga wata.😨😨


Masu comment Allah yabar kauna ina godiya sosai Allah yamuku albarka.


Semun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy πŸ‘πŸ™.



via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8
πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺




Story & written by ✍️
MRS 🌹 ISHAM 🌹



πŸ””πŸ“š JARUMAI WRITERS ASSOCIATION πŸ“š





Page 4️⃣5️⃣






Abinda be taba faruwa ba a tarihin agidan yau shine yafaru , ko da wasa basa yiwa iyayensu musu akan duk abinda zasu zartar amma yau ya usman ne da kanshi baba yayi magana yana cewa bazeyuba tabbas yayi nisan da bazeji kira ba soyayya yariga da yarufe mishi ido,yanzu duk abinda zasu fada baze taba sauraran su ba , babban abinda fanan take tsoro kenan dan tasan so mugun abune in mutum ya fada tarkon so tofa komin munin abu baze taba gani ba gaba daya tausayinshi ne yakamasu dan sun san ya daukowa kanshi dala ba gammo ne hakan baze taba faruwa ba bil adama da jinni. Mama kam tsaban takaicin daya cikata ma ka sa magana tayi da wanne zataji, da tafiyar fanan zataji ko kuma da abinda ya usman ya jajibo musu .
Cikin kwantar da murya baba yace " usman yanzu zaka fara bijire min kenan saboda so ya rufe maka ido ? Kasan bazan taba hanaka duk wani abu ba sede inde yakauce hanya hakan kuma bazan taba lamunta ba daga yau kama fara tunanin cireta aranka dan ba samunta zakayi ba nagama magana " ya usman dafe setin zuciyarshi yayi da yakeji kamar ana watsa mishi wuta dan bala'in zafin da yake mishi murya na rawa yace " baba bana fatan ranar da zezo inzama mara biyayya ga iyayena! Amma zanso kuji abinda nakeji wallahi baba in ban samu khairat ba mutuwa zanyi, ku taimakeni kumin wannan alfarman" ya matukar bawa Mr azaad tausayi bama shi kadai ba duk wani wanda yake falon seda ya kashe musu jiki mikewa Mr azaad yayi yarike hannun ya usman suka fita waje.
Sallamar khairatyyy fanan tayi nan take ta bace azuciyar fanan kuwa tana tunanin abinda yakamata tayi dan ceto dan uwanta. Auta kam duk abinda akeyi se binsu da ido takeyi kasancewar takan fahimmci wata maganar wata kuma bata fahimta saboda kananun shekarunta ,ta riga da tagane duk wannan maganar akan khairaty ce da ya usman inde ta ita zaabi khairaty tayi mata kyau sosai, ( kuji auta fah ahhh lallai yaro yarone) fanan da ya al ameen ne suka kwantar wa su mama hankali akan zasuyi iya kokarinsu domin ganin ya usman yacire khairaty a ranshi, kirane yashigo wayar suhaima ganin sunan "my hubby" yabayyana akan screen din ne yasa tabar falon tashige daki.

Haka a bangaren Mr azaad duk da yakasance mara son magana haka yabawa ya usman shawara sosai har yasamu yadawo normal suka dawo falo ko zama ya usman beyi ba ya shiga dakin shi , zama Mr azaad yayi yana shafa lallausan sumar kanshi kafin yace " baba kuyi hakuri ku mishi uzuri yariga da yayi nisa na lura usman yana matukar sonta , dole muyi kokarinmu domin ganin ya cireta aranshi " sake baki da hanci fanan tayi tana kare mai kallo jin maganganunshi tunani tafara yaushe Mr azaad yafara damuwa da damuwar mutane amma hakan yamata dadi ganin ya damu da damuwar ahalinta sonshi ne takaraji yashiga cikin zuciyarta, duk maganar nan da Mr azaad yakeyi auta na kwance ajikinshi tayi lamo kamar wata me bacci can kuma ta mike zaune ta kalli Mr azaad tace " Yaya balarabe kasanme ? " Kallon fuskanta yayi me kama da na fanan se an nutsu sosai zaa gane kamar tasu saboda skin color dinsu ba daya bane auta farace sol kamar tsada fanan kuma chocolate color ce ,ita kadaice me color skin din agidan , girgiza kai yayi tare da cewa " cutie bansaniba sekin fada " cigaba tayi da " nikam budurwan ya usman tamin kyau sosai especially her eyes that are so big like ball tayi kyau sosai kaima tamaka kyau ko?" Basu taba tsammanin abinda auta zata fada ba kenan amma se sukayi laakari da wayon datake dashi domin basuyi tsammanin harzata fahimci akan abinda ake magana ba kenan , shisa bakowani magana akeso adinga yi agaban yara ba saboda yaran yanzu sun wuce duk yanda kuke tunani , satan kallon fanan yayi yaga se aikin gallawa auta harara takeyi jin tana tambayarsa shima tamasa kyau, murmushi yayi dan yasan akan abinda yasa take hararan auta , lakatar hancin auta yayi yace " karki kara magana akan abinda manya suke tattaunawa bakyau this is improper" gyada Kai tayi takoma jikinshi ta kwanta .
Sun dan taba hira kafin Mr azaad yakalli agogon diamond dake daure a hannunshi sannan yace " baba mu zamu wuce dare yayi seda safe " sallama sukayi ya fita shida ya al ameen fanan ji tayi kamar karta tafi dakinta tashiga ta canza kayan jikinta zuwa riga da wando falazo tasa hijab dinta har kasa dama kayanta duk suna cikin wardrobe dinta,

Haka tanaji tana gani tayiwa su mama sallama, suka fito ita da suhaima tana rike da hannun auta ajikin motar suka samu Mr azaad da ya al ameen suna tattaunawa game da yanda zaa shawo lamarin ya usman bude motar yayi ya dauko fashion bag dake cike da chocolate kala_kala yaba auta karba tayi tana fadin " thank you yaya balarabe god bless you" murmushi kawai yayi azuciya ya amsa da Ameen motar suka shiga fanan na musu bye-bye.

Sun danyi nisa da tafiya se taga yacanza hanya kallonshi tayi tace " Mr azaad ina zamuje naga nan de ba hanyar gida bane" batare da ya kalleta ba yace " namanta ban fada miki ba dazun nagama cinikin kanki to yanzu zamuje a fille ne" iya tsorata fanan ta tsorata saboda ko kadan bataga alamar wasa a fuskanshi ba he sounds very serious mazgewa tayi tana turo baki tace " da ka siyawa kanka rashin kwanciyar hankali dan wallahi nadinga maka fatalwa kenan" tuntsirewa yayi da dariya tare da taka birki motar gudun kar asamu matsala sosai yake dariya kamar ba Mr azaad ba, ya salam wani irin kyau yakara da yake dariyar kyawawan fararen hakoranshi su kansu abin kallo ne zuba mishi ido kawai fanan tayi yayi masifar mata kyau tun daga saninta dashi izuwa yanzu bata taba ganin yayi dariya irin haka ba se yau seta ga ma dariyar yafi mishi kyau ,koda shekara dari zasukai ahaka da wannan dariyar dauke akan fuskanshi bazata taba gajiya da kallonshi ba. hura mata iska yayi a fuska sauke idonta kasa tayi tana wasa da yatsunta jan motar yayi sukaci gaba da tafiya beyi packing a ko ina ba se a ice cream planet zallan ice cream ake siyarwa awajen wajan ya hadu sosai kaff gombe inde wajan da ake siyar da ice cream ne to yafisu kyau da tsaruwa, se fitar da hasken wuta kala_kala yakeyi tunda suka iso gun wajan yadauki hankalin fanan se kallon wajan takeyi tana sakin lallausan murmushi, " muje " kawai yace mata ya bude motar ya fito fitowa itama tayi suka shiga ciki , ice cream yazaba yafi kala biyar masu tsada mika mata ledar yayi yabada atm card suka cire kudinsu motar suka koma tun kafin yatada motar fanan tabude roba daya tafara sha se lashe baki takeyi ice cream din yamata dadi bata taba shan ice cream me dadi irin wannan ba , ahaka harta sha roba uku ta bude na hudu kenan zata fara sha yayi karaf yarike hannunta yakarbe ya ajiye kafin yace " yanzu ke in anbarki se ki tazubasu a cikin ki ko ? Keda yakamata ki hana wani shine ke kikeyi to wayan nan se gobe" yatsina fuska tayi idon nan nata dasuke manya dasu yayi rau_rau kamar me shirin kuka tace " ayyah Mr azaad kabarni in shanye Allah yanzu in bansha ba kwadayina ze tashi " kallonta yayi ta gefen ido yaga yanda takoma abin tausayi aranshi yace " wani abu se yarinta in bahaka ba mutum yata durawa cikin shi sanyi" afili Kuma yace " idan kwadayin yatashi inada abinda zan bashi " ganin ya manna mata hauka ne yasa tayi shuru tana bin ledar ice cream din da ido ahaka har suka iso gida.

Gyara packing yakeyi ta faki idonshi tadau roba daya tasa a hijab dinta tafito daga motar da gudu tayi ciki , murmushi kawai yayi dan yaga abinda tayi wato shi zatayiwa wayo , bin bayanta yayi yanda tasamu falon ba kowa shima haka yasamu duk sunshiga sun kwanta dakinshi yashiga yayi wanka ya sauya kaya izuwa sleeping dress ya kwanta.



Tana zaune a tsakiyar titi misalin karfe 2 nadare kafa yadauke babu kowa ba alamar koda kafar mutum se haushin karnukan dake tashi , zaman yan bori tayi gashi duk yarufe mata fuska ga mutum kwance agabanta cikin jini dake malala ajikinshi sanadiyar yaga cikinshi datayi kayan cikin duk suna waje itakuma se aikin cin namanshi takeyi zaro dogon hanji tayi tasa abakinta dake dauke da dogayen hakwara duk sun rine da jini , tana janshi kamar yanda akecin indomie harta gama cinyewa tass bata kyaleshi ba seda ta cinye duk wani nama ajikinshi yarage qashi bakinta ta kafa adede wuyanshi tana zuqan jini seda ta tsotse jinin kaff kafin ta dago kanta bakinta yayi dama_dama da jini zaro dogon harshenta tayi ta sude baki hade dayin gyatsa mikewa tayi tsaye tamaida gashinta baya nan take fuskanta ya bayyana ba kowa bace face zeenat Muhammad mainasara......



Kuyi hakuri da yanayin read more din yau wallahi yau nidince se a slow.

~Semun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy πŸ‘πŸ™~

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺



Story & written by ✍️
MRS 🌹 ISHAM 🌹




πŸ””πŸ“š JARUMAI WRITERS ASSOCIATION πŸ“š






Page 4️⃣6️⃣ & 4️⃣7️⃣




Duk abinda takeyi suna kallonta a madubin tsafi sun san yanzu zasu samu abinda sukeso tunda yar family sunsamu sun jawota cikin kungiyarsu bako wani kungiya bane wannan da yawuce vampires union, kungiya ce da suke shan jini da kuma cin naman mutane da dabbobi sunada matukar hadari Kuma sun bawa zeenat maita ne dan su rama abinda mommy ta aikata musu.


Taya akayi zeenat tazama daya daga cikin kungiyar vampires union, yau fitansu da safe ita da ya fawwaz and areef zasuje gidan anty amina daga nesa ta hango wata yarinya na tallan guiva setaji ya shiga ranta magana tayiwa fawwaz yatsayar da motar tasiya tafara sha acikine tasha maitar batare data sani ba .

Bayan sunzo gidan anty amina ne tafara jin wani irin sauyi ajikinta setaji kamar abu na mata tafiya hade da magana akunne. dakin su aslam da islam tashiga tadan kwanta ciwon Kai ne yafara damunta shisa dasu fawwaz sukace zasu tafi tace suje kawai ita se gobe zata dawo aikuwa tafiyar sukayi abinsu, anty amina data lura da yanayinta kamar bata da lafiya yasa ta tambayeta amma se kawai tace mata bakomai.

Around 10 duk sun kwanta ita kam takasa bacci wani azabebben yunwa ne yafara ciyota ,kitchen tashiga har lokacin ciwon Kai din besauka ba bude food flask din tayi dan ta dibi abinci toshe hanci tayi jin abincin namata wari kamshin danyen nama ne yadaki hancinta bin direction din da takejin kamshin tayi har izuwa fridge dauko namar tayi duka tana kallon shi , tunani" tafara taya zanci danyen nama " jitayi andaka mata tsawa akunne cike da umarni taji murya nafadi " ki tabbatar da kincinye naman nan " tun kafin yagama magana tahau cin naman haka tacinye namar da yafi kilo goma , wani sabon yunwa tafaraji jitayi naman dataci yatayar mata da kwadayi kamar wata mahaukaciya haka ta birkita kitchen din tana neman nama amma babu daki takoma kamshin su aslam da islam ne yacika mata hanci shinshinasu tayi tana ajiyar zuciya tasamu nama hankali kwance bude baki tayi nan take dogayen hakwara suka fito , jitayi namar aslam yayi tauri sosai kamar dutse haka ma Islam duk yanda takai da son cinyesu to abin yagagara badan komai ba sedan adduah da mamansu da babansu sukeyi musu afusace ta tashi tabar dakin jikin bango ta shige fitowa tayi abakin titi kwance taga mutum da sauri ta karasa wajan ta farka cikinshi tafara cin naman dama su suka ajiye mata ganin abin yafara aiki ajikinta yasa sukayi murna sunada ya kinin se ta cinye yan gidansu kaff.

Washe gari.

"Mr azaad ! bansan meke faruwa ba amma yau natashi da faduwar gaba Allah shine masanin dede" cewar fanan dago Kai Mr azaad yayi yadan kalleta shikanshi inya tuna zata tafi seyaji wani irin aranshi amma babu yanda suka iya, kwantar da kanta yayi a cinyarshi sannan yace " inkin ji faduwar gaba kidinga karanta innalillahi wainna ilaijiraji unnn in sha Allah ze dena, " murmushi tayi ta sakeyin lamo ajikinshi , tunda sukayi breakfast suke zaune afalo yana duba wasu files, yaseer ne ya kirashi awaya ya sanar mai yana falon ummi okay kawai yace mishi kallon fanan yayi yace " dauko hijab dinki muje falon ummi" tashi tayi dan ta dauko hijab din jikinta na sanye da Riga da skirt na kanti ,fitowa tayi tasamu ita yake jira rike hannunta yayi suka nufa falon ummi, duk suna zaune afalon banda abba da ya fita meetings ummi, yaseer, fawwaz,areef tsungunawa tayi ta gaidasu sannan ta zauna , yaseer ne kasa_kasa kamar wani munafiki yace " dude two days kayi wuyan gani ina kashiga " hararanshi Mr azaad yayi shida yadena nemanshi tun zuwan dayayi last harsuka so yin fada akan fanan amma yanzu yana ce mai ya buya , dariya yayi da yaga hararanshi kawai Mr azaad yayi bece mai komai ba , sallamar zeenat ne yasasu kallon bakin kofar tun kafin ta iso cike da tsokana yaseer yace " yanzu haka ake bakunta zeenat daga zuwa kin kwana shine za ki dawo da sassafe kamar wacce aka koro " turo baki tayi tace" ya yaseer kaiko ni nayi missing din ummina ne shisa na dawo " itade ummi batace musu komai ba suna yar hira da fanan da gudu zeenat tafada jikin fanan tana rungumeta, ummi ne tace " nikam zee kina da hankali kuwa karyata zakiyi" kafin takarasa maganar sukaga fanan tasa iya karfinta ta ture zeenat ajikinta seda ta kusa faduwa yaseer yariko ta dukkansu kallon mamaki suke

1 Comments On NI DA PATIENT DINA book 2
avatar
aisha-9-6-3

11 months ago

Reply

I like this book

Please Login or Register in order to submit comment