Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

azaad baya son fanan, haka itama fanan bata sanshi auren kawai Allah yayi de zaayi shine .

Duk sunyi sallah isha suna zaune akan dinning zasuyi dinner kowa ya hallara harta Mr azaad yafito serving dinsu akayi suka faracin abinci kwarewa fanan tayi tana yar tari kadan_kadan suna mata sannu abu kamar wasa tari yayi karfi hartana biga kanta da table din gaba daya rudewa sukayi suna mata sannu anty Amina da ummi suna bubbuga bayanta. Nan take kuma tarin yatsaya suka bata ruwa tasha idonta yayi ja dan wahala , rike wuyanshi yayi dayaji kamar anshake shi jin shakewan yayi yawane yasa yamike rike da wuyanshi yana kakari kamar wanda zemutu tashi sukayi arude suna nufo wajanshi sosai aka shakeshi amma su basa kallon kowa se rike wuyanshi dayayi babu yanda basuyi ba dan su cire hannunshi akan wuyanshi amma sun kasa. lokaci daya jikinta yayi wani irin kaduwa akayi walkiya da karfi farin haske yarufe ko ina tashin hankali baasa mata rana gaba daya yau sunga abinda basu taba gani ba hasken seda yakai 5mint kafin yawashe duk sundukufa akan Mr azaad dake kakarin mutuwa se adduah sukeyi mishi ga farin hasken daya tsorata su mikewa azaad yayi yazauna yana sake wuyanshi jin ansakeshi , Karan sarkan kafa sukaji duk taku daya idan tayi se yayi kara juyawa sukayi domin ganin ta idan karan kefitowa tozali idonsu yayi da SARAUNIYAR nasminaya cikin shiga ta jarumar sarauniya dakuma sadaukiya wacce ta amsa sunan ta jaruma farin wando ne me fadi kamar wandu nan Pakistan kafan wando kamar ansa mishi roba se riganshi me hannun vest tsayinshi har kusada guiwanta farin kayane sol anmishi kwalliya da zinari domin kayan da sarki da sarauniya suke sawa ma daban ne asaman kayan kuma ga irin rigunan nan kamar nakarfe da akesawa idan zaa fita yaki bayanta nadauke da kwari da baka dasuke cikin gidansu akillace suna jiran kota kwana. se kugunta dake dauke da wukane dogo na sarauta awajan , kunnent,wuyanta duk suna sanye da sarka da dankunne harta dantsen hannunta nadauke da wasu irin saraquna , kafanta tana sanye da sarkokin kafa na zinari dawo da kallona na iya izuwa fuskanta da kanta gashinta nagani yakara tsayi amma bawani sosai ba yayi curly anzubasu agefen wuyanta nadama dana hagu sauran kuma suna gadon bayanta anmusu kwalliya da sarkan kai ( head band chain) ga crown 👑 akanta me matukar kyau fuskanta kamar wacce akayiwa kwalliya ( umm to aidole ma aga fuskar sarauniyar aljanu da kwalliya ) dan karamin bakin nan yasha dark maroon janbaki idonta na sheki sosai .
Fuskanta ahade kamar hadari gaba daya ta tashi daga fanan din dasuka sani se takoma ainihin sarauniya babu abinda takeyi daya wuce yalki saboda gwala gwalan dake jikinta gaba daya gakuma daddadar kamshin dake fitowa ajikinta wani irin masifar kyau takara . Suman tsaye sukayi suna kallonta tunani suka farayi kode yaune ranar komawarta masarauta gaba daya sukaji tayi musu gwarjini jikinsu yayi sanyi, tafiya tafara kamar wacce take lankwasa jiki da gangan takaraso wajansu ko kallon direction din dasuke batayiba tasa hannu tashake iska tunani suka farayi meye to tashake dansu basu ga komai ba. Cikin wata murya me zaki da amo tayi magana tana karkata kanta gefe kamar wata robot " ki bayyana kanki " seda falon ya amsa da muryanta aikuwa tana gama fadin haka wata halitta tabayyana cikin bakaken kaya mara kyaun gani seda sukaja baya banda azaad.

Dagata tayi suka fara tafiya a sararin iska acikin falo seda suka kusa roof din falon suka bace batt.



Sunshiga cikin damuwa yanzu shikenan bazasu sake ganin fanan bah kenan zeenat se kuka takeyi, iyayenta zasuji zafin tafiyanta batare da sunyi bankwana ba, Mr azaad ne yace " Amma ai waadin tafiyanta beyi ba bekamata ace tunyanzu harta tafi ba " abbane yace " Kuma hakane waadin tafiyanta beyi ba taya zaayi ta tafi yanzu kila abinda yafaru harin da aka kawone yasa jaaazana bayyana ajikinta da sauri " jimami suke tayi har sha Daya nadare basu kwantaba wani security ne yashigo falon da gudu haryana kokarin faduwa zuba mishi ido sukayi suna kokarin tambaynshi lafiya yayi saurin fadin " ranka yadade naje zanrufe kofan garden ne naga mutum akwance awajan jin haka yasa Mr azaad fita da sauri yafice yanufi gadin din suma suka rufa mishi baya tundaga nesa daya hango hijabin jikinta tana kwance plat bata motsi yaganeta sa hannunshi yayi yadagota kamar yar babyn roba yayi ciki da ita ahanya yahadu dasu ummi duk sunfito sunbi bayanshi ganinshi dauke da itane yasa suma suka koma ciki haurawa yayi da ita part dinsu dakatawa sukayi afalon suna alhamdulillah sannan abba yacewa kowa yaje yakwanta se gobe haka kowa jiki amace suka tafi.

Direct bedroom dinshi yayi da ita yakwantar da ita akan bed hannu yasa yacire mata dogon hijab din jikinta da kayanta yarufeta da blanket yashiga bedroom dinta yabude wardrobe yadauko sleeping dress white color me guntun wando yadawo yasa mata kallon kirjinta dake cike da dukiyar fulani yayi nan take yaruntse ido yanajin haushin kanshi naganin dayayi mata yagyara mata kwanciya, yayi toilet bayan kamar 15mint yafito yayi wanka yasa sleeping dress dinshi yahau bed din dan nesa da ita kadan yaje yakwanta yana rufe jikinshi da blanket yayi musu adduah yakashe wutan dakin yabar bedside lamp.
____ cikin dare tafarka da zazzabi jikinta rau zafi cikin bacci yaji kamar sheshekar kuka tashi yayi zedubata yagansu manne da juna yana rungume da ita ajikinshi kokarin raba jikinsu yakeyi tasake rikeshi tana " uhmm uhmm sanyi nakeji karka tashi" tafada ashagwabe kallon fuskanta yayi da hasken dake gefen bed din idonta arufe ga hawayen datakeyi gashin idonta sunyi zara_zara seturo baki takeyi duk abinda take fada acikin baccine da zafin zazzabi kallon cute face dinta yayi yasamu cikin dabara yatashi toilet yaje yadibo ruwa a bowl medan fadi yafito da karamar towel ahannunshi zama yayi akan bed din yatallafo ta jikinshi so yakeyi yadan goge mata jikinta da ruwan sanyi saboda zafin da jikinta gashi dole seya cire yacire mata riga amma yana tunanin karta tashi tayi tunanin wani abu tazo ta renashi he has no choice hakan yayi yacire rigan yafara goge mata jikinta da towel din jin hannunshi na gogan kirjinta ne yasa yahakura yamaida mata rigan yakwantar da ita locker dayake ajiye magunguna shi yabude yadauko mata magani tashinta yayi , kallon fuskanshi tayi tace " miye! miye ? katasheni nikam bacci zanyi " sa mata magani yayi ahannunta yace tasha bata fuska tayi ganin kwayan magani fashewa dakuka tayi nikam " bazan shaba " tafada tana make kafada ganin inya biye mata dagasken bazata shadin ba, yasa yawatsa kwayoyin maganin cikin glass cup suka jiga dan kwantar da ita yyi ajikinshi yasa hannu yamatse bakinta yadùra mata kakarin amai takeyi yahade bakinsu waje daya seda yatabbatar aman ya koma kafin yakwantar da ita shima yakwanta manne da ita ajikinshi



Karfe 5 dede tafarka jinta ajikinshi yasa tayi saurin tashi sosai abin yadaure mata kai metakeyi ajikin Mr azaad akuma dakinshi duk abinda yafaru adaren jiya ta manta kallon jikinta tayi taga kayan datake sanye dasu waro ido waje tayi data tuna ai ita dogon riga ne da hijab ajikinta taya akayi suka dawo kayan bacci kuma gata a dakin Mr azaad zuciyarta ce tace " waye kike tunani zeyi haka Mr azaad ne mana" cikin sauri takalleshi bacci yakeyi abinshi hankali kwance sadaf _ sadaf ta tashi tabar dakin tashiga nata dakin wanka takesonyi dan kwata_kwata batajin jikinta da karfi.


To bari muleka bangaren mommy.


Awurge a tsakiyar falonta nahangota acikin mawuyacin hali se numfashi takeyi dakyar kamar zata mutu kayan jikinta duk ya yayyage ga jikinta nafitar da jini kamar wata al majira. Abinda yafaru shine bayan tayiwa aneesa alkawarin gamawa da babin fanan atime din dasuke dinner taje da niyar kasheta tayi iyayinta ana haka taji anbuga ta da kasa kallon wacce tamata hakan tayi taga ashe khairatyyy ce ganin mission dinta na kashe fanan beyi bane yasa takoma kan azaad kokadan khairat batayi yunkurin hanata ba domin ita umarnin kula da sarauniya kawai jakadiya tabata. Ganin zaayi kisane yasa wani bangaren jaaazana yamotsa shisa fanan ta bayyana a ainihinta ta sarauniya domin takareshi cike da jindadi ganin sarauniya tabayyana khairaty ta duka kasa cikin girmamawa, lokacin da sarauniya ta rike mommy suka bace sararin samaniya takaita tamata mugun duka kokarin ramawa mommy tayi amma ina ko kadan karfinta beze iya da sarauniya ba haka tanaji tana gani taji mata mugun raunika ajiki sannan tasaketa tafado kasa dakyar mommy ta iya lallabawa takoma gida.
___ wasu irin sambatu tayi nan take tanzarzar yabayyana yana wannan dan iskan dariya nashi mara dadinji kafin yafara magana " hafsat nadade da fada miki da ki nisanta kanki da ita gashi yanzu kinjawa kanki ina matsayin shugabanki amma kikasa bin umarni na wannan shine hukuncnki babu abinda zanmiki kije kiyi jinyar jikinki taurin kai yanzu yamiki rana ai" ya karashe maganar yana dariya me karfin gaske kafin yabace bat.






Masha Allah masoyana inata ganin ruwan comments da adduah ina godiya sosai Allah yabar kauna love you Lodi lodi 🌹🫂🥰🥰🥰🥰




via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺




Story & written by
MRS 🌹 ISHAM 🌹





Page 3️⃣7️⃣ & 3️⃣8️⃣



Haka tanzarzar yabace yabarta batare dawani taimako ba , fitowa Mansoor yayi daga bedroom dinshi rikeda shisha pot idonshi ne yasauka akan mommy dake kwance tana fitar da numfashin wahala arazane yanufeta yana " mommy meya sameki haka? Waye yamiki wannan abu?" Ahankali ta iya cemai yakaita dakinta ciccibarta yayi yakaita yana mata sannu.

_____ tana zaune agaban mirror tayi light make up tana sanye da dakakkiyar lace me tsada dinkin dogon riga fitted gown wuyanta yasha sarka da dan kunne na gold tayi kyau sosai takafa dauri , Allah Allah takeyi tagama shiryawa taje ta gaida su abba dan rana harya dan fito karfe 10:30 gama shiryawan tayi tadau gyale tasa da takalmi hill tana tafiya kamar wata me tsoron taka kasa shigowa falo tayi tanajan kofan bedroom dinta jin muryan aneesa tayi se zuba surutu takeyi mamakine yakamata wai ita wannan bata da aikinyi se makalewa mutane, karasowa falon tayi taganta tana zaune atare da Mr azaad jikinsu amanne yakwantar da kanshi ajikin kujeran dasuke zaune idonshi alumshe kamar wani me bacci dan gaba daya surutun aneesa ya isheshi, cike da neman magana taje kusa dasu tatsaya akansu tana rike kugu " ke kam aneesa wace irin mayyace mara zuciya ban rabaki da mijina ba? Kinzo da sassafe zaki hanashi hutawa to baki isaba ki tattara kibarmin part ko kuma inyi maganinki " tana magana ta jijjiga jiki kamar dagaske in anbarta da aneesa din iya dukanta zatayi . Slowly yabude idonshi akan kyakyawar fuskanta shide yagaji da lamarin fanan ciwon kai takesashi dan yalura bajin magana takeyi ba inya biye mata ze iya karyata abanza a wofi.

Sake shigewa jikin azaad aneesa tayi tana fadin " to badole inzo ba keda kwata_kwata bakya bashi kulawa baki masan yanda zakiyi da miji ba so he needs me by his side ! Kinga ni zan mishi abinda bazaki iyaba tunda haryanzu baki gama girma ba" dan zare ido fanan tayi tama rasa mezata fada mata wanda ranta zeyi mugun baci, samun kanta tayi dafadin " aneesa shiyafada miki haka ? To bari kiji jiya kwana mukayi bamuyi bacci ba gabaki daya yanzu haka agajiye nake kawai karfin hali nayi zanfita gaba daya yasa jikina se ciwo yakeyi abinki da yarinya nasan dakece goggiyar yar duniya nasan Koda wasa bazakiji kingaji ba to nina tafi se anjumanku ! Honey sugar bye" tana fadin haka kuwa tayi waje batare da jira amsar da aneesa zata miyar mata ba.
Mr azaad kam he's totally out of words lamarin fanan goge mishi hadda takeyi yarinya karama da zaro manyan maganganu kwafa yayi yana fadin " zaki dawo kisameni" ya shige bedroom dinshi yabar aneesa afalon ta cika tayi bam kamar zata fashe.

Ahankali take taka staircase din gaba dayansu sun hallara afalon daga gani abu me mahimmanci suke tattaunawa, tsugunawa tayi tagaida abba da ummi,anty Zainab dasu anty Amina gaba dayansu seda tabisu tana gaidasu, suka amsa da murmushi akan fuskansu areef ne yace " Ina kwana anty ? " Hararan wasa tawurga mishi tana " Allah ya areef banaso kabari " zeenat ma tace " anty fanan ina kwana" banza tayi da ita, dariya sukayi duka , anty shayida tace " yauwa kingama maganarki akeyi segaki nan " murmushi tayi tace " to anty gani " fawwaz ne yace " daman maganar bikinku akeyi kinga kwata_kwata baayi komai ba, so nan da 1 week ko 2 weeks zaayi event din bikin dinner ne da kamu se walima " shuru tayi tana tunanin itada zasu rabu da Mr azaad meye kuma na wani shagalin biki, tana jinsu se tsara yanda bikin ze kasance sukeyi.
Abba ne yace " Fatima gobe dukanmu zamuyi tafiya zamu tafi dubai yiwa kakansu zeenat yajiki kwana biyu bayida lafiya bazamu dade ba munso tafiya dake amma kinga ke bakida visa inmun dawo zaku tafi tare da mijinki daga yanzu zuwa lokacin komai dinki zezama ready" cike da kunya tace " to Abba Allah yakaimu" Suna haka se gashi yasauko cikin shirinshi nazuwa office yasha kyau suffarshi ta larabawa yakara fitowa, sakai yayi zefita abba yace " azaad zo nan" dawuwa yayi yazauna kusada abban .
__" yauwa namanta banfada maka ba next week inmun dawo in sha Allah zaayi event din aurenka " kaff dinsu zuba mishi ido sukayi dan sonjin mezece.
Yau tunda yatashi bayajin yin wata dogon magana ciki_ciki yace " auren waye din ake magana?" Ganin yamanna musu haukane yasa ummi cewa " son auran kai da fanan mana kuma bawai shawaranka muke nema ba! Ah ah munriga da munzartar seka fara shiri zaka iya tafiya" mikewa yayi besake ce musu komai ba dan shibawai ya iya musu bane kuma yasan insukayi magana ba canzawa zasuyi ba.



8:00pm tana zaune afalo tana kallon series din India atashan zee word me suna the promise, jikinta nasanye da guntun wando jeans boom short da wata yar ficikar riga iya cibiya batasa bra ba rabin dukiyar fulaninta awaje wandon yadámeta tam tayi donot da gashinta sosai tayi kyau kamar wata bakar balarabiya, duk da kana nan kayane amma haka taji sundame ta haka tadaure taci gaba da kallon.
___ bashi yashigo gida ba har 9:00 part dinshi yanufa hannu yakai kan handle din ze murda yaji kamar karan tv shiga yayi yahangeta tana zaune tana kallo se shan fruit takeyi batama san da shigowanshi ba, zama yayi akan kujeran dake facing dinta se anan ne taganshi " barka da dawuwa Mr azaad" bece mata kalaba yacire socks din kafarshi yafincike necktie din , tunda tagaidashi be amsa ba bata kara kallon inda yake ba .
" Ke tashi kikawo min tea " tashi tayi tashiga kitchen tahada mishi tea tadawo falo bata sameshi ba yasa tawuce bedroom dinshi nanma baya ciki ajiyewa tayi akan center table tana kokarin juyawa taga yafito daga toilet yana daure da towel akugunshi, runtse idonta tayi gam dan tunda take bata taba kallon namiji ahaka ba , karasowa wajanta yayi yasa dukka hannunshi yatallafo fuskanta
Murya anarke yace " miyasa kike rufe idonki bayan kina gaban mijinkine ! Ohhh namanta ashe yanzu lokacin dazaki bani kyakyawar kulawa ne oyah Start" gabanta ne taji yana duka da karfi tuna abinda tamusu da safe shine yanzu yake dauko mata maganar, dasauri tajuya da niyar tafiya fincikota yayi tafado akan faffadar kirjinshi dayake dauke da kwantaccen gashi jikinshi gashi ajike da ruwan dayayi wanka gashin kanshi se diga yakeyi mannata yayi da jikinshi hannunshi daya narike da waist dinta.
Wani kalan kunyarshine yarufeta tarasa yazatayi tabar dakin. Ganin haryanzu taki bude idanunta ne yasashi sake matseta ajikinshi ba shiri tabude ido,
Kallon fuskanshi tayi taga kalan kallon dayake mata nan take tasunkuyar dakai kasa dan bazata juri kallon kwayar idonshi ba , sa hannu yayi ya dauketa kamar yar baby besauketa a ko inaba sekan bed dinshi . kokarin tashi takeyi yasa hannu yamaida ita yamata rumfa kwanciya yayi ajikinta yasake mata nauyinshi duka nan take tafara nishin wahala dan jitayi kamar wanda aka dorawa buhun cement ajiki tureshi takeyi amma ko motsawa beyiba zatayi magana yadaura yatsanshi a libs dinta " shhhh don't say a word ! Kikace jiya bamuyi bacci ba saboda kinbani hakkina? Tom bari inbaki yanzu tunda haka kikeso , aibansan kinaso ba da tun ranar da aka kawoki gidan nan nabaki " fanan ido yarena fata inbanda danasani babu abinda takeyi nan take hawaye yafara wanke mata fuska dan talura Mr azaad babu wasa alamarinshi. Slowly yafara zame mata rigan jikinta harya kawoshi zuwa cikinta sa hannunta duka biyu tayi tarufe kirjinta tana kuka " please Mr azaad don't do this to me" dede kunnenta yafurta " I will! abinda kikeso kenan tunda har kika iyayin shela na gajiyar dake bari ayi na gaskiyan karki damu it won't be hurt" daduk karfinta take dukan kirjinshi tana kuka da rokonshi daya kyaleta bazata karaba.
Hade bakinsu yayi waje daya yafara bata hot kiss harda na mugunta na cizon libs dinta da karfi sosai take kuka tana tureshi amma ko motsawa bayayi seda yatabbatar da ta mugun galabaita kafin yadakata yadago yakalleta yana wannan killer smile din nashi dayake kara mishi kyau, shafa libs dinta yakeyi da yayi jajir yadan kumbura dan bakar wahalar dayasha yace " tom yanzu saura inbaki hakkinki ko?" Hawaye na gangarowa daga idonta tace " kayiwa Allah daya halicceka Mr azaad kayi hakuri kabarni" watsa mata harara yayi yace " stupid girl bakince ke mara kunya ba naso yau inga karshen inda rashin kunyan zetsaya yarinya tunbaki tafasa ba kina kokarin konewa harkinsan kicewa wata mijinki ya gajiyar dake saboda taji haushi ko? " Girgiza kai tayi alamar ah ah matse libs din yayi seda tayi kara" ni kurmane dazaki girgizamin kai kokuma ke kurma ce? common open your mouth and talk joo" cikin muryan kuka tace " ah ah " kwafa yayi " I warned you several times amma naga kamar kwata_kwata taurin kanki yahanaki saurarata to muzuba nidake agidan nan kedajin dadi kuma se randa narubuta miki sakinki as from today you're my maid duk wani aikace_aikacen part din nan ke zaki dingayi inkuma ba hakaba " ya kyasta yatsunshi afuskanta, yatashi daga jikinta kifa kanta tayi akan pillow tana kuka daga baya ta tashi tashige bedroom dinta ahaka tacigaba da kuka daga baya bacci yasaceta.


Karfe 5:00am tana kwance tana bacci yana tsaye akanta hannunshi rike da karamin bucket cike da ruwa ahannunshi dagawa yayi ya kwarara mata daga sama har kasa afirgice ta tashi tana salati four eyes sukayi " kitashi aibakiga ta bacci ba kiyi sallah kisameni a bedroom dina" to kawai tace mishi ta tashi tacire bedsheet din da suka jike da ruwa takai toilet ta tasasu a drying machine itama tayi wanka tayi alwala tacanza kaya.

Bayan ta idar da sallah tanufi bedroom dinshi samunshi tayi yana zaune yana pressing din system idonshi sanye da farin glass daga gani wani aiki yakeyi me mahimmanci muryanta ahankali tace " Mr azaad gani" batare da yakalli inda takeba yace kishiga kiwanke toilet dina da jikin toilet din sannan akwai kaya acikin washing machine kifito dasu ki wanke su tass inkin gama kuma banason inga dirty ko kwallin zarrah acikin part din nan and try to finish it before 9" batace komai ba tashiga toilet din tabude washing machine ganin tulin kaya aciki kuma dukkansu wankakkune agoge wasuma baa taba sasu ba sunfi set 50 haka tafito dasu tafara wankewa tuntanayi ta dadin rai hartaji gaba daya tagaji bayanta har rikewa yakeyi. Ba ita tagama komai ba se wajajen 11:30am ko ina tayi kall dashi jiri take gani saboda gajiyan datayi ga yunwa bataci komai ba.
Lallabawa tayi tashiga kitchen tadafa indomie da tea tagama ci kenan tadan mike akan kujera har baccin wahala yafara daukanta yadawo tsayawa yayi akanta yana binta da eyes fridge yaje yadauko bottle water yabude yazuba mata afuska dasauri ta mike ganin shine tafashe da kuka " shhhhh yimin shuru dukanki nayi ko zaginki nayi kitashi yanzu muje " yafadin haka yayi gaba babu yanda ta iya haka tabi bayanshi wata kofa taga yashiga bata taba sanin akwai wani bedroom aciki ba seyau shiga ciki sukayi. Sake baki tayi ganin wani room and falon ne aciki sede alamu yanuna kamar yadade duk yayi mugun kura sosai wanda ko mutane uku ne sesunsha wahala kafin sugama gyarawa , tana cikin wannan tunanin taji yace " oya ki gyara side din nan dan zuwa gobe nan zandawo " fita yayi yabarta aciki tunani tafarayi shin ta ina zata fara gyara nan ,neman tsintsiya tayi tashare ko Ina sannan tafara mopping haka tabirkice kamar ba itaba babu abinda yake tsayar da ita se sallah.
Har karfe 9 nadare bata gama ba. Hango jakadiya abashiyya nayi da khairatyyy suna tsaye duk wani movement dinta suna wajan gabaki daya ransu abace yanzu sarauniyarsu ake aizabtarwa haka . Khairatyyy tace " shugaba meze hana mudauki mataki akanshi " girgiza kai abashiyya tayi tace " ah ah khairatyyy wannan bangaren rayuwar sarauniya ne shidin mijinta ne mukuma babu ruwanmu da shiga tsakaninsu, domin tsakanin mata da miji se Allah amma abu daya ne nasani shine zeyi matukar dana sani arayuwarshi seyaji yatsani kanshi jizeyi komai na duniya bayamai dadi"

Yinin yau curr su ummi basuji dúriyan fanan ba harsun fara tunanin ko wani abune yasameta , fitowan Mr azaad zasuje masallaci ne yasa suka tambayeshi lafiya kuwa fanan shuru sece musu yayi tana nan lafiya kawai yau batajin fitowane zeenat ne tace " to bari inje intayata hira" mugun kallo yawatsa mata yace koda wasa kar wanda yashigamin part yayi gaba abinshi.

Shigowa yayi bedroom dinta yasamu bata nan side din dayace tagyara yashiga anan yasameta akwance akan tiles ta dukun kune waje daya tana baccin wahala duk tagama aikin dayasata sa hannu yayi yadauketa yanufi bedroom dinshi da ita ajiyeta agan bed tashi tayi tana murza ido kallon ta yakeyi sosai can yace " bace min da gani " atsorace tabar dakin nashi dan ita yanzu tafarajin tsoronshi , batare data cire kayan jikinta ba ta fada toilet tasakarwa kanta shower warm water seda tadau 30mint kafin tafito daure da towel ajikinta duk tagaji batare data shirya cikin sleeping dress ba takwanta dakyar ta iyayin adduah tasamu tayi bacci, haka takwanta batare dataci komai ba.


Yau tun 5:00 ta tashi tafara nafila kafin aka kira asuba tanajin motsinshi lokacin daya tafi masallaci, yau ko komawa bacci batayi ba tafara aikace_aikace koda yadawo yasameta tanayi bece mata komai ba yashiga bedroom dinshi yakwanta , haka tasha aiki se 8:30 tagama komai tahada breakfast taci sannan tashiga tayi wanka tasa riga da wando tazura hijab dinta sadaf_sadaf take tafiya tanason taje gunsu ummi suyi sallama dantasan tsaff zece ze hanata fita tunda yanzu yasata agaba, kamar daga sama taji daddadar muryanshi yana fadin " karki yarda kifita a part din nan kijira tukun " ko waigowa batayi ba haka bata koma tazauna ba fitowa yayi yana sanye da farar jallabiya yabude suka fita.
Kowa ya hallara suka dai kawai ake jira sufito jinsu shuru ne yasa ummi tacewa zeenat taje ta kirasu kila basu tashi bane har zeenat tafara tafiya se gasu nan sun sauko sunkuyawa tayi tagaidasu, suka amsa suna tambayarta ko lafiya jiya bata fito ba satan kallon Mr azaad tayi ganin yakafeta da ido yanason yaji mezatace yasa tace " ummi jiyan ne nadan tashi bana wani jin dadi sosai shine Mr azaad yasamomin magani" sannu suka dinga

1 Comments On NI DA PATIENT DINA book 2
avatar
aisha-9-6-3

11 months ago

Reply

I like this book

Please Login or Register in order to submit comment