Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata ‘kakkarfar ajiyar zuciya, ‘kirjinsa ya samu salama don bai ta’ba zaton zai zo ya risketa da rai ba, ya ‘dauka gawarta zaiyi arba da ita kamar yarda yake ta hasashe a cikin jirgi. Mommah idanunsa a cikin nata, duk da tana fushi dashi tayi farin cikin ganinsa cikin ‘koshin lafiya ta tabbatar yana cikin kwanciyar hankali tunda gashi har ‘yar ‘kiba yayi, ya kuma ‘kara haske akan nasa Na da duk da haskennasa disashshen haske ne, ba mai irin fau ‘dinnan bane.

Hawaye ya fara ‘kokarin kwaranyo masa a idonsa, da sassarfa ya ‘karasa wajen su ya dur’kushe a gabanta cikin wani yanayi ya dam’ki hannayenta yasa fuskarsa a ciki, sai a lokacin ya samu sukunin kwararrar da hawayensa, wanda yake nuni da zallar farin cikinsa Na riskar Mommah cikin ‘koshin lafiya. Hannayenta kawai akan bayansa ba tare da furta komai ba. zuciyarta a cunkushe tana tunano mata girman laififfukan da ya aikata mata musamman sakin Shatu da yafi tsaya mata a rai. Hajiya Mama sa’ke tayi tana kallonsu zuciyarta cike da tausayinsu duka tana addu’ar Allah ubangiji ya daidaita lamarinsu ya kawar da dukkan lamarin da yake lullu’be.
Kamar ‘kiftawar ido suka ga Mommah ta mi’ke a zafafe ta shige ‘daki ta kullo ha’de da murza key, sai sannan kukan yazo mata duk ‘kokarin da tayi Na danneshi. Imran da sauri ya bi bayanta sai dai kafin isarsa ya tarar ta datse da key. Jikinsa a salu’be ya dawo gaban Hajiya Mama ya zauna idanunusa kawai ya ke aikin murzawa. Yana duban Hajiya Maman kafin ya saki wani huci da zallar tururi ya fito daga bakinsa, ya gaishe da Hajiya Maman. Ta amsa fuskarta ba yabo ba fallasa tace “Ai ta samu sau’ki sosai ma kuwa,kwana uku da suka shige tuni muka cire rai da ita, duk da Allah yace Latakna’du min rahmatillah.” Imran yace “Alhamdulillah,amma Hajiya Mama menene musabbabin ciwon?” “Musabbabin ciwo Imran ya wuceka? Kai da dangin mahaifinka da ka biyewa kuke ‘ko’karin kai mahaifiyarka ‘kasa, saboda baka san ciwon kanka ba, Idan ta mutu wallahi kune kuke da asara ba ruwan danginka, in Banda sakarci ya za’ayi ka saki Shatu kasan ‘yar uwarka ce kuma itace za’bin Ta, amma ka zubawa idonka toka ka saketa ka bamu mamaki wallahi, kuma Alhaji Baba ma yana nan yana jiranka.” Shiru Imran yayi yana jin tsanar Shatu tana sake hauhawa a zuciyarsa, sa’banin da yake turkey da kullum yake kwana da tunaninta har yayi Al’kawarin duk ran da yazo Nigeria zai saka a mayar da aurensu, amma yanzu duk wannan soyayyar da begen ya kau, gani yake duk itace musabbabin sake samun sa’bani tsakaninsa da mahaifiyarsa, ban da haka kafin zuwan ta ‘kalau suke zaune. Ransa a ‘bace ya mi’ke yayi hanyar waje bayan ya amshi key ‘din part ‘din Hisham a wajen Hajiya Mama.

Hajiya Mama kuwa binsa tayi da kallo zuciyarta Na sake girmama ‘kiyayyar da Imran yake yiwa Shatu da ko sunanta baya son a ambata, tabbas al’amarin sai ta tashi tsaye da addu’a don alamar sihiri maigirma a tare dashi.

Mi’kewa tayi ta isa bedroom ‘din Mommah bayan tasa Yaseerah ta kai masa abinci, duk da ta san bai ci zaiyi ba.
bugu ‘daya tayi tace da Mommah “Bu’de, nice nan Addarsu.” Da sauri Mommah ta bu’de Hajiya Mama ta mayar da ‘kofar ta rufe.

A gefen Gado ta zauna, Idanunta akan Mommah da yayi jazur dashi. “Sau nawa zan gaya miki ki daina wannan fushin akan Imran? Addu’a ta kamaceshi don na gano tabbas akwai sihiri a tare dashi.” Murmushi Mommah tayi tace “Mai kika gani Hajiya Mama? Kada ki sawa kanki wannan tunanin, ke fa kike cewa mu daina beleiving da asiri.” Hajiya Mama ta girgiza Kai “Tabbas da asiri a jikin Imran, saboda yau zancen Shatu kawai nayi masa amma kamar na sanar dashi ranar mutuwarsa, ban ta’ba yarda a zuciyata Imran Zai yiwa Shatu wannan ‘kiyayyar da ba gaira ba sabab ba.” Mommah ta saki murmushi” “Hajiya Mama baki san Imran bane, tun a farkon fari ya tsani Shatu shine ma dalilin da yasa na ha’dasu aure, amma ya nuna min ban isa ba saboda yana tunanin ya fi ‘karfin Shatu da tazo daga Daji yana yi mata kallon bata waye ba. don haka ki cirewa zuciyarki wannan tunanin, ni yanzu ko Shatun ma bana son ya ha’du da ita wallahi.” Hajiya Mam cewa tayi “Allah ya kyauta” ba tare da ta amince da maganar Addarsu ba.




———————————
Ran kawu sa’idu a ‘bace yake kallon Alhaji Babba yace “lamarin mutane ya zama abin tsoro, duk jan kunnen da nayi mata sai da aka sake kwantantawa shikkenan ka barni dasu Insha Allah Na san maganinsu.” Alhaji Babba yayi masa sallama suka rabu cikin farin ciki da fahimtar Juna.




——————-
Da safe Imran ya shiga gidan, Hajiya Mama na ganinsa ta fara addu’oi a cikin ranta, Mommah kuwa fuskarta ta ha’de tana godiya ga Allah da baiga Shatu ba. Ha’kuri ya shiga bata ta ta’be baki kafin tace “Bakomai ni mai kayi min? Aure ai a hannunka yake tun da ka riga ka saketa kuma ai shikkenan Allah yasa hakan shi yafi alheri.” Jikinsa a sanyaye ya mi’ke Hajiya Mama tace “Ina zaka? Ba zaka tsaya ka karya ba?” Lumshe idanunsa yayi yace a kawo min garden can zanje...” ya nufi garden ‘din da sassarfa, gaban Mommah ya fa’di sanin Shatu a can take lesson kafin tayi ‘ko’karin hanashi har ya Tura ‘kofar da zata sada shi da Garden ‘din........ Mommah ta ware ido ita kanta Hajiya Maman bata son had’uwar Shatu da Imran a yanzu sai dai kana taka Allah Na tasa, Zahiran kuma ta Allah ce Gaskiya.....
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zan yi da ita?

36


Kiran da Alhaji Baba yayi masa ne yasa sh jiyowa, hakan yasa shi fasa shiga garden ‘din. Alhaji Baba ya yafito shi da hannu alamar yazo. Hakan ya saka shi nufar kakannasa.

A parlourn sa ya zaunar dashi, yana dubansa zuciyarsa cike da begen jikannasa. “Ka shigo jiya bamu ha’du ba? Ko da yake ni na hana Hajiya taso ka, Na san baka samu isashsshen barci ba anyi tafiyar da ba shiri, ya iyalinna ka?”
“Suna lafiya” “Masha Allah” nan ya zaunar dashi suka karya, yana ta tambayarsa cigaban da ake samu a business ‘dinsa.



Mommah da Hajiya Mama suka saki ajiyar zuciya a kusan tare, ganin Imran bai shiga ba. Mommah tace “Alhamdulillah, ke basirah maza kije kice ta koma sitroom da karatun nan.” Basira ta mi’ke ta fita isar da sa’ko, ita kanta mamakin yarda taga Shatu da ciki take yi.



——————————

Cikin masifa Kawu Sa’idu ya kalli Hajja, sannan ya dubi Manga “Tunda ya sake ta ba mahalu’kin da ya isa yasa ya dawo da ita, ai ni tun farko ban san da wata manufa kika ha’dashi aure da zainabun ba da ba zan amince ba wallahi, kuma yafiya dole ki yafe masa matu’kar ba kina so nima na janye hannuna a kanki ba, ban ta’ba ganin shashanci da zubar da mutunci ba irin naki, amma an zo ‘karshe tun da gashi iyayenta sun ‘dauketa, to ina dalili yarinya da gatan ta da komai ku saka ta a gaba har ciwon zuciya na neman hallakata, magana ta ta ‘karshe kenan tsakani na dake ki bar Manga da Iyalinsa su huta, kafin ubangiji ya nuna miki Ishara, kuma ya zama dole ki bi ni Abuja ki duba yarinyar nan ki kuma bawa iyayenta ha’kuri ke da marasa kunyar ‘ya’yanki.”
Hawaye ne ya ‘balle mata jin yace sai taje Abuja ta basu ha’kuri, gaskiya abinda ba zata iya ba kenan, a dai sake wata mafitar. “Don Allah kawu ayi ha’kuri ba sai naje ba, na amince ba zan sake shiga hurumin gidan sa ba.” A harzu’ke Kawu Sa’idu yace “Baki isa ba dole kije wallahi kuma ‘kafa ta ‘kafarki, dake da fitsararrun yaranki.” Daga haka ya mi’ke ya fice.

Yana fita Anty Amarya ta sakawa Hajja kuka “Don girman Allah Hajja ki bawa Manga ha’kuri na koma ‘daki na. Hajja hannu bibbiyu kawai ta zuba tagumi ta rasa ma mai yake mata da’di. Wai kamar ita ace zata je ta bada ha’kuri tayi ‘kwafa a fili tace “Ai kuwa Dijah idona idonki Allah ya dawo dake lafiya, ke kuma Zainab ki sha kuruminki komawa ‘dakinki kamar kin koma indai nice uwar da ta haifi Manga. Sai sannan hankalin Zainab ya kwanta, Hameedah kuwa ta cika ta tumbatsa jira kawai take ta fashe.



——————————
Kwanan Imran biyu yayi shirin komawa, Ammar Kuwa Dahda yace ya zauna ba sai yazo ba tunda yaga jikinnata da afuwa.

Ranar da zai tafin da sassafe ya shigo cikin gidan, direct kitchen ya nufa, dai-dai lokacin Shatu tana kitchen ‘din Burger take ‘ko’karin ha’dawa, don tana son ta birge Mommah. Basirah kuma na gefe tana hidimar ha’da Alkubus da miyar taushe. Ji suka yi kawai an turo ‘kofar, da sauri Shatu ta juya ta kuma ja mayafi ta rufe fuskarta da shi. Tuni ‘kamshin turarensa ya baje kitchen wanda hakan yasa bugun ‘kirjin Shatu ya tsananta. Gaisuwar Basirah ya amsa yana bu’de fridge. Har ya juya zai fita sai kuma ya waigo yana Mallon Shatu ba tare da ya san wacece ba ya dai yi mamakin rashin gaisheshi da ba tayi ba. Ta’be baki yana mur’de murfin ruwan ya kai bakinsa, da sauri ya fice.

A parlour yayi wa su Mommah sallama ta amsa masa ba yabo ba fallasa. Tana saurarar Hajiya Mama da take mi’ka masa takardu “Addu’oi ne na tsarin jiki ka dage da yinsu saboda rayuwar nan ta zama abin tsoro ba’a zama haka. Allah ya tsare ya kiyaye ka gaishe mana da iyalinnaka.” A gaggauce ya amsa mata yana ficewa da sauri don gudun rasa flight.



——————

Tunda ya tafi gaba ‘daya walwalar Shatu ta tafi gaba ‘daya, tunaninsa ya sake bun’kasa a zuciyarta, a le’kensa da tayi tana hango tsananin kyau da ya ‘kara alamar ba abinda yake damunsa sai zallar nutsuwa da kwanciyar hankali. ‘Kamshinsa yana nan ya kama gidan ra’dam tamkar lokacin ya bar gidan. Ita kanta ta amince Soyayyar Imran a jininta yake, idan ban da haka ya za’a yi ta kasa manta shi duk da butulcin da yayi mata, amma ina madadin raguwar lamarin kullum sabunta abin yake musamman yau da taji turarensa gaba ‘daya ta sake tunowa da first Night ‘dinsu, duk da soyayyar tasa bata jin zata sake komawa gidansa ko da ya bu’kaci hakan, gwara ta tsira da mutuncinta bakin da ya furta ‘ki baya ta’ba dawowa ya furta so.


———
Kashegarin ranar su Hajja da Kawu Sa’idu suka zo, Hajiya Mama tayi musu tarba ta mutunci da girmamawa, fuskarta fal da fara’a tasa aka jere musu abinci iri-iri, amma haka suka dubi abincin a wula’kance ba tare da sun ci ba, duk da kajin da suke ta zaginsu. Hajiya Mama tana fita Kawu Sa’idu yasa musu fa’dan da dole suka ‘debi abincin suka fara ci, sai dai suna ta jan addu’oi a zuciyarsu wai kar Asiri ya kama su. Kawu Sa’idu yace “Aikin banza ai shi mai yin abu shi yake tunanin wani ma irin abinsa yake. Ku dai daga ganin gidannan kun san sun fi ‘karfin su tsaya yi muku Asiri shashashai kawai da babu Allah a ranku, wani yayi min abin rashin kyautawa a gidannan yaga yarda zan yaga mutuncinsa, kun samu mutane masu mutunci da karamci ma wallahi idan banda haka da wasu ne ya za’a yi su kalleku da ko ruwan sha balle su ha’da muku wannan daular.” Tsit suka yi baka jin sautin komai sai na cokula sai kuma gashi sun cinye abinci tas ragowar shinkafa kawai suka bari. Kawu Sa’idu yace “Aikin banza kuna so kuna kaiwa kasuwa.”


Bayan gama cin abincinnasu Alhaji Baba da ‘kannensa biyu suka shigo, sannan Hajiya Mama da Mommah suka shigo. Har ‘kasa kuma Mommah ta dur’kusa ta gaida Hajja ba tare da ko canjin fuska ba balle fitsara. Jikin Hajja yayi sanyi a karo na farko ta ji kunyar Mommah ita kanta ta shaida Mommah mai ha’kuri ce, don koda wasa bata ta’ba nuna mata ba’kin hali ba, kullum a cikin yi musu uzuri take. Ba yabo ba fallasa ta shiga amsa gaisuwar tare da tambayarta jikinta. Fa’da sosai Kawu Sa’idu yayi, ya kuma bada ha’kuri tare da cewa insha Allah anyi na farko an yi na ‘karshe.” Ya saka su Hameedah ma da ‘yanuwanta suka bada ha’kuri, haka dole suka bayar ba da son ransu ba.
Sannan ya koma da yi musu nasiha sai dai gaba ‘daya ba jin nasihar suke ba, musamman Hameedah da take gani kamar an zubar mata da ajinta. Alhaji Baba yace “Ni kuma tunda ka gama ina da magana, kayi ha’kuri yaronnan ya mayar da matarsa Zainab alfarma na nema. Kawu Sa’idu yace “Sun ci albarkacinka dattijon arziki na amince masa ya mayar da ita, amma a bisa shara’di ko kallon banza ban yarda ta sake jifan Dijah dashiba balle zagi, don iya shege saboda ta Samu ‘daurin gindin uwar miji.” Alhaji Baba yace “Godiya nake, Allah ya basu zaman lafiya ya ka’de duk fitina.” Ameen suka amsa wasu a fili wasu a zuci. Taro ya watse, wasu sun kar’bi nasiha irinsu Fanna da Falmata wasu kuwa anan suka zubar tare da ‘daura ‘damarar sabon shiri.

A ranar suka juya maiduguri a jirgi. Su Mommah kuwa kashe gari ta bi Dahda suka koma. Wannan karan ma da kuka Shatu ta rabu da Mommah.



——————-
Bayan Wata biyu, lokacin cikin Shatu ya isa haihuwa, a asibiti kuma suka bada shawarar ayi mata c.s duk da dai zata iya haihuwa amma suna gudun faruwar matsala, saboda cikin yayi girma sosai ita kuma ga ‘kan’kantar shekaru.


Ana saura kwana biyu ayi mata aiki Ammar ya samu labari don haka yayi shirin tahowa daga Qatar yafi so ayi a gabansa, ji yake tamkar Shatu shi zata haifawa babyn. Siyayyar da ya jibgo kuwa har da ta banza, kaya ne akwatina kusan biyar duka unisex na haihuwar.

Cikin murna Shatu ta tare shi, da abinci kala-kala tana girmama Ammar sosai tana ganin mutuncinsa musamman ganin yarda yake ‘dawainiya da ita da aljihunsa da jikinsa.

A ranar ma Mommah ta iso tare da Basirah, bayan tayi wa Dahda ‘karyar Shatu ce ba lafiya. Ammar ne ya saka hannu a madadin uban ‘da aka shiga da Shatu theatre....
Shatu sai muce a fito lafiya..


Kuyi hakuri ba yawa yau ciwon kai nake, wallahi.
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zanyi da ita?


37

Nimcyluv ubangiji ya baki lafiya, Allah yasa kaffara. Ku saka marubuciyar Zain abeed a addu’a da bakunanku masu albarka.


Alhamdulillah nagode sosai da wa’danda suka kira ni ko text messages domin yi min fatan samun lafiya, nagode ‘kwarai da ba zarku nake taka rawa, Alhamdulillah ala kulli halin, wa astagfirullah min kulli zanbin.




Tsawon lokaci suka ‘dauka a cikin theatre Room ‘din. Kafin lokacin fitowar tasu su Mommah addu’oi kawai suke zubawa domin samun nasara.

Da sauri wata nurse ta iso wajensu, idanunta cikin na Hajiya Mama tace “Alhamdulillah, an yi aiki successfully, an ciro Baby Boy yanzu za’a fito da ita.” Gaba ‘daya wajen suka ha’da bakin fa’din “Masha Allah.” Hajiya Mama ta bu’de jakarta ta ciro ku’din da bata san adadinsu ba ta dam’kawa matar. Ita kuma ta juya da sauri ta koma dama tukwuicin take yiwa.


Juyawarta kenan, suka ga ta dawo da sauri tace “Hajjaju ashe biyu ne, tukwuicina yafi haka duk da yanzu kishiya aka zanka’do miki.” Wani tarin farin ciki ne ya wanzu a zuciyarsu, wannan karan Ammar ne ya zura hannu a aljihunsa ya ciro dalolin Amurka guda uka ya dam’kawa matar. Mommah kuwa burinta taga Shatu domin ta gama biyanta a duniyar nan ta khali’ku.



Bayan mintuna Goma aka fito da yaran, Tubarakallah shine abinda su Mommah suke cewa kawai yayin da su kayi arba da zanka’da-zanka’dan yaran tamkar ‘diyoyin larabawa. Hannu bibbiyu Mommah ta saka ta rungumesu tama manta da wata kunya balle ta tuna Hajiya Mama a wajen, zallar farin ciki ya sata shatatar hawaye cikin wani rin shau’ki take bawa yaran sumbata a kumatukan su, tana jin tsananin ‘kaunarsu na ratsa dukka sassan jikinta, fiye da lokacin da ta haifi Imran da Ammar, tabbas ta yarda da maganar malam bahaushe da yace Abin cikin ‘kwai yafi ‘kwan da’di.

Hajiya Mama kuwa sai kallon Mommah take fuskarta cike da murmushi a zuciyarta tace “Dijah dole ne kiyi farinciki ni kaina da aka haifi Imran nayi fin haka balle ke da aka yiwa biyu lokaci ‘daya, kuma tuwo na maina don kuwa Shatu ‘yar Mommah ce halak malak.

Dai-dai lokacin aka fito da Shatu a wheel bed idanunta a lumshe hawaye yana zirara ta cikin su, hannu ta mi’kawa Mommah, da sauri kuwa Mommah ta mi’kawa Ammar Babies ‘din ta nufi ‘yarta. Da ita aka tura ta har zuwa Amenity1 ‘dakin da zata huta.


Ammar farin ciki ne ya baibaye zuciyarsa, yana ayyana ko yanzu kallon Shatu take kamar ta zama tasa domin dai kuwa yau ta gama idda. Babu shamakin da zai katange shi da furta mata zahirin abinda yake zuciyarsa, da zarar sun isa gida an sallamesu, tunda Mommah ce tayi masa al’kawarin ko ranar suna za’a iya yi musu aure.

Idanunta a lumshe alamar barci yana son ‘daukarta, Mommah ta haska mata fuskokin yaran tana cewa “Shatu na bu’de idonki kiga ‘kurrati ainun. Shatu ta ware idonta tar tana kallonsu tare da girmama hikimar ubangiji ta yarda yaron yayi kama da Imran kwabo da Kwabo, ita kuma jaririyar tayi kama da ita sak kamar tayi kaki ta zubar. Cikin zuciyarta tace tabbas ‘kudirar ubangiji girma gareta ubangiji yayi muku albarka, ko a tunani ban ta’ba tunanin haihuwar biyu ba. Sai ta lumshe ido sai kuwa ga hawaye ya sake zubo mata na tsantsar farinciki da godiya da ni’imar Azza wa Jallah.


Bayan sun nutsu Hajiya Mama ta kalli Mommah “Ai sai a fara sanar da dangi haihuwar.” Mommah ta girgiza kai “Wallahi Hajiya bana son kowa ya san da haihuwar nan...” “Ai kuwa gan-gan kenan zancen banza zancen wofi a na wani dalilin zaki ce ba za’a sanar dasu ba, shikkenan sai a ‘boye ciki haihuwar ma a ‘boye, sai kace an haifi shegu to ba dani za’a yi wannan iya shegen ba. Ki ‘dau waya ki kira mijinki ki fa’da masa, sannan a gayawa duk wanda ya dace.” Cikin takaici Mommah ta shiga bin umarni Hajiya Mama don taga ta hau da yawa.


Dahda ta fara kira ta sanar dashi, kasa’ke yayi da wayar ba tare da ya iya furta komai ba. Ransa ya kai ‘kololuwar ‘baci. Jin yayi shiru yasa Mommah fa’din hello!hello! Mamaki ya kamata jin ya saki ajiyar zuciya alamar yana jinta.

A sanyaye tace “Dahda kaji kuwa mai nace?”
“Naji mana” ya amsa a ginshire
Mommah cikin sanyin jiki tace “Naji ba kace komai ba, ko ba kayi farinciki da abinda nace ba?” “Farin cikin me zanyi? Tunda ni baki mayar dani komai ba a rayuwar Aishatu, babu abinda zance sai Allah ya raya, haihuwa ai ke aka yiwa tunda ke kika san da Cikin...”
Daga haka ya kashe wayar da sauri, ran sa yana matu’kar suya duk da yayi farinciki da haihuwar amma yayi mamakin dalilin da yasa Dijah ta ‘boye masa samuwar Cikin.

Hankalin Mommah ba ‘karamin tashi yayi ba, hawaye ya fara tsere a fuskarta. Cikin tashin hankali Hajiya Mama tace “Lafiya? Ko bai yarda da ‘ya’yan na Imran bane?”

Mommah Ta ‘daga kai “Hajiya Mama, ai gwara yace bai yarda ba, akan fushin da yayi yanzu, haushi yaji bai san da cikin ba sai haihuwar yaji.....”

“Au kina nufin shima ‘boye masa cikin kika yi? Inna lillahi wa inna ilaihirraji’una Addarsu wani irin shirme kika aikata?” Kuka ta fashe dashi “Hajiya Mama idona ne ya rufe wallahi sai yanzu na gano kuskure na na san fushin Manga ba abune mai kyau ba balle naga ya hau da yawa yanzu ya zanyi?” Hajiya Mama ta ja tsaki “Ni yanzu mai zan ce miki? Sai kiyi maza ki kira Hajja ki fa’da mata haihuwar kafin ki ‘karawa kanki wani laifin, na rasa irinki Addarsu kina girma amma tunaninki baya girma.”


Mommah Ta ‘dau waya ta fara kiran Hajja, ta da’de tana kira kafin Ta ‘daga.
Kwmar bata so haka ta dinga amsa gaisuwar Mommah, zuwa lokacin da Mommahn tace “Dama kira nayi na sanar miki Shatu ta sauka.” Da rawar murya Hajja tace “Shatu kuma wata ce Shatun?”
Ran Mommah a ‘bace tace “Matar Imran nake nufi.” Hajja ta ta’be baki kafin tace “Au har kun sake mata wani aure kenan, bayan rabuewarta da Imran? To Allah ya raya, meye nawa a ciki? Da
Baki wahalar da kanki wajen gaya min ba.”
Daga haka ta kashe wayarta ta bar Mommah da waya a hannu cikin tsananin ‘kunar zuciya.

Hajiya Mama ta kalleta ta ta’be baki.. “Tsun-Tsun da ya ja ruwa dai shi ruwa kan doka ita kuma me tace miki?”
Mommah tana hawaye ta sanar mata. Hajiya Mama tsaki tayi kafin tace “Ai ba kuka za kiyi ba sai ki kirata ni nayi mata bayani, cikin Imran ne aka haife, idan kuma sunce basu yarda ba sai Na ‘kyalesu suje da halinsu. Kai ni wannan masifa ta dangin mijinki Addarsu ta fara isa ta wallahi.”

Hannu na rawa Mommah ta sake kiran Hajja. Wannan karan a zafafe Hajja Ta ‘dauka. “Wai Dijah lafiya? Kin sanar dani haihuwa nace Allah ya raya to meye Na ‘kara kira na?”

“Ba Ita bace, uwarta ce kuma kira nayi na sanar miki haihuwa dai ta jikan ki Imran ce an haifa masa ‘yan biyu sai ki sanar da Dangi.” Daga haka ta kashe wayar ranta yana hassala da ‘bacin rai da ba’kin cikin surikar Mommah, ta ayyana idan bata fito musu a mutum ba ba zasu barsu su sha’ki iskar ‘yanci ba.

Hajja kuwa gabanta ne ya shiga dukan Tara-tara tana sake jin amon sautin uwar Dijah da take sanar da ita haihuwar Imran aka yi mata. Bata yi murna sam da samuwar ‘ya’yan nan ta tsatson Shatu ba, ina ma ta jikin Shaheedha suka fito da ba mamaki rabin burinsu ya cika, yanzu kuwa ta sani Dijah aka haifawa su dole dai wannan karan ma Dijah ce ke da riba. Wa zaga gayawa wannan abin takaicin su raba ba’kin cikin tare? Hameedah ta fara kira kafin ta kira Zainab uwar Shaheeda. Gaba ‘dayansu babu wanda bai girgiza da lamarin ba don kuka kawai suka Saka zuciyarsu a hassale, burikan rashin alheri kuwa sun ci alwashin tabbatar dasu akan ‘yan biyun Shatu.


Hajiya Mama sai da zuciyarta ta huta da ‘bacin ran sannan ta danna kiran Imran, dai-dai lokacin yana wanka, sai Shaheedah ce tayi saurin ‘dauka ba tare da tayi maganaba taji Hajiya Mama tace “Albishirinka Imrana! Matar ‘ki ta haifa maka ‘yan biyu mace da namiji.” Gaban Shaheedah yayi wani mummunan fa’duwa, tana ji Hajiya Mama tana fa’din hello! Hello! Shaheedah tayi saurin datse kiran.

Kafin wani kiran ya shigo Shaheedah tayi saurin rubuta text kamar haka.


Naji da’di da haihuwar da tayi Allah ya raya su, sai dai ba zan ‘boye muku ba nayi ba’kin ciki da suka fito daga jikin Shatu har yau ina kan baka na. Yara idan na samu lokaci zan zo na gansu idan kuma ban samu ba ku saka musu duk sunan da kuka ga dama fatan alheri.” Daga d’anku Imran.


Da sauri ta danna send ta kuma yi deleting, tare da bin contacts tayi blocking duk wata number da ta danganci family ba ta so ko ka’dan ya samu labarin haihuwar nan. Kafin ta gama ta ji’ke da gumi sharkaf. Hawaye ya fara bin idanunta, sautin amon muryar Hajiya Mama kuwa bai bar kunnuwanta sun zauna sa’kat ba.


Hajiya Mama ta duba wayar taga dai tabbas yayi receiving, to me zai saka shi yin shiru, “Bai yi farin ciki da haihuwar ba ko? Na san za’a rina.” Direct Hajiya Mama ta kalli Mommah tabbas ta samo mata amsar tambayar ta Imran kam baiyi farin ciki da labarin ba, asalima ba mamaki tu’kukin zuciya ne ya saka shi yin tsit da bakinsa.

Bata sake ‘ko’karin kiransa ba taji message ya shigo wayar, da sauri ta kai idanunta kan message ‘din kafin kace kwabo Hajiya Mama ta fara zurarar da hawaye ta kwarmin idanunta, lamarin da ya girgiza zuciyar Mommah ta tabbatar ba alheri a cikin sa’kon da ya shigo cikin wayar yanzu. Da sauri ta

1 Comments On ME ZANYI DA ITA
avatar
hafsat-bello

12 months ago

Reply

Complete

Please Login or Register in order to submit comment