Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

, five 5 digit din last number ya kare da 99999 seda aka kira kusan sau uku kafin ta daga tasa akunne tayi shuru daddadar muryanshi me tafiya da Kuma ratsa mata jijiyoyin jikine taji ya sauka mata akunne yana " hello " nauyayyar ajiyar zuciya tasauke wanda yasa suka dago suka kalleta tace " assalamualaikum habiby " suhaima, zeenat,amira tsaban shakiyanci har suna hada baki wajen cewa " awwwwwwwwn ! Habiby" hade da shewa pillow fanan ta wurga musu hade da harara sannan tayi kwafa shagwabewa tayi tace " habiby ka gansu suna tsokanata ko ?" Jan numfashi yayi kamar wanda yaci yaji lokaci daya yaji ta tayar mishi da hankali idan tana mishi wannan shagwabar kawai daurewa yakeyi dan shi kadai yasan yanda yakeji katse kiran yayi , tabe baki tayi tace " Allah zanyi maganinku kafin in tafi " kiran hairah tayi ta zauna akusa da ita tadinga janta da labari dan tasamu tasaki jiki ,
Bayan 30mint har lokacin basu fito ba suna dakin suna hira gani sukayi an yaye labuyen bedroom din , Mr azaad ne tsaye ajikin kofa fuskan nan adaure tamau duk seda sukasha jinin jikinsu lokaci daya suka nutsu suka shiga taitayinsu hatta ita fanan din .
" Wato matar tawace kuke tsokana ko?" Kamar zasuyi kuka suka girgiza kai alamar ah ah watsa musu harara yayi kafin yayi kwafa inda fanan take yaje yasa hannu yadauketa cak yayi hanyar fita falo mutsu_mutsu tafara ganin abinda yake shirin aikatawa tasan akwai mutane a falon yazataji in suka gansu haka ahankali tace " habiby kayi hakuri ka saukeni kasa zan iya tafiya da kaina" ko sauraranta beyi ba suka fito falo babu kowa afalon duk sun watse mama da ummi suna daki suna hira, gauron numfashi ta sauke tana godewa Allah .

Be sauketa ako ina ba se a motar yaja suka hau kan titi , cikin nutsuwa yake driving zubawa kyawawan fuskanshi ido tayi tana kallonshi cike da so da kauna, batare da ya kalleta ba yace " baby wannan kallo haka ?" tace " to ai bana gajiya da kallon kane " cize libs dinshi nakasa yayi jiyayi magana ma kadai idan tayi kara ingizashi take bece mata komai ba ya nufi migration office barinta yayi a motar yashiga ciki after some few minutes yafito hannunshi dauke da envelope daura mata yayi akan cinya ya tada motar suka dau hanya bata ko dauki envelope din ba saboda bece mata komai ba yanda yadaurashi hakan tabarshi kallonta yayi yace " open it" sa zara_zara chocolate color yatsunta tayi ta bude passport da visa ta gani nata daduk wani abu da mutum yake bukata inzashi abroad duk akwai jujjuyasu tayi a hannunta kafin ta kalleshi tace " habiby to sukuma wannan fah tafiya zamuyi ?" driving dinshi kawai yakeyi be kalli direction dinta ba ya gyada mata kai, bata sake cewa komai ba ta maidasu ta rufe , cikin makay shawarma suka shiga yayi packing motar fita yazoyi tarike hannunshi tace " habiby nide bazaka barni nidaya anan ba " matso da kanshi yayi ya manna mata kiss a libs dinta yace " bazaki iya tafiya ba kibari inje in fito" kwabe fuska tayi tana kokarin yi mishi kuka bayanson ta tayar mishi da rigima yasa yafito yazo yabude mata itama tafito duk idon jamaa yadawo kansu se kallon akeyi saboda sun burge jamaa sosai musamman ma wayanda suka ganesu , rikota sosai yayi ajikinshi yanda bazataji zafi sosai ba intana tafiya dukda tanajin zafin ba sosai ba haka ta sake daurewa tana hada tafiyanta. makay shawarma babban joint ne a gombe yana da girma dakuma kyau sosai babu abinda babu a ciki , rike hannunta yayi suka fara tafiya har ciki wajan shopping tsayawa yayi yace ta dauki abubuwan da take bukata side din su perfumes taje ta diba masu kamshi da dadi hade da lotion's se shower gel, body spray, mouthwash, sannan takoma kan kayan kwalama ta dibe chocolate sosai da ice cream security wajan ne yariko keken kayan yatura har wajan yin bills ATM ya bada suka cire kudinsu suka hada musu komai a leda karba security yayi akasa a bayan motar suka shiga suka tafi duk tunaninta daga nan gida zasuyi setaga ya sakeyin packing a yahuza suya yafita ya karbo nama da yogurt dinsu masu matukar dadi .

Agajiye de suka dawo gida fanan duk ta gaji jira kawai takeyi taganta akan gado , bude motar yayi yadauketa cakk yama daya daga cikin securities dinsu alama da ido ya kwaso kayan cikin motar yabisu dashi har part din su direta yayi akan bed dinshi ya koma falo ya karbi ledojin ya ajiye akan kujera, cire rigar jikinshi yayi wannan hadaddiyar surar nashi ya bayyana especially his 6packs and muscles amurde suke bathroom yashiga ya sakarwa kanshi shower yafito daure da karamin towel a kugunshi se dingan ruwa yakeyi tana zaune akan gadon yanda yafita yabarta haka yasameta sede ta cire hijab din jikinta ta ajiye a gefe jin yanda ya dameta wajanta yanufa yahau kan gadon ya kwantar da kanshi akan cinyarta ya lumshe ido kamar mejin bacci sa hannunta tayi ta cusa cikin gashinshi tana yamutsawa hade da shafawa burgeta gashin yayi musamman da ruwa yajika shi se yayi wara_wara gwanin burgewa, duk abinda takeyi yana jinta beyi yunkurin mikewa ba ahankali hankali reaction dinshi yafara canzawa , rike hannunta dake kanshi yayi yadawo da hannun kan faffadar kirjinshi dake dauke da kwantaccen suma baki me laushi yakwanta luf , batayi tunanin wani abu ba tafara shafa kirjin nashi musamman inda gashin yafi yawa kasa hakuri yayi yadaura hannunshi akan dukiyar fulaninta yafara yawo dasu da sauri ta cire hannunta akirjinshi tana kokarin mikewa dan bata shiryawa hakan ba a irin wannan halin da take ciki bata manta da bakar azaban datasha jiya ba qin dagata yayi yasa hannu yamaida ita ta kwanta ya mata rumfa dede kunnenta yakawo face dinshi yace " wifey where are you going to? karki tafi ina bukatarki akusa dani" sake tsorata fanan tayi jin yanda muryanshi one time ya canza ga idonshi dasuka rine suka canza kala mutsu _ mutsu tafara mishi hade da kuka runtse ido yayi dan bayason jin kukanta har cikin ranshi yakejin hakan dagata yayi yace " am sorry wifey bawai wani abu zan miki kawai bacci zamuyi " ba ta yarda da maganarshi ba ,gani takeyi kamar ze sake mata abinda yamata jiya , yasa ta maqe kafada, dafe goshi yayi ahankali yafurta " oh my goodness" tashi tayi tafara tafiya tana bin bango taje wajan kujeran tadubo ledar naman daya siya hade da yogurt dan yunwa_yunwa tafaraji dawuwa tayi inda yake tabude ledar kamshin gashashiyar naman kaza dayasha kayan hadi ne yadaki hancinta ,cike da nutsuwa tafaraci tana hadawa da yogurt din harta koshi zuba mata ruwa yayi a glass cup yayi yabata tasha tayi hamdala ta koshi qat.
Mikewa tayi dan tanason tayi wanka , dakyar takai kanta bathroom dinshi tashiga tayi wanka tafito sanye da rigar towel fari kal samunshi tayi ya kishingida da pillow kanshi na kallon sama damuwa karara ya bayyana akan kyakyawan fuskanshi ganin yana kokarin sauke kanshi ne yasa ta dauke kanta daga gareshi tazauna a gaban mirror tashafa lotion dinshi da perfume ta shiga dressing room dinshi , dubawa takeyi ko zataga wani kana nan kayanshi dazata samu su mata dede dan qiwiyan komawa nata dakin takeji, idonta ne yasauka akan wata trolley me kyau sosai pink color burgeta yayi taji tanason ganin meye aciki durkusawa tayi tasa hannu ta bude akwatin kayan bacci ne kala kala aciki sunfi set 30 masu kyau da daukan hankalin duk wani da na miji daukan na farkon tayi ta bareshi a ledarshi , wata yalolon rigace me tsantsi da kuma raga_raga rigar transparent ne onion color tsayinshi iya guiwanta yatsaya hade yake da pant dinshi aciki shima onion color sunyi kyau sosai dauka tayi tasaka ajikinta babu abinda baa gani komai yana waje muraran harta pant din datasaka , rufe akwatin tayi tamaidashi inda yake tasa slippers tafito gaban mirror taje tasake feshe jikinta da different perfumes masu dadi dakuma sanyayyar kamshi ta gyara gashinta.
Karfin hali tayi tasamu tahau kan gadon tana ciccije libs dinta yana nan a kishingiden taje ta kwanta akan kirjinshi da har lokacin besa kayaba dagashi se towel , tun kafin ta iso inda yake kamshin turarenshi sun sanar dashi zuwanta bude sexy eyes dinshi dasuka canza kala su da kansu suke lumshewa tsabar wutar shaawar dake damunshi yazuba mata na mujiya dagowa yayi yazauna yana bin jikinta da kallo daukewa numfashinsa yayi na wasu yan dakiku ganin dressing din datayi ta matukar tafiya da duk imaninshi kallon hips dinta dake da fadi da tudu yayi yana kallonsu duka awaje gana shanunta dasuke gaisheshi , hannu yasa yazagayo dashi a kugunta yakai kanshi kan wuyanta yana shakar kamshin jikinta dake sake birkitashi , fanan duk a tsorace take . kamar zeyi kuka yace " baby please I need you karki cemin ah ah" dukda yabata tausayi amma bazatayi gangancin barinshi ba muryanta na rawa tace " Mr azaad akwai stitches ajikina fah " tunawa yayi da anmata dinki yasa jikinshi mutuwa janta yayi ajikinshi suka kwanta yaja musu blanket yana manne da ita yanata tabe_tabe bata hanashi ba.


Su ummi basu tashi ankara da fanan bata gidan ba se bayan isha tukun nan ,anzo zasuci abinci suka ga duk sunfito mama ce ta tambayi hairah " Ina antynki " amsa mata hairah tayi da " bata nan dazun yaya yazo yadauketa " dake bayan fitar Mr azaad da fanan seta tambayesu waye shi sukace mata ai mijinta ne, jinjina rashin kunya irin na Mr azaad ummi da anty amina sukayi itakam ma anty amina duk tsoronta daya kar Mr azaad yace ze kusanci fanan da dinki ajikinta Allah_Allah takeyi sugama cin abinci su koma gida kafin me afkuwa ta afku. se wajajen 9:00 su ya Usman,ya al ameen, fawwaz, areef suka dawo gida tare da hafiz da yaji sauki sosai suna sallama hairah ta mike da gudu taje ta rungumeshi tana tsallen murna ganin yayanta jikinshi yayi sauki zama sukayi shida ita a kujera daya baba ma yana falon , kasa hafiz ya durkusa yana musu godiya sosai na taimakonshi da kanwarshi da sukayi murmushi kawai sukayi suna yabawa da hankalin yaran baba ne yace " hafiz tunda baku da kowa zaku zauna atare damu kunzama yayanmu da yardan Allah! kanwarka zata zauna a gidan nan zan maida ita makaranta! Kai kuma dazun kafin azaad yabar asibitin yamin magana kancewa tunda ni nadauki hairah shikuma yadaukeka zaka koma gidansu da zama ze mayar dakai makaranta duk sanda kakeso zakazo kaga kanwarka haka itama sanda ba makaranta zatazo ta ganka, kun zama jininmu yanzu in sha Allah bazaku sake kukan maraici ba kusaki jikinku munzama daya" tsabar farin ciki hafiz da hairah har hawaye sukeyi basuyi tunanin akwai irin wayan nan mutanen a doron duniya ba dan duk inda sukaje neman taimako sede abisu da kyara da tsangwama.

Ummi tace " bari mu gudu dare na yi hafiz mutafi ko ?" Gyada mata kai yayi ya mike shida su fawwaz rike hannun hairah yayi har waje yana ce mata " hairah kinga yanzu munsamu wayanda zasu taimakemu tsakani da Allah dukda nasan halinki bakida kiriniya da neman fada duk da haka dole insake fada miki kinji banda rashin kunya dukda shima ba halinki bane kimusu biyayya kamar appu da amma Allah yajikansu karki zama me manta halacci " ya karisa magana yana shafa kanta gyada mishi kai tayi tace " in sha Allah yaya zanyi yanda kace " ummi dake bayansu basu sani ba tajiyo duk abinda suke fada tayi murmushi tasakejin yaran sun kwanta mata arai.

Sallama suka musu suka tafi hairah se bye-bye takeyiwa yayanta hafiz , rike hannunta suhaima tayi zasu koma ciki yar gyaran murya ya usman yayi yama suhaima alama da ido tashiga ciki tagane abinda yake nufi , yasa tasaki hannun hairah tashiga ciki tabarsu a compound din gidan su biyu , kallonshi tayi da manyan idanunta tace " laaah ya usman kaine ?" Yace " eh khai.... "Sekuma yacanza tunawa da yayi ba khairaty bace yace " hairah yayanta nine zo kitayani hira " zama sukayi akan plastic chairs dasuke cikin compound din, haka yadinga janta da labari harta sake itama tadinga zuba mishi hira nan yagane itama gwanar surutuce gashi ko magana tayi se angane akwai tsantsan yarinta a tattare da ita haka yabiye mata suka dinga hira har karfe goma yace mata taje ta kwanta dare yayi gobe zasu karasa tashi tayi tashige dakinsu shima yashiga daki ranshi fess komai normal yakeji yana tafiya mishi yasan yau zeyi bacci me dadi.


Karfe 2:30 nadare fanan tafarka sakamakon Kiran sunanta da taji akeyi cikin sigan bada umarni dakuma girmamawa tashi tayi taga Mr azaad na baccinshi hankali kwance sauka tayi akan gadon tabude kofar ahankali yanda bazeji karan ba fitowa falo tayi tana sanye da kayan baccin jikinta falon ne yasauya daga falo zuwa wani irin hadaddiyar daji me dauke da shuke_shuke gwanin ban shaawa ga kamshi hade da dusan kankara sama kuma sararin samaniya ne , batayi mamakin hakan ba ji tayi an kara kiran sunan nata acan saman sararin samaniya yasa tabude hannayenta duka biyu tafiya tafarayi akan iska tana firewa sama inda sautin muryan ke fitowa seda ta kusa isowa wajan tukun kayan jikin yacanza zuwa doguwar riga fara sol komai din jikinta seda yacanza yazama hadadde hatta gashin kanta style dinshi canzawa yayi takoma sarauniya sak, isa wajan tayi taga bakowa babu alamar mutum ko tsuntsu kallon kudu da yamma tayi can ta hango jaaazana shi kadanshi akan iska yana daukar ido hular mulkin da yake ran kowa daga mutane har aljanu kowa burinshi ya mallakeshi , shine yayi wannan kira ga fanan wajanshi taje ta tsaya tanajin sanyi na ratsata , jitayi magana na fitowa daga jikin jaaazana " sarauniya fadima shin kinsan da lokacin ki yakusa karewa a duniyar bil adama? lokaci kalilan ne yarage miki da ki fara gabatar da abinda yakamata"



To semun hadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy πŸ‘πŸ™.



Masu comment Allah yasaka muku da aljanna ina godiya sosai matuka.

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

πŸ§‘β€βš•οΈπŸ§‘β€βš•οΈ NIDA PATIENT DINA 🩺🩺



Story & written by ✍️
MRS 🌹 ISHAM 🌹

πŸ””πŸ“š JARUMAI WRITERS ASSOCIATION πŸ“š

( J. W. A πŸ“šπŸ“šπŸ“š)






PAGE 5️⃣3️⃣



Shuru kawai sarauniya fanan tayi tana sauraran jaaazana har ya gama fadin abinda ze fada ya narke ya shige cikin jikinta , bangarewa tayi idonta suka fifito sosai hasken su da sheki yakara fitowa kulle idonta tayi ta sake budewa ta ganta a tsakiyar falonsu ajiyar zuciya tayi tanufi bedroom din Mr azaad slowly ta bude kofar dan gudun kar ya tashi yahau tambayarta ina taje shigowa tayi tamaida kofar ta rufe , juyawa tayi zata je ta kwanta kawai taga Mr azaad a tsaye a gabanta idonshi akanta kallon tuhuma yake binta dashi kafin yace" wifey daga ina?" tace nadanje kitchen na sha ruwa ne" ta karishe maganar tana inda_inda " karya be dace dake ba domin baki iyashi ba karki fara ! sannan naga ga can bottle water akan center table ko me sanyi kikaje sha?" cewar Mr azaad da haryanzu ya tsura mata mayun idonshi da yasa takasa nutsuwa duk ta birkice se sosa wuya takeyi bazata iya sanar dashi lokacin tafiyarta ya qarato ba dan batason ya shiga wani halin damuwa, canza maganar tayi da " habiby kazo muje mu kwanta bacci nakeji" be sake dauko mata wata tambayar ba ganin bataso taki bashi amsa se kauce_kauce takeyi yasa yakoma kan bed yakwanta hawa gadon tayi itama ta shige jikinshi rungumota yayi kamar wani ze kwace mishi ita.

Washe gari 5:20am


Tashinta yayi daga bacci " baby time for prayer" tashi tayi tazauna tana mika da salati bin kirjinta yayi da kallo, kallon setin da yake kallo tayi taga yazubawa kirjinta ido kashe mata ido yayi kafin yafita zuwa masallaci . Sallah itama tayi yau alhamdulillah ta tashi tana iya takawa ba laifi kuma baya mata zafi tana zaune akan sallayar tana azkar shuru_shuru Mr azaad be dawo daga masallaci ba har 7 tashi tayi ta share bedroom dinshi tagyara kan bed, tayi mopping ta wanke toilet komawa falo tayi tagyara ko ina hade da bedroom dinta ta kunna turaren wuta ko ina yayi fess yana kamshi kitchen tashiga nan ma ta gyara ko ina sannan tafara tunanin me yakamata ta musu na breakfast. Cikin store tashiga ta dauko doya madedeci tasa ruwa acikin bowl tadauki wuka ta fareshi tsaff ta yankashi acikin bowl dake dauke da ruwa , kunna gas tayi ta daura ruwa acikin tukunya yafara zafi tasa doyan da gishiri ta rufe , bayan doyan yadafu tasashi a basket yadan sha iska eggs ta dibo guda shida ta fasa acikin separate kwano tasa magi,albasa
se ginger kadan saboda karni kwai ta kadashi yakadΓΊ,daura frypan tayi akan gas din tasa oil tasa albasa sannan tafara sa doyan acikin kwai tana soyawa harta gama daga ido ma kadai mutum ya kalla yasan zeyi dadi ba dan kadan ba, cabinet taje ta bude tadauko dinner set food flask masu kyau dukda sabbine seda tasake wankesu tagogesu da dry towel tazuye soyeyen doya da kwan aciki tarufe ta ajiye agefe. Fridge din ingredients (kayan miya) ta bude takwaso abubuwan bukata saboda miyar kwai takesonyi kamar su attarugu,albasa,Karas, green pepper , green beans ta gyarasu, tayi blanding attarugu . fasa eggs din datasan zeyi mata miyan tayi tayanka albasa acikin kwan ta ajiye agefe , ruwan zafi ta dibo tafasheshe a heater tasaka karas din da green beans da baking powder kadan rufe bowl din tayi ta barshi few minutes, budewa tayi ta tsameshi, sake wankewa tayi sannan shidinma ta ajiye agefe ,
Daura tukunya tayi akan gas tasa butter ta narka shi tasa albasa yasoyu sama sama . attarugun datayi blanding dinshi tasa aciki da curry, thyme, tasa ruwan zafi kadan aciki tajuyashi tarufe da marfi , can tabude tasa kwanta data fasa acikin tukunyan tarage wutan tasake rufe tukunyan tabarshi nawasu mintuna tasa mishi karas da green beans tajuya ahankali tabarshi ruwan yatsotse ta tabbatar da yayi ta kashe gas din tajuye miyar kwan acikin food flask ta kaisu dinning ta jera tadawo tadafa tea dayaji kayan kamshi shima takaishi dinning, wanke duk wani abinda tayi amfani dashi tayi tanufi bedroom dinta tacire kayan jikinta tadaura towel tashiga bathroom tashiga jacuzzi dake dauke da zuwan zafi ta gasa jikinta sosai sannan tayi wanka tafito tana tsane jikin da dogon gashinta da tsayinshi yakai kugunta zama tayi agaban mirror tadauki hand dryer ta busar da gashin ta shafa mayukan gashi ta tajeshi tayi packing da ribbon fari, lotion tashafa tayi light make up ta fesa turare kaya tadauko Pakistan riga da wandonshi fari da pink hade da gyalenshi ,wandon pencil ne rigar kuma yanada tsayi yakawo mata har guiwa gefe da gefenshi a tsage yanada dogon pencil hand yasha stones, yafa gyalen tayi akanta da bashida wani girma sosai tasa farin plate shoe, tayi kyau sosai kasancewarta chocolate color,se color kayan suka karbeta white and pink sake feshe jikinta tayi da body spray tafito falo ta tsaya tana jiranshi ta bawa kofar falon baya, shigowa yayi shakar kamshin dayaji yake tashi apart din hade dana jikinta yayi ahankali ya hada jikinshi da nata ya rungumeta ta baya ya saukar da kanshi awuyanta yana shakar kamshin turarenta hannunshi duka biyu ya daura akan kugunta seda suka kai almost 5mint ahaka , rike kafadunta yayi ya juyo da ita suna facing juna , manna mata light kiss yayi a libs yace " morning kiss ! Kinyi kyau baby kullum Kara kyau kikeyi " sa hannunta tayi tazagayo dashi awuyanshi tana shafawa kadan kadan tace " morning habiby " be amsa ba kawai yamata murmushi tsayar da ita yayi yana binta da kallo from toe to head, godewa Allah yayi daya bashi mata me hankali dakuma sonshi tsakani da Allah, me tsafta kamarshi dukda akwai masu aiki a gidan amma ita take komai da kanta ta iya kula da jikinta.
( to mata gareku , kurike tsafta! kurike tsafta maza sunason mace me tsafta da tattalin kanta ,karki kasance ballagaza da bata damu da jikinta ba bare tayi tunanin gyara muhalli . Babu na mijin da bayason mace me tsafta Koda shi yakasance kazami bayida tsafta amma ke inkina da tsafta zakiga shikanshi ze rage , zekuma jidadi duk sanda yadawo gida yasamu ko Ina tsaff dakuma ke kanki kinyi wanka da kwalliya kin feshe jikinki da turare kina tashin kamshi , tsafta na daya daga cikin abinda yake kara soyayyarki azuciyar miji dan bakowa bane zeyi toleranting kazanta ba , mata da yawa aurensu ya mutu ta dalilin rashin tsafta .
To adage adinga tsafta dan faranta ran oga ,bama dan oga ba kema kanki inkina tsafta sekinfi jindadin jikinki da rayuwarki,a shigo gidanki ma aganshi tsaf ai da dadi bazakiji kunya ba . ) rike hannunshi tayi ta langwabar da kai hade da turo dan karamin bakinta me red libs tace " habiby aina ka tsaya haka inata jiranka baka dawo da wuri ba" tsurawa dan karamin red libs dinta ido yayi dake fitar da kalma daddaya kamar bata iya magana ba tsaban shagwaba, ji yayi kamar yakama libs din yata tsotsa , tallafo habarta yayi yasa idonshi cikin nata yace " am sorry baby ! na tsaya a falon ummi ne " sake turo bakin tayi takoma kamar wata teddy tace " to yanzu muje kayi wanka sekazo muyi breakfast nafara jin yunwa " ta fada tana kai hannunshi kan cikinta ,shafa shamulallen cikinta yayi dayake plate kamar batacin abinci kai hannunshi yayi kan maranta yadan shafa yace " baby yanzu baya miki zafi sosai ko" ganin yana kokarin zarcer da hannunshi kasa ne yasa tayi saurin rikewa kam tace " muje kayi wanka" dariya taso tabashi ganin lokaci daya tadan tsorata jan hannunta yayi zuwa bedroom dinshi yana " yau ke zakimin wankan " zaro ido waje tayi tafara zazzaresu gasu dama masha Allah manya_manya dasu tace " nide ah ah".

Sake hannunshi tayi yashiga toilet din, fitowa yayi daure da towel akugunshi karami kuma ahannunshi yana goge kanshi dake digar ruwa, karban towel din tayi ta goge mishi jiki zama yayi akan kujera ta shafa mishi lotion se kallonta yakeyi especially her cute face satan kallonshi tayi taga ita yake kallo. tana gama shafa mishi man tabarshi awajen tashiga dressing room dinshi tana tafiya ahankali tadauko mishi kaya kana na marasa nauyi takawo mishi tana tsaye agefenshi yasaka riga murmushin mugunta yayi kafin ya kunce towel din dake kugunshi ya fadi kasa, kara tasa tarufe idonta tazuya baya batayi tunanin ze iya hakan agabanta ba zuciyarta se bugawa yakeyi da karfi ita kadai tasan me tagani , Mr azaad kuwa se dariyar mugunta yakeyi harda dan rike ciki dan abinda yayi tsammanin haka kuwa yafaru tsoron fanan yayi yawa saka kaya yayi kafin ya rungumeta ajikinshi yanaci gaba da dariyar , kukan shagwaba tasa mishi tana dukan kirjinshi da duka hannunta rike hannayen yayi yana dariya yace " Meye abin tsoro baby ?" murguda mishi dan karamin bakinta tayi tace " nide munyi fada tam " rike kunnenshi yayi yace " afuwan wifey " make kafada tayi, daukarta yayi cak be zarce ko ina ba se a dinning table yazaunar da ita akan kujera shima yazauna, bude warmers din tayi nan take kamshin abincin yadaki hancinshi seda yarufe ido sannan yabude ya kalli abincin dake cikin kulolin seda ya hadiye yawo, burinshi kawai yakai abincin bakinshi , serving dinsu doya da kwan tayi a one plate sannan ta zuba musu lafiyayyar miyan kwan tarufe warmers din, hada musu tea tayi sannan ta ajiye mishi plate

1 Comments On NI DA PATIENT DINA book 2
avatar
aisha-9-6-3

11 months ago

Reply

I like this book

Please Login or Register in order to submit comment