Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata. Ahaka suka fito motoci guda 10 ne yakejiransu banda na securities, rungumeta zeenat tayi tana " anty zanyi missing dinki" " zanyi missing dinki nima sosai zee" cewar fanan, zuwa fanan tayi tarungume ummi, murmushi ummi tayi tace" my feena ba dadewa zamuyi ba kinji take care of yourself in son yamiki wani abu kifadamin" tom ummina, haka abba yasake jawa Mr azaad kunne akan yakula da fanan kamar gaske yace " to" sosai tamusu adduah Allah yakiyaye hanya yakaisu lafiya yadawo dasu lafiya, sunjidadin addu'arta sosai.
Haka suka shiga motar zuwa airport suna musu bye-bye fanan kam jitayi kamar tayi kuka antafi anbarta da Mr azaad dakyar inzasu dawo susameta araye cewarta.
Haka yafinciki hannunta suka koma cikin gidan.

Tundaga wannan ranar fanan bata Kara sanin meye farin ciki ba duk wani hanyar dazata huta taji dadi Mr azaad yadatseshi gaba daya tafita ahayyacinta azabtar da ita kawai yakeyi da aiyuka masu matukar wahala duk tabi tarame tadanyi duhu abun tausayi ko kyakyawar bacci batayi yayi nasarar jefa mata tsoronshi aranta ko muryanshi taji jikinta daukan rawa yakeyi , kuma duk wahalar daze bata baya barinta da yunwa.

Yauma kamar kullum tunda garin Allah yawaye take faman wanke mishi wankakkun kaya da lafiyarsu kalau babu abinda yasamesu haka take tawanki kamar baiwa kwala mata kira yayi da " keee " naman jikinta ne yafara bari tsabajin tsoro haka tafito atsorace tace " Mr azaad gani" cike da izza da gadara yace hadamin black tea " dasauri tafice tashiga kitchen 3mint yadauke tagama tafito dashi hannunta narawa taza mika mishi yadan zuba ajikinshi wani gigitaccen mari yazabga mata a kumatu wanda seda tadena ganin komai nakusan minti uku kawai jinshi tayi yana" ke wacce irin mahaukaciya ce dazaki kona ni da hot tea" hawayen daya wanke mata fuska tagoge tana bashi hakuri dan tasan inya fusata yanzu ze kara mata wani marin daukan cup din tayi takai dustbin dan yadan fashe, tagoge wajan tana danne kukan daya ciyota kiranshi yaseer yayi yasanar mai yana falo.

Hira sukeyi da yaseer tashigo hannunta dauke dasu drinks takawo mishi tunda tashigo yaseer yake kallonta da mamaki ganin lokaci daya tayi wani rama kamar wacce tayi jinya fuskanta asake tace " ya yaseer ina wuni " amsawa yayi yana kare mata kallo dole akwai abinda yake faruwa , harzata juya cikin tsawa azaad yace " ke zonan " jikinta har bari yakeyi itaduk a tunaninta wani laifin takarayi nan da nan hawaye yafara zuba a idonta, kallonta yayi kafin yace " meye nafada miki dangane da falon nan ?" Tana share hawaye tace " kace karna kara shigowa " " okay yanzun renine yasa kika shigo " cewar Mr azaad ja da baya tayi tana" kayi hakuri Mr azaad bazan sake ba"
Inbanda salati babu abinda yaseer yakeyi aranshi dama abinda azaad yake aikatawa yarinyar nan kenan tabbas yasan azaad ze aikata haka koma abinda yafi haka amma dayaji shuru yayi tunanin yarungumi matarshi ne suna zaman lafiya ashe bahaka bane, kallon fanan yaseer yayi yace " zeki abinki" dagudu tashige cikin bedroom dinta dan gani takeyi kamar zebiyota yadaketa.
_____ Maida kallonsa kan Mr azaad yayi dake danna wayarsa ko ajikinshi gyara zama yayi yace " yanzu dude abinda kake aikatawa dedene? dan Allah wallahi baka rike amana ba wannan karamar yarinyar inka azabtar da ita meye ribarka " kallon yaseer yayi yace" dama aina nace nakarbi amanarta? Laifi tamin shisa nake hukuntata tana gama karban punishment dinta kuma zan saketa " girgiza kai yaseer yayi yace" karkayi haka azaad wallahi fanan ba kamar sauran mata bace ! Koma me take maka kamata yayi kayi hakuri ko kamanta lokaci kadan yarage mata dazatama barmana duniyarmu takoma inda ake bukatarta haba dude kaji tausayinta mana zata tafi tabar kowa nata amma dukda haka kana wulakanta ta wallahi insu ummi sukaji bazasuji dadi ba" daga kafada sama yayi alamar I don't care kafin yace" tafiyanta dakuma rashin tafiyanta nifa duk bedameni ba tatafi har yaumu takumu karta dawo dan nima ba kaunar ganinta nakeyi ba cos she's like a burden to me! Abinda nasani shine intamin laifi zan hukuntata " yaseer gani yayi inya biyewa azaad yanzu zasu iyayin fada yasa yatashi yatafi abinshi.


Yau Kwanan su Abba 5 da tafiya kullum insuka cewa Mr azaad yabawa fanan waya sugaisa ceyata basu uzuri, ummi de tanaji ajikinta kamar akwai abinda yake faruwa gashi wayarta yana hannunshi.

" Mr azaad dan Allah kabarni yau inje gidanmu ko kuma kayi hakuri kakiramin mama awaya " idonshi alumshe kamar bayajinta tunani tafarayi kode bacci yakeyi sake nanatawa tayi nanma yayi banza da ita haka taci gaba da mishi magana harta gaji be kulataba yasa takoma bedroom dinta takwanta tana kukan halin data shiga , daga hannunta sama tayi tana adduah " yah Allah ina rokonka kakawo karshen zamana da wannan bawan naka dayake kuntatawa rayuwata ! Allah kabashi ikon rubutamin takardar saki yau zuwa gobe " haka tadinga adduah tana kuka......



Tom se mun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy 👍🙏


Masu comment damin adduah nagode sosai Allah yasaka da alkhari, kukuma da sede ku karanta kuyi shuru ba sannu bare Allah ya isa🤔 kallonku kawai nakeyi kowa yayi dede yasani .





via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺

Story & Written by
MRS 🌹 ISHAM 🌹




Page 3️⃣9️⃣ & 4️⃣0️⃣




Haka sukaci gaba da rayuwa acikin gidan daga ita seshi se yan aiki wahala babu irin wanda baya bata haka kurum zesata wankin manya_manyan bedsheets da blanket ga fada da tsawa gakuma maruka.

Ana gobe su ummi zasu dawo taje tasameshi yagama shiryawa zefita office " Mr azaad inaso muyi magana " okay kawai yace , tadaura da " Mr azaad badanni ba kayiwa Allah daya halicceka kayi hakuri kasakeni bana kaunar zama dakai dede da dakika biyu banajin zanci gaba da zama dakai yanda ka tsaneni na tsaneka yanda baka sona haka nima bantaba sonka ba duk abubuwan dakamin na yafe maka ka sauwakemin intafi wajan iyayena sukadai ne nazama musu dole " ko kadan kalamanta basu bata mishi rai ba, hasalima tunda tafara magana yake kallonta babu ko kyaftawa yakafeta da wayan nan mayun idon nashi , gyara tsayuwarshi yayi ajikin kofa hannayenshi na harde akirjinshi yana kallonta murmushin gefen baki yayi yace " saurin mekikeyi haka base kinsake tunamin ba am aware kawai Jiran lokaci nakeyi " besake sauraranta ba yafice zama tayi akan kujera tana tunanin rayuwa anrabata da gidansu yan uwanta da kowa nata gashi farin ciki yakaurace mata, haka ta yini jiki asanyaye jitakeyi kamar bata da wani lafiya, sosai takejin sanyi nan take jikinta yabara barin sanyi bedroom tasamu tashiga takwanta taja bargo tarufe jikinta.

Zazzabi me zafin gaske ne yariketa ko kwakwaran motsi bata iyayi tana kwance tun safe daya fita yabarta be dawo ba balle yasan halin datake ciki ko aikin dayasata bata samu tayi ba.



Kwance take adaki se sakin murmushi kawai takeyi waya na manne akunnenta lumshe ido tayi giyar soyayya na dibanta murya anarke tace " hubby wallahi nayi missing dinka!katafi kabarni uhmm uhmm Allah inbaka dawo dawuri ba zanyita kuka kuma bazanci abinci ba haka zanbar kaina da yunwa" ajiyar zuciya fawwaz yasauke yana karajin tsananin kaunar suhaima nakara shiga ranshi besan wani irin so yake mata ba tariga da tazama wani bari na rayuwarshi yanzu sunriga dasun kamu da son juna, kara rungume pillow yayi yana fadin " am sorry baby nima nayi missing dinki fiyeda yanda bakya zato gobe zamu dawo" ihu tasa seda yacire wayar akunnenshi " hubby are you serious? " Dariya yayi dan suhaima itama ba laifi akwai dan sauran yarinta yace " in sha Allah baby gobe zamu dawo just pray for us kinji " nutsuwa tayi ta shagwabe fuska kamar yana gabanta tace " hubby kamin alkawarin kana dawuwa zakazo inganka " murmushi yayi yace " I promise Ina dawuwa ko gida bazan shigaba zanzo inga babynah " rufe fuska tayi tana kyalkyalewa da dariya " baby tsarabar me kikeso in kawo Miki?" Shuno baki tayi tace " hubby i want nothing than you kai kadai kawai nakeso " haka suka dinga zubawa junansu kalaman soyayya masu dadin gaske ( nida ba soyayya nakeyi ba gajiya nayi da hirar nayi gaba abuna karsusa in fusata)

Yana zaune a office dinshi yana duba wasu files dinda sakatariya jamila takawo mai na sabobbin ma aikatan dazaa dauka ga faisal shima azaune yadukufa yana aiki a system, ringing wayarshi yayi yayi picking yasa akunne yana fadin " my sweet mom kuna lafiya ?" Abangaren ummi ta amsa mai " da lafiya Lau son yakuke ina fanan tunda mukazo kullum senace kahadamu amma abu yagagara! Kasiya mata waya kabata kasan badadi yan uwanta nason magana da ita sujita shuru" harga Allah seda ummi ta ambaci sunanta tukun yama tuna da ita dan kwata_kwata yamanta da lamarinta okay yacewa ummi sukaci gaba da hira kafin tayi hangup, system dinshi yakunna yashiga footage din gidan na CCTv camera, tun daga sa'ilin dayake gida be fitaba yashiga harzuwa lokacin datashiga daki takwanta around 10:00 besake ganin ta motsaba haryanzu duba time yayi yaga 4:00pm mamakine yakamashi ganin harzuwa time din tana kwance tunani yakeyi ko bacci takeyi sekuma yatuna duk baccin dazatayi seta tashi tayi sallah amma yau shuru ko breakfast batayi ba.
Basarwa yayi yaci gaba da aikinshi can kuma yamike yayi switching din system din daukan jacket din suit dinshi yayi. faisal ganin oganshi yatashi yasa yamike yadau briefcase dinshi suka fice tada motar driver yayi dayaga sunfito shiga sukayi suka nufi gida , direct bedroom dinta yashiga yasameta kudundune acikin bargo numfashinta nafita sama_sama batama san yaye blanket din yayi yasa hannu taba jikinta dasauri yacire jin zafin daya dauka daukanta yayi yakaita bedroom dinshi , lalubo wayarsa yayi yakira doctor ammar, within 20mnt doctor ammar yashigo shikanshi yasha mamaki ganin fanan awannan yanayin ga ciwo datake fama dashi , kallon Mr azaad yayi yace " amma tadade tana ciwo ne Koh?" Amsa yabashi da " I don't know" jin haka yasa besake mishi magana ba yafara bata taimakon gaggawa yadaura mata drip yayi mata allurai " ga magungu nanta tana farkawa tasamu tasha abu me dumi like tea setaci abinci kafin tasha magani Allah yabata lafiya " yatabi yabarshi zama yayi agefenta yana kallon beauty face dinta dayayi fayau sa hannu yayi yana shafa gashin kanta daga bisani yakoma kan cusion yazauna.
______ karfe 8 ruwan yakare cire mata drip din yayi yana kokarin cire calular , ahankali tafara bude idonta dasuka mata nauyi dishi_dishi take kallon fuskanshi harta fara ganin komai clearly fisge hannunta tayi daga nashi takoma can kuryan gadon ta dukunkune awaje daya tana " Mr azaad kayi hakuri dan Allah karka dakeni kaina ne yakemin ciwo amma yanzu zanyi aikin kayi hakuri kamin rai bazan sakeba" haka tadinga sambatu tana bashi hakuri, jikinshi ne yadanyi sanyi hawa gadon yayi yanufeta ganin tunkarota yakeyi duk tunaninta dukanta zeyi ko yamata tsawa yasa ba shiri tasauka akan gadon zata gudu jirine yafara dibanta tayi tangal_tangal zata fadi yatarota tafado jikinshi muryanta dabaya fita tace " Mr azaad kabarni intafi dakina" tana magana manyan idonta na lumshewa dagata yayi yamaida ita kan bed din sannan yadanna line din gidan wanda in aka kira masu aiki zasu daga , dagawa abu me aiki tayi umarni yabata data shirya abinci da tea yanzu takawo part dinshi aikuwa haka akayi , bata jima ba tazo tayi sallama jin muryanta yasa yaje yakarbo tana zaune atsakiyar gado tana binshi da ido ita haryanzu gani take kamar ze mata wani abun dan batayi abinda yasata ba .
Sa tea yayi acikin cup yamika mata karba tayi tafara sha kadan_kadan hartasha fiyeda rabi taji dadin shan tea din sosai ajiye cup din tayi akan bedside table , food flask yabude jallof din arish potato ne dayasha kifi banda da vegetables diba yayi yadawo gabanta , zefara bata kai mata spoon din yayi zebata abaki taki bude bakin se kawai kallon mamaki datake binshi dashi tafara tunani aranta anya Mr azaad ba poison yasa mata acikin abincin ba kuwa abinda betaba mataba yau shiyake mata.
Ganin taki bude bakin yasashi kara tamke fuska yana watsa mata uwar harara bashiri tabude bakin haka yadinga feeding dinta hartace ta koshi maganinta yamiqa mata tasha nan take tabara bata fuska zatayi kuka , lura yayi da kwata_kwata bata kaunar magani hakan yasa yajika maganin a cup yamatseta kamar wata yar jaririya yamata dúre dakyar tasha kokarin amayar da maganin take fuska ahade yace kina amar dashi adaren nan zanbaki hakkinki , aikuwa ba shiri tamaidashi. Kara daukanta yayi yashiga toilet da ita yadireta akasa yafice ,cire rigar jikinta tayi tana kokarin hanging dinshi yafada acikin jacuzzi cireshi tayi ta ajiyeshi a gefe wanka tayi tare da alwala rasa yazatayi tafito tayi iya towel ne a toilet din gashi kayanta din ruwa yajiqashi tafi mint goma tana tunanin mafita daura towel din tayi tafito, godewa Allah tayi dataga baya dakin hanyar fita tanema, harta kusa bakin kofa yafito daga dressing room hannunshi narike da jallabiya.
Idonshi ne yasauka akan kyakyawar surar da Allah yamata , kasa motsawa yayi sebin shape dinta da kallo yake musamman hips dinta dasuke acike masha Allah mamaki yafarayi dama wannan yarinyar haka ainihinta surarta yake ga brest dinta da rabinsu suka fito waje aranshi yace" how could that be possible yarinya da jikin manya?" Ganin irin mayen kallon dayakebin jikinta dashine yasa tayi saurin murda handle din dakin tafice tafada bedroom dinta tasamu tasa doguwar riga da hijab ta tada sallah , duk sallolin da akebinta seda tayisu kafin tasa kayan bacci jikinta bawani karfi sosai ta kwanta.

Shikuwa gogan naku gaba daya kasala ce tarufeshi lokaci daya barinma inya rufe idonshi yahasko mishi hoton surarta ,haushin kanshi yafaraji taya zetsaya yana tunanin wannan karamar yarinyar da ko cikekken hankali bata gamayi ba.



Karfe 1:00 na rana jirgin su abba yayi landing,Mr azaad damasu tsaransu ne sukazo tarbansu fawwaz de car key kawai yakarba dan beda burin daya wuce yaje yacika alkawarin daya daukawa babynshi .


Duka suna zaune afalo ummi tace " son ina feena ?" Yana danna waya yace " tana bedroom " "okay jeka kirata " tashi yayi tahaura upstairs din afalo yasameta tana yar goge_goge, kallonta yayi up and down kafin yace " ummi nakiranki afalo " cike da Al ajabi take bin bayanshi da kallo wato su ummin sundawo shine baze fada mata ba lallai Mr azaad. Dama doguwar rigar abayace goldin color ajikinta komawa bedroom tayi tasa gyale me girma tasauko.
Tun kafin ta iso gaba ki daya mutanen falon hankalinsu yakoma kanta ganin yanda lokaci daya tayi uwar rama sosai suke kallonta, tashi zeenat tayi suka rungume juna cike da murna tukun suka karasa falon duqawa tayi tagaishesu amsawa sukayi suna kallonta, zama tayi abinta akan lallausan carpet din falon , Abba ne yakalli Mr azaad yace " meyake damun fatima? datayi wannan ramar haka azaad?" Kallonta shima yayi yana neman ramar da akace tayi bayan ko ina najikinta acike bulbul. Shuru yamusu dan besan amsan daze bayarba tunda shide bega wata rama ajikinta ba, girgiza Kai abba yayi yakalli fanan " Fatima meyake damunki kika rame haka kode azaad yana miki wani abune bayan tafiyarmu?" Satan kallonshi tayi taga ko ajikinshi wayarsa ma yake latsawa abunshi , murmushin yaqe tayi tace " Abba babu abinda yakemin kawai de kwana biyu ne nayi rashin lafiya " ran ummi yabaci dajin haka domin kullum sesunyi waya da Mr azaad kuma seta tambayeshi ya fanan take yace mata" lafiyanta Klau" ashe baiwar Allah tana nan tana fama da ciwo amma dan bakin hali irin nashi yaki sanar da kowa.
Dago kai yayi suka hada ido da ummi dake doka mishi harara sunkuyar dakai yayi dan yasan dalili.
______ Rai abaci abba yafara magana " yanzu kai azaad ka kyauta kenan matarka bata da lafiya kusan kwana biyu amma baka taba fadawa kowa ba! Sannan kabata wayarta ko kasiya mata wani abu yagagara kullum semun ce kahadamu da ita amma ka kasa to ka kiyayeni kaduba yarinya duk tabi ta lalace kamar ba itaba " shide ko uffan bece musu ba saboda shibega abinda suke magana akai ba daga karshema tashi yayi yabar musu gidan , aranar kam fanan tahuta se lallabata sukeyi kamar kwai da dadin baki ummi take samu tama fanan wayo tasha magani har goma suna hira , jitayi kamar ta cewa ummi zata kwana apart dinta amma inta fadi haka zasuyi zargin wani abu tanaji tana gani sukayi sallama tawuce nasu part din.


Bari muleka Romeo and Juliet

Girki suhaima tayi mishi me ji da lafiya taci ado suna zaune suna sunashan hiran love Yanacin abinci se shagwaba takeyi mishi , bakaramin gigitashi takeyiba intana wannan shagwabar haka sukasha love dinsu ya ajiye mata tsarabanta tarakashi har bakin motar shi yatafi.
Komawa gida tayi tadauki fashion bag din daya ajiye mata tashiga dakin mama tanuna mata budewa tayi dogayen ruguna ne masu shegen kyau yan dubai da sarka da dankunne na gold se zobe, murmushi mama tayi tace " ohhh su suhaima anyi saurayi " kunya taji yarufeta tarufe ido suna dariya , " tun jiya babanku yace inbada miki ki mishi magana inde da gaske yake auren zeyi yafito" cike da kunya tace " to mama zan fada mishi".






Haka rayuwa taci gaba da tafiya yau yakama 1 month dayin auren fanan da Mr azaad, yana nan yana mata abinda yagadama wata rana yasata aiki wata rana kuma kota kanta bayabi, tun su ummi basu farga ba har suka fara fahimtan wani abu wani lokacin fanan setafi kwana biyu bata sauko downstairs ba kuma baya taba yarda wani yaje ciki ,sanda ze barta kuma se inzaayi dinner gaba daya tacanza, kuma komin tambayar dazasu mata amsa daya take basu shine " bakomai bayamin komai" ummi ce ta siya waya iphone 14 pro max tabawa fanan da sim taloda mata kati da data aciki,tacewa Mr azaad saura kuma kar inganshi ahannunta, tanan ne fanan tafara samun saukin wasu kayan bakin cikin kullum setayi waya da yan gidansu, suhaima da amira,auta sunzo wajanta harso biyu suma sunyi mamakin yanda takoma wata shuru_shuru da ita .

Alhamdulillah su Abba da yan uwansu sunje sun tambayawa fawwaz auren suhaima kuma anbasu ansa date nan da wata hudu zaayi ( tom Romeo and Juliet ankusa angoncewa kenan Allah yakaimu musha biki)


Ayau ne ranar asabar akatashi da wani irin gagarumin tashin hankali agarin gombe sakamakon ganin gawawwakin yara da manya , maza da mata ancire wasu sassa najikinsu anyi ritual dashi( tsafi) ansamu gawawwaki kusan 30 lamarin yadagawa mutane hankali kowa yanutsu da iyalanshi agida , jami'an tsaro se bincike sukeyi akan case din daga zaran yaro yafita haka zaa daukeshi baze dawoba sede aji labarin antsinci gawanshi.

Wannan aikin bana kowa bane face kungiyar SATANIC and BAPHOMET dasuke ritual domin yakar junansu domin duk wanda yayi nasara akan daya shize kwaci jaaazana haka suka dinga tsafi da mutane da basuji ba basu gani ba ,babu ruwansu dakoma waye yafita kana yin waje zaa daukeka cakk shikenan kuma katafi, wannan dalilin yasa akasa lockdown agombe.


Duk suna gida suna jin abinda yake faruwa Abba yace karwanda yafita, dukkansu suna zaune afalo sunata kallon labaran da akeyi .


Bangaren mommy kuwa tun ana kwana biyu zaa fara ritual din abin duniya yadámeta gashi bahalin zuwa ayi da ita dan haryanzu bata warke ba tanata kan jinya dan tasan dataje anyi da ita tasan dole tanzarzar yakara mata matsayi.


Jikin fanan ne yafara wani irin kadawa kamar wacce akasawa shocking , nufanta sukayi cikin tashin hankali ,riqeta gam azaad yayi duk jijigan datakeyi tana jikinshi yaki saketa can kuma seta dawo normal, kallonsu tayi gabaki dayansu tana zubda kwalla tace " shin akwai abinda ake boyemin ne daban sani ba? Kufadamin jinake kamar zanmutu yanzu inbanji ba wayyo Allah na" takarashe maganar da karfi tana rike kanta da yasara mata tabbas abu takeso ta tuno amma takasa sede yadinga mata flash, duk shuru sukayi sun rasa abin fada shin yau ne fanan zatasan ko ita wacece? Kokuma yau ne zatabar duniyarsu? gaba daya tambayar dasukewa kansu kenan.

Areef ne sukaga yaje gabanta yazube akan guiwowinshi kanshi akasa , nan ne jikinsu yasakeyin sanyi domin sunsan tabbas wannan ba areef bane.
Cike da mamaki takalleshi ganin yadúrkusa agabanta goge hawayen fuskanta tayi tace" ya areef Meye haka ?" Girgiza kai yayi cikin muryan daya manyanta " yace sarauniya ba areef bane! Sunana abdud Shakur nine galadiman masarautar nasminaya! Nazo ne domin in amsa miki tambayoyinki sannan insanar dake ko kedin wacece.......




Hakikanin gaskiya inajin dadin adduah dakukemin dakuma comments dinku it means alot to me, wallahi ina matukar kaunar ku sosai Allah yabarmu tare daga nan har gidan aljanna 🙏😘😍, ku Kuma masu karantawa kuyi shuru ba sannu balle Allah ya isa kallonku nakeyi kawai kowa yayi dede yasani amma zaazo time dinda mutum in yaganshi awaje karyaga laifina domin nima mutum ce ba engine ba.


Se munhadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy 👍🙏.


via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺



Story & Written by
MRS 🌹 ISHAM 🌹
JARUMAI WRITERS ASSOCIATION ✍️✍️





Assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhum iname mika sakon taaziyata ga alhalin anty hadiza salisu sharif dakuma marubuta da kowa gabaki daya, Allah Ubangiji yajikanta da rahama, Allah yasa tahuta , Allah yakai haske kabarinta ya yafe mata 🙏🥺 Allah yasa innamu yazo mucika da imani da kalman shahada , Allah yagafarta mata 🙏🙏 Ameen ya hayyu ya qayyum.


꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁



Page 4️⃣1️⃣ & 4️⃣2️⃣



Fa ra bata labarin tun daga lokacin da take ciki har zuwa haihuwarta da kuma abinda take dauke dashi a jikinta da yakar kungiyoyin kaff seda ya fada mata sannan yakara da " labari mara dadinji shine! gaskiya sarauniya a ko wani irin lokaci za ki iya tafiya domin yawan rashin adalcin da akeyi yana kusantoki! Jaaazana nakara bayyana a jikinki , duk inda aka samu irin wannan bar nan ya afku sau uku nan take zaki koma masarautar ki , ko da kuwa kin shirya ko baki shirya ba yanzu de anyi biyu ina tunanin saura daya".
Takasa cewa komai se hawaye da kuma murmushin datakeyi atare lokaci daya ,
Tabbas masarautar take gani yana mata flash dakuma sarki abdud daar ashe itadin shugaba ce dazata kawo gyara .

Se yanzu take jinta cikakkiya amma dà se ta dinga jinta kamar akwai abinda ta rasa ,kamar ta rasa wani bàri a tare da ita amma yanzu da tasan ita wacece se taji duk wani gurbi yacike,

Duk suna jira suka reaction dinta ya zataji intaji wannan labarin, abinda basu taba zata ba tayi sujjada tayi ta daga hannunta sama tana yiwa Allah godiya " Allah nagode maka dakasa nazama zabàbbiya ! tabbas zanyi aiki da duk wani wani karfi danake dauke dashi domin kare rayukan al'umma daga jinsin bil adama harzuwa jinni koda kuwa zezama sanadiyar rai ne , Allah kasa ta dalilin haka in zama me rabo a aljanna "
amma data tuna za tabar iyayenta da duk wayanda ta sani se taji gaba daya duniya bata mata dadi. Kallon Abdud Shakur tayi dake jikin areef tace " inson magana da kai sirri" dago kai kawai yayi ya wuro iska a bakinshi yace " sarauniya za ki iya maganarki ayanzu babu wanda zeji me muka tattauna " kallon yan falon takeyi dan ta tabbatar yasa tace " zeenat kinaji ?" Shuru zeenat bata mata reply ba sede ta bita da ido .
Su kuwa su abba kallonsu kawai suke suna magana amma basajin abinda suke fada azaad de ya kafe bakinta da

1 Comments On NI DA PATIENT DINA book 2
avatar
aisha-9-6-3

11 months ago

Reply

I like this book

Please Login or Register in order to submit comment