Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ayi ba su haihu, zai zubar mata da cikin tunda bai wuce 3months ba tablet kawai zai bata, cikin zai fice. Maganin tsarin iyali kuwa zai d’orata akan methoe d’in da zaiyi dai-dai da tsarin jikinta, har zuwa sanda zasu bu’kaci haihuwar, idan ma bata son d’aukar ciki da haihuwa zasu iya yi mata dashen kwalba ko a samu wata macen a dasa mata cikin ta haihu ta yarda halittarta ba zata canja ba, tunda bata so. Hakan yayiwa Shaheedah sosai ta kuma raya a ranta idan time d’in yayi abinda zata yi kenan.



———————-

Doctors sosai suke ‘ko’karin ceto ran Mommah, duk da hankalinsu suma a tashe yake don har zuwa lokacin numfahsinta gaba d’aya ya d’auke sunyi-sunyi ya’ki ya dawo.

Dahda hankalinsa a tashe yake zirga-zirga yake kawai bakin emergency d’in zuwa lokacin da
Yaga fitowar Doctor d’in daga d’akin. Yanayin yarda yaga fuskar Doctor d’in yasa zuciyarsa matu’kar bugawa da ‘karfi.....

ME ZANYI DA ITA?


34


Dahda yayi saurin dafe ‘kirjinsa yana ambaton addu’oin da duk suka zo bakinsa, a zahirin gaskiya shi kansa bai san abinda bakinsa yake furtawa ba.
Har zuwa sanda likitan ya iso wajensa. Ya dubeshi kafin yace sai dai kuyi ha’kuri mun yi ‘ko’karin ganin ta dawo hayyacinta, sai dai still she is unconscious, amma dai muna saka rai za’a samu nasara insha Allah. Dahda ya saki wata wawuyar ajiyar zuciya, ji yake a rayuwarsa bai ta’ba samun kyakykyawan labarin da ya zarce wannan ba. Alhamdulillah ya furta a hankali har yana sakin d’an guntun murmushi yace “Doctor Allah ya baku nasara, ni kuma nayi al’kawarin yi muku kwaskwarimar asibitin nan cikinsa da bai. Amma Doctor kana ganin meye musabbabin ciwon nan?” Doctor yace “Gaskiya ba zan ‘boye maka ba,musabbabinsa ‘bacin raine mai tsananin gaske da ya cunkushe zuciyarta ya hanata functioning yarda ya kamata.” Dahda yace “Na san za’a rina, Dijah da na sani ban amince da zuwanki bikinnan ba, amma wallahi sunyi na farko sunyi na ‘karshe yau zan nuna musu bad side d’ina da za suyi mamaki, in dai na tabbatar su d’inne silar ciwon Dijah.” Duka wannan zancen Dahda a zuciyarsa yake yinsa, sam bai san ma Doctor d’in tuni ya wuce da sauri ba ya koma ‘dakin da Mommah take dama abu yazo ‘dauka.
Basirah ya kalla ransa a ‘bace ya shiga rattabo mata tambayoyi, tamkar dai ‘dan jarida.
Basirah kuwa bata ‘boye masa ba, ta bashi labarin zahirin abinda ta sani. Dahda ransa ya shiga ‘kunci da tunanin anya Hajja tana sonsa kuwa? Tabbas da tana sonsa, da ta so farin cikinsa Dijah, su ba su san Dijah zai iya fad’a kansa tsaye itace rayuwarsa ba. Uwa-Uwa ce dole ya ‘daga mata ‘kafa, amma Hameedah kam tabbas yau zata san waye shi, zai je mata a zahirinsa na Ahmad ba Mangan Hajja da suka sani ba.



———————

Hajiya Mama hankalinta a tashe, ta shiga kiran wayar Manga, bayan ta gwada ta Mommah sau shurin masa’ki ana sanar mata is switch off. Bugu biyu ta ci nasarar Mangan ya ‘dau wayar. Bayan gasiheta cikin girmamawa, ta tambayeshi isarsu lafiya sannan ta d’ora da tambayar Dijah. “Na kira Addar tasu ya fi sau nawa bana samunta, Allah dai yasa lafiya?” Manga ya saki ajiyar zuciya Uwa kenan, ita ce mafi kusanci da zuciyar ‘ya’yanta, gashi dai har taji a jikinta Dijan ba lallai ta zama tana lafiya ba. “Bakomai Hajiya Mama, sai dai tana bu’katar addu’a don tana kwance anyi admitting d’inta a hospital, amma dai Alhamdulillah cikin hukuncin ubangiji da sauki.” Maimakon ta shiga ru’dani kamar yarda Manga ya yi hasashe sai yaji tace “Ubangiji Allah ya bata lafiya, yasa kaffara ne, zuwa gobe idan yanayin jikinnata ba afuwa insha Allah zan biyo flight, a kuma cigaba da addu’a ba’a ja da hukuncin ubangiji, cuta da mutuwa duka lamarin ubangiji ne, shi ya saukar da cuta ya kuma samar da maganinta.” Manga ya saki ajiyar zuciya yana gasgata ‘karfin Imani na surikar tasa a zuciyarsa, shi yake ganin girmanta a ko da yaushe. A hankali yace “Nagode Hajiya Mama, idan ta farka zan ha’daku a wayar.” “Allah ya farkar da ita lafiya yasa muji alheri. Allah yayi muku albarka gaba ‘daya.” “Ameen” Manga ya furta. Yana disconnecting wayar.



Sai da ta kashe wayar sannan ta dubi Shatu da duk nutsuwarta ta tattara ta akan Hajiya Maman tana jiran ‘karin bayani. “Ki kwantar da hankalinki, Mommah ba mutuwa tayi ba, tana dai kwance bata da lafiya, mafarkinki kuma insha Allah ba zai zama gaskiya ba.” Shatu hawayene ya sake zubo mata gaba ‘daya hankalinta yafi ‘dazu tashi tunda taji Mommah ba lafiya hankalinta ba zai ta’ba kwanciya ba har sai Mommah ta samu lafiya.
Hajiya Mama cikin zafi ta katseta “Bana son sakarci kin ji ko? Menene abin kuka wa yace miki a yanzu kukanki take bu’kata? Idan kika cigaba da yi min kuka tafiyata zanyi wajenta Na barki, dama dalilinki zan zauna ban tafi ba sai Na ji yarda ta kaya gobe tukunna.
Kuma ki tashi ki je ki nemi abinci ki ci, kafin kisa mu wani tashin hakalin, ayi haihuwar guzuma ‘ya kwance uwa kwance.”




——————————-

Tablet ‘din abortion ‘din da ta sha, bai tashi yi mata aiki ba sai cikin dare. A mugun razane ta farka hannunta dam’ke da mararta da take jin tamkar zata dare. Cikin tashin hankali ta fara dukansa tana kiran sunansa. Shima a ‘dimauce
ya farka yana duban yarda take mur’kususu. “Imran help please!” Ta fad’a da ‘karaji, yayi saurin mi’kewa yana tayar da ita, ganin shegiyar rigar barcin da take jikinta ya sashi sauri zaunar da ita, ta mi’ke da sauri don ta ma kasa zaman, shi kuwa ‘ko’kari yake ya suturce mata jikinta, ganin duk ta ru’de ya sa shi zira mata hijabi kawai ya sunkuceta cak a guje suka fita compound ‘din gidan.


An sha gwagwarmaya sosai a asibitin kafin cikin ya fita, sannan aka yi mata wankin ciki aka bata hospital Gown tasa, don rigarta tayi kaca-kaca da jini.

Tana kwance akan gadon ya shiga ‘dakin, idanunsa akanta, yana mamakin yarda ta zabge lokaci ‘daya, sai ga shi yau dai yaga zallar muninta, don bai ta’ba ganinta ba makeup ba sai sau ‘daya shima bata kai haka lalalcewa ba.” Ya zauna a gefenta, yana kallon asalin gashinta, ashe wanda da yake gani duk gashin doki ne, sai yau yaga nata na ainahi wanda ba zai fi nasa da kad’an ba. Ya dai ta’be baki yana zama a gefe yace “Ya jikin?” Cikin kunyar kanta da yanayin da ya sameta yanzun na bayyanar ainahin halittarta ta shiga kau da kai. “Mu tafi gida Habibi wallahi ina son hutawa.” Ya girgiza kai “sun ce ba yau ba, ba ma wannan ba za suyi miki planning d’in da kike so sunce a tambayeki za’bin wanda kike so.” Zura masa ido tayi kafin a zuciyarta tace “Ina? Ai wallahi gida zan tafi ba zan zauna ka dinga ‘kare min kallo ba a haka har sai ka hango muni na.” Murya a sar’ke tace “planning daga baya ai sai muzo ayi ni nafi son su saka min inplan.” Ya ta’be bakinsa. Ta lura sosai da wani irin kallo da yake jifanta dashi, abinda yake dake ‘daga mata hankali.




——————————————-

Cikin Iko da izzar khali’ku, Mommah ta farka, idanunta akan dandazon likitocin da suke tsaye a kanta su kusan goma. Tana ganin sanda suka fara fa’din Alhamdulillah, suna mamakin yarda suka samu nasara haka, don da har sun cire rai. Ni kuwa nace Allah ai maji ro’kon bawa ne Hajiya Mama da Shatu da duk wani da yake da kyakkyawar ala’ka da Mommah ranar baiyi barci ba, addu’a suka kwana suna yiwa Mommah da fatan samun lafiya. Tabbas naga tasirin addua da girman ubangiji.

Bayan an gama kimtsata, sannan suka tura ta zuwa ‘dakin da zata huta. Sai lokacin Manga da Basirah suka san ta farka. Da sauri Manga ya ‘karasa wajen idanunsa cikin na Mommah da take sakar masa kyakkyawan murmushi, wanda kana ganinsa ka san na tsagwaron ‘karfin hali ne. Kawai likitoci da malaman jinya sai gani su kayi Manga ya dur’kushe ya kai goshinsa ‘kasa yayi sujjada. Gaba ‘daya wurin sun gasgata da girman soyayyar Manga da Matarsa. Dariya kawai ake masa, musamman ganin yarda yake hawaye hannayensa a sama ya mi’ka godiyarsa ga Jalla wa Azza.




A Amenity aka ajiyeta, hannayenta cikin na mijinta, nurses suka zo zasu ‘da gata, da sauri ya tsayar dasu da kansa ya zaunar da ita ya jinginar da ita a jikinsa, yana shafa bayanta. Ita kuwa tayi lamo a jikinsa cikin shau’ki da tsananin son Mijinta. Suna fita Basirah itama Ta bisu bayan ya mi’ka mata key d’in gidansa na maiduguri “Kije ki yiyo break-fast, sannan ki ha’do mata kayan da zata bu’kata.” A kunyace ta amshi key ‘din ganin yarda ya rungume Mommah da tsam tamkar wani zai ‘kwace masa ita. Suna fita ya ra’da mata a kunnenta “I love you Dija na, tabbas da wani abu ya sameki, ban san ya rayuwata zata kasance ba, dole nayi azimi uku na godiya ga rabbil izzah.” Murmushi tayi tana wasa da fingers ‘dinsa, shi kuma ya ciro waya yana kiran layin Hajiya Mama. Bugu ‘daya ta ‘dauka alamar dama a ‘kage take ya kira ta. Ba tare da yayi magana ba ya kangawa Mommah wayar a kunne, cikin kasalalliyar muryar ta tace “Assalamu Alaikum.” Hajiya Mama bata san sanda murmushi ya su’buce mata ba tace “Alhamdulillah ala ni’imatihi tatummussalihati Addarsu ya jikinnaki?” Mommah tayi murmushi cikin kasalalliyar murya tace “Alhamdulillah, wallahi naji sau’ki Mama, ina Shatu?” Hajiya Mama ta mi’kawa Shatu wayar da take jin tamkar ta fisge. Tana sawa a kunne cikin dariya tace “Mommah kin warke?” Dariya tayi tace “Insha Allah Shatu, Allah yasa dai baki saka damuwa a ranki ba kin san...” sai kuma tayi saurin katse maganar ganin idanun Dahda a kanta. Ta ‘karasa da “komai na Allah ne.” Shatu tace “To Mommah na har naji da’di Allah ya baki lafiya idan Hajiya Mama zasu taho anjima zan biyosu.” Da sauri Mommah tace “A’a kada ma ki fara, kin manta abinda nace miki?” Kamar tayi kuka taji Mommah tace “Mi’kawa Hajiya Mama wayar, tana bata Shatu ta fice tana hawaye ita haka kawai dalilin wani ciki a hanata ganin Mommah, cikin jin haushi ta kaiwa cikin duka “ladan janyowa da kai ka hanani ganin uwata, da ‘katon kanka kamar na Babanka.” Sai kuma ta ri’ke baki Oh kuji shashanci na ko a ina naga kanna sa?” Ta saki murmushi kawai tana shigewa kitchen jin zaburar da cikin yayi “Acici na san yunwa yake ji, ko kuma don na masa ‘dan wannan dukan ne, yaro baka sha duka ba sai kazo duniya tukun in rama duk abinda ubanka yayi min a kanka.”



————

Tana gani su Hajiya Mama suka tafi, ita kuma aka barta da Iya shugabar ma’aikatan cikin gidan, Haushi ne ya kama Shatu ta le’ka ta windown motar tace “kuma wallahi Hajiya Mama kafin ki dawo sai na shanye duka kayan za’kin gidannan ba dai kin hanani ba.” Hajiya Mama ta ware ido kafin tace “Au ta’bargazar da zakiyi kenan! To na san maganinki muje cikin gidan.” Shatu ya wuce tana tura ciki, da har mamaki girman cikin yake bawa Hajiya Mama kamar ba cikin fari ba, yayi girma sosai ga Shatun ta sake bud’ewa. Hajiya Mama tace “Allah ya raba lafiya.” Sai da ta kwashe kaf kayan za’kin gidan tas, ta kuma kira masu aiki ta basu dokar kada wanda yaba Shatu kayan za’ki, sannan ta tafi. Alhaji Babba Babnsu Mommahn da zasu tafi tare sai dariya yake mata ita da Shatun da take ta sake tunzira Hajiya Maman. Kuka ta zauna ta dinga yi a parlourn kamar yarinya sai watsi take da throw pillow d’in parlourn. Masu aiki sai dariya suke mata suna fad’in SHATU DANGER kamar yarda suka ji Hisham yana gaya mata.




Isar su Airport ‘din ke da wuya suka tari taxi suka nufi asibitn bayan sun gayawa drivern sunan Hospital ‘din.

Dahda ne ya fito harabar Hospital ‘din bayan sun sanar da isowarsu ta cikin waya.


Sun tarar jikin nata da sau’ki, sai dai har yanzu numfashinta bai koma normal ba, tana yi tana hutawa. Hajiya Mama da Alhaji Baba sun tausayawa ‘diyar tasu sosai, musamman ganin duk juriyarta an wayi gari zuciyarta ta kasa, dama duk cikin ‘ya’yansu ta fi kowa ha’kuri. Alhaji Baba ya dubi Manga bayan sun fita yace “ina son ganin Doctors d’in nata domin naji ainahin abinda yake damunta, idan kuma ba matsala zan fitar da ita waje ko egypt haka ko Germany.” Dahda ya girgiza kai “ Bakomai Alhaji Baba amma kamar hakan nauyi nane kuma ko baka fa’da ba nayi niyyar aikata hakan. Sannan matsalar dangina ce musabbabin wannan ciwo nata ba zan ‘boye maka ba.” Nan ya shiga bawa Alhaji Baba labari.

Kafin a gama bashi labarin gaba ‘daya ransa ya ‘baci cikin wani yanayi yace “Ashe har yanzu jahilcin nan ba zai kau daga zuciyar malam bahaushe ba, me ye laifin yarinyar da ta auri ‘danki ko ‘dan uwanki? Sannan kuma mai yake jawo wannan muguwar tsanar da gaba ta dangin miji? Da suke tsangwamar mutum bai ji ba bai gani ba a nawa tunanin jahilci ne da hassada, da kuma jayayya da lamarin ubangiji, haka ne mana kina ganin Allah bai iya ba da ya bawa ‘danki mata wance, ko kuma bai iya ba da ya bawa ‘dan uwanki mata wance, a wannan zamaninfa ba dama aga mace tana zama da mijinta lafiya sai ace ai ta mallakeshi ta asirceshi alhalin ba a san mizanin ha’kurinta akan shi mijin ba, ya kamata mutene su farka a daina jayayya da hukuncin ubangiji. Sannan kayi ha’kuri Manga an zo ga’bar da ya kamata ‘yan uwanka su san Dijah tana da gata, sannan karamci da kawaici na mahaifiyarta yasa nake ‘dauke kai nake ha’kura kamar yarda taso idan banda haka da tuni na nunawa danginka ina son yarinyata, don duk cikin ‘ya’yana ba na biyunta a biyayya, zan ‘dauke Dijah zuwa gida na har sai ta samu lafiya sannan kuma sai maza daga zuri’arku sun zo an zauna, don bana fata na wayi gari ace zuciyar Dijah ta buga dalilin kyara da tsangwamar danginka. Ba kuma don komai zanyi haka ba sai don kanku kai da Dijan su sakar muku mara su barku ku sha’kata ina dalili shekara da shekaru ayi tayin abu kamar cin ‘kwan makauniya.” Manga shiru yayi ba don zuciyarsa ta amince a tafi masa da Dijah ba sai don
Baya son jayayya da surikinsa dattijon arziki, da duk abinda ake bai ta’ba magana ba sai yanzu da tura ta kai bango. Alhaji Baba ya dafa shi yana murmushi yace “kada ka damu ba rabaka zanyi da Dijah ba, asali ma sashe guda zan baku a gidana kafin mu ga abinda hali zaiyi. Sannan kuma ka gayawa su Imran bata da lafiya?” Dahda ya girgiza kai, Alhaji Baba yace “Hakan bai dace ba kayi ‘ko’karin sanar dasu su zo su dubata, ko bakomai uwa-uwa ce, kuma ita kanta zata so ta gansu yanzu. Allah yayi muku albarka gaba ‘daya.” Ameen manga yace, hankalinsa ko yanzu ya kwanta jin sashe guda zai basu da Dijah.


Basu bar gurin ba sai da kuwa Dahda ya kira Ammar ya sanar dashi, cikin tashin hankali Ammar yace yana nan tafe ko zuwa dare idan ya samu jirgi. Ya kira Imran ya gaya masa Imran sak yayi zuciyarsa Na bugu yace “Please don’t hide the truth ka gaya min idan Mommah mutuwa Tayi? Na shiga uku ya zanyi...” cikin tsawa Dahda yace “idan mutuwar ma tayi kai kana da asara ne ba dai ka za’bi farincikin wasu ba fiye da Na mahaifiyarka. To Na baka 24hours duk abinda kake kazo ka ganta ba ta da lafiya kuma umarni Na Baka.” Daga haka ya yanke kiran ya bar Imran da waya a hannu hawaye Na bin ‘kuncinsa zuciyarsa Na wani irin bugu da ‘karfin gaske tamkar Zara bud’e ‘kirjin ta fito. Da azama ya mi’ke yana kallon Shaheedah da take kwance a gadon asibiti ya ‘dau car key ‘dinsa tare da furta “Nigeria is calling......! Shaheeda ta waro ido tana kallonsa.




(Ku fito mu tattauna, shin me yake kawo ‘kiyayyar dangin miji da matar ‘dan uwansu? Me yake kawo rashin jituwa tsakanin uwar miji da surikarta? Kowa dai ya san abubuwan da suke yawan faruwa kenan a duniyar mu ta yanzu. Mecece Mafita? Sannan laifin wanene?”)



Jikar Nashe ‘yar mutan makwarari mai ta’kama da ikon Rabbi. Sai naji daga gareku!
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zanyi Da ita?


35


Cikin ‘bacin rai ta kamo hannunsa, idanunta cikin nasa kafin ta furta “Haba Habibi yanzu Nigeria zaka tafi? Ka bari na samu sau’ki mana sai mu tafi tare, wai shin mai ma ake yi a Nigerian?” Zame hannunsa yayi kafin yace “Zuwa ta Nigeria ba shi zai hanaki samun lafiya ba, Mommah ce ba lafiya kuma Dahda yayi min umarnin lallai na tafi. Ko da ma baiyi min ba ya zama tilas naje na ga jikin Mommah.” Har ya kai ‘kofa ya jiyo yace “zan sanar da grace tazo ta zauna dake.” Yana fita ta saki ajiyar zuciya, ‘kirjinta yana matu’kar suya da saboda tsananin ‘bacin rai. Da sauri ta lalibi numberr Anty Amarya ta shiga danna mata kira ba ji ba gani.

‘Daga wayar ke da wuya, Shaheeeda ta sa mata kuka “Ki taimakeni Anty, wallahi kamar komai ya warware ina hango tsanata a idanun Imran, duk da bai furta ba ina jin tsoro Anty. Yanzu ma fa Nigeria zai taho wai Mommah ba lafiya.” Anty ya ri’ke kanta, ga shi time ‘din tana cikin dangin su, ana ta sha’anin biki ba damar tayi wani abin. “Kiyi ha’kuri, zan san abin yi, ba dai Nigeria zai zo ba Allah ya kawo shi lafiya.” Shaheedah ta kashe wayar ranta a ‘bace don ba haka Ta so ta ji ba, so tayi Antyn ta san yarda aka yi ta hanashi zuwa Nigerian gaba ‘daya.



—————-
Bayan fitar Dahda daga hospital ‘din direct Family House ‘dinsu ya tafi ransa a ‘bace matu’ka, dama rashin mai zama da Mommah ya hana shi zuwa yayi musu maganar.


Tun daga corridor ‘din sashen Hajiya yake jiyo ihunsu da shewarsu, yana jiyo Anty Amarya tana cewa “Ai cewa yayi bata da lafiya, shi yasa bai zo ba tun jiya.”
Hameedah tayi zumbur tace “Shegiya ina ma mutuwa tayi muka huta da gayyar tsiya.” Hajja tace “Wallahi kuwa, wannan masifa har ina? Ni na rasa yarda zanyi na datse wannan auren, amma kam na tsani yarinyar nan.” Zuciyarsa ce ta sake dugunzuma kamar mai? A zafafe ya danna ‘kofar ‘dakin da ‘karfin gaske,da yasa su saurin ‘dagowa suna kallonsa. Gaba ‘daya suka firgita har Hajja, musamman ganin yarda idanunsa suka ka’da su kayi jazur, ya kalli Zainab sai kuma ya mayar da kallonsa kan ‘yan uwansa mata, “Duk abinda kuke fa’da ina jinku, a yau kuma na sake tabbatar da al’amarin tsanarku da Dijah mai girma ne, ba tare da sanin wani laifin Dijah tayi muku ba, laifinta ‘daya da ta aureni take tattalina da nuna min soyayya, ku kuma abinda ba kwa so kenan kun fi son ku ganni da macen da zata dinga ‘daga min hankali, don haka ayau ba sai gobe ba zan tabbatar muku mahaifiyata kawai nake shakka, kuma ita ka’daice wacce ba zan iya rabuwa da ita ba, kun saka mata a gaba gata can a gadon asibiti zuciya ta cunkushe da ‘bacin rai, ku ko kunyar yaranta ba kwa ji? To daga yau na yanke ala’kata daku matu’kar ba zaku zauna da matata ‘kalau ba, ke kuma zainab kije na sakeki saki ‘daya.” Gaba ‘daya wajen ihu aka saka da salati, Zainab kuwa cikin tashin hankali take kallon Hajja tace.” Hajja please kice wani abu mana, kina ji yace ya sake ni.” Cikin takaici Hajja tace “Ince mai Zainab? Ina da mutunci ne a idonsa? Kina jin irin maganganun da yake fa’da a gaba na saboda baya gani na da mutunci, zuciyar Manga gaba ‘daya an canja ta, ni kuma yarda ya rabu da ‘yan uwansa akan Dijah ya kuma sake ki, ina tabbatar masa nima na zare hannuna daga lamarinsa, yaje dangin Dijah su zame masa uwa da uba. Na sallama musu shi wallahi.” Hawaye ne taf a Idonta, don lamarin Manga ya kere tunaninta. Cikin wata irin karayar zuciya Manga ya zube idanunsa cikin na Hajja ji yake tamkar yasa hannu aka yayi ta ihu, ba tare da yayi magana ba ya juya ya fice, da sauri tamkar tashin iska.




———————
A ranar aka sallami Mommah, cikin hukuncin ubangiji jikinnata da sau’ki sosai. Fargabar ta ‘daya komawa Abuja da aka ce zata yi bata so ta koma saboda bata son a san Shatunta na da juna biyu.

A ranar kuwa suka bi Flight zuwa Abuja, bayan Hajja ta sanar da ita ba matsala, suna da c.c.t.v camera yanzu a gidan, suna ganin mai shiga da fita a gidan duk wanda yazo zata saka Shatun Ta shige bedroom. Hakanne ya kwantar da hankalin Mommah, ita ma kam wannan ciwon ya razana ta kuma yanzu tana bu’katar a kar’bar mata ha’kkinta bata son ta rasa rayuwarta a garin kawaicin ta na banza.




Tun safe Shatu ta shiga gyaran gidan, bayan Hajiya Mama ta sanar da ita da Mommah za’a taho, tsananin murna yasa ta fara shiryawa Mommahn girkuna masu da’di burinta Mommahnta ta san a yanzu itama ta fara zama ‘kwararriya a ‘bangaren Girki-Girke na mu na gargajiya da na ‘kasashen ‘ketare. Mandi Rice tayi mata, sai chines Rice aka kuma Gasa mata kaji Gashin larabawan Oman, sannan aka yi mata Gizdodo, da kunun aya da Dinger drink sun kuwa yi da’di sosai, ‘bangaren snacks kuwa had’addiyar pizza tayi mata da fish roll don ta san tana matu’kar sonsu sosai. Ta gyare mata ‘daki tsaf, inda ta saba sauka sam Shatu yau ko nauyin cikinta bata ji burinta ta kyautatawa Mommahnta.



——————————


‘Karfe 6:00 jirginsu yayi landing, a Nnamdi azikwe International airport, kamar ha’din baki dai-dai lokacin da jirgin su Imran yayi landing kenan, tsakaninsu mintuna ‘kalilan ne. Sai dai basu had’u ba don su Mommah sun riga shi fita saboda nasu jirgin na gida ne.

Wayar Dahda ya shiga kira don ya gaya masa isowarsa Abuja da safe kuma zai biyo jirgin Kano. Dahdan ya sanar dashi Suna Abuja suma a yanzu hakan gidan su Mommahn. Gaban Imran ya fa’di, addu’a ya dinga yi Allah kada ya tabbatar da Hasashensa ace Mommah mutuwa tayi, idan banda haka mai zai dawo da ita Abuja.

Gwiwoyinsa a salu’be ya samu taxi don tafiya gidansu Mommahn da yake unguwar Gwarinfa. Zuciyarsa cike da fargaba.


—————

Tunda su Mommah suka isa take bin Shatu da kallo, ganin yarda take ta hidima da ita ko nauyin jikinta bata ji, ga cikin yayi mata wani turtsetse, sai jansa take yi, kuma Shatun tayi duhu ka’dan ta kuma kumbura ka’dan. Sai da ta gaji da zirga-zirgar sannan ta zauna a hankali tana furta wash. Mommah ta jata jikinta tana matsa mata yatsun hannunta, murya a ‘kasa alamar ta marasa lafiya tace “Shatu haka kika canja? Mai Hajiya Mama take baki? Naga cikin yayi girma sosai kamar ya wuce watanninsa.” Murmushi Shatu tayi tana duban Hajiya Mama da take cewa “Yo wannan uban ci da Shatun taki take yi ai dole kiga Haka, ban da likita yace is better ayi mata aiki ai da ta gane kurenta wajen haihuwa yarinya kullum hannu a Kwano.” Basirah da take gefe ta tuntsire da dariya, Shatu ta hurgeta da pillow tana ‘dora kan ta a cinyar Mommah tace “Mommah kin ganta ko? Zata fara zolaya ta.” Mommah ta harari Basirah tace “Allah ya ha’daku zaku fara ko? To ki bari ta haihu sai ku cigaba don yanzu ba ita ka’dai bace.” Kamar ance Hajiya Mama ta ‘daga kanta ta hango Imran yana shigowa ta jikin t.v ‘din dake hasko camerar gidan. Da sauri tace Shatu ta shige ‘dakinta don basa son Imran ya ganta.

Ba’a fi mintuna biyar ba kuwa suka ji knocking ‘dinsa a bakin parlourn. Basirah ce ta bu’de masa ‘kofar, ‘kamshin turarensa tuni ta baza parlourn, jikinsa a sanyaye hannunsa janye da ‘Yar ‘karamar trolley da ba zata gaza ‘daukan kayan da suka fi 2set ba. idanunsa ya sauka cikin na Mommah, ya saki

1 Comments On ME ZANYI DA ITA
avatar
hafsat-bello

12 months ago

Reply

Complete

Please Login or Register in order to submit comment