Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

batace musu komai ba ta tadawo main falo tazauna ganin hakane yasa suma suka fito . abu me aikice ta sanar da ummi angama shirya komai a dinning " to kutashi dukkanku food is ready ko " mikewa sukayi dukansu suka zauna akayi serving dinsu fried rice da kaji se farfesu , masa da Miyan kifi. Yaseer ne yafara gamawa yamike yakoma falo yana kiran layin azaad seda yamishi almost 5miss called kafin yadaga " haba ango wannan wani irin iskancine akawo maka amarya kawani fita kayi sauri kadawo" yana jiran abinda azaad din zece yaji dogon tsaki Mr azaad yaja yakashe wayar dariya yayi dan yasan zaa rina bayan sun gamacin abincin suka dawo falo wayar suhaima ce tafara ringing dubawa tayi taga number yaya inlaw ne murmushi tayi kafin tamike tafita a falon taje compound tadaga wayar " hello yaya Ina wuni " adayan bangaren aka amsa " lafiya da nayi fushi dake bansan ya akayi nakiraki ba babynmu ne takeson jin muryanki shine mimi tace inkiraki " dariya yabata wai babynsu ce takeson jin muryanta kai ya amir sarkin zolaya " uhmmm kuda kuka manta dani ma aini yakamata inyi fushi bakuba" tafada tana murguda baki " yanzu bawa mimin " amir mikawa matarshi mimi yayi sunkusan 10mint suna waya kafin sukayi sallama yakashe, juyawa tayi zata koma ciki kawai taga mutum atsaye abayanta yaharde da hannunshi tadan tsorata ganin fawwaz ne tace " laaaaah ya fawwaz wannan aisekasa inzura da gudu " murmushin gefen baki yayi yace " hmmm ai hankalina ne yakasa kwanciya shisa nabiyoki a tunanina ma wanine yakeson min kwace ashe yayanmu ne " daure mata kai yayi da kalamansa " bangane mekake nufi ba ya fawwaz" daga mata giran sama yayi kafin yace " lokacin da wayarki tayi ringing ganin irin murmushin dakikayi yasa zuciyata tsinkewa dan nadauka wani ne yakesonmin kafa agun matar danake buri tazama uwa ga yayana " sosai tazaro kyawawan idonta tana kallonshi wura mata iska yayi a ido kauda kanta gefe tayi hannunshi yasa yakarbi wayarta yayi dialing din number sa ya mika mata murmushi yayi yace" naji kinyi shuru kifada mini namiki ne ko ko banyi ba ?" Dariya tayi jin yanda yake magana da wakar dan musa tafiya sukeyi suna yar hira harsukazo falo ja tayi tatsaya tace" ya fawwaz kabarni infara shiga " gyada mata kai yayi tashige tazauna sedaga baya yashigo yazauna akan kujera dake facing dinta daga sun hada ido se yasakar mata murmushi itama tamayar mishi babu wanda yalura dasu se fanan wani irin dariya tafashe dashi wanda rabon datayi irinshi tun ranar agida itada suhaima seyau kuma dariya takeyi ba qaqqautawa harda rike ciki zuba mata ido sukayi suna kallon iKon Allah suna mamakin meye yasata irin wannan dariya haka sedata kai kusan 5mint kafin ta dakata ganin suna kallonta ne yasa taboye fuskanta ajikin ummi tana yar dariya basu kawo komai aransu ba su a tunaninsu wani abun ne yasata farin ciki amma yawan da dariyar yayine yabasu tsoro .
___ Abba ne yace " fanan daga yanzu kidaukemu kamar iyayenki bawai surakanu ba domin ke yace awajanmu matsayinki daya da zeenat so dan haka kisake jikinki nanma gida ne kinji ko ?" Fitowa tayi daga jikin ummi tace " in sha Allah abba nagode " mikewa anty firdausi tayi tace " kutashi muyi shirin tafiya " tashi sukayi suna musu sallama fanan jitayi kamar tayi kuka rungumeta suhaima da amira sukayi atare kasa_kasa amira tace " to besty azage akula da miji abashi kulawa atarerayeshi kamar kwai nan da 5 months muzo sunan yan hudu" tsaki fanan taja " kefa iskancin kine yake hadani dake kifita a eyes dina tam" kafin tajuya kan suhaima " kekuma dama kin iya kallon love haka inyaah " amira de batasan akanme take magana ba suhaima kuwa hararanta tayi tace " to ina ruwanki yarsa ido kawai " jarare jikinta fanan tayi tana " uhmm jeki can da yawar soyayyarki ni karkimin rashin kunya" cewar fanan ahaka suka dingayi harsuka je bakin motar suka shiga daga musu hannu tayi tana musu bye_ bye tafiya sukayi suma suka koma ciki Abba kam already yawuce part dinshi su fawwaz ma haka anty shayida da anty zainab kuwa ko wacce mijinta yaturo driver sun maidasu gida, yazamana daga ummi, zeenat,anty amina se fanan din ne afalon ummi ce tayi magana " fanan kitashi kije ki kwanta kihuta kinga gobe kunada program zaku fita karfe 10:00am nasafe ! Sannan a part dinku duk wani abinda zaku bukata akwai aciki kayan girki kidingawa mijinki girki koda bazeci ba kimishi de yasan kinyi kinji ko " "to ummi" cewar fanan dake mikewa zata wuce part dinsu seda safe tamusu tashige atare ummi da zeenat suka sauke ajiyar zuciya dan yau burinsu na fanan tazama sirka agidan yacika sunyi farin ciki sosai.
Ita atunaninta yadawo gida dan dazun taji su fawwaz sunce baya nan dakinta tawuce cire rigar tayi tadaura towel tashiga toilet tayi wanka da ruwan zafi tayi alwala tafito goge jikinta tayi da towel din tashafa turare masu dadin kamshi wardrobe din tabude kayan baccin tazubawa ido ganinsu da yawa wani me riga da wando black silky tadauko tasaka tasa hula akanta takwanta taja blanket tana adduah bacci aikuwa bacci barawo yayi awun gaba da ita.

Se karfe kusan 12:00 nadare tukun yadawo gidan kowa ya kwanta yashiga part dinshi toilet yafada yayi wanka yafito towel daure a kugunshi shafa lotion yayi ajikinshi yafeshe jikinshi da perfume kayan bacci yasa ajikinshi yakwanta.


Washe gari 5:30am

Tana zaune akan sallaya ta idar da sallah tana azkar se karfe 6:30 ta tashi takoma kan gado takwanta dan bacci be isheta ba, se karfe 10 ta farka ta shiga toilet tayi brush tawanke fuskanta fitowa tayi tana shafa cikinta dake kukan yunwa falo tafito jikinta nasanye da kayan baccin dube_dube takeyi tana neman kitchen wata kofa tagani akusa da inda dinning area yake wajan taje tabude kofar katon kitchen ne irin nayan gayu komai akwai aciki kamar wanda tundama mace na ciki tunani tafarayi to dama Mr azaad na girkine karewa kitchen din kallo takeyi yaburgeta sosai wani kofa tagani tabudeshi store ne kayan abinci ne aciki iri_iri kwalin idomie tabude tadauki guda daya se kwai biyu da gesher tafito standing gas takunna tadaura tukunya akai tahada indomie ta jollof da gesher kwai din ta dafashi daban kamshine kawai yaketashi a kitchen din tana gamawa tazuye a plate tasa cokali tafito falo tazauna kure A.C tayi dan tasamu yahuce dawuri seda tafaraci ne talura da basket din dake kan dinning ashe ankawo musu abinci cigaba tayi da cin indomie ta se shishitan yaji takeyi sekace wani ne yasata sawa dayawa ahaka tacinye abincinta , fitowa yayi daga bedroom dinshi babu riga ajikinshi dagashi se short din three quarter kokadan beyi tunanin zesameta ba bema kawo apart dinshi zaa ajiyetaba zama yayi akan kujera yana amsa kiran Faisal dake sanar dashi komai ready su kadai kawai BBC news suke jira okay kawai yace jin muryanshine yasa tadago tace " Ina kwana Mr azaad" kamar bejitaba yacigaba da danna wayarsa tabe baki tayi aranta tana fadin " kaika sani karka amsa din " haka suka zauna a falon kamar wasu kurame can yamike haryakai bakin kofar bedroom dinshi yace " kishirya yanzu zamu tafi and banason jira" yashige bin bayanshi da harara tayi tana kwaikwayan yanda yayi magana sannan tamike tayi wanka tafito da atamfa super wax me touches din pitch da sky blue riga da skirt dinki yayi kyau sosai duk pattern yasha stones ajiyesu tayi tadauko gyale da takalmi half cover se jaka masu matukar tsada zama tayi agaban mirror tadanyi light make up tayi kyau sosai ta gyara gashinta tayi packing dinshi se kyalli yake kayan tasaka sun zauna mata ajiki kamar dama sundauki measurements dinta das das da ita dawuwa gaban mirror tayi da dankwali ahannunta dauri tayi mekyau me shigen ture kaga tsiya wanda akesa mishi kwali aciki amma ita batasa komai ba tayi abunta daurin yazauna sosai akanta akasan daurin kuma gashinta ne wanda tayi packing dinshi feshe jikinta tayi da daddadan turare masu masifar kamshi, gyale tayafa yanada dan girma yarufe mata jiki tadau jakanta tasa takalmi tayi masifar kyau dan karamin bakin nan seyayi kamar tasa janbaki kasancewar libs dinta ja ne gashi tasa mishi libs gloss se shinny yake. fitowa falon tayi tazauna zaman jiranshi seda takusa 10mint tana jiranshi se gashi yafito, yana sanye da tsadadden yard milk color half jumfa gashin nan yasha gyara yayi matukar kyau , wuceta yayi abinshi bece mata ci kanki ba ganin haka yasa tamike tabi bayanshi suka gangaro main falo su Abba da ummi da kowa suna zaune afalon jin takun takalminsu ne yasasu juyawa suna kallonsu bakaramin burgesu sukayi ba sunyi making perfect match zama Mr azaad yayi, tsungunawa fanan tayi har kasa tana gaishesu suka amsa fuska asake zama tayi akusa da zeenat " kai anty fanan wallahi kinyi kyau sosai dama wai kin iya kwalliya shine bakyayi wallahi baki ganki bane " hararanta tayi jin takirata da anty tace " bansan wani iyayi dazaki wani cemin anty tam " batagama magana ba taji areef nafadin " antynmu Ina kwana " waro ido tayi cikeda mamaki qin amsawa tayi kara nanatawa yayi " anty ina kwana" kwabe fuska tayi da shagwaba tace " Abba kanajin su ko kace musu subari banaso " takarashe maganar kamar zatayi kuka dariya sukasa banda azaad daya wurga mata harara , Abba yace " to ai fatima dole suce miki anty tunda yanzu ke matar yayarsu ce " Kara daure fuska azaad yayi jin abinda abba yace karsusa ta renashi mikewa yayi yace " ke tashi mutafi " yayi gaba tashi tayi tace " to muntafi semun dawo " Allah kiyaye hanya suka musu tabi bayanshi ganin motoci har guda goma sunyi shirin fitane ga securities da Sojoji suna fitowa suka dinga kwasar gaisuwa ganin ogansu da wata macen dake jikin hotunansu da aka yada yasa suka fara tunani bude musu motar tsakiya akayi yashiga tsayawa tayi bata shiga ba dagowa yayi yace " dallah malama kishigo mutafi karki batamin lokaci mana" bashiri tashige tazauna nesa dashi fita motocin sukayi agidan suka hau kan titi.

Tunda suka fara tafiya babu wanda yakula dan uwanshi harsuka iso bude musu motar akayi suka fito kusan atare shiga ciki sukayi manager jikinshi na rawa yamusu sannu da zuwa yakaisu har inda zaayi hira dasu.


Photographer's masu shooting videos duk sun hallara suna jiran afara saboda direct live zaayi kowa zega shirin alokacin da akeyinsa , wanda ze gabatar da shirin ne yace start nan da nan suka fara shooting.

Gyara zama yayi yafara da " assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhum jamaa kamar yanda kuka sani nine naku me suna jamilu abubakar wanda yau nazo muku da manyan baki wato bakowa bane bace wannan shahararren dan kasuwan damuka dade muna jiran opportunity samun hira dashi Allah beyi ba seyau wanda ayanzu ake zargin kancewa shidin womanizer ne ahausance manemin mata zakuji komai de daga bakinshi wannan kuma itace Fatima muhammad Umar mahaddaciyar Al qur'ani wacce ta taciyo kyaututuka da dama saboda kwazonta itama zamuji komai daga bakinta "

Seda azaad yayi kusan 5min fuska adaure kamar wanda akawa wani abu cike da izza yace " kamar yanda kuka sani am azaad muhammad mainasara sauran labarina kuma beshafe ku ba dan bawan nan ne yakawo niba nazo ne akan qazafin dakukamin nida wife dina kuka bata mana suna saboda kawai biyan bukatarku saboda kawai kusamu kudi kuke watsa abinda ze taba rayuwar mutane batare da bincike ko wani abu ba acikin abinda befi 20 mint ba kuka bata mana suna" mamaki dauke akan fuskar jamilu yace " shin kana nufin kace mana hafeza fatima matarka ce? Amma tayaya? yaushe ? Kayi aure ba tare da sanin duniya ba Mr azaad? Zamuso Karin bayani " azaad kamar bazeyi magana ba yace " itadin matatace anyi aurenmu nida ita a lokacin da saukanta saura 1week aka bari se anyi sauka tukun nan ayi biki nasan jamaa da dama sunganni awajan walimar to bari kuji infada muku nayi shuru ne saboda wasu yan dalilai narabu daku amma ayau din nan banfito ba seda natsayar da matakin dazan dauka akanku kukuma al umman duniya wayanda basawa yan uwansu musulmai kyakyawan zato hakkinmu nakanku irin mugayen alkaba'in dakuka dinga binmu dashi ku kuka sani da Allah " bakaramin sanyi jikin duk wani wanda yake kallon gidan tv yayi ba dasu kansu BBC news seyanzu sukasan sun tabka babban kuskure .

Sallama tayi da muryanta me dadin sauraro sannan tace " Kun batamin suna dukda ni matar aure ce amma haka yayi matukar taba darajata abisa kalaman dakuka rubuta ko tsoron Allah bakuji ba kuka kirani da dadiro harda cewa wai nasha zubar da ciki innalillahi wainna ilaijiraji unnn karku manta kuma kunada yaya mata in baku dashi kuma kunada kanne mata ko kun mantane khamatu dhinu tudanu kunjefa ni ama wuyacin hali saboda bakowa bane sukasan munyi aure ba bakomai nayafe muku amma kusani inkunwa wasu sun yafe wasu fah sede ku hadu agaban Allah tunda ku kwata_kwata bakwabin yan uwanku da kyakyawan alkhari se sharri " sosai jikin jamilu yayi sanyi saboda shi yayi editing da printing din labarin. Murya asanyaye yace " to jamaa ansamu babban kuskure domin labarin nan ba gaskiya bane duk masu bukatar karin bayani ko tambaya zasu iya kiranmu awannan layin wayanmu ayanzu " aikuwa yana gama fadin haka telephone din dasuke amsa kira dashi tayi ringing dannawa yayi yadaga wanda duk maganar dazaayi acikin duniya zataji . " Assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhum sunana sheikh Sulaiman Ahmad gombe nakirane domin bada shedan ido! Aranar da malama fatima tayi sauka nida kaina naje nasamu malama fatima domin nayaba da dabi'un ta nabukaci tabani daman insamu iyayenta da maganar aure amma taban hakuri ta shaida min ita matar aure ce agaskiya musulman duniya muji tsoron Allah muguji yada karya da jita_jita kokuma sharri " jamilu ne yace" to masu gani da sauraranmu fatan kunji abinda sheikh Sulaiman Ahmad gombe yace muna gdy da shaida sheikh Allah yakara girma " yakatse kiran yaci gaba" agaskiya mun tabka kuskure...



via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
🧑‍⚕️🧑‍⚕️ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺




Story & written by
MRS 🌹 ISHAM 🌹


Page 3️⃣5️⃣ & 3️⃣6️⃣



" Batare da hujja ba munyi abinda be kamataba a madadina da tashar BBC news muna me matukar bawa Mr and Mrs azaad mainasara hakuri akan laifin da muka musu " shigowa manager da chairman sukayi suname basu hakuri akan kuskuren da akayi domin sunsan muddin Mr azaad yabar wajan nan batare daya hakuraba to kashinsu yabushe. Kafin nan da abinda be wuce 1hr ba labari yabaza duniya kota ina se sakon bada hakuri ne yake shigo TikTok, YouTube, Facebook, Twitter, Instagram, mikewa Mr azaad yayi yace " Nina gama abinda yakoni nan dan haka banda lokacin batawa " yafada yana rike hannun fanan suka fara tafiya se hotuna da video ake musu har suka fita bin bayansu masu tsaronshi sukayi suna bude musu marfin motar shiga yayi yana rike da hannunta zama tayi tana kallon fuskanshi sake hannunta yayi haka sukaci gaba zamansu kamar kurame harsuka iso gida ana bude motar tayi gaba dan sotakeyj taje tabawa su ummi labari , aharzuke ta hango aneesa ta nufota, tana isowa gurinta ta wanketa da mari ta shaketa " wallahi yau sena kasheki ko ni ko ke " kakari fanan tafara saboda shakan da aneesa tayi mata bana wasa bane cikin sauri azaad yakaraso yafisge aneesa daga jikin fanan rike wuyanta fanan tayi tana kuka mari azaad yawanka mata yana fadin " bakida hankali ne kasheta kikeson kiyine " kuka tafashe mishi dashi " baby you betrayed me nizaka yaudara kaje kayi aure a munafurce bayan anmana baiko dama kai munafiki ne bansaniba " ji yayi tabashi tausayi yasan baa kyauta mataba riko hannunta yayi yace" calm down muje ciki " wuce fanan sukayi dake tsaye tana kuka kallonta aneesa tayi tana mata gwalo, goge fuskanta tayi tashiga falo babu kowa aciki haurawa tayi part dinsu afalo tasamesu aneesa nakwance akan kafadarshi shikuma yana aiki a laptop ko kallonsu bata sakeyi ba tashiga bedroom dinta tarage kayan jikinta zuwa wata dogon riga me hannun vest mara nauyi yakamata sosai duk shape dinta yafito tasa hula fitowa falon tayi still suna zaune suna kallon labaran da akeyi akan sharrin da akamusu an wanke sunansu tare dabasu hakuri tanajin sanda Mr azaad yayi kiran waya yana cewa adakatar da su dukda batasan dawaye yake magana ba Amma tafahimci BBC news yabada umarnin adakatar . Jin haka yasa fanan tashiga matsanancin farin ciki jitayi duk bacin rai dinda take ciki ya yaye kitchen tashiga tayi jallof din macaroni da beef yasha vegetables se tashin kamshi yakeyi tadawo falon dan nesa dasu tanacin abincinta gaba daya kamshin yacika musu ciki sedataji ta koshi ta ajiye plate din gefe kasa hakuri aneesa tayi tamike tashiga kitchen din bude tukunyan da fanan tayi girki tayi kozata samu sauran macaroni babu komai aciki dan iya cikinta tadafa dawuwa falon tayi " baby yunwa nakeji kuma abinci kadan tayi basaura kace mata tamin wani kaji" shuru yamata be kulata ba sake nanata maganar tayi ganin zata dameshi ne yasa ya kalli fanan dake zaune tana kallon tv tanashan drinks hankalinta kwance yace " Meye dalilin dazesa kiyi abincin dan kadan tunda yakare seki dafa mata wani " dariyar renin hankali tayi ta kalli aneesar cike da tsiwa tace " ohhh really indafa abinci wata katuwa taci ? To ni baa kawoni gidan nan dan indafawa wata katuwar banza abinci taci ba" cike da mamaki azaad ke binta da kallo with his sexy voice yace " me aka kawo ki kiyi?" Ko ajikinta tace bautar aure da kula da miji dan haka kar wata takara cemin inmata abinci yauwa" mamakin yanda take zaro zance yakeyi yar yarinya da ita wato hartasan wani bautan aure .
Akule aneesa tace " to dakike maganar wani kinzo bautar aure nasan komai baby yafadamin dalilin auren naku kuma yanzu da sunanshi yawanku zesake ki ya aureni kinzo kina wani iyayi " magana fanan tayi azuciyarta yazama dole in koya mata hankali , fari tayi da manya_manyan idonta tadaura kafa daya kan daya, Mr azaad de da ido kawai yakebinta . Sa idonta tayi cikin na aneesa tana fadin" kalleni dakyau namiki kama da wacce zaa aura asaka? To shi saurayin naki daya fada miki hakan yafadane dan kawai yakwantar miki da hankali amma inbanda haka meye zeyi dake nifa yarinya ce me kananan shekaru shisa yakyasa yatakura, hankalinshi be kwanta ba seda yaga nazama matarshi kuma yana bani kulawa sosai ko bahaka bane honey sugar ?" Tafada tana kashewa Mr azaad ido daya, yama rasa mezece mata kullum iyayin yarinyar nan da yarintar ta karuwa yakeyi cize libs dinshi nakasa yayi.
Kuka aneesa tasa tafita da gudu zuwa part din mommy tana kudurta aniyar ganin bayan fanan domin yau ta wulakanta ta setadau mataki .
Seyanzu tafara danasanin abubuwan data fada meya kaita nema, mikewa tayi simi_simi tashige dakinta takwanta tana dariya inta tuna abinda tawa aneesa , kamar amafarki taganshi atsaye akanta tashi tayi tazauna tana narai_narai da ido dukufowa yayi, ja baya tayi, rumfa yamata da faffadar kirjinshi da hannayenshi guda biyu , kallon cikin idon juna sukeyi without a blink sa hannu yayi yazame hulan dake kanta gashinta yazubo akan bed din hannunsa yasa yadamki kan da karfinshi ihu tasa jin azaba rike hannunshi tayi da duk hannayenta biyu tana kuka dagota yayi tsaye still yana rike da gashin. dayan hannunshi yasa yamatse dan karamin bakinta yace " banason inga ina hurting din mutum amma kinja dole sena hukuntaki abinda nakeso dake stay in your limits don't try to cross it inba haka ba sekinyi dana sanin sanina! Bantaba sonki ba kuma har abada bazansoki ba dan ke yarinyace dakanta ke cike da yarinta impact ke bakima kai girman dazan yi rayuwar aure dakeba kinmin yarinya kikarewa kanki kallo dakyau reason din dayasa akayi auren nan shine saboda awanke sunanmu and komai yanzu is steady zansake ki kije kiyi rayuwarki freely kwaila kawai " duk maganar dayakeyi besaketaba yana damke da gashin kanta da kuma bakinta daya matse seda yagama magana tukun yayi wurgi da ita kan gadon yafice.
Kukanta tasha mecin rai ahaka bacci yadauketa.


" Mommy wallahi sena kasheta inbahaka ba hankalina baze taba kwanciya ba " cewar aneesa dake magana tana kuka tsaki mommy tayi tace " yanzu ke ko kunya bakiji ba kanwar bayanki zaki tsaya kina mata kuka baki kamata ba kin manta jakin duka ! Wallahi shame on you" sake fashewa tayi da kuka tazo tafada mata instead of sunemi solution tahau ta da fada lura da hakan ne yasa mommy takwantar da murya " is okay my angel karki damu yau yau din nan zandau mataki setayi danasanin abinda ta aikata miki karki kara shiga part din se gobe kinji ko angel din dadi" sake fuska tayi tana murmushi seyanzu hankalinta yakwanta jin mommy tace zatadau mataki akanta.


Har seda time din sallah yayi ta farka taje tayi sallah har time din tana tuna bakaken maganganun da Mr azaad yamata haka tazura dogon hijab dinta tayi falon ummi samun zeenat tayi afalo tana shan rufaida yogurt zama tayi tana karban roban yogurt din tafara sha sake baki zeenat tayi dan batasan da shigowarta ba tace " ikon Allah anty fanan yaushe kika shigo " tana Shan yogurt din tace mata " sanda kike kwadayi mana" dariya zeenat tayi tace" to naji ya kike ya program munganku a tv alhamdulillah komai yatafi successful yanda akeso" " hmmm kede bari kawai nikadai nasan irin farin cikin danake ciki " hira sukeyi har anty Amina tafito tasamesu kallon fuskan fanan tayi taga alamar tayi kuka kiranta tayi wajanta fanan taje tazauna waigawa tayi ga zeenat tace " to anty kwadayis kidan bamu waje zamuyi magana " tashi tayi tayi dakinta maida kallonta tayi kan fanan sannan tace " my fanan meke damunki wani abu azaad yamiki " dasauri ta girgiza mata kai alamar ah ah ta fahimmci tanason boye mata ne yasa tace " karkimin kallon sirka kidaukeni amatsayin antynki firdausi duk wata damuwarki karki boyemin dakuma tsakaninki da azaad semu samo solutions kinji" sosai hankalinta yakwanta dan dama tarasa wazata fadawa damuwarta , bata labarin tun daga dawuwarsu da shaketa da aneesa tayi har izuwa abinda Mr azaad yamata dakuma maganganu daya fada mata. Jinjina kai tayi dan tasan zaa rina kuma bakomai yasa yakula aneesa ba sedon taji haushi amma yanzu dole tadaura fanan akan hanya dazata gyarawa azaad zama dakuma ita kanta aneesa datakeson takurawa rayuwarsu.
____" kinaji abinda kikayi yau kinmin dede domin inkika sake kika kyale aneesa tsaf zata renaki sannan inason kinunawa azaad ke ba yarinya bace kamar yanda yafada shida kanshi zedawo yana baki hakuri da lallabaki ! Tunda harya ce miki kwaila yayi mukuma zamuyi iya kokarinmu dan muyi proving dinshi wrong " zare ido tayi tana kallon anty Amina kamar amafarki " yanzu Mr azaad dinne zewani lallaba mutum har yabada hakuri tabb " sosai anty Amina ta dinga bata shawarwari tayanda zatajawo hankalin Mr azaad duk da fanan tanajin kunyan wasu Abubuwa amma haka tanutsu tana sauraran anty Amina dan tadau aniyar nunawa Mr azaad ita ba yarinya bace. Farin ciki anty Amina tayi ganin fanan tadauki shawararta dakuma wayon data mata yayi tasiri dan ita tayi hakan ne da tasamu su dede ta kansu dan tasan yanda Mr

1 Comments On NI DA PATIENT DINA book 2
avatar
aisha-9-6-3

11 months ago

Reply

I like this book

Please Login or Register in order to submit comment